Showing 222001 words to 225000 words out of 230725 words
sai na juya da zummar zan dawo na same ta don ba na kaunar Husseini ya gan ni. Bayan kwanaki biyu, a wani yammaci na isa kofar gidan, cikin saa na isketa tana kokarin shiga cikin kyauren, ganin ita kadai ce na yi hon ta juyo, ni kuwa na ja na tsaya na fito. Ta shiga bi na da kallo kamar na neman ƙarin bayani da kuma son tuna inda ta san fuskar, nan take ta tambaye ni. "Kamar na sanka." Na ba ta amsa da eh, kafin na ce kin manta Modibbo na Kwari? Nan da nan ta saki fuska muka kara gaisawa. Na ce "Yaushe kika dawo?" Nan ta ke sanarmin ai ta kai shekara guda da dawowa, daga nan kuma na nemi mu keɓe don mu tattauna wata muhimmiyar magana. Sai dai na tambayeta ko akwai wani saurayinta a ciki? Idan akwai na juya. Ni kuma na dadi haka don na gane irin zaman da suke yi da Husseini, burina ta cemin ba zaman aure ba ne.
Abin ya ba ta dariya. "Aa ai kuma yanzu an girma da wannan kalar rayuwar, aure nayi." Na jinjina kai ina murmushin da bai kai zuci ba don ba haka na so ba. Sai dai ina bukatar mu zauna na ji bayani sosai. Koda muma shiga ciki, ta sanya aka kawomin lemo da ruwa, abinci kuma na ce aa. Bayan mun nutsu na kara kai duba ga hoton Husseini da ita wanda tun shigowata ya dauken hankali, shakka babu aure ne suka yi. Anan na sanar da ita gaskiyar alaƙarmu da Husseini, a farko ta razana sosai har ma ya ɗaure fuska tamau. Nayi dariya sosai na ce ta kwantar da hankalinta ina bayanta domin ba na shiri da iyayensa, don haka ni ko nan da bangon duniya ma tana iya kai Husseini muddin ba za'a gan shi ba. Faɗin hakan keda wuya ta kwantar da hankalinta saboda na biyomata ta sigar da dole ta samu nutsuwa. A karshe ta ban labarin duk yanda aka yi na dinga dariyar mugunta. Ni kuma na yi mata alƙawarin ko na ji ana raɗe-raɗin an gan shi zan sanarmata, zan kuma yi asirin da zan rufe bakin duk wanda naji yana raɗe-raɗin ya ga ko mai kamarsa ne a kwaryar Kano. Na kuma kara mata da cewa dole tana bukatar asirin da zai kara jin nan duniya ya tsani a tayar da zancen danginsa ko a tambayeshi, amma ta bar komai a hannuna. Wannan ne abinda na san na aikata, ya kasance ana neman Husseini, ni kuma nasan inda ya ke, amma na yi gum. Shiyasa koda Ramlatu ta zo da zancen Husseini, na kore ta na ce ba ruwana. Ban yi ƙasa a gwuiwa ba na sanar da Zeenatu, nan muka ce kawai a kashe ta yanda babu wata hanya da za'a san labarin komai. Sai dai kuma abinda Allah Ya riga ya tsara, ba wanda ya isa dakatar da shi."
Kawu Modibbo na kaiwa nan ya dakata ya ci gaba da kuka sosai. Falon banda salatin da Baffa Surajo ke maimaitawa cikin zubar hawaye, ba ka jin komai sai sheshshekar kukan yaran Kawu Modibbo.
"Ku yafemin, ku yafemin don Allah. Na tsaneku akan ba ku aikatamin komai ba, na cutar da rayuwarku. Na hana yarana zumunci da ku duk don bana kaunarku. Ku yafemin. Husseini ka yafemin, Aminatu, Hassa.."
Ya kasa ci gaba saboda kuka, Hussein kawai miƙewa ya yi ya bar falon, Baffa ya yi nasiha mai ratsa jiki gami da nuna ladan da ke tattare da wanda ya yi hakuri. Dada nan take ta yafemasa, ta ce komai ya wuce, hakanan shima AlHassan. Wannan abu ya yiwa Kawu da iyalinsa dadi, itama Hajja Fatuma ta nemi gafarar Dada na yanda ta dinga wulakanta ta ita mai miji dadi, Dada na murmushin da ya fi kuka ciwo ta ce babu komai ya wuce. Haka dai aka yi ta neman yafiyar juna. Taheer sai satan kallon Hafsat ya ke, ita kuwa gaba daya kunyarsa ta ke ji, a gefe guda tausayi da kaunar dan uwanta Hussein ya kara mamayeta, wato dai shi ya san dalilinsa na tsanar Kawu. Ashe mugun abu ya ƙulla masa har haka.
***
Ramlat da ba ta san hawa ba ba ta san sauka ba, ta ga mutum ya fado falon, kallo daya ta yi mishi ta gane ba lafiya. Ya zube saman kujera ya runtse idanu, fuskarsa abinka da farar fata ta koma jawur da ita. Ta shiga ambaton Allah a ƙasan ranta, miƙewa ta yi ta zauna gefensa, ba ta ce komai ba amma ta kamo tafin hannunsa ɗaya tana murzawa a hankali, a ranta addu'oi kawai ta ke karantomasa. A hankali kuma ya shiga sauke ajiyar zuciya, ya bude jajayen idanunsa ya dubeta. Sai da ta ji gabanta ya fadi, gaba daya sai ta tsinci kanta cikin damuwa mai tsanani.
"Lafiya Haskena?"
Gyara zama ya yi, bai ɓoyemata duk abinda ke faruwa ba, kawai sai ta shiga hawaye tana mamaki da tsoron lamarin mutum. Idan naka ya yi maka haka, ina hujjar da za ka ji haushin wani don ya yi maka? Sai kuma ta fahimci kuskurenta, hawayen ba zai ƙarar da Hussein da komai ba face ya kara ganin girman laifin da Kawun ya mishi har ya kasa yafemasa. Don haka ta yi azamar sharesu, ba ta kai ga magana ba sai ga AlHassan ya yi sallama ya shigo, Dada tafe a bayansa. Ta mike da sauri tana musu sannu da zuwa, Allah Ya taimaka ma tun fitarsa ta suturta jikinta sakamakon shanyar da ta kwaso a bayan gidan wurin shukoki. Ta gaida su Dada, Dada ta amsa fuska a ɗan sake. Sai dai itama fuskarta kamar na Husseini, ta yi ja, kuka kam ko ba'a faɗa ba sun yi shi, balle AlHassan.
Za ta shige ɗaki, Dada ta hanata, ta bata umarnin zama. Shiru ya ɗan biyo baya. A hankali kuma Dada ta shiga yiwa Hussein nasiha, sosai ta ke yi mai ratsa jiki tana kawomishi misalai na irin hakurin da Annabi s.a.w ya yi da yan uwansa da ma sauran mutane.
"Ka yi hakuri ɗana, ka yafemishi, idan ba ka yafe ba, da me zai ƙare ka? Me kake nema a duniya yanzu da Ubangiji bai maka ba? Babu shi, ka saka a ranka ba yanda ka iya, haka Allah Ya so ya jarabceka kuma Ya jarabta. Idan har na isa da kai, kuma har zuciyarka kana jin za ka iya yafewar, domin Allah muje ka fadi ya ji da bakinsa ka yafemasa."
Hussein wanda gaba daya jikinsa ya yi la'asar, ba shi da sauran kataɓus, miƙewa kawai ya yi suka fita tare da Dada zuwa sashinta. Ta ba Ramlatu umarnim biyo ta, hijab kawai ta sanya ta bisu a baya.
Kawu ya yi murnar sake ganin Husseini, da kansa ya mike jiki na rawa ya kasa gareshi ya rike hannunsa, kawai sai ya soma kokarin durkusawa yana kuka. Da sauri Hussein ya rike hannunsa ya ɗagoshi tsaye.
"Ya wuce Kawu, na yafemaka a bar zancen haka."
Ba wanda kalaman Hussein bai wa dadi ba, Ramlat ta gaishesu, itama dai gafararta Kawun ya nema, take kuma ta ce ba komai ya wuce.
Nan fa gida ya yi dadi amma Hussein bai wani sake sosai ba, sai da aka yi Magriba kafin su Kawu su wuce, Baffa Surajo ya ce lallai gobe duka a hadu a babban gida yana neman kowa da kowa. Ya bada umarnin a sanarwa wanda ba ya nan, na nesa kuwa a rabu da su. Da wannan komai ya wuce.
***
Washegari kuwa misalin karfe biyu, Baffa Surajo ya haɗa taron da kowa na zuri'ar Gidado dake a Adamawa ya hallara. Bayan addu'a da doguwar nasiha, ya ba Kawu damar neman afuwan yan uwansa. Nan Kawu ya ba kowa hakuri da kuma daukar alkawarin ba zai kara aikata ko makamancin hakan ba. Kowa ya ji dadin hakan kuwa, karshe kuma ya nemi alfarmar haɗa auren Taheer da Hafsat, nan take Dada ta ce ita ba ta da ja. Hussein zai yi magana ta harareshi, murmushi ya yi.
"Cewa zan yi an bayar." Maganar ta ba kowa dariya, Baffa Surajo ya yi mishi daƙuwa.
"Ai ba kai ke da alhakin bayarwar ba."
Bai ce uffan ba, Hafsat kuwa ai kamaran mata albishir da gidan aljanna.
***
MURFI....
I just published "BABIN ƘARSHE" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1035704431?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=ahGlFX6GFRN4rYLxQybIWR9WrkgGWE36szhMfA7kRFxFwQXwS03Sgp8YSmnHzMO1lgoFTgL30%2Brf0xbkWKei5hlm6ZnndGuZExstbOwboUAs%2BBmTygvZgHsBmhnEg64g
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA* 🕯️
_Rufaida Umar_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
*BABIN ƘARSHE*
ADAMAWA
BAYAN WATANNI BIYAR..
Amarya Ramlat ta kara kyau da ƙiba sai dai ba irin mai munin nan ba. Sanye take cikin doguwar riga na leshi lemon green an mata dinkin bubu, ta fito daga motar yayinda Hafsat da Rasheeda suka yi gaba niƙi-niƙi da kaya, ita kuwa tare suka jera da Kausar rike da wasu ledojin. Dawowarsu kenan daga kasuwa, zuwa lokacin sun yi nisa da shiryen-shiryen bikin Hafsat har ma da Rasheeda wacce za ta auri ɗan Barrister Hansatu (Babbar Yayar su Kawu Modibbo), Mujaheed.
Tun da suka rubuta jarrabawar karshe kasancewar tare suke tafiya da Hafsat a karatu, sai Rasheeda ta tubure ta ƙi zaman Kano, ta dawo gidan Adamawa wajen Dada ta yi zamanta. Wannan abu ya yiwa Dada dadi, wai yau ta budi ido ta ga jinin Kawu Modibbo a gidanta, kuma da son ran mahaifin, sai ta ji inama ɗan uwanta baban su Hussein na raye ya ga ranar da ya dinga ce mata za ta zo in sha Allah, ashe kuwan tana tafe.
Hamida babbar ƴar Dada wacce aure ya lula da ita har Saudiyya, ta jima rabonta da ƙasar don ko Ramlat tsakaninsu sai dai ta waya ko kuma idan ta kira Hussein videocall suke gaisawa. Ta dube su da kulawa tana ba karamar ɗiyarta Mama.
"Sannunku da zuwa. Kun sha wunin kasuwa."
Suka yi murmushi lokacin da kowa ke kokarin zama.
"Wash!" Fadin Hafsat tana mai kwantar da kai jikin Dada. Ture ta Dada ta yi.
"To raguwa, ni matsa ki ban wuri. Gwara ma ki tattara ki bar gidannan ko na huta."
"Aa Dada, ina hutu ba kya ganin Auta? Faɗa dai ki ke yi."
Cewar Adda Zahra, mai bi wa Hamida, ita a Lagos ta ke da zama.
Aka yi dariya. Haka kuma aka shiga bude kaya ana ganin siyayyar da suka yi na abinda ya yi saura na tarkacen kayan girki har ma da sauran kayan kicin da ba'a siya ba. Sosai an yaba da kayan, sai da suka ci abinci kafin Ramlat ta koma sashinta. Wanka kawai ta yi don wani irin zafi ta ke ji, ta sanya kananun kaya riga da siket marasa nauyi kafin ta faɗa kicin. Lissafi ta shiga yi a ƙasan ranta, su Rafee'ah bai fi saura kwanaki shida su zo ba saboda biki. Ta ƙagu ta ga yaranta da kuma Aisha da babynsu. Ta shafi cikinta kaɗan tana murmushi, tana burin Allah Ya ba ta haihuwa ko don ta ga kalar farin cikin Hussein wanda yanzu koyaushe ba shi da zance sai na baby, baby. Haka dai Ramlat tana aiki tana tunane-tunanenta. Sai da ta yi nisa, sai ga Kausar ta shigo, itama kam ciki ne da ita wata uku. Sallama ta yi mata akan za ta tafi, har ƙofa ta yi mata rakiya.
"Kai aa ki koma hakanan, ga mijinki can na baro sashin Dada, idan ya ganki haka kin fito ai ni zai ɗorawa laifi."
Ramlat ta yi dariya, sai yanzun ta tuna da kalar suturar dake jikinta. Ko ba komai daga rigar mai hannun vest har siket din wanda yake dogo amma kamar roba, duk sun matse ta.
"Toh Maman Twins, Allah Ya saukeki lafiya. A gaidamin da Fatina sosai."
"Twins dai yana jikinki Madam, amma ba ni ba. Ki bar yimin wannan fatan. Fati kuma za ta ji sosai."
Ramlat abin ma ya ba ta dariya, tana mamakin yanda Kausar ke gudun twins. Ita kam da ace za ta samu tana son abinta. Anan dai suka rabu ta koma kan aikinta. Babu jimawa Gogan ya shigo. Ganin tana kicin kawai ya nufi ɓangarensa ya watsa ruwa. Duk tana ji, Allah Ya taimaka dama girkin ƙarashe ne don ta dafa markade ta kuma yi tafashen kazarta kafin su wuce kasuwa. Wannan yasa kawai miyar ta haɗa ta kuma dafa kuskus da ya sha karas da koren wake. Komai ta haɗa a gaggauce ta kawo falon ta jera saman ledar cin abinci.
Ƙamshinsa ya soma dukan ƙofofin hancinta, ta ɗaga kai ta kalleshi. Wando ne mai jikin cotton ya sanya sai farar tshirt mai gajeran hannu. Koyaushe Hussein ƙara kyau yake yi a idanunta, kullum ƙuruciyarsa ta ke gani. Har kullum idan zai fita daga gida hakanan sai ta ji wani kishi ya kamata. A kwanakin baya sai da ta kwashi takaici sadda wata Meena ta matsa mishi da kira, hankalinta bai kwanta ba sai da ya tabbatar mata babu komai tsakaninsu karshe ma ya rufe Meenar ta yanda babu damar da za ta ƙara kiransa. Da wannan ya samu hankalinta ya kwanta.
Har ya ƙaraso ta shagala ba ta ko lura ba sai da ya kai hannu ya shafi mafi soyuwa a wajensa. Ta dawo hayyacinta ta sauke ajiyar zuciya lokaci guda ta ɗan harareshi da wasa gami da murguda baki. Ya shafi lebbanta da yatsa hana murmushi.
"Ni kike wa haka? Tunanin me kike?"
"Ba komai."
Ya matso da ita jikinsa ya kwantar da kanta saman kirjinsa.
"Ko? Faɗamin gaskiya Malama."
Ta lumshe idanu tana shaƙar ƙamshinsa mai sanyamata nutsuwa.
"Dagaske fa ba komai. Tunaninka nake yi."
Ya sumbaci saman kanta yana murmushi.
"Uhum, faɗamin, me kike tunani alhalin ni ɗin naki ne."
Ta yi wani tattausan murmushi a hankali ta ɗago kai har hancinta na gogar sajensa. Suka dubi juna. Ya ja karan hancinta.
"Ko ba haka ba?"
"Hakane."
"To kin gani, me zai dameki?"
Ta jinjina kai kawai ta murmusa. Nan kuma ta zubamishi abincin, koda ta ce ta ci bai matsamata kan lallai sai ta ci ba.
Haka dai a kwanakin nan kusan kullum sai sun fita siyayya, sai da suka jera kwanaki uku, kafin Hussein ya murtuke ya ce abin ya ishe shi. A gaban Dada aka yi, suna zaune ne sai ga Waleeda cikin shiri ta dubi Ramlat.
"Adda Amal, muje ko?"
Ya haɗe fuska, ita kuwa Ramlat da ido ta nunamata Hussein alamar bai yarda ba. Waleeda ta dubeshi baki sake sai dai tuni ta haɗiye abinda ta yi niyyar faɗi dalilin kallon da ya yi mata. Dada ta dara.
"To kai Husseini banda abinka, ai fitar ta su ce, ɗinkinsu za su kai. Ka yi hakuri su je a auna su."
Ya mike zaune.
"Aa bari na aunata sai ita Waleedar ta kaiwa telan. Ba shikenan ba?"
Kunya ta kama Dada, ba ta kara uffan ba ta mike ta yi daki, Hussein dama ba yau ya saba ɓaram-ɓaramarsa ba. Ramlat da ta ji kamar ta nutse ta rasa bakin magana. Waleeda dake dariya ciki-ciki ta dubeshi kawai yayinda Hamida ta hau dariyarta sosai a fili don kusan sa'anni suke da ƴan biyu. Sai da ma ta faɗo duniya da watanni biyu aka haifesu.
"Me na ce ne?"
Ya furta yana neman ba'asi ganin Dada ta mike ta yi daki, su kuwa na falon na dariya.
"Au ba ka san me ka ce ba kenan? To ai Dada wuri ta ba ka idan ka auna matartaka sai ta dawo."
Ya taɓe baki yana yamutsa fuska.
"To meye a ciki? Dada dai ta so jin kunyarta ne. Idan muka haifamata jikoki ta daina. Tashi ita kuma wannan ta ɗauko abin awo."
Ramlat ta mishi wani irin kallo kamar ta yi kuka. Ya yi murmushi ya girgiza, kallon ya ji shi a dukkan wata gaɓa ta jikinsa. Miƙewa ya yi ya mata duban zan haɗu da ke kafin ya musu sallama ya fice wurin aiki, lokacin goma da ƴan mintuna.
"Dagaske dai mijinki bai bari ba. Ai shikenan, kawai ki ɗauko rigar da za ta yi maki daidai a yi amfani da ita."
Waleeda ta faɗi tana murmushi. Kafin Ramlat ta ce wani abu sai ga kiransa. Ta ɗaga da sallama.
"Kwalliya ta biya kuɗin sabulu, amma kallon da aka yimin yanzu idan na dawo zan zauna a yimin sau ɗari. Kuna iya tafiya, Allah Ya tsare. Drive carefully."
Daga haka ya katse kiran bai jira cewarta ba, ganin yanda ta ke zabga murmushi yasa Hamida kallonta.
"Ya bar ki kenan ko?"
Ta gyada kai, suka yi dariya. Mikewa ta yi ta koma bangarenta, mayafi kawai ta dauko sai jaka da mukullin mota ta rufe ko'ina. Koda ta dawo, Dada na zaune ta dawo falon. Sallama suka yi mata suka wuce. Wani tsadadden leshi da ya haura dubu ashirin, iyakarsu ne kawai, iyalan Dada, surukai da kuma ƴaƴa, ranar Dinnerparty zasu sanya. Sai atamfar da zaa sanya ranar wuni gaba daya dangi. Sai kuwa wata shadda ta Ramlatun da za ta sanya ranar ɗaurin aure.
***
Ana gobe za'a sanya Amare a lalle ne, ƴan Kano suka iso, dama iyalan Kawu Modibbo tun ana saura kwana uku suma dira. Ramlat ta rasa inda za ta sanya su Rafee'ah don murna. Ga yaranta, Affan ya zama babban mutum, ba kuka sai ma yawan sunkuyar da kai wai shi a dole mai kunya. Yaran sun yi wata irin ƙiba da kyau ga murjewa. Ta dauki Babyn Aisha, kyakkyawa da ita, sunan Mahaifiyar Hisham ta ci su na kiranta da Afnan. Kyau kam wane iyayenta.
"Ke kina ta cewa wasu sun yi kyau, kina kallon kanki kuwa a madubi Ramlat? Lallai aurennan ya karɓeki tubarakAllah."
Maman Twins ke maganar tana kallonta sosai. Nan fa sauran suka shiga tofa albarkacin bakinsu, ba wacce zuwanta ya ba ta mamaki sai Bilkisu don ita Hunainah ba ta zo ba saboda laulayin ciki na biyu da ta ke yi, ba ta jima da haihuwar ɗanta ba kafin ta kai ga yin wani tsarin iyalin sai ga ciki. Bilkisu kuwa wata uku kenan da dawowarta gidan Muniru, nan ma sai da ta sha baƙar wuyar rayuwa a gidansu, ta duba ta hango babu rayuwar da ta fi ta gidan mijinta dadi wannan yasa dakyar da siɗin goshi ta lallaɓa Muniru har ya sauko ya maidata ɗakinta. Tun komawarta musamman ganin su Yasmeen babu wani alamar wahala tattare da su, sai ta yi sanyi, ta kuma karɓi Hunainah hannu bibbiyu suka zauna lafiya.
Hussein sosai ya ke jan yaran a jiki, wani irin