Showing 78001 words to 81000 words out of 185502 words
zamuyi yanzu? Basu san me ake ciki ba fa?"
A zabure ya kalleshi kamar marinshi yayi a fuska, sai kuma ya d'aga kai ya kalli su malam da Abban Mimi ga Abban Asma'u a kusa dashi, girgiza kai yayi ya sunkuyar da kan shi k'asa, shiru aka sake yi ana ta kallon kallo ba wanda yace wani abu.
Gashi sheikh Bala dake d'aura aura yana ta magana, a hankali Saleh ya kalli Abban Mimi cikin rawar murya yace "Kuyi hak'uri, d'aurin auren nan ba zai yiwu ba."
Da wani matsiyacin sauri suka kalleshi suna rarraba ido, cikin kid'ima Abban Asma'u yace "Me yasa? Wani abu ne ya faru?"
Abba kam tuni yayi k'asa da kanshi da tunanin ko wani abun kuma aka ji Mimi tayi, cikin alhini Saleh yace "Ba komai, saidai Ashraf Allah yamasa rasuwa, d'azune aka kira daga gida aka sanar mana."
Kusan duk wanda y'a ji saida ya fad'i kalmar nan ta daga Allah muke kuma gareshi zamu koma, sosai aka jijjiga aka shiga jajantawa ana tattaunawa k'asa k'asa.
Wani iska sheikh ya feso a bakinshi mai zafi tare da tattara babbar rigarshi ya yunk'ura zai mik'e yana fad'in "Ku gafarceni, zan koma gida."
Da kallo wasu suka bishi sai Saleh daya shiga lalubo wayarshi dake ziiii! Ziiiii alamar vibration, yana ciro ya d'auka ganin lambar Hajia ce, d'orawa yayi a kunne yana kallon Bala daya ci gaba da d'aurin auren.
Cikin sauri da gaggawa Hajia tace "Saleh ya maganar d'aura aure?"
Saida ya d'an kare bakinshi da tafin hannu yace "Hajia ba'a d'aura ba."
Da saurin bala'i tace "Karku kuskura, a d'aura auren nan da sheikh, karku bar yarinyar mutane tayi alhini, dan Allah ya karb'i aurenta."
Tsam yayi yana kallon k'eyar sheikh dake tafiya a hankali har ya kusa fita, da sauri ya mik'e tsaye yana fad'in "Kin tabbata Mari?"
"Eh, a d'aura." Ta fad'a cike da k'warin gwiwa, hannu ya d'aga ma na gabanshi yana musu alamar su dakatar da sheikh, cikin ladabi kam wani matashin ya mishi magana, juyowa yayi yana kallonshi da ido da alamar tambaya, da hannu shi ma ya mishi alamar taho kawai, a hankali ya sake juyowa yana dawowa yana jin yana so ya cire babban rigar nan dan zafi yake ji sosai, ac da pankokin dake wurin kamar basa aiki yau kam.
Saida ya koma ya zauna inda yake Saleh ya kalleshi sannan ya kalli k'anan babansu sheikh Alhaji Ibrahim yace "Hajia tace a d'aura auren nan da sheikh, ya kuka gani?"
Wani kallo sheikh ya watsa mishi da sauri inda Abba ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi, shi kam me zai hanashi ya so had'a zuri'a da Abdul Waheed? Su Abban Asma'u da malam da shi kanshi Alhaji Ibrahim duk murmushi sukayi, hakan yasa Saleh ciro kud'i ya damk'awa Alhaji Ibrahim yace "Ka karb'a mishi auren ta."
Kallonsu yake kamar ya d'ora hannu yace wayyo shi wayyo kan shi, girmanshi da darajarshi ta hanashi mik'ewa yace " *Wallahi bana so, bana son yarku ku rik'e abarku, ni uwa ta gari nake nemawa yarana*."
Ganin da gaske suke har sun fara daddala mishi nauyinta a kai yasa shi sunkuyar da kai yana furta "Allahuma ajirni fi musibari, waklufli khairan minha."
Ba komai yake tunawa ba sai wani wa'azinshi da yake fad'in "Duk wanda a rayuwarshi ya auri ballagazar mace wacce ta riga ta zubar da mutumcinta, to hak'ik'a ko a kyauta aka baka ita kayi asara, dan ba zaka samu tsatso mai kyau ba bare ka haifi yayan da zakayi alfahari da su, ba lallai ka fad'a mata ta ji ba saboda babu wani abu da ke d'ad'ata a k'asa a game da harkar namiji..."
Yau shi ne aka d'orawa wannan nauyin na yarinyar da shi dai ya tabbatar hidimar da take wa kanta wasu ne k'ashin bayan hakan, son zuciya watak'ila da halin rayuwar da suke, yarinyar da mahaifinta ke neman abinda zai ci, amma ita tana rik'e da waya IPhone, yarinyar da mahaifinta ma ya kasa yarda da ita, munin halinta yasa likitar ma ta kasa fad'a a gabansu saida ta nemi da a sirrinta. Salati kawai ya shiga farawa yana jin gumin na tsatsafo masa.
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:55 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*26*
Ana gama d'aurin auren ya lumshe idonshi yana jimk'e hannunshi kamar zai naushi wani, kabbara aka d'auka a masallacin dan shi ne aure na k'arshe da aka d'aura tsakanin *Maryam Adam Shehu* da kuma *Abdul Waheed Salman Aliyu Sharif*, duk mik'ewa mutane sukayi ana fita da magana a baki, wasu hakan ya musu daidai da son zuciyarsu, wasu kuma hakan bai musu ba ko kad'an, sheikh kam bai motsa a wurin ba haka aka dinga bashi hannu ana mishi addu'ar fatan alkairi, su Abba ma fita sukayi yana kiran gida ba'a samu, dan haka mijin Sahura da suke tare ya jaraba kiranta kuma aka samu, shi ne fa suka sanar musu dan karsu ji abun daga sama kafin su isa gida. Saida yaji masallacin yayi shiru alamar ba mutane kafin ya d'aga kan shi, ai kamar wanda aka kora da gudun tsiya sai kuwa yayi wuf ya mik'e yana sab'a babbar rigarshi ya fita shi ma su Alhaji Ibrahim da Saleh suka rufa mishi baya tare da jami'anshi.
Duk motocinsu suka shiga inda sheikh ya kalli dreba yace "Dan Allah kayi sauri, gidan Hajia zamu je."
"To sheikh." Ya fad'a yana sake murza sitiyarin da kyau, ji yake an k'i kawowa gidan, gaba d'aya gani yake ba'a sauri kamar ya fita yaje da gudu a k'afarshi, tambayar "Anya kuwa Hajia tasan wa ta bani?" Yake yi, numfashi kawai yake saukewa lokaci zuwa lokaci, da wannan tashin hankali suka isa gidan daya k'ara kaurewa da mutane maza da mata, a k'ofar gidan motar ta tsaya sheikh ya fita, duk da hankalinshi a tashe yake kuma sauri yake sosai, amma tafiyar a nutse yake yin ta cikin hankali, gaisheshi ake da girmamawa kamar wani sarki shi kuma yana amsawa da murmushin yak'e a fuskarshi, har suka shiga cikin gidan ya fara hango Hajia a b'angaren Asas zaune a k'ofar shiga falon, mutane duk anyi cirko cirko wasu zaune wasu kuma tsaye babu mai magana.
Da sauri ya isa garesu saida ya kai daf dasu ya fahimci matar Alhaji Ibrahim ma tana tare dasu Kubra da matar Saleh sai Hafsat zaune kan ta a k'asa, kallonta yake yana karantar yanayinta, sosai ta bashi tausayi dan alamu sun nuna tasan abinda Hajia ta aikata musu.
Kallon juna sukayi da Hajia cikin rikitacciyar murya yace "Hajia ya haka? Ina Asas?"
Sake rumgume hannayenta tayi tace "Yana ciki likita na dubashi."
Sake kallon Hafsat yayi, matsawa yayi kusanta ya durk'usawa ya kamo hannayenta cikin na shi, da k'yar ta d'aga idonta ta kalleshi tana mai danne abinda ke zuciyarta tare da dakatawa da karatun suratul nisa'i data shiga tunda abun ya faru dan ta tunawa kanta cewa hukuncin Allah ne fa, shi ne ya hukunta musu suyi, da k'yar ta k'ak'aro murmushi da shi yana gani yasan bai kai ciki ba tace "Barka, ina tayamu murnar k'ara girma, ina tayaka murnar k'ara samun wanda zaka ciyar fisabilillah, Allah tayaka rik'o sheikh."
Yanda muryarta ke rawa yasa ta dakatawa dole dan bata so tayi kuka, girgiza kan shi yayi tare da d'ora hannunshi a cikinta shi ma kamar zaiyi kukan yace "Kin tabbatar kuna cikin k'oshin lafiya?"
Saida ta d'ora hannunta akan na shi ta jinjina kai tace "Eh, ba komai."
Girgiza kai ya sake yi yace "Da komai Hafsat, zamuyi magana a gaba kinji."
Mik'ewa yayi tare da sakin hannunta ya kalli likitan daya fito, yanda suka zuba mishi ido yasa shi girgiza kai yace "Saidai kuyi hak'uri, Allah ya gafarta masa."
Da sauri ya rab'ashi ya wuce d'akin haka Alhaju Ibrahim da Saleh ma da kuma Sadeeq da suka samu a nan, tabbas dai abinda kowa ke gani shi suma suka gani, a hankali ya zauna bakin gadon yana k'arewa fuskar Asas kallo, lallai duniya *budurwar wawa*, jiya suna tare da bawan nan har safe ma haka, kai har k'arfe 10:45 suna tare dashi yana mishi mitar ya bashi jaka d'ari biyu shi babu kud'i a hannunshi, kuma banki a lokacin yasan ba zai samu ba dan juma'a ce, shi ne yanzu kwance haka a gabanshi baya motsi.
A sanyaye ya sauke wani numfashi kanshi k'asa yace "Zamuyi mishi sutura yanzu, bayan sallah la'asar insha'Allah saimu kaishi gidanshi na gaskiya."
Jinjina kai Saleh yayi tare da kallon Sadeeq da idonshi zasu tabbatar maka kuka yayi yace "A samo mana abinda ya dace a mishi wanka."
Jiki a sanyaye ya fita yana sako da wasu hawaye, a kullum Asas fad'i yake "Aure na shine silar warakata." Ashe wannan warakar yake nufi? Duk tunaninsu zai warke ne daga ciwon ashe warkewa ta har abada yake nufi, bayan wani lokaci ya dawo gidan a lokacin kowa yayi zugum anyi zaune kan tabarmi an shirya zaman makoki, yana kawo musu abubuwan buk'ata sheikh ya mik'e yana aje hularsa akan gadon, cire babbar rigar yayi tare cire machette na wuyan hannun rigar ya aje ya tattare hannayen, cire agogo yayi da takalminshi haka ma safar k'afarshi fara tas, sunkuyawa yayi ba tare da jin nauyin gawa ba ya tallabi Asas kamar yaro ya shiga dashi ban d'aki, akan tabarmar da Saleh ya shinfid'a ya aje shi a hankali kamar k'wai.
Farin towel babban ya rufa mishi daga k'ugu zuwa gwiwanshi kafin yayi dubara ya cire mishi singlet d'in daya saka da wandon shaddar da kuma na ciki k'arami, fararen ruwan masu kyau da aka jik'a da ganyen magarya ya d'iba ya fara da bismillah zai mishi tsarki. *Kamar* jira ake dama a zuba mishi ruwan sai kuwa Asas yayi *zunbur* kamar dukanshi ne aka yi, abun ka ga namiji mai zuciya sam sheikh bai girgiza ba bare ya tsorata saidai idonshi kawai daya zaro yana kallon Asas daya mik'e haka kamar wanda aka maidowa rai da k'arfin tsiya.
Kallon juna suke sosai Asas yana so yayi magana bakinshi ne yayi nauyi, hannu sheikh ya kai ya tab'a goshinshi yaji babu wani sanyi k'alau, a hankali ya kamashi ya mik'ar dashi tare da d'aura mishi towel d'in a k'ugu, d'aukar kayanshi yayi ya bashi yace "Saka wannan."
Karb'a yayi hannayenshi sunyi mugun nauyi, lura da haka yasa sheikh kamo hannunsa hakanan suka fito zuwa falon, da k'arfi Saleh ya mik'e yana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."
Su ma mik'ewa sukayi har saida ya zaunar dashi bakin gado, kallon kallo suka shiga yi babu wanda yayi magna, sun jima haka kafin Asas ya d'aga kai ya kalli sheikh, kamar mai koyon magana yace "She..ikh...Au...rena,,,an d...aura?"
Ruf sheikh ya rufe ido da kunyar kallon Asas yace ai kanshi aka maida auren, a hankali ya rab'a Asas ya zauna gefenshi tare da dafe gaban goshin shi, Alhaji Ibrahim ne ya kalli Sadeeq yace "Kira mahaifiyarsa."
Da sauri ya fita inda Saleh kuma ya karb'i kayan dake jimk'e hannun Asas har yanzu ya saka mishi rigar, aje k'amarin wandon yayi ya durk'usa ya zura mishi dogon, yana cikin d'aure mishi zariya Hajia da Hafsat suka shigo tare, da farin ciki Hajia ta fad'a jikin Asas tana fad'in "Allah nagode maka, Allah ka yaye mishi wannan ciwo dake rabashi da rayuwa idan ya taso."
Kamar baya fahimtar me ke faruwa haka ya kalli Hajia data d'ago yace "Hajia, Mimi...aure...an d.aura?"
Tarrr! Hajia ta sauke ido a kan shi, saidai dake ita d'in ba masu kwalo kwalo bace sai tace "Ai tunda muka ganka kwance kamar gawa muka d'auka shikenan, har za'a fasa d'aura auren sai kuma na ce kar ayi haka ko dan ita yarinyar, shiyasa na ce a d'aura auren da d'an uwanka sheikh."
Shi ma dai wani kallo ya bita dashi duk da ya gane hausar da tayi, amma sai yaji yana neman k'arin bayani a sauk'ak'e, ya jima haka kafin ya iya cewa "Hajia matata sheikh ya aura?"
Girgiza kai tayi ta kamo hannunshi tace "A'a autana ba matarka ya aura ba, da matarka ce ai da bai aureta ba."
A sanyaye murya na shak'ewa yace "Hajia matata ya aura, ni ne fa zan auri Mimi."
Had'e fuska tayi tace "Ashraf Mimi dama *ba matarka* bace, baka ga gaba d'aya numfashinka saida ya bar gangar jikinka ba kafin ya auri *abar sa*? Ko kana so ka ce min baka yarda da hukuncin Allah bane? *Maryam matar sheikh* ce shiyasa ka lek'a lahira kafin ka dawo aka d'aura aurensu."
Kamar zai fashe da kuka yace "Hajia hakan ba daidai bane, wannan hukuncin bai yi ba sam, ina son matata, ina son ta Hajia dan Allah a bani matata tunda dai ban mutu ba."
Wata tsawa ta daka masa tana fad'in "Kai kanka d'aya kuwa? Ya auri matar ne zaka ce a mayar maka da matarka? Ita d'in yar tsanace ko wata abar wasa? Ko kumaa auren kake so kayi wasa dashi?"
Alhaji Ibrahim ne yace "Maryama ba haka za'ayi ba." Kallon Asas yayi yace "Kai Ashraf zauna kaji."
Cikin sako hawaye ya juya ya kalli sheikh da kanshi ke k'asa yana ta matse tafukan hannayenshi, shi kanshi fatanshi shine su amince ya sauke wannan nauyin dake kan shi, dan ba zai iya d'auka ba, ba zai yarda ya fara zaman aure da yarinyar da har ga Allah yake jin k'yamarta da kuma zarginta a ranshi ba. Zaune yayi k'asa kusan k'afafun sheikh yana kallon Alhaji Ibrahim daya gyara tsayuwarsa yace "Ashraf, kasan da cewa a duniya *wani* baya *auren* matar *wani*?"
Cikin kuka yace "Eh Abba."
Jinjina kai yayi yace "Sannan kaji ana cewa *matar mutum k'abarinsa*?"
Jinjina kai ya sakeyi yace "Na ji Abba."
Jinjina kai yayi yace "To ka yarda da wannan maganganun na hikima sannaan ka d'aura abinda ya faru akaan mizani sai ka bawa kanka amsa cewa *Mimi matar waye a cikinku*?"
Alhaji Saleh ne yace "Gaskiya ne, haka Allah ya so shiyasa abinda ya faru har ya faru, duba da ita kanta yarinyar jiya guba tasha mai had'arin gaske, amma a k'arshe Allah ya tashi kafad'unta, sannan kai ma gashi ka d'auki awanni a doguwar suma, amma kuma aka sake ara maka numfashi Asas, wannan ya isa ya nuna maka dama can Mimi sheikh ne mijinta."
Hafsat da Asas kallonshi suke kamar basa gane me yake fad'a, cikin magiya Asas yace "Yanzu kuna nufin na hak'ura kenan bayan ni ne zata aura? Shi fa ba son ta yake ba ita ma haka? Kenan auren dole kuka musu?"
Hajia ce tace "Wane irin auren dole kuma? A duniya ina ga bayan matarshi akwai wani mahaluki da zai nuna maka sanin sheikh ne? Ai kasan b芒 zai k'untata rayuwarta ba."
Cike da k'arfin hali da dakiya da kuma jarumta da son yin abinda Allah zai yarda da ita tayi k'ok'arin kawar da komai a tausashe tace "Gaskiya ake fad'a maka Asas, na tabbata da Mimi matarka ce da ka aureta ko da kuwa minti d'aya ne da d'aurawa kai kuma kabar duniyar, zaka fahimci ba matarka bace tunda har Allah yasa bata da rabon yi maka takaba, kuma da matarka ce da igiyar aure bata had'ata da *mijina* ba."
Cike da tausayawa Hajia tace "To kaji yar albarka ma."
Alhaji Ibrahim ne ya kalli sheikh yace "Sheikh ana ta magana ba ka ce komai ba."
Wani wawan numfashi ya sauke ya d'aga kan shi ya kallesu, sake sunkuyar da kai yayi yace "Da zaku min lamuni a gaskiya dana sawak'e mata, bana son shiga hakk'in d'an uwana, bugu da k'ari ni ko ita babu maganar fahimtar juna a tsakaninmu."
Hajia ce tace "Ka sawak'e mata? Ka mayar musu da yarinya bazawara kake nufi daga d'aura auren?"
Da sauri ya kalleta yace "A'a Hajia, dana saketa sai a d'aura musu aure tunda babu iddata a kanta."
Saleh ne yace "A gani na fa da Allah bai hukunta wani abu a tsakaninka da ita ba da haka bata faru ba."
Alhaji Ibrahim ne yace "Ni ma abinda nake so suyi duba dashi kenan, amma suna rufe idonsu."
Caraf Asas ya rik'e k'afar sheikh yana fad'in "Dan Allah sheikh ka saketa tunda kai ma baka son ta, sheikh na ci buri sosai wajen tsara rayuwata da Mimi, ka taimaka min dan Allah sheikh."
K'ura masa ido yayi yana kallo yana sauraren magiyarshi tare da yanda shi ma zuciyarsa ke wani tsalle tana duka, da sauri ya mik'e tsaye tare kallon Asas yace "Ka shirya zamu tafi gidansu *yarinyar*."
Jiki na b'ari Asas ya fara kakkarwa saka rigar kayanshi da Allah bai nufeshi da sakawa ba, sheikh ma takalminshi ya saka ya d'auki babbar rigar ya saka ya d'auki agogo ya zuba aljihu, hula ya d'auka ya d'ora a kai zasu fita Alhaji Ibrahim yace "Sheikh karka manta wani abu, kai babban mutum ne bai kamata kayi abinda zai tab'a kimarka ba."
Saleh kam cewa yayi "Ba ma zasu tafi su kad'ai ba, muje tare dasu kawai Alhaji."
Hajia ma cewa tayi "Ku jira muje na ga me zakuyi, wallahi ba zaka saki yarinyar nan ba."
Zasu fita Hafsat ta rik'o hannunshi hakan yasa suka kalli juna ido cikin ido, marairaicewa tayi ta girgiza masa kai tace "Na yarda da kai, nasan ba zakayi abinda bai dace ba, kayi tunani mai kyau kafin ka yanke hukunci, sannan kayi tunanin makomar yarinya da iyayenta, sannan ka duba girman wanda ya umarceka da aurenta."
Tana fad'a ta saki hannunshi tare da kaucewa a hanyar, jiki a sanyaye ta kashe mishi gabb'an jikinshi suka k'arasa fita, Asas dad'i yake ji za'a je a sakar masa matarshi ya aura, inda iyayen suke ciki zulumi da tunanin hukuncin da zai yanke. Saleh ne ya tuk'asu a mota d'aya suka tafi inda Hajia ke gaba sai su sheikh baya tare da Asas da Ibrahim.