Showing 48001 words to 51000 words out of 230725 words
laifi, ki yafemin don Allah."
Zuciyar uwa mai rauni, ta cika da tausayinta. Tausayi na abinda take hangomata wanda ita ba ta hanga ba. Shaye-shayen da Abba ya ce Aliyu na yi ya tsayamata a ƙahon zuciya. Ta daure ta mike bayan ta zame jikinta.
"Ku wuce Uwani, dare yana yi. Allah Ya bada zaman lafiya."
Ba tare da ta ƙara magana ba ta shige banɗaki, Zulaihat wacce ko a jikinta ta amsa da Amin kafin ta ɗago Ramlat.
"Mrs Aliyu mu karasa ga Abba ko?"
Ta riga ta ɗan kusan da biyu Zulaihat ke kiranta da hakan, suka shiga Abban na zaune saman darduma yana karanta Alkur'ani mai girma. Ya ɗago ya dubesu, tunda ya dora idanu akan Ramlat bai kifta ba.
"Ramlatu an fito?"
Yanda ya furta cikin taushi ya sanya zuciyarta kara narkewa. Ya yi ƴar dariya.
"To mene abin kuka? Yanzu kin zama matar aure. Komai ki ka yi, ko za ki yi ki sani cewa Allah Yana kallonki. Ki ji tsoronSa wajen gudanar da lamuranki. Ramlatu duniya da kike gani tana da faɗi, sai dai zuƙatanmu sun fi ta faɗin. Idan mun yarda da hakan, mun cikata da alhairai masu yawa, mun yi irin aikin da Allah Zai farin ciki da mu. Mu zama cikin ceto AnnabinSa s.a.w. Duk isa da taƙamar mace, ba komai ba ce a wurin mijinta. Ki rike wannan, ki bi mijinki sau da kafa. Kar ki sake ki zama mai tona asirinsa."
Abba ya ci gaba da koro jawabai, ba Ramlat kadai ke kukan ba, hatta da Zulaihat kukan take. Kukan tausayin wannan uba mai matukar don ɗiyarsa da alheri, mai mafarkin ya ga ta yi aure a inda ba za ta taɓa wulakanta ba. Sai dai kash, burinsa bai cika ba.
"Nagode Abba, Abba kaima ka yafemin. Hajiya ta ƙi yafemin. Abba ka tayani roƙonta."
Nan take ya umarci Zulaihat ta kira Hajiya. Ta bi umarninsa sai gasunan tare.
"Na yafemata idan don haka ka kirani."
Ta tari hanzarinsa don tasan kafiya irin ta Ramlat da naci.
Murmushi ya yi.
"Mun gode Hajiyarmu. Ban riƙe ki ba a rai kinji Ramlatu? Tashi ki tafi dakin mijinki. Allah Ya yi muku albarka. Ya dauwamar da ku a dakunan da'iman."
Daga nan suka mike zasu fita, dakatar da su ya yi. Da kansa ya taso ya lalubo hannun Ramlat wacce lallenta na tun bikinta da Hilal shi ne a hannun, har baƙin ya soma gogewa. Alkur'ani mai girma ya sanyamata a ciki.
"Babu wani hasken da ya wuce haskenSa. Babu magani da kuma waraka face ta hanyar karantashi da kuma addu'a. Kar ki yi wasa da tilawarsa."
Wani kukan ta kara kecewa da shi, maimakon Abban ya koma mazauninsa, sai ya kama kafaɗarta ya yi mata rakiya har cikin motar da Aliyu ya turo. Iyayen Aliyu su na kallo, sannan ya koma cikin gidan zuciyarsa a karye.
***
_*MRS ALIYU*_
Ya kara jawota jikinsa ya rungume, kuka take sosai. Duk kuwa da cewar ta tsarkake jikinta ba ta bar jin radadi-radadi ba.
"Haba Baby, damuwa kike son na shiga ne? Sai kuka kike, ya zan yi miki ki daina?"
Ta soma ƙoƙarin tureshi daga jikinta.
"Ni ka rabu da ni."
Ya yi murmushi gami da kara kankameta.
"Ni ba zan iya rabuwa da ke ba Baby. Ki yimin duk abinda kika san zai sa ki huce. Kinji?"
Ta turo baki, ya sa hannu ya shiga sharemata hawaye.
"Fadamin me kike son na yi miki a rayuwa kwatankwacin wannan farin cikin da kika ban, kinsan an ce yaba kyauta tukuici."
Ta tsinci zuciyarta da jin dadin kalamansa. Ba ta san sadda ta yi murmushi ba. Damarta kenan, ya kuma kamata ta yi amfani da shi kar ya wuce.
"Karatu nake son ka bar ni na ci gaba."
Ya rungumeta yana ƴar dariya.
"Wannan mai sauki ne Baby. Ki ajiye a ranki kin yi karatu kin gama, wannan ya zamemin kamar farilla, fadi wata bukatar."
Ta yi shiru, jin saukar dumin hawaye saman fatar kirjinsa ya sanya shi ɗago haɓarta yana dubanta.
"Baby, meyasa?" Ya yi maganar kamar mai raɗa. Ta sauke kwayar idanunta daga kallonsa.
"Sanadinka na shiga tarin matsaloli. Na jure dukkan wuya, na karya dukkan alƙawura, don Allah ka rikeni amana, ka bani kulawar da iyayena da dangina zasu aminta da zaɓina. Ina son mu ba marar ɗa kunya."
Ya yi murmushi.
"Kina shakku a kaina ne? Ko kina kokwanto akan son da nake miki? To ki daina, har mai ɗa sai mun ba kunya a zamantakewarmu. Ki kwantar da hankalinki."
Ta yi murmushi, so da kaunarsa na ninkuwa cikin ranta. Nan kuma labarin ya sauya.
***
Soyayya ce tsantsa ke gudana a gidan masoyan, Aliyu dakyar yake iya fita kasuwa ya ga yanda yaransa ke tafiyar da lamura. Iya soyayya da shagwaɓar Ramlat har mamaki yake ba shi. Hakan ke kara susutar da shi. A wannan lokacin yana takatsantsan da shan dukkan wani abun maye a gaban Ramlat.
Sai da suka cika sati biyu da aure sannan suka shirya zuwa gaida iyayensa. Ta haɗe cikin leshinta maroon ta yafa farin mayafi sai takalmi da jakarta suma farare. Ta yi ado daidai gwargwado, ta ciko kadan, ramarta ta ragu sosai. Hakan ya ƙaramata kyau.
"Babyna kin yi kyau kamar mu fasa fitar."
Ya fadi yana rungumo ƙugunta. Ta watsamishi kallon soyayya ya kama saitin kirjin gami da lumshe idanu yana murmushi.
"Ahh, kasheni za ki yi ko?"
Dariya sosai ta shiga yi ta kwace jikinta.
"Muje don Allah."
Ya kamma hannunta suka nufi motarsa. Tafiya suke suna jinsu kamar a gajimare. Wakar Nazifi Asnanic mai taken Jamila da Jamilu shi ke tashi a motar, hannunsa na dama cikin tafin hannunta. Ji take kamar ba ta da wata matsala da ta yi saura a duniya, kamar wata sarauniya haka take ji musamman yanda Aliyun ke rera wakar yana dubanta jefi-jefi. Har suka iso wakokin soyayya daga Asnanic da Nagudu kawai suke ji.
"Mun iso Madam."
Ta ɗan harareshi da wasa sannan ta yunkura da zummar maida takalminta da ta cire a zaman motar. Kafafunta suka taka wani dunkulallen abu kamar takarda. Ta sa hannu ta dauka sa'ilin da ta zura takalmin. Daidai sadda Aliyu ya bude mata murfi ta fito. Kirjinta ne ya buga, ko ba ta shan sigari, ta san wannan dai karan sigari ne.
"Mene wannan?" Ta tsinci kanta da watsa tambayar duk don ta samu tabbaci. Yatsuntsa ta ji ya sa ya karba gami da yin cilli da shi yana tsaki.
"Wannan banzan ne, G Baba ya sha min a mota."
Ta ji hankalinta ya kwanta, ta sauke ajiyar zuciya.
"Muje Baby, yau Kakus za ta ganki."
Ya karasa zancen da riko hannunta su soma tafiya cikin son basarwa. Har ga Allah ta yarda da zancensa.
***
"Masha Allah, ashe kishiyartawa itama ba baya ba kamar wata balarabiyar Sudan."
Dariya Aliyu ya yi, itama Ramlat murmushi ta yi gami da ƙara sunne kai. Abulle kuwa har ranta ta ji tana son Ramlatun, ta dage akan sai ta ci abinci, a dole ta tsakuri tuwo miyar agushin da ta diremata. Daga nan suka fice sashin mutan gidan. Jikin Ramlat ya yi sanyi matuka da irin tarbar da ta samu a gurinsu, ta dauka zasu kaunaceta kamar yanda Abulle ta nuna, sai dai abin ba haka ba.
Bangaren karshe da suka shiga, bangaren Justice. Aliyu ya nufi falon Justice yayinda ya ce ta shiga ciki. Shi kam banda ma dole da Abulle ta yi mishi da ba zai shiga ba. Hajiya Maryam ta kalleta ta watsar, tun kan su shigo labari ya zo mata daga bakin Autar Kawu AbdulRashid, Hannatu.
Sanye cikin hijabi ta fito daga dakinsu don amsa kiran Mamarta. Ta ci karo da Ramlat zaune ƙasan kujera ga Mamar ta kurawa talabijin idanu abinta.
"Muhibbat, ga matar Aliyu ta zo a gaisa."
Kusan lokaci guda suka kalli juna, kowannensu kallon ƙurillah yake yiwa ɗan uwansa. Kowacce so ta ke ta gano abinda ta fi ƴar uwarta.
Bangaren Ramlat, kammanin Aliyu take gani a fuskar Muhibbat. Shakka babu ba ta hango abinda za ta gwada mata ba.
Hakanan Muhibbat, sai dai ta ce da Ramlat din baƙar fata a kanta, banda wannan ba za ta ce ga abinda za ta gwada mata ba itama.
Murmushi suka saki a tare, murmushin da ya fi zama na yaƙe. Kowanne na kokarin danne abinda ya ke ji game da ɗan uwannasa.
Suka gaisa a mutunce sannan Muhibbat ta koma ɗakinta. Rufe kofa ta yi ta sauke ajiyar zuciya. Ya dace ta shafe komi a yanzu itama ta ci gaba da gudanar da rayuwarta.
A bangaren Ramlat, sai ta hango wani sanyi da taushin zuciya a wurin Muhibbat din, ba ta taɓa zaton ma za ta jure ganinta koda da sakan daya bane. Sai ta kasance mutan gidan ga dukkan alamu su ke tayata kishin. Tana nan zaune har Aliyu ya turo a kirata, ya dubi kwayar idanunta yanda ya sauya. Cikin sauri ya tallafi fuskarta.
"Baby meke faruwa? An fadamaki wata maganar ne?"
Ganin hanyar baranda ce ta shiga falon Justice, sannan hanya ce ta jama'a yasa ta kauda fuskarta tana murmushi.
"Ba komai. Mu tafi."
Sauke ajiyar zuciya ya yi.
"Na dauka wani abin suka fadamaki yanzun na shiga na nunamusu ainahina."
Mamakin kalaman ya sanya ta dubansa, sai dai tuni ya soma tafiya yana bata umarnin ta biyoshi.
'Kin manta sunansa Aliyu? Gadanga ƙusar yaƙi. Ba dai zuciya ba.'
Faɗin wani bangare na zuciyarta. Ta samu tarba mai kyau kamar yanda ta zata, don dukkan dattawan sun karɓeta hannu bibbiyu da salama. Banda mata da sauran yan uwan Aliyu, wasu ƴan mata ma tana jin sadda suka saki wata shewa da guɗa, ta kuma san da ita ake.
A mota shi ke ta zuba hira banda ita, ta karanci abubuwa da dama a gidansu Aliyu.
Amman kuma suna isa gida ta bar zancen a gefe guda a ƙasan ranta saboda soyayyar da Aliyu ya shiga nunamata mai kashe duka lakan jiki.
***
Tsakaninta da iyayenta sai waya, za ta kira su dauka a gaisa. Yaya Munir kuwa ta tabbatar blocking dinta ya I daga kiransa don a farko sai ta jira ya yi ta ringing ba zai ɗaga ba, yanzun kuwa gaba daya ma ta bar samunsa. Amrah kuwa ƙarara ta fito ta yi mata kaca-kaca akan ba ta son kiranta. Itama karshe ta nunamata tana da zuciya, ta tattara ta watsata a kwandon shara.
Sakamakon jarrabawarsu ta fito, Aliyu da kansa ya shiga fafutukar nemarmata Admission a B.U.K.
_"Kai Baaba, kar ka yarda matarka ta fi ka Degree idan kuwa ba haka ba kana cikin kwale-kwale."_
Sa'ad ke ba shi wannan shawarar sadda ya shiga jami'ar Bayero wurinsu. Shi kam bai jin wannan a dalilin da zai tauye farin cikin Ramlat. Ko ba komai shi ma DAN ADAM ne, yana da zuciya, ya kuma yarda da cewar ta mishi halacci.
_"Bar ɗan iska! Wato kai za ka yi jidalin kudin karatun ma?"_
G Baba ya furta hakan. Aliyu ya toshe kunnensa ya kuma zagesu tas. Karshe suka zuba ido su ga gudun ruwansa.
***
*WASA FARIN GIRKI*
Tsalle ta shiga yi har da juyi kafin ta kara wani tsallen ta faɗa jikin Aliyu, ya kuwa yi mata kyakkyawar runguma suna dariya. Murnar ba ta komai ba ce illa ta samun Admission a jami'ar Bayero.
"Wash! Baby karyamin wuya za ki yi wai?"
Ta sakeshi suka yi dariya.
"Ban isa ba Sweet Aliy. Nagode sosai sosai. I love You so much."
Ya ja hannunta ta faɗa jikinsa.
"Muje ki nunamin a zahiri."
Daga nan ya shiga yi mata raɗa a kunne. Ta kauce suna dariya.
Sai da komai ya kammala sannan ta yi mishi rakiya har wurin motarsa, kamar kar su rabu haka ya ja ya fice Kasuwa.
Wayarta ta dauka da zummar kiran Hajiyarta su gaisa, sai dai abin takaici ba kudi a ciki. Nan take ta tuna katin da Aliyun ya siyamata a darenjiya da suka fita shan ice cream, yana tsokanarta akan ba zai bata ba sai ta ce tana sonsa sau cikin carbi, ita kuwa dariya kawai ta yi. Daga nan ya zura a aljihu ta mance ba ta karɓa ba.
"Alhamdulillah." Ta furta a bayyane cike da nishadi, ta nufi dakinsa. Kai tsaye wandon da ya cire jiya ta fiddo a kwandon zuba kayan wanki. Zura hannunta keda wuya, ta ji kwali da wani abu. Ba ɓata lokaci ta ciro duka. Kirjinta ya bata dam!
"Kwalin taba da lighter?"
Ta faɗi a mamakince, zama ta yi gefen gado jiki ba ƙwari, ta kasa yarda Aliyu mashayin taba ne. Ganin komai ta ke kamar a mafarki.
'Ba ki ganin yanda leɓɓansa keda duhu?'
Faɗin wani sashi na zuciyarta. To ta ya za ta yanke hukunci da hakan bayan cewa akwai masu irin halittar? (Baƙin leɓe)
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Allah Yasa tunanina ba gaskiya bane."
Ta fadi a fili. Kamar ta maida inda ta ganshi, sai ta barshi a saman gadon don kawai ta ji me zai ce. Jiki ba kwari ta shiga laluba daya bangaren, anan ta ci karo da katin wayar ta ciro, ta maida wandon kayan wanki ta fita.
Murnar da take duk ta dusashe don haka koda ta gama shigar da katin a waya, sai ta ɓige da rubutawa Abba text tana mai sanarmishi da cewa ta samu Admission a B.u.k.
***
Abba na zaune sun karyawa a falo, da iyalinsa. Wayarsa ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ya kai duba sa'ilin da yake kokarin kurɓar shayin citta da kanumfarin Hajiya. Ganin sunan Ramlatu na yawo a saman wayar yasa shi ajiye kofin a gaggauce ya bude sakon. Murmushi ya ɗan yi.
"Madallah."
Ya furta cike da dakiya. Hajiya ta dubeshi tana murmushin itama. Suka hada ido.
"Ƴarki ta samu gurbin karatu a jami'ar Bayero. Sai ki bita da addu'a."
Idan ya ce ƴarki, ta gane wacce yake nufi, don haka ta kauda kai ciki-ciki ta ce.
"Allah Ya bada saa."
Abba ya amsa da Amin gami da godiya. Ita mamakin Abban ma take yanda yake nuna halin ko'inkula da abinda Ramlat ta yi musu. Mutum mai tsauri idan aka taɓosbi, shi ne ya sauko har haka. Tana mamaki kam. A wajenta abu ne da bai da saukin wucewa, ba kuma ta jin kafafunta za ta taka gidan Ramlat har abada.
***
Ɗaure fuska ya yi.
"Binciken kuma na menene kike yimin?"
Ta bude baki gami da tattara fatar gira tana kallonsa.
"Bincike? Ni ba bincike na je ba, katin da ka siyamin na je ɗauka. Sweet Aliy don Allah ka fadamin gaskiya. Hankalina ya kasa kwanciya wallahi, sigari ka ke sha?"
"Idan ina sha sai me? Please Baby Ina roƙonki ki kyaleni. Haba, na shigo gida ba ki kai ga ban abinci ba za ki ƙara min yunwa? Tunda nake da MUHIBBAT ba ta taɓa yimin irin haka ba. Bana so please ki bari idan kina so a zauna lafiya."
Yana kaiwa nan ya shige bandaki gami da rufo ƙofar. Da ace tasan asarorin da suka hau kansa a Kasuwa, da ba za ta tareshi da batun wani banzan sigari ba. A dalilin ya burgeta, ya yi amfani da maƙudan kudadensa na saro kaya ya haɗa lefe, bai tsaya anan ba sai da ya haɗa da cin bashi. Yanzun kwanciyar hankalinsa daya, ya samu Abulle ta shigemasa gaba wurin Justice ko zai ga haske.
Ta kasa kwakkwarar motsi, kamar dai kunnuwanta ne basu ji daidai ba. Ta fi tunanin mafarki ne, za kuma ta farka.
*Wannan zahiri ne, mai dogon zango!*
I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/Cxvlk7xM09
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
_Littafin Ƙarfen ƙafa dungurugum sadaukarwa ce gareki yar uwa kuma mai bani kyawawan shawarwari a dukkan tafiyata. Barr Firdausi Kabir. 🤩🤩🤩👏🏿Allah Ya bar zumunci. Baki ba zai iya misalta godiyata gareki ba. Allah Ya bar kauna fisabilillah. Ameeen. 💞💞Madallah da yar uwa kuma ƙawa ta gari._🤲🏿💃🏿💃🏿
16)
Juyi kawai take amman baccin ya ƙi zuwa. Tunanin Aliyu na shan sigari ya fi komai dagula lissafinta. Kishin yabon Muhibbat da ya yi a gabanta ya fi komai ci mata tuwo a kwarya. Ga kewarsa da take ji, tun zuwanta gidan basu taɓa raba makwanci ba. Wannan na daga dalilan da ta kasa bacci ba tare da shi a kusa ba.
Kamar yanda ba ta yi bacci ba, haka shima. Karfe kusan ukun dare ta fito falon da zummar daukar ruwa. Ji ta yi an rungumeta ta baya, za ta yi ihu ya rufe bakin.
"Baby ni ne fa." Sauke ajiyar zuciya ta yi, sai kuma ta shiga kokarin tureshi.
"Ka rabu da ni."
Ba ta yi aune ba ta ji ya ɗauketa cak zuwa dakinsa, duk yanda ta so ta kwace abin ya ci tura, sai da ya ajiyeta saman gado kafin ya yi saurin ƙarasawa ya datse kofar yana nishi.
"Baby kin soma nauyi wallahi. Wai! Kin ji hannuna?"
Ta kara murtuƙe fuska sai hawaye.
"Ni ka budemin na fita, ƙishin ruwa nake ji."
Ruwan ya miƙomata na roba, ta karɓa ta sha. Zama ya yi gefenta gami da narkar da murya. Gaba daya ya koma kalar tausayi.
"Baby na tuba. Ba zan ƙara ba. Zan yi kokari na daina idan hakan zai sa ki farin ciki."
Ta ɗan soma jin sanyi, ya sa hannu ya shiga sharemata ruwan hawayen. Yana kara kashe jikinta da kalamai masu dadi, duk inda ta ɓullo sai ya toshe. Har dai ya ci nasarar shawo kanta.
***
"Kai Zakina, kana da hankali kuwa? Duka-duka yaushe Alƙali ya ba ka gudunmuwar biki? Yanzu don rashin ta ido ka ke so ya karamaka jari? Kar fa ka manta ba haifarka ya yi ba."
Kalaman Abulle sun matukar ɓatamasa rai.
"Eh ki gorantamin! Dama kema nasan ba sona kike ba, kowa ma a gidannan ya tsaneni ya tsani ci gabana. Toh ai shikenan, duk abinda zai faru ya faru. Idan aka soma bi da ni ofishin ƴan sanda kwa fidda kudi wurin belina."
Yana kaiwa nan ya sa kai zai fita, Abulle tuni ta yunkura ta rike gefen rigarsa.
"Haba Zakina, Gadanga ƙusar yaƙi. Me ya yi zafi shi ba wuta ba da za ka dinga batun ƴan sanda, da yardar Allah ba za ka taɓa tozarta haka ba har abada. Jari ko? Ka kwantar da hankalinka ai ni na haifi Alƙali ba shi ya haifeni ba, don haka dolensa ya yi yanda nake so. Sha kuruminka anyi an gama. Haba