Showing 15001 words to 18000 words out of 230725 words

Chapter 6 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1045

bisani suka yi sallama.
  
    "Mene?" Ta furta tana mai duban Maman twins da Rafee'ah.

  "Kin fimu sani ai, har kin samu wani majnun ɗin ba labari ko?"

Ta saki baki kawai ta kasa magana.

"Bar ta. Ni kai da naga ana shirin kasamin in law."

Hajiya ta dubi Maman twins.

"Wa kenan?"

"Baba Bashir yayan Baban twins mana, wanda matarsa ta rasu. To ai shi ne ya ga Ramlar kwanaki can ya nunan ana so. Maganar kenan da nake son nayi da ita amma ƴar albarkar ba ta kirani ba, ba ta zo gidannawa ba."

Ramla ta ja guntun tsaki.

"Don Allah ku bar wannan maganar, shi fa da kuke ganin mun yi waya, takalmi ne na tayashi zaɓar ƴarsa shi ne dalilin da ya kira suka yimin godiya don takalmin ya burge ƴar. Maman twins shi kuma Bashir ai kin ba shi lambata, sau ɗaya ya taɓa kirana kuma na ɗaga mun gaisa na ba shi hakuri. Mai kuma zan daga kiransa ya kara cemin?"

Daga haka ta kwashi tarkacenta ranta na zafi ta kama hanyar barin falon.

   "Ai fa, wannan zafin rai da taurin kan ba zasu taɓa bari ki yi gaba ba Ramla. Ki dai bi sannu tunda yanzu ke mai ba wa wasu labari ce. Kinga dai makomarki."

Ba ta san sadda ta juyo gaba dayanta ba tana duban Rafee'ah wacce ta fusata. Ba dai ta ce komai ba ganin Hajiya na tsawatarwa ta juya ta wuce ciki, sai dai kafin ma ta kai ga shiga dakin tuni ta soma fidda hawaye. Tana ƙarasawa ta rufe gam da muƙulli ta faɗa saman gado. Ta yiwa kanta illa, tun ran gini tun ran zane, tana kyautata zaton dalilin ne yasa abu kadan ta aikata sai cibi ya zamo mata ƙari. Miƙewa ta yi ta rage kayan jikinta ta faɗa wanka. Koda ta fito shiryawa ta yi cikin doguwar jallabiya mai ɗankwali. Idanunta ya kai ga ɗan akwatin mai kalar golden da ke ajiye saman mirror dinta. Ƙarasawa ta yi ta buɗe, wani envelope ta fiddo ta zauna gefen gado ta buɗe. Hotunan ta ciro tana ƙaremishi kallo. Wani lokaci ta tuno wanda har abada ba zai gushe daga kwakwalwarta ba.

***
   *MATAR MUTUM*

Tun tafiyar Hilal ta ƙara jin kewa ta cika zuciyarta. A bangare guda ga tunanin Aliyu da ya zamemata abin yi safe da rana. Wannan ta sanya suna kammala zana jarrabawarsu ta zango na biyu a makaranta, (2nd term), ta tattara Abba ya kaita Yakasai ta yi hutun a can ko ta sami nutsuwa.

   Ta ci sa'a kuwa jikokin gidan wadanda suka kasance sa'anninta duk suna nan suma. Aikuwa suna ganinta suka ruƙunƙumeta da murna.

"Oh yarannan shikenan kuma za ku hana bakinmu ya huta da bari-bari kamar wasu ƴan shekara hudu. Ai ko su A'isha sun fi ku hankali." Cewar Talatu ƴar kawun Abba wacce ta dawo nan da zama daga Daura.

"Bar su su yi son ransu Talatu idan ba so kike yanzu Hajja ta maidaki Daura ba." Fadin Abba yana dariya. Hajja dake taunar goro tana tayashi.

"A'a to, rabu da su. Wataran sai labari duk suna gidajen aurensu."

Maganar Hajja ta ba su Ramla kunya, duk suka mike su ka yi ɗaki har suna bangazar juna.

"Magulmata." Fadin Hajja cikin dariya. Abba ya shantake har da cin kwaɗon zogale kafin daga bisani ya yi musu sallama.

  Washegari da misalin karfe uku na yammaci ƴanmatan su biyar, Usaina, Maryam, Jidda, Nafisa sai Ramla. Suka shirya suka fita zuwa gidan babban ɗan Hajja Zulai, Kawu Kabiru don ziyara.

Tun kafin su fita titi Ramla ke mitar ita kam ba wacce za ta dauka saman cinyarta sai dai su yi abin hawa biyu.

"Kai Mrs Hilal, don ɓarnar kuɗin mota?" Fadin Jidda tana auna abinda zasu kashe daga Yakasai zuwa Zoo road.

"Aa fa, da gaskiyar ƙawalli, ba zan yarda nima na ɗora kowaccenku a cinya ba, ke kuma Jidda idan har za ki iya hawa bayan kujera shikenan."Faɗin Usaina.

Ta ƙasashe suna dariya don ita kanta ta faɗa ne, a ƙiba kam duk Jidda ta fi su.

"Allah Ya kiyaye." Cewar Jidda.

Aikuwa dai sai rabawa suka yi, kusan a tare suka samu abin hawa, Ramla da Usaina su biyu kacal a adaidaita sai Jidda, Maryam da Nafisa wuri guda.

Sai da suka kusa Zoo road ya samu fasinja. Sallama ya yi ya shigo, kusan da sauri ta dubeshi. Shi ne, shima yana zama ya kai duba gareta. Duk da yanda ta yi saurin kauda kwayar idanunta gefen Usaina wannan bai hanashi ganeta ba. Ta ƙara matsawa jikin Usainar ganin yanda jikinsu ke ɗan gogar juna. Murmushi ya yi ya matsa ta yanda ya san za ta fi sakewa.

Bai ce uffan ba banda murmushin da yake faman dokawa, abin mamakin shima Zoo road ya nufa. A hankali ta kai duba gareshi ta cikin karamin gilashin ɗan sahu. Kwayar idanunsu ya sarƙe da juna ta yi azamar janyewa. Ba ta ƙara gangancin kallonsa ba, mutumin da take kwana da tashi da tunaninsa. Kirjinta bai bar bugu ba, ba ta fahimtar zantukan da Usaina ke yi.

"Sauka mana." Ta ji muryar Usaina karo na biyu, sai sannan ta dawo nutsuwarta ta dubi gefenta, tsaye ta hangoshi a waje yana sallamar mai adaidaita. Ta kauda ido ta fito, Usaina na bayanta.

"Ɗauka har da nasu." Ya furta ga ɗan sahun.

Nan suka ce a'a, ya rantse shi zai biya, Ramla na shirin jan musu ta ji Usaina ta ɗan bugi kafaɗarta alamar ta yi shiru. Godiya suka yi mishi, hango su Jidda sun tsaya ya sanya Usaina nufarsu.

"Ramlat."

Ta tsaya cak gami da juyowa ta dubeshi, ba ta yi mamakin jin ya ambaci sunanta ba don Usaina ta kira sunan ya fi a ƙirga cikin adaidaita. Ya ɗan matso kaɗan.

"Karo na biyu Allah Ya yi haɗuwarmu. Tun sadda na sanyaki a idanuna har yau bani da sauran sukuni. Wallahi ina sonki!"

Ya furta fuskarsa na nuna alamar gajiyawa da kuma gaskiyar abinda ke ransa.

Ta matse yatsun hannunta jin yanda kirjinta ke bugu, ta ɗan kuramasa idanunta da suka cicciko da kwalla. Shima kallonnata yake da nashi mayun idanun wadanda tuni sun dulmiya cikin tafkin kauna da shauki.

"Ayya ka yi hakuri Malam, wallahi an sakamata rana. Nan da shekaru uku ba kaɗan bikinta."

Kalaman Usaina ya maidota hayyacinta, ta tsinci bakinta da maimaita abinda aka ankarar da ita.

"Eh, an sanyamin rana. Ka yi hakuri."

Ya yi murmushin yaƙe. Ya dubi Usaina.

"Kaicon wanda zai yi wasa da damarsa. Akwai kuskure a jan lokaci har haka. Watakila kuma rabon Aliyu ce. Ina muku fatan alheri."

Ya dubi Ramla da fuskarsa wacce ta yi narai-narai.

"Matar mutum Ramla, matar mutum.."

Daga haka ya juya ya bar wurin. Ramla ta tsaya kamar wata mutum-mutumi. Kafaɗarta aka jijjiga.

"Ke dillah can! Mene hakan? Waye shi? Ko kin manta da sanya ranar da ke kanki? Ke Usaina waye shi?"

Duk Nafisa ke wannan kalamin daidai sadda suka ƙaraso, zantukan ƙarshe sun sauka saman kunnuwansu.

Tuni ta soma tafiya kanta a ƙasa, tana ji Usaina na basu labarin abinda ya faru suna jan tsaki da kiran kwalelansa. Can kuma ta ji suna koɗa iya ɗaukar wanka da kuma kyan da Allah Ya mishi daidai gwargwado. Ta shiga tariyowa.

Milk shadda ya sanya da aka yiwa aiki daidai da zamanin, ya dora hula brown da ratsin milk din. Dogo ne don har ya fi ta da kaɗan, yana da hasken fata. Tafiyarsa ma kadai za ta burge mutum. Yana da ɗan duhun lebba, gashin kansa a cike luf-luf wanda ya taho har gefen fuskarsa ya haɗe da ɗan ƙaramin gemunsa. Lafuzzan Aliyu ma kadai abin burgewa ne.

Murmushi ta yi wanda ya taho tare da hawaye, ta yi azamar sharewa lokacin da Maryam ta dafa kafaɗarta. Ta kai duba gareta.

"Ina za ki?" Sai sannan ta waiga ta gansu tsaye a ƙofar gidan yayinda ita kuwa ta ɗan yi gaba. Tabbas tunanin Aliyu ba zai kasheta ba. Ta yarda matar mutum kabarinsa don haka ta haramtawa rai da gangar jikinta tunaninsa tunda har shima ya fahimci Hilal ne zaɓin Allah a rayuwarta, kamar yanda shima ya samu daidai shi.

'Allah Yasa hakan kake nufi.'

Ta furta a ƙasan ranta.

Sun wuni cur a gidan Kawu Kabiru tare da iyalinsa, tun Ramla na ƙin magana da faɗawa tunani har dai ta yi watsi da komai sai dai ta kasa yakice kalmar Ina sonki da Aliyu ya furta. Da zarar ta tuno a karon kanta sai ta saki murmushi.

Sai yamma suka bar gidan.

Haka ta ci gaba da rayuwa gidan kakanninta tare da su Jidda, duk kuwa hakan bai tafiyar da tunanin Aliyu ba. Abinda ke tsorata ta bai wuce yanda so da kaunarsa ke neman rinjayar zuciyarta ba. Har yakan maida tunanin Hilal gefe guda ya ajiye.

Sai da ya rage sauran kwanaki uku su koma makaranta sannan duk aka watse kowannensu ya koma gidansu, nan ma ji suke kamar kar a rabu.


***

"Wai ke ba za ki buɗe kofar ba? Me kenan hakan? Ba'a isa a faɗamaki ki ji ba?"

Muryar Maman twins ta bugi kunnuwanta, ta share hawayenta ta tattara hotunan ta maida mazauninsu sannan ta bude kofar fuska a haɗe.
Shigowa ciki Maman Twins ta yi tana fadin

"Allah Ya shiryamana ke Ramla, bansan sadda za ki rabu da wannan bakin ran naki ba. Haba jama'a! To sai ki fito Hajiya na nemanki."

Ta miƙe ta bi bayanta zuwa falon. Hajiya sosai ta buɗe mata wuta kan ba ta son irin haka, dole ta ba Hajiyar hakuri itama Rafee'ah ta bata.

Kafin su bar gidan sai da ya kasance komai ya wuce kamar ba su yi ba.

***
Kwanci tashi asarar mai rai, cikin ikon Mai Duka bikin A'isha ya taho gadan gadan, ana saura sati ƴan Daura suka dinga cika gidan. Wasu a can Yakasai wasu kuwa anan wurin Hajiya.

Ana saura sati a sanya A'isha a lalle Ramla ta ɗauki katukan daurin aure da na wuni ta kai ofishinsu. Ranar da ta kama Asabar kuwa, takanas ta shirya yara sai gidan Muhibbat wanda daga nan zasu wuce gidan Ramla rabon kati. Mutane biyu masu muhimmanci a 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem

07)

Daga ita sai Affan suka fita. Unguwar Gwammaja nan suka soma nufa gidan Muhibbat don ta tabbatar idan ta shiga gidan Amrah za ta ɓata lokaci, ko ba komai an dade ba'a hadu ba dalilin tafiyar da Amrah ta yi zuwa Lagos tare da Maigidanta wanda rabin aikinsa a can ne.

"Don Allah ina iya ɗaukar fasinja?"

Muryar ɗan sahun ta katse tunaninta, ta kai duba ga wanda ke tsaye shima yana kallonta yana jiran amsa, abubuwa da dama hakan ya tunamata, ta daure ta dubi mai adaidaita fuska a haɗe.

"Ba haka muka yi da kai ba. Ko ka mance shata na ɗauka?"

Kafin mai adaidaita ya ce wani abu mutumin ya kauce gami da bata hakuri. Wannan tasa ɗan sahun fisgar abin hawar da alama ransa bai mishi dadi ba. Ta ƙara riƙe Affan kar ya tuntsira ba ta ko damu da yanda ɗan sahun ke shirga uban gudu ba. Hankalinta ya tafi ga tunani. Meyasa abubuwa da dama suke ƙin ɓacewa daga kwanyarta? Ba ta jin har ta mutu za ta mance da Aliyu.

***
   _*ABIN ƁOYE*_

Tafiya na kara yin nisa, makonni na shuɗewa zuwa watanni, har ta kai lokacin da Ramla suka kammala aji na hudu a Sakandire suka wuce SS2 kai tsaye. A wannan lokacin idan ta ce ta huta daga tunanin Aliyu tasan ƙarya ne. Motsinta da komai ya zama shi, ramarta na tada hankalin Hajiya.

"Na tsammaci ko kujiba-kujibar bikin Rafee'ah ne ke ramar da ke yanzu kam na tsorata. Ki fadamin mene damuwarki? Ko ba ki ga yanda kika bi kika lalace bane? Idan ma tunanin aure kike ki tattara ki ajiye a gefe tunda sanin kanki ne Abbanki ba zai aurar da ke ba sai kin kammala Sakandire. Wannan ai shirme ne. Kalli yanda ko abin kirki ba ki yi ba a jarrabawa, ni ban ga amfanin wayar da Abbanki ya siyamaki yanzu ba, na tabbata kuma zai kara dauke hankalinki ne kurum daga karatu!"

Duk wannan bambamin da Hajiyar ke yi, Ramla na zaune tana fidda hawaye ga wayar da Abba ya damƙamata Nokia mai tocila rike a hannunta, ƙala Hajiya ba ta ce ba sadda aka yi budurin ba ta wayar sai bayan fitar Abban ta ke fitar da abinda ke ranta. To itama ta gaji! Ta gaji da tunanin mutumin da ba ta san inda za ta ƙara ganinsa ba. Tunaninsa na taɓa walwalarta, ya kasance ba ta murna da kiran Hilal, ba ta murna idan ya yi mata aike ta hannun Yaya Munir. Yakan tambayeta ko lafiya ta ce ba komai. Duk a rashin sanin cewa yanzun ba shi take da muradi ba, soyayyar wani can da ba ta san inda za ta ganshi ba, ya fi komai dagula lissafinta.

"Shikenan, kin yi shiru ina magana kin rabu da ni! Tunda haka kika zaɓa ki yi ta zama da kuncinnaki, sai dai wallahi kin ji na rantse muddin wannan shekarar a zangon karatunki na farko (1st term) naga ba ki tsinana abin a zo a gani ba, da kaina ba Muniru ba, zan kwace wayar na kuma hanaki fita. Shashasha kawai!"

Ta dawo nutsuwarta sa'ilin da Hajiyar ta miƙe za ta fice daga falon. Da sauri ta ƙarasa ta sha gabanta, kallon da Hajiyar ta mata sai jikinta ya yi sanyi, ta sunkuyar da kai tana ci gaba da kuka a hankali. Tsakanin ɗa da uwa sai Allah, ba ta san sadda ta ja hannunta ba suka zauna saman kujera.

"Menene Ramlatu? Kun samu matsala da yaron ne?"

Ta na nufin Hilal, ta tsinci kanta da gyaɗa kai.

"Amma mun shirya, don Allah kiyi hakuri Hajiya. Na miki alƙawarin chanjawa, wannan karon ba zan ƙara ba ku kunya ba a karatuna."

Jikin Hajiya ya yi sanyi, nan ta shiga yi mata nasiha akan kar ta sake ta sabarwa da kanta haka.

"Don kin yi faɗa da mutum bai zama dalilin da za ki sauya rayuwarki ba. Kenan ko kun yi aure haka za ki dinga yi? To kul! Shi rashin jituwa idan an yi nan take ake yiwa juna sulhu kuma a nemi gafarar juna. Idan ba mai fahimta bane sai ki bari idan ya huce daga baya ki nemi gafararsa. Wannan damuwar bana so, kar ki ƙara."

Ta amsa da to gami da godiya. A ranar ta yi kokarin sauyawa kuwa, ta rage kulle kanta a ɗaka tana tunane-tunane, gidan yanzu daga ita sai Auta A'isha tun bayan bikin Rafee'ah. Hakan da ta yi sai ya kwantar da hankalin Hajiya. Ita kuwa duk abinda take daurewa take gudun matakin da Hajiya za ta dauka a kanta.

   Yau wunin gidan Rafee'ah zasu yi tare da Auta A'isha. Tun safe suka shirya Abba ya ragemusu hanya ya basu kudin mota. Sai da direbansa ya taremusu abin hawa drop har gidan Rafee'ah sannan suka rabu. A hanya suna tafe tana yin game na snake a waya, kusan a lokacin kaga budurwa da irin wayarta ba karamar babbar yarinya bace. Wannan ta sa take latsawa cike da jin ta isa.

A daidai junction suka tsaya, ba ta ankara ba ta ji an zare wayar daga hannunta. Cikin razana ta juyo har tana shirin fasa ƙara, yana kan mashin yake dubanta  yana dariya. Kirjinta ya buga da ƙarfi, ta kasa gaskata cewa shi ɗin ne. Hakan ya sa ta lumshe ido ta kara budewa. Ya sauya, ya yi wani fresh, wannan karon ƙananan kaya ne cikinsa. Bakin jeans da riga green wanda ya karɓeshi sosai.

"Barkanki."

Ta yi kasa da kai gami da amsawa murya na rawa.
"Yauwa."
Ta ɗago ta mika hannu.

"Bani wayata."

Ta ƙarashe a kasalance, sai dai wani irin annashuwa take ji can ƙasan ranta, ta kasa daina murmushi. Kullum adduarta Allah Yasa ta ƙara ganinsa.

"Allah Ya karɓi addu'ata, ba zan bari ki tafi ban da lambarki ba."

Maganarsa ta katse tunaninta, ta saci kallonsa ya shiga latsa wayarta. Daidai nan aka basu hannu ya ce ma ɗan sahun su tsallaka sai su yi parking. Ba musu akai hakan. Ya danna kira wayarsa ta dauki ƙara, ta saci kallon wayar, wata ƴar ƙaramar waya ce Lg flip mai murfi ya fiddo. Wayarta ya miƙamata gami da kasheta da kallo.

"Nagode, Allah Ya kaiku lafiya."

Daga nan ya ja mashin ɗinsa sabo fil ya yi gaba, suma suka wuce. Ranar wuni ta yi cikin annashuwa, ji take kamar an mata albishir da aljanna.

  Tun daga wannan ranar suka yi wani irin ɗinkewa da Aliyu. So da kauna mai karfi ya shiga tsakaninsu, duk kuwa a sannan ta ji cewar ya yi aure har tsawon sati hudu. Kishi mai tsanani take yiwa matarsa kuma ƴar uwarsa MUHIBBAT.

  Duk yanda ta kai ga ɓoye alaƙarta da Aliyu abin ya ci tura don tuni Abin Ɓoye ya fito fili.

  ***
"Gwammaja daidai ina?"

Muryar ɗan sahun a zafafe ya katsemata tunanin baya da ta faɗa. Ta sauke ajiyar zuciya tana mai gyara Affan da ya fara bacci ta hau yin kwatance har suka isa kofar gidan Muhibbat. Ta sallami ɗan sahun ta tashi Affan, ya kuwa farka suka kama hanya.

  Gidan Muhibbat take karewa kallo, gani ta yi kamar koyaushe ƙara ƙawatashi ake da sabbin furanni da kuma abubuwan ɗaukar ido. Da sallama suka sanya kai falon.

  Matar gidan ba ta nan sai masu yi mata hidima su biyu sun shantake suna kallon fim na  AfricanMagic Hausa. Sai kuwa yaran Muhibbat su biyu a saman kujera wasa. Babban zai yi sa'ar Ansar yayinda ƙaramin ya girmi Affan da kadan. Fuskarta ba baƙuwa ce garesu ba, aka gaisa, Mujahid da Ammar suka gaidata. Fuska a sake ta amsa kafin ta dubi Affan.

"Ba gaisuwa?"

Ganin haka ya sunne kai yana wangale baki.

"Bari a kirata." Cewar ɗaya cikin masu aikin tana nufar sama, yayinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login