Showing 39001 words to 42000 words out of 230725 words

Chapter 14 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1047

murna ƴata, Allah Ya sanyamaku albarka a abinda ku ka karanta yanzu da ma wanda za ku yi nan gaba."
Itama da fara'a ta amsa da Amin.

"Ina ƙawartaki?"

Fadin Abban a karo na biyu, shi kuwa Munir karaf idanunsa suka faɗa kan Ramlat, bai ga wanda suke tare ba, sai dai tabbas kuka take hannunta kuwa idan ba idanunsa ke mishi gizo ba, yana cikin tafukan hannun namijin. Da sassarfa ya soma tafiya da nufin zuwa wurin, ji ya yi an riko kafadunsa, juyawa ya yi. Hilal ne, ba shi kadai ba har da kannensa biyu, Jidda da Zahra. Jidda ta fi sa'ar Ramlat ba ita kuwa Zahra za su yi kai ɗaya da Auta A'isha. Musamman ya taho da su don su taya sahibarsa murna, har iyayen na mishi dariyar yanda yake rawar ƙafa babu kunya. Sun cakare cikin wasu rantsastsun abaya kalar ruwan toka da kwalliyar baƙin fulawoyi a jiki. Farare tas kamar shi Hilal din, don za'a iya cewa sun ma fi shi kyau. Suka gaida Yaya Munir. Ya amsa, kafin ya mikawa Hilal hannu su yi musabaha.

A wannan lokacin idanun Ramlat suka kai garesu, a gigice ta dubi Aliyu kafin ta zare hannunta ta mike tsaye. Ya dubeta sannan ya dubi inda ta kura idanun, wasu gayu biyu da kuma mata ƴan kwalisa ne. Yasan Yaya Munir don a gabansa Abba ya mishi kashedi. Ɗayan kuwa ne bai san ko waye ba.
    "Me ya kawo Yaya Munir da Hilal? Abba ya zo kenan?"

Jin ta ambaci Hilal ya sanya Aliyu kara dubansa dakyau, da ka kalli idanun za ka hango tsananin kishi balle kuma fuskar da ta sauya nan take har wani ja ja take yi. Bai san lokacin da ya ja tsaki ba, ya mike yana dubanta.

"Saboda wannan ne dama aka ƙi ni a gidanku? Don bani da kudi? Don Aliyu talaka ne ba shi da komai sai rufin asirin Allah? Shikenan Ramlat, bari naje don ba zan tsaya a wulakantani ba. Ga wannan, ya fiddo karamin akwati daga aljihu ya ajiye a kujerar da ya tashi, daga haka ya sa kai da sassarfa ya tafi.

Da sauri ta dauki akwatin tana kokarin bin bayansa, caraf aka rike hannunta. Yaya Munir ne.

"Yau sai kin raina kanki da wayonki! Don ubanki wato har taɓa jikinki yake? Sa'a daya kika ci, Hilal ya zo wurin nan wallahi da yau sai na miki cin mutuncin da ba za ki manta ba. Ƴar iskar banza da wofi!"

Sai ta ɗauke wuta, hawaye kawai ke zuba babu amon kukan. Ƴar iska yau ta zama a wurin Yaya Munir. Zafi goma da ashirin ya haɗarmata. A hankali ta bude jaka ta zura ƴar akwatin da Aliyu ya ba ta ciki daidai sadda Munir din ya saki hannunta.

"Ki zauna nan ki gyara fuskarki tun ban saɓamaki ba!"

Tana kumburin da komai ta share fuska. Koda ta ciro saboda kaifafan idanun Yayannata dake a kanta, a dole ta ɗan murza, ta maida jaka. Sai dai kafin a je ko'ina wasu hawayen sun taho ba shiri ta ɗaukesu da hannu sakamakon hararar da Yaya Munir ya watsamata. Daga haka suka nufi wurin da suke tsaye har su Abba.

"My sweet Aunty."

Faɗin Jidda sa'ilin da ta rungumeta a jiki, ji ta yi kamar ta watsamata garwashin wuta sai dai idanun su Abba ne ya hanata daukar matakin da zuciyarta ta rayamata, wato ta tureta ta faɗi.  Dole ta kakalo murmushi suka kara gaisawa. Itama Zahra haka ta yi mata, Hilal dai na gefe yana kallonta yana kara wassafa yanda so ya koma ƙi.

   Abba ya yi mata murmushi, a kallo daya ya karanci abubuwa da dama  a cikin kwayar idanunta, ya kauda kai sadda ta karasa ta gaidashi.

"Allah Ya muku albarka." Aka amsa da Amin. Nan kuma aka ɗauki hotuna, bayan wucewar Abba da su Yaya Munir har iyayen Amrah. Jidda dake rike da karamar Camera na Hilal ta ce.

"Yayana matso na muku hoto da Aunty."

Ya saci kallon Ramlat dake tsaye gefen Zahra, ba musu ya matso yayinda Zahra ta ja baya.

"Ina wuni." Ya gaidata, gaisuwar da ya ankarar da ita ashe fa ko kallon inda yake ma ba ta yi ba balle ta gaidashi. Ciki ciki ta amsa.

"Lafiya kalau."

"Oh, don Allah ku daina magana, ku kallo nan."

Maganar Jidda ya sanya su dubanta lokaci guda, aikuwa ta shiga hotuna ba kakkautawa. Don kanta Ramlat din ta ja baya. Hakan yasa Hilal kallon Jidda.

"Ya ishemu haka, ke idan kin soma ba ki san ki daina ba."

Ta yi dariya, jiki a sanyaye ta ke duban gefen Ramlat din, tuni ta soma tafiya da nufin barin wajen.
"Lah, Aunty ina za ki? Dawo ku yi hirarku bari mu ɗan zagaya. Dama akwai wata old schoolmate dita a nan, bari naga ko zan ganta."

Da wayo ta ja hannun Zahra suka tafi suka bar su, abinda tunaninta ya bata da sauyin Ramlat shine sun samu saɓani da yayannasu ne shiyasa ta sauya, barinsu su kadai zai sa ta sauko daga dokin fushin.

"Idan ba damuwa mu ɗan fita daga hayaniyarnan please."

Ta kalleshi, idanunsa sun kaɗa, ko menene yau Hilal ta kai shi bango. Yanayinsa ya sanya ta kasa yin musu, suka soma tafiyar kamar ba sa so har suka fice daga Hall din. Can parking space suka isa kasan wata itaciya saman kujeru suka zauna.

   Duk kalaman da Hilal ke zubamata na ban hakuri da rokon ta dawo da soyayyarshi a ranta, ba ta san ya na yi ba, hankalinta na ga ta hanyar da zasu tattauna da Aliyu. Wannan ta sanya ta dubansa.

"Za ka yimin wata alfarma?"

Ya ƙuramata idanu, sai ya murmusa

"Ba abinda za ki nema wurina ban miki ba."

Ajiyar zuciya ta saki, ba kuma ta ji a ranta ya burgeta ba, duk kuwa da cewa tana danne wani tausayi  dake tasomata yana son mamaye zuciyar, ganinta hakan ne daidai.

"Ka sanya Yaya Munir ya ban wayata, ka nunamusu yanzu komai ya wuce. Don Allah ka yimin wannan alfarmar."

Kamar ya ce mata sadda aka kwace bai san dalili ba, bai kuma kamata ya shiga tsakani ba, sai dai ya share.

"Zan san dabarar da zan yi a ba ki wayarki."

Ga mamakinsa sai lokacin ya ga murmushinta.

"Nagode sosai."

Wata ajiyar zuciya ya sauke gami da miƙewa tsaye tun kan kishi ya ci gaba da nuƙurƙusarsa.

"Ki jirani ina zuwa."

Bai jira amsa ba ya wuce. Ta bishi da kallo. Handsome da shi, zai burge kowace mace, amma banda ita. Tana son tuna wani mugun abu da Hilal ya taɓa yi mata sai dai babu ko daya banda tarin alkhairai.

"To ya zan yi? Banda iko da zuciyata."

Ta furta a fili sa'ilin da idanun suka cika da kwalla. Ba ta ji takunsa ba sai wani kwali mai kyalli da ta gani, ta dubeshi. Murmushi yake mai kama da yaƙe.

"Karɓa, kyauta ne gareki. Ina kara tayaki murna."

Ta murmusa itama gami da karɓa.

"Nagode sosai."

"Muje ko? Ina son zuwa wani wuri ne."
Ta amsa da toh, daga nan suka koma ciki ya hada kan su Jidda suka tafi. Jidda ta ji dadi ganin sauyi a saman fuskar Ramlat, wannan yasa ta fahimci abinda take zargi a farko hakanne. Wato dai saɓani suka samu.

***
  "Wai nikam Rabi'atu, ina yiwa yarannan daidai? Hukuncin da na yanke akan auren Ramlatu da yaronnan ban mata gata ba?"

Yanda yake maganar murya a karye ya ɗarsa tausayinsa ba kaɗan ba a zuciyar Hajiya.

"Babu wani hukunci mai tsauri da ka taɓa yankewa Abban Yara. Kowane uba burinsa ɗiyarsa ta auri kamilallan yaro mai kyakkyawar nasaba. Kuma Alhamdulillah, Yaronnan ya kai yanda ake so. Don Allah ka bar sanyawa ranka tunani na daban har ya taɓa lafiyarka."

Ya yi murmushi gami da kara rungume matarsa.

"Aliyu da Ramlatu ke so, yaro ne mai kyakkyawar nasaba sai dai a iyaka bincikena yana shaye-shaye. An sanar da ni goyon kaka ne, ba wanda ya isa ya fadamasa ya ji. Uwa uba bai yi wani zurfi a karatun boko ba balle kuma na addininsa, koda ace na yi niyyar bai wa Ramlatu zaɓinta, ba zan iya daukarta na kai inda za ta yi baƙin jini ba. Ina son yarana. Ina son su samu wanda zai kularmin da su ko bayan ranmu. Meyasa Ramlatu ba za ta yiwa kanta faɗa ba?"

  Tashin hankalin Hajiya dai ganin Abba ta yi yana hawaye, itama ba ta san sadda ta fara ba.

"Yaran ne muke haifarsu bamu isa mu haifo da halinsu ba. Addu'a kawai ya kamata mu ci gaba da yi musu. Allah Ya shiryamana su, Ya bamu ikon kula da amanarsu da Ya damƙamana. Sai dai hakkinsu ne su bi mu, hakkinsu ne su so abinda muke so. Mun tayasu son abinda suke so, meyasa su ba zasu hakura da son ransu su yi mana biyayya ba? Gani suke muna yin wani abin ba don muna sonsu ba. To ya zamu yi? Addu'ar ce dai. Ina tabbatar maka sai ta fi mu alfahari da wannan zaɓin in sha Allah."

Ta ƙarashe tana ci gaba da daukemishi hawayen, ba tare da ta damu da natan dake kwarara ba. Shima ya sharemata yana murmushi gami da sumbatar goshinta.

"Allah Ya yi maki albarka. Ina alfahari da dukkan yaran da muka haifa. Ramlatu ma tausayi take ban, sau tari ne idan ta aikata wani abun sai na cika da mamaki, kamar ba jininmu ba."

"Kar mu yi saɓo, addu'ar ta fi duk wannan."

Suka ƙara murmusawa cike da jin wani ɗaci a kasan ransu kafin kuma su hau tuna yanda a lokacin iyayensu ake auren ɗiya ba ta ko samu damar ganin mijin ba kuma ta yi biyayya ta zauna.

Karshe suka tattara komai suka ajiye gefe suka fuskanci rayuwarsu.

***
   A satin biki aka kawo lefe da komai da ya kamata.
  Gyaran jiki sosai aka shiga yiwa Ramlat, mutanen Daura sun soma zuwa gidan. Yau ma tana zaune wata gwaggonta, ƴar dan uwan mahaifinta daga Daura, ta tasata a gaba da wani hadin magani ta shanye. Dole ta kwankwaɗe ta mike ta bar wurin suna zolayarta. Kai tsaye wayarta ta ciro wanda tuni Hilal ya sanya an damƙamata. Aliyu ta hau kokarin nema a waya, ba zato ta ji an zare wayar a hannunta. Amrah ce tsaye fuska ba fara'a.

"Kar ki cemin har yanzu kina kiransa? Kwana uku ya yi sauran a sanyaki a lalle Ramlat, ki ji tsoron Allah. Kar ya kasance har bayan aurenki za ki ci gaba da kula wannan mutumin."

Tun soma maganar take watsamata banzan kallo kafin ta ja tsaki ta kwace wayarta.

"Ai an so hakan ta faru shiyasa aka yi gangancin haɗani aure da Hilal. Ba zan fasa ba, nace yanzu na fara Amrah. Idan kin ga dama ki yi shiru idan ma ba ki ga dama ba ki yimin terere a dangi. Mtsw."

Ta gifta ta wuce cikin banɗaki ta rufe.  Ta san nan ne kaɗai wurin da za ta yi wayar sirrin da Aliyu. Amrah ta saba da wannan cin fuska na Ramlat akan Aliyu, wannan ta sanya ta girgiza kai da fadin Allah Ya kyauta. Daga nan kuma ta dauki kyallen anko don abinda ya maidota dakin kenan, zasu fita kasuwa siyowa wasu mutan Daura anko. Su Naja'atu ne zasu yi mata rakiya. Saboda biki nan gidan duk suke kwana.

  ***
Tana fitowa daga banɗakin ta ga Bilkisu zaune a gefen gado tana shayar da ɗiyarta. Fuskar Bilkin a daure take dubanta, ta kauda kai itama. Maganar duniya ba ta ɓuya, tuni Bilkisu ta gane komai ta sanar da su Fareeda, har ma can dangin Hilal sun soma ƙananan magana. Babansa ne ya tsawatar da abin ya kuma ce kar ya ƙara ji.

Mamar Hilal da kannensa kuwa sun soma jin tsanar Ramlat, banda Hilal na gyara wasu lamuran da kalamai, da wutar da Bilkisu ta kunnamishi a gidan ta janyo mishi fasa aure da Ramlat. Sai dai mahaifinsa mutum ne mai magana ɗaya, yanda ya dage akan ba wanda ya isa ya hanashi aurawa Hilal abinda yake so, hakan ya kashe bakin kowa sai ƙananun magana da ba'a rasawa wurin mata.

"Ina wuni Anti Bilki."

Ta gaisheta ciki-ciki don yanzu ba wani mutunci suke ba.

"Lafiya kalau Laila ta Majnun."

Sanin cewa magana ta yaɓamata ne yasa ba ta ce komai ba.

  "Ni na rasa abinda Hilal ya gani ya maƙale maki alhalin yanzu ba kya ta ta shi. Wallahi mata hudu ya so zai iya aura a lokaci guda. Amma da yardar Allah ko ya aureki sai mun mishi aure."

Cewar Anti Bilki tana mai kwantar da Yasmin a saman  tana jijjigata don ta yi bacci. Ramlat dake shirin tayar da sallah ta dubeta rai a ɓace.

"To ko hakan za'a yi? Ki tambayeshi wanda ya nacewa wani tsakanin ni da shi. Nace bana so, bana yi, wai dole ne?"

Ta ja tsaki ta fice daga dakin zuwa can bayan gidan wurin ciyayi ta zauna tana aikin kuka.

Ita kuwa Bilkisu ranar wuni ma ba ta yi ba a gidan yanda ta yi niyya, ta goye diyarta ta fice ba da sanin mijin ba.

Duk borin da ta je ta tayar a gidan su Hilal game da kalaman Ramlat din, iyakar su matan kawai ta tsaya don su Jidda har da kukan takaici da tausayin yayansu. Ji suke kamar a fasa gaba daya  sai dai ba su da ta cewa tunda iyaye maza sun tsawatar.

***
Duk wani hidima da za'a yi Abba ya ce ayi kafin a daure aure, don a cewarsa ana daura auren to fa dakinta za'a miƙa ta.

  Shagulgulan koda sun yi armashi, basu yiwa Ramlat ba. Baƙin komai take gani. Dinnerparty Hilal yace ya fasa ganin irin shirin da ƴan uwansa ke yi na gasawa Ramlat magana a ranar.

  "Shirun Ramlat na nufin abubuwa da dama."

Fadin Hajiya bayan daurin aure, a sadda Zulaihat ta bi ta sashin Abba don amsar laffayar da Ramlat din za ta sanya.

"Nima nayi mamakin yanda ta kwantar da kai ake bikin lafiya ba kamar yanda na zata ba. Amma ko ma mene ita ta sani. Mijinta ne yanzu, idan ma ta wulakantashi ita za ta kai kanta wuta."

Cewar Zulaihat cikin halin ko in kula.

"Uwani kenan, ku dai dinga zagayawa kuna yi mata faɗa. Ta dauki duniya da zafi, ta sauke."

Ba ta son ma zancen, don haka ta sungumi karamin akwatin da aka zuba kayan da duk Ramlat din za ta yi amfani da shi a ranar farko bayan kai ta gidan kafin a kawomata sauran akwatin, ta fice daga falon.

Hajiya sai ta tsinci kanta da kasa fita wurin yan uwanta, ta zauna ta yi shiru cikin tunanin meke tafiya a zuciyar yarinyarnata.

"Allah Yasa dagaske kike Ramlatu."

Ta furta cikin faduwar gaba kafin ta yunkura ta mike ta fita.

***
  Dogon hijabi ta sanya a saman leshin da ke jikinta. Ga kunshi da kitso an mata. Kwalliyar fuskar ta kara fiddo kyawunta sosai.

"Ina zuwa?" Cewar wata Hannatu ƴar Gwaggonsu Sa'adu ta Daura.

Murmushi ta ɗan yi.

"Yanzu zan dawo."

"Ki sauri don Allah, yanzu za'a zo nemanki tunda an yi magriba."

Ta ja guntun tsaki ta fice. Allah Ya taimaketa har ta fice ba ta hadu da su Zulaihat ba.

"Malam Hassan. Malam Hassan."

Ya fito daga dakin gugar. (Daki karami a gidan inda Malam Hassan ke musu gugan kaya)

"Na'am."

Ta ɗan waiga sai kuma ta yi shiru sanadin wasu da suka zo wucewa. Ta kauda fuska har suka fita. Cikin sauri ta dubeshi.

"Ya ake ciki?"

Cikin rashin gaskiya ya kalli jama'a kafin ya ba ta amsa.

"Bayan gidan na ajiye, na tabbatarmaki ba wanda zai kawo komai don kusa da inji ne."

Ta yi murmushi.

"Nagode." Daga nan ta daga zani ta fiddo kudi masu yawa kulle a leda ta mikamasa.

"Abinda kake zargi ba shi zai faru ba kamar yanda na rantsemaka. Barazana ce kawai."

Ya yi murmushi ya gyada kai. Shi ko mene ba damuwarsa ba ce tunda ya ji dumus. Hankali kwance ta koma ciki, suka yi kiciɓus da Zulaihat.

"Ina kika je?"

Ta yi murmushi.

"Shikenan kuma ba damar na yawata a cikin gidanmu?"

"Nan da awa kadan za ki bar gidan zuwa gidanki kema."

Fadin wata abokiyar wasansu Asabe. Aka yi dariya, ita kuwa ta shige don kaucewa kaifafan idanun Zulaihat din dake kanta, kallon rashin yarda tsantsa take mata.

***
Aka kammala shirin kai ta gidan miji, Abba ya ce aje zai je har gidan washegari ya yi nashi fadan. Hajiya kuwa ta ce wanda yayyunta da gwaggonni suka yi ya wadatar.

"Saura ku yafemata."

Cewar Dije abokiyar zaman Hajja. Daga Abba har Hajiya suka ce sun yafemata duniya da lahira.
Tana kuka aka tafi da ita gidan Hilal. Gidan da ta ke mishi kallon wuta.

  Aka watse aka bar ta, jikin Amrah a sanyaye, ta kara juyowa ta dubeta da lulluɓin har lokacin. Dawowa baya ta yi tana hawaye ta lalubo hannunta ta rike.

  "Na sanki Ramlat, ba ki fiye cire abu a ranki da wuri ba. Na sanki kamar yunwar cikina. Kiji tsoron Allah. Ki ji tsoron Allah."

A hankali ta ji Ramlat ta zare  hannunta daga nata.

"Amrah muje, suna jiranmu."

Fadin Maryam da ta leƙo. Amrah ta mike tana kallon Ramlat, kafin kuma a sanyaye ta juya ta fita bisa gargadin Abba da ya ce ba ya son abar mutum ko daya da zummar wani siyan baki.

Kamar jira ta ke sahu ya dauke, kamar jira ta ke ta bar jin motsin kowa a gidan. Ta bude lulluɓin laffaya gaba daya ta fito. Babu kowa kamar yanda ta zata, ba ta damu da dukiyar da aka zuba a gidan ba, bai isheta kallo ba hakan yasa a gaggauce ta fita. Komai da sauri take yi tana kara waigen kofa har ta zagaya bayan gidan. Nan ta iske baƙar ledar da ta tabbatar shi ne saƙonta. Ta dauka ta jijjiga sannan ta murmusa. Ledar ta cire ta dauki sakon zuwa ciki. Ta adana a karkashin gadon ta zauna.

  "Komai zai zo karshe a yau, daga yanzun ba wanda zai kara tadamin hankali akan Hilal. Babu shi!"

Ta furta a fili, ƙarar bude gate da ta ji ne ya sanya ta warware ɗankwali da yin wurgi da ribbons dinta a gefe. Idanunta kuwa dama kallo ɗaya za ka yi mata ka gane irin kukan da ta ci.

"Yau ko ni! Ko kai Hilal!"

Ta ƙara fadi.I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/iRW2CA35T9



🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login