Showing 63001 words to 66000 words out of 185502 words

Chapter 22 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

495

ke me yake damunka ne?"

"Sonki." Ya fad'a yana kallonta kafin yace "Ranar na zo gidanku ai muka had'e da babanki, bai fad'a miki sak'o na bane? Me yasa ina kiranki ba kya d'agawa."

Wani wawan tsaki cikin takaicin rashin girmama mata iyaye tace "Ban yi mamaki ba, ni nasan dama wani jakin ne ya jaza min sababi a gidanmu."

Tsaki tayi ta kama hannun Yaseen zata wuce ya sake tare gabanta yana fad'in "Ke ni ne jakin?"

A harzuk'e tace "E kai d'in, an fad'a da abinda zakayi ne?"

Wani sakaran murmushi yayi ya sha wani d'an iskan sajenshi yace "Ba komai yarinya, soyayya ta jawo haka, yanzu fad'a min me yasa wai ba kya d'aga wayata ne?"

Kai tsaye tace "Saboda zanyi aure." A firgice ya waro idonshi a kan fuskarta yace "Me! Aure fa kika ce?"

"Eh." Ta fad'a tana yatsina fuska tace "Ko da matsala ne?"

Gyara tsayuwa yayi yace "Babba ma Mimi, kinga fad'a min gaskiya?"

Gyara tsayuwa tayi ita ma tace "Wallahi gaskiya nake fad'a maka, yanzu haka ma daga kan d'inki nake na shigar biki na, aure zanyi da wanda ya dace dani."

Girgiza kai yayi tare da sunkuyar da kanshi, ya d'an jima kafin ya d'ago ya kalleta ba alamar wasa yace "Mimi, na fad'a miki a baya cewa idan har ban sameki ba babu wani d'an iskan da zai sameki, wallahi wallahi Mimi idan na rasaki kowa ma saidai ya rasaki."

Cikin rashin tsoro tace "Me zaka min? Kasheni? To bismillah kasheni Muttaka, idan ka min haka ni ka hutar dani dakon tunanin abinda ke neman lalata min rayuwata, amma ka sani hakk'i'a da alhakina zasu rataya a wuyanka ne."

Sama da k'asa ta harareshi zata wuce ya rik'e hannunta gam, jujjuya hannun ta shiga yi tana son k'wacewa amma ya rik'e jim a hannunshi, had'e fuska ya sake yi sosai cikin dakakkiyar murya yace "Na rantse miki da Allah indai ina raye babu wanda zai sameki Mimi, ko dai ki aureni hankalinki ya kwanta, ko kuma ki ci gaba da shirye shiryen bikinki da wani amma fa tabbas ba za'a d'aura auren ba."

Cikin tsiwa da haushin rik'e mata hannu tace "Insha'Allahu zaka ga d'aurin aurena da mutumin da bakayi zato ba, sunanshi kawai zaka ji ya jijjigaka dan ko kusa dashi ka tsaya sai kayi fitsari a wandonka, kallon fuskarshi kula yafi k'arfin idaniyar mashayi kamar ka, kusa dashi ma idan ka tsaya sai zuciyarka ta buga tsabar tsoro da kwarjinin *mijina*."

Sakin hannunta yayi yace "Shikenan zaki gani kuwa, ba dai ni kika wa haka ba saboda nace ina sonki? Wallahi ko a haukace sai kin zauna dani, banza 'yar k'ananan mutane."

Juyawa yayi a fusace Mimi kam takaicin an tab'o iyayenta yasa ta duk'awa ta kwashi tsakuwa ta watsa mishi cikin k'arajin murya tana fad'in "Kai ne banza d'an k'ananan mutane, mashayi da baisan ciwon kanshi ba, kai baka san miye soyayya ba ma bare har ka samu wacce zata so ka, banza alade kawai."

Da matsiyacin mamaki ya juyo ya kalleta, takowa yayi a hassale yana zuwa ya d'aga sangamemen hannunshi ya kasheta da mari yana fad'in "Ni ne banza alade? Ni ne aladen? Bari na nuna miki abinda dabba irina take aikatawa."

Yanda ta fad'i k'asa ne yasa shi yunk'urin fad'awa kan ta, cikin k'arfin hali Yaseen ya jawo rigar Muttak'a yayi baya dashi da k'arfin da Allah ya hore mishi, yana tangal tangal kamar zai fad'i ya kalli Yaseen, cikin zafin nama ya sake kawo mata hari, durk'usawa yayi duka gwiwoyinshi k'asa ya shiga kiciniyar rik'e hannayenta da take kai mishi duka dasu.

Cike da jarumtar data samo asali a jinin yan uwantaka, cike da rashin tsoro da kuma yarda da cewa Allah ya bashi makaminshi Yaseen yayi kukan kura ya bugawa Muttak'a faffad'an kanshi. Yanda abun ya zo a bazata yasa Muttak'a jin wani gummmmmmm! Cikin kanshi, duk yanda ya so ya bud'e ido kasawa yayi saboda gaba d'aya kanshi kamar ba'a jikinshi yake ba, suna ganin ya fad'i kwance a wuri dafe da kai yana mirginawa Yaseen ya kama hannunta ta mik'e da sauri da gudu gudu suka barshi nan wurin, saida suka kai daf da gida ta kama hannunshi ta durk'usa tana sauke numfashi, kallon hannunta yayi dake ta rawa yace "Mimi ba zan fad'a musu ba, nasan abinda zaki rok'a kenan, amma kiyi k'ok'ari ki dakatar da rawar da jikin naki ke yi, zasu iya ganewa."

Ajiyar zuciya ta sauke tana jinjina kai, shafa kanshi tayi tace "Baka ji ciwo ba?"

Girgiza kai yayi yace "Ai babu abinda na ji."

Murmushi tayi tace "Lallai kaine magajin Abba, tunda gashi ka ceceni."

Murmushi yayi shi ma yace "Kullum fa muka ji fad'anki a unguwar nan akan mu ne ko iyayenmu, ni ma zan tsaya miki babu abinda zai sameki."

Murmushi tayi ta shafa fuskarshi tace "Nagode k'anena."

Mik'ewa tayi suka shiga gidan da sallama, Abba na tsaye ya maida hannaye baya alamar su yake jira, ko sallamar babu wanda ya amsa Abba yace "Me ya tsaidaku har minti shida ya hau kai?"

Kallon Yaseen tayi da yayi saurin cewa "Abba k'asa muka dawo, har zata tare mana taxi na ce mu taho k'asa."

Harara ya dalla mishi hakan yasa Mimi durk'usawa tace "Wallahi Ab..." Hannu ya d'aga mata yace "Dakata, bana buk'atar rantsuwarki."

Hanyar fita ya nufa yana fad'in "Gobe ku k'ara."

Suna ganin fitarshi Mimi ta mik'e ta shiga d'aki ta cire hijabinta ta d'an kwanta a kan gado ta shiga dawo da had'uwarsu da Muttaka baya, tsoro ne fal taji ya cika mata zuciya da tunanin abinda zai iya yi mata, d'an k'waya kam tasan zaiyi abinda ya fad'a, saidai me zaiyi? Kasheta zaiyi ko fyad'e zai mata? Idan kisan ne ta wace hanya zai kasheta? Idan fyaden ne wani iri zai mata? Da wannan firgitaccen tunanin har bacci ya d'auketa a kan gadon.



馃グ *Comment masha'Allah, shiyasa kuka sameni dayawa.*馃グ



*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:55 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*22*


Saida ta wayi gari ne ta lura da illar da marin Muttak'a ta haifar mata, dan fuskarta kumbura tayi ga kuma shatin yatsunsu kwance a kai, haka tayi ta fama da hijabi har ta shiga wanka ta fito ta shirya a sauk'ak'e, Mama kam dama tun jiya da tayi baccin ta fahimta shiru ne ta mata, Abba kuma da safen daya gani sai hankalinshi ya tashi sosai, amma bai nuna ba saida ya fita daga gidan sai kuma ya lek'o ya kira Yaseen, da ladabi ya amsa mishi yayi tsaye yana jiran yaji me zai ce, cikin magiya ya kama hannunshi yace "Yaseen, kaga dai jiya tare kuka fita da uwata ko? Kuma kaga ina tafiya da ku wurin karatun malam, kuna jin yana yawan fad'a k'arya ba kyau, sannan kaga k'aryar da uwata ta mana ne ya sa mukayi hushi da ita, indai baka so kai ma nayi hushi da kai to ka fad'a min abinda ya faru bayan fitarku jiya?"

Tsatsareshi yayi da ido yana tunanin me zai fad'a, baya so dai wani wulak'ancin ya sake biyowa baya akan yar uwarshi, dan haka ya gyara tsayuwa yace "Abba, ai tare muka tafi ko? To wani ne muka had'u dashi bamu san shi ba, saiya tsaidata zai mata magana, amma kuma sai yake tab'a kaina yana min izgilanci, shine ta ji haushi ta buge hannunshi a kaina ta ce mishi jaki, shi kuma yace mata banza yar wadanni, shi ne ta sake ce mishi banza alade sai yaji haushi sosai ya mareta."

Sakin hannunshi Abba yayi yana binshi da kallo yace "Ka tabbatar?"

Jinjina kai yayi yace "Eh Abba."

Jinjina kai yayi tare da shigowa cikin gidan Yaseen ya biyo bayanshi, Mimi zata shiga d'aki kenan taji yace "Ke uwata."

Tsayawa tayi tare da durk'usawa tana kallonshi gabanta na fad'uwa, cikin fad'a yace "A garin nan da ma kewayenshi, duk uban da ya sake cin zarafinki a kan wulak'anta miki iyayenki to ni ki fad'a min, ba a iya k'asar nan ba wallahi zan iya tsayawa da mutum a kowace kotun shari'a."

Juyawa yayi zai fita mama tace "Lafiya malam? Wani abu ne ya faru kuma?"

A hassale ya juyo yace "Maganar banza, ya za'a mayar min da yarinya kamar wata mahaukaciya ko marar gata, ko wane tsinannen albarka da baisan darajar mutum ba sai ya dinga tsokanar hallitarmu a gabanta, idan tayi magana har a dinga tab'a min lafiyar yarinya, to na daina hak'ura daga yau, duk wanda yake son mu zauna lafiya a shirye nake, wanda ke buk'atar daru ma a shirye nake da shi."

Juyawa yayi ya fita a gidan Mama na kallon Yaseen tace "Me akayi?"

Maimaita mata abinda ya fad'awa Abba yayi, hakan ya sata satar kallon Mimi dake kallonshi da mamakin lauyar da yayi, saidai kuma tana farin ciki akan abonda Abba ya fad'a, ko ba komai ya nuna zai hak'ura nan gaba kad'an.


*Asas*


A gaggauce yake shiri yana kallon wayarshi dake kan gado, sosai hoton da aka had'a shi da ita ya birgeshi, dama an ce lamarin duniya baya b'uya, yayi mamakin ta inda hoton ya fito har aka had'ashi da ita da kayan lefenta, sosai yaga dacewarshi da ita sunyi machtin sosai, agogo ya d'auka zai d'aura sai kuma yaji cikinshi ya tsamuka mishi kamar yanda ya saba mishi, da sauri ya aje agogon tare da zaunawa bakin gadon ya rik'e ciki yana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!"

Shiru yyi jin kamar da sauk'i, sai kuma ya sake murd'a mishi da tsananin azaba, a tare ya durk'ushe k'asa yana neman yin sujada yana wash wash cikinshi, da iya k'arfinshi yake k'wala kiran sunan Hajia amma tayi nisa, b'angarenshi zuwa nata da yar tazara kam, murk'ususu ya dinga yi a d'akin baccin nashi ga masifar gumin da yake idonshi har sunyi jajir.

Hannu ya kai yana son ya d'auki wayarshi yayi kira amma ya kasa lalabota akan gadon, a hankali jikinshi ya fara yin sanyi ya fara lumshe ido yana cije leb'enshi, numfashinsji na yin sama da k'yar kamar zai suma ko ya mutu, a daidai lokacin Sadeeq ya sallamo d'akin na shi yana fad'in "Asas zan maka iskanci fa wallahi, kai kasan sauri nake muna da wurin zuwa, ya zaka..."

Da sauri ya k'araso ya durk'ushe yana kiran "Asas, lafiya? Me ya sameka?"

Da k'yar Asas ya d'an mirgina yayi kwance a k'asa yana sake matse cikinshi, da sauri ya tallabeshi suka mik'e yana fad'in "Muje asibiti, cikin ne ko?"

Durk'ushewa ya sakeyi yana fad'in "B芒...ba zan."

Bai iya magana ba sai komawa da yayi ya kwanta a k'asa, da sauri Sadeeq ya fita yana hango mai gadi ya k'wala masa kira, da sauri ya taho suka koma d'akin, tare suka tallaboshi suka fita dashi, saida ya suka sakashi mota ya kalli mai gadi yace "Ka kira Hajia sai mu tafi tare."

Da gudu ya juya yayi b'angarenta yana ta sallalami, jim kad'an kam sai gashi tare da Hajia har ta fara kuka da Salamatu a bayanta tana bar mata sallahun ta kula da yaran idan sun dawo daga makaranta gyalenta a hannu, baya ta zauna inda Asas yake suka bar gidan zuwa asibiti.

Da isarsu aka karb'eshi kuma kamar kullum taimakon da yake kwantar masa da ciwon aka fara basho kafin a k'ara masa ruwa ya samu nauyayyen bacci. Lokacin kad'ai Hajia ta samu damar kiran sheikh ta fad'a masa halin da ake ciki, a sanyaye ya shiga fad'in "Hajia insha'Allah Asas ya kuma samun sauk'i, yanzu haka ina neman k'wararran likita a nan da zai iya bamu randez vous na had'uwa dashi sai na zo da Asas ko da kuwa hakan na nufin a d'aga bikinshi ne."

Cikin muryar kuka tace "Sheikh ko dai za'a dakatar da bikin nan ne? Gaskiya hankalina yafi karkata kan lafiyarshi, idan ba damuwa a barshi ya samu lafiya mana."

A tsanake yace "A'a Hajia, a kullum Asas yana fad'in yana ji a jikinshi aurenshi shi ne silar warkewarshi, watak'ila Allah ya nuna mishi ne a ilhama, muyi k'ok'ari muga an gama bikin nan lafiya, ko da anyi auren ne zai iya tafiya ai."

Ajiyar zuciya ta sauke tace "Shikenan sheikh yanda ka ce, Allah ya bashi lafiya."

"Ameen Hajiarmu." Ya fad'a a tausashe kafin ya d'ora da "Zan sake kira anjima."

"To shikenan, sai anjima." Suka datse kiran a haka suna mai mishi fatan samun lafiya.


*Washe gari*


Ko da Abba ya shigo da yamma yake fad'a ma mama ya samu labarin Asas na kwance asibiti har lokacin, dan haka yayi alwala zai fita sallah magriba daga nan yaje ya ganshi, har yana fad'in "Ba dan uwata ta zama wata kala ba ai ita ma ya ci taje ta dubashi, amma ba komai zan wakilceta."

Murmushi mama tayi tace "A gaidashi da jiki, Allah ya bashi lafiya."

"Ameen." Ya fad'a yana fita daga gidan, Mimi na d'aki tana jin komai dake wakana, saida taji kamar ta nemi alfarmar taje ta ganshi, dan kwanan baya ya fara labarta mata ciwon nan dake sakashi suma idan ya taso, amma babu halin zuwa ganinshi da kanta dan haka ta bishi da addu'ar samun sauk'i.


*Asibiti*


Cikin dattako yayi sallama da muryarshi da bata da maraba data yara, duk zubawa k'ofar ido sukayi dan ganin me shigowa, da sauri k'anin Hajia wanda shi yasan kowanene dan tare suka nemo auren Mimi ya mik'e da fara'a yana fad'in "Kai malam Adam, kai ne tafe?"

Cike da murnan yanda ya karb'eshi ya bashi hannu sukayi musabiha yana fad'in "Ni ne, anwuni lafiya."

"Lafiya lau, bismillah zauna." Ya fad'a yana nuna masa kujerar daya mik'e, d'an zaunawa yayi yana kallon Asas dake bacci da k'arin ruwa, a hankali kuma ya kalli Hajia dake binshi da kallo yace "Ina wuni."

Kafin tayi magana k'aninta yace "Maryama ai shine surukin Ashraf, mahaifin yarinyar nan takwararki."

Da k'yar ta k'ak'aro mirmushi a fuskarta tace "Ayyah! Ina wuni? An zo lafiya?"

Murmushi yayi shi ma yace "Lafiya lau, ya mai jikin?"

"Jiki da sauk'i, angode ma Allah."

Sake kallon Asas yayi yace "Allah k'ara afuwa."

Sai lokacin Aisha dake zaune sun kawo abinci tare da dreba tace "Ina wuni Abba."

Da fara'a ya kalleta yace "Lafiya lau yarinya, kina lafiya?"

"Lafiya lau." Ta fad'a cike da alhinin halin da kawunta yake ciki, k'anin Hajia ne yayi murmushi yace "Jika ce ga ita Maryama, 'yar sheikh ce ta fari, sunanta Aisha."

Fad'ad'a fara'arshi yayi yace "To to masha'Allah, ah abu yayi kyau."

Kallon Aisha yayi yace "Allah ya shi albarka, malam d'in ma kwana biyu na ji shiru ko ba'a gari?"

Da murmushi Hajia tace "Baya nan ai, sun tafi Paris amma sun kusa dawowa insha'Allah."

"Allah sarki, Allah ya kawosu lafiya." Ya fad'a da fara'a, jim kad'an kuma saiya mik'e yana fad'in "Alhaji *Saleh* ni zan wuce, dama na samu labarin bai da lafiya ne na zo na gaisheshi, ita ma yarinyar da mahaifiyarta duk sun ce a gaisheshi da jiki."

Cike da jin har ranta an kula da d'anta tayi murmushi tace "Har zaka koma? To angode Allah ya saka, a gaishesu da kyau."

Saleh kuma hannu ya bashi suka sake musabaha yana fad'in "Idan ya farka za'a sanar mishi."

Saida ya rakashi har k'ofar fita kafin ya dawo, hakan y'a ma Abba dad'i sosai da bai ga k'yama ko izgilanci a tare da Hajia ba, hakan ba k'aramin kwanciyar hankali ya haifar masa ba. Ita ma kanta Hajia wannan dubiya da kuma ganin shi ya tabbatar mata dattijo ne na arziki ba tsoho ba, dan haka sai taji wani shauk'in auren Asas da Mimi tare da fatan tabbatar lafiyar da yake ikrarin zai samu idan yayi aure.



*A gurguje*


Tuni jikinshi yayi sauk'i har ma sun ci gaba da shirye shirye, komai yana tafiya musu daidai dan komai a walale yake, sheikh ma sun gama hutunsu sun dawo, saidai a ranar da suka shigo a daren kuma ya d'auki hanyar Maradi sakammakon wa'azi na k'asa da k'asa da ake yi duk shekara, hakan yasa Hafsat mayar da hankalinta ita ma kan bikin.

Mimi kam bata ji dad'i ko kad'an, ana sabgar bikinta amma babu k'awarta kuma aminiyarta Asma'u, daga Jamila sai su Salma kawai ke yawan shige da fice, hakan yasa ma yanzu haka daya rage sati d'aya Sahura ta zo gidan kawowa Mama sabuwar katifar data siya ta kalli Sahura kamar zatayi kuka tace "Aunty Dan Allah idan kika koma gida ki turo min Zeinaba, ina so ta zauna a nan har a gama bikin nan."

Da mamaki Sahura ta kalleta tace "Zeinaba kuma? Ke kuwa Mimi me zata zo tayi a cikin 'yan mata kamarku?"

Tsuke fuska tayi tace "Aunty ni dai dan Allah ki turo min ita, idan ba haka ba wallahi zan fasa auren ma."

Zaro ido tayi tace "Fasa aure saboda ban turo ta ba Mimi?"

Cikin shagwab'a tace "Eh mana, aunty ki duba fa ki gani dan Allah duk yan uwana babu wanda ya zo inda nake, bansan me yasa suke min haka ba, har gayyatarsu nayi amma da sun zo zasu dinga yin baya baya."

Ajiyar zuciya Sahuta ta sauke tace "Maganar gaskiya Mimi abinda yasa kika ga suna ja baya saboda kinga ke da k'awayenki duk dogaye ne, yan uwanki kuma tsaranki duk kusan hallitarsu irin ta mu ce, sannan k'awayenki duk wayayyi ne yan boko, shiyasa suke ja baya a lamarin."

Kamar zata fashe da kuka tace "Yanzu aunty saboda hallitarsu sai su k'i zuwa inda nake, ni fa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login