Showing 153001 words to 156000 words out of 185502 words

Chapter 52 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

495

hanyar zuwa gidansu Iya Delu, haka ta dinga kakkare fuskarta dan bata so yan unguwar su ganeta musamman da take d'auke da akwati shak'e da kaya.

Tana zuwa gidan malam na cin tuwo Iya na gefenshi suna hirarsu a nutse, ko sallama ba tyi ba ta k'arasa cikin shagwab'a tana saki akwatin ta fad'i ta cire hijabi ta zauna tsakiyarsu, mamakinta na neman kashesu da k'yar Iya ta kalleta galala tace "Ke kuma fa daga ina?"

D'ora kan ta tayi a gwiwar Iya ta shiga rera kuka a sanyaye tana fad'in "Kakani na bani da g芒ta a duniyar nan, kasheni zasuyi da bak'in cikinsu da bautarsu, dan Allah ku zame min gata kunji."

Cire hannu malam yayi a tuwo ya kalleta ya dafa kafad'arta yace "Ta gaban goshina, waye ya tab'a min ke?"

D'agowa tayi ta kalleshi cikin Luka tace "Malam na gaji da zaman gidan sheikh, dan Allah ku barni na zauna anan na huta, na je can Abba bai ma saurareni ba ya koroni da takalmi."

D'ora kanta tayi shi ma a kafad'arshi tare da rik'e damtsenshi gam, cikin tausayawa da nutsuwa yace "Me ya faru amaryata?"

Ba tare data d'aga kan ta ba ta shiga labarta masa komai daya faru tun daga farkon abinda Aisha ta fara mata har zuwa yau d'in, saida ta gama abinda bata tab'a tsammani ba daga Iya ta ji tace "Maganar banza, yo an fad'a musu ke d'in a bishiya muka tsinkoki? Ya zasu taru gard'ama gard'ama dasu su nuna miki fin k'arfi."

Gyara zama tayi ta jawo Mimi ta shiga daddab'ata tana fad'in "Ke rabu dasu kinji, nan zaki zauna na ga wanda ya isa ya maidaki k'arfi da yaji, kaga iskanci."

Dariya malam yayi yana girgiza kai bai ce komai ba, dan gaskiya yanda yake son Mimi shi ma sai yaji bai ji dad'i ba musamman da ita kan ta uwar yarinyar ta fad'a mata maganganu sannan shi bai tsaya ya bincika ba kuma ya d'ora mata da fad'in matarshi matarshi, yana gama cin abincin shi ya wanke hannayenshi ya d'auki k'aramar r茅dion shi zai fita ya kalli Mimi yace "Ki shiga da kayan ciki ki kwanta zuwa safe zan san abun yi."

Mik'ewa tayi da sauri tana fad'in "Ni da safen ma makaranta zan tafi, kawai ka k'yaleshi yana tsohonshi dan ma ya samu na kulashi." Da kallo suka bita malam na dariya ya fita a gidan.

*Ya jima* nan amma bai ga wulgitawarta ba sai kawai ya sake kiran wayarta, a lokacin tana d'akin Iya tayi kwance a gadon k'arfe tana d'an lilawa kad'an kad'an, d'aga wayar tayi ta d'ora a kunne cike da gatsali tace "Ina ji?"

Shiru yayi idonshi lumshe murya k'asan mak'oshi yace "Ryammm."

Tsam tayi tare da dakatawa da lilawar da take a gadon, wani tsammm ta ji gaba d'aya jikinta saida ya amsa, d'an basarwa tayi tace "Ina jinka."

Cikin sanyi da taushin murya yace "Kina ina Ryam? Dan Allah ki dawo."

Cikin shagwab'ar da bata san tayi magana ba tace "Um um! Ni ba zan koma ba tunda ba so na kake ba, Abdul baka so na kuma baka son zamana a gidanka, sannan 'yarka da mahaifiyarta basa so na sun tsaneni, kawai ka zauna da iyalinka na yafe musu kai har abada, kaga ai dama ni ma kawai had'ani ne aka yi da kai ba dan ina so ba."

Da sauri kamar wanda zai fashe da kuka yace "Ba haka bane Ryam, nasan an miki ba daidai ba amma ki yafe mana kinji, Ryam in kin san yanda nake ji wallahi da baki tafi kika barni ba."

Tashi tayi zaune tace "Ba wani nan, kawai wayo kake so ka min dan ina yarinya, to ni ma da hak'orana ashirin da bakwai."

Dariya ce ta kubce mishi har tana jin sautinta a kunne kafin yace "Ryam, kenan bakiyi hak'oran hankali ba."

Turo baki tayi irin bata ji dad'i ba kafin tace "Ni dai saida safe, kaga yanzu ba gidanka na ke ba."

Zata kashe wayar yayi saurin fad'in "Inna Issa ina kika je?"

Cike da yarinta tace "Ina wani wuri."

D'if ta kashe wayar ta aje gefe ta kwanta, wayar ya bi da kallo sai kuma ya aje ta ya wa motar ky, ba zai iya tafiya gidansu ba a yanzu dan haka zai bari har da safe, duk da yana jin wata irin kunyar had'uwa da iyayen na ta, dan gaskiya abin nan ya dakeshi sosai, kuma yasan yana da laifi ta wani b'angaren, da wannan tunani ya isa gida kai tsaye b'angarenshi ya wuce.

Hafsat ma ta jima zaune kafin ta mik'e dan duba yaran ko sun kwanta, saida ta shafawa dukansu addu'a kafin ta nufi d'akin Aisha, zaune ta sameta tsakiyar gadonta tana karatu da Qur'ani, k'arasawa tayi ta tsaya gabanta tana kallonta, ita ma d'aga kai tayi ta kalleta tace "Amie baki kwanta ba?"

Ba sakin fuska a tare da ita tace "Ta ya zan kwanta bayan bansan halin da kike ciki ba."

Murmushi tayi na jin dad'i tace "Amie lafiya ta lau, kiji ki kwanta ke ma."

Wani malalacin murmushi tayi tace "Yayi kyau, haka yayi kyau tunda gashi har ina ganin murmushinki saboda yau kina farin ciki mahaifiyarki tayi fad'a a kan ki."

Wani kallo ta mata baki sake irin tana jiran k'arin bayani, ruugume hannaye tayi tace "Kin fahimta mana, ya kamata kiyi farin ciki a zuciyarki tunda dai Mimi ta tafi gidansu."

Zabura tayi tana aje Qur'anin tace "Me? Ta tafi Amie?"

Wani dogon tsaki ta ja ta juya zata bar d'akin Aisha ta sauko tana rik'e hannunta tace "Amie da gaske ta tafi? Amie ku yafe mi..."

Tureta tayi ta fizge hannunta tace "Shiru dallah! Hak'urinki na banza da wofi kike ba mutune, kullum ki ce kin tuba kuma ba zai hana anjima ki sake aikata abinda kika aikata ba, Aisha me yake damunki? Me aka miki da zafi haka da kike neman tarwatsa mana zaman lafiyar gida? Tunda kike kin tab'a ganin sab'ani tsakanina da mahaifinku? Kawai saboda an yi min kishiya k'waya d'aya, ba dan mahaifinki ya kasance mutum da bai san matsala da a yanzu Mimi ta hud'u ce ita."

Nunata yayi tana k'yasta hannunta tace "Ki ji da kyau zan daidaita gidana da kai na, wallahi wallahi wallahi kinji uku ko? Na rantse miki da Allah Aisha kika sake wani abun da bai min ba a gidan nan sai na miki d'an banzan duka sannan na wankeki a haka na kaiki d'akin miji."

Harara ta watsa mata sannan ta wuce ta barta nan tsaye, wani iri take ji gaba d'aya ta ma rasa inda zata saka kan ta ta huta, haka ta koma kan gadon ta zauna ta buga tagumi tana tunanin abun yi.




*Washe gari*


Tunda sassafe malam ko da yayi sallah ya samu Abba a masallacin unguwarsu ya fad'a musu abinda ya faru, rai b'ace duk da kunyar sirikina shi saida ya kalleshi yace "Yanzu malam can ta tafi kenan? Dama bata ji magana ta ba?"

Saka takalminshi yayi yace "Malam muje gidan nan dan Allah ka yarje min na daki hancin yarinyar nan."

Dakatar da shi malam yayi yace "A kan me? Kaga ni bana fad'a maka bane dama dan ka je ka d'aga min hankalinta ba, na fad'a maka ne dan ka sani kuma ko da mijin na ta ya nemeka ka sanar da shi inda ta ke."

Jinjina kai yayi alamar gamsuwa yace "Shikenan malam, insha'Allahu da kai na ma zan kirashi."

Jinjina kai malam yayi yace "Hakan ma daidai." Da wannan suka rabu kowa yayi gida, Abba na zuwa da fad'a ya shica fad'awa Mama tare da d'aukar wayarshi ya fara kiran lambar sheikh, yana ganin kiran amma bai d'aga ba saida ta tsinke sannan ya d'aga, a mutumce kuma a kunyace suka gaisa kafin Abba ya d'an sosa kai yace "Gafarta malam dama shiriritacciyar yarinyar nan ce jiya da dare ta zo mana da wani hauka, to ko da ta zo ma na maidata ashe bata tafi can ba."

Shiru sheikh yayi kamar bai ji, har ga Allah lamarin yi masa yake kamar a mafarki, da k'yar ya cira bakinsa yace "Ayi hak'uri malam, insha'Allah idan na dawo daga aiki zan zo da kaina gidan muyi magana, ina mai bada hak'uri dan Allah, insha'Allah haka ba zata k'ara faruwa ba. "

Cike da girmamawa Abba yace "Shikenan sheikh ba komai, ban da ma abin yara ina abun hushi a nan? Allah dai ya shirya mana su."

"Ameen." Ya fad'a a hankali, sallama sukayi kafin Abba ya kalli Mama dake kad'a miyar d'umame yace "Ban san me uwata take son zama ba, ki ji yanzu babban mutum kamar wannan yanda yake kwantar min da murya yana bani hak'uri."

K'wafa yayi ya mik'e zai nufi d'aki yana fad'in "Yarinyar nan in batayi sannu dani ba saina b'ata mata rai wallahi."

Mama dai da kallo ta bishi dan ita ban da ganin 'yarta babu abinda take son yi, dan wannan kamar a dakeka ne a hanaka kuka, yarinya kamar Mimi a kai wa dattijo kamar sheikh, shin in bai bita a sannu ba ya za'ayi?


*Mimi*


Tana zaune ta tank'washe k'afafu tana cin tuwo tare da malam hannunta hannunshi suna ta ma Iya tsiya wai ba zasu ci da ita ba wayarta tayi k'ara, juyawa tayi ta d'auka tana dubawa ta ga Asma'u, wani murmushi ta saki ta danna ok ta d'ora a kunne, cikin nutsuwa tace "Hum! Ashe kina iya tunawa da mutane?"

Dariya Asma'u tayi daga wajenta tace "Dan kar na fara miki k'orafin shi ne kika rigani?"

Tab'e baki tayi tace "Ba wani nan, kin manta da mutane saboda kina shan amarcinki."

Asma'u dai na dariyarta tace "Kedai tafi can, yanzu har sammakon da na yi na kiraki ban tsira ba kenan?"

Gwalo ido tayi tace "Oho! Kenan kin kirani da safe ne dan na yafe miki?"

Cikin marairaicewa Asma'u tace "Kiyi hak'uri to, amma ke me ya hanaki kirana? Ke ma amarcin kike sha da yayanmu ko?"

Yatsina fuska tayi tana kallon malam tace "Ba wani nan dan Allah, ni da ma na bar muku yayan na ku ku dafa ku cinye tunda baku san mutumci ba."

Dariya Asma'u tayi tace "Kamar ya? Su waye marasa mutumcin?"

Kai tsaye tace "Ke da yar uwarki mijinki mana."

Da sauri Asma'u tace "Wani abu ya faru tsakaninku? Me Hafsat d'in ta miki kuma?"

Tab'e baki tayi tace "Rabu dasu can su k'arata tunda ni dai na baro musu gidan."

Hankali tashe a kid'ime Asma'u tace "Kamar ya Mimi? Ban gane kin baro musu gidan ba? Kina ina yanzu ke?"

Kallon kwanon tuwon tayi tace "Ina gida wajen Iya gani ma ina cin tuwo da angona."

Wata nauyayyar ajiyar zuciya Asma'u ta sauke tace "Me ya had'aku Mimi? Me yayi zafi haka?"

Mik'ewa tayi ta cire hannunta a d'umamen burabuskon da Iya tayi ta fito waje ta shiga d'akin Iya t zauna ta shiga labarta mata abinda ya faru, Asma'u kam kamar tana gabanta girgiza kai ta shiga yi kafin ta saita nutsuwarta ita ma ta bar d'akin da Asas yake kafin tace "...



*Hohoho, gaskiya fa an sha muhawara, sannunku sannunku, sunana har ya kare馃榿.*



*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*51*



Asma'u kam kamar tana gabanta girgiza kai ta shiga yi kafin ta saita nutsuwarta ita ma ta d'akin da Asas yake kafin tace "Assha kuwa? Mimi ke da kan ki kikayi kuka a gaban kishiya? Ke ce kika rasa sanin hanyar shawo kan matsalarki har kika bari aka fara sakaki yaji ko kwana bakwai bakiyi ba, ya akayi haka ta faru? Ni da nake tunanin ke ce malamata ta wannan fannin, sabida kin tab'a fad'a cewa ko a cikin mata uku aka kaiki zaki iya zama dasu kuma ki k'waci kanki a hannunsu."

Numfasawa tayi tace "Kinga Mimi duk yanda nake k'aunar yar uwar mijina bai kai k'aunar da nake miki ba dan ke tare muka tashi, ban ce ina so ta zama mowa a gidan nan ba, amma kuma ina so ki zama bora a gidanki ke ma, dan haka kiyi wani abu Mimi, a sanina dake kina da shiga mutane da kutsa kan ki inda yafi k'arfinki, kina karance karance da saurare da kallo sannan ga babbar waya a hannunki, dan Allah ki daure ki samu shawarwarin da zasu taimaka miki zama da mijinki da abokiyar zamanki da ma 'ya'yanku."

Mimi da tayi shiru tana saurarenta saida ta ji ta dasa aya ta numfasa sannan tace "Nagode k'awata, kin k'arfafa min gwiwa kuma zanyi aiki da abinda kika fad'a min."

Da fara'a Asma'u tace "Yawwa Mimi ko ke fa."

D'orawa tayi da fad'in "Ni fa na kiraki ne dan muyi wata magana."

Da zumud'i Mimi tace "Wace magana fa?"

Cikin jin kunya Asma'u tace "Dama wani abu nake so ki d'an fad'a min da zanyi na k'arin..."

Shiru tayi hakan yasa Mimi fad'in "Ina jinki?"

Cikin dariya tace "Kedai kawai zan miki magana ta WhastAp."

Kyab'e baki tayi tace "Kin samu babbar waya kenan?"

A sanyaye tace "Na yi, idan mun had'u zaki gani."

A take Mimi tace "Yaushe ma zamu had'un?"

Cike da tsokana Asma'u tace "Ga bikin 'yarki da za'ayi juma'a."

D'an gajeran tsaki tayi tace "Hummm! 'Yar masu ita dai."

Suna sallama Mimi ta fito da sauri ta wanke hannayenta ta koma d'akin, wayarta ta shiga dannawa tana duba abubuwan k'aruwa musamman a WhastAp, duk abinda ta ga an turo a grp ta kan tsaya ta dubashi a tsanake, ita da Asma'u ma hira suka sha inda Asma'un ta fad'a mata tana son abun k'arin ni'ima ne, wanda ta sani ta fad'a mata sannan tayi alk'awarin binciko musu wasu.Tana tsaka da aikin gabanta kiran sheikh ya shigo wayarta, tana ganin kiran kawai ta datse shi tare da ci gaba da aikin gabanta, haka yayi ta kira dan su gaisa amma ta k'i d'agawa, sai sak'o ya tura mata da _"Amincin Allah ya tabbata a gareki, da fatan kin wayi gari cikin k'oshin lafiya?"_

Shiru yayi ta jiran amsa amma bata maida ba dole ya sake tura mata _"Da alama ba zaki yafe min cikin sauk'i ba, Ryam ki yi hak'uri kinji."_

Nan ma shiru bata maida ba sai kawai ya aje wayar ya buga tagumi yana kallon na'urar gabanshi dake jiran ya loda mata wasu bayanai dake gabanshi a takarda amma ya kasa.

Saida tayi sallah azahar ta d'auki wayarta ta rubuta duk abunda take da buk'ata sannan ta shirya ta fito Iya na tsakar gidan tana gyara wake, tsaye tayi gabanta inda Iya ta shiga kallonta da mamaki tace "Ke kuma ina zaki je kika wani shirya haka?"

Turo baki tayi tace "Iya kasuwa zan je akwai wasu abubuwan buk'ata da zan siyo."

Cike da raini ta kalleta tace "Ke fita ido nq in rufe? Wato ga marainiyarki ko? Daga tahowarki jiya zaki ce zaki fita a gidan nan? To da izinin wa?"

Bubbuga k'afafu tayi tace "To Iya dan Allah ba gidanmu ne nake ba kuma na fad'a miki."

Cikin fad'a tace "A'a, dan kin fad'a min a banza tunda ba ni ke aurenki ba, ke Mimi in kikayi wasa wallahi saina hau bishiya na tsinko tsumagiya na ci ubanki a gidan nan, ni zaki mayar tsohuwar banza?"

Galala ta kalleta tace "Ka ji min tsohuwar nan da wata magana, to ki hau bishiyar mana dan Allah, ni na fad'a miki ki daina zagar min uba fa."

A harzuk'e tace "An zaga d'in, kiyi abinda zakiyi na gani."

Murmushi tayi ta durk'usa gabanta ta dafa hannunta tace "Iya ta, kinga fa idan na je kasuwar nan zan siyo miki goro da tantak'washi da kifi d'anye, sannan yanzun nan Asma'u ta fad'a min wani abu da ake sha ana zama mowa a wurin miji, shine fa zan je na siyo."

Hararanta ta dinga yi amma ba tayi magana ba, sun jima suna kallon juna kafin Iya ta sassauta murya tace "Shikenan na yarda ki je, amma Mimi kar kiyi abinda zaki sa a zageni dan Allah."

Shafa kuncinta Mimi tayi tana mik'ewa tace "Yawwa Kakata, shiyasa nake son ki."

Girgiza kai tayi tace "Kiyi sauri dan Allah kinji, ni ma zan je wajen malam Hadi na sa ya maki rubutu na bakali a wurin miji."

Wata lalatacciyar dariya Mimi tayi ta jinjina kai dan tuni ta hango yanda zatayi ta tsokano sheikh kafin ta fice a gidan.

Ta d'aya hanyar ta bi ta kusa da makarantarsu anan ta samu taxi ta wuce, tana ciki Salma ma ta kirata bayan sun gaisa take sanar mata jibi fa zata shiga lalle, da rawar kai da zumud'i Mimi take ta fad'in Allah kai su ranar su sha biki.

Gurin masu siyar da litattafan hausa ta fara zuwa ta siyo na girki da kuma wasu na ki gyara da kan ki da saurarensu, daga nan gurin masu kayan marmari ta nufa ta shiga had'owa kala kala, ta gama siya ta juya zata nufi Inda zata samu dabino da cukui suka had'e da yayar Asma'u Rayya, gaisawa sukayi saidai jikinta har rawa yake tsabar ta kwab'ar da zance tace "Mimi ke ce kasuwa a lokacin nan? Dama malamai na barin matansu fita haka?"

D'an murmushi tayi dake tana kallonta kamar yar uwa sai tace "Ni ma na je gidan Iya ne shine na biyo siyan wannan."

Murmushi tayi ita ma tace "Lallai fa su Mimi an shiga sahun manyan mata, kin ga yanda kikayi wani fresh dake wallahi kamar na saki a jakata."

Dariya Mimi tayi ba tace komai ba, kama hannunta tayi tace "Zo muje ki gani, ni ma nan ga ne zan je neman d'anyen madarar rak'umi."

Mimi dai bin ta kawai tayi suna tafe take fad'in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login