Showing 159001 words to 162000 words out of 185502 words
k'arya kike, sannan na bashi carbita ya zane min ke da kan shi."
Wani marayan kuka ta saki a hankali tare da fad'in "To ai ba zan k'ara ba ko, kayi hak'uri."
Kallon gadon yayi yana jin ina ma ba gidan da yake jin matsananciyar kunya bane, da cak zai d'aga gadon ya fito da ita su kalli juna, amma saiya d'aure fuska yace "Haka kike fad'a kullum amma ba kya dainawa, Innar Issa duk randa kika kaini bango a game da k'aryar nan wallahi zaki gane shayi ruwa ne."
K'wafa taji yayi ya laluba aljihunshi ya aje mata d'aurin kud'i akan gadon tare da fita a d'akin, da sauri ta fito tana murnar bai tafi da ita ba, kwance ta sake yi akan gadon dan kar Abba ya dawo ya ganta ya wulak'anceta, jin alamun ta zauna abu yasa ta lalubawa ta jawo kud'in, d'auka tayi tana dariya ta jawo k'aramar jakarta ta sokasu a ciki.
D'akin Iya ta shiga tace mata "Ya kike jin jikin yanzu? In kinsan baki jin dad'i ki tashi muje asibiti."
Mik'ewa tayi zaune tana yatsina fuska tace "Iya aman ma ai ya kwanta, ki bari na gani zuwa safe."
Jinjina kai tayi tace "To shikenan, ni dama bana son k'aramin ciki a saba mishi da likitar nan, sai ya zama komai kaji sai ka je asibiti."
A zabure ta kalleta tace "Iya waya fad'a miki ciki ne dani? Haba dan Allah bana son haka fa."
Turo baki tayi ta juya kan ta, dak'uwa ta mata tace "Ubanki ne ya fad'a min, in b芒 ciki ne da ke ba uban waye dake saka ki jin amai."
Cike da tsiwa tace "To wai ke Iya dole komai sai dai ki zagi ubana ne, me yasa baki tab'a zagin Mama ba? Dan baki haifeshi bane, kuma ni ba abinda nake da."
Juyawa Iya tayi zata fita tana fad'in "Ina zan tsaya fad'a dake ki ja min jafa'i, ina tab'aki a ce ni ce silar komai, can ki k'arata da jarabarki."
Kallonta tayi har ta fita saidai ran ta a b'ace dan sosai ta ji haushin maganar wai tana da ciki, cikin sheikh? Tsoho wanda ya girme ma Abbanta? A tsiwace ta murgud'a baki tace "Allah ya rabani."
*Washe gari*
Saida ta gama shirinta tsaf kawai ta zauna bakin gado ta d'auki wayarta ta danna masa kira. Suna tafe a nutse cikin mota zai fara biyawa wajen Hajia ya gaisheta su wuce ya d'aga kiran cike da farin cikin yau ita ta fara kiranshi, cike da karsashi yace _"Assalama alaiki."_
Cikin yarinta ta amsa da _"Wa'alaika salam, ina kwana?"_
Kyab'e baki yayi yace _"Ban gan shi ba."_
Kallon wayar tayi sai kuma tace _"Ya aiki, ya gajiya, ya gari, ya hak'uri, ya fama damu?"_
Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi yace _"Allah nake rok'a ya k'ara min hak'uri da juriyar iya tafiya dake, dan na lura Ryam d'ina tana son gayyato min ciwon da har yanzu ko Hajiarmu bata da."_
Wata shak'iyiyar dariya tayi ta yan duniya tace _"Ni Maryama a wa? Da zan d'ora maka wannan ciwon?"_
Samun kanshi yayi da kalar dariyar da tayi kafin yace _"Ke mai mulki a zuciyar Abdul mana."_
Waina idonta tayi tace _"Daina zolayata malam, ni dama na kiraka ne na fad'a maka ina so zan fara tafiya makaranta."_
Wani dam! Ya ji gabanshi ya buga, makaranta ta me kuma? A nan zaman lafiya zata wani tsokano masa fitina, d'an girgiza kan shi yayi yace _"Wace irin makaranta kuma?"_
Turo baki tayi alamar bata so tambayar ba tace _"Amma fa kana da yara, kuma kasan tun jiya an koma makaranta."_
A hankali ya fara sauke numfashi yana sauraren na ta bugun numfashin a kunnenshi, a sanyaye sosai kamar mai rad'a yace _"A'a Ryam, karki d'auko min abinda zai fi k'arfina dan Allah, ni ban yi maganar karatunki da iyayenki ba, bana so gaskiya, ki hak'ura kinji."_
Mik'ewa tayi tsaye tana dafe k'ugu irin fa da gasken nan take tace _"Me? Baka so fa ka ce? Kasan matakin karatu na ne da za'a datse min shi ban shirya ba? Ina so na zana jarabawar bac shekara mai zuwa, dan Allah Abdul ka barni na tafi ka ji."
Saurarenta yake tas yayi shiru abun shi, yanda ta fara maganar da zafi da farko sai ya bashi mamaki, amma a k'arshen nan da ta kashe murya tayi a sigar rarrashi ta kirashi da sunan da saka mi shi jin k'uruciya sai ya murmusa akan labb'enshi, tunani ya shiga yi ya barta ne ko kuma dai ta hak'ura, sanda aka yi aurensu da Hafsat ma tana tsaka da karatu kamar yanda shi ma yana tsaka da na shi karatun a Madina, yana tafiyarshi k'arasa karatunshi ita ma ta ci gaba da na ta a gidan Hajia, saidai inda matsalar take Hafsat da Mimi ba d'aya bane a halaye da yanayin zubin halitta kai har ma yanda yake jin su a zuciya, yana da yak'ini d'ari bisa d'ari Hafsat bata karya dokoki da sharud'an daya gindaya mata ba, amma Mimi? Wani iska ya feso yace "Ba zai yiwu ba gaskiya."
Da sauri Mimi tace _"Yanzu duk magiyar da na maka ba zaka barni ba? Haba sheikh na Allah, haba ustaz haba Abban Humaira da Munzeer, haba an tsohon yan matanshi."_
K'yalk'yalewa yayi da dariya yana fad'in _"Ryam, na ji to na ji."_
Da zumud'i tace _"Yawwa ka amince?"_
A take yace _"A'a, yanzu ki fara fad'a min me ye burinki idan kin kammala karatun?"_
A sanyaye ta feso iska ta koma ta zauna tace _"Abdul."_
A tausashe kamar zai k'urma ihu saboda yanda ta kirashi yace _"Na'am."_
Cikin shagwab'a tace _"Kud'i na zasu k'are, ka kirani da wayarka."_
K'it ta kashe kiran tana murmushi, shi ma dariya yayi yana maida mata kira da fad'in "Allah shirya min baiwar nan ta ka ta min sauk'in juyawa."
Tana ganin kiran ta d'aga shi kuma yace _"To ina jinki."_
A ladabce tace _"Ka ga dai idan na gama karatu ina so na samu babban aikin da zan siyawa Abbana gida, na siya mishi mota na siyawa Mama mota na had'ata da dreba, sannan na d'auki nauyin karatun su Yaseen a makarantar kud'i mai kyau ba kamar ni da nayi ta gwamnati ba, sannan na cika musu d'aki da kayan abinci da masu aiki a kewaye dasu, sannan duk shekara ina kaisu aikin hajd, shikenan."_
Cikin farin cikin jin burinta ba wani mai tsanani bane yace _"To ke kuma baki da abunda kike son yi ma rayuwarki ne?"_
Sauke ajiyar zuciya tayi tace _"Ni kam ba wani babban abu na ke so ba, dama dai burina bai wuce na samu d'an yaro ba na aura, wanda zai dinga kai ni shan ice cream sannan duk shekara ya kai ni k'asar waje nayi yawon bud'a ido, sai kuma na dinga haihuwa duk bayan shekara bakwai bakwai."_
Dariya ya shiga shek'awa kamar yaron daya samu kallon kartoon d'in Tom and Jerry hannunshi rik'e da sweet, sakin baki tayi tana mamakin me ya bashi dariya haka? A marairaice ta sake fad'in _"Abdul in tafi ne? Lokaci na tafiya."_
D'an tsagaitawa yayi da dariyar yace _"A'a Ryam, zamuyi magana a kan karatunki idan kin dawo gidana."_
Kyab'e fuska tayi irin zatayi kuka tace _"Yanzu duk yanda na gamaka da Allah baka ji ba, ku fa malamaina magada Annabawa, ko bakuyi niyyar abu ba aka had'aku da Allah kuna yi, ka tuna da cewa Imam Malik har mata ya aura saboda kawai ta had'ashi da Allah, kuma ya zauna da ita da kyautatawa duk da baya sonta a zuciyarshi, amma kai...shikenan sheikh ba komai, ka nuna min ban da mahimmanci a wurinka da zaka iya yi min wannan alfarmar."_
Sheikh ban da saurarenta da girmama lamarinta babu abinda yake yi, rik'e hab'a yayi a ranshi yace "Oh Allah! Wai ka haifi mutum a shekaru amma ya ce da tsiya zai maka wayo."
Cikin sakin murmushi yace _"Ya kike so na yi Ryam? Bana so ki je gaskiyar magana, amma tunda kika had'ani da Allah zan miki wani lamuni."_
Gyara zama tayi da zumud'i tace _"Yawwa ina ji."_
Sanyaya murya yayi yace _"Ki girka min abinda zan ci anjima."_
Yatsina fuska tayi tace _"Girki kuma?"_
A hankali yace _"Um! Ko ba zakiyi ba dan ki samu lada?"_
Da sauri tace _"Ni d'in me da zan ce ba zan yi ba? Zan yi mana."_
Murmushi yayi yana hangen falon Hajia dan tun d'azu suka shigo kafin yace _"Da kyau yar albarka, Allah ya faranta miki yanda kika faranta min."_
Wata dariya tayi tana nunashi da hannu kamar yana gabanta tace _"Abdul wannan addu'ar wallahi ta wayo dan kayi galaba a kai na, ba komai ka ci gaba da yi min yawo, wata rana zan rama ni ma."_
Dariya yayi yana fitowa a motar yana me jin kamar ya zauna yayi ta hira da ita yace _"Ai kin rama tun jiya, ko kin manta na je bikonki kika min wayon baki da lafiya, haka na dawo ni da k'atuwar rigata."_
Tintserewa tayi da dariya _"To wai idan na dawo yanzu me zan maka? Ga matarka nan da kake so da kuma 'yarka da kuka shigar ma fad'a kuka min taron dangin, dan kunga bana da wanda zai shigar min ne ai."_
Cikin murmushi yace _"Ryam ba na bayar da hak'uri ba? A yafe mana dan girman Allah mana."_
D sauri tace _"Na yafe, wallahi na yafe tunda ka ce girman Allah."_
Da jin dad'i yace _"Yawwa ko ke fa, ina sonki Ryam, na sumbaceki a bakinki."_
Da baki sake tace _"Ta ya ya? Bayan ban ji sumbatar ba."_
Dariya ya bushe da ita cikin tsokana yace _"Ke wata Mairama, ashe ma kina so na sumbaceki."_
Rufe fuska tayi da kunya tace _"Ni bana so, kawai tambaya ce na yi."_
K'it ta datse kiran tana dariyar jin kunya, shi ma soka wayar yayi aljihu yana girgiza kai da murmushi a fuskarshi yana shafa k'eyarshi, jami'an su dai da kallo suka bishi har ya shige falon suna mamakin wannan sabon shehi na su, su dai kam tun daga ranar da aka d'aura aurensu suke ganin bak'in abubuwa a tare da shi, kuma basu ga laifinshi ba tunda yarinya ya aura wacce ko su dake da k'uruciyar da baya da suka auri sa'arta zasuyi fiye da haka ma bare kuma shi.
A nutse yake zaune k'asa gaban Hajia yana d'an jujjuya kofin tangaren d'in data aje masa da zazzafen shayin na'a na'a a ciki, bayan sun gaisa ne Hajia ta numfasa cikin d'an fad'a fad'a da dattijuwar uwa kuma wacce take gaba dashi ta kalleshi a zafafe tace "A ce duk abubuwan nan na faruwa amma ni babu wanda zai iya fad'a min, ba ma wannan ba sheikh akan menene zaka zauna k'aramar yarinya 'yar cikinka har tayi sanadiyar barin matarka d'akinta? A kan me?"
Kuma sunkuyar da kai yayi bai yi magana ba yana son bata damar fad'an abinda take son fad'a, d'orawa tayi da "Yanzu fa kwana biyu kenan, tunda Hafsat ta fad'a min tun shekaran jiya ta tafi, ni abunda ya ke k'ona min rai shi ne yanda ku ma dana ha茂fa kuka min biyayya kuka karb'i Mimi da hannu biyu, bare kuma 'yar da kuka haifa a ce ita ce zata bamu matsala."
Cikin ladabi da nutsuwa da girmamawa ya kuma sadda kan shi yace "Ayi hak'uri Hajia, insha'Allahu zamu gyara kurenmu."
Kawar da kai tayi tace "Shikenan Allah yasa, amma ku sani ban ji dad'i ba, kuma nayi niyyar tafiya gidan na ci uwar Aishan a gabanku, in ya so na ga zaku rama mata ne kamar yanda kuka taru akan baiwar Allahr yarinya, wannan ma ai shirme ne sai kusa na ji kamar tusa muku ita ne nayi a dole kuke zaune da ita."
Girgiza kai yayi ya d'an d'aga kai ya kalleta yace "A'a Hajiarmu, sam ba haka bane, mu kanmu iyayenta kun isa damu bare kuma ita."
Sake d'auke kai tayi tana sauke numfashi da k'arfi, dan har ga Allah jarumta ce tayi wajen yi mishi fad'an nan, abu ne da bai tab'a faruwa ba a tare dasu, shiyasa ko da Hafsat ta fad'a mata a waya abinda ya faru tare da cewa ta rok'a mata gafararshi yasa ta yanke shawarar dole ta nuna masa ita ma kamar uwa ce a gareshi. Cikin sanyin murya kuma ta d'ora da fad'in "Sannan Hafsat ta ce tana mai baka hak'uri akan abinda tayi, ta fad'a min ita ce da laifi ba Mimi, ita ta fad'a mata magana mai zafi, sannan ta ce na fad'a maka a d'an zaman da sukayi babu wani abu mai sunan raini daya shiga tsakaninsu, Mimi yarinyar kirki ce kawai wannan ma shed'an ne ya shiga tsakaninsu, kayi hak'uri ka ji."
Shi ma wani sanyayyen numfashi ya sauke yana lumshe ido lokaci d'aya kuma ya bud'e, kallon kofin hannunshi yayi yace "Ba komai Hajia na yafe mata, dama kuma ni babu abinda ta min, abinda na gani ne a ido ya min kama da za'a ci mutumcinta, ni kuma ba zan bari haka ta faru ba indai ba na daina numfashi bane, shiyasa na yi haka."
Jinjina kai tayi cike da k'aunarshi tace "Mun gode Allah ya biya, kuma ni ma insha'Allah zan je na samu iyayen na ta na sake basu hak'uri, dan kuwa ni ce nan na karb'a maka aurenta, dole wasu abubuwan su rataya a wuyana, kamar yanda idan kuka cuta mata to ni kuka ci amana."
K'anshi sadde kasa yace "Insha'Allahu ma haka ba zata sake faruwa ba Hajiarmu, amma kuma..."
Da kulawa ta kalleshi tace "Amma me?"
Cikin jin kunya yace "Bata gidansu tana wajen kakaninta, ina ga kamar bata san komawa ne ita ma shiyasa da muka tafi jiya tace bata da lafiya."
Dariya Hajia tayi tace "Allah sarki Mimi, ina k'aunar yarinyar wallahi, ai ko ni ce ita zanyi abinda ta yi, dole ta tsorata daku ta ga baku da adalci a rayuwarku."
Rufe ido yayi sai kuma yayi saurin d'aga kan shi yace "Hajia ki je ki bata hak..."
Shiru yayi dan ya tuna zai yi kwafsi fa a gaban suruka kuma uwar ta shi, murmushi Hajia tayi tana girgiza kai tace "Ba damuwa zan je na bata hak'uri, sannan na fad'a mata ba haka kake ba akasi ne aka samu yanzu ma, amma kai ma abinda nake so da kai shi ne ka bita a hankali kana lallab'ata har ta koma, kaga fa haka kawai sai kirana kayi a waya ka ce min ta tare a gidanta, na tabbata bata ji dad'in haka ba, to bana so yanzu ma tayi yaji a tilasta mata dawowa."
Yar dariya yayi yana jin wata kunya na rufeshi tare da tuna washe garin ranar daya angwnce ya kira yace ai ta tare gidanta, k'eyarshi ya shafa yana mai d'an turo hularshi a gaba yana sissine kai. Murmushi t sake yi tace "Shikenan Allah yayi albarka, Allah ya baku zaman lafiya da hak'urin zama da juna, ka tashi ka tafi lokaci na wucewa."
Da ladabi yace "Ameen Hajiarmu, nagode Allah k'ara lafiya."
Mik'ewa yayi suka sake sallama ya fita yana mai godiya ga Allah da yasa yau akwai wanda zai iya zaunawa gabanshi kanshi k'asa ya masa fad'a, lallai wannan ma babbar ni'ima ce a gareshi ace akwai mai fad'a maka ka ji.
Yana daf da shiga mota motar Asas ta danno hancinta cikin gidan, shiga yayi suka saita na su motocin zuwa k'ofar fita, tsayawa sukayi inda Asas ya tszya a daidai da motar sheikh, sauke glas duk sukayi suka kalli juna, dukansu mamakin yanda zumuncinsu ke neman ja baya sukeyi saboda mata, tunda akayi aurensu ta waya dai babu wanda ya nemi wani, Asas bai sake zuwa gidan shi ba har yau, hakan duk saboda abinda ya faru ne?
Murmushi Asas yayi cike da kunya yace "Sheikh barka."
Lumshe ido yayi alamar amsawa, cike da zolaya yace "Gashi kuma ganinka na zo kai zaka fita, tunda na ga yanzu amarci yasa ka manta da d'an uwanka."
Harara ya watsa mishi yace "Tunda kasan inda nake ka sameni a can."
D'aga gilashinshi yayi ya ma dreban umarni da su tafi, dariya Asas yayi yace "Zan zo har gidan na sameka."
K'arasawa yayi shi ma su kuma suka fice a gidan zuwa wurin aiki.
*10:46*
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:59 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*53*
Sak'o ta tura masa gahere kamar haka _"Me za'a dafa?"_
Sanda sak'on ya riskeshi dubawa yayi da kyau dan baya tunanin ta tambayeshi, a gajarce shi ma ya maida mata da _"Idan zan samu had'in salade ma ya wadatar."_
A gajarce ta sake maidawa da _"An gama."_
Shi ma a gajarce ya maido da _"Nagode."_
Fitowa tayi ta samu Iya zaune a cikin rumfar da take girki, zaune tayi Iya ta kalleta sama da k'asa ta girgiza kai tace "Mimi Allah ya shiryaki, kuma tun jiya ciwon bai sake dawowa ba."
Dariya tayi irin ta 'yan zamani tace "Haba Iya share zancen nan, kin san wani abu ma?"
Tab'e baki tayi tace "Sa茂 kin fad'a."
Cikin nutsuwa tace "Kinga sheikh ne yace na had'a masa salade, kinga kuma yanzu ba yara ke akwai ba da zan aika, shi ne na ce na aikeki mana."
Dak'uwa Iya ta mata tace "Uwarki! Wato ni da aurena ba aure bane ko?"
Dariya Mimi tayi tace "Ba haka bane Iya, to idan kinyi niyya ki barni na je da kaina mana na siyo."
Wata dak'uwar ta kuma yi mata tace "Uwaki, an k'i a barkin."
Turo baki tayi ta tura k'afafunta kamar zata hamb'are Iya tace "To ni wanga tsohuwar na rasa gane miki, yanzu kuma so kike na sab'a umarnin mijin na wa ko me? Na ce ki je