Showing 177001 words to 180000 words out of 230725 words
Zeenatu da Hussein na karshe ta fashe da kuka ta nunamasa idan har yana sonta ya amince ya biyota su wuce Kano a dauramusu aure don kuwa ta tabbatar ba wanda zai amince da aurensu a danginsa tunda ta girmeshi. Hussein ya ji maganar babbarakwai, hankalinsa ya tashi. Yana so ya ce mata a'a amma abin ya faskara, ganin bai ce komai ba ta ƙulla gaba da shi ta ce ya rabu da ita har abada ba ta sonsa. Kowa ya kama gabansa.
Ta fadi hakan ne don ta san ba mai yiwuwa bane, tuni ta juyamasa ƙwaƙwalwa ta hanyar zubamishi siddbaru a abinci da abin sha. Wani irin soyayyarta ke addabarsa da wani irin tsoro.
Sai dai batun ya bar ƴan uwansa dominta ne ya ji kamar ya mishi nauyi. Da wannan suka rabu ta koma Kano kamar yanda Hajiya Batool ta bata shawara, sun riga sun san zai biyo bayanta don aikin da aka yi mishi mai karfi ne. Layu ne aka sanya a gaban gawar mace. Hakanan an kwaƙule idanun jariri sabon haihuwa an haɗa da maganin.
***
Kwanaki uku ya biyo baya Hussein ya rame ba walwala. Wannan ya tashi hankalin kowa. Aka haɗa meeting aka zaunar da shi don jin bayani.
"Aure nake so a yimin. Na samu matar aure amma ta girmeni don za ta yi shekaru arba'in. Wallahi ita nake so, don Allah kar ku hanani aurenta."
Ran kowa ya ɓaci, nan Baba Naziru ya rantse ya kara ba zai aureta ba. Kowa kuma ya goyawa hakan baya ba tare da sanin abinda hakan zai haifar ba. Ga mamakin kowa Hussein ya mike a fusace.
"Eh dama ai kun fi son Hassan! Shi da ya kawo wacce ya ke so wane ne ya hanashi? Sai don zan auri bare? To ai nima uwata bare ce a cikinku don haka ba wanda ya isa hanani auren wacce nake so!"
Daga nan ya fice daga dakin ya bar kowa baki a sake. Dada kuka ta sanya saboda kunyar da Hussein ya bata.
A karshe Baba Naziru ya fusata ya ce da kansa zai zaɓamasa matar aure.
***
Washegari cikin dare Hussein ya shirya kayansa da takardunsa masu muhimmanci, ya kalli Hassan dake bacci na ƴan dakiku. Kirjinsa na faduwa hakan bai sa ya sauya ƙudurinsa ba. Hannu ya kai ga wani hotonsu da suka yi a tsaye da ƙananun kaya, asalin hoton a waya suka yi amma saboda kyansa suka wankeshi suka sanya a frame. Ya dauka ya cusa a jakarsa. Ji yake kamar muryar Hajiya Zeenatu na amsa kuwwa a kunnensa. Gani yake idan har ya kara kwana bai je inda take ba haukacewa zai yi. Daga wannan tunanin ya sa ƙafa ya bar gidan. Maigadi na can yana sharar bacci ya fice gaba daya.
Wannan tafiyar da Hussein ya yi, shi ne tafiyar da bai ƙara takowa gidansu ba har wannan lokacin.
***
Koda ya isa Kano ya nemi Hajiya Zeenatu, ji ta yi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. Da kanta ta daukoshi daga tasha zuwa gidanta.
"Nasan dama ba za ka iya rayuwa babu ni ba."
Da jajayen idanunsa ya dubeta ya bi ta da murmushin yaƙe.
Ta mike zuwa dakinta ta faɗa bandaki, zirr ta yi ta wanke jikinta da ruwan magani kafin ta dawo ta shirya ta rambaɗa kwalli. Wani gari ta ɗebo a hannunta ta dawo falon.
Yana kallonta har ta zauna, a hankali ta bude tafin hannun ta huramasa a fuska. Tun yana ganinta daidai har ya yi luuum ya soma lumshe ido.
Wani magana ta shiga yi mishi a dodon kunne yana nanatawa.
"Ni kadai ce a wajenka, ni kadai ce a zuciyarka, ba ka da dangin da ya wuce ni. Ba ka da kowa a duniya sai ni."
Ya nanata, tun yana yi har a hankali ya kwanta kamar mai bacci. Wani mahaukacin dariya ta sanya.
***
Malami har gida ta kirawo ya daura aurenta da Hussein. Rabon goro da aka yi a makwafta ne ya sa suka san ta yi aure. Daga wannan lokacin Hussein ya zama mallakin Hajiya Zeenatu ita kadai, jallin jal!
Ya samu aiki a wani babban kamfani ta hanyarta, tun yana matsayin ma'aikacin har a karshe saboda jajircewa da amanarsa da kuma sanin makamar aiki, ya zama Manajan kamfanin.
Hajiya Zeenatu likkafa ta ci gaba, ta gina shaguna da dama, auren Hussein sai ya zama kamar wani buɗi a kasuwancinta. Ta dinga samun albarka a ciki kamar me. Har ya kasance ta bude shagon siyar da gwala-gwalai a sabon gari, tana kuma da na abayoyi, takalma da jaka a sabon gari. Suka hadu ita da mijinta suka bude katafaren shagon kayan maƙulashe mai suna A&Z Snacks and more.
***
CI GABAN LABARI...
I just published "BABI NA HAMSIN DA UKU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1012068713?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=j0FhiwXlITINd2s%2FHQAEEJr6H0gN34Yx%2FYGs482Ps7p3eJzBM%2FSmZhkqmfmpfxwFqACqKgF4HYZBiBOLOGtFCjGLt%2FaBpqaFBTls4fQJ%2Fq25n%2BYh6%2FU6TYbmPJBSRTTM
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
53)
ADAMAWA
Hafsat ce tsaye a farfajiyar gidan suna hira da Tahir, murmushi sosai ne saman fuskarta, ko ba'a faɗa ba duniyar ta mata daɗi. Tahir kuwa jin komai yake yi kamar a mafarki, dama an ce mai hakuri kan dafa dutse har ya sha romonsa, yanzun gashinan ya gani. A hankali soyayyarsa ta kama zuciyar Hafsat.
"Dariya na ba ki?" Ya fadi yana murmushin shima. Hafsat ba ta kai ga ba shi amsa ba, suka ji hon. Nan da nan ta rude, ta san AlHassan ne don ya kira Dada ya sanarmata cewar yana hanya, ba wanda zai zo gidan da darennan idan ba shi b, hakan yasa ta dubeshi.
"Mu yi magana ta waya. Bari na shiga ciki."
Ba ta bari ya kai ga amsawa ba ta yi gaba da sauri. Tahir ya shafi ƙeya yana murmushi. Daidai sadda motar AlHassan ta faka, ya nufi wurin. Sai dai ya tsaya cak yana kallon wanda ya soma fitowa daga mazaunin gefe. Kamar AlHassan kamar ba shi ba, kafin ya kai ga tantancewa sai ga AlHassan ya buɗe murfin ƙofar ya fito
Wani tsalle da Tahir ya yi ya rungume Hussein yana ihun murna sai da ya ba AlHassan mamaki, sai kuma ya yi dariya. Duk wanda ya zauna da Dada ko na minti talatin ne, sai ya san yanda take kewar Hussein. Balle kuma Tahir wanda dama shi a baya ya san Hussein din, duk da ba su wani saba ba. Sanadin zamansa a garin kuma a gidan yasa shi damuwa da damuwar Dadan har yakan taya ta addu'a.
Suka dunguma ciki zuwa falon, Hussein jikinsa har rawa yake, burinsa kawai ya sanya Dadarsu a ido.
Tana falon zaune, a gefenta Fatima ce ke cin Popcorn duk ta ɓata hannunta da madara. Hafsat kuwa ɗaki ta shige gudun kar AlHassan ya gan ta. Sallamarsa ta yi yanayi da ta AlHassan, hakan yasa Fatima wurgi da ledar Popcorn a guje ta nufeshi idanunsa akan Dada, ya durkusa ya ɗaga ta cak kafin ya rungumeta. Dada tsam ta miƙe jiki na rawa tana mai ƙuramasa idanu, a hankali idanunta suka ciko da kwalla. Nan da nan ta shiga zubar da hawaye, ta kalli AlHassan ta dubeshi, da sauri ya ajiye Fatima wacce ta yi turus tana kallon wanda ya ɗaga ta alhalin ga babanta a baya ya shigo. Da sassarfa ya isa ga Dada ya rungumeta kawai sai hawaye masu ɗumi suka zubomishi.
"Dadata." Dada ta lumshe idanu ta bude, shakka babu ba mafarki ta ke yi ba. Da sauri ta ɗago kan Hussein ta na shafa fuskarsa da duka hannuwanta biyu. Kukanta bai tsaya ba hakan ya jawo mata rawar murya.
"Husseini, kai ne? Dagaske kai ne tsaye a gabana? Allahu Akbar."
Kawai ta kara ƙarfin kukanta. Ya ja hannunta suka zauna saman kujera, ya zame hannunsa guda cikin nata. Ya shiga sharemata hawaye.
"Ni ne Dada, Hussein dinki ne. Na dawo gareki Dada. In sha Allah ba zan ƙara nesanta kaina da ke ba. Ki yafemin, wallahi ba ni da laifi."
Ta shiga girgiza masa kai amma ina! Ta kasa magana don kuka sai kuma ta shiga dariya da hamdala.
"Yaya Hussein?" Hafsat ta fadi a hankali bayan fitowarta daga ɗakin hayaniya ta ƙi ƙarewa. Ta ƙarasa itama ta rike hannunsa, kallonta ya ke yi da mamaki kafin ya yi ƴar dariya ya dubi Dada.
"Auta kenan?"
Ta yi murmushi kawai, ba ƙaramin mamaki ya yi ba.
"Shekaru bakwai fa Husseini, jiya ba yau ba. Tun kana da shekaru ashirin da takwas muka rabu da ganinka."
Hawaye Dada ta share tuna irin jinyar da ta yi adalilin rashinsa.
"Ya isa kukan please Dada. Mu godewa Allah tunda yanzun ya cika buri."
AlHassan ya furta don har ga Allah ba ya son ganin ana kuka, musamman ma kukan Dada.
Nan fa aka shiga nan nan da Hussein, abinda ya fi so a baya, wato fura da kuma dambun shinkafa, shi Dada ta sa Hafsat ta yi. Dakyar Hussein ya rarrasheta akan a bar Dambun dare ya yi sai zuwa gobe.
Bayan sun gabatar da sallar isha'i suka zauna zaman hira. Shiru ya yi yana jin AlHassan na waya da su Hajiya yana sanarmata cewa sun sauka lafiya. Bayan ya kammala ne aka shiga hira. Tiryan-tiryan AlHassan ya ba Dada labarin komai tun daga farko har ƙarshe. Dada kuka ya dawo sabo. Takaicinta yanda matar ta ɓatawa ɗanta ƙuruciyarsa.
"Me ka ke jira ba za ka saketa ba Husseini?"
Murmushi Hussein ya yi gami da ɗan matsa ƙafar Dada kaɗan.
"Komai yana da lokaci My Dada, ki kwantar da hankalinki."
Ba haka Dada ta so ba, sai dai kuma ba ta tsoron komai tunda ta san ki mene yanzun da asiri a ciki. Da yardar Allah kuma hakan ba zai ƙara faruwa gareshi ba.
Tahir dai kallonsu yake kawai, ya lura da ɗan sauyin da Hussein ya soma gwadamishi tun da ya ji alaƙarsa da Kawu. Bai yi mamakin komai ba don ya san dama za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Shi kam yana tunanin fasa tafiya Kano da zai yi a goben sai zuwa jibi duk kuwa da irin wayar da Kawun ke dokamishi akan ya dawo.
Washegari da safe dangi suka cika ganin Hussein, Gwoggo Karime har da kukanta, takanas ta tahowa da Hussein lafiyayyen farfesun da ta girka da hannunta. Hakanan shima Kawu Adamu, hatta da sauran yaran Inna da ke a Adamawa da yaran Hajjo sun zo ganin Hussein. Gida ya cika ana murna, ya yi mamakin yanda suka sauya. An sha hira kamar ba gobe. Fatima tunda ta gane dan uwan mahaifinta ne ta maƙale masa, wannan kaunar nata da ya soma yi tun bai san dangantakarsu ba yana nan daram a ransa sai ma ƙaruwa da ya yi. Kowa ya yi Allah wadai da Hajiya Zeenatu, har da masu kuka.
Ranar dai har dare bai samu kansa ba sai dakyar. Hajiya Zeenatu ta kira sai hakuri ya ba ta ya nunamata ana ta tambayarta da son ganinta.
"Ko na biyo hanya gobe na zo?"
Ya yi murmushin mugunta jin irin wannan wauta daga matar da ta kusa dosar shekara hamsin.
"Aa Hajjaju, ki yi zamanki, idan zan ƙara zuwa sai mu dawo tare. Dawowar dindindin."
Wannan amsar ya ba ta sai ta ɗan yi turus, a karshe dai ya yi mata dabara ta sake kafin su yi sallama.
Ƴan Maiduguri labari ya riskesu su ma sai murna. Hussein ya san zama bai gan shi ba, zaga dangi ya zamar masa dole.
***
BAYAN SATI BIYU..
KANO
Ta fito daga motarta a farfajiyar asibitin Baba Dakta. Amrah aka yiwa aiki sakamakon faɗuwar da ta yi a bandaki da ya jazamata naƙudar dole, cikinta bai jima da shiga wata na takwas ba, an ciromata Baby Boy. Yaron sai ka rantse ya shiga watansa tara cif sannan ya fito duniya. Ta zagaya ɗayan gefen ta ɗauki kwandon abincin da ta kawomusu Da ka ganta za ka fahimci tana cike da farin ciki. Tun da ta ji labarin auren da Chairman zai yi na huce haushi take jin ta kamar an mata albishir da gidan aljanna. Yanzun ta kara tabbatarwa babu abinda zai ƙara haɗa ta da shi. Ta sha adonta cikin laffaya dark brown mai adon milk flowers a ƙarshensa. Fuskarta babu wani heavy make up, hoda kawai ta shafa sai man leɓe mai danƙo. Ga duk wanda ya ganta sai ya ƙara kalla, Allah Ya ba Ramlat ƙira mai kyau, sai ka rantse ba ta taɓa haihuwar ko ƙwai ba ballantana ɗan mutum. Da wannan takun ta ƙarasa cikin asibitin zuwa dakin da aka kwantar da Amrah. Ta murda kofar da sallama ta shiga.
Umman Amrah na zaune gefe tana kurɓar ruwan shayi, ta karasa suka gaisa. Amrah na bacci. Ajiye kwandon ta yi ta ƙarasa ga gadon Babyn, murmushi kawai ta ke yi tana ƙaremishi kallo, duka-duka yau kwanansa hudu a duniya.
"Ki ciro shi mana Ramlat, ke da ɗanki."
Ta juyo tana dariya kadan.
"Um um, gwara ya yi baccinsa Umma. Ni gani ya yi yana juyewa zuwa kamannin Zaituna."
Umma ta yi murmushi.
"Gashinan dai, sai sauya kamanni ya ke."
Ta jinjina kai.
"Naga kin warware sosai yanzu, ko don kin ji labarin auren Chairman ne?"
Umman ta karashe da dariya, itama dayake abinda ke ranta kenan sai ta sa dariyar.
"Umma bari kawai, sosai fa na ji dadin rabuwa da alaƙaƙai."
Dariya sosai ta ba Umma.
"Kai Ramlatu ba ki da dama, wato alaƙaƙai? Ko ya suka ƙare da Kawunnaki?"
Ta ɗan taɓe baki. Chairman a farko cewa ya yi dole Kawu Bello ya biyashi kudaden da ya kashemusu, daga karshe dai ya yafemasa ya ce komai ya wuce.
"Yanzu ki ka zo?"
Muryar Amrah ta katse su. Suka dube ta.
"Yanzu na zo, sannu ya jiki"
Amrah ta amsa tana kokarin mikewa zaune, cikin sauri Ramlat ta karasa ta taimaka mata. Ita ta yi mata rakiya bandaki ta yi fitsari da kuma brush sannan suka dawo. Umma kuwa ta gyara shimfidar ta kwantar da ita.
Ramlat ba ta wani jima ba ta yi musu sallama ta fice zuwa wurin aikinta. Tana tafe tana tunani, idan har Hussein zai iya mance ta ko a whatsapp bai neme ta ba, ita kuwa meyasa ba za ta dangana ta hakura da shi ba? Ta gama saddaƙarwa babu ita a ransa, ba ya ta tata. Don haka tana ji har zuciyarta ta hakura da soyayyarsa. Da gaskiyar Auta A'isha da ta taɓa ce mata gani take kamar Hussein ya fi ƙarfinta, yanzun kuwa ta yarda kuma ta gasƙata. A hankali ta sa bayan hannu ta share kwallar da ta cika idanunta. Muddin zai faɗomata a rai to fa sai ta ji kwalla.
Wayarta ta ɗauki ƙara, ta kai duba. Baban Hanif, kamar yanda ta sanya sunansa, wani ne da ba su yi ko sati da haɗuwa ba, ta kai yara shopping, a farko ya dauka tana da aure don haka ya hakura, sai dai haduwarsu ta biyu a kofar gidan Hisham kasancewar shi gidansa a Badawa Layout yake, ya ganta. Ya san Hisham don haka bai ƙasa a gwuiwa ba ya faka motarsa ya sauko suka gaisa da Hisham, ta gaidashi ta shige cikin motarta. A bakin Hisham ya ke jin cewar ba ta da aure, anan ya nunawa Hisham yana so. Hisham ya yi shiru a sannan, a karshe ya nunamasa ba ruwansa ya nemi soyayyarta. Da kansa ya yiwa Ramlat magana ta fito daga motarta, ta tsaya ta dan saurareshi. Ita kuwa ganin tunda har Hisham bai hana ta kulashi ba, kuma aminin Hussein ne, to tana da tabbacin babu alamar Hussein na sonta. Wannan yasa ta dangana ta hakura ta ba Baban Hanif dama.
Sauke ajiyar zuciya ta yi ganinhar wayar ta katse ba ta ɗaga ba. Ya ƙara kira ta ɗaga. Bayan amsa sallama ta ba shi uzurin tuƙi dole ya hakura.
***
"Shi kika tsayar kenan matsayin miji?"
Tambayar Baba Dakta ya sa gabanta ya faɗi, kanta a ƙasa yayinda yake zaune saman darduma idanunsa sanye da gilashi yana duba wani littafi na addini. Ta haɗiyi miyau, ta hakura yanzun za ta auri Baban Hanif. Ko ba komai ta yaba da hankali da nutsuwarsa. Hatta da Hajiya wannan karon da ma yan uwanta kansu, hankalin ya kwanta da shi.
"Eh Baba."
"Ramlat, kamar yanda ki ka amince da aurensa, bana son jin wata magana ta ɓullo daga baya."
A hankali hawayenta ya zubo, ba wanda ya fadomata a rai sai Aliyu da kuma yanda aka yi gumurzu a lokacin bikinsu. Abbanta ta tuna wanda a yanzun ta ke kallon Baba Dakta kamar shi. Basu da hadi sai zumunci tun shekara da shekaru da ya kasance Baba Dakta har yana da karfin ikon yanke hukunci a kan iyalin Abbansu, kuma ta zauna.
"Na ba ki nan da kwanaki uku, ki yi tunani dakyau, idan har kin amince ki zo ki sanar da ni. Zan ba shi damar ya turo magabatansa. Allah Ya zaɓamaki abinda ya fi alheri."
Ta kasa amsawa a fili sai a zuci, jiki a sanyaye ta mike ta mishi sai da safe ta kama hanyar gida. Kiran kenan daman, koda ta isa gida ba ta ɓoyewa Hajiya komai ba. Hajiya ta yi murmushi.
"Yaron ya san abinda ya ke yi da alama, kuma ko ba komai ɗan babban gida ne tunda Kakansa ma abokin Kakanki ne, wato Mahaifina. Zuri'ar Imam Shu'aibu Lawwali bani da shakku a kansu da yardar Allah. Kuma ke a dadinki ma tunda ba gida daya zai haɗaku ba da matarsa."
Ramlat ta yi shiru jikinta a sanyaye kawai tana sauraron Hajiya. Ta daure ta yi murmushin da bai kai zuci ba. Tana ji a ranta ko mutuwa za ta yi, wannan karon ba za ta ba iyayenta kunya ba. An yi ta kuma an ƙare.
A wannan yanayin Munir ya shigo gidan a fusace, suka dube shi. Oyoyon da su Affan ke mishi bai amsa ba. Bayan zamansa Hajiya ta dubeshi bayan amsa gaisuwarsa.
"Lafiya kake kuwa?"
Ya yi kwafa.
"Hajiya, wallahi Bilkisu ta haukace. Ba ta da hankali. Akan zama a gaban mota ta kama Hunainah da duka."
"Da cikin?!" Fadin Hajiya da Ramlat har suna hada baki.
"Na gaji! Wallahi na gaji da wannan rigimar ta Bilkisu. Haka kwanaki ta kawo wannan ƴar iskar ƙanwarta Salma, yan iskan samarinta na zuwa tafiya da ita night club ni kuwa na kora ta gidansu ba zan iya ba."
"Kai ba wannan ba, ka ce ta daki yarinya, yanzu ya ake ciki?"
Munir da har lokacin bai huce