Showing 177001 words to 180000 words out of 185502 words
a ganinki dan bana son ta ne na auroku? Ai da tsohuwar zuma ake magani."
Da sauri ta kalleshi tace "Lahhh! To sabuwar fa?"
Kyab'e fuska yayi yace "Tafi haukatamutum."
Tintserewa tayi da dariya ta d'auki jakarta ta rataya kafin suka fito a tare, Iya na had'a ido da ita ta wurga mata harara tana d'auke kai, Mimi ma d'auke kai tayi tace "A zo gidana kuma a harareni."
Kallon sheikh tayi tace "Yallab'ai ina angulayen nan suke wai?"
B'oye dariyarshi yayi yana kallon Iya yace "Iya kiyi hak'uri ta tsaidake."
Kallon Mimi yayi yace "Ku je dreba na jiranku."
Mik'ewa Iya tayi tana fad'in "Nagode Allah daya zamana ana allura a awon fari."
Zaro ido Mimi tayi tana kallonta sai kuma ta kalli sheikh, girgiza masa kai tayi tace "Um um! Wai da gaske ana allura?"
Lura da Iya zata b'allo musu aiki yasa d'an saisaita murya yace "Ina jin fa wasa take miki."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Haba, tunda ai ka ga bana jin ciwon komai ko?"
D'aga kai yayi alamar e, juyowa Iya tayi ta kalleta da kyau sai kuma ta gyara tsayuwa tace "Ke! Doguwar riga ce kika saka?"
"E." Ta fad'a tana kallon kan ta, cikin fad'a Iya tace "Ke bana son k'ananan iskanci, awon cikin ne zakiyi mje da doguwar riga, to ya zakiyi idan za'a miki awon kwance? So kike ni ma d'in a ce mahaukaciya ce kamar ke?"
Cikin jin haushi Mimi tace "Kamar 'ya? To me rigata tayi kuma? Haihuwar ce zan je yi?"
Matsowa tayi irin a zafaffen nan tayo kanta tana fad'in "Ke ki kiyayeni wallahi."
Baya ta ja sai sheikh daya kalleta da alamar gargad'i yace "Je canza kayan ki fito."
Juyawa tayi ta shige d'aki inda suka bita da kallo, a sanyaye Iya ta kalli sheikh dan sai taji ma ya fara bata tausayi, a ladabce tace "A yi ta hak'uri dan Allah, yarinyar ce kamar mai shafar aljanu wani zubin, ka d'an dinga tofa mata ayatul kursiy wasu lokuta."
Murmushi sheikh yayi yace "Insha'Allah."
Suna nan tsaye ta fito sanye da riga da zane mai kamar siket ya fito mata da tsarin zubin k'ugunta sosai, tuni sheikh ya bita da kallo "Lahaula walaquwatta illa billahil-aliyul azim!"
Sai kuma ya had'e yawu ya ci gaba da kallonta tana saka hijabinta da d'aura nik'ab, kallon Iya tayi tace "Sai mu tafi ko?"
Harara Iya ta banka mata tayi k'wafa, ita ma hararen gefenta tayi tace "Wannan awon ni sai na ce ma na fasa."
Cikin sub'atar baki Iya dake daf da fita tace "Yo fasa mana, ni na ce kiyi cikin ko a jikina yake?"
Da sauri Mimi ta juya ta kalli sheikh daya d'an zaro ido sai kuma ya kalleta ya saki murmushi, cikin fashewa da kukan sangarta ta nuna Iya data fita tace masa "Ka ji ko? Wai ita ce tace nayi cikin?"
Matsawa yayi kusanta yana share mata hawayen da ko alamarsu babu yana fad'in "Yi shiru haba rabu da Iya, kinga fa so take ta tsufar min dake, shiyasa take yawan sakaki jin haushi da surutu, daina kukan kinji ko tawajena."
Turo baki tayi tace "To na yi, amma ka min alk'awarin kafin na dawo zaka siya min tsire.?"
Jinjina kai yayi yace "Zan siya, kuje Allah ya tsare."
Juyawa tayi ta nufi hanyar fita tana fad'in "Kuma ka kira Rakiya ka fad'a mata wallahi ban da allura."
"To." Ya fad'a yana kallonta har ta fita, yana hangensu daga nan ma yana kallon bakunansu na ta motsawa alamar dai sun d'ora a inda suka tsaya, girgiza kai yayi ya k'arasa ya rufe mata d'akin ya kulle kafin ya nufi d'akin Hafsat, dan nutsuwa yake son samu yayi bacci cikin sallama tunda an bashi hutu a wurin aikin. A gidan nan kuma indai nutsuwa mai sunan nutsuwa yake so da hutu to fa dole sai wajen uwar 'ya'yansa, mahutarsa kuma annashuwar gidansa wato Hafsat.
Amma Ryam! Ryam! Ryam! Zuciya ce kawai da abunda take so, b芒 dan haka ba irin gwaramar da yarinyar ke had'a masa da babu soyayya to tabbas tuni ya yanka mata ticket, idan ba zuwan Ryam ba wa ya tab'a gigin taka rawa a gidanshi, sai gashi a gaban idonsa ake yi tun yana kakkawar da kai har ya fara kallo wani lokacin ma yaji ta birgesa har ya juye da ita a cikin kogi su shiga iyo.
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:59 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*58*
*A gurguje*
Yau Mimi ce ta bud'e idonta k'afarta akan babbar birnin k'asar Duba茂 wato Abu Dhabi, lokaci lokaci sa茂 mta kalli sheikh ta tintsire da dariya, shi kuma sai dai ya girgiza kai yana kallonta kawai, da haka suka isa babban masaukinsu suka shiga wanka kafin su zauna cin abinci, buga kai tayi a k'asa wallahi ba zata ci wannan kalan abinci ba, da k'yar ya lallab'ata ta ci gasassar kazar da ita ma tace babu d'and'ano ba yaji ita kawai ba dad'i.
Da fari dukansu sun d'auka ko rashin sabo ne da tafiya ya jawo mata zazzab'i da kuma ciwon k'afafun, amma data kwana uku babu sauki sai ya nemi su tafi asibiti, data nuna a'a k'yaleta kawai yayi dan ba zai manta da suka tafi awo da Iya ba, iya d'ibar jinin da ake na kan yatsa ma bata yarda an mata ba, haka aka zo allura bata tsaya ba kafatanin asibitin saida aka san Mimi ta halarta, mutane dayawa sun sa baki kan ta tsaya a mata dan lafiyarta da ta abonda ke cikinta, amma bata saurari kowa ba ta ce gida zata koma, haka wasu suka dinga fad'in ai tayi raguwar dubara tunda ta yarda ta d'auki cikin, zasu su suka ga yanda zata haihu d'in. _(Ina nak'udar Khalid na ga mai cikin da bata son allura,馃ぃ haka na manta da nak'uda nake na shiga kallonta ana neman tausheta a mata allura, wallahi a k'arshe sai likitocin ransu ya b'ace suka ce mijinta ya d'auki tsiyarshi馃ぃ su basu wuri)_
Haka sheikh ma sukayi saida rana da suka dawo gida aka kira Hajia tare da Rakiya ta mata abinda ya dace shi ma saida sheikh ya had'e fuska ya nuna sam bai san ta zai ma kikkifa mata mari kad'ai ta tsaya.
Magani dai yake mata dubara a sauk'ak'e tana sha, saida ta d'auki sati a haka kafin jikinta ya warware da kyau, daga ranar fa ta ce k'afa mai na ci ban baki ba? Sa茂 ta bud'e shafin yawo ita da sheikh, soyayya suke bugawa mai rai da lafiya mai cike da yarinta da wauta a ciki, tunda suka zo sheikh zanzarewa yake da k'ananan kaya irin wanda suka dace da shi dattijon arzik'i.
Yanzu kam ya fara zarmewa shi ma, dan ranar farko da suka fara fita Mimi b'oye fuskarta take wai kar a ganta a d'auka ko kakanta ne? Da fari maganar cakarsa tayi sosai a zuciya, amma daya d'auki hak'uri ya d'ora bai san sanda ya sureta ba ya labta a bayanshi, wutsil wutsil ta fara yi sai ya sauketa shi kuma ya k'i saida suka yi nisa, har saida ta kai ta gyara kwanciyarta a bayanshi tayi shiru dan ta fahimci babu ma wanda ya kula da su, tun daga ranar ne ya zama ko fita sukayi bata shakkar tab'a shi a wani sassa na jikinshi shi ma baya jin d'ar d'in tab'ata ko sumbatar goshinta ko kunci.
Wasa wasa sai ga Mimi ta sake wata k'iba masha'Allah wacce ita kan ta ta fara jin ta fara mata nauyi yanda take ganin idan ta k'ara fiye da haka zata takura mata, shi kan shi sheikh da wasa wasu lokutan yake fad'a mata "Ryam ki dakata da k'ibar nan haka dan Allah, bana so ki kai matakin da ba zan iya d'aukarki ba, kinga dai tsufa nake k'arawa ke kuma kina k'ara k'iba."
Marairaicewa kawai take tace "To ya zanyi? K'ibar ce lokacinta ya zo ni kuma ban tara ko sisi ba, zan zubawa sarautar Allah ido kawai."
A haka suka kwashe wata d'aya cir a k'asar Abu Dhabi wanda a wannan lokacin har Paris saida suka lek'a kwanansu hud'u, zuwa lokacin kuma shirye shirye ya kam-kama sosai saboda gabatowar watan azumi, hakan yasa suka juyo zuwa dawowa k'asarsu dan duk yanda abubuwa zasu taso ma sheikh da zasu iya sa shi barin k'asa ban da wannan watan, ko ma menene ya kan hak'ura d shi dan ya samu damar azumtar watanshi a cikin iyalenshi da kuma jama'arshi.
*Ramadan*
Kaf ya gama da duk wata buk'ata ta gidanshi, kama daga kayan sallahnsu zuwa kayan abinci da yasan ya kan tanada na bud'a baki da suhur. Dan haka suka zauna duka a falonshi bayan ya kalli kowace yace "Muna saka ran tashi da azumi gobe, mu d'ora niyyar azumtarshi, idan Allah yasa mun riskeshi mu tsawwala aiyukanmu na alkairi, kada mu raina aikin lada komai k'ank'antarshi, mun fahimta?"
Jinjina kai duka sukayi inda ya kalli Hafsat yace "Kinsan komaai Hafsat a game da watan nan, Mimi ce bak'uwata a yanzu."
Ya fad'a yana kallon Mimi dake ta jijjiga k'afafunta dake mata masifar ciwo, d'orawa yayi da "Sai kinyi hak'uri Mimi da yanda zaki sameni a yanzu, duk watan azumi abubuwan sukan taru su sak茅 min yawa, hakan na jawowa iyalina rasa kaso mai yawa a cikin lokacina, amma idan kikayi hak'uri kamar yanda 'yar uwarki tayi, zaki zo ki saba ke ma har ma wata rana ki k'arfafa min gwiwata."
Saida ta cije leb'enta na k'asa sosai kafin ta sauke numfashi, nauyi sosai take ji a jikinta wallahi gaba d'aya bata jin dad'in jikinta, a sanyaye tace "Ba komai Abban Humaira, Allah ya mana jagora, Allah ya taimakeka a dukan lamuranka ya bada sa'a."
"Ameen." Ya fad'a da farin ciki tare da kallon Hafsat yace "Ba wani abu dana manta ban yi ba? Ko kuma kuke da buk'atarsa?"
Girgiza kai tayi da fara'a tace "Ba komai yallab'ai, ban sani ba dai ko uwar yan hud'u."
Tare suka kalli Mimi da ita ma ta kalli Hafsat d'in suna mata dariya, turo baki tayi cikin shagwab'a tace "Ka gani ko? Wai saita dinga kirana uwar hud'u?"
Dariya ya sake fashewa da ita yace "Haka ta gani ai."
Sake turo baki tayi ba tace komai ba ta kawar da kai, cikin dariya yace "To Hajia ba abinda kike buk'ata?"
Girgiza kai tayi tace "Babu, idan ma akwai ba zai wuce yakuwa da nake son ci ba, kuma zan sa su Yaseen su kawo min."
Murmushi yayi yana girgiza kai yace "Nagode Allah da ba'a ce na je na tsinko da kai na ba."
Hafsat ce ta kalleta ta k'yabta mata ido tace "Tab'! Da ni ce kam sai ya cirota da kan shi."
Wani kallo Mimi ta mata ta murmusa tace "Bar shi auntyna, akwai abinda zai min ne na musamman shi."
Zaro ido yayi yace "Ba dai ni zan kwad'a miki ba ko?"
Fari ta masa da ido tace "Wannan ai mai sauk'i ne."
A hankali ya kanne mata ido ya d'auke kan shi tare da mik'ewa tsaye, har zai fita ta marairaice tace "Dan Allah taimaka min na koma d'aki na kwanta yallab'ai."
Cike da kulawa da tausayi Hafsat tace "Har yanzu k'afafun basu daina ba?"
Cike d jimami tace "Aunty idan na sha maganin ma kamar k'arawa yake."
Mik'ewa tayi ita ma tsaye tace "Allah ya sauk'ak'a miki, ya baki ladar."
"Ameen." Suka fad'a tare da sheikh daya kama hannayenta ta mik'e tsaye, a hankali suka shiga takawa tana jin kamar tana takawa akan garwashin wuta, haka suka k'arasa d'akinta zai zaunar da ita tayi tsaye tace "Um um!"
Kallon tuhuma ya mata yace "Me?"
Cikin shagwab'a tace "Ni d'akina nake so nayi bacci."
Kama hannunta yayi yace "Muje to."
Mak'ale kafad'a tayi tace "Sai dai ka d'auke ni."
Girgiza kai yayi yace "Nawa zaki biya?"
Kashe masa ido tayi tace "Ka yarda na shayar da kai?"
Da sauri ya matso da ita kusa da shi yana mata wani mayen kallo yace "Zan fi son haka fiye da komai, d'an bani naji."
Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um, sai mun shiga d'aki ko."
A hankali yasa hannunshi cikin rigarta daga sama ya fito da nononta, sannu sannu ya kai harshenshi kan nononta yana zagayawa da harshenshi daga haka har...
*Bayan wata hud'u*
Wahala iya wahala Mama ta yi ta a wannan ciki har kawo yau da take nak'uda, dama ita ke haihuwa da kan ta yanzu ma haka likitocin suka tabbatar zata haihu, saidai yau kwana biyu kenan tana ta nak'uda a asibiti shiru, Abba hankalinsa ya tashi ya fita hayyacinsa, dan kamar dai yanda tayi nak'udar cikinta na farko ne na Mimi.
Suna zaune dukansu a tabarmar da suka shinfid'a wayar Abba tayi k'ara, yana dubawa ya ga lambar sheikh ce, da sauri ya kalli malam dake gefenshi yace "Kunga malam sheikh ne ke kira, bana so yarinyar nan ta ji halin da mahaifiyarta ke ciki, shiyasa tun shekaran jiya ina ganin kiranta bana d'agawa."
Malam yace "Gaskiya ne, ga Mimi da saka abu a rai ga kuma ita ma halin da take ciki."
Iya ce tace "To ka d'auka mana tunda ba ita bace."
Da sauri ya danna ok ya d'ora a kunne yana rangad'a sallama, fashewa tayi da kuka cikin tashin hankali tace "Abba me nai maka baka d'aga kirana? Abba kwana na uku ban da lafiya shi ne nake ta kiranka dan na nemi gafararku, amma baka d'aga kirana."
K'urawa su Iya ido yayi sai kuma ya sunkuyar da kai a sanyaye yace "Uwata me yake damunki?"
Cikin shashek'ar kuka tana sunkuyar da kan ta ita ma tace "Abba jikina ne gaba d'aya babu dad'i, k'afafu na sun kumbura sosai, jiya da muka je asibiti sun ce ban da jini ne."
Sai kuma ta sake fashewa da kukan da yasa sheikh sake rumgumata a jikinshi yana jin kamar zaiyi kukan shi ma, dan sosai yake tausaya mata halin da take ciki. Da k'yar Abba ya b'oye damuwarshi yace "Kiyi hak'uri uwata, zan zo na dubaki da kaina to."
A raunane tace "To Abba, yaushe zaka zo?"
A hankali yace "Gobe." Sai kuma yace "Ina sheikh?"
Mik'awa sheikh wayar tayi tana fad'in "Gashi."
Karb'a yayi cikin nutsuwa yayi sallama, sama sama suka gaisa dan kowa da abinda ke damunsu na larurar matan na su, daga b'angaren Abba ne yace "Kwanan biyu yau a asibiti mahaifiyarta na kan gwiwa ne, bana so ta ji dan bansan wane hali zata shiga ba, gashi ita ma tace bata da lafiya."
A hankali sheikh ya zameta a jikinshi ya mik'e tsaye ya shiga uwar d'akinshi yana fad'in "Subhanallah, Allah ya bata lafiya, Ubangiji Allah ya sauketa lafiya, amma ai da ko ni an sanarma, amma ba komai insha'Allah zan zo asibitin yanzu."
Godiya Abba ya masa kafin sukayi sallama ya fito, kusanta ya zauna ya d'auki madarar daya kad'a mata yace "To karb'i ki shanye, kin min alk'awarin zaki sha idan na kira miki Abba da ma."
Yatsina fuska tayi tana sako da hawaye ta rik'o hannunshi gam gam tana kallon fuskarshi tace "Sheikh tsoro nake ji, tsoro ya kamani sosai akan cikin nan, ji nake kamar ba zan rayu ba wallahi, sheikh ka yafe min ka ji, na san nayi maka abubuwa da dama..."
Da k'arfi ya fizgo kan ta ya d'ora a k'irjinshi ya k'amk'ameta, numfashi mai zafi ya shiga saukewa a saman kan ta daya dunk'ule sosai ya cukurkud'e saboda rashin gyara dan halin da take ciki ya fi k'arfin wasa, yanda zuciyarshi ke suka tana k'onewa, tausayinta na ratsa duk wata gab'a ta jikinshi sai ya ji idonshi sun cika taf da k'walla, a hankali ya lumshe idonshi sai kuwa hawayen suka sauko a kumatunshi, hakan yasa shi k'ara rintse ido ya furta "Ya isa haka Ryam, baki min komai ba kinji, na yafe, na yafe miki, ni ma ki yafe min dan Allah, duk ni ne silar shigarki wannan halin, ki yafe min dan Allah."
D'ago kan ta tayi suka kalli juna tana zaro ido tayi saurin saka hannunta ta share mishi hawayen tana fad'in "Lahhhhh! Sheikh? Kuka kuma? Haba dai, sai ka karya min zuciyata ai."
Sake kwantawa tayi a k'irjinshi tayi luf tana fad'in "Ni ma baka min komai ba, kawai ka tayani da addu'a na sauka lafiya."
Yana k'ara k'amk'ameta shi ma yace "Ina ta miki addu'a Ryam d'ina, tunda kika samu cikin nan nake miki addu'ar sauka lafiya, insha'Allah zaki haihu lafiya."
Shiru sukayi babu wanda ya sake magana saida ya ji tana sauke numfashi a hankali a hankali alamar bacci, cikin nutsuwa ya zameta daga jikinshi ya gyara mata kwanciyarta, d'aukar k'afafunta yayi da suka zama sumtuma sumtuma ya d'ora a kujerar, tsaye yayi yana k'are mata kallo yanda ta sauya kamar ba ita ba, tayi fuyau da ita alamar babu jini a jikinta, babbar damuwarshi da tashin hankalinshi da suka jawo masa rage walwala da cin abinci bai wuce yanda Rakiya ta fad'a masa wai jinin Mimi ya hau a awon ta na satin daya wuce, jinin Mimi ya hau kamar ya? Me ya kawo mata hawan jini? Ga matsalar rashin jini ga ta rashin cin abinci ga kuma kumbura da kullum k'afafunta ke k'arawa, ga nauyi da take jajen jikinta na dad'a yi mata kullum, hatta da alwala fa yanzu indai yana gidan sai ya taimaka mata, akwai ranar da taimama ya ce tayi dan shi baya gida kuma ta kasa ta shi a inda take ga lokacin sallah n wuce kawai yace tayi taimama a waya.
Madarar ya d'auke ya kai fridge kafin ya rufo mata k'ofar da makulli saboda ko Munzeer ba zai so ya tasheta ba, dan baccin kan shi ba samu take yi da dare ba, sauk'inta d'aya da Hafsat ta