Showing 120001 words to 123000 words out of 185502 words

Chapter 41 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

484

"Yanzu nan shikenan ba za'ayi biki ba ayi shagali? To yaushe ne sunan ya kama?"

Cikin sakin murmushi yace "Ranar laraba, idan kika k'idaya kwanakin zaki ga a ranar ne bakwai."

Shiru tayi ta ma rasa me zata fad'a, jin haka sai kawai yace "Katin dana bar miki na ga har yanzu bakiyi aiki dashi ba, ai ya kamata ke ma ki bawa Khadija wata kyauta ko?"

A sanyaye jiki a mace tace "Zan yi, sai gobe insha'Allah."

Cike da rarrashi yace "Ryam, dan Allah idan zaki tafi karki manta da hijabanki manya da kuma nik'abi kinji, sannan karki jima ki dawo gida ki huta."

"To." Ta fad'a a hankali, da haka sukayi sallama ta aje wayar kan cinya tana kallon Asma'u tare da labarta mata abinda ya faru, dariya Asma'u tayi haka ma Kabiru dake tuk'i murmushi yayi yana jinjina lamarin wannan sabuwar sirika ta gidan yar gayu kuma da alama ma yar casu ne.

Washe gari tsaf suka shirya ita da Asma'u zasu je banki, Hajia dai da addu'a ta rakasu dan tasan da mijinta bai bud'e mata bakin aljihu ba me zai kawo maganar zuwa banki, Kabiru ne ya kaisu kuma basu jima ba dan tana nuna katin wa wani ma'aikaci aka shiga girmamata alamar sani, saida ta d'ibo kud'in sai kuma ta kalli Asma'u ta fashe da dariya tace "To wai me zanyi da kud'in nan ma?"

Tab'e baki Asma'u tayi tace "Kud'i ana rasa abunyi ne dasu dama?"

Rik'e hannunta tayi suka nufi mota tana fad'in "Muje zanyi tunanin abun yi."

Bin ta tayi tana fad'in "Allah yasa dai ba a leshe da atamfa zasu k'are ba."

Dariya tayi tace "A'a zan san me zanyi kedai, ba mijinki zai dawo ba?"

Mota suka shiga Asma'u na fad'in "Me ya shafi kud'inki da shi kuma?"

"Zaki gani kedai." Ta fad'a suna barin wurin, daga nan gidan Hafsat ya ajesu dan yau ma nan zasu wuni, suna zuwa sun samu Hafsat dake zaune tana magana da Salamatu tana fad'in "Baaba Salamatu ki fara d'ora min su na fi so na yi anfani dasu anjima."

Juyawa tayi zata shiga madafa tace "To bari na wanke su sai a d'ora silalarsu."

Da ladabi Mimi tace "Aunty Hafsat me za'a d'ora ne?"

Da fara'a tace "Hanji ne na ke son romonsu, ita kuma da tana so ta fara da girkin rana."

Mik'ewa tayi tana cire zumbulelen hijab d'in tace "Bari na d'ora miki to."

Asma'u ma mik'ewa tayi tana fad'in "Bari ni saina kama ma Salamatu girkin to."

Da jin dad'i tace "Ba kwa gajiya da aiki, to sannunku." Wucewa sukayi madafar suka shiga aiki gadan gadan.

Sanda ta gama silala ganin ta juye ruwan silalar zata zubar yasa Salamatu saurin fad'in "Ke ke! Baki da hankali ne zaki zubar? Ko dai baki san miye silala ba?"

Numfashi ta sauke ko kallonta ba tayi ba ta juye ruwan ta zubar, Asma'u ma kallonta take saidai tasan akwai dalilin da yasa tayi haka, saida ta tsane hanjin kafin a tsanake ta shiga soya miyarta da kayan miya masu yawa, sanda ta gama girkinta tsaf ta zubawa Hafsat a kula mai kyau ta kai mata falo, dawowa tayi ta zuba a k'aramin plate ta b芒 wa Salamatu tace "Iya ne sunanki ko Baaba? Ki d'and'ana ki ji kiga kalar dahuwarki ce, a ido kawai zaki tabbatar da banbanci."

Tana fad'a ta fito daga madafar, cikin sakin fuska ta kalli Hafsat tace "Aunty ko na zuba miki ne?"

Da fara'a tace "Da kin barshi ma ai."

Mik'ewa tayi ta d'an zauna bakin katifar ta shiga zuba mata, mik'a mata tayi kafin ta koma kan kujerar, Hafsat na kai lomar hanta bakinta ta kalli Mimi ba tare da bak'in ciki ba tace "Mimi dahuwar nan ta min dad'i, kinga kuwa miyar batayi irin kaurin nan ba wani har kaga yana tayar ma da zuciya."

Murmushi kawai tayi ba tace komai ba, sosai Hafsat ta ci naman nan kamar zata tsinka harshenta, saida ta kammala tasha ruwa tace "Wannan a ranar da sheikh zai dawo zaki girki masa wannan, dan mutum ne shi mai son miyar hanji sosai."

Dariya ita dai kawai tayi ba tayi magana ba sai a zuciyarta da take fad'in "Sheikh d'inki dai, zaki dafa masa ne yarinya in kuma ba haka ba to yunwa zata kamashi."

Ko da k'arfe 01:00 tayi su Asma'u ma suka gama girkinsu suka cire ma kowa na shi, lokacin Mimi ta shiga sallah a d'akin da aka ware bak'i na sallah Mamanta ta zo gidan yin barka tare da Shapi'a da Sahura.

Asma'u ce ta karb'esu inda Hafsat ma ta shiga girmamasu ta nuna musu murnarta a fili, Mimi na fitowa ta gama sallah ganinsu yasa ta k'arasowa da farin ciki tana fad'in "Mama, aunty."

Tana zuwa bata zauna akan kujera ba k'asan carpet ta zauna tana rik'e hijabin Mama tana fad'in "Mama yanzu kuka shigo? Me yasa baku fad'a min zaku zo ba? Mama ina su Yaseen? Ina Abba na Mama?"

Mama sunkuyar da kai tayi cike da kunya dan ita Mimi ma kunya ta bata sosai, ganin ba zata amsa ta ba yasa ta kallon su Shapi'a tace "Aunty Ina wuninku?"

Da fara'a suka amsa mata suka gaisa sosai, Hafsat ce tace "Mimi ki kawo musu abinci ko?"

Mik'ewa tayi zata tafi su Sahura tace "A'a Mimi barshi, saida mukayi abinci a gidan kafin muka taho."

Duk yanda Mimi ta so matsa musu su ci abincin k'iyawa sukayi saboda dattako, basu fi minti ashirin ba suka mik'e zasu tafi, cikin kukaan shagwab'a ta bi bayansu dan rakiya Mama na fad'in sa ta ci uwata idan tana mata shiriritar nan, saida suka kai farfajiyar Shapi'a ta mik'a mata wani dogon bidon da zuma a ciki tace "Yar albarka karb'i tsaraba kinji ki sha abarki."

Karb'a tayi tana kallon robar Mama tace "To dan hauka ki shiga da shi a haka sai kin nunawa kowa sirrinki."

Dariya tayi murya k'asa k'asa tana fad'in "Wai nan su fa tsuma ni suke saboda tsohon nan, ko me ya fad'a musu zai iya?"

Sahura ce tace "Magana kike?"

Da sauri tace "A'a ban ce komai ba." Rakasu tayi suka fita tana jin kewarsu kamar ta bi su."

Tana dawowa kuma Hafsat da kallon birgewa ta bi ta dan yanda suka mik'e suna tafiya daga yanda take bin bayan iyayenta tana risinawa zai nuna maka tana girmamasu ne bata son ta fi su tsayi.



*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:57 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*39*



Da dare suna komawa gida saida sukayi shirin kwanciya ta samu zumar nan saboda kwad'ayi tayi ta sha duk da ana jin d'and'anon magani, saida ta ji cikinta ya fara k'ullewa kamar zai mata ciwo ta mik'awa Asma'u tace "Sha ke ma."

Murmushi tayi ta karb'a tana fad'in "Sai yanzu kika da damar bani saboda kina so ki nuna min ke babban Alaji gareki."

Duka ta kai mata tana dariya tace "Shegiya Asma'u, ke ni me zaanyi da wannan d'an uwan naku, wanda ya haifi kamata?"

Murmushi ta sake yi tace "Ke dai kika sani."

Har suka kwanta cikinta na k'ulle mata daga baya sai taji har mararta ma wani ciwo ciwo take mata,da haka dai bacci ya d'auketa dan abun ba wani mai tsanani bane.


Kullum hakane ke faruwa Mimi da Asma'u sukan wuni gidan Hafsat ne suna kama aiki, kuma duk da ba taron biki ake ba amma lokacin na matsowa sai aka shiga yin lalle da kitso wasu ma har da d'inki kamar Hafsat da Aisha da sauran yaran.

A gefe guda kuma an gama shirin tariyar Mimi lokaci kawai ake jira, ranar da su aunty Shapi'a suka zo kamar yanda Hajia ta buk'ata dan ganin b'angaren da sheikh ya ware mata da kuma kayan da aka zuba mata bata zo gidan ba sai Asma'u kawai, masha'Allah abun ya birgesu tare da neman zautar dasu, tunaninsu bai wuce yanda yake babban malami ba amma ya daki dukiya haka kamar zatayi kuka, kaya ya mata na kece raini aka cika mata falonta da kuma d'aki biyu.



*Ranar talata*


Cikin tsantsar farin ciki da murmushi d'auke a fuska sheikh ya mik'awa likitan hannu bayan sun gama biyan duk cajin da aka musu yana fad'in "Alhamdulillah, naji dad'i sosai likita, Allah ya saka maka da alkairi, munyi farin ciki sosai."

Shi ma da fara'a yace "Ba komai, wannan aiki na ne dama, d'an uwanka ya samu lafiya kenan."

Kallon Asas sukayi dake ta murmushi shi ma cikin zolaya likitan yace "Idan ka ga yayi ciwon cikin nan mai tsanani, ina tabbatar maka fad'a yayi da madame ta daina kulasa a shinfid'a."

Dariya sukayi shi kuma ya sunkuyar da kai yana murmushi, mik'ewa sukayi suna musabaha kafin sukayi sallama suka fito a ofishin, suna fitowa daga asibitin sheikh ya tari taxi ya kalli Asas yace "Kai kaje masauki ni zan je na ciro mana ticket na komawa gobe insha'Allah."

Zaro ido Asas yayi yace "Da wuri haka? Na warken ma ba zaka barni na d'anyi yawon bud'a ido ba."

Tab'e baki yayi yace "Kana da damar da zaka tsaya bud'a ido amma fa ba tare dani ba."

Murmushin shak'iyanci Asas yayi yace "Sheikh dai na ganoka so kake ka koma wajen matanka ba."

Hararenshi yayi yace "To kaga laifina ne? Mace biyu kamar d'aya ce aka fad'a ma? Sannan karka manta har amarya gareni fa."

Tsuke baki yayi yana shiga taxin yace "Dad'inta dai nima amaryar gareni."

Murmushi kawai yayi shi ya samu wata taxin zuwa filin jirgi dan kam yayi niyya gobe saiya bar k'asar nan dan bayan iyalinshi da yake son had'uwa dasu akwai abubuwa da dama yake so yaje ya d'ora a inda ya tsaya.



*Ranar laraba*


A masallacin aka zanawa Khadija sunanta, sai jibgegiyar sa da aka yanka yan uwa aka shiga sarrafata, duk da ana cewa ba'a biki amma fa dangi an ci kwalliya har mai jego kan ta, sannan mmak'wabta da yan uwa sun cika falo da farfajiya.

Mimi kam tare da Asma'u da su Aisha da Fanna suka je salon aka musu kwalliya, yau kam Fanna duk wayewarta da k'aryar kud'in saita shafawa Mimi lafiya, ba wai kyan da tayi ko tsarin shigarta ba, yanda take kashe tsayuwa ta d'auki hoto su kansu har tana nuna musu yanda zasuyi sai ta jinjina mata. Saida suka gama shirmen hotunansu kafin suka kama aikin da mutane keyi.

*06:00* daidai suka sake gyara shirinsu bayan sunyi wanka Mimi ta sake cab'a kwalliyarta, suna tsaka da shirin Hajia ta shigo d'akin Aisha tana fad'in "Aisho zo mana na aikeki."

Yatsina fuska tayi tace "Kaji tsohuwar nan kuma, ina zaki aikeni."

Dak'uwa ta mata tace "Uwaki, sauri ake mana ki zo, gidan Hajia Kubra zan aikeki ga Kabiru nan na jiranki."

Cikin shagwab'a tace "Hajia Kubra kuma? Ba yaanzu ta tafi daga nan ba."

Dak'uwa ta sake mata tace "Uwaki Aisha, dan Allah ta so mantuwa tayi kuma abu mai mahimmanci."

Mik'ewa tayi tana turo baki tace "Ni faa ko gidan data koma ban sani ba."

Jim ta d'anyi kafin ta kalli Mimi tace "Mimi ai kinsan gidan Hajia Kubra ko?"

D'aga kai tayi a hankali tace "E, amma ban tab'a zuwa ba."

Cikin rarrashi tace "Yawwa yar albarka to tashi rakata dan Allah."

Jinjina kai tayi sai Fanna da ita ma tace "To muje tare ko?"

Kallonta Hajia tayi tace "Ba komai kuje, amma kuyi sauri kafin magriba ku dawo."

Mik'ewa sukayi duk suna gyara mayafensu har Aisha da ba sabonta bane, dan mayafin ma na Fanna ne ta bata ta saka, suna zuwa suka shiga Kabiru ya d'auki hanya da su, hirarsu suke sha sosai har suka isa unguwarsu Mimi a gidan Hajia Kubra, Aisha ce kawai ta fita da ledar a hannunta ta shiga, tana fitowa ba jimawa suka juyo, yanda aka bi ta k'ofar gidansu Mimi yasa Mimi kallon Kabiru tace "Dan Allah Kabiru ka tsaya na shiga na ga gidanmu, wallahi kuka zanyi idan ka wuce."

Tsayawa yayi inda suka shiga mata dariya, dukansu suka fita sai Asma'u da ita ma ta nufi gidansu tana fad'in "Nima bari na ga namu gidan to."

Shigewa duk sukayi saidai Aisha ta bi Asma'u ne Fanna kuma Mimi.

Yanda Mama ke kallonta da mamaki da kuma Abba dake alwala yas ta saurin duk'awa k'asa tace "Abba, mama ina wuninku.

Abba ne yace " Ke uwata daga gidan uban wa kike ana shirin magriba?"

Mama ce tace "Ina ce ma yau ne bikin gidanku? Halan sato hanya kika yi ba wanda ya sani?"

Zunbur Abba ya mik'e yana d'aukar takalminshi da fad'in "Ai kuwa zan ci ubanta a gidan nan, sheikh d'in zaki wa satar hanya?"

Bata motsa daga inda take ba tasa kukan shagwab'a tana rik'o hannun Fanna da ita ma take durk'ushe tana ta kallonsu tace "Wallahi Abba ba satar hanya nayi ba, Hajia ce ta aiko mu gidan Hajia Kubra."

A zabure yace "Wacece hakanan kuma?"

Nuna mishi k'ofa tayi tace "Abba Hajiar data dawo nan gaban gidansu Bello."

Mama ce tace "To kuma sai tace ki zo nan? Yaushe ma aka yi aurenki da zaki zo gidan?"

Cikin tsawa Abba yace "Ke tashi ki koma gidanki."

Sai lokacin Fanna tace "Ina wuninku?"

A tare Abba da Mama suka amsa cikin fara'a, Yaseen ne ya fito daga ban d'aki yana ganinta ya k'araso da murna yana kiran "Mimi ke ce? Lahhh!"

Rik'e hannunshi tayi tace "Yaseen kana lafiya? Shi ne baka j茅 ka ganni ba ko?"

Dariya yayi yace "Mama ce ta hana, amma zamu je tare da Amir."

Abba ne ya nunota yace "Uwata ki tashi fa ki koma inda kika fito?"

Marairaicewa tayi tace "Abba dan Allah ka barmu muyi sallah magriba to, kaga fa ba kyau fita ana magriba."

Jinjina kai yayi jin an fara kiran sallah yasa shi cewa "To kuyi sauri amma."

Da farin ciki ta mik'e tsaye ta d'auki buta ta mik'awa Fanna, Abba na gama alwala suka fita tare da Yaseen Mimi na fad'in "Yaseen ina Amir?"

"Yana gidan Iya." Ya fad'a yana wucewa, cikin d'aga murya tace "Ka fad'awa Kabiru ya je yayi sallah zamuyi sallah m没 ma."

Mama dai kallonta kawai take tana karantar duk yanayinta, ba tace mata k'ala ba har sukayi alwala suka laulaya mayafensu suka kabbara sallah akan tabarmar da Mama ta shinfid'a.

Kamar jira take su gama Mama tace "Tunda kun idar tashi ku tafi."

Turo baki tayi tana kallon Mama, had'e fuska tayi tace "Wato sai mun siyar da hali kike so?"

Girgiza kai tayi ta mik'e tana kallon Fanna tace "Muje." Mik'ewa Fanna tayi tana jin iyayen sun birgeta akan wannan kulawar ta su, kamar zatayi kuka tace "Mama idan su Yaseen sun zo dan Allah ki tura min su gobe, sannan ki ce Abba ma ya je na ganshi."

Sororo Mama ta kalleta sai kuma tace "To." Tana kallo suka fita kafin ta bita da addu'ar shiriya da farin ciki, suna fitowa gidansu Asma'u suka fad'a dan su basu fito ba, da sallama suka shiga saidai babu wanda Mimi ta kula kamar yanda ta saba, d'akinsu Asma'u ta wuce kai tsaye Fanna na binta a baya, suna shiga zaune suka samu Asma'u akan sallaya Mamanta daf da ita suna magana k'asa k'asa, Aisha na gefensu duk ta matsu ko su koma, dan ita inba hali na larura ba sai silamiyya ce ke fitar da ita a irin wannan lokacin a gida.

Tsaye sukayi Mimi tace "Malama ki tashi mu tafi ko? Ko nan zaki kwana?"

Mik'ewa Asma'u tayi tare da Aisha suna gyara mayafansu tace "A'a muje."

Kallon Maman Asma'u tayi suka gaisa sosai kafin su fito, suna shiga mota wayar Mimi tayi k'ara, tana dubawa ta ga Hafsat ce ta d'aga da sauri tana fad'in "Assakama alaiki."

Daga b'angarenta ta amsa da "Wa'alaiki salam, Mimi Aisha na kusanki ne?"

"E, gata." Ta fad'a tana mik'awa Aisha wayar, saida Kabiru ya fara tafiya kafin Hafsat cikin k'arfin hali na abinda bata tab'a yi mata ba tace "Aisha dan uwarki me ya tsaidaku?"

Gabanta ne ya fara fadkuwa kafin jiki na rawa tace "Amie gamu nan a hanya."

A dak'ile tace "Ba tambayarki nayi kina ina ba? Me ya tsaidaku shi na tambaya, Aisha fitarku kenan mahaifinki ya dawo gidan nan, duk mutanen dake wurin ke ya fara tambayata kina ina? Na lallab'a shi na fad'a masa Hajia ta aikeku amma ba zaku jima ba, shi ne har ki zauna acan an gama sallah, yanzu haka yana shigowa daga masallaci ke ya sake tambaya?"

Tuni bakinta ya fara rawa idonta ya kawo hawaye tana ji aurenta ya tabbata tace "Amie gamu nan tafe, dan Allah ki ba Abie hak'uri kar ya min fad'a."

K'it! Ta kashe wayar inda Aisha ta mik'awa Mimi ta ta jiki a sanyaye, tagumi ta buga tana tunanin hukuncin da zai mata, Mimi kuma fad'uwa taji gabanta naa yi tana tambayar kan ta "Yaushe kuma ya dawo?"

Duk jugum sukayi a motar har suka isa gida babu wani nishad'i, tare suka rankaya zuwa falon saidai kamar ba'a yi wata hidima a ciki ba, babu kowa saai Hafsat da yaranta zaune an share ko ina anyi turare, Fanna ce ta nufi d'akin Aisha tana fad'in "Bari nayi shirin gida nima."

Asma'u maa bin bayanta tayi tace "Bari nima na had'a mana kayanmu Mimi."

Hafsat ce tace "Ki had'a kayanki mijnki zai zo nan ya d'aukeki."

Da sauri ta kalleta tace "Ya zo ne?"

Da murmushi tace "Sun zo, dama suna so su shammace mu ne."

Juyawa tayi jiki a sab'ule duk ta rasa me ke mata dad'i, kallon Mimi tayi data zauna tana cire mayafin tace "Ya akayi kuka jima haka?"

Cikin ladabi tace "Wallahi dan naga kusa da gida ne shiyasa na ce mu tsaya na ga gida daga nan mukayi sallah."

Jinjina kai tayi tace "Hajia ta gaji da jiranku tayi tafiyarta tun kafin ayi sallah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login