Showing 6001 words to 9000 words out of 185502 words
ta had'a kayansu dan tafiya bata kula da su ba yace "Na fad'a a gaban Hajia ma bare kuma kai."
Hajia ce tace "Ni ai murna zanyi da faruwar haka, tunda arzik'i ne zai ci uban na da."
Dariya sukayi sai sheikh daya sake sunkuyar da kai dan bai d'auka tana jin su ba, suna had'a kayan suka fito da sauri masu tsaronshi su biyu suka karb'i kayan hannunshi wanda ya karb'a a hannun Hajia, dake a mota biyu suka fito yau dan wajen aikinshi zai tafi yasa d'aya motar masu tsaronshi ne d'ayar kuma shi da su Ashraf da Hajia har suka isa gida, sai dai bai shiga ciki ba saboda lokaci ya tafi sosai.
*Maryam*
Hutun minti talatin aka fito dan mai buk'ata yayi buk'atarsa, a cikin ajin suke zaune tare da k'awayenta suna ta hira inda wasu ke cin abinci, ita ma robar alala ce gabanta inda Asma'u ke kallonta da mamaki dan bata d'auka zata iya cinye wanda ta siyo ba, saida ta ga ta ida ta d'auki ledar pure water ta tsotse ta jefar Asma'u tace "Masha'Allah, lallai yau na tabbatar Mimi ba matar k'aramin mutum bace ke."
Harara ta wurga mata tace "Ban gane ba, me ya faru?"
Saida ta kalli robar ta kalleta tace "Alalar dala arba'in fa kika cinye ke kad'ai."
Tsaki tayi ta sake hararenta tace "Miye a ciki? Kud'inki ne ko nawa?"
Girgiza kai tayi tace "A'a naki ne, Allah baki hak'uri."
Tab'e baki tayi ta kalli wacce ke kusanta tare da zura mata hannu tace "In ga wayarki Jamila na tura vid茅os."
Wayar ta mik'o mata tana fad'in "Ban da sababin vid茅os fa har yanzu, na wa'azi ne kawai aka turo min jiya."
Saida ta fara dubawa kafin ta kalleta tace "Wai duk wa'azin shi ne kika turo?"
Da murmushi tace "Eh, yana birgeni wallahi saboda ya iya wa'azi."
Tab'e baki tayi tace "Shi ne ke birgeki? Ko kuma wa'azinshi? Ko kuma ilimin da Allah ya bashi?"
Cikin rashin damuwa tace "Duka ma wallahi." Dariya 'yan matan suka saka inda Asma'u tace "Da alama dai Jamila da sheikh Abdul Waheed zai ce yana sonki da gudu zaki auresa."
Da sauri ta kalleta tana dariya tace "Wallahi tsaf kuwa, ai ko bai fad'a ba da zan ganshi ido da ido ma ni saina rok'eshi ya aureni."
Da mamaki Maryam ta kalleta tana nuna wayar tace " *Tsohon*? A hakan ma ke zaki rok'esa?"
D'auke kanta tayi tace "Tabb'! Lallai da kin wulak'antamu."
Jamila ce ta turo baki tace "Wallahi b芒 tsoho bane, dubeshi da kyau fa."
Tab'e baki tayi tace "Na gani, amma akwai wa'azin da yayi yake bayanin wani abu daya faru, a lokacin ya ce yana da shekara ashirin da shida, ni kuma Abba na ya fad'a min yana neman auren mamana aka yi wannan al'amarin, a lokacin shi yana ashirin da shida shi ma, hakan na nufin shekarunsa *arba'in da bakwai* fa, kinga kenan tsoho ne tunda sa'an babana ne."
Dariya sukayi sai wata dake kusa da Asma'u tace "Gaskiya indai hakane tsoho, fuskarshi ce dai bata cika nunawa ba."
Asma'u kam cewa tayi "To ko ni dai da zai aureni wallahi zan amince, tunda yana da ilimi."
Maryam kam tab'e baki ta sake yi tace "Allah ya rabani na rasa wa zan aura sai sa'an babana."
Jefawa Jamila wayarta tayi ta mik'e zata fita dan wanke hannu tana fad'in "Wannan ai lalata k'uruciyarku kuke son yi."
K'arar da wayarta tayi yasa Asma'u d'auka tana dubawa tace "Mimi Mas'ud ne ke kiranki."
Shiru ta mata saida ta wanke hannayen ta dawo ta zauna ta karb'i wayar, datse kiran tayi tare da kashe wayar gaba d'aya, Asma'u dake kallonta tace "Me yasa kika kashe?"
Kallonta tayi tace "Shi mahaukacin ina ne da zai kirani yanzu bayan yasan ina makaranta."
Jamila ce tace "Watak'ila dan yaga lokacin hutu ne, wallahi ya damu dake mutumin nan Mimi."
Banza tayi da su hakan yasa Asma'u cewa "An tab'o mata hirar data tsana a duniya, kuyi harkar gabanku kawai."
Tab'e baki Maryam tayi tace "Da dai yafi kam."
Wata hirar aka shiga saidai Asma'u kam ta damu sosai da abinda Maryam d'in ta fad'a mata cewa Alhaji Saminu ya bata kud'i, dan haka hankalin kowa na tafiya wani wurin ta sake gyara zamanta tace "Mimi, me yasa da Alhaji Saminu ya baki kud'in nan kika karb'a? Ba kya jin tsoro ke?"
Kallonta tayi tace "Tsoro kuma? Na me?"
D'an numfashi ta sauke sai kuma tace "Idan fa yace yana son ki?"
Wata dariya ta kece da ita har da d'an bubbuga table d'in kafin ta tsagaita ta kalleta tace "Ya ce yana so na? To sai me? A gaban idonsa zan fad'a masa ba zan iya aurensa."
Ba tare data d'auke idonta daga kanta ba tace "Me yasa? Amma naga mutumin kirki ne."
Wawan tsaki taja tace "Ke yanzu dan ina mahaukaciya sai na yi soyayya da Saminu? Bayan kasancewarshi tsoho fa kin ganshi k'ato da shi, me zanyi da shi ni kam."
Murya k'asa k'asa tace "To indai hakane ki daina karb'ar komai daga hannunshi dan Allah, ni wallahi tun rannan da muka je gidan naga ya cika kallonki da yawan kiranki na ji ina zargin akwai abinda yake nufi a kan ki."
Yatsina fuska tayi tace "Wannan shi ya shafa wallahi, ni ko a jikina."
Jin an busa usur d'in dake nuna lokaci ya k'are kowa ya shiga aji yasa Mimi sassauta murya tace "Malam yace da yamma wajen walimar sabka zamu tafi, da uniforme zamu je ko kayan gida?"
Ita saida ta sassauta murya tace "Bari a tashi sai mu tambaya mu ji."
Shigowar malamin yasa akayi shiru babu mai magana sai mayar da hankali a kan shi da kowa yayi, inda duk wani mai waya tuni ya kasheta dan an hana zuwa da ita, masu taurin kai ne ke tahowar da ita.
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:50 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*4*
A marairaice ya kalli Hajia yace "Dan Allah Hajia ki barni na fita, wallahi na fi jin dad'i idan ina waje."
Ita ma a marairaice tace "Ashraf ba wai na hanaka fita bane, ka jira jikinka ya k'ara sauk'i mana."
Kamar zaiyi kuka yace "Hajia na ji sauk'i fa, ba abinda nake ji a jikina yanzu."
Da alamar tuhuma tace "Ka tabbatar?"
Cike da tabbaci yace "Na tabbata Hajia, insha'Allah babu abinda zai faru ki kwantar da hankalinki."
Jinjina kai tayi tace "Ashraf burina d'aya ne a duniyar nan naga ka samu lafiya, ciwon cikin nan naka yana d'aga min hankali fiye da tunaninka."
Murmushi ya mata yace "Kenan Hajia baki da burin ganin nayi aure?"
Turo baki tayi tana dukanshi a kafad'a tace "Dan na ga kayi auren har 'yan mata na dinga lissafa maka dake cikin ahalin nan, amma ka rufe ido ka nuna baka so basu ma ka ba."
Jujjuyar da kan shi yayi yace "Hajia ai duk cikinsu ne babu wacce ta dace da kalar tsarina."
Baki sake da mamaki tace "Iyeh! Wato har wata kalar tsarinka kake fad'a? To fad'i na ji ko zan iya samo maka."
Dariya yayi ya gyara zamanshi yace "Hajia ni wayayya nake so mai ilimi, 'yar zamani da kuma tsafta wacce ta iya kwalliya, sannan wacce zata dinga kwantar min da hankali."
Rik'e hab'a tayi tace "Ashraf matar sakawa a gaban mota kake nema?"
Tintsirewa yayi da dariya ya mik'e ya fita har da d'an gudunshi har ya bar gidan a galleliyar motarshi.
*Sheikh*
A hankali yake juya kujerar kanshi na kallon sama amma idonshi rufe, hannunshi rik'e da katin gayyatar da aka kawo masa daga wata islamiyya da zasuyi sabkar Alqur'ani mai girma, jefi jefi ya kan sauke ajiyar zuciya saboda tunanin da zuciyarshi ke bijiro masa, dan gaskiya yana matuk'ar son ganin ya k'ara aure, ba dan Hafsat ta gaza ba ko baya jin dad'in zama da ita, kwad'ayin ladar da zai samu yake, yana son ganin shi ma kimarshi ta k'aru fiye da ta mai mace d'aya. Saidai abinda ke hanashi bai wuce tunanin 'yan matan yanzu ba, yaran da ko iyayen da suka haifesu basa iya tank'warasu, yaran da idonsu a tsaye a kai saman kai suke nuna maka baka waye ba, yaran da basa da hak'uri da juriya, yaran da waya da k'awaye suka fi komai mahimmanci a garesu, hakan yasa yake d'an dakatawa wasu lokutan, saidai kamar yanda yanzun zuciyarshi ke raya masa kawai zai rufe ido ne ya je ya nemi alfarmar malamin kan ya duba masa yarinyar daya yarda da tarbiyarta da nagartar iyayenta, idan ya masa haka shi da kan shi zaiyi yak'in neman k'uri'ar aurenta. A hankali ya bud'e idonshi tare da d'ora yatsanshi a kan kybord d'in na'urar ya turawa sakataranshi sak'on ya amince da gayyatar kuma zai je da kan shi da misalin 04:30 na yamma.
*Maryam*
12:00 cif na rana suka taso, a hanya ma dai hirarsu bata fahimtar juna bace tsakaninta da Asma'u, dan akwai banbanci ra'ayi sosai a tattare dasu, tana cikin b'acin ran da Asma'un ta k'unsa mata a kan maganar wani saurayi da ita har ta manta da lamarinshi ma wai ta ci kud'inshi dayawa, bata tsoron ya k'i yafe mata? Shi ne fa ta hau take ta masifa take fad'in "Ai bani na ce ya so ni ba, kuma ni ban tab'a bud'a baki nace a bani ba saidai kai ne ka d'auka ka min."
Mas'ud suka tsinkaya a kan dallelen mashin d'inshi yana danna wayarshi, wani uban tsaki ta kuma ja tace "Shi kuma me yake mana a k'ofar gida?"
K'wafa tayi hakan yasa Asma'u cewa "Sai ma kin tambaya? Wurinki ya zo mana."
Tab'e baki tayi tace "Duk da dama ina son ganinshi, amma ba zan ganshi yanzun ba, dan ni ba'a min haka wallahi."
Rab'a Asma'u tayi zata giftata ta wuce tayi saurin rik'e hannunta tace "Ina zaki tafi Mimi? Karki masa haka mana."
Tsaki ta kuma yi tace "Ke sake ni, shigewa zanyi na barsa mana."
Da mamaki tace "Amma kinsan wurinki ya zo ko?"
Fizge hannunta tayi tare da wucewa da sauri ta barta tsaye tana mamakinta, ai kam ko kallon kusurwar da yake ba tayi ba ta shige cikin gidan tana mitar ita zai wa dirar mikiya kamar wani ubanta? Shigewarta kawai ya gani hakan yasa shi tsayawa sagale da baki yana kallonta, saida ya tabbatar ita ce dai kafin ya d'an d'auke kan shi yana basarwa, kad'an daga aikin Mimi kenan, ya rasa gane wane irin so yake mata da har yake iya shanye komai daga gareta haka, ta masa wulak'anci ta ja masa aji ta yarfa shi fiye da kima, amma ya jure ya nace saboda tunanin ta kusa zama tashi, lokaci kad'an ya rage shi ma ya fara nashi salon mulkin, duk da dai ya tabbatar ba zai iya muzguna mata ba, amma saiya rama ko da na kwana d'aya ne dan taji idan da dad'i.
Shi yasa baya nuna bai ji dad'i ba idan ta b'ata masa, ko ba komai Mimi ta yi, ta had'u iya haduwa da kowane namiji zai so samunta a matsayin ta shi, ga ta da wani siddabarun saurin dukan k'irjin namiji, indai kana da rai da lafiya sannan tsufanka bai kai k'adamin da baka sha'awar mace ba, to idan kaga Mimi zuciyarka zata amsa ma ka saidai kayi shiru da bakinka kawai, ba wai tsananin kyan da take d'auke dashi bane a'a, wata irin halitta ce da ita da kuma yanayin dake saurin d'ad'a namiji a k'asa warwas. Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin murmushi yana mai jinjina lamarin ubangiji, wai yarinyar data fito daga gidan nan na k'asa, sannan ta fito daga tsatson wadanni har take yagawa mutane rigar mutumcinsu? Lambarta ya shiga kira amma sam ta k'i d'agawa dan a lokacin ma wanka ta shiga yi.
Tana fitowa ta saka riga da siket na atamfa ta feso turare kafin ta d'auki gyale ta yafa ta d'auko wayar ta cire layinta da card ta fito, a farfajiyar gida ta samu mamanta zaune ta zuba tagumi, tana kallonta tace "Mama lafiya?"
D'agowa tayi ta girgiza kai tace "Ba komai, ina kuma zaki je?"
Yatsina fuska tayi tace "K'ofar gida, Mas'ud ne a waje."
Jinjina kai kawai ta yi ita kuma ta fita, cikin takonta mai birgewa ta k'araso ta tsaya tare da d'ora hannunta akan hannun mashin d'in ta juya mishi baya, kakkauran hannunta ya kalla wanda ya tabbatar zai yi matuk'ar kyau da awarwaron zinare kafin ya kalli k'eyarta yace "Ko dan sarauniyata tafi kowa sanin hushinta shi ne silar shiga damuwa shi ya sa take son tsokano damuwata?"
Ba tare data juyo ba tace "Idan gaske ne me yasa kai ma za kayi abinda kasan baya daga cikin tsarina?"
Murmushi yayi mai sauti yace "Na d'auki laifina da hannu biyu, a gafarceni ba zan k'ara ba, dama na zo ne saboda tun jiya nake kiranki, amma Mimi kin k'i d'aga min waya ban san me yasa ba? Shi ya sa na zo saboda ina da muhimmiyar magana da ke."
A hankali ta juyo ba tare data d'auke hannunta ba tace "Wace irin magana kuma?"
Leb'enta ya bi da kallo wanda bata shafawa komai ba, hakan yasa na k'asa tsayawa a kalar pink d'inshi sosai na sama kuma bak'i dashi, saidai na k'asa ya fi na sama girma da d'an tsayi daidai da fuskarta, numfasawa yayi yace "Dama akan maganar aurenmu ne..."
Da sauri ta katseshi tace "Aurenmu? Aka ce me?"
D'an zaro ido yayi yana mata murmushi yace "Mimi ko dai kema kin matsu?"
Yatsina fuska tayi tace "Ina jinka."
D'orawa yayi da cewa "Dama jiya malam sun had'u da Alhaji a wajen karatu, shi ne suka tsayar da ranar da za'a kawo kaya a saka mana rana, nasan malam ba zai fad'a miki ba sabida ke 'yar fari ce shi yasa na zo na sanar dake."
Wani galala tayi ta bud'e idonta da kyau tace "Na ji dad'i daka fad'a min, dan kaga da sunyi kuskure."
Da mamaki yace "Kuskure kuma? Na me?"
Ba tare da damuwa ko d'aya ba tace "Kuskuren aurar dani mana ban shirya ba."
Da wani sabon mamakin yace "Baki shirya ba kuma? Mimi sai yaushe zaki shirya?"
Gyara tsayuwarta tayi ta mik'o masa wayar hannunta tace "Ga wayarka, kayi hak'uri Mas'ud a gaskiya ban tashi aure ba yanzu, idan ma na tashi ba zanyi da kai ba saboda wasu dalilai."
Girgiza masa kai ta sake yi tace "Kayi hak'uri, Allah ya baka wacce ta fini."
Da sauri ya shiga kakkarwa zai sauko daga mashin d'in kamar zai kifa ya fad'i, idonshi da suka rine sukayi ja ya shiga lumshewa yana fad'in "A'a Mimi! Mimi dan Allah tsaya kiji, Mimi..."
Da sauri ya sha gabanta tare da durk'ushewa yana kallonta hawaye na sauka a idonshi yace "Mimi me na miki? Fad'a min wallahi zan gyara, bana so na rasaki Mimi ke ce rayuwata, dan Allah kiyi hak'uri kinji, wallahi idan ma auren ne ba kya so na janye, zan jiraki Mimi har sanda kike so sai ayi."
Girgiza kai tayi tace "Mas'ud ka gane wani abu, idan muka ci gaba a haka zan yaudareka ne, shi fa aure ana ginashi ne da soyayya, ni kuma har yanzu bana jin sonka a cikin zuciyata."
Tsam yayi tare da mik'ewa tsaye yana kallonta yace "Ba kya so na? To Mimi watannin da muka share muna soyayya fa? Duk murmushi da kalaman da kika min fa? Dan Allah Mimi ki ce wasa kike min."
Idonshi ta kalla tace "Kayi hak'uri, dama gudun kar na wulak'anta ka yasa tun farko ban fad'a maka ba, yanzu ma nasan zaka d'auka yaudararka nayi, amma ba haka bane gaskiya ce na fad'a maka."
Da mamaki ya girgiza kai ya juya ya kalli yanda idon mutanen dake kai kawo duk idonsu a kan su, sake kallonta yayi yana ci gaba da girgiza ai yace "Wulak'anci? Ai kin riga da kin gama wulak'antani, Mimi ki fad'a min wani dalilin da yasa kika guje ni, idan ba haka ba zan zargeki da cin amanata."
Ajiyar zuciya ta sauke ta sake kallon fuskarshi tace "A gaskiya bana sonka ne." Rab'ashi tayi ta wuce tana fad'in "Kayi hak'uri."
Juyawa yayi ya bita da kallo harta shige, ji yayi wasu hawayen sun sake taho mishi, d'an tsaki yayi na jin haushin kan sa, ji yayi kamar ya d'auki takalminshi ya jefa cikin gidansu, amma zuciyarshi sai b'ari take ga zazzab'in da yake jin zai rufe shi, haka ya juya yana saka wayar a aljihu ya hau mashin d'inshi y'a bar unguwar.
Tana shiga ta kusa da mamanta ta zauna tana fad'in "...
Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.
Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.
Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa