Showing 93001 words to 96000 words out of 185502 words

Chapter 32 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

515

samu waya."

Suna fita a falon ta zauna a kan kujera, tunda ta ga ya zauna a k'asa ya tabbatar mata yau uwa ake da ita kenan, dan akwai ranar da zasu zauna kan kujera ita dashi, to ranar ana matsayin malami kenan, cikin dattako ta k'ara gyara zamanta tace "Sheikh, nasan nayi maka hawan k'awara a lamarinka a game da auren nan, saidai ka sani ba nayi bane dan na nuna na isa da kai, na tabbata auren nan zai zame maka alkairi insha'Allah, ina fatan baka k'ullaceni ba ko?"

Da sauri ya girgiza kai yace "Subhanallah Hajia! K'ullata kuma? Ko d'aya wallahi, na d'auki hakan a matsayin abu ne da dama Allah ya rubuta zai sameni, tabbas da ita d'in ba *matata* bace da ban sameta ba ko da kuwa ina son haka."

Jinjina kai tayi tace "Naji dad'in haka, yanzu maganar tariyarta nake so naji, yaushe ka tsara?"

Sunkuyar da kai yayi yana mai jin kunyarta sosai, to shi ya zai ce? Ya fad'i ranar da za'a kawo masa tsarar Aisha? Shiru kawai yayi ya kasa magana har saida Hajia tace "To idan ya maka mu barshi a sati d'aya, lokacin na tabbata ka gama gyara mata na ta b'angaren."

Numfashi ya sauke a sanyaye yace "Allah ya sa haka shi yafi zama alkairi."

"Ameen." Ta fad'a ita ma, d'orawa tayi da "Sannan sheikh dan Allah kayi hak'uri da yarinyar nan, kaga fa shekarunta k'alilan ne, dole sai kana kawar da kai da hak'uri, inba haka ba zatayi abu a cikin k'uruciya kai ka ga kamar wauta ce ko kuma da gangan."

Jinjina kai yayi yace "Insha'Allah za'a kiyaye Hajia."

Murmushi ta masa tace "Naji dad'i, Allah ya maka albarka, sai kuma magana ta gaba."

Jinjina kai yayi alamar saurare, d'orawa tayi da "Waya na ce me zai hana ka siya mata? Kaga zata dinga kiran iyayenta ai."

Da wani irin k'arfi ya d'aga kai ya kalli Hajia yana kiran "Waya kuma?"

Ita ma da mamakin yanda taga firgici a tare dashi ta amsa da "E, waya."

Iska ya feso tare da duk'ar da kanshi yana ambatar "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Shi ya siya mata waya? Yarinyar da baisan irin girma da mahimmancin data bawa waya a rayuwarta ba, idan fa ya bata ta ci gaba da rayuwarta data saba, har shi fa sai Allah ya hukuntashi dan yana da kamasho. Cikin nutsuwa da salon bayar da umarni Hajia tace "Zan jira zuwa gobe da safe sai ka kawo mata."

Lumshe ido yayi tare da d'an sinne kai ya jinjina shi alamar to, shiru babu wanda ya sake magana har saida ya d'an tank'ware k'afafunshi yace "Hajia."

Da kulawa ta amsa da "Na'am." D'orawa yayi da "Ki fara shirin aurar da jikarki Eesha, insha'Allah na mata miji kuma bana tunanin za'a d'auki lokaci mai tsayi."

Da fara'a sosai tace "A'a masha'Allah, wannan ai abun farin ciki ne, Allah ya sa alkairi ya nuna mana ranar."

A sauk'ak'e ya amsa da "Ameen." Jim ya d'anyi kafin yace "Hajia ni zan wuce gida."

Mik'ewa dan ta fahimci so yake ta mik'e kafin yayi tsaye a kan ta shi ma, a hankali ya mik'e sukayi sallama a mutumce tana fad'in "A gaishe min da mazajen kwabon nan."

Murmushi yayi yana amsawa da zasu ji ya fice kamar yace "Wayyo Allah." Hajia ta umarceshi ya siyawa Ryam waya, me zatayi da ita? Su wa zatayi mu'amula dasu? Ko dai ma ita ta ziga Hajia kan a siya mata wayar? Da tunane tunanen nan ya isa gida.



*Saminu*


"Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Abinda ta fad'a kenan sakamakon ganin Saminu zigidir babu kaya a jikinshi da wayarta a hannunshi yana kallon hoton Mimi wanda sukayi ta d'auka ranar kamu, yana kallonta yana ta lailaya dokinshi a dole yake son biyan buk'atarshi daga kallonta, juyawa tayi hankali a watse zata fita, da gudu ya biyota ba tare da jin nauyin jikinshi ba yana d'aura towel d'in shi yana kiran "Maimuna, Maimuna tsaya kiji."

Juyowa tayi a hassale ta kalleshi tace "Me zan ji? Wannan wace irin rayuwa ce? Me kake aikatawa haka dan Allah?"

Fashewa tayi da kuka hankali tashe cikin son rarrashi ya rik'o hannunta, da k'arfi ta fizge tana fad'in "Karka k'ara tab'ani."

Da alamar rarrashi yace "Naji to shikenan, amma dan Allah ki saurareni, Maimuna ba abinda kike tunani bane, wallahi..."

Sai kuma ya rasa me zai fad'a, sake juyawa tayi ya yi saurin shan gabanta yace "Ina zakije Maimuna? Dan Allah ki rufa min asiri, na yarda nayi laifi ki yafe min kinji."

Cikin sako hawaye tana kallon fuskarshi tace "Dama kana sonta ne? Ko kuma dai gaske ne abinda nake ji a gari a game da kai na neman mata?"

Da sauri ya girgiza kai yace "Ko d'aya Maimuna, wannan jita-jita ne na mutane karki yarda, Mimi kuma kamar 'ya ko k'anwa take a garemu ai, ban tab'a jin haka a kan ta ba."

Cikin d'aga murya tace "To me yasa kake kallonta kana son dole sai kaji dad'i ta haka? Fuskarta ce ke birgeka ko kuma albarkatun jikin da Allah ya hore mata?"

Sassauta murya yayi yace "Ba haka bane, Maimuna ina da buk'ata ne kuma ke naga kina saurin gajiya dani, bana so na zama mai takura miki shiyasa ban nemeki ba."

Tsareshi tayi da ido tana kallon fuskarshi, ta jima haka kafin ta sauke numfashi tace "Alhaji zan daina maka k'orafin gajiya idan ka min alk'awarin ba zaka sake kula mata a waje ba."

Da sauri jiki na rawa yace "Na daina, dama kuma bana yi wallahi, yanzu muje to."

A sanyaye ta bi bayanshi suka koma d'akin, d'auke wayar yayi ya aje gefe tare da kwantar da ita akan gadon, saidai tsaf abinda bata sani ba yana saduwa da ita ne amma kuma a idonshi Mimi yake gani, zuciyarshi ta gama haska mishi ita tare da k'awata mishi ita, musamman idan ya tuna kwancin nan nata a asibiti, yanda nonuwanta sukayi carrr daga sama kuma yake iya hangen matashiyarsu jajir dashi, ga s'uwawunta da suka kwanta akan gadon su ma sosai. Da haka har ya samu biyan buk'atarshi saidai babu gamsuwa dan hankalinshi a wani irin yake.



*Ahalin Mimi*


Aje abincin tayi gabanshi tare da zama gefenshi tace "Malam gashi."

D'an zabura yayi ya kalleta da alamar nisa yayi a tunani, Yaseen da Amir da suke gefensu ne suka kalleshi Amir na fad'in "Abba kaga yau ma mama shinkafa ta dafa mana har da nama."

Kallonshi yayi yana dariya yace "Da gaske? To ka k'oshi dai ko?"

Da dariya shi ma yace "E, Abba."

Murmushi yayi tare da jawo kwanon gabanshi zai fara cin abincin, da sauri Mama ta mik'e ta koma gefe kusa da k'ofar shiga ban d'aki, durk'usawa tayi ta shiga kwaranya amai, mik'ewa yayi hankali ya tashe ya k'arasa gareta yana fad'in "Subhanallah, uwar uwata lafiya? Baki da lafiya ne dama?"

Kakarin aman ta take yi bata kulashi ba, saida ta gama ya bata ruwa ta kurkure baki, mik'ewa tayi ta zauna kan tabarbar tana dafe kanta dake ciwo, gabanta ya zauna yana fad'in "Rabi'atu, baki lafiya dama? Me yake damunki?"

A hankali cikin muryar galabaita tace "Ba komai, ba wani abu bane."

Da kulawa yace "To ko gajiyar bikin nan ce?"

Da sauri tace "E ita ce."

Yanda ta bashi amsar ya sa mishi shakku, kallon tuhuma ya mata yace "Uwar uwata, ko dai Amir zaki wa k'ane?"

Da sauri ta kalleshi tana rufe baki tace "Kai." Sai kuma ta kalli su Yaseen, su ma su suke kallo, cike da kunya ta mik'e ta shige d'aki, dariya yayi tare da bin bayanta ya sameta zaune, kusanta ya zauna yana fad'in "Masha'Allah Rabi'a, nagode miki kinji, hak'ik'a wannan abun alkairi ne da farin ciki, Allah ya rabaki da abinda ke cikinki lafiya."

Sunkuyar da kai tayi tace "Malam kunya nake ji wallahi, mun aurar da 'ya kamata yayi ace mun aje wannan gefe yanzu."

Da mamaki ya kalleta yace "Iyeeeh! Kaji min matar nan, me zamu aje gefe d'in? Haramun muka aikata?"

Turo baki tayi ta sake yin k'asa da kanta, mik'ewa yayi yace "Uwar uwata fito ki ci abinci kinji, bayan wannan ma idan da wani rabon ni zan antayo dashi zuwa duniya."

Baki wangale ta kalleshi tace "Inna lillahi! Rashin kunya."

Juyowa yayi ya nunota da yatsa yace "Ke Rabi fita idona in rufe, na lura take-taken iya shegenki ne duk uwata ta d'auka, har take kallona ni da sheikh take fad'a mana tsofaffi."

Dariya Mama tayi ta sunkuyar da kanta, fita yayi ya zauna ya fara ci abincin cike da farin ciki a zuciyarshi, Mama kuma bata sake fita ba a k'arshe ma Yaseen da kansu sukayi shinfid'a suka taka kujera suka d'aura gidan sauro.



*Mim-Sheikh*


Da yake ba mai son zama da hijabi bace yanzu ma haka ta fito daga ita sai riga da siket d'inta na leshe, simple d'inki ne mai rap-rap amma dake tana da jiki sai ya mata wani irin kyau ya zauna a jikinta, gashinta data d'aure tayi irin d'aurin daya fi birgeta wanda tsakiyar gashin ke fitowa ta zauna a gadon bayanka. Duk da ta hangeshi amma bai dameta ba, k'arasowa tayi a sanyaye tana furta "Assalama alaikum."

Da fara'a Hajia ta amsa da "Wa'alaiki salam, takwarata kin tashi?"

Da ladabi ta zauna k'asa kusan k'afarta tace "Na tashi, ina kwana?"

"Lafiya lau, ya jikin naki? Da sauk'i ko?"

Da fara'a ta amsa "Da sauk'i sosai." A hankali ta d'aga idonta ta kalleshi, karaf idonsu suka had'e dan kallonta yake a lokacin ganin wani wata arniyar shiga da tayi, da sauri ya janye na shi idon yana fad'in "Astagfirullah wa'atubu ilaikh."

Sunkuyar da kan shi yayi har sanda siririyar muryarta ta dakeshi tana fad'in "Ina kwana malam?"

Da sauri Hajia ta kalleta tana murmushi, saidai bata ga laifinta ba dan bata san abinda yake so ba da wanda baya so, kallon sheikh tayi da a lokacin ya d'ago matsakaitan idonshi ya zuba mata harara yace "Ban ganshi ba nima, kun had'u dashi ne?"

Kallonshi tayi sai kawai tayi mar-mar-mar da ido tace "Allah huci zuciyar gafarta."

Da sauri Hajia ta gumtse dariyaarta dan ta fahimci wata yar tsama ce ke numen kunno kai tsakanin d'a kuma sirikinta da sabuwar amaryar ta shi, kwalin wayar dake gefenshi ya d'auka ya jefo mata sai a cinyarta, da sauri ta kalleshi sai kuma ta d'auki kwalin tana dubawa, a zuciyarta ta furta "Samsung galaxy."

Muryarshi ta ji a d'aure yana fad'in "Hajia tasa na siya miki waya, ki kula ki kuma san abinda zakiyi da ita, wallahi na kamaki da wayar nan kina abinda bai dace ba jikinki zai fad'a miki."

Kallonshi tayi a raunane tace "Amma malam ai ka ce baka dukan mutum, ni fa banaa son duka wallahi."

Bud'e baki yayi da jinjina rashin kunyar Ryam, gyara zama yayi ya nunata da yatsa yace "Ki jaraba yin abinda zan dokeki ki gani, ke sai na d'aureki kafin zan sa a zane min jikinki da tsumagiya."

Galala tayi sai kuma ta kalli Hajia ta sunkuyar da kanta, cikin muryar son yin kuka tace "Ai Hajia ta ce ni amanarta ce, babu wanda zai dakeni ta k'yale mutum."

A d'an hassale yace "Ke..." Sai kuma yayi saurin kallon Hajia, jinjina kai yayi irin zamu had'u d'in nan, Hajia dake ta son kecewa da dariya rufe baki tayi, yau kam tana ganin ikon Allah, ko abokan wasa fa yanzu sun ajiye wasar gefe guda basa yin ta da sheikh, amma kaga yarinya yana fad'a tana fad'a, shi kuma har da wani biye mata wai kamar ba wannan mai taka tsantsan d'in ba?

A hankali Mimi ta yunk'ara zata tashi tace "Hajia ki masa godiya."

Rintse ido yayi yana addu'ar Hajia ta matsa daga gurin nan ya cabki wuyan yarinyar can, kai kutmelesi inji yan duniya, shi wai ake wa wannan iskancin? Da kallo Hajia ta bita tana jin wata irin k'aunar yarinyar na sake ratsa zuciyarta, dan abunda tayi yanzu sai ya nuna ba yarinta bace tayi ba kuma k'uruciya bace ko raini, aji ne, ajinta ta ja da kyau, dan har yanzu ita dashi basu keb'e ba bare su zama d'aya ta yanda zata zama mai arha a gareshi. Maido kallonta tayi ga sheikh da niyyar mishi magana sai taga ya bi Mimi da harara, saidai wani abu data k'ara fahimta a cikin hararar akwai kallon birgewa duk da shi baisan yayi ba, amma dai tabbas yanayin fuskarshi yanayi ne na shagala da kuma kallon birgewa da d'aukar hankali, idonshi ne kawai ke hararen suma gaba kad'an akalar hararan zata canza ba tare da sanin mai su ba.

Juyawa tayi ta sake kallon Mimi dake daf da shiga d'akinta tace "Mimi."

Juyowa tayi tace "Na'am Hajia." Dawowa tayi a nutse a sanda sheikh ya d'auke idonshi daga kallonta yana fad'in "A'uzu billahi mina shaid'ani rajim."

Tana zuwa kan tebur ta nuna mata tace "Je ki fara cin abinci ina zuwa yanzu."

Jinjina kai tayi tare da nufa kan teburin, sosai ya sunkuyar da kanshi yana son dole yafi k'arfin zuciyarshi ba sai ya kalleta ba, kallonshi Hajia tayi tace "Da wani abu da kake buk'ata sheikh?"

Girgiza kai yayi a hankali yana jin wani irin mutuwar jiki da kasala a lokaci d'aya, jinjina kai tayi ta mik'e tace "To muje ka ci abinci?"

Girgiza kai ya sake yi da k'yar ya iya cewa "Na k'oshi."

Jinjina kai tayi ta nufi teburin tana fad'in "Bari na ci abinci ni, kasan uclerta bata jurar yunwa."

Jinjina kai yayi alamar gamsuwa, so yake ya mik'e amma kallon fitinanniyar yarinyar can ya canza mishi yanayinshi, bayan kasalar da yake ji na sauko mishi har da wani shauk'i yake ji, a hankali ya d'an gyara zamanshi cikin dubara ya saki 'yar mik'a a zuciyarshi yana fad'in "La'ilaha ilallah Muhammadu Rasulullahi sallalahu alaihi wa sallam."

Mik'ewa yayi ya d'an k'arasa kusa da su, yanda take tsaye tana zubawa Hajia abinci sai yaji yana sha'awar k'are mata kallo, yanda ya ganta yar dagwai dagwai d'in nan ga kayan nan da suka mata kyau, a hankali ya kalli kwabar madubin dake geffen shi saidai Hajia ta bawa kwabar baya ne, tsaf ya hangota a ciki tana zuba abinci, take ya jefawa kanshi tambayar "Wai me yasa ta fitsare ne tun a waje?"

Haushin wannan tambayar da jin wani mahaukacin kishi yasa shi kallon Hajia yace "Sai anjima." Da sauri ya shiga takawa ya bar falon, Hajia da kallo da mamaki ta bishi har ya fita a gidan ma.




*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*31*



Zumud'i ne ya hanata zama ta ci ta k'oshi da kyau, mik'ewa tayi tana d'aukar kwalin wayar tace "Zan shiga ciki."

Da murmushi ta kalleta tace "Har kin k'oshi?"

D'aga kai tayi alamar eh, wucewa tayi dakinta tana shiga ta zauna kan gado, jiki na rawa ta ciro wayar tare da k'ok'arin kunnawa, samunta tayi a kunne da kuma sim a ciki lokacin da komai nata daidai alamar dai an saita mata ita, gidan sim d'in ta gani da lambar a rubuce, murmushi ta saki dan irin lambar nan ce manya gata kuma duk suna kamanceceniya da lambar sheikh da yake kiranta a da da kuma lambar Ashraf.

Tunani ta shiga wanda zata fara kira, Abba dai yanzu tasan an fita buga-buga neman na kai, Mama dama ba waya ne da ita ba, lmabar Asma'u kawai take da a kan ta, dan haka ta saka lambar tare da danna mata kira, ta d'an jima tana k'ara kafin Asma'u dake zaune suna kari tare da Asas jiki na mata rawa ta d'auki kiran tana satar kallonshi, dan tsoronta d'aya kar a zo namiji ne ya kirata tunda ba kowa yasan tayi aure ba, a sanyaye sosai Asma'u tace "Hello."

Daga b'angaren Mimi ma a tausashe tace "Hello, Asma'u ta Mimi."

Wani basaraken murmushi ne ya sub'uce mata tare da aje cokalin hannunta tace "Mimi ta Asma'u, kina lafiya? Ya kike? Kin daina kuka?"

Da sauri ya aje cokalin hannunshi shi ma sai kumaa ya basar tare da d'auke idonshi daga kan Asma'u, cikin murmushi da jin dad'in k'aunar da Asma'u ke mata tace "Na daina, amma idan kika ga Abbana ki fad'a masa na daina masa magana, dan shi ne ya aurar dani ga sa'anshi."

Dariya Asma'u tayi ta mik'e tsaye tana jan kujerar baya dan bata so su siyar da halin a gaban Asas, cikin fara'a ta nufi d'akinta tana fad'in "Ba wani nan, ai ke da Abba bata b'acewa, shi kuma wanda kike kira tsoho zakiyi bayani ne da bakinki a gaba."

Da sauri Mimi tace "Me kike nufi? Wai ni zan zauna wannan tsohon ya lalata min k'uruciya?"

Da mamaki Asma'u tace "Kayya Mimi! Da alama dai har yanzu baki fahimci karatun da nake so ki fahimta ba, kina fariya da cika baki akan rayuwar da baki da ikon tsarawa kanki ko da yanda zakiyi atshawa, bare kuma rayuwarki ta 'yanci, abokin rayuwarki."

Sauke numfashi tayi cikin shagwab'a tace "Asma'u ke ma fad'a zaki min? Me yasa ba zaku dubi abin ta wata fuska ba, 'yarshi fa Aisha na tabbata ko na girmeta shekara d'aya na bata, ni yanzu ne nake fara tawa rayuwar, shi kuma ya gama cinye tashi contract d'in, so kuke na zo nayi masa takaba ne? Shikenan ni ba k'uruciyata k'arshe na shiga layin zawarawa yanda farashi na zai zube k'asa warwas."

Dafe gaban goshi Asma'u tayi tace "Mimiiiii!"

Yanda ta kira sunanta yasa Mimi fad'in "Me ya faru? Ko mijinki naa gida ne?"

Sai kuma taji kamar zatayi hawaye, tana jin Asas sosai a cikin zuciyarta, irin yanda ta tsara rayuwarta dashi da yanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login