Showing 33001 words to 36000 words out of 185502 words

Chapter 12 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

487

ce wai ke kika shiga kika fita, ta ina kika shiga to bare ba ki fita?"

Daga nan zaune Iya tace "Wallahi na sameki d'akin nan sai na ci uwaki Shapi'a, yar banza mai zubulin larabawan maroco, ba dan kina da d'an tsari a jikinki ba da yanzu ba kina nan a lalace ba."

Mimi kam ba tace komai ba dan a lokacin tana duba jerin sunayen wanda suka kirata, kama daga d'an beauty, bak'uwar lambar da take kyautata zaton ta Saminu ce, d'an wahala da kuma sauran 'yan wahalan suna take masa baya, har da d'an ajinsu na islamiyya da sauran lambobi barkatai. Sai lambar Salma data turo mata hotunan ta wanda aka had'a da suke nuna an kawo lefennta, taji dad'i sosai kuma saida tad'ora a status a take. Murmushi kawai tayi ta sake kashe wayar dan kar Iya ma ta gani ba tare data tuntub'i lambar kowa ba.


*Bayan kwana biyu*

A kwana biyun nan babu kiran wayar data d'aga musamman ma bak'uwar lambar data fi kyautata zaton ta Saminu, dan ko kallon k'ofar gidan bata sake yi ba tun daga ranar, dan jiya Maimuna har shigowa tayi da kan ta dan dubata, amma tana jin sai ta nuna bacci take a d'aki kawai har ta ban gidan tana jin tana wa mama k'orafin ta tafi ranar bata sani ba. Duk wani abu da zai b'ata mata rai ne yanzu bata k'aunarshi tunda daren jiya Abba ya bata izinin sauraren Asas idan ya zo, ba wannan ne yafi komai faranta mata rai ba kamar yanda ya ce ya turo magabatanshi, duk da tana jin d'ar a kan hakan dan bata san wane iri ne su d'in ba.

Da wuri suka gama shiryawa ita da Asma'u zasu je ganin kayan Salma da basu samu an kawo dasu ba, tun a kan hanya suke hirar Asas saidai ba wani sani ne da su ba sosai.

Suna karya kwanar gidansu dan isa bakin titi suka had'e da motar Muttak'a, saida ta feso wani iska a bakinta tare da furta "Iska na wahalat da mai kayan kara."

Tsayawa sukayi suna kallo har ya fito fuskarshi a had'e babu alamar wargi, yana tsayawa gabanta ya shiga kirta mata wani kallo irin na 'yan k'waya mai tsoratarwa, da yatsa ya nunata yace "...



*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:52 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*12*


Yana tsayawa gabanta ya shiga kirta mata wani kallo irin na 'yan k'waya mai tsoratarwa, da yatsa ya nunata yace "Ke wannan wane irin rashin mutumci ne da ake kiranki baki d'aga? Akan me zaki tsaya kina min wasa da hankali ne wai? Dan kinga ana sonki ne zaki tsaya yi wa mutane iskanci? Mimi surarki da albarkatun da Allah ya hore miki a jiki ba zasu hana ni daddarza miki buru'uba fa, ki kiyayeni kinji na fad'a miki."

Tunda ya fara magana suke kallonshi kowace gabanta na fad'uwa sun yi sak'e, dan gaba d'aya yanayinshi da alamu sun nuna wani abun yasha dan idonshi ma a jajir suke, duk ta daga ciki kam a mugun bala'in tsorace take, amma a zahirinta sai ta k'i nunawa a fuskarta bare kuma jikinta, dakewa tayi kawai tana binshi da kallo da matsakaitan idonta, sai kakkauran leb'enta na sama data turo gaba amma fuskarta a had'e sosai. Ganin yanda take kallonshi sai kuma ya sassauta murya yace "Mimi, dan Allah ki d'auki wayata kin ji, damuwa nake shiga sosai idan ina kiranki ba kya d'aga min, kin gani ko Mimi?"

Ya fad'a yana nuna mata k'irjinshi yace "Wallahi a nan ne kawai nake jin zafi, bansan me yasa ba amma an jarabceni da sonki sosai, Mimi zaki aureni?"

Da sauri ta yatsina baki a ranta tana fad'in "Kana d'an k'wayar? Allah ya tsareni."

A zahiri kam ko alamar magana ma ba tayi ba sai binshi da ido, cikin wata irin murya yace "Mimi ki min magana mana, bana son shirun nan naki fa, ko dai yan jan ajin ne suka motsa?"

Da sauri Asma'u ta kalleshi sosai tace "Eh wallahi su ne, ni ma tunda muka fito har yanzu bata min magana ba, sai fa kana hak'uri da ita."

A rikice a kuma shagalce yayi ram da hannun Asma'u yana fad'in "K'awar matata, dan Allah ki fad'a min tana so na? Tana baki labari na wata rana?"

Mutsu-mutsu Asma'u ta fara na son ya sake mata hannu, ganin bai saketa ba yasa Mimi d'ora hannunta akan na shi hannun dake rik'e dana Asma'u, kallon hannayen nasu duka sukayi, hannun Asma'u dake da sirkin fari mai masara, sai na Muttak'a dake bak'i wulik, sai kuma na Mimi dake da kauri da tuwon hannu ga shi kuma jajir akan na su. Washe baki yayi tare da sakin hannun Asma'u ya kalli Mimi yana fad'in "Mimi na kinji lallausan hannunki kuwa? Shi yasa kullum nake k'ara son ki."

Wata uwar harara ta wurga masa tare da kama hannun Asma'u ta rik'e gam, cikin amon muryar gargad'i tace "Kar ka sake tab'a jikinta, bana so."

Fizgar Asma'u tayi suka barshi nan tsaye, juyawa yayi ya bisu da kallo da d'umbin mamaki, amma kuma sai yayi murmushi yace "Ai ce wa tayi bata so, kishina ne take wallahi, da bata jin so na ai ba zatayi kishi na ba, daga yau na daina Mimi ba zan kuma kula kowace mace ba ma, amma fa idan kin min alk'awarin aurenmu nan kusa."

Tunda suka barshi babu wacce tayi magana saida taxi ta d'aukesu sukayi nisa, da k'yar Asma'u ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in "Kin gani ko? Abinda nake fad'a miki kenan Mimi, wallahi mutumin nan d'an k'waya ne na gaske."

Wani dogon tsaki taja tare da d'aga mata hannu alamar ya isa tace "Kinga dallah ba'a son yin magana akan waccen shashashan banzan."

D'auke kanta tayi ta juya tana k'ara had'e fuskarta sosai alamar hushi, babu wacce ta k'ara magana har suka isa gidansu Salma ana shirye shiryen magriba.

Saida suka fara gabatar da sallah kafin suka zauna kallon lefen, sosai kayan suka birge Mimi suna kallo kuma tana bata labarin Asas daga had'uwarsu har matsayar da ake kai yanzu.

Wayarta dake cikin jaka ta samu ta cire ta a silent ne ta shiga ruri, saidai sautin kiran ya tabbatar mata da layinta na Moov ne ake kira wanda ba sosai ta cika aiki da shi ba, d'aukar jakar tayi ta ciro wayar ta duba lambar, gabanta ne ya tsinke ya fad'i sakamakon ganin lambar sheikh ta fito, yanda tsoro da fargaba suka ziyarce ta ne yasa Salma lek'o screen d'in wayar tana fad'in "Besty halan wani jakin ne kika samu."

A rashin sanin me tayi da kuma jin zafin abinda Salma ta fad'a kawai ta kai mata bugu a baya tana fad'in "Ke ce jaka marar mutumci, wannan d'in?"

Salma da taji zafin bugun sosai ta dafe bayanta tana fad'in "Wai-wai-wai! Ni kika daka haka besty?"

Tsaki tayi tace "Dan Allah ni ku min shiru na amsa kiran ya sheikh, kinsan abun laifi ba kad'an yake a wurinsu ba, ni kuma ina so mu rabu lafiya da shi wallahi."

Shiru kam sukayi suka daina k'wak'waran motsi, danna ok tayi tare da saka amsakuwa ta aje wayar akan wani akwati mai kaya. Sheikh da tashin hankali ne ya d'ugunzuma shi har ya saka shi kiranta bai shirya ba shi ma yayi shiru, a kwana biyun nan yake jin sabon abu a game da yarinyar, matuk'ar son had'uwa da iyayenta yake sosai, amma har yanzu bata kirashi ba ta ce Abbanta ya dawo, sai kawai ya kasa hak'ura ya d'an dannawa lambar kira, dan so yake idan komai ya tabbata ayi aurenshi tare da Asas wanda yau yake sanar dashi an ce ya tura magabatanshi, kuma yayi alk'awarin tafiya anjima tare da kawun Ashraf d'in.

Kamar babu wanda zaiyi magana sai kuma ya rangad'a sallama a tausashe, d'an numfashi ta sauke ta amsa mishi kamar yanda ya mata, d'orawa tayi da fad'in "Barka da yammaci, anwuni lafiya?"

Murmushi ya saki daga inda yake yana mamakin me yasa ita bata iya kambama abu ba? Asma'u dai kallonta take tana kuma mamakin yanda take gaisawa da babban mutumin nan, haka, a tausashe ya amsa da "Lafiya lau, ya kike?"

Da fara'a da kuma ladabi tace "Lafiya lau, ya fama da mu?"

Murmushi yayi wannan karan ma mai sauti yace "Fama da ku? Ke zan tambaya Ryam ya aka ji da hak'uri da mu?"

Murmushi ita ma tayi tace "Alhamdulillah, amma ai mu ne iyayen k'iriniya."

Yar dariya yayi yana jin wani nishad'i na ratsashi, a hankali yace "Ryam kar ki ga na kiraki ki d'auka na haukace fa, a gaskiya ina son sanin idan Abba ya dawo ne, a matse nake sosai da son tattaunawa dasu."

A d'an ladabce da kuma sigar mamaki tace "Me yasa haka? Wani abu ya faru ne?"

Saida ya girgiza kai kamar yana gabanta kafin yace "Ba komai, kawai dai zamuyi magana ne a kan ki."

Tsam tayi ta kalli su Salma da Asma'u tana musu alama da ido a kan ta kuma? Saita nutsuwarta tayi tace "A kai na malam? Allah yasa dai ba laifi nayi ba."

Murmushi yayi bai ce komai ba na tsayin dak'ik'u kafin yace "Ryam, shekaruna sun fara ja gaskiya, saidai a shekarun nan nawa na ji ina son yin aure sosai, shin zaki *iya aure na*?"

Wani bahagon fad'uwa gabanta yayi har saida ta dafe k'irjinta da hannu ta waro ido tana kallon wayar, aurenta? Sheikh Abdul waheed? Da sauri ta zabura ta d'auki wayar ta cire amsakuwar ta d'ora a kunne, saidai bakinta ya gaza furta komai, d'an sautin murmushin shi ta ji yana fad'in "Na yi tunanin haka Ryam, nasan zaki ce na miki tsufa dama, ni kaina nasan wauta nayi dana bari zuciyata ta fara k'aunarki, ba komai zan hak'ura."

Jikinta yayi mugun sanyi duk sai take jin ba dad'i, da k'yar ta d'aga labb'anta tace "Ni ban ce fa."

Cikin fara'a yace "To me kike nufi da shirun kenan?"

Sai kuma ta kasa bashi amsa ta k'yale, wani murmushi ya sake yi yace "Ina jin ki mana, zaki iya aurena a haka?"

A zuciyarta tace "Ba zan iya ba gaskiya, ka min tsufa Abdul."

A zahiri kuma sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsar k'afarta cikin fitar da kalmomi da d'ad'aya tace " *Zan iya mana*, ai ba shekarun ne abun dubawa ba, nagartar da kuma dacewa."

Lumshe ido yayi daga inda yake tare da sakin murmushi, shiru kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace "Da gaske Ryam?"

Jinjina kai tayi tace "Eh, gafarta malam."

Cikin jin dad'i yace "Kenan kin amince yanzu na zo gidanku neman aurenki?"

Rarraba ido tayi tana tunanin abun yi, gaskiya har zuciyarta take jin bata son b'ata mishi rai, shiyasa ko kira yayi a na farko take d'agawa, amma shi kan shi Asas da take begen yin hira da shi bata damuwa dan ta share kiranshi, gashi tun had'uwarsu ta farko ta mishi k'arya da dama, bata so ya gano hakan zai zubar mata da kimarta, kawai ta fad'a mishi y'a zo ta tabbata idan ya zo za'a ce an bayar da ita, daga nan ita kuma saita cire layinta na Moov ta shiga sha'aninta, zai manta da ita ya kuma shiga rayuwarshi, idan kuma dole ne k'ara auren to zai nemi wata. Da wannan shawarar tayi ammana kawai ta sanyaya murya sosai tace "Eh, amma sai Abba ya dawo."

Da sakin fuska yace "Naji dad'i Ryam, yaushe Abban zai dawo?"

A hankali tace "Nan da kwana biyu ne inji Mama."

Jinjina kai yayi yace "Shikenan Allah ya nuna mana, zan kashe waya dan bana son kaucewa shari'a, magana da nayi da ke ma babu izinin mahaifinki saina nemi afuwarsa akan haka, saida safe."

Jinjina kai tayi ita ma tace "Saida safe." Aje wayar tayi ta sauke ajiyar zuciya, kallon Asma'u tayi ta mik'e tana fad'in "Tashi tashi malama mu koma, hankalina a tashe yake wallahi na yi wa malam k'arya."

Mik'ewa Asma'u tayi tana fad'in "Ke kuwa me yasa kikayi haka to?"

Saida ta saka hijab d'inta tace "Ba zaki gane ba Asma'u, muje kawai."

Salma ma mik'ewa tayi suka fita tana fad'in "Besty zan kiraki fa ki bani labarin wannan sabon kamun."

Dariya kawai tayi tace "In kika kira ban d'aga ba karkiyi hushi."

Dariya ita ma tayi tace "Wane hushi kuma? Ai har na saba, shiyasa na matsu iyayenki su san kina rik'e waya wallahi."

Da sauri ta shiga takawa tana fad'in "Bari kedai, zasu sani kinji." Da azama suka fita kamar wasu masu laifi suka samu taxi suka nufi gida, a taxin kam yaua saida sukayi baram baram dan Asma'u fad'a ta mata akan me zata mishi k'arya? Babban mutum ne fa ya zata mayar da shi wani shashasha haka? Ita kumaa ta ji zafi har sukayi fad'a, ana saukesu kowace ta shige gida babu mai yi ma wata magana.

Tunda suka dawo take d'aki kwance tana waya da Asas d'inta, da ta ji motsi za'a shigo take saurin b'oye wayar har sai ta ji shiru, a haka har Amir ya shigo yana fad'in "Mimi Alhaji ne ya aiko yaro yana kiranki ki kama ma aunty Maimuna aiki."

Zaune tayi cikin jin haushi tace "Kai je ka ce masa bana nan, jaraba kai."

Juyowa yayi yana turo baki ya fito, saukowa tayi ta durk'usa k'asan gadon ta jawo akwatinta ta saka wayar, ta mik'e kenan Mama ta shigo tana fad'in "Wace buru'ubar ce yau kika tashi da ita da zaki k'i zuwa kiran Alhajin, Maimuna ce bata jin dad'i ya ce ki je ki kama mata aiki."

Turo baki tayi ta rarumi hijabinta akan gado tace "To." Hanyar fita ta nufa Mama tace "Yanzu aikin da zaki masa ne kike wannan kumburar? Mimi anya kina tunawa da alkairi kuwa?"

Sake kumburo fuskar tayi tare da k'arasa fita a d'akin ta saka takalminta, a k'ofar gidan ta samu Abbanta zaune har da Alhaji Saminu akan tabarma suna hira, yatsina fuska tayi ta harareshi ta wuce, shigewa tayi cikin gidan kan ta tsaye ta shiga falon da sallama, ba wani abu daya nuna mata mai d'akin nan na faman da jinya, dan haka suka gaisa a sama sama tace "Mama ta fad'a min kin shiga gidan ai ina bacci."

Da fara'a tace "Eh wallahi, ranar na ga babu sallama sai fitowa na yi ban gan ki ba, sai Alhaji ne yace ya had'u dake a k'ofar gida kin fita ai."

Yak'e tayi tace "Hakane wallahi."

Jim ta d'an na wasu mintuna sa茂 kuma ta mik'e tace "Aunty Maimuna saida safe, dama dan mu gaisa ne."

Da fara'a tace "To Mimi saida safe."

Tana fitowa daga falon suka had'e ya shigo, had'e fuska tayi ta sunkuyar da kan ta tana jiran ya kauce, a yanda idonshi suka rufe sai yaji baya shakkar Maimuna tasan komai, kan shi tsaye kawai yace "Me yasa ina kiranki baki d'agawa?"

A dak'ile cikin b'acin rai tace "Haka kawai, ka kauce min na wuce ko na maka ihu yanzu."

Wani malalacin murmushi yayi ya d'an kauce mata yana fad'in "Malam ya ce mu tayashi karb'an bak'i, ina fata dai ba aurenki zasu zo nema ba?"

Saida ta saka takalminta tace "Eh, su ne, aurena zai basu insha'Allah."

Wata yar dariya yayi sanda take fita a k'ofar d'akin shi kuma cikin wayancewa saboda kallonshi da Maimuna tayi yace "Allah yasa alkairi Mimi, ai haka ake so."

Banza tayi da shi har ta fita a gidan gaba d'aya, sai dai shi kam haushi kamar zai kasheshi, ba wai rashin girmama shin da ba tayi ba, ba kuma yanda bata d'aga wauarshi ba kamar da ta tabbatar masa masu neman aurenta ne zasu zo, to kenan shi jiran banza yayi mata kenan? Tana fita gida ta sake shiga mama na tambayar ta "Har kin mata aikin ne? Ko kuma had'e mata fuskar kikayi ta gane tace ki tahowarki?"

Sakin fuska tayi tace "A'a mama, dama dan na juye mata abinci ne a kwanuka."

K'ala mama ba tace ba har ta shige d'aki, tana zaunen ne d'aki ta ji tsayawar mota a k'alla guda biyu, tana jin Abbanta ya shigo ya d'auki ruwa masu sanyi ya fita, gabanta fad'uwa kawai yake sai wani sabon fargaba da take ji yana ziyartarta, a k'alla minti talatin kafin ta ji bak'in sun bar k'ofar gidan.

Abinda bata yi tsammani bane kuma shi ma bai fad'a mata ba, sa茂 ga Abba da mahaifin Asma'u da suka tayashi karb'an bak'in sun shigo da akwatina har da goro da kuma kud'inta, akwati set biyu aka shigo da su masu kyau na zamani, goro d'auri biyu da kuma kud'in lefe million d'aya da rabi. A tsakar gidan kam tana jin hayanuyarsu har da kakanta ma suna tattaunawa su fa basu d'auka da kayan zasu zo ba, sai kakanta dake fad'in ai haka shine harkar girman, kawai a musu addu'ar fatan alkairi.


*To fa*

Da safe tsaf ta shirya ta tafiyarta makaranta, saidai tana zuwa abun mamaki labarin har ya riga ta isa, dan kuwa Asma'u ce ta sanar wa su Jamila su ka suka yayata, saidai abun d'aure kan shi ne yanda Mimi bata cika bakin nan ko shan k'amshi da jin dad'i, murmushi kawai take musu sai tace "Hummm!"

A gida ma tana fita mama ta fara karb'an bak'i daga makwabta har zuwa dangi suna taya murna na abun arzik'i. Har Mimi suka taso ta riski yan uwan mahaifiyarta su biyu aunty Shapi'a da aunty Sahura suna ta hira, d'aki ta shiga bayan ta durk'usa ta gaishesu, kayanta ta cire ta fito ta shiga ban d'aki ta dawo, har zata koma d'aki Shapi'a tace "Mimi zo."

Tahowa tayi tare da durk'ushewa dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login