Showing 120001 words to 123000 words out of 230725 words
ya samu ya dace. Da ace Fa'iza ta kwantar da hankalinta, babu Hilal a zuciyarta, ba ta yi mishi so irin na aure. So take mishi na ƴan uwantaka, tana mishi kallon yayanta da suke ciki ɗaya. Ajiyar zuciya ta saki kafin ta maida hankali ga kallon yanda hadari ya yiwa garin luf. Wani murmushi ta saki mai ciwo tana share hawaye, addu'a ta yiwa Aliyunta sannan ta kunna karatun Alkur'ani, ta ja motarta.
Ba ta faɗa wa Hajiya abinda ya faru ba sai dai har dare wayarta a kashe. Kamar daga sai ga Hilal, lokacin suna falo zaune saƙon zuwansa ya isketa daga bakin Malam Bala. Ta yi shiru, Hajiya ta dubeta don dama ta lura gaba daya ba ta da walwala. Sanin da ta yi koda ta tambaya babu amsa yasa ta yin shiru kawai ta zubamata idanu. Yanzun da saƙon zuwan Hilal ya risketa, ta lura da yanda ta ƙara ɗaure fuska.
"Meke faruwa ne da ke? Tun shigowarki kin wani cukune, yanzu an ce ana kiranki kuma kin ji wanda ke tafe amma ba ki da niyyar zuwa."
Ramlat ta dubeta kamar ta yi kuka.
"Hajiya ba komai, kawai..."
"Tashi ki je." Ganin umarni ne kai tsaye ta ba ta yasa ta miƙewa ta shige daki, can ta fito yafe da gyale akan doguwar rigar atamfarta ta fice.
Yana tsaye kamar koyaushe jikin motarsa, ta karasa ba tare da ta bari sun hada idanu ba. Sallama ta mishi kafin su gaisa sannan ta ja bakinta ta yi shiru.
"Ramlat na miki laifi, kiyi hakuri."
Murmushin yaƙe ta yi.
"Ba abinda ka yimin, asalima ko me Fa'iza ta fadi gaskiya ce ta faɗa. Sai dai don Allah ina roƙonka akan muyi hakuri hakanan. Kaunar da ka nunamin Allah Ya saka da alheri. Har abada nasan banda masoyi kamar ka."
Ta ƙarashe da wani irin rauni, kuka ke son kwacemata, tunaninta ya tafi a shekarun baya na irin cin kashin da ta yi mishi. Hawaye ta shiga fitarwa ba tare da ta sani ba.
Ta ɗago ta kalli farin hankicif da ya miƙomata kafin ta dubeshi, murmushi ya ke mata wanda ya fi kuka ciwo yayinda idanunsa suka kaɗa. Zuwa yanzun shima ya saduda kuma ya ji zai hakura ko don kar ya faɗa fushin iyayensa. Akan Ramlat, yau Fa'iza ta kai ƙararsa gurin iyayensa. Sosai aka buɗemishi wuta kuma sun kara rantsuwa akan tsinuwa gareshi idan ya dage akan aurenta.
Ta sa hannu ta karɓa ya soma magana.
"Ramlat kar ki damu, nima na ji a raina yanzun zan iya hakura da ke ba kuma don ina so ba. Ina miki kyakkyawan fata a koyaushe. Ina roƙon Allah Ya kawomaki sauyi a rayuwa, Ya zaɓamaki mijin da ya fi ni, mijin da zai kularmin da ke ya kuma nunamaki dukkan kauna da soyayya. Allah shaida ne, na so na aureki, sai dai a matakin da nake kai yanzu zan iya faɗawa fushin iyaye da na Mahaliccina. Ya zamemin dole na hakura kar biyewa son zuciyata ya jazamini."
Ya ci gaba da kalaman da ke nuni da irin alhininsa na rabuwarsu. Haka ta yi ta fidda hawaye a karshe suka rabu ran kowannensu babu dadi.
Allah Ya taimaketa Hajiya ba ta falon sai yara da suka sheme duk sun yi bacci, jiki a saluɓe ta kai kowannensu makwancinsa ta yi musu addu'a sannan ta koma falon da zummar kashe kayan kallo.
"Yaushe kika shigo?" Ɗagowa ta yi bayan ta kashe socket din talabijin ta dubi Hajiya.
"Ban jima da shigowa ba."
"Lafiya?"
Ta watsomata tambayar ganin yanda take fidda hawaye, ta kasa danne kukanta, kawai sai ta fashe da kuka. Umarni ta bata akan ta zauna su yi magana. Nan ta zayyanemata yanda suka yi da Hilal. Jinjina kai Hajiya ta yi.
"Allah Sarki, yaron kirki. Dole ki yi kuka Ramlatu, rashin mutum mai hakuri da nagarta kamar Hilal abu ne mai ciwo. Da ace ba mai hakuri bane, hanyar ma da kika bi ba zai kalla ba ballantana har ya bi ɗin. Allah Ya sasanta shi da mai ɗakinsa, ke kuma Allah Ya yi maku zaɓi."
Ta amsa sannan suka yi sallama kowannensu ya shige ɗaki. Wanka ta soma yi ta sauya kaya gami da kwanciya saman gado. Tausayin Hilal kawai ta ke ji yana nukurkusarta, a karshe ta yi addu'a ta kwanta.
***
Washegari tun safe ta shirya ta fita da yara makaranta. Caa suka yi mata kowanne da nashi kalar ƙorafin, daga ba'a ga fensir ba sai mai kawo ƙarar Antinsu ta bugeshi. Ita dai ban da murmushi ba abinda ta ke yi, idan da sabo ta saba, kowanne da nashi ƙorafin musamman Ummi da Ansar wadanda har sun soma koyawa Affan.
Ƙarar wayarta ne yasa ta dauka, ganin sunan Mr Wuff ya ba ta mamaki. Ta dakatar da hayaniyar su Ummi kafin ta ɗaga da sallama daidai sadda aka tsayar da su a junction.
"Yaranmu ne suka sanyaki murmushi ko tunanin bazawarinki?"
Abinda ya ce kenan bayan amsa sallamar, hakan ne yasa ta saurin kallon titi. Gaban wata Jeep ta hangeshi zaune a kujerar kusa da direba. Da alama wani abin ya tsayar da su, kallonta ya yi kafin a hankali ya rufe gilashin motar.
"Hey, kar ki cinyeni da kallo. Kamar ma kin manta cewar tuƙi kike ko?"
Harara ta bankamasa don ta san koda ita din ba ta kallonsa, shi idanunsa yana kanta.
"Meye abin kallo a fuskarka? Nikam ban ganshi ba. Na kalleka ne don na tabbatar kai dinne da sassafe haka ba wani ba."
Murmushi ya yi tamkar tana kallonsa.
"Allah Ya tsare hanya, drive carefully."
Daga haka bai jira cewarta ba ya katse kiran. Ta ajiye wayar ba ta kara kallon inda motarsu take ba amma ya sanyata dariya.
A bangarensa kuwa, ƙara jingina ya yi yana ƙaremata kallo daga ita har yarannata, ya lura babbar ta fi ɗiban kama da ita akan na tsakiyan da ƙaramin. Yanda suke ta hira suna karkatowa da zummar kallon fuskarta ba karamin burgeshi ya yi ba.
Direba dai ya yi bakam, ga labari na sukarsa amma ba wani da zai faɗawa. Burinsa kawai su kai gida ya samu Joseph mai gadinsu, inyamuri kuma mai jin yaren Hausa sosai su tsegunta. Da alama dai Yallaɓai aure zai yi, sun tabbata ba karamin bomb ne zai fashe ba.
Har aka ba su hannu yana satar kallon Ogannasu, hankalinsa duka yana ga Ramlat da yaranta. Kusan tunda ya daukoshi daga Airport bai yi mishi wani kwakkwaran magana ba sai yanzun da ya ga budurwarsa. Farin ciki sosai direban ke yi, ko ba komai Yallaɓai zai samu sa'ida daga wurin Hajiya Zeenatu. Su kansu suna mamakin yanda akai ya ƙare da auren mace kamarta.
***
Har ta sauke yaranta a makaranta ta kama hanyar ofis ba ta bar tunanin wayar da suka yi da Hussein ba. Sosai ta ke mamakinsa, idan da a farkon ganinta da shi wani zai ce mata yana da sauƙin kai har haka toh fa za ta musanta, za kuma ta ƙaryata nan take. Da alama wannan yana daga cikin nasarar jihadinta. Ta shaƙu da shi sannan a ƙarshe ta shiryashi da ƴan uwansa. Wannan kaɗai ne burinta.
Tana faka motarta ba ta kai ga barin parking space din ba, suka ci karo da Halima. Wani irin kallo Halima ke bin ta da shi tana murmushi. Bayan sun gaisa ta ce.
"Sakatariyar Chairman, wato ko nemanmu ma kin daina."
"Ko rannan na shiga ke kuma ba ki zo ba." Fadin Ramlat cikin dakiya don yanzun ba ta kaunar shiga duk wani lamari da ya shafeta. Ta riga ta gane ba masoyiyarta ba ce. Halima ta ɗan taɓe baki.
"Oh, haka fa. Ai mancewa na yi, an faɗamin. Ina fatan dai za ki saki jikinki ki ajiye kauyanci gefe ki ci arziki inda kika ganshi."
Ɗan haɗe gira Ramlat ta yi tana mata duban ido cikin ido.
"Bangane hausarki ba, me kike nufi?"
Dariyar ƴan duniya ta yi.
"Dama ba lallai ki gane ba, amma nidai ina mai ba ki shawarar kar ki yi wasa da damarki."
Daga nan ta ficewarta ta bar Ramlat tsaye. Wani murmushi ta yi gami da girgiza kai itama ta soma tafiya nutse.
Ta rasa ranar da Halima za ta nutsu ta yi hankali, kullum tunaninta iri guda ne.
'Allah Ya shirya.' Ta furta a ƙasan ranta.
***
"Wannan asarar kuɗi har ina wai?!! Duk aikin da na ɗauko sai ya lalace! Abu ne da bai taɓa faruwa da ni ba duk tsawon wannan shekarun! Ina tsoro kuma."
Hajiya Zeenat ke wannan ƙorafin kamar ta zubda hawaye a tsakar falon Hajiya Batool da misalin ƙarfe uku da mintoci na rana.
"Ni na rasa ma me zan ce. Kusan duk yanda aka kurantamana wannan mutumin ba haka muka riska ba. Kinga yanzu wai yaronnan Dubai zasu wuce da shegiyar yarinyarnan siyayyar kayan haihuwa? Ban isa na faɗi aibunta ba zai hau ni da faɗa kamar shi ya haifen."
Tsaki Hajiya Zeenatu ta ja.
"Ke naki ai da sauƙi tunda ba mijin bane, ni ina miki maganar duk aikin da nayi sai ya lalace. Duk abinda na ɗauki niyyar na yi sai kiga an yi rashin sa'a a kai. Jikina ne ke yin sanyi, amma ba zan karaya ba. Har abada kuwa."
Ta ƙarashe tana mai goge zufa sa'ilin da kwakwalwarta ta tafi ga tunanin wani abu da ya kasance a can baya wanda nan da nan ya jefamata tsoron da ta ke gujewa a zuciya.
"Toh wai me zai hana mu koma wajen Gora? Kamar dai aikinsa ya fi na wannan buzun. Duk buge ce."
Jinjina kai Hajiya Zeenatu ta yi.
"Kuma hakane, kin fadi gaskiya."
Cewar Hajiya Zeenatu cikin karaya, yanzun dai ta saduda, banda ma asarar kuɗi, aikin ma da ta yi nema ya ke ya rushe, nema yake ya zama tamkar ba ta taɓa yi ba. Ita da kanta ta soma ganin sauyi acikin rayuwar Hussein. Ya rage shakkarta.
Suka yi ta tattauna yanda zasu ɓullo wa matsalolinsu kafin su yi sallama su rabu zuƙatan duk babu dadi.
***
BAYAN SATI ƊAYA.
Tun shigowarsu garin na Dabo tumbin giwa Fatima ke ji kamar tayi fiffike ta yi ta zagaye gari tsabar farin ciki da jin dadin yau ga ta a Kano. Da wayonta haka dai ba ta taɓa zuwa ba. Don haka bakinnan nata a wangale ga hannunta riƙe da cakulet tana sha.
Uban ya dubeta yanda ta hakimce gaban mota, duk son uwar da haka, hakura ta yi don ba ta iyawa rigimar Fatima wani sa'in, zamanta ta yi kusa da Hafsat da Dada.
"Wai nikam Fatima kodai a Kanon zamu bar ki ne?"
Fadin Kausar tana dariyar yanda yarinyar ta kifa goshi a kan gilashi tana ƙarewa waje kallo.
Da wani ɗoki ta dubi Mamarta ta gyaɗa kai, yanda ta yi duk sai ta ba su dariya.
"Allah Ya rayaki dai Fatin Biyu"
Dada ta furta da dariya. AlHassan wanda walwalarsa ta ɗan ja baya tun shigowarsu garin sai a sannan ya ɗan saki fuska. Autar Dada ta ɗan dunguro kanta.
"Ke da ace za'a bar ta kinga alamar ba za ta zauna ba?"
Aka dara. Haka suka yi ta hirarrakinsu har suka kai gidan Kawunsu Modibbo.
Yana parking ya budemusu ƙofa kafin ya zagaya ya sa yara su fiddo akwatunan. Ya ɗaure fuska ya sauya kamar ba AlHassan ba mutum mai yawan fara'a.
"Zan je na dawo."
Abinda ya ce kenan, Dada ba ta yi mishi dole ba ganin sauyinsa, ta kauda kai don tasan ba da son ransa suka zaɓi kwana a gidan Modibbo ba madadin ɗaki a Hotel da ya yi niyyar kama musu. Suna shigewa ciki shima ya ja motarsa ya fice.
***
Kausar ce tsaye bayan ta dawo daga ɗakin Amarya tana duban yanda Dada ta zage tana faman aiki tuƙuru a sashin Hajja Fatuma. Tana kallon yanda jikokin Hajja Fatuma suke yin yanda suka so babu mai kwaɓa balle magana, yaranta mata na hakimce saman kujera suna hira da sha'aninsu ita kuwa ta shiga cikin ƴan aiki ana gyaran kaji. Juyawa ta yi ta koma sashin Amarya dakin da suka sauka. Nan ta tarar da Hafsat tana sauyawa Fatima sutura zuwa na bacci, a gefenta Rasheeda ce, ɗiyar Amarya da zasu yi sa'anni da Hafsat. Su dai kam dama jininsu ya hadu don har chatting suna yi. Ganin yanda Kausar ta shigo fuska a ɓace yasa Hafsat gane inda zancen ya dosa.
"Anti kin ce ta zo ta ci abinci?"
Sai a sannan ne ma ta tuna abinda ya kai ta wurin Dadar, ta ja guntun tsaki.
"Kinga halin mantuwa ko?"
Miƙewa Hafsat ta yi a fusace, ita kam yau sai ta taho da uwarta don ba bauta ta zo ba.
Za ta fice Kausar ta riko hannunta. Ta dubi Rasheeda.
"Don Allah kirawo Dada."
Rasheeda ta mike ta fita. Ta riga ta san komai dangane da irin tsangwamar da Dada ke sha a wurin Hajja da Modibbo mahaifinsu har ma da wasu cikin ƴan uwansa. Ta kuma rasa dalilin wannan ƙiyayya, a ganinta abinda ya wuce ya riga da ya wuce.
"Kai Adda, nidai wallahi da kin bar ni na je, na gaji da wannan abu. Tun zuwanmu awa nawa yanzu ace Dada ko abincin kirki ba ta ci ba? Daga zuwa gaishesu ta dawo sun haɗata da aiki don rashin tausayi, kuma shi ne ita ta karɓar? Nidai sai na gayawa Hamma.."
"Kul! Kar ki soma. Kinsan dama ba da son ransa aka yi wannan tafiyar ba, abin ya zo mishi ne a ba yanda ya iya. Yanzu kika kirashi tayar da hankalinsa kawai za ki yi kuma ranmu ya ɓaci. Ke dai ki bi gargadin da Dada ta yi maki a rabu lafiya. Gasunan dai kinga su Hanifah duk suna zaune, nima ban ishesu kallo ba tunda a cewarsu ina auren AlHassan."
Yamutse fuska Hafsat ta yi.
"Wallahi Adda, Adda Hanifah ƙarya take. Son Hamma take yi kamar yanda ɗan adam ke son rayuwarsa. Ai inada labarin komai, kuma ma.."
Sai ta yi ɗif, sai yanzun ta ke tuna katoɓarar da ta yi, ta ɗan datse harshe da haƙori ta yi shiru. Dada da ke tsaye bakin ƙofa ta ƙaraso ta bata rankwashi a kai, ita kuwa Kausar dariya ma ta yi. A saninta ko giyar wake AlHassan ya sha ba zai auri Hanifah ba. Har abada ya tsani zuri'ar Modibbo. A wani ɓangaren kuma itama ta san da wannan soyayyar ta Hanifah ga mijinta, takan ga kiranta sau tari a wayarsa, bai yi saving lambar ba, amma ita tana da lambar a wayarta. Allah Ya hana bincike, shiyasa ba ta zurfafa ba. Sai kuma sanin da ta yiwa Modibbo na bala'in son kansa da kuma ƴaƴansa, wannan ne waekness dinsa. Duk abinda yaransa ke so koda ba ya son abin, zai yi yanda zai yi ya nemamusu farin ciki. Wannan ya yi sanadin lalacewar wasu a yarannasa.
"Ke za ki biyewa wannan shashasha har ki wani tsaya zurfafa tunani? Kin yarda da abinda ta ce kenan?"
Dariya Kausar ta yi tana girgiza kai.
"Ko kadan." Suka ɗan dara, Hafsat ta turo baki.
"Toh nidai gaskiya Dada ba zamu yarda da wannan aikin da kike fita ba, idan kika ci gaba zan kira Hamma."
Dada ta yi murmushi cikin harshen fulatanci ta amsa.
"Dayake shi ya haifeni ko? Banda abinki Hafsatu, ni da gida ɗan uwana? Wa ya fadamaki abinda na yi faɗuwa ce? Babu, zumunci na sadar kuma Allah zai duba."
Ita dai Hafsat ta ja hannun Fatima suka fice zuwa falon Amarya. Banda Dada ta tilastamata kuma tana son zuwa gurin Rasheeda, ba abinda zai sa ta tako ƙafarta Kanon, a yanzun ma ji take da ace akwai wasu ƴan uwannasu can za ta yi tafiyarta.
Da yammacin ranar AlHassan ya iso ƙofar gidan Modibbo, waya kawai ya yi ya ba Hafsat umarni fitowa tare da Fatima su yawata. Da wani irin ɗoki Hafsat ta mike ta shirya Fati suka fice ba su ko tsaya sallama da kowa ba banda Adda Kausar da suka faɗawa ta sanar Dada.
Fuska ta daure ganin yanda Taheer ɗa ga Hajja Fatuma ya tsuramata idanu yana kallo. Bafulatanin usuli wanda daga ka ganshi ka ga jinin Mamman Gidado.
Dagasken gaske tana lura da yanda yake wani safa da marwa a sashin Amarya wanda hatta da Rasheeda sai da ta nuna mamakinta a fili, acewarta abu ne mai wahala ka ganshi a sashin nasu.
Har ta isa ta buɗewa Fatima gaban mota ta shiga itama ta bude gidan baya ta faɗa babu walwala. Alhassan ya dubeta yana murmushi sadda ya ja motar.
"Ke kuma ke da wa?"
Turo baki ta yi.
"Bakomai."
Ya taɓe baki. Ko me ya faru ai su suka sani, shi dai kam dama bai nunamusu yana son zuwan ba.
"Daddy ina zamu je?"
Cewar Fatima a ɗokance. Ya ja kumatunta da murmushi.
"Surprise ne."
Ya yi ta biyemata su na surutu har suka iso tafkeken shagon na A&Z.
Hafsat sai a lokacin ta saki ranta, suka fito suka jera ciki. Da ka gansu ka san jini ɗaya ne.
Kai tsaye suka hau sama, ma'aikatan sai kallon AlHassan suke yi kusan a mamakance. Duk a zatonsu Mijin Madam ne, ganinsa da budurwa ya ba kowa mamaki, har da samari da ƴanmatan da suka mayar da wurin wajen zuwansu. Shi kuwa Alhassan wayar da aka kirashi ce ta sanya shi ba Hafsat kudade tare da ba ta umarnin ta suyamusu duk abinda ya dace, yana jiranta a waje.
Sauri yake sosai yana son barin hayaniyar cool music da ke tashi a wurin ganin Director ɗinsa na wurin aiki ke kiran. Magana ce za su yi mai muhimmanci. Karo ya ci da ita sadda ta sanyo kai nan take wayarsa ta faɗi, ya ɗago ita kuwa ta matsa baya gami da fadin.
"Yi hakuri fa."
Ɗagowar da zai yi sai da ta ji hantar cikinta ya kaɗa. Ba don ace tare suke tafe da mijinta Hussein ba, kuma yana cikin mota sanye da kananan kaya, madadin wannan da ke sanye da shadda blue, za ta rantse shi ne tsaye. Murmushi ya yi mata da nunamata ba komai kafin ya yi gaba. Har tana tuntuɓe haka ta juya ga mararta da ta cika taf da fitsari, haka ta karasa ga Hussein wanda ya juyamusu baya yana kokarin rufe motar. Ganinta a gigice yasa shi dubanta da mamaki.
"Lafiya?"
Dafashi ta yi gami da riƙe kai.
"Lafiya, a'a ba lafiya, muje don Allah. Jiri nake ji shiga mu