Showing 99001 words to 102000 words out of 185502 words

Chapter 34 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

520

juyi da shi kamar biri da abokin wasansa.

Murmushi ya kuma yi ya juya ya nufi ciki ta d'ayan b'angaren ba tare daya ce komai ba, daga Hajia har Salamatu sun jinjina lamarin Mimi, Hajia na janye da hannunta har suka koma cikin d'akin sannan ta saketa ta nufi d'aki abin ta.

Tana shiga ta kwanta tana lumshe idonta, k'amshin turaran Dadyn nan na mata dad'i a hancinta bata san dalili ba, ga wani tattausan hannunshi daya rufe mata baki dashi, yanda ya matsa a jikinta sosai sai abun ya nemi tsaya mata a kai da zuciya.

Idonta ta sake lumshewa ta kuma bud'ewa tana tab'e bakinta ta shiga kiran lamber Abbanta.
Tana fara ringin ya d'aga, amma daga nesa nesa take jin maganarsa yana fad'in "Kina gani kuwa wata lamba ce ban santa ba, kin san masu shan jinin nan fa an ce da gaske ne?"

Yar dariyar mamanta ta ji tana fad'in "To kayi sallama mana malam ka ga fa kud'in mutumen na tafiya."

Dariya tayi a bayyane ta furta "Abba ni ce fa."

Dai-dai ya matso wayar ya ji muryarta a sanyaye tana kuma dariya tana kiran sunansa hakan ya saka shi fad'in "Uwata ce?"

Wata yar dariyar tayi tace "Ni ce nan Abba."

Shi ma dariyar yayi sai kuma da sauri ya gimtse yana fad'in "Ke wa ya baki waya?"

Bakinta ta turo a sanyaye tace "Shi mana."

Mamanta dake sauraro tace "shi wa?"

Bakin ta kuma turowa tace "Shi akaramakalahun mana."

Mama bata san lokacin da murmushi ya k'wace mata ba tana girgiza kai tana jin Abban na amsa gaisuwarta ta mik'e ta shiga kakkauda kayayyakin dake ajiye hankali kwance.

Cikin sangarta tace "Abba yaushe zaku zo? Dan Allah idan ma ba zaku zo ba ku turo min su Yaseen mana."

Abba yayi murmushi yana girmama rashin hankalin mamansa, su su zo? Ko a turo mata Yaseen? Sanin da yayi ita d'in ba 'yar a kwatantawa a laluma bace sai kawai ya datse kiran yana d'an murmushi, ko ba komai muryarta ta saka shi farin ciki, a bayyane yake yi mata addu'ar samun nutsuwa.


Hajia na zaune saman kujera, sheikh na zaune saman kafet ya tank'washe k'afafunsa bayan sun k'ara gaisawa da kyau har an kawo masa ruwa ya d'an sha, da yanayin da take ciki ta dube shi a sanyaye tace "Sheikh, na rasa ina autana ya shiga, ka ga tunda aka yi abun nan ban ganshi ba ba shi ba labarin iyalinsa, idan na kira baya d'agawa, tun abun baya damuna har ya fara damuna, ka ga magungunansa duka a nan bayan nan ka sanshi da wasa da cikinsa, shin laifi nayi mai girman da ya saka yayi fushi har haka dani?"

Sheikh da yake saurarenta ya kawar da kansa gefe guda yana d'an nazari kafin ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye yace "Ki yafe masa, sannan gobe insha'Allah zai zo ya gaishe ki, kar ki saka damuwa a ranki na tabbata da yana cikin matsala daya nemi uwa, kiyi masa addu'a sannan ki masa nasiha, idan ya zo ki saurareshi ki rarasheshi."

Hajia na gyad'a kanta tana jin girma da soyayyar Sheikh kamar na wanda ta haifa a cikinta, a gaskiya shekarunsa basu kai irin girman da duniya ke bashi ba, amma da yake tun bai kai haka ba yake da halayya na dattako, girma da darajar Alk'ur'ani dake kansa ya k'ara masa kima da darajar da ko mutum ya tsofe shi sai ka ga yana neman zubewa ya gaishe shi sai idan shi yayi gaggawar tarewa domin kuwa arzikinsa da baiwar da Allah ya bashi bai saka shi barin kansa ganin manya na gaishe shi a tsugune ba.

Da haka yayi masu sallama ya fita domin yana da wajen zuwa har uku, ga kuma na hud'u ya k'aru dan kuwa zai je ya same shi a wajen daya tabbata baya wuce nan.

Saida ya je yayi yawace yawacensa, duka wajen da yake da na zuwa ya je ya gabatar da ayyukansa a tsanake kafin ya nufi wajen da ya tabbata Asharf na cen.

Kusa da masallacin kadafi ne wajen da yake zama tare da abokansa, motocin sheikh na tsayawa samarin uku dake zaune suka mik'e duk suka yo wajen motar ciki har da Ashraf da sai da gabansa ya fad'i amma haka ya dake yana murmushi a lokacin da d'aya daga cikin mai kare lafiyar sheikh ya bud'e samarin duk suka duk'a suna mik'a hannayensu suna mik'a gaisuwarsu.

Cike da kamala da daraja d'an adam yake amsa masu d'aya bayan d'aya har suka gama gaisawa kafin ya juya cikin halin kyauta irin nasa ya d'auko enveloppe ya mik'a masu kamar yanda ya saba indai zai tsaya sai ya basu duk da duk cikinsu ba zauna gari banza, amma a matsayinsa na yayansu kuma uba a wajensu sannan mai kyauta yakan yi hakan wanda hakan ke saka su nishad'i da farin ciki, su kansu suna koyan halayya irin nasa domin suma suna yiwa gajiyayyu da k'annensu bare kuma iyayensu.

Ashraf na masu sallama ya shiga motar ya zauna aka rufe suka d'auki hanya, shiru ba wanda yayi magana har suka iso k'ofar gidan Ashraf, kuma ba waya suke daddanawa ba hasalima cikin motar ba hayaniyar komai sai shirun da yayi yawa.

Muryarsa na rawa rawa yace "Dan Allah kayi hak'uri." Dan yau sheikh d'in tsoro ya bashi tare da jin shakkarshi da kwarjininshi ta yanda yake jin ba zai iya masa wasa ba yau.

Sheikh kam d'an juyar da kansa gefe yayi ya kuma juyowa a hankali ya dube shi har ya d'an fad'a kad'an, a hankali ya cire dubansa yana jin zuciyarsa na tsintsinkewa, abinda yake son fad'a shi ne "Kai Ashraf shin dan na auri Ryam ne kake irin haka? Shin matata na zuciyarka ne ko me? Shin baka cire min iyali a ranka ba ko me? Kai marar kunya halan baka d'auki k'addarar aurenka ba? Shin ka isa ka auri matar wani ne?" Sannan ya d'an wanwanka masa marin da zai farkar da shi, sai dai kasantuwarsa da wanda yake a wajensa ya saka shi kawar da kansa a sanyaye yace "Gobe da safe wajen 11:00 ka zo gidan Hajia da iyalinka, insha'Allah zanyi jiranka a cen."

Daga haka ya d'auke kansa a duban Ashraf wanda ya gyad'a kansa yana k'ara sadda kan nasa ya bud'e ya fita yana mai yi masa saida safe.

Daga nan gidansa ya k'arasa, sai dai bai shiga ba sai da ya gabatar da wasu karatuttuna a masallaci sannan ya nufi cikin gidansa.

K'arfe 10:30 ce, hakan ya sa ya samu yaransa duk sun yi bacci, Hafsat kuwa na saman kujera ta mik'e k'afafunta a sama tana jan carbi idaonta lumshe. Sanyi yaji a zuciyarsa a lokacin da yayi arba da fuskarta, sanyin idaniyarsa ce ita, sanyin zuciyarsa ita d'in, kwanciyar hankalinsa ce ita wacce ta amsa sunan *mar'atus-saliha*.

Duk'awar da yayi a gabanta ya sakata bud'a idonta masu cike da bcaci tana kallonsa, murmushi ta sakar masa hakan ya saka shi lumshe idonsa a hankali ya d'ora hannunsa saman cikinta yana kallon fuskarta yace "Shin ajiyar *Abdallah* na ci gaba da wahalar da Nurul ayni ne?"

Murmushi tayi masa a hankali tana d'an girgiza kanta, domin yanzun da sauki bata jin curewar nan saidai mugun baccin da take yawan yi ta kamo hannunsa tana dubansa tace "Ai komai nauyin kayan jagorana zan iya rik'ewa da hannu bibbiyu abu na."

Murmushi yayi yana mik'ewa a hankali ya kamata ya mik'ar da ita ya nufi d'akinsa da ita domin ya san cewa ta gama da yaren ta gama da b'angarensu shi kuwa tuni ya rufe daya shigo.

Saman lallausan gadon ya shinfid'eta ya d'an rank'wafa a hankali ya kama leb'enta na k'asa ya bata kyakyawan sumba mai sanyi, a hankali ya shiga tofa mata addu'a yana shafa gashinta kafin yace "Allah yayi maki albarka, Allah ya tashe ki lafiya cikin hayyacinki, Allah ya yafe maki kurarenki wad'anda kika sani da wad'anda baki sani ba, Ina son ki Manga na."

A gaskiya ba zata iya kwatanta irin farin cikin da mijinta ke sakata ba, gata dai aure ne na had'i amma tunda ya fuskanceta suke zama irin na fuskantar juna, kowa na yin kaffa-kaffa da lamarin d'an uwansa, har zuwa yanzu da auren wata ya kuma hawa kansa bai saka rud'u da rawar kai irin na yawancin mazan da zasu d'auko yarinya ke shiga ya ringa nuna mata wasu abubuwan ba, yana bata lokacinta da kuma isashen darajarta, tana jin kanta tamkar ita d'aya ce tak a duniyarsa kuma tana jin dad'in hakan, ita kam ta yaba kuma tana k'ara yaba auren YA SHEIKH.

Tun yana nan bacci ya kwasheta, a hankali ya nufi bayi dan yin wanka da alwala domin yana son kwantawa da wurin shi ma yau dan tashin tsakiyar dare yin nafilfili cikin nutsuwa.


*Washe gari*


A yau shigar sheikh ta gama tafiya da nutsuwarta, tsaye take gabansa ta d'an taka pillow d'in daya ajiye mata tana rik'e da hiraminsa ta k'ara d'an yin d'add'age ta d'ora masa a saman kansa shi kuwa yana tallabe da bayanta sanan ta tsaya tana kallon fuskarsa, zata iya rantsewa wannan dan tsili tsilin farin gashin dake gemunsa k'ara masa kyau yayi ko na mutum da masoyi ne? A hankali ta d'ora hannunta saman faffad'en k'irjinsa da kuma shafafen cikinsa , idonnta ta lumshe muryarta cen ciki tace "Kishin mijina nake, shin idan ya fita a haka ya ya yan mata zasu yi da begensa? Kayi kyau har ka gaji ya habibi."

Murmushi yayi cikin nutsuwa yana k'ara tareta a jikinsa yace "Ke kike ganin haka ya Mar'atusaliha, kyau kuma ai an barshi tun k'ananun shekaru, ki kular min da kanki kafin na dawo, ban yarda ki yi aikin da zai wahalar min dake ba."

Murmushi ta masa tana manna masa sumba a kumatunsa shi kuwa bai saketa ba sai da ya sauketa daga saman pillown sannan ya d'aga mata hannu ya juya ya nufi waje cikin sasaukar shiga irin ta larabawa domin doguwar riga ce ta jalabiya da dogon wandonta sai hiramin da ya d'ora, kayan sababi ne sannan manyan kaya ne masu tsadar gaske da daraja gashi sun amshi jikinsa sosai.

A lokacin daya zo dan shiga falon Hajia ya samu takalma a k'ofa na mata hakan ya saka shi juyawa cikin nutsuwa ya koma cen wajen motocin gidan ya ajiye kujera ya zauna yana rik'e da wayarsa Android da d'an tissu ya shiga danna wayar dan yana son kiran Hajiar ya ji idan bak'in na gida ne ya shiga domin yanzun goma ce har da rabi duk inda Ashraf yake ya tabbata yana hanya.

Yar hayaniyar da ya jiyo ce ta saka shi d'an duba gefen da yake zaune.

Su Salma ne su uku sai Mimi ta hud'unsu sun fito sun nufo hanyar tsakiyar gidan wace take d'an kusa da motocin gidan suka ja suka tsaya.

Idonsa ya so cirewa yana dan tab'e bakinsa saidai me? Da sauri ya maida kanta sakamakon ganin ba ko hula a saman kanta bare d'an kwali ko hijabi.


Dariyar da Mimi tayi ne ya saka shi zuba mata ido ta dafa gefen kafad'ar k'awarta tace " Na dai ji, kina ta maganar na isheku tsoho tsoho gani daram a matsayin matar tsohon na ji, aman ai ko ya ya dai Old man ya fi mijinki wallahi tunda shi ban ga tumbi a tare da shi ba!"

Salma ce ta zaro ido tace "Shegiya! kar dai ki ce min har kin gano girman oga? Wayo duniya wayo aure mai daraja yanzun Mimi ke din na da nake gani a b'agas har kin je cen da Haj man ya sheik?"

Mimi ta yatsina bakinta tace "Kunga ni fa irin wannan zancen naku ke had'ani daku, shikenan ba damar a had'u da ku sai ana kauce layi? To bama wannan ba ke yanzu wannan kayan nawa ai kin san mai iya jansu sai d'anye sabon jini ...." Ta fad'a tana mai d'an juyawa a gabansu ta d'an juya mazaunanta

A hankali ya lumshe idonsa yana furta " A'uzubillahi mina-shaid'anin rajim! subhanallah, subhanallah, subhanallah, hasbunallahu wa'imal wakil, Innalilahi wa'inna ilaihi raju'ne!"

A hankali ya ringa jin ransa na biya tayin neman rigimar yarinyar cen, wai yanzun shine old man kuma bata jin kunyar fad'a a gaban kowa? Uwa uba yanzun su yaren nan ina iyayensu da suka fito da sassafe suke son fitar da matar mutane har suke maganganu na rashin d'a'a haka? Shin wai yaya aka yi tarbiyar 'ya'yanmu ta lalace? Wai Ryam ita ce da cewa shi ba zai iya juya wannan abin dake jikinta ba?

Wani d'an murmushi mai ciwo yayi yana datse leb'ensa na k'asa, idonsa da suka yi ja suka kad'a ya kuma d'orawa a kan k'ugunta, lallai sai ya nunawa yarinyar cen meye namiji, meye mai sunan namiji, sai ya banbance mata k'arfin namiji ba a shekarunsa yake ba, sai ya danna mata abinda zata ji har mak'ogwaronta, sai ya jijiga rayuwarta da hajijiya ya timata a k'asa ta yanda ko an ce ga namiji gabanta zai fad'i! Da haushi haushi ya kalli yanayinsa yana mai jan tsaki a bayyane yayi gagawar d'ora k'afa d'aya kan d'aya ya matse k'afafunsa sannan ya dafe gaban goshinsa da hannunsa mai d'auke da agogon azurfa.

Ruky ce tace "Kun ga ku wuce mu tafi dan Allah, shiyasa ban so muka biyo ba yau wallahi, zama na musamman nake so muyi dake ai."

Salma ce tace "To wai yaya ke ma zaki koma makarantar?"

Cike da tabbaci tace "Me zai hanani kuwa, ku zuba ido ku gani."

A haka suka ringa yar hirarsu ta k'awaye suna shan dariyarsu kafin suyi gaba tana nan tsaye da rigar dake jikinta doguwa kalar bleu, rigar sosai take rawa a jikinta koda bata da abin kad'awa bare tana da su.

Mik'ewar mai gadi ya nuna alamun zai bud'e k'ofa ya saka sheikh saurin mik'ewa tsaye daga zaunen da yake.

Da sauri ya kuma kallonta ganin tsaye take ta zubawa motar dake danno hancinta cikin gidan ya saka shi d'aga k'afarsa da saurin da bai tab'a tunanin yana da shi ba sakamakon irin yadda zuciyarsa ke bugawa ya ware yan yatsunsa da kyau ta yadda zata shiga juwa idan ya isar mata da sak'on da yake son isar mata wanda ya tabbata duk dukan da Abanta zai mata da muciya bai tab'a shigarta haka ba ya nufeta gadan gadan idonsa har rufewa suke da tsabar kishi da tsoron kar Ashraf ya tarda ita da wannan shigar.

Bata ankara ba, bata lura ba kamar yanda bata san dashi ba, hannunta kawai taji an figa da wani irinu k'arfi dake nuna wanda ya mata rik'on a hassale yake, da sauri ya shiga janta zuwa falon ita kam kamar zata kifa a k'asa, Hajia da fitowarta kenan tun da Mimi tayi bak'i ta shiga d'aki ta gansu tare, saidai yanda fuskar sheikh ke d'auke da mafificin b'acin rai sai kawai ta shiga furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!"

Fatanta d'aya kar sheikh yayi abinda za'a bugashi a jarida, mutum ne da ba zaka ce ga abokin fad'ansa ba, amma dai bai iya hushi ba ko kad'an.

D'akinta ya wuce da ita tare da wurgata ta fad'i k'asa, k'ara ta saki da k'arfinta ta furta "Ahhhhhh...."

Tsaf ta had'iyeta sakamkon fizgo damtsenta da yayi ya mik'ar da ita da k'arfi, bata gama gane ko da fuskarsa ba kawai ya damk'i damatsanta ya shiga jijjigata kamar b'era a cikin kwano cikin wata irin muryar ban tsoro yake fad'in "Ke wai har yaushe kikayi girman da maganganu irin wannan zasu riga fita a bakinki? Ni ne kike wa duk abinda kika ga dama Ryam? To ki sani na karb'i wannan tayin rashin mutumcin na ki, wallahi ba dan tsoron Allah ba da inna kirta miki wata buru'ubar ke sai kin d'auka ko ni kad'ai ne d'an iska a duk fad'in niger, amma a haka ma zan miki daidai da kalar naki rashin mutumcin, ni zaki dinga kallo kina kirana da sunayen da kika ga dama har a gaban k'awayenki, ke duk duniya babu wanda ya tab'a kwatanta yi min abinda kike min a yanzu, wallahi idan kika ci gaba ba zakiyi sati a gidan nan ba gabana zan mayar dake dan na kula k'arancin sani ke damunki."

Tureta yayi hakan yasa tayi tangal tangal zata fad'i dan sosai ya wujijjigata, hanayyenshi ya zagaya ta k'ugunta ya jawota da k'arfi, take ta fad'a kanshi tana zaro idonta tana kallonshi a matuk'ar tsorace dashi, bai tsaya jiran komai ba y'a damk'i d'uwawunta da hannayenshi yana matsawa yana fad'in "Wai har wannan kike juyawa kina fad'in ni ba zan iya jansu ba, na tabbata dan Allah ya tsara kowace halitta da mazaunai shiyasa ke ma kika mallakesu, amma ba dan haka ba ke ina abinda zai isheni a nan bare har ya d'aga min hankali na."

Ba tare da tunanin komai ba ya kama hannayen rigarta yayi k'asa da su hakan hakan yasa nonowanta dake hulu-hulu farare tas dasu suka bayyana dan ita fa zuwan su Salma ne suka tasheta daga bacci, ba tayi wanka ba barre ta saka bras. Sheikh da yana zage rigar yace "Har wannan b'erayen..."

Cak ya dakata dan ganin abinda ke neman fin k'arfinshi, bai tab'a hasashen zata kai haka ba sabida yanayin shekarunta da fuskarta, tabbas ko hannu zaisa ya damk'a zasu cika girman tafin hannunshi, hakaan ya haddasa mishi wani mugun jiri ya nemi kayar da shi, da sauri ya tureta a jikinshi ya juya baya yana rufe ido tare da furta "Ya Hayyu ya Qayyum."

Mimi kam a gigice ta juya da gudu ta shige ban d'aki ta rufe k'ofar ta jingina, sulalewa tayi ta sako da wasu hawaye masu zafin gaske, a rayuwarta bayan mamanta ba wanda ya tab'a kwatanta tab'a inda mutumin nan yau ya tab'a, a hankali ta saki wani kuka mai tsuma zuciya tare da gyara rigarta, wani irin bugu zuciyarta ke yi kamar zata fito daga k'irjinta.

K'wank'wasa k'ofar da Hajia tayi ya dawo dashi hayyacinshi, a hankali kuma a nauyaye ya shiga taka k'afafunshi da k'yar ya k'arasa fita, tsaye take bakin k'ofar duk a tsure take da tunanin abinda zai faru, cikin girmamawa tace "Ashraf ne suka k'araso."

A hankali ya lumshe ido alamar to, takawa ya fara yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login