Showing 81001 words to 84000 words out of 185502 words
*Mu ci gaba*
Da sauri Mimi ta d'ago ta sauke ido akan Iya Delu data fashe da kuka, sallalamin da gidan ya d'auka yasa Mimi ta shiga bin kowa da kallo, yanda ta bud'e baki tana lumshe ido alamar jiri na d'ibarta ne yasa Sahura saurin rik'eta ta shiga d'aki da ita, zauna da ita tayi akan gado tana yaye mata darar dake kanta, k'ura ma Sahura ido tayi tana kallonta, d'an girgiza kan ta Sahura tayi tana fad'in "Yi magana ina jinki."
Kamar wata doluwa saikuwa tace "Aunty, Asas ya mutu? Da gaske ya rasu? Yau ne fa aurenmu, shi ne ya rasu ya barni."
Fashewa tayi da wani kukan tare da k'amk'ame Sahura da suka kawo kai d'aya sanda take zaune ita kuma aa tsaye, daddab'ata ta shiga yi tana fad'in "Dangai dangai, dangai yar Abbanta, shiru karki masa kuka kinji."
A sanyaye suka ji sallamar su Iya da yayar Malam sun shigo d'akin, amsawa su Asma'u sukayi hakan yasa Iya kallonsu tace "Yan mata, dan Allah ku d'an bamu wuri zamuyi magana da ita."
Mik'ewa sukayi jiki a sanyaye cike da tausayi Asma'u har ta fara zubar da k'walla, Sahura ce ta rik'e hannun Asma'u ta mata alamar ta zauna kusa da Mimi, zaunawa tayi sai su Zeinaba da Salma da suka fita k'ofar gida, Sahura ma zaune tayi tana kallonsu Iya su ma suna kallon Mimi, cikin nutsuwa Iya tace "Mimi, *wani hanin ga Allah baiwa ne* ki yarda ubangijin daya halliceki shi yafi sanin abinda ya dace a game dake, Asas ba alkairi bane a gareki ko nace ba mijinki bane, shiyasa Allah ya d'aukeshi a sanda lokaci k'alilan ne ya rage ku zama d'aya a baki wanda ya fi shi cancantarki."
Yayar malam ce tace "Gaskiya ne, kuma dama ai *matar mutum* k'abarinsa, ya mutu ne saboda babu rabon aure a tsakaninku."
Dafe kan ta tayi da hannu tana sako hawaye tace "Kai na juyawa yake Iya, waye ya daceni? Waye ya fi Asas alkairi a gareni? Jiya ni na kusa mutuwa yau kuma shi ya mutu."
A hankali Iya tace "D'an uwansa ne, sheikh."
"Me!!!" Ta fad'a a razane tana mik'ewa tsaye kamar zata had'esu da ido, girgiza kai tayi cikin d'aga murya tace "Abdul? Ba zai yiwu ba bana son shi, ban shirya aurenshi, akan me za'a d'aura min aure dashi? Shi ne ya buk'ata saboda hukuntani akan k'aryar dana masa?"
Kama hannunta Sahura tayi tace "Yi hak'uri Mimi ki zauna kinji, babban mutum ne fa mai ilimi, na tabbata ba zai wulak'antaki ba."
Kallonta tayi tace "Kawai ni ma bana son shi ne aunty, bai min ba ko kad'an, *tsohon*?"
Yayar malam ce tace "Ke kin ci uwaki! Waye tsohon? An fad'a miki namiji na kad'an ne ko yayi yawa?"
Cire darar tayi ta jefa akan gado tace "To ni bai min ba, bana son shi ko kad'an, kawai a warware wannan auren."
Zata fito Sahura ta rik'e hannunta tare da Asma'u, rarrashi suka shiga yi da nuna mata tayi hak'uri, Mama na waje tana saurarensu, saida ta ji abun ya bata haushi ne ta lek'o d'akin, kallonsu tayi tace "Iya dan Allah ku k'yaleta, idan mahaifin na ta ya dawo saita fad'a mishi a warware auren tunda haka take so."
Sakin labulen tayi zata fito Abba da malam suka shigo tare da Abban Asma'u, gaisawa sukayi da mutanen dake nan suna taya juna murna da kuma jimami, d'akin suka wuce da sallama inda matan suka gyara musu suka zauna a kujerun da Asma'u ta d'auko ta aje musu.
Kallon Mimi Abba yayi yace "Uwata, kin ga abinda ya faru ko?"
Cikin kuka tace "Abba ni kawai a warware auren nan, Abba bana son shi wallahi."
Da mamaki Abba yace "Subhanallah! Ba kya son shi? Me yasa?"
A take tace "Saboda bai min ba, Abba sa'anka ne fa, ya zan auri sa'an Babana."
Salallami suka d'auka a d'akin inda malam yayi dariya ya zura hannunshi yana fad'in "Zo nan amarsu."
Mik'o mishi hannun tayi t taso ta zauna a k'asa kusa da k'afafunshi, cikin dattako yace "Amarsu wani ne ya fad'a miki tsoho ne shi? Dama ba'a auren tsoho ne? Miji irin wanda kika aura ba'a kiransa da tsoho saidai dattijo, dan dattijon arziki ne daga gidan dattijai, Mimina, ni dai banga abun a had'in nan ba ko kad'an, kiyi wa iyayenki biyayya ke ma sai Allah ya baki masu yi miki biyayya, kinji ko?"
Fashewa tayi da kuka tace "Kakana baya so na, na tabbata ya karb'i aurena ne dan ya hukuntani."
Abba ne yace "Hukuntaki kuma? Kar dai wata tsiyar kika tabkawa babban malamin nan."
Turo baki tayi ba tace komai ba, Abban Asma'u ne yace "Mimi 'yata kiyi hak'uri kinji, tabbas can dama Allah ya tsara shi ne mijinki, karki damu kanki bare kiyi k'ok'arin cutar da kan ki, nasan kina da ilimi kuma kinsan cewa zab'in Allah shi ne daidai."
Suna kan tattaunawar nan Rauda ta shigo da sallama d'akin, amsa mata sukayi inda tace "Abban Mimi kunyi bak'i a waje."
"Su waye?" Ya fad'a yana kallonta, da kamar tsoro a fuskarta tace "To har da dai Asas, da kuma sheikh sai wasu guda b..."
Bata gama fad'a ba Mimi tayi tsaye tace "Asas kika ce?"
D'aga mata kai tayi ai da gudu tayi niyyar fita a d'akin tana fad'in "Asas kuma?"
Rik'ota Abba yayi yana fad'in "Zubar mana da mutumci zakiyi? Maza zauna acan."
Komawa tayi ta zauna kusa da Asma'u inda Abba ya kalli Rauda yace "Ki ce su shigo ciki."
Sahura kuma darar Mimi ta d'auka ta shiga gyara mata ita a jikinta, an d'an d'auki minti biyu zuwa uku kafin suji sallama da gaisawarsu da mutane, har suna jin mama na tambayar Asas Hajia na fad'in "Haka Allah ya nufa, suma yayi saidai gaskiya bai tab'a mana irin haka ba."
Muryar Mama suka ji tace "Ku wuce ciki suna nan."
Da sallama a bukansu suka shigo inda Abba' Asma'u ya kalleta suka mik'e yana fad'in "Malam Adamu na ga magana ce ta cikin gida, zan jiraka a waje."
Da girmamawa yace "Haba malam *Bashir* ni da kai ai mun zama d'aya, dan Allah ka zauna zaka iya wakilta ta ai."
Komawa yayi ya zauna inda Hajia ma ta zauna bakin gado, mazan kuma duk kujera aka basu suka zauna, a hankali ta d'aga dararta dan so take ta kalli fuskar Asas d'inta, tana d'aga darar tare da idonta sai kuma idonsu suka had'e da nashi.
Da sauri ta ja darar ta koma gabanta na fad'uwa tana turo baki tace "Bana son ka dai, ba zaka bar nan ba saika sakeni."
Alhaji Ibrahim ne ya shiga fad'a musu duk abonda abinda ya faru daga farfad'owarshi har zuwanshi gidan, malam ne ya kalli sheikh yace "Yanzu kenan ya zo ya bata takardar saki a gabanmu ne?"
Da sauri sheikh ya kalleshi sai kuma yayi k'asa da kai cike da kunya, murya a raunane Asas yace "Ku taimaka min dan Allah, ina da buri sosai akan matar da zan aura, ina ji a jikina samun lafiyata zai ta'allak'a ne da matata, ku taimaka min dan Allah iyayena."
Ajiyar zuciya Saleh ya sauke yace "Idan hakane Asas kayi hak'uri da Mimi, a dangi akwai yara birjik sai ka zab'i wata a ciki."
Saida ya share hawaye yace "Tarbiyar Mimi ta min a rayuwa, halayenta na fad'in gaskiya tana birgeni, Mimi tana da *wayewa* daidai gwargwado, saidai ba kowa ke fahimtar kalar wayewarta ba sai wanda ya zauna da ita."
Kallonshi Asma'u tayi haka ma sheikh da yaji kamar ya gaura masa tapi a kunci, d'an satar kallonta ya sak茅 yi amma bai iya ganin komai ba a jikina sai jar darar kawai.
Abba ne ya gyara zama yace "Indai wannan ne yasa kake so Mimi, ni nasan wacce tafi ta komai, me zai hana ka amince sai a d'aura muku aure?"
Duk kallon Abba sukayi inda Asas yace "Wacece zata fi Mimi a wajena?"
Kallon Asma'u yayi yace "Gata nan, k'awarta Asma'u."
Da sauri ta yaye darar fuskarta idonta tas akan fuskar Abba, sai kuma ta kalli Asas sannan ta juya ta kalli Asma'u data mik'e tsaye dafe da k'irjinta, wani murmushi ta saki tare da sunkuyar da kan ta k'asa. Asas ma kallon Asma'u yake data mik'e tsaye, ba ta da wata makusa namiji zai iya cewa bata mi shi ba saidai in baka son kyakyawa kuma fara, d'an kallon sheikh yayi da shi ma yake kallonshi, a tausashe cikin ladabi yace "Sheikh kai ne babba, ka zab'a min abinda ya fi dacewa dani, idan ta maka na amince ka min wakilci."
Yana fad'a ya done kanshi k'asa cike da Alhini, d'an murmushi sheikh yayi ya kalli Abba yace "Wannan karamci ne, mun gode sosai."
Kallon Asma'u yayi yace "Kin amince a had'in nan? Ki fad'i abinda yake zuciyarki."
Mimi da ta ji kamar da ita ake kai tsaye tace "Bai min ba, bana so."
"Uwata." Yanda Abba ya kira sunan yasa ta saurin d'aga kai ta kalleshi, sai kuma ya fashe da kukan shagwab'a tace "Abba na fad'..."
Mik'ewa yayi cikin fad'uwar gaba kar ta fad'i abinda take fad'a a bayan idonsu kamar zai mareta, cukuikuye Sahura tayi tana kwamtsa k'ara da fad'in "Abba zai kasheni."
Hannunta ya kalla dake kan k'irjin Sahura wanda yayi masifar yi mishi kyau a cikin k'unshin nan gwanin birgewa, d'auke idonshi yayi yana d'an girgiza kai a hankali, Abban Asma'u ne ya kalleta yace "Asma'u."
A sanyaye tace "Na'am Abba." Zubewa tayi k'asa gabanshi cire da taradaddin wannan abun, cikin nutsuwa yace "Me kika ce akan zab'in nan?"
Satar kallon Mimi tayi ita ma a lokacin lek'en fuskar Asma'u take, sunkuyar da kanta tayi tace "Abba ku iyayena, kun fi ni sanin daidai da ba daidai ba, duk abinda kuka yanke a kai na daidai zanyi biyayya insha'Allah, amma..."
Shirun da tayi yasa Abbanta yace "Amma me? Yi magana kinji."
Kamar zatayi kuka tace "Ina so k'awata Mimi ta amince da zab'in nan, bana so ta kalli hakan a matsayin cin amana."
Duk kallon Mimi akayi har da sheikh daya bita da kallon banza yana so yaji me zata ce, tabbas indai ta hanata aurenshi to zai sa yarinyar nan a bak'in jadawakinshi, dan shi kam Hafsat rainon gata ta masa bai saba da wahala ba, yakiceta zaiyi a jikinshi ba tare da shakkun komai ba.
A hankali Mimi ta kamo hannun Asma'u ta zaunar da ita kusa da ita, kallon Asas tayi tace "Indai uwa ta gari ka ke nemawa yaranka to Asma'u ta kai ta zama uwar kowa, gareni ta zama aminiyar da babu kamarta, gareka miji nasan zata zamar maka b'aren jiki, bata da k'yashi a zuciyarta bare ta ji tana hassada da kai, tana so ne dan Allah kuma tana k'i ne dan Allah, duk wani mugun abu dana aikata a baya ita ce mai nusasheni, mun yi fad'a da ita bila-adadin akan na daina ba kyau, *Ashraf da ina da yaya namiji dana nema mishi auren Asma'u*, ko mahaifina bai mishi tayin aurenta bane saboda a gaskiya ba zan so ta auri *tsoho* ba."
Dak'uwa Abba ya mata yace "Uwaki ce tsohuwar, mutuniyar banza."
Dariya Iya da Sahura sukayi har da Hajia ma sai Asma'u data sinne kai, Mimi kam gimtse fuska tayi tace "Ko sanda nake cika baki ina nuna nafi k'arfin na auri tsoho, ita ce ke dakatar dani tana nuna min kamar fariya nake, ashe gaskiya take fad'a tunda gashi na auri *sa'an babana*."
Da sauri sheikh ya kalleta yace "Allah ka yafe min akan ashar d'in nan da zanyi."
Jinjina kai yayi yace "Jar uba! Wai dama haka rashin kunya da fitsarar yarinyar nan ta kai? Lallai ashe dai *kallon kitse* nayi ma rogo ban sani ba."
Numfashi Hajia ta sauke ta kalli Mimi tace "Kiyi hak'uri kinji takwarata, shi ma ba tsoho bane zaki gane haka gaba kad'an."
Cikin k'arfin hali Asas ya d'aga kai ya kalli sheikh yace "Hajia tsoho ne mana kar ki sa ya ji dad'i a ransa."
Kallon Mimi yayi saidai ba da waccen idon ya kalleta ba, a yanzu yanzun nan da idon ke *matar yayana* ce ya kalleta yace "Matar yaya karki yarda kin ji, idan kuma ana da ja ba tsoho bane ya cire hularshi mana."
Dariya suka saka a d'akin bai da Mimi da Asma'u da kuma sheikh, Ibrahim ne yace "To yanzu ya zamuyi kenan? Za'a sake saka wata ranar ne kafin a d'aura musu aure?"
Da sauri Asas yace "A'a dan Allah Abba, ni dai kawai a d'aura mana aure yanzu idan sun amince, bana so a k'ara jan lokaci wani abu ya biyo baya."
Jinjina kai Saleh yayi ya kalli Bashir yace "Abban Asma'u ya kace?"
Nuna Abban Mimi yayi yace "Ga uban yarinyar ai, duk yanda yayi wallahi d'aya ne."
Abba ne ya gyara zama yace "A gani na kamar yanda ya buk'ata, indai akwai shedu da sadaki kawai a d'aura."
Alhaji Ibrahim ne yace "To ina ga ai kamar maganar maza ce, muje waje sai mu tattauna."
Mik'ewar da sukayi yasa Mimi kallon sheikh da tambayar kanta "Wai ba zai sakeni ba yake nufi?"
Da sauri tace "Abba shi f..."
Kallon da Abba ya mata yasa tayi shiru, cikin fad'a yace "Wai ke kina lafiya kuwa? Me yake damunki ne Mimi?"
Fashewa tayi da kuka ta fad'a jikin Iya tana fad'in "Abba na fad'a maka ni bana so wallahi, kawai a sawak'e min."
Wani uban rank'washi ya zuba mata a kai daya sata d'agowa dafe da gurin tana lumshe ido da suke rufe mata k'arfi da yaji, hannu ya kai kamar zai mareta yana fad'in "Ke dan ubanki har kinyi tsaurin idon da a gabana zaki dinga fad'in a sakeki? Yaushe aka d'aura auren Mimi, ina wasa dake ne da z..."
Malam ne yace "Dan Allah wuce m没 je zaka tsaya kana biye mata."
Hajia ce tace "Wai kuna nufin yanda zaku mata kenan idan mun barta a hannunku? A halin da take ciki kuma har ta cancanci duka da fad'a irin haka? Gaskiya ba zai yiwu ba jama'a."
Kallon Iya tayi tace "Mama dan Allah ki mana alfarma yau kam 'yata ta tare a gidana kafin mijinta ya sama mata gurin da zata zauna."
Cike da dattako iya tace "Wannan ai ba matsala bane Hajia, tunda dama ai a yau d'in ake da shirin tarewarta."
Da fara'a Hajia tace "To a shirya mana ita zamu d'auki abarmu, dan nan kam naga matsi zata sha."
D'an dungure ma Mimi kai Iya tayi tace "Gwara ta tafi ai ko na huta da jarabar taurin kan ta, dan in nan zata zauna saina fasa mata jikinta da duka."
Da raha Hajia tace "Ai na ga alama ne Iya."
Malam ma cewa yayi "Hajia kin kyauta min da zaki d'aukemin amaryata daga gurin sak'agunan nan, abinda suka iya kenan su sakata gaba suyita narka."
Duk wannan rahar da suke su sheikh na tsaye na saurarensu gaba d'aya jikinshi ya mutu jin hukuncin da Hajia ke ta yankewa a kan shi, haka suka fita Mimi kuma ta sake b'allewa da kuka, Asma'u ma duk da halin da take ciki saida ta taya su Iya rarrashinta, a k'arshe dai wajen kukan nan baccin wahala ya d'auketa dan wajen kukan har jan numfashi take sama sama.
Ai kuwa suna fita a masallacin unguwar sukayi sallah la'asar, ana sallamewa mutanen dake nan aka tattarasu aka d'aura auren Asma'u Bashir da Ashraf Sabi'u Aliyu Sharif, tuni unguwa aka d'auka kowa ya shiga fadin abinda ya ji ya kuma k'ara da abinda ya fahimta a kai, haka dai gidansu Asma'u ma sai suka fara wani shirin daban suma, inda kishiyoyin mamanta suka shiga bak'in cikin wannan had'i musamman da aka ce sheikh ne yace zai mata lefe bayan ta shiga d'akinta, tunda shi ma Asas ne yayi wa matarshi馃榿, abun bai musu dad'i ba ko kad'an sai ma da aka ce yau ita ma zata tare tunda dai da lallenta da kitsonta, ango kuma ya gyara d'akinshi to babu abinda za'a fasa.
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:55 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*27*
Sosai dangi suka ci gaba da bikinsu saidai kusan duka angaye da amaren zuciyoyinsu babu dad'i, Sadeeq kan shi yayi wani iri a zuciyarshi da ya ji an d'aura auren Asas da wacce yake da burin aura, amma sai bai nuna ma kowa ba kawai suka ci gaba da shagalinsu, Asas ma sosai yake k'ok'arin nuna dauriya amma abun ya gagara, yayi kuka sosai na rashin Mimi, yana tunanin yanda zai fara rayuwa da wacce sam ba ita ce a tsarinshi ba, sannan ya rayu a kusa da sheikh da matar daya ci burin aura, a wuni d'ayan nan duk sai ya zabge ya fita hayyacinshi, kana kallonshi zaka san yana da damuwa. Haka ta b'angaren Mimi ma ta kafe ta k'i cin duk abinda aka bata ta k'i shan komai ta fad'a ta nanata ita fa asa sheikh ya saketa, tun ana bata maganar har akayi banza da ita aka ci gaba da sabga, labari kuma ya karad'e gari da kewayenshi, sheikh Abdul Waheed yayi aure amarya shakaf, wasu na fad'in dalilin auren wasu kuma a iya auren suke tsayawa. Amma a wajen k'awayen Mimi abun ba haka bane, sosai suke Alhini da kuma son ganin yanda Mimi zata rayu a gidan sheikh, wacce take wanda suka auri tsoho iskanci, ita me fad'in Allah ya rabata da auren sa'an babanta, yau gashi ta samu a b'agas ba fahimtar juna ba soyayya? Abun kam ya jijjigasu inda kowace jiki yayi sanyi tare da komawa gefe dan suga me zai faru.
*D'aukar amarya*
Ta wajen Asma'u kam motoci ne manya da k'anana guda goma sha hid'u suka d'auki dangi da abokan arziki aka nufi da ita gidanta cikin