Showing 105001 words to 108000 words out of 185502 words

Chapter 36 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

516

fahimci me ya faru, kallon k'ofar shigowa tayi tace "Kabiru."

Daga falo drebanta ya amsa da "Na'am Hajia."

"Ku shigo ku kama mana shi." Da sauri suka shigo tare da mai gadin, wani ikon Allah yau Hajia sam bata jin wannan rud'ewar da furgicin da take shiga idan ciwonshi ya tashi, sauta samu kanta da fad'awa zuciyarta "Idan har wannan ita ce warakar Allah ya yafe kurakurenshi, idan yana da sauren shan ruwa a gaba, Allah ya tashi kafad'unshi."

Kallon Asma'u tayi sanda zata fita tace "Yata ki nutsu kinji, ki zauna ki kula da kanki kafin jikinki yayi tsami, ina tare dashi insha'Allah zan kula dashi."

Cikin kuka Asma'u tace "A'a Hajia zan biku nima, a tsorace nake gaskiya ina so nasan halin da yake ciki."

Girgiza mata kai tayi tace "A'a Asma'u, ki zauna ki samu euwan zafi kiyi wanka kinji, ki kula da kanki nima zan kula dashi."

Cikin marairaicewa tace "Hajia ina so na je na ga halin da... *mijina* yake ciki."

Murmushi tayi ta shafa kumatunta cike da tausayinta tace "Yanzu ki fara gyara jikinki, idan gari ya waye zan turo k'awarki sai ku tafi tare."

Da sauri ta kalleta tace "Mimi?" Da fara'a ta d'aga mata kai alamar eh, jinjina kai tayi ta bita da kallo harta fita, jiki a sanyaye ta fito falon ta shiga madafa dan d'ora ruwan zafin kamar yanda Hajia ta fad'a.



*Washe gari*

Tunda asuba sheikh ya zo asibitin ganin halin da yake ciki, cikin nutsuwa Hajia ta shiga fad'a mishi abinda Dr. D'in ya fad'a "Ya ce dai wannan karan ciwon ba kaman waccen ba, dan haka ruwa suka k'ara mishi ba tare da alluran da suka saba yi mishi ba."

Numfashi ya sauke yana sake gyara tsayuwarsa yace "Insha'Allah Hajiarmu komai ya kusa zuwa k'arshe, jiya da dare nima na sak'o a email d'ina daga wani abokin karatu na dake Tunisie, kuma ya fad'a min ya sama mana lokacin had'uwa da wani babban likita daya k'ware a wannan fannin, insha'Allah yau zan gama shirya mana tafiyata da shi, gobe ko jibi zamu bar k'asar nan da izinin Allah."

Da farin cikin jin haka tace "Masha'Allah, Allah nuna mana, Allah yasa ayi a sa'a."

"Ameen." Ya fad'a a sanyaye yana kallon Asas, d'an sake kallon Hajia yayi yace "Ina iyalinsa?"

Kallonshi tayi tace "Tana gida, amma na tura Kabiru ya d'auki Mimi a gida saiya kai ta can wajenta, dan na lura hankalinta ya tashi sosai kuma kamar bata da lafiya, amma na ce Salamatu ta fad'awa Mimi idan ta ga jikinta da sauk'i su zo nan tare ta ga jikinshi."

K'uri! Yake kallon Hajia duk sanda tace Mimi yana jin wani b'all! A zuciyarshi, kallon fuskar Hajia kawai yake yi yana tunanin "Anya kuwa Hajia tasan wacece yarinyar nan?"

D'an d'auke kan shi yayi a hankali yana sauke numfashi, jim kad'an ya sake kallon Hajia yace "Hajiarmu zan wuce gida, dama daga masallaci nake, amma idan na shirya kafin na wuce aiki zan sake biyowa na ganshi."

Da sakin fuska tace "To sheikh ba damuwa, sai ka dawo."


*Mim-Ma'u*



*Assalama alaikum*

_Kwanakin da suka wuce zaku ga na zage ina ta baku page bibbiyu a wuni d'aya wata rana ma har uku, ba komai ya kawo haka ba sai ganin kuna comment masha'Allah. Watak'ila lura da kukayi ina yi akai akai ne yasa wasu tunanin ko zaman banza ya min yawa, dan haka zakuyi tunanin barin comment da tunanin ai zan ci gaba da sako muku, magana ta gaskiya abinda yasa a can ma kuke ganinshi a kai a kai comment d'inku ne ya ban k'arfin gwiwa, yanzu kuma da kuka rage sai gaba d'aya na mayar da hankalina kan harkokina da kuma rayuwata, *jiya* da k'yar da taimakon *Kwate ta* (Sajida) na samu na saki page d'in jiya, to da irin haka wata rana ma kasa rubutun zanyi._

_Dan *Allah* mu daure mu k'arasa yan tsirarun page d'in da suka rage mana, dan *MATAR MUTUM* ba labari ne ba da zan ja shi da tsayi ba, kuma ina fata matar mutum ya zama labarina na k'arshe a harkar rubutu, idan Allah bai nufeni da hakan ba kuma ina fatan nayi hutu mai dogon zangon da har za'a fara mantawa da sunana kafin na ci gaba, dan Allah ku karfafa min gwiwa ta hanyar sambad'a comment ko na samu na kai k'arshen labarin nan, a grp d'ina a k'alla sama da mutum 50 suna karanta labarin nan a sanda na turashi, amma mafi aksarinku saidai ku turo stekers da sunan kun yi naku comment d'in shikenan, ba zan sake ganin motsinku ba sai na jinkirta yin posting. To a gaskiya idan haka ta ci gaba da faruwa zan dakatar da posting zan kammala rubutu ne saina had'a document na ajiye kayana, dan ni bana tsayar da rubutu idan na fara, kunga kenan shi ma zai shiga sahun litattafaina dana mallaka._


*MOM LATEEF*



*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*34*



Duk da duhun safiya ce amma haka Mimi ta shirya tsaf abinta a cikin atamfarta riga da siket d'amammu ta saka hijab d'inta mai hannaye iya gwiwa tsayinshi, gashi kuma hijab ne irin na zamani mai wuya biyu ga kwalliya, dreba na ajeta gidan Asma'u ta shiga kallon gidan daga waje har ciki, saida ta kai daf da shiga falon ta sauke wata ajiyar zuciya tana jinjina kan ta, sosai tsarin gidan ya birgeta dan kamar yanda Asas yake fad'a mata haka ta samu gidan.

Saida ta bud'a k'ofar ta shiga a tausashe ta furta "Salam."

Asma'u da dama zaune take tana jiranta da sauri ta fito daga uwar d'akin tana amsawa da "Wa'alaiki salam."

Murmushi Mimi ta sakar mata inda Asma'u ta mata murmushin yak'e, cikin ciccije lab'e ta k'araso gareta tana fad'in "Muje."

Hararanta tayi tace "Wai ke duk kin damu ko? Ke ga mai miji."

A raunane tace "Ba zaki gane ba Mimi, halin da nake ciki Allah ne kad'ai ya sani kuma zai sama min mafita."

Cikin gimtse fuska tace "Wani abu yana faruwa ne?"

Kama hannunta tayi tace "Muje, zamuyi magana."

Yanda ta ga Asma'un na tafiya ita ma sai ta shiga bin ta a haka har ta rufe gidan suka fita, dukansu zaune suke a bayan motar sunyi shiru suna kallon titi. Numfashi Mimi ta sauke tace "Hajia tace min ba kya jin dad'i na zo na taimaka miki, ke kuma hankalinki yana gun mijinki."

D'an murmushi tayi tace "Hummm! Na ji sauk'i ai."

"Kin tabbata?" Ta fad'a taana binta da kallon tuhuma, dan duk da bata da sani akan wannan harkar amma dai a karance karance da kutse kutse tana iya gane kad'an daga ciki, shiru kawai tayi bata sake cewa komai ba har suka isa asibitin clinique de gazobi.

A wajen ajiyar motocin ya paka suka bud'e cikin nutsuwa suka fita. Tsaf daga shigowarsu har fitarsu daga motar duk a kan idon Sheikh da shi ma shigowarshi kenan zai shiga d'akin da Asas yake, tsayawa yayi yana k'are mata kallo kamar ya d'ora hannu a kai yace "Wayyo shi wayyo Allah ya shiga uku!"

Akan me zata fito babu hijab d'in daya bata? Babu nikab a fuska bare safar ta k'afa, kenan ba zata tayashi kare martabarta ba? Wani huci ya sauke mai d'auke da siracin bala'i da gudummuwar kishi ta haifar, a sauk'ak'e ya shiga takowa cikin shigarshi ta kamala da mutumci.

Zasu wuce kenan suka ji drebansu Hajia na gaisheshi cikin girmamawa da ladabi, dakatawa sukayi inda Mimi cikinta ya fara juyawa ga fad'uwa da gabanta ya fara yi, Asma'u ma juyawa tayi tabbatarwa da tayi shine yasa ta sunkuyawa tace "Assalama alaikum."

Da sakin fuska ya amsa mata da "Wa'alaiki salam, ya jikin na ki?"

Tsili tsili tayi da ido da tunanin wai haka Hajia ta mata terere? Da murmushi ta amsa da "Na ji sauk'i ma."

Da fara'a yace "Masha'Allah, a ci gaba da hak'uri kinji, insha'Allahu zai samu lafiya, dan muna shirin fitar da shi waje."

Jinjina kai tayi cikin girmamawa tace "Allah ya aminta."

"Ameen." Ya fad'a yana d'an satar kallon mutuniyar da tayi tsaye k'erere tana ta sinne kai alamar rashin jin dad'in had'uwa da shi duk ta bayyana a tare da ita, d'auke idonshi yayi ya mayar kan Asma'u da ita ma kan ta ke k'asa yace "K'arasa ciki."

Gyad'a kai tayi da ladabi zata wuce Mimi ma kamar wutsiya ta bi bayanta, cikin dakakkiyar murya yace "Inna Issa."

Kyab'e fuska tayi ta juyo ta kalleshi, wani kallon gargad'i ya mata yace "Zo mana."

Turo bakinta tayi ta kalli Asma'u data shiga tafiya, a hankali ta shiga takowa tana ta turo baki gaba, ba tare daya kula da mutanen dake kai kawo ba ya rik'o hannunta dake waje dan ta saka hannayen hijabin, shi kuma abinda ya b'ata masa rai kenan yanda jan lallenta ya fito sosai kowa na kallo, cikin nutsuwa ya shiga nufa da ita wurin da motocinshi ke pake, jami'an na ganin haka su ma suka bud'e mishi mazauninshi, da hannu ya mata alamar ta fara wucewa. Kallonshi tayi ta fashe da kuka ta girgiza kai alamar a'a, wurga mata ido ya sake yi alamar fa ta shiga, d'aga kanta tayi tare da d'add'age yanda zata hangi Kabiru dan yanda yake tsaye gabanta masha'Allah ya gaje wurin da girman jikinshi da kuma manyan kayan.

Tana hangen Kabiru sai kuwa ta d'aga murya iya k'arfinta cikin kuka tace "Kabiru, ka fad'a ma Hajia an d'aukeni...."

Hararar daya wurga mata yasa ta saurin shiga motar tana sake fashewa da kuka tana ja baya har ta dangane a d'aya murfin k'ofar tana fad'in "Ustaz kayi hak'uri, kaga dai ni wallahi ban yi komai ba, ai ka karb'e wayata tun jiya ko? Kuma na hak'ura ban ce komai ba, dan Allah yanzu kuma me na yi? Kuma kuka hana cin zalin na k'asa, ni dai yanzu kayi..."

Jin an tayar da motocin sanda ya shiga yana kallon zasu bar asibitin yasa ta jujjuyawa, duka motocin guda uku kuma suka bar asibitin, shiru tayi da bakinta ta sinne kan ta da k'ura mata ido ne yayi yana kallo kamar zai cinyeta d'anye.

Tunani ne kala kala ke ta bijiro masa na yanda zai tsawatar mata ta fara gane idan ya ce tayi to kawai tayi ko bata so, zuciyarshi na ta hasaso mishi abubuwa da dama saidai ba d'aya wanda yayi ammana da su. Amma fa k'wala kiran sunan Kabiru da tayi ya masa zafi, a bainin nasi zata fitar da muryarta haka, to wai ko bata da ilimin addini ne? Amma kuma ai tana zuwa islamiyya.

Numfashi ya sauke a ranshi yana fad'in "Watak'ila asarar lokaci ne bata fahimtar komai."

Da sauri ta kalleshi dan abinda ya fad'a ya fito fili, yanda ta kalleshi yasa shi farga da abinda ya aikata, fuska kawai yayi yace "E, ko kina ganewa ne?"

Had'e fuska tayi ta kumburo baki alamar fa ranta ya b'ace, waro idonshi yayi yace "Idan da kina ganewa ai da kin zama mai suturta kanki a cikin gida ma bare idan zaki fita, kinsan kuwa me Allah ya fad'a akan ku mata yanda zaku saka jalbab d'inku?"

Girgiza kai yayi yana sake tausasa murya yace "Ba zaki sani ba, shiyasa nake so na mayar dake islamiyya."

Kawar da kanta tayi tana gunguni tare da fatan ya kaita inda zata sauka ta fad'i abinda ke ranta. K'ofar gidansu Hajia taga motocin sun paka sun tsaya, a hankali cikin nutsuwa ya bud'e b'angarenshi ya fita, mamaki da rashin sanin me ya dawo da ita nan yasa tana kallo har y'a zagayo b'aren da take, bud'e mata k'ofar yayi ya mik'a mata tafin hannunshi yana sakar mata murmushi da fad'in "Yan matan tsohonta muje."

Marairaicewa tayi ka rantse da Allah marainiya ce, k'in mik'a masa hannun tayi ta fita a motar ta rufe da kan ta, gaba ta shiga zata wuce cikin sanyin murya mai kama da rad'a yace "Jirani."

Cak ta tsaya amma bata juyo ba, saida ya tsaya kusa da ita kafin suka k'arasa shiga ciki, bai bi ta kan kowa ba sai wucewa da yayi har d'akin daya zama na ta a yanzun, tana kallo ya d'auki makullin d'an wani fau da fleurs alamar dai yasan inda ake ajewa ko kuma aljanunshi ne suka fad'a mishi, bud'e d'akin yayi tare da mata alama ta shiga, jiki a mace ta shiga kafin shi ma ya shiga maida k'ofar ya rufe.

K'yak'yabta mishi ido ta fara yi wanda suka kawo ruwa dan gani take irin na jiya zai sake mata, jan majina ta faraa yi a dole ita kuka take, cike da rarrashi ta kalleshi sanda yake zama bakin gadon ta shiga fad'in "Bawan Allah, ai dai yau ban maka komai ba? Amma idan akwai laifin dana maka wanda ban sani ba dan Allah ka yafe min, kaga kai babba ne mai halin girma, biye ma yarinya mashiririciya iri na b'ata lokacin ka ne zakayi."

Cike da izza da gadara ya d'ora gwiwar hannayenshi akan cinyoyinshi yana kallonta, a dak'ile cike da d'aure fuska yace "Ina kayan dana kawo miki jiya?"

Da sauri ta nuna wurin kayanta tace "Suna can."

"D'auko." Ya fad'a ba alamar wasa, jiki na rawa ta nufi kayan ta shiga kakkarwar d'aukowa, tana zuwa ta zube gabanshi tare da durk'usawa tace "Gasu."

D'an d'aga hannayenshi yayi daga tangalewar daya musu ya kalleta da kyau yace "Ryam."

Tarr! Ita ma ta sauke nata idon cikin nashi, a ladabce ta amsa da "Na'am."

A sanyaye ya shiga fad'in "Mutum ne ni dake da tsari a rayuwa, ina so idan na ce wa mutum yayi to yayi abun nan ba tare da nayi maimaici ba, kamar yanda kika fad'a ni babba ne ke kuma yarinya mashiririciya, Ryam na fahimci kanki yana rawa sosai, hankalinki ba wuri d'aya yake ba, sannan nutsuwarki bata tare da ke. Abu d'aya nake so ki sani shi ne idan na baki uamrni kawai ki bi, kin fahimta?"

Samun kanta tayi da kallon cikin idonshi tare da furta "Ko da umarnin ya sab'awa ubangiji?"

Yanda ya kalleta yasa ta sunkuyar da kai, cikin muryar shan k'amshi yace "Bana fatan na umarci wanda ke k'asa dani da sab'awa mahaliccina."

Numfashi ya sauke yace "Yanzu d'auki hijab d'in nan ki saka, dan wannan na jikinki ba hijabi bane shirme ne da hauka."

Da sauri ta kalleshi ta bud'e baki irin mamakin nan, sai kuma ta jinjina kai ta mik'e, d'aukar d'aya daga cikin hijaban tayi ta cire wannan ta saka, yanda ya sauka k'asa ya rufe mata k'afafu ne yasa ta kallonshi tace "Abdul amma wannan hijabin na mamansu Aisha ne ka d'auko min ko? Dubeshi fa sharb'eb'e ya zanyi tafiy..."

Shiru tayi dan ashe kallonta yake tana maganar nan, mik'ewa yayi tsaye tare da figota da k'arfi ta fad'a kan shi, lab'e fuska tayi alamar zatayi kuka tayi k'asa da kanta, cikin tsatsareta da ido yace "Maimaita na ji."

Rarraba ido tayi tana d'an jan majina a hancinta sakamakon yanda k'amshin turarenshi ke shiga hancin na ta, cikin rawar murya tace "Mmm..ee?"

Ba tare daya d'auke idonshi a kan ta ba ya saka yatsanshi manuniya ya shiga zagaya labb'enta yana fad'in "Abdul mana, maimaita na ji."

Wasu yawu ta had'e masu nauyi tana kakkauce fuskarta tace "Kus...kure.. ne."

Tallabo hab'arta yayi yana son tilastata ta kalleshi, duk da fuskarta suna kallon juna ne amma idonta k'irjinshi suke kallo sai kuma hawaye masu d'umin gaske da suka shiga kwaranyo mata, cikin tattausan murya yace "Ni kuma kuskuren na ki nake so, sake fad'a naji."

Idonta rufe ta girgiza kai alamar a'a, ba tare da shi kan shi yasan yayi ba y'a marairaice yace "Dan Allah Ryam, sake fad'an Abdul na ji."

Rintse idonta ta sake yi gaba d'aya take ji kamar an zare mata rai dan ta kasa motsi, labb'enta ne suka shiga hard'ewa tana fad'in "Aaaaabbbbdulll."

Murmushin gefen labb'a yayi tare da jan dogon hancinta yace "Mai tsiwar tsiya."

Sakinta yayi yana fad'in "D'aura nikab d'in."

Sharb'ar majina tayi irin shmmmmm! D'in nan kafin ya d'auki nikab d'in, d'orawa tayi zata d'aura sai kuma wata zuciyar tace "Kenan ma yin abinda yace kiyi zakiyi ?"

Sai kawai ta d'aura ta ba daidai ba ta fito da ido da hanci duk waje, wani k'ayataccen murmushi ya saki yana girgiza kai, matsawa yayi daf da ita yana kallon k'wayar idonta yace "Wato dai ni za'a ma wayo ko? Kin manta sanda aka haifeki ina daf da haifo kamarki ni ma."

Cike da sangarta da sub'utar baki tace "Ai mamanmu ma ka girmeta."

Sake bud'e idonshi yayi fes a kan ta yace "Inji wa?"

K'asa tayi da idonta tana turo baki, hannu ya kai tare da kunce d'aurin da tayi, a tsanake kamar yanda yasha ganin Hafsat na yi ya d'aura mata, cas kuwa ya fito mata da idonta biyu tare da kallonta ya saki murmushi yace "Daga yau haka nale son ganinki, ya kamata kisan cewa ke yanzu matata ce, akwai buk'atar shigarki ta nuna kamala, nutsuwa, tarbiyya da kuma ilimi, kin fahimta?"

K'ala ba tace ba hakan yasa shi zaro mata ido yace "Ryam..."

"To." Ta fad'a tana kawar da kan ta, hannu yasa ya d'aga nikab d'in yasa yatsu biyu ya cabki leb'enta na k'asa kamar yanda ya mata shekaran jiya, wata k'walla ta matso cike da azaba tana rintse idonta sosai, ba alamar wasa a tare da shi yace "Muryarki, fuskarki, surarki, mutuncinki, duk mallakina ne a yanzu, kuma ina matuk'ar kishin wani ya hangi inuwar gonata, kada ki sake min d'anyan kan da kika min d'azu wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login