Showing 90001 words to 93000 words out of 185502 words

Chapter 31 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

503

dad'in jikinta, murya a d'an dak'ile yace "Zan baki kyautarki zuwa gobe insha'Allah."

Jinjina kai tayi alamar to, da haka suka isa gidan, a farfajiyar ya sauketa ta tunkari shiga ciki, da kallo ya bita har ya hangi Hajia ta tarbeta tana ta tab'a jikinta, lumshe ido yayi ya bud'e ya feso iska yana fad'in "Ina ma baki lalata k'uruciyarki ba."

Jingina yayi a kujerar motar ya sake lik'e idonshi, a hankali abinda ya faru a asibitin ya fara dawo mishi, a gaskiya ya tabbatar mace ce har da k'ari, dan kuwa a yanda yaji indai ba gizo ko rud'un zuciya bane, to yaji komai ya nuna kuma a tumbatse yake. Wani dogon tsaki yaja sakamakon tuna waccen ranar da aka mata tereren nan, hakan na matuk'ar tayar masa da hankali, yana jin zafi da kuma d'aci a zuciyarshi idan ya tuna k'aramar yarinya kamar waccen tasan ta bayar da kanta a bata kud'i tayi sutura mai kyau da tsada sannan ta rik'e k'atuwar wayar da mahaifinta zai iya jan jari har da d'aukar nauyin gkdan shi ma. Saida ya ga b'acewarsu ita da Hajia sun shige falon kafin ya ja motar ya bar gidan shi ma.

A falo Hajia ta zaunar da ita duk da har a lokacin akwai sauran mutane, abinci tasa aka kawo mata dan ta ci tasha magani, saidai rashin k'warin jiki da d'and'ano a baki ga kuma kunya yasa ta kasa cin komai, sai madara ta d'an sha ita ma saida yan uwan Hajia suka sa baki.

Magani Hajia ta b'alla ta mik'a mata, girgiza kai tayi kamar zatayi kuka tace "Um um."

Harara ta cilla mata tace "Ban gane um um ba, takwara karb'i nan kisha kafin kiji a jikinki."

Karb'a tayi amma ta rik'e a hannu ta kasa sha, cike da rarrashi Hajia tace "Yawwa yar albarka shanye kinji, saboda lafiyarki ne ai, ko kina so ciwo ya kwantar dake ayi ta d'irka miki allurai?"

Girgiza kai tayi alamar a'a, wata tsohuwa dake zaune sun gama shirin tafiyarsu ce tace "Ki barta ai kar ta sha, idan zazzab'i ya kayar da ita ni ba abinda zai hanani yi mata siraci da ganyen darbejiya."

Murmushi Hajia tayi tace "Haba Hajia ai ba za ayi haka ba, amarya guda ta kwanta rashin lafiya kuma bata arzik'i ba."

Kallon Mimi tayi tace "Kinga yar albarka shanye kinji, dubi fa guda uku ne kawai."

Cikin marairaicewa tace "Idan nasha amai zai sakani ne."

Girgiza mata kai tayi tace "Ba zakiyi ba kinji, idan kika saka a ranki zakiyi ne shiyasa kike yi."

Sake marairaicewa tayi ta d'an d'aga hannunta tana so tasha, sai kuma ta sauke tana rintse idonta, ganin haka yasa Hajia kallon wata yarinya a cikin yaran bak'in tace "Ke Khadija tashi madafa d'auko min muciyar nan ki gani, na ga ita ma kamar d'an gidana ne wajen rashin son magani."

Dariya mutanen d'akin sukayi inda Mimi ta shiga rarraba ido tana kallon hanyar madafar da yarinyar ta nufa da kuma Hajia, tsohuwar nan ce tace "Shi ma fa haka yake bai son magani, kuma kai gashi Allah ya jarabeka da ciwo."

Cike da jimami Hajia tace "Ki bari kawai Hajia, Ashraf idan zai sha magani saina titseyeshi da mabugi kafin yasha."

Da mamaki wata ta kalleta tace "Mabugi fa? Da girman na shi?"

Cike da tabbaci Hajia tace "Wallahi kuwa, har yau har gobe idan zai sha magani sai raina ya gama b'aci na rik'e abun duka."

Kallon Mimi tayi tace "Da fari da yake fad'a min aurenshi zai zama silar warakarshi na d'auka ke d'in zaki jajirce ne wajen kula da maganinshi, ashe kema kamar shi d'in ne a rashin son magani."

Dariya tsohuwar tayi tace "Ashe da an taru an lalace."

Sunkuyar da kai Mimi tayi dan k'awarta ce kawai ta zo mata a rai, "Ko ya ta kwana a gidan?" Shi ne abinda ta tambaya, cike da k'arfin hali ta d'aga kan ta ta jefa k'wayar magani d'aya a baki ta kora da ruwa da sauri, tana had'ewa ta sake jefa sauran idonta duk a rufe kamar zatayi amai, tana had'ewa aje kofin tayi tare da mik'ewa dan nufa masaukinta, kallonta Hajia tayi cikin tausayi da tunanin maganar Asas da akayi ne ta jawo mata sabon yanayin, rik'e hannunta tayi tace "Kinyi waya da mamanki kuwa?"

Girgiza kai tayi a hankali tana jin amai na taso mata, da d'an mamaki tace "Me yasa to? Ya kamata ki kirata ki gaisheta, kinsan uwa mace tana kwana cikin zulumi da fargaba a ranar da aka d'auki 'yarta zuwa gidan wani da sunan aure."

A hankali ba tare da ta fahimci zancen Hajia ba tace "Bana da waya ne."

Zaro ido tayi tace "Ba kya da waya? A'a ai wannan kafin kiyi aure kenan, yanzu wuce ki kwanta zan kira *mijinki* na fad'a masa."

Da wani irin kallo Mimi ta bita kafin ta d'auke kanta tana jin kamar ta d'ora hannu a kai tace "Wayyo ni wayyo kaina." Wai mijinta, mutumin daya haifeta shi ne ake kira mijinta? Ohh wannan wace irin rayuwa ce? Da k'yar ta kai kanta d'aki ga aman dake taso mata ga kuma rashin k'warin jiki. Tana shiga da gudu ta shige ban d'aki ta sako aman nan, kaf maganin da tasha ta amaye kafin ta kuskure baki ta fito ta kwanta a galabaice.



*Asa-Ma'u*


Da safe daga gidan Hajia aka aika musu da abun kari, bayan sun karya kuma Asas ya fita ya bar gidan ba wata hira a tsakaninsu, da fitarshi ba jimawa yayarta Rayya ta zo gidan bisa umarnin mamansu, kayanta data zo mata dasu ta shiga gyara mata har da wasu kayan aiki na mata da mamanta ta tara mata da kwanukan cin abinci, saida ta gama gyara mata komai a lokacin k'anwar Mamansu ma da kuma yayarta suka zo.

Sosai Asma'u ta ji dad'in zuwansu dan sun mata nasiha da nuna mata tayi hak'uri sannan ta shiga jikin mijinta amma fa ba da fitsara da bud'ewar ido ba, anan har suka d'an dafa mata tamtabaru ta ci aka bata zuma tasha, da taimakon Rayya sukayi girkin rana mai rai da lafiya dan kauan abinci babu abinda babu, haka suka ci suka k'oshi suna raharsu har saida sukayi sallah la'asar suka tafi, lokacin ita kuma ta shiga d'ora girkin dare a nutse ta fara da gyara namanta, duk da ba wani girki ta iya na zamani mai kyau ba, amma dake Mimi uwar jaye-jaye ce da shige shige, wannan ma data d'ora yanzu Mimin ta ga sun tab'a yi ita da Maimuna shiyasa ta fara, hakan yasa ma sai taji kewar k'awarta da tunanin ko me take yanzu? Ya take a sabon gidan data samu kanta?

Daf da magriba ta kammala ta gyara komai ta tsaftace gidan kamar ba tayi ba, ganin magriba ta gabato sai tayi alwala ta fara yin sallah, tana idawa ta shiga wanka tana jin kamar kar ta fito a ban d'akin, har yanzu zuciyarta ta kasa yarda ita ce a wannan daular, ta kasa yarda ita ce ta auri mijin da k'awarta tayi muradin samu, ta kasa yarda ita ce dai Asma'u ta auri Asas namijin da har k'awayensu gulmarsa suke wajen had'uwarsu akan komai.

Tana fitowa a sauk'ak'e ta shirya cikin shaddar da sukayi ita da Mimi da niyyar suyi shigar bikin Mimi da ita a musu hotuna kafin su canza na d'aukar amarya, saida ta gama shirinta a tsanake lokacin har an gama sallah isha'i ta fito falon tana baza k'amshinta. Cak ta tsaya gabanta ya buga da k'arfi sakamakon ganin Asas zaune yana kallo fuskarshi a had'e sosai, rarraba ido ta shiga yi da tunanin me za tayi?

K'amshin turarenta ne ya kai mishi a hanci da sauri ya juyo inda yake jin k'amshin, yana ganinta yayi saurin lumshe ido tare da hango surar Mimi a idonshi, farar fuskarta mai d'auke da dogon hanci da kakkauran labb'a da matsakaitan ido, ajiyar zuciya ya sauke tare da bud'e idonshi a hankali ya sake kallonta, k'ak'aro mata murmushi yayi tare da mata alama da hannu "Zo."

A hankali cikin ruwan sanyi ta k'arasa tana daddafe cikinta dake motsawa, tana zuwa gefenta ta tsaya kusa da k'afafunshi ta zauna k'asa, da sauri ya nuna mata kan kujera yace "Zauna a nan."

Girgiza kai tayi alamar a'a, shiru yayi ya na d'an kallon fuskarta da tayi kwalliya mai sauk'i ko gira bata zana ba, shi kuma a yanda yake son matarshi ta kasance mai cab'a kwalliya da ado ne kamar ba gobe. Jin bai ce mata komai ba yasa ta bud'a bakinta daya mata nauyi tace "Ina wuni?"

A dak'ile ya amsa da "Lafiya lau, ya gida."

Kasa amsawa tayi dan duk a duburburce take, sam bata tab'a ganin irin wannan had'ewar a tare dashi ba, kullum tsakaninsu wasa ce da raha irin ta mijin da k'awata zata aura da kuma aminiyar amaryar da zan aura, mik'ewa tayi kamar an cijeta ta kalleshi tace "Na kawo maka abinci ne?"

D'aga manyan idonshi yayi ya kalleta, sai kuma ya mayar da kallonshi kan tv yace "Um."

Da sauri ta juya hakan yasa shi bin bayanta da kallo, wani murmushi ya saki mai kama da kuka saboda tuna yanda *lokaci* yayi k'uli-k'ulin Rakiya da shi ya canza masa komai, duk da bai tab'a mata kallon daya wuce k'a'ida ba kula bata tab'a tsayawa gabanshi cikin shigar rashin kamun kai ba, amma dai a yanda yake ganin sittin saba'in a cikin hijabin Mimi yasan ba k'aramin kaya ta mallaka ba, duk da kuwa ita ma Asma'u tana da su saidai kawai a *barwa rai abinda ya ke so.*


Kan k'aramin table ta aje kwanukan ta shiga zuba mishi hannayenta sai rawa suke, tana idawa ta aje mishi gabanshi ta koma gefe a k'asa ta zauna, cikin jin haushi ya kalleta yace "Ya zaki dinga zama a k'asa? Koma sama."

Da sauri ta mik'e ta zauna kan kujerar tana mayar da kanta k'asa, jawo plate d'in yayi ya fara cin abinci a wani yatsine kuma a yangance, ita dai da ta ji ta k'osa da zaman sai ta mik'e tace "Da wani abu da kake buk'ata na yi maka ne?"

Wani irin kallo ya jefa mata yace "Kamar me?"

Yanda ya mata tambayar yasa Asma'u saurin durk'usawa tace "Kayi hak'uri." Mik'ewa tayi har tana had'a hanya ta bar falon ta shige d'akinta, da kallo ya bita sai kuma ya d'an ja tsaki ya ci gaba da cin abincin dan ba laifi ya masa dad'i a baki.

Yana idawa yasha ruwan data zuba mishi ya mik'e da kanshi ya d'auko lemu a fridge ya dawo ya zauna, kallo ya shiga yi tare da giccirawa yana kuma tunanin abinda ya faru ranar *juma'ar jiya* wacce ta gigita mishi komai na shi, bai gushe a nan ba saida 11:00 ta buga kafin ya mik'e ya kashe komai ya nufi d'akinshi, shiryawa yayi cikin kayan bacci kafin ya dawo d'akin Asma'u dan kawai ya zauna d'akin kar ya bar yarinyar mutane ita d'aya.

Yana shiga tuni ta jima da baccinta a cikin doguwar rigar bacci, kitsonta ya fito ras dan d'an kwalin ya fad'i, kashe fitilar yayi ya kwanta gefenta ba tare daya rufa da zanin data rufa ba.




*Mim-Sheikh*


Bayan sallah azahar Shapi'a ta zo gidan ganin Mimi, yanda ta sameta babu lafiya sai taji kamar ta mata kuka, Hajia ma cikin zulumi da jimami take fad'in "Kin ganta wallahi da zazzab'in nan ta kwana, tasha magani na d'auka yayi sauk'i ashe a banza, kuma sun je asibiti ta ce ba'a mata allura ba, ta sake shan magani da k'yar amma har yanzu jikin."

Kallon Mimi Shapi'a tayi tace "Mimi da bata son magani, anya kuwa tasha?"

Cikin rashin sani Hajia tace "Na fari dai bata nayi na fita, amma bayan dawowarsu daga asibiti a gabana tasha."

Cike da kallon tuhuma ta kalli Mimi tace "Kin tabbata baki amaye shi ba Mimi? Na fa sanki a kan magani."

K'asa tayi da kanta tana layi tana so ta koma ta kwanta, Hajia ma dake kallonta cewa tayi "Kenan da gaske maidoshi kikayi?"

Shapi'a ce tace "Tabbas indai Mimi, da wuya ai ta had'e magani ya zauna mata."

Hab'a Hajia ta rik'e tace "Oh Allah! To kinga ko mijinta zan kira ya maidata asibiti a k'ara mata ruwa ko allura?"

Jinjina kai Shapi'a tayi tace "Gaskiya kam, dan a hankali yanzu nan tsaf zata rasa jini a jikinta."

Waya Hajia ta ciro zata kirashi Mimi tasa kuka tana fad'in "Dan Allah karku fad'a masa, aunty ai kinsan Mamana jibda take shafa min ko? Dan Allah ki ce karta kirashi a shafa min jibda zan daina."

Dakatawa Hajia tayi ta kalleta tace "Kin tabbata?"

Cike da tabbaci tace "Wallahi jibda Mamana ke shafa min duka jikina saina daina."

Juyawa Hajia tayi zata fita tana fad'in "Abu mai sauk'i, dana sani ma tun tuni da ba an wuce wajen ba."

Fita tayi sai Shapi'a data kalleta tace "Yanzu Mimi me ke anfanin haka? Kina bak'unta ma amma sai an gane halinki na taurin kai?"

Turo baki tayi tace "Amma aunty ai kuma kunsan bana son magani ko."

"Mun sani Mimi." Ta fad'a tana tsareta da ido tare da d'orawa da fad'in "Amma ko dan bak'uwar fuska ai sai ki sha."

Sake turo baki tayi tace "Ai nasha maidoshi ne nayi."

Jinjina kai tayi tace "Dama zuwa nayi naga ya kika kwana, mamanki da tace ma ba sai na zo ba tunda dai b芒 gidanki bane aka kawoki, ni dai nace sai na zo dan bai kamata ace babu wanda ya zo dubaki ba kamar wata marar dangi."

Kyab'e fuska tayi tace "Aunty ita Mama sai yaushe zata zo?"

Zaro ido tayi saidai kafin ta bata amsa Hajia ta shigo rik'e da kwalbar jibda babbar a hannunta, tana zuwa mik'awa Shapi'a tayi tace "Gashi to shafe mata jikinta."

Karb'a tayi tana dariya da fad'in "Kina ji da ita ko? Wai yaushe mamanta zata zo?"

Dariya Hajia tayi tace "Mamanki zata zo amma bayan tarewarki gidan mijinki."

Hira sosai suka sha har kusan la'asar Shapi'a bata tafi ba kuma sosai jikin Mimi yayi sauk'i dan har wanka tayi ta canza kaya, Hajia na mamaki sosai yanda ita jibda ce maganin zazzab'inta duk da tasan dama tana magani da dama.


10:30 daidai ya kawo k'ofar gidan, mai gadi na bud'e mishi zai shiga kawai ya tuna da akwai fa wani nauyi a kan shi, tunda suka dawo daga asibiti bai sake sanin abinda ke faruwa ba, dan ko Hajia basuyi waya ba saboda hidimar dake gabansa, juya akalar motar yayi dan ba zai yarda hakk'in k'aramar yarinyar nan ya zamar masa babban nauyin da zai kasa saukewa ba.

"Bawan Allah..." Wannan sunan data ambata ne ya dawo a kunnuwansa, wani k'asaitaccen murmushi ya saki tare da sake murz sitiyarin dan yau kam shi kad'ai ya wuni yawo a gari yana fad'in "Marar kunyar yarinya kawai, gata yar firit amma firita ce a jininta."

Da wannan ya isa gidan su Hajia tare da tunkarar falon kan shi tsaye...




*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*30*



A tausashe ya rabka sallamar da tasa Salammatu amsawa tana kimtsa zamanta daga kallon tv, kamar zata nutse k'asa dan girmamawa ta shiga, gaisheshi, da girmamawa shi ma ya shiga amsa mata dan ba yarinya bace, cike da kulawa yace "Hajia tana ciki ne?"

Nuna mishi d'akin Mimi tayi tace "Ta shiga ciki zata dubata."

Da ido ya amsa alamar to tare da nufa d'akin, da kallo ta bishi da mamakin yanzu nan fa aka barshi da yarinyar can fitsararriya sai ka ganta da ciki wata rana, tab'e baki tayi tana mayar da kallonta kan tv da fad'in "Maza ho."

K'wank'wasa k'ofar ya fara yi daga ciki Hajia tace "Waye?"

A sanyaye yace "Ana."

Da fara'a tace "Shigo sheikh."

A hankali ya bud'a k'ofar tare da d'ora idonshi akan Hajiar dake tsaye, bai yarda ya kalli inda ya tabbatar tana nan ba saida ya gama gaisawa da Hajia, cikin sakin fuska take fad'in "Da na ga dare yayi ai na d'auka ba zaka zo ba, kuma dana tuna kai ne fa sai na sa a raina zaka zo komai dare."

Wani lallausan murmushi yayi tare da d'an shafa sajenshi yace "Hajiarmu kenan, sabgogi ne dayawa, har zan shiga gida kuma na taho."

Da fara'a tace "Allah sarki, Allah ya bada ladar d'awainiya."

"Ameen." Ya fad'a tare da d'an kaikata idonshi ya kalleta, da sauri ya ji zuciyarshi ta fara bugawa, doguwar riga ce a jikinta ta bacci mai laushi, kan ta kuma babu d'an kwali sai gashinta data d'aure, jibda ce take k'ara shafawa a jikinta gaba d'aya.

Tunda ya shigo bata kalleshi ba, kuma sam bata da niyyar zata kalleshi sai murzawa hannayenta jibda take, d'an cije leb'enshi yayi na k'asa kafin yace "Ya jiki?"

Sai lokacin ta d'aga kai ta kalleshi, a cikin ranta tayi k'wafa tuna abinda ya mata a asibiti da tunanin "Zan rama, sai na mayar da kai kamar *kakana*."

Sakin fuskarta tayi tace "Da sauk'i *malam*."

K'uri ya sake mata da ido da nanatawa a ranshi "Malam?"

Hajia dake ta murmushi tana kallonsu ne ta d'an gyara murya tace "Bari na baku wuri ko."

Da wani matsiyacin sauri Mimi ta kalleta tace "A'a Hajia, ba abinda zai min."

A lokacin shi ma yayi saurin juyawa cike da kunya yana fad'in "A'a Hajia, saida safenku."

Amma jin abinda Mimi ta fad'a sai yasa ya tsaya ya sake juyowa, sai kuma ya jinjina kai ya juya zai fita, bayanshi Hajia ta bi tana fad'in "Dama ina son magana da kai."

Da kallo Mimi ta bisu da addu'ar "Allah yasa ta masa maganar wayata, ina so na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login