Showing 111001 words to 114000 words out of 185502 words

Chapter 38 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

509

Asas yayi da son gano yanayinshi murya k'asan makoshi yace "Sheikh kana lafiya?"

Ba tare daya bud'a idonshi ba murya na rawa a rashin sanin yanda yayi magana yace "Banda lafiya Asas, jikina ya min nauyi, zuciyata bugawa take da sauri, ban da lafiya gaskiya."

Da sauri Asma'u ta kalleshi cike da tausayi dan tasan yanda ya ga Mimi ne, tsaf suka k'araso sai Asas daya shiga binta da kallo yana jin kamar ya tsawatar mata, sheikh dai har ya kasa kawaici ya iyaa furta haka? Lallai abinda yake ji a game da ita babba ne. Da sauri Asma'u ta fizgi hannunta suka koma gefe Hajia kuma na kallonshi da mamaki ganin idonshi a rufe.

Cikin b'acin rai tace "Me ye haka Mimi? Ya zaki fito babu hijab kuma kinsan zaki had'u da sheikh?"

Yatsina fuska tayi tace "To sai me? Tsirara na fito."

A hassale tace "Ba tsirara kika fito ba a wajen mutane, amma a wajenshi tsirara ne, haba Mimi wai me yake damunki ne? Ya kike abu kamar mahaukaciya wani lokacin?"

Da d'umbum mamaki Mimi ta kalleta tace "Mahaukaciya? Asma'u akan sheikh d'in ne kike kirana da mahaukaciya, saboda kina so ki nuna min kin fini zama d'aya daga cikinsu kenan?"

Juyawa tayi zata bar wurin Asma'u ta rik'o hannunta cikin jin haushi tace "Ni ba mahaukaciya na kiraki ba, amma Mimi ke ma kinsan baki kyauta ba, a ganina ko dangata ta jini ce ta had'aki da shi ya zama dole gareki suturta jikinki, yanzu ya kike so mutane su kaalleshi idan aka san ke ce matarsa?"

Fige hannunta tayi da k'arfi tace "To sai me? Ya sakeni mana idan ba zai iya ba, ni na ce dama ya aureni ne? Kinga ba zan iya rayuwar takuran nan ba, tunda yanzu ke ma ahalin Sharif ce ki fad'a ma masu fad'a masa yaji ya sawak'e min."

Juyawa tayi a hassale ta nufi hanyar fita mayafin na sauka a kafad'unta, gyarashi tayi cikin hushi ta sab'a a kafad'a d'aya ta shiga takawa da sauri na b'acin rai wanda ya haddasa k'adawar mazaunanta da kyau tare da tsallen zuciyar sheikh kamar zai suma a wurin yana binta da ido.

Numfashi ya shiga saukewa da sauri sauri da kuma k'arfi k'arfi, Hajia na d'an gefe tare da Asas dan tunda suka kula baya hayyacinshi suka matsa suna tattaunawa na tsakanin d'a da uwa, matsowa Asama'u tayi ta rumgume hannaye cike da jimami, idonshi kawai ya iya wulk'itawa ya kalli Asma'u cikin k'arfin hali kuma har yanzu hannunshi na kan k'irjinshi yace " *Wacece ita*? Wacece Mimi da take son na sakata a cikin jarabawar da Allah ya min, yanayin nan sabo ne a gareni da ba lallai na iya sabawa da shi ba, ina tsoron kar a fara fahimta har na fara zama mahaukaci a idon jama'a, me yasa k'awarki ba zata bini a baya ba yanda zamu jima muna tafiyarmu? Wanene dalili ne yasa dole take so sai na mutu a kan ta? Me yasa? Me yasa Asma'u."

Gaba d'aya jikinta sanyi yayi kanta a k'asa tana sauke numfashi, tunaninta shine ta yanda zata fara bashi amsar tambayoyin nan bayan gaisuwa ma har yanzu a kunyace take mishi, amma tunda akan abinda ya shafi k'awarta ne sai ta aro jarumta tayi k'arfin halin gyara muryarta tace "...



*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:57 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*36*



Aro jarumta tayi k'arfin halin gyara muryarta tace "Mimi da kake gani a zahiri haka bad'ininta yake, ba kowa bace ita amma tana da suffa mai ban tsoro, sani na halayya babu wanda ya santa sama dani, dan ko iyayenta suna zarginta, saidai Mimi tana da sauk'i sha'ani idan kuka fahimci junanku, tana da ladabi da biyayya idan har tana girmama abu, matsalarta d'aya taurin kai, wanda shi ma nake fatan ka zama wanda zai canza mata wannan d'abi'ar."

Gyara tsayuwa tayi ba tare data kalleshi ba tace "Idan halinku ya zo d'aya da Mimi zaku jima kuna tafiyarku, ni k'awarta saidai akwai wasu halaye na ta da muke samun sab'ani akan su, saidai hushin Mimi kamar d'igon ruwa ne, taurin kan ta ma haka na tabbata zaka iya ji da haka."

D'an takawa tayi ta matso kusanshi ta kalli fuskarshi da har yanzu yake kallon hanyar da Mimi ta bi tace "Tana da suffar kura ne a jikinta, ga *tsoro* ga ban *tsoro*, ga wanda bai santa ba har ya had'a da tagomashin *zarginta*, amma nasan gaba kad'an kai ne zaka bamu masaniya akan wacece Mimi."

K'arasawa tayi kusa dasu Hajia, a lokacin lokaci ya cika har an fara kiran sunayen matafiya, kamar wanda aka tsikara da tsinin allura sai kawai ya d'an zabura yana fad'in "Hasbunallahu wani'imal wakil."

Da wani irin sauri ya shiga takawa yana nufa hanyar fita, kallonshi suka shiga yi inda Asas yace "Ina kuma zai tafi?"

Cike da dagiya Hajua ta d'auke kanta tace "Barshi zai dawo."

Yana fita bakin k'ofar ya hangeta tsaye jikin motar ta rumgume hannaye sai cika take tana batsewa, tana ganin ya nufi inda take ta had'e fuska ta gyara tsayuwarta, ai akan shi ne Asma'u ta kirata mahaukaciya ko? To ta daina yi masa wasa daga yanzu (Kaji k'arfin hali ga uwata).

Yana zuwa bud'e motar yayi tare da kama hannunta ya wurgata ciki da k'arfi, shiga yayi yana rufe motar Kabiru ya fita a mazauninshi na dreba ya koma gefe. Sam sai ta k'i ta nuna tsoron yanayinshi, had'e fuska tayi sosai ta k'ura masa ido tana kallo, yanda take kallonshi sai ta dubutburtashi ya rasa me zai mata.

Hannayenshi ya d'aga da niyyar sake cakumota ya mata irin jijjigar ranar, sai kawai ya sauke a hankali ya kamo hannayenta ya rik'e a cikin na shi, sunkuyar da kan shi yayi k'asa baki na rawa rawa yace "Ryam *ya kike so dani ne? Dan Allah ki taimaka ki killace min kan ki, kinga wallahi zan iya fasa tafiyar nan idan kika ci gaba da yi min irin haka, Ryam kuka na ke so nayi saidai bansan ko zaki iya rarrashi na ba, Ryam hankalina tashi yake idan kina fad'in ba kya son tsoho, hankali na bari jikina yake idan kina fad'in na sakeki, gaba d'aya rasa nutsuwata nake idan kina min irin rigingimun nan, shin so kike na ajiye babbar rigata ne na dinga saka k'ananan kaya? Ryam so kike na ajiye sanina a gefe na dinga yawo dake a gari muna tafe muna shan ice cream?* Ryam ina ake rage shekaru? Zan je a rage min indai zaki zauna dani, Ryam ina jin ki a zuciyata sosai kuma ina kishinki, sannan ina jin haushin wanda suka fara kalle min surarki, da zan iya hukuntasu to hukuncinsu shi ne k'wak'ule idonshi ne kawai abinda zan iya yi mai sauk'i, dan Allah Ryam ki taiamaka ki daina saka zuciyata na bugawa sosai a kan ki, kinga fa zan iya haukacewa dan rigimarki yawa gareta."

Sakin hannayenta yayi ya tallabo fuskarta, yanda gaba d'aya tayi wani sororo tana kallonshi zai nuna maka kalamanshi sun sakata a wani yanayi na mamaki da d'imuwa, bakinta ya kalla da babu komai a kan shi sai kalarshi ta asali wato pink da bak'i, a hankali ya shiga matsawa da fuskarshi kusa da ta ta har saida ya d'ora labb'anshi a na ta labb'an.

Wani irin salo ya shiga mata mai tsayawa a zuciya, yanda yake zura harshenshi a bakinta yana zagayawa da shi ko ina, yanda yake d'an tattauna leb'enta a hankali, ga hannunshi d'aya daya jima da shiga rigarta, cabkar nononta yayi hakan yasa ta waro ido sai kuma ta lumshe saboda idonshi a kan na ta suke, a hankali a nutse ya shiga mulmula kan k'irjinta yana lailayawa yana shafasu, Mimi da gaba d'aya jikinta ya mutu yayi wani irin sanyi lak'was, ji take kamar ana mata tafiyar tsutsa, yam-yam d'in da take ji da kuma k'yak'yayi a gabanta sai kawai ta shiga sako hawaye masu zafi, hannu tasa cike da k'arfin hali ta fara tureshi, da k'yar ya cire bakinshi a nata tare da sake damk'ar fuskarta ya d'aga yana kallo, hawayen dake zubo mata ne ya shiga saka harshenshi yana lashewa, saidai abun ya fi k'arfin d'aukar hankalin Mimi, sai labb'anta suka shiga rawa tana son yin magana hawaye kuma suka ci gaba da sintiri, cike da k'warewa ya tsayar da bakinshi kusa da kurmin idonta yana tsotse hawayen da zaran sun zubo.

Kasancewarsu a kusa yasa ana kiran sunanshi tayi gaggawar bud'a idonta wasu hawaye na fitowa, tar ta sauke cikin na shi idon tana son tace masa "Ana kiran sunanka." Saidai ba wannan kuzarin.

Murmushi ya sakar mata cikin muryar da shi ma yasan ya sake tak'alowa kanshi fitina yace "Ryam...indai..baki daina zubo...da haway..nan ba..., to babu inda zan tafi."

Rufe idonta tayi tana jin yanda yake ci gaba da murza nononta, sunanshi da aka sake kira yasa ta k'arfin halin ture hannunshi taja baya ta dangane a jikin motar, sake matsawa yayi daf da ita ya mata rumfa ya had'a goshinshi da nata, sumbatar bakinta ya sake yi yana murmushin mugunta, harshenshi yasa a kunne yana zagayawa dashi, tuni ta fara k'amewa tare da sarewa da lamarin old man d'in, dan wani irin abu take jin yana taso mata da shi da bata tab'a ji a rayuwarta ba, wani marayan kuka ta saki daya fallasa sirrin muryarta na halin data shiga ita kan ta na son a sosa mata wajen dake k'yaik'yayi, d'agowa yayi ya kalleta ba tare daya daina murmushin nan ba, k'wank'wasa glas d'in motar akayi, juyowa yayi ba tare daya d'aga daga rumfar daya mata ba, d'aya daga cikin jami'anshi ne sai kuma Hajia a can gefe, wani numfashi ya sauke wanda iskar bakin ya sauka a fuskar Mimi, sake rintse ido tayi inda shi kuma ya zauna daga rank'wafawar.

Hannunshi yasa aljihu ya ciro katinshi na banki na aikinshi na gwamnati, kamo hannunta yayi ya damk'a mata yana kallon fuskarta yace "Dan Allah Ryma ki kula da kanki, daga million d'aya har abinda yayi sama ki d'iba a asusun nan, amma ki sani *ba zan tab'a yafe miki ba idan kika nemi kud'i a hannun wani gara*."

Sakin hannunta yayi tare da tallabo kumatunta ya manna mata sumba a goshi, fuskarta ya sake kallo yace "Ki shiryawa tarewarki kafin na dawo."

Bud'e motar yayi ya fice tare da rufowa, wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sake jingina a kujerar, numfashi ta shiga saukewa d'ai d'ai hawaye sun kasa tsayawa a idonta, d'ora hannunta na dama tayi a k'irjinta ta dafe tare da katin daya bata, cak tunaninta ya tsaya ta rasa me zatayi inba hawaye ba da kallon titi.

Yana fita shima had'e fuska yayi sosai bai ko kalli jami'in ba ya nufi inda Hajia take tsaye, dake manyan kaya ne a jikinshi sai bai ji wani d'ar ba dan ya tabbatar asirinshi a rufe yake, sallama sukayi da Hajia a kunya ce kafin ya wuce ciki da hanzari ya samu Asas har yayi gaba ya barshi.

A tare Hajia da Kabiru suka shiga motar, tana jinsu amma sai ta kasa motsawa bare ta kalli b'angaren da suke, har suka fara tafiya Asma'u ma dreba ya d'auki hanyar mayar da ita gida, saidai Hajia ta ce ta dawo ta zauna tare da ita tunda bak'uwa a gidan har yanzu. Tunda Hajia ta fahimci yanayin Mimi tasan an d'an matseta ne sai batayi magana ba kawai har suka isa gidan sheikh, kallonta Hajia tayi tace "Mimi zan shiga na duba saina fito mu wuce."

D'an k'yabta ido kawai tayi alamar to dan jikinta a mace yake sosai, shiga tayi ta sameta a falo ita kad'ai zaune yaran suna d'akin karatun mahaifinsu, yanda ta ganta ne yasa tana zama tace "Hafsat haka kike zaune gida ba zaki tafi asibiti ba?"

Murmushi tayi kawai tace "Hajia wallahi ni duk tsoron zuwa asibitin nake, bana so na je su fad'a min abinda zai d'aga min hankali ne."

Cikin fad'a Hajia tace "Saboda haka kuma sai kiyi ta zama a gida har ciwo ya cimmiki? Ni sai naga kamar ma nak'uda kike."

Zaro ido tayi tana dariya tace "Hajia nak'uda kuma? Wata shida ne fa da sati biyu."

Tab'e baki tayi tace "To miye a ciki? Ba'a haihuwa a wata bakwai ne?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace "Ana yi Hajia, amma bana fatan nayi."

"To yanda Allah ya tsara ai shine daidai." Cewar Hajia tana gyara zaman jakarta, jinjina kai tayi tace "Hakane."

Kallonta tayi tace "Kinga tafiya zanyi, daga filin jirgin muke dama na ce bari na biyo naga jikin na ki."

"Har sun tafi Hajia?" Ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa da k'yar sanda Hajia ta mik'e, tana gyara hijabinta tace "Sun tafi, sai fatan sauka lafiya da kuma dacewa."

A sanyaye tace "Allah yasa a dace."

"Ameen." Hajia taa fad'a, saida suka kai daf da k'ofa Hajia tace "Tare da Mimi fa na ke."

Wani fad'uwar gaba ta ji ya ziyarceta har saida ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."

A tsanake Hajia ta kalleta tace "Lafiya?"

Girgiza kai tayi tace "Ba komai, bayana ne."

Wani murmushi tayi tace "Kiyi hak'uri kinji Hafsat, insha'Allahu Allah yana tare dake, nasan kina mamakin wace irin uwace ni? Ni kaina Hafsat sai bayan na yanke hukunci na fahimci me na aikata, hakan ya tabbatar min da k'arfin dake a cikin *tafiyar k'addara*, na tabbata auren Mimi da sheikh shine rubuce a *laulil mahfuz*, Asas kawai sanadi ne na tabbatar da auren, ba kuma za'a rasa samun rabo ba."

Jiki a sanyaye ta danne kukan dake son taho mata tace "Hajia baki mana komai ba, nima na gane aurenta da shi ne abu mai yiwuwa shiyasa ya yiwu."

Jinjina kai tayi tace "Ni zan wuce, saida safe."

"A gaida gida Hajia." Ta fad'a tana kallonta, tana hangenta har ta shiga mota suka fita a gidan sai kawai ta sako wasu hawaye zuciyarta tana fad'in "Allah ka bani juriyar cinye wannan jarabawa, hak'ik'a ba dan mahaifiyata bace da sai na nunata a matsayin wacce ta fi kowa tsanata a duniya, had'a min sheikh da wata mace ba k'aramin rud'u bane a tare da ni."

Juyawa tayi tana share hawayen fuskarta ta koma ta zauna tana shafar cikinta tana tasbihi da hailala dan samun sassauci a zuciya.


Suna k'arasawa gida da k'yar ta kai kanta d'aki ta kwanta ruf da ciki tana rufe fuskarta da mayafinta, zumbur ta mik'e tana yakice mayafin a fuskarta, shinshinawa ta sake ta tabbatar dai k'amshin turaren shi ne, shinshina jikinta ta shiga yi sai ta ji kamar ita ta shafa shi, fad'awa ta sake yi rairan tana kallon sama a hankali ta furta "Ya Allah."

Wasu hawaye ne suka taho mata masu zafi ta had'e wayu masu nauyi, yanayin da take ji wallahi kaamar ta k'wala masa kira ya dawo. (馃槼 Ya dawo yayi me uwata?)


*Sheikh*

Sararin samaniya suke jirgi na tafiya ba da gudu sosai ba, jingine yake a kujerar idonshi ruf kan shi na ta dawo mishi da abinda ya faru, wata masifaffiyar sha'awar yarinyar ke ciciyarshi, yanda yake lailaya kan mamanta saida ya ji sha'awar kai shi a bakinshi, lokaci ne kawai bai bashi damar haka ba, sosai yake ciki da bege da shauk'in kasancewa da ita.

Asas na gefe shi dai kallonshi yake yana murmushi, yasan abubuwa dayawa a ge da Mimi haka kuma baisan abubuwa dayawa a game da ita ba, babban abinda ya tabbatar yana birgeshi da ita kuma shi ma sheikh tunda namiji ne zai birgeshi shi ne k'amshi, akwai yawan anfani da tunani ga kuma iya d'aukar ado, riga t-shirt da zani zata d'aura sai kaga yarinyar ta bada kala sosai.

Sheikh kuma har maganganun Asma'u saida ya d'orasu a mizani, dan a wajenshi ta sake tabbatar mishi da Mimi fa tana bin maza a rayuwarta ta baya, lokacin data fad'i "Mimi da kake gani a zahiri haka bad'ininta yake..."

Haka kuma maganarta ta cewa "Ni k'awarta ce saidai akwai wasu halaye da na ta da muke samun sab'ani..." Tabbas ya yarda Mimi ce jarabawarshi a rayuwa, kuma a yau ya yarda d'ari bisa d'ari zai karb'i jarabawar da Allah ya mishi ya rumgume da hannaye bibbiyu, ba k'aramin abu bane musamman daya kasance babban mutum, yasan daga lokacin da za'a fahimta al'umma zasuyi mishi tofin Allah tsine, sannan za'a iya kafa mishi hujja da maganganunshi na wa'azi da yake fad'in "Mace 'yar duniya ko a kyauta aka b芒 wa namiji ita an cuceshi, an cuci zuri'arshi."

Kusan kowa a wurin ya rintsa idonshi da sunan bacci amma ban da sheikh dake tunanin Ryam da abubuwan da suka faru daga d'aura aurensu zuwa yau.

Bayan awannin da suka kwashe sai gasu tsaye akan k'afafunsu Allah ya saukesu lafiya, su ma kamar sauran matafiyan abokin sheikh da kan shi ne ya zo ya d'aukesu zuwa gidanshi, duk da a wajensu ba dare bane a lokacin amma saida suka ci abinci sukayi wanka suka kwanta dan huta gajiya.


*Niger*

Sam a daren kasa bacci tayi, gaba d'aya tunanin sheikh da abubuwan daya mata ne ya tsaya mata a rai, ga masifaffen k'amshin turarenshi daya tsaya mata a jiki, har saida tayi wanka ta goge jikinta da kyau amma a banza, ga wani sabon yanayi daya bayyana a tare da ita, wani irin shauk'i ke d'ibarta kamar tayi kuka. Dap da asuba ta mik'e tayi alwala ta d'auro alwala ta shiga nafilfili duk ita d'in ba mai k'ok'arin yin nafilar bace, saida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login