Showing 1 words to 3000 words out of 230725 words

Chapter 1 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1035

https://my.w.tt/9J8gWVc


🕯️*ƘARFEN ƘAFA* 🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmanir Raheem.



(1)

Ta faka motarta ƙirar Peugeot 406 , kalar sararin samaniya. Ta kai duba ga agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta na dama. Ganin akwai sauran mintuna ya sa ta zare wayarta daga chaji ta shiga dannawa. Hankalinta ya kai ga saƙon da ya faɗo wayarta kai tsaye maimakon daya cikin kafafen soshiyal midiya da take amfani da su. Murmushi ta yi wanda har siririn wushiryarta ta bayyana a fili ganin sunan wacce ta turo saƙon.
"Muhibbat." Ta furta a fili. Saƙo ne kamar koyaushe na gaisuwar juma'a. Ta aikamata da reply sannan ta ajiye wayar a gaggauce ganin har sha biyu ta gota. Fitowa ta yi bayan ta gyara zaman mayafin abayarta. Ba ka ganin komai a jikinta face fuskarta da tafukan hannunta sai kuwa ƙafafunta da suka sha jan lalle. Bayan security man ya tsayar da motocin dake shige da fice don bada dama ga iyaye da yara su tsallaka, ta shige kanta tsaye cikin makarantar. Tun kafin ta karasa garesu suka taho a guje suka rungume ta. Ta rungumesu sosai, gami da saka yatsa saman goshin babbar ta tura ta baya kadan.
"Ji, ke ko kunya ba kya girma? Har da ke a waɗanda za'a runguma?"

Yarinyar ta turo baki tana gyara zaman jakarta gami da hararar kannennata dake faman yi mata dariya.

"Mommy ki musu magana, kuma ai kin ce ni ce mai sunan Hajiyarki kin fi sona."

Nan da nan yaran suka yi mata ca kowanne da kalar korafinsa, idan da sabo ya ci ace ta saba da hakan, ba ranar da za ta zo ɗaukarsu daga makaranta basu chajamata kai ba. Su uku amma hayaniyarsu ta fi ta wasu biyar din. Dakyar ta haɗa kansu, wannan yana bai ga jarkar ruwansa ba(water bottle), wannan yana an yagamasa littafi. Bayan ta samu sun zauna a motar ta yi musu tsawar da duk suka nutsu, sannan ta soma tuƙi. Ta madubi ta saci kallon autansu Affan yana yiwa ɗan uwansa raɗa a kunne. Murmushi ta yi gami da girgiza kai daidai lokacin da ta ɗau hanyar da za ta sadata da unguwar Sharaɗa. Tana son yaranta har cikin ranta, zama tare da su ya fiyemata komai. Tana ƙara tabbatarwa su ne mahaɗin rayuwarta, farin cikinta da komai ma, ba don ta rasa mahaifa ba, a'a sam, sai don kasancewar su din kusan basu da kowa da zasu kalla su yi alfahari da samunsa a rayuwarsu sai ita. Ita ce komai nasu a yanzun da rayuwa ta zo musu da tarin sauye-sauye. Bata ankara ba sai ji ta yi ta ci karo da abu. Nan da nan ta ja burki tana salati, shima mai motar bai ko motsa ba, ta kai duba ga ta'adin da ta yiwa motar. A kudi da tsaruwa, ba za'a haɗa motar da nata ba, mota ce red in colour, ƙirar Hyundai Accent. Diyarta wacce tuni ta wangale baki tana girgiza harshe sama da kasa cikin fadin "Lalalala, tab!" Ta ƙarashe ganin yanda Mominsu ta tarwatsawa mai motar fitilar baya (tail light). Ba ta ko kalli ƴar ba don hankalinta ba karamin tashi ya yi, ta bude murfin motar ta fito a gigice. Jama'ar da ke wurin wadanda tare aka tsayar da su a junction duk suka zuba ido suna jira su ga kalar rashin mutuncin da mai motar zai yi mata, tana tsinkayar muryar wani dake goye a baya babur yana fadin.
"Ahaf, ai sai macen, dama daga ganin tuƙin kalar ta matan ce. Allah dai Ya kyauta."

Ba ta ko kalleshi ba ta ƙarasa ga motar tana mamakin rashin fitowar mai motar wanda daga ɓarnar da aka yi gareshi ya ci ace ya fito, idan ma faɗan ne ko marin ayi a wuce wajen. Cike da fargaba ta kwankwasa gilashin zaman direba. Ba ta yi na biyu ba, aka zuge gilashin, ta ji faduwar gaba nan take. Da alama ba ma a hayyacinsa yake ba.

"Yes?"
Ta shanye razanar da ta yi a farko ta amsa tana mai nuni da inda ta ɓarnatar.

"Wallahi bansan na yi ba, don Allah ka yi hakuri."

Ta ƙarashe ba don tana da tabbacin ya karɓi tubannata ba, itama a jikinta ta ji cewar ta rainamishi hankali. Ta yi ɓarnar dubunnai kuma ta tsaya bada hakuri.

Ta gaji da kallonta da yake ta janye nata kwayar idanun cikin fidda tsammanin zai yafe ganin har an bada hannu motoci na shan gabansu suna ficewa. Ya kauda kai gami da fadin.

"Kar ki damu, ba komai."

Bai bata damar godiya ba ya zuge gilashinsa ya ja mota. Ta koma nata motar bayan kallon gilasan da suka tarwatse a ƙasa, a sanyaye ta tashi motar ta bar wurin.

'Kamar a buge yake fa.' Sai kuma ta yi saurin jan istigfari da saƙe-saƙen zuciyar da take kan abinda ba ta da hujja.

"Momi ba kowa a motar?" Tambayar ɗanta na biyu ya katseta. Ta basu umarnin su yi shiru kafin ta cigaba da tuƙi jiki a sanyaye, har ga Allah ta gama tsorata da ɓarnar da ta yi, ba ta son rikici ko tashin hankali. Sai kuma lamarin ya zo mata ba yanda ta zata ba.
Ta share zancen sa'ilin da ta iso gidannasu. Maigadi ya bude babban kyauren suka shige yaran na ɗagamishi hannu yana maida martani cikin dariya. Sai da suka fita sannan ta saita mazaunin motar can ƙasan ƙaramin rumfar ajiye motocin gidan.

Da gudu yaran suka faɗa jikin wata dattijuwar mace dake zaune a falo tare da baƙuwarta. Tana dariya ta rungumesu.

"Oyoyo yaran Hajiya, maza aje a cire kaya. Ke kuma ƙawata wa ya taɓa min ke?"
Hajiyar ta furta tana miƙawa yarinyar hannu. Ta kuwa karasa ta zauna cike da shagwaɓa ta ce.

"Ba Momi ce ba, wai nayi girma ba za ta rungumeni ba."

Ta ba Hajiya da baƙuwarta dariya, ya yi daidai da sallamarta. Ganinta ne yasa yarinyar miƙewa da gudu ta yi ciki. Ba ta ce uffan ba ta ƙaraso ta zauna tana gaida baƙuwar Hajiya.

Da fara'a ta amsa kafin ta maida kai ga Hajiya.

"Yanzu wannan Ramlatu ce ta girma? Kar ki cemin duka wannan bataliyar ƴaƴanta ne?"

Jin matar ta ambaci sunanta ya sanya ta kallonta dakyau duk a kokarin ta ga ta tuna fuskarta, sai dai Allah bai sa ta tuna ɗin ba.

"Ita ce Hajiya Karama, ai shekarun ba kaɗan ba. Ba ki ganeta ba ko? Kin tuna makwaftanmu na tsohon gida na Yakasai? Duk da dai lokacin ba ki fi ƴar shekara goma ba, da wuya ki ganeta."

Ramla ta yi shiru tana dan murmushi, tabbas sai yanzu ta dau fuskar. Tambayar a inda take aure da matar ta yi ya sanya ta daukar jakarta ta mike bayan ta dubi Hajiya.

"Bari na ga yarannan." Daga haka ta yi gaba zuwa ɗan corridor da zai sadata da dakunan baccinsu. Wacce aka kira da Hajiya Karama ta bi ta da kallo cike da mamakin daukewar murmushinta alokaci guda, Hajiya wacce kunya duk ta kamata na watsawa Ƙawarta ƙasa a ido da Ramla ta yi, ta yi kokarin sauya akalar hirar, itama ba shiri ta saki don ta yi dana sanin tambayar.

Sai da ta tabbatar yaran sun kimtsa, kowanne ya sha kwalliyar juma'a sannan ta koma ɗakinta bayan ta gargaɗesu da shigowa. Daga nan ta kama hanyar fita, idanunta ya kai ga Affan da ya sha jalla iya fara ƙal, ya turo baki kamar zai yi kuka. Danne dariyarta ta yi sannan ta wuce, ta san hukuncin ne bai mishi ba, yaro ne mai maƙon uwa, ba ya kaunar abinda zai sa shi nisa da mahaifiyartasa. Ita kuma a yanda take jinta ba ta kaunar hayaniya ko kusa, so take ta samu kaɗaici ko za ta ji sassaucin abinda ke shirin dawomata. Takan tsinci kanta cikin wannan yanayin duk sadda aka yi mata batun aure ko abu makamancin hakan.
Kwanciya ta yi saman gadon bayan ta cire doguwar abayar dake jikinta ya kasance daga ita sai shimi da dogon wando tight. Shiru ta yi tana kallon akwatin dake saman sif dinta, abubuwa da yawa ne acikinsa, kusan za ta iya cewa kaf tarihinta yana ƙunshe cikin wannan tsohuwar adakar. A gaggauce ta juyawa sif din baya gudun kada ta aikata abin dana sani. Lumshe idanunta ta yi a hankali bacci ya dauketa.

Ba ita ta farka ba sai wuraren karfe uku da mintuna, shi dinma sanadiyyar tokaremata ciki da ta ji anyi ne, ta ƙurawa yaron ido tana kallonsa, babu ta inda ya baro mahaifinsa. Ko kaɗan bai dauki komai daga halittarta ba. Gyara kwanciyarsa ta yi, ita ta sani, Affan ba ya hakurin rashinta a kusa matukar ba makaranta ya tafi ba ko kuwa ita din tana wurin aiki. A hankali ta dafa kansa ta mishi addu'a sannan ta sauko ta faɗa wanka. Babu sallah a kanta kasancewar tana fashi don haka tana zura doguwar rigar atamfarta falon ta nufa. Wannan karon Hajiya ba ta nan sai yaran dake zaune tare da Kanwarta wacce ake dab da bikinta, A'isha, suna kallon Frozen 2 a tashar mbcmax. Ba ta ce da su uffan ba ta faɗa kicin. Talatu mai aikinsu ta iske tana hada-hadar ɗora girkin dare. Suka gaisa sannan ta fito rike da robar ruwa sai lemun, saman dining ta nufa ta ɗibi shinkafa da miyar da aka dafa sannan ta dawo wurin yaran ta zauna.
"Ina Hajiya?" Fadin Ramla bayan ta soma kokarin kai lomar abinci baki tana duban A'isha.

"Yaya Munir ne ya zo, su na ciki suna magana." Ta gyada kai kafin ta maida kan yaran da suka ƙurawa farantinta idanu kamar ba su ci ba. Kallo daya ta yi musu duk suka juya kai basu kara marmarin kallonta ba. Ba kaɗan suke shakkar uwartasu a lokuta da dama ba.
Sai da ta kammala tsaf ta sha ruwa gami da gyatsa da hamdala kafin ta mike ta kai komai kicin ta nufi hanyar ɗakin Hajiya.
Da sallama ta shiga, kallo daya Yaya Munir ya yi mata ya ja kai gefe. Ta yi kokarin shanye wannan ɓacin ran da ya assasawa zuciyarta wanda har ta ji kamar ta juya ta fasa gaidashi. Sai dai kuma ba yanda ta iya ganin Hajiyar ta ganta, ta karasa shiga ta gaida Yayannata. Bai ko kalleta ba ya amsa da "Lafiya." Ya maida hankali ga Hajiya da ke lissafa mishi duk wani abu da suke bukata a gidan dangin cefanen kayan masarufi.

"In sha Allah zan sallameki Hajjaju nan zuwa anjima komai da kika bukata zai iso. Allah Ya kara rufamana asiri dai."
Da murmushi ta amsa da Amin kafin ta daga murya ta kira Ramla wacce tuni ta kai ƙofa. Shi Munir mutum ne marar dadin sha'ani a wasu lokuta, ga riƙo da fushi. Sau da yawa sai tunaninta ya dinga faɗamata cewar ai don ya yi abin duniya ne sama da kowa a gidan shiyasa yake gorantamata game da lamuran da babu wani da ya isa ya goge faruwarsa cikin kaddarar rayuwarta tunda dai haka Allah Ya tsara.
"Na'am." Ta amsa tana duban Hajiya, ya yi daidai da mikewar Yayannata zai fice, Hajiyar ta dakatar da shi ya koma ya zauna ransa a hade don yasan tatsuniyar gizo bai wuce na ƙoƙi. Itama ta zauna ta russunar da kai, har yau tambayar da ta kasa ba yaranta cikakkiyar amsa shi ne. 'Meyasa Uncle Munir ba ya son mu?' Ta hadiyi miyau dakyar, maƙogwaronta har ɗaci yake.

"Meyasa haka? Wace irin rayuwa ce? Wane irin halayya ku ke son nunawa? Muniru ba ka jin magana, ba ka ji. Muniru komai lalacewarka naka, naka ne. Hakanan za ka yi hakuri ka shanye dukkan wani abu da zai aikata mai muni ko akasinsa. Ba zai yiwu a sauya abinda ya riga ya faru ba, wanda aka yi a baya ya isa! Ya isa don Allah, ban taɓa sanya maku baki kan wannan lamari ba sai dai hakan ba wai yana nufin abin ba ya damuna ba. A manta da komai ko don albarkacin yaran da basu ji ba kuma basu gani ba. Kai ne babba, yau ba ran Alhaji, kai da ya kamata ka janyo ƴan uwanka a jiki ku hada kai a lokacin da nima ƙiris ya rage ƙasa ta rufen nawa idon, sai ya zamana ba haka ba. Wannan riƙo naka ba inda zai kai ka, inace ko Hilal a yanzu wasa da dariya yake da Ramlatu? Sai kai mai daukarwa kanka dala ba gammo? Da alama kai ne Bilkisun."

Hajiya ta jefamishi baƙa sannan ta ci gaba da fada, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, daga uban gayyar har ita suka hau bata hakuri, Ramla banda kuka ba abinda take yi. Sai da Hajiya ta tsagaita sannan ta magantu.
"Ya zan yi mishi Hajiya? Ya zan ɓullowa mutumin da ko arzikin gaisuwata idan ya amsa bai wuce don ganin idanun jama'a ba? Shikenan na fita a sahun Dan Adam? Ashe ba zan yi laifi da zan roki Dan Adam irina gafara ya yafemin ba? Kar fa a manta nima ajiza ce, idan hakan bata kasance ba ina ƙaddara za ta jefani? A titi zan haifi yarannan uku?"
Kuka ya ci karfinta, Munir ya yi shiru kansa a ƙasa, maganganun Ramla sun shige shi sai dai bai ko kalleta ba ya kara maida hankali ga Hajiya murya a raunane.

"Ina mai neman gafararki Hajiya, In sha Allah ba za ki ƙara kuka akan matsalata da ita ba. Daga yau na yafemata. Zan kuma ci gaba da kula da ku gaba daya. Allah Ya yafemu baki daya."

Hajiya ta murmusa tana mai amsawa da amin, sai lokacin Ramla ta sassauta kukan ta rarrafa ga Yayannata ta soma magana.

"Ka yafemin Yaya Munir, nasan na yi maka laifi. Ka yafemin don Allah."

Ance jini jini ne, ya ji tausayinta sai dai bai ji cewar zai iya mance abinda ta yi ba. Kallon da yake mata ya sanya ta jin kunya da nauyi, ta ya za ta mance munanan kalaman da bakinta ya taɓa furtawa gareshi? Ta ina? Sam a'a, sai ta ji kamar a yau ne take fadi, kamar a lokacin take kallonsa tsakar ido tana fadin abinda ke ranta babu ko shakka. Ta sadda kanta kasa tana sharar hawaye.

"Shikenan, ya wuce. Allah Ya yafemu baki daya." Daga nan ya mike ya musu sallama ya tafi, ta karasa jikin mahaifiyarta gami da kwantar da kai bisa cinyarta, Hajiya ta dafa kanta tana murmushi.

"Ai an gama Ramlatu, da yardar Allah tunanin Muniru ba zai ƙara jefa zuciyarki cikin kunci ba. Allah Ya yi maku albarka, Ya jikan mahaifinku." Ta ƙarashe cikin rawar murya, ta amsa itama tana mai jin saukar hawaye. Sai dai can ƙasan ranta, zuciyarta na fadi mata akwai saura! Kada ta yi saurin yarda da zantukan Yaya Munir.

Suka dan taɓa hira da Hajiya sannan ta fito falon, nan ta hangi Affan tsaye yana kuka yayyun na mishi waƙar Amalala. Duba ta kai ga A'isha wacce ke latsa waya tana dariyarsu, dama ba ta sa a rai za ta taimaka mata da wanke jikin yaron ba. A zamanin da ake ciki zai yi wuya a samu kanne masu wannan biyayyar ga ƴan uwansu. Kowacce son jiki da kwuiya ya mata katutu.

Sai da ta tsawatar ta kimtsa yaron yana kai ƙararsu cikin jagwalgwalon maganarsa, ta lallaɓashi suka fito falon bayan ta danna inda ya yi fitsarin. Abinci ta zubamishi tana sanyamishi a baki, a hankali ta kai duba ga katon frame din su na family photo dake manne a can bangon wurin dining ɗinnasu. Sau da dama sai ta ga kamar mahaifinnasu bai mutu ba. Kamar ka kira sunansa ya amsa.

"Wai nikam Anti Ramla, ba ki da labarin Yaya Munir shima zai yi aure?"

Muryar Aisha ta maidota daga duniyar tunani. Ta ji maganar banbarakwai wai namiji da suna Hajara.

"Kai A'isha."

Cikin sanyin jiki A'isha ta mike zaune gami da taɓe baki.

"Wallahi kuwa. Za ki gane wata ƙawata Hunainah? Wacce muka hadu a chat? Duka-duka zuwanta gidannan bai fi uku ba suka hadu. Ashe soyayya suke, ai yanzu ko magana ba na yi da ita. Ban kuma nunawa Anti Bilki sanadiyyata Yaya Munir ya ga Hunainah ba. Bana fatan ma ta sani."

Ta ƙasashe tana yanƙwane fuska, ga dukkan alamu auren na Munir bai mata ba. Ita kuwa Ramla kai ta shiga jinjinawa, ikon Allah kenan. Har aure Yayan zai yi ba ta da labari? Ta kasa cewa komai sai ta yi yaƙe.

"Na ganeta kam, wata ƴar Gombe da ziyara ya kawota Kano. Allah Ya sanya alheri, Ya hadamishi kan iyalinsa."

A'isha ta amsa da Amin kafin ta shiga labartamata irin rashin mutuncin da Uwargidansa Anti Bilki ke tata mishi. Murmushi ta yi, duk da a yanzu ko magana Bilkin ba ta mata, amman ta tayata kishi. Ta kuma san yanda suke da A'isha, kusan duk gidan ma jininsu ya fi haduwa da ita.

"Banda abin Anti Bilki, ta kai zuciyarta nesa mana. Komai idan ya faru mai wucewa ne, wuyarta a yi."

A'isha ta taɓe baki ba ta kara maganar ba ganin kamar wacce take yiwa, ba za ta bata damar aibata lamarin ba. Karshe ta kira yaran su zo ayi Ludo Game a waya. Aikuwa har da Affan a ƴan kallo. Ta tattara wurin da ya abincin ya ɗan zube kafin ta mika kicin. Da sauri-sauri ta koma ɗakinta ta kulle da muƙulli. Zama ta yi gami da fashewa da kuka. Anya watarana hawayenta ba zasu ƙare ba? Anya ba za'a wayi gari sun ƙafe ba? Rasuwar miji kan zama tonon silili dama? Ko kuwa dai abinda ta shuka ne take girba? Har ɗan uwanta na shirin ƙara aure ba ta da masaniya? Ta kai duba ga hotonsu dake cikin frame saman bedside drawer dinta, su biyar cif da iyayensu suka haifa. Kowannensu fuska cike da fara'a, a sadda suka yi hoton duka-duka shekarunta tara a duniya. Ta kai hannu ta dauka tana duba.
Mahaifinsu Alhaji Khalid Mu'azzam dattijon arziki mai kamala. Ya taso a maraya, ya rayu gidan ɗan uwan mahaifinsa Malam Abdullahi har zuwa girmansa a hannun Uwargida Hajja Zulai. Asalinsu garin Daura dake jihar Katsina, neman kudi ya kawo iyayensu nan Kano aka yada zango har suka zama ƴan gari. Alhaji Khalid bai da ilimin boko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login