Showing 66001 words to 69000 words out of 185502 words
tun farko ban b'oye ma Asas daga ina na fito ba, sannan danginshi ma sun san komai dan haka dole zasu ga mutane kala biyu, aunty Sahura, wallahi na rantse da Allah zan iya fasa auren nan idan aka ci min mutumcin yan uwa."
Mik'ewa tayi zata shiga d'aki tace "Kuma a turo min yan uwana, ina so na gansu kewaye dani suna kai da kawo a sabgar bikina, dan ni abun kunya ne ma gareni ace ba'a ga gajera ba a cikin yan mata, ni yar halak ce kuma ba butulu ba."
Da kallo kawai suka bita har ta shige d'akin, murmushi Sahura tayi tace "Mimi kenan, ita dai ba ruwanta da k'yamar mutane."
Tab'e baki mama tayi ba tace komai ba, haka suka ci gaba da tattaunawarsu kafin Sahura ta bar gidan.
Saida tayi sallah magriba ta shirya tare da Yaseen zasu tafi karb'an d'inki, a k'ofar fita suka had'e da Maimuna ta shigo gidan, gaisawa sukayi sosai kafin ta shiga ciki dan tunda aurenta ya matso take zuwa suna yan shawarwari da Mama, fita sukayi ita kuma a daidai k'ofar suka had'e da Asma'u, cak duk suka tsaya suna kallon juna, tunda abun nan ya faru ko sautin muryar juna basu ji ba bare ganin juna, cike da murna Mimi ta fashe da kuka ta ruga a guje ta fad'a jikin Asma'u, ita ma kukan ta saka tana k'ara rumgumeta.
Cike da k'aunar juna Mimi ke fad'in "Asma'u me yasa zaki bari su rabamu? Kinsan yanda nayi kewarki kuwa? Babu masifa babu fad'anki bare nusar dani daidai da ba daidai ba."
D'agowa tayi tana sake fad'in "Bikina sati d'aya ya rage, amma Asma'u ko ki lek'o ki ganni kin shareni kawai."
Cikin kuka ta shiga girgiza kai tana fad'in "Ba shareki nayi ba Mimi, Abbana ne ya hanani shiga gidanku, ya ce ko bisa hanya bai yarda na kulaki ba."
Jinjina kai tayi tace "Na sani Asma'u, dan nima na zo gidan ya hanani shiga na ganki."
Hannunta ta kamo jim ta jimk'e tana fad'in "Dan Allah Asma'u ki zo ayi hidimar bikina dake, idan baki zo ba ko an d'aura auren ba zan yarda a kaini gidan ba."
D'an murmushi tayi tace "Na miki alk'awari Mimi ko da satar hanya ne na zo gidanku."
Da sauri tace "A'a! Banda satar hanyar Asma'u, ba zan so ki jefa kanki a halin dana jefa kaina ba, a dalilin abubuwan dana aikata har yanzu gidanmu bana sakewa, iyayena sun daina sakin jikinsu dani kamar bak'i muke, duk yanda na motsa sai mama ta kalli kalar motsin da nayi, idan na sauke numfashi saita kula da wane iri ne na sauke, uwa uba ace na fita waje, tsaf take cajeni taga miye a jikina."
Wani murmushi mai kama da kuka tayi tace "Ranar ma tsaf tasa na kwab'e kayana ta dubani saboda kawai Asas ya zo da daddare munyi hira ya tafi."
Fashewa tayi da kuka mai cin rai, share mata hawayen Asma'u ta shiga yi tana fad'in "Kiyi hak'uri ki daina kuka dan Allah, komai zai wuce kinji daina kuka, kinga ynzu..."
Cak ta tsaya saboda jin Abbanta ya fito daga gida yana fad'in "Asma'u."
Da sauri suka kalleshi suna rarraba ido, a tsawace ya kauce daga bakin k'ofar yana fad'in "Maza shiga ciki, ban hanaki tsayawa da ita ba."
Da sauri Asma'u ta taka zata shiga Mimi ta rik'e hijabinta gam, takawa tayi saida taje gabanshi ta durk'usa, kamar zata rik'e k'afarshi tana kuka tace "Abba dan Allah na rok'eka ka taimaka ka bar Asma'u ta halarci bikina, Abba ban da wata k'awa sama da ita, ita ce aminiyata da ita nayi wasar k'asana, ita ce take da zarrar fad'a min gaskiya gaba da gaba ba tare da tsoro ko shakku ba, bani da wacce take so na sama da ita a duniyar nan a cikin mutanen da ba iyayena ba, dan Allah dan Annabi karka raba k'awance da ita dan ni ce mai k'aruwa da hakan, ita take d'orani a hanya take nuna min b芒 daidai ba. Wallahi ban tab'a k'ok'arin kama hannun Asma'u ba na kaita a hanyar da zata halaka ba, na maka alk'awari Abba Asma'u zata ci gaba da zama a kamilalliyarta har ka damk'ata a hannun mijin daya dace."
Shiru tayi tana ci gaba da kuka ba tare data saki hijabin Asma'u ba, tabbas jikinsa yayi sanyi da abinda ta fad'a, hakan yasa ka shi jinjina kai yace "Shikenan tashi daina kukan?"
Girgiza kai tayi tace "Ba zan tashi ba Abba har sai ka hak'ura."
A hankali yace "Na hak'ura mana, tashi tsaye."
Mik'ewa tayi tana kallonshi, d'orawa yayi da "Na amince ku ci gaba da shagulgulanku, amma ki cika min alkkawarin da kika d'auka, bana so wani abu marar kyau ya faru daku kinji."
Jinjina kai tayi tace "Insha'Allah Abba, nagode sosai."
Murmushi yayi yace "Ba komai, Allah ya muku albarka."
Da Murmushi ita ma tace "Ameen Abba." Sakin Hijabin Asma'u tayi ta juya tana fad'in "Sai gobe, karb'o d'inki zamu je."
Abban Asma'u ne yace "To ku tafi tare mana, ba ita ce babbar k'awa ba?"
Wata dariyar data jima batayi bane ta kubce mata tace "Ita ce Abba, ita ce."
Da zumud'i ta sake kama hannun Asma'u ita ma Asma'u tayi ram da hijabin Mimi suka shiga takawa da k'arfinsu kamar zasiyi gudu, a baya Yaseen ya bisu shi ma yana murmushin jin dad'in ganinsu tare.
*Da safe* tana farkawa bakinta kawai ta wanke mama ta mik'a mata dahuwar tamtabarun data mata tun asuba, karb'a tayi ba musu dan duk wani abu da mama ke bata ko ci bata cewa, saidai ta mik'a mata kawai ita tasan yanda zatayi tasha ko ta ci, yanzun ma ba dan tana so ba take ci duk da dahuwar tayi, amma ba wasu isashin kaya aka saka ba, tana ci tana b'ata rai kamar za tayi amai. Tana ji su Zeinaba sukayi sallama, murmushi ta saki na jin yan uwanta sun zo inda take, tanna jin su suna gaisawa da Mama kafin tace "Ku wuce ciki ku aje kayanku."
Da fara'a suka wuce suna sake sallama, amsawa tayi da farin ciki tana fad'in "Marasa mutumci kenan an taho?"
Dariya duk sukayi suna aje kayan hannunsu, Zeinaba irin gajerun nan ne sun fi wada tsayi kuma basu da tsayi sosai (ba wada haushi), Rauda ma bata da laifi amma Zeinaba ta fita tsayi, gaisawa suka dinga yi sosai har Mimi na fadin "Yanzu da ban nemeku ba kenan ba zaku zo ba?"
Dariya sukayi Zeinaba tace "Kin san me? Ni bana jin dad'in shiga cikin dogaye ne, sai na sak茅 zama 'yar duk'ul dani."
Wani wawan tsaki taja tace "Dallah ni karku b'ata min rai, wai me yasa kuke hakane?"
K'yaci tayi tare da ci gaba da abinda take, sama sama suka dinga hira har ta sake saukowa suka ci gaba da hira, suna haka Asma'u ma ta shigo, gaisawa sukayi kafin Asma'u tace "Kinga ba zama zanyi ba, siyan ankona zan tafi yanzu saina dawo."
Kallon Zeinaba tayi dake sun san juna tace "Zeinaba muje ki rakani mana."
Mik'ewa tayi tana fad'in "Nawa zaki biya to?"
Dariya tayi tace "Karki damu, muje zan biya."
Mimi ce ta kalli Asma'u tace "Asma'u dan Allah karb'i kud'i wajen Mama ki siyo min madara peak."
Kallonta tayi tace "Me zakiyi da ita?"
Kashe mata ido tayi tace "Ina ruwanki? Sirri ne."
Dariya duk sukayi Asma'u tace "Wato kin raina gyaran Mama ko?"
Murmushi tayi tace "Ni na fad'a miki haka? Kawai ina buk'atarta ne dan nasha."
Girgiza kai Asma'u tayi tare da ficewa a d'akin ita da Zeinaba, tana jin sautin Asma'u sanda take tambayar Mama kud'in, da fari ta shiga zulumi na tunanin ba zata bayar b芒, amma da taji ta bata saita saki murmushi.
*Masu comment nagode, wanda basa comment ma godiya nake*馃榿馃
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:55 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*23*
Sosai suke shan hirarsu ita da Rauda suna raharsu, Mama saidai ta shigo tayi wani abun ta fita tana jinsu, 09:05 Hafsat ta zo gidan tare da rakiyar Salamatu, yanda ta shigo da nutsuwa da sallama ya saka mama d'aga kai tana amsawa, masha'Allah ta fad'a a ranta saboda ganin Hafsat d'in, indai had'uwa, kyau, aji, kamala ake nema a gurin mace tabbas alamun Hafsat sun nuna mata hakan, gata jajir da ita gwanin sha'wa ta fito a bafulatanarta sak, ga bak'in hijab kuma dogon daya fito da doguwar fuskarta har k'asa.
Mik'ewa Mama tayi tana fad'in "Lale maraba, sannunku da zuwa."
Da fara'a da girmamawa tace "Yawwa sannu Mama."
Da fara'a ita ma tace "Sannu, ina wuni?"
"Ina wuni?" Ta fad'a a matuk'ar tausashe, saida mama ta d'auko kujera ta aje tace "Lafiya lau, anwuni lafiya?"
A ladabce ta zauna tana sauke numfashi kafin tayi murmushi ta sake gaisheta da mutumtawa, ruwa ta kawo ta aje musu Hafsat kam saida tasha dan kar Mama ta ji ba dad'i duk da bata da k'ishin ruwa, shiru ne ya d'an biyo baya kafin Hafsat tace "Mama baki ganeni ba ko?"
Da fara'a tace "Gaskiya kam ban shaidaku ba? Dan na fara tunanin ko b'atan kai kukayi."
Dariya Hafsat tayi ta kalli Salamatu dake k'arewa gidan kallon tsaf har zuciyarta take jin haushin wannan zab'i na mai gjdan nata Asas, sam abun bai mata ba sai take ganin kamar wannan shi ne *kaska* rab'i mai jini, matsayinshi da dukiyarshi yafi k'arfin a ce yarinyar da zai aura kenan. D'an gyaran murya Hafsat tayi hakan yasa ta maido hankalinta gareta, da ido ta mata alama hakan yasa Salamatu aje ledojin hannunta gaban Mama tana fad'in "Wannan ai ita ce yayar Alhaji Asas, uwa d'aya uba d'aya suke."
Da fad'ad'a fara'a sosai mama tace "Masha'Allah, ko ita ce Hafsat d'in da nake ji?"
Da murmushi Hafsat tace "Ni ce mama."
"Abu yayi kyau kam, ya su Hajiar suna lafiya?" Ta fad'a cike da kulawa, amsa mata sukayi kafin Hafsat tace "Mama dama sak'o na zo kawowa amarya, nasan kunsan babu wani shagali da za'ayi a bikin kamar yanda addini ya tsara, amma daga baya sai muka yi shawara duba da yanayin zamani da kuma ita kanta amaryar, shi ne ango yace za'ayi kamu kawai na amarya, amma fa shi ma ita da k'awayenta ban da shi da abokanshi, haka kuma kowa a dangi ma ga mai buk'ata zai iya halarta."
Shiru mama tayi tana saurarenta tana jinjina kai, saida ta kammala kafin tace "Wannan ai ba wata matsala bace, duba da kwana nawa ya rage Mimi ta shiga a k'ark'ashin ikonku? Ko yanzu kaso mafi girma yana hannunku ai, dan haka ba wata matsala wallahi, saidai idan mahaifinta ya dawo shi ma zan sanar dashi dan yasan abinda ake ciki."
Cike da gamsuwa da maganganun Mama Hafsat tace "Masha'Allah, mun gode sosai Mama, wannan ba matsala bane dama."
Ledar da Salamatu ta aje gaban mama ta nuna mata tace "Wannan kayan da amarya zata saka ne ango ya turo m没 dasu, insha'Allah ranar alhamis za'ayi kamun washe gari kuma d'aurin aurensu a babban masallacin juma'a."
Cike da jin dad'i mama ta jinjina kai tace "Hakane, Allah ya nuna mana ya kai mu lokacin da alkairi."
Cikin dariya Hafsat tace "Ina amaryar ne wai mama? Ko bata nan?"
Cike da kunya mama tace "Tana ciki kam, ai kusan wata d'aya ma kenan ta daina fita, shiga ciki tana nan."
Mik'ewa Hafsat tayi tana fad'in "Lallai mama kina kula mana da amaryarmu, Allah ya biyaki da aljanna, wannan sai mun bayar da tukuici ai."
Dariya mama tayi tana amsa addu'arta a zuciya tana kallo har ta shiga d'aki, Salamatu kuma na zaune tana ta yatsina fuska tana wa mama wani gani-gani, mama kam har ga Allah bata ma kula ba bare ta sa wani abu a ranta taji ba dad'i ko kuma tunani.
Mimi kam da suka kasa kunne tunda taji wacece ta d'auko hijabi ta labta ta haye gado tayi shiru, tana shigowa da sallama suka amsa mata da fara'a Mimi kuma na sinne kai k'asa, zaune tayi kusanta tana fad'in "Amaryarmu sannu? Ya hidima?"
Da d'an murmushin jin kunya tace "Alhamdulillah."
"Masha'Allah, yanzu ma na kawo kayanki ne na kamu ranar alhamis insha'Allah." Ta fad'a tana kallonta, k'ala ba tace ba sai ma sunkuyar da kai k'asa, cikin kulawa Hafsat ta sake fad'in "Gashi dai har kin kusa shigowa hannunmu baki sake zuwa gidana ba, na so ya kaiki ki wuni amma Allah bai nufa ba, dan zuwanki na ranar naga kuna sauri."
Murmushi ta sake yi tace "Zan je." Dariya Hafsat tayi tace "Yaushe kuma amayar? Kwana biyu ana uku fa zaki shiga lalle, ai k'anena ba zai yarda ki fita ko ina ba."
Cike da kunya ta sake sinne kai tace "Zan je insha'Allah."
Dariya ta sake yi tace "Na yarda zaki je, amma fa bayan aure."
Murmushi tayi sosai tana rufe fuska da hijabi, cike da jin dad'in ganin Mimi ta mik'e tana bud'e jakarta, enveloppe ta fito da ita ta aje kusa da Mimi tace "Wannan angonki ne yace na baki saboda ranar kamu zasu miki anfani."
Juyawa tayi bata jira me zata ce ba ta fita tana fad'in "Sai anjima amaryarmu, sai ranar kamu insha'Allah."
Da kallo Mimi ta bita kafin tayi saurin kallon enveloppe d'in, zaro ido tayi ta kalli Rauda dake ta murmushi tana saurarensu tace "Rauda na shiga uku, ta bani abu ta juya ta fita, ya zanyi da mama?"
Jin su Hafsat na fita a gidan suna ban kwana yasa ta d'aukar enveloppe d'in tana fad'in "Shi ma fa na fad'a masa bana buk'atar komai daga gareshi, me yasa zai min..."
Bata kai k'arshe ba mama ta d'aga labule ta d'auko kayan da aka kawo mata, cikin rashin gaskiya da tsarguwa da kuma sabawa da sabon halin Mama na cajeta yasa ta saurin sakin enveloppe d'in ta durk'ushe tare da fad'in "Na rantse da Allah mama bansan menene a ciki ba, ita kawai ta d'auka ta bani ban tambaya ba, kuma ga Rauda ki tambayeta zata fad'a miki."
Girgiza kai Mama tayi ta zuro k'afarta d'aya ta aje ledar tace "Miye anfanin rashin gaskiya yanzu? Gashi abinda bai kai ya kawo ba ya firgita miki nutsuwarki, me yasa mimi kika dinga yi mana k'arya? Da kina ganin yanzu haka ta faru?"
Girgiza kai tayi ta juya tana fad'in "Ko me suka baki a yanzu indai ba rok'onsu kikayi ba su suka ji suka gani zasu iya."
Tana ganin ficewar Mama ta share yar guntuwar k'wallarta ta d'auki enveloppe d'in ta zauna bakin gado ta bud'e, wani irin fad'uwa gabanta yayi sakamakon ganin kud'i ne sababi far dasu yan jaka jaka, mayarwa tayi ta aje ta kalli Rauda tana fad'in "Nufinshi nayi lik'i da kud'in nan?"
Wani murmushi tayi kawai ta girgiza kanta ta gyara kwanciyarta akan gadon ta shiga neman bacci.
*05:30*
Su Salma na fita a gidan sakamakon k'aratowar magriba yasa ta d'aukar madararta a kofi data b'oye k'ark'ashin gado had'e da yar zuma a ciki da karanfani da dabino data saka Asma'u mata a gida ta kawo mata, da sauri ta kifa kai ta shanye abinta, dan a gaskiya ranar taji su Sahura na fad'in har yanzu fa maganin zahi da kuma na sanyi (infection) ne aka mata, sai shi dai na zafi yanzu haka idan tasha tana jin yana saukar mata da d'umi a jikinta har ya saka ta kama ruwa. Yanzu ma da su Zeinaba zasu fita maltina ta basu su siyo mata amma tace su b'oye kar Mama ta gani (ba'a daddara ba kenan uwata?馃槬).
Asma'u na shigowa da sauri taa fad'a d'akin hankali tashe, cikin rad'a ta shiga fad'awa Mimi "Ke yanzu na ga Muttak'a a k'ofar gidan nan, ya ce wai na kiraki na fad'a masa an hanaki fita saboda aurenki ya matso, ke kinga tashin hankalin?"
Gyara zama tayi tace "Wallahi rantsuwa ya mana wai ba zaki auri wani ba shi ba, tunda har kika wulak'antashi kika yaudareshi to zaki gani."
"Zan ga alheri." Ta fad'a tana mik'ewa dan shiga wanka, cikin nuna damuwa Asma'u ta mik'e ita ma tace "Mimi bana son matsala fa, mutumin nan tunda ba hankaline dashi ba me zai hana ba zaki fad'awa Asas ba? Watak'ila ya mana maganinshi."
Kallonta tayi tace "Na ce masa me? Saurayi na ne dana ci kud'insa kamar hauka shine ya ke min barazana kayi wani abu a kai?"
Tab'e baki tayi ta d'auki hijabi zata saka ta fita Asma'u tace "To ya kike so a yai? A barshi har sai wani abu ya faru marar kyau? Sannan mu sake shiga damuwa da tashin hankali."
Dafa kafad'arta tayi tace "Ba abinda zai faru Asma'u, kwantar da hankalinki."
Ture hannunta tayi tace "Kwantar da hankalin banza, wai me yasa kika cika taurin kai ne Mimi? Haka a baya kike fad'a min kwantar da hankali babu abinda zai faru, da nayi shiru kamar yanda kike buk'ata miye bai faru ba?"
Tsaki tayi tace "Kinga idan wani abu ya faru wallahi babu ruwana ni dai, na fad'a miki d'an giyane mutumin nan kuma yana mana rantse rantse da cin alhwashi."
Gyara tsayuwa tayi tace "D'an giya miye baya fad'a? Rantsuwa ko ruwa zai sha sai yayi rantsuwa da alhwashin shan su alhalin gasu sa gabanshi, dan haka ba zan saka matsalarshi a kai na ba."
Jinjina kai Asma'u tayi cike da jin haushi ta fita tana fad'in "Ke kika sani ai."
Ganin yanda ta fita ya tabbatar mata sunyi fad'a kenan ba zasu shirya ba sai kuma gobe, girgiza kai tayi tana murmushi a ranta take ayyana irin k'aunar da Asma'u ke mata, indai zasuyi fad'a to akan wani abu da Mimi tayi ba daidai bane musamman mai barazanar cutar da ita game da lafiyarta ko kuma zai shafi mutumcinta.