Showing 123001 words to 126000 words out of 230725 words
tafi."
Hussein dai abin ya dauremishi kai, zai yi musu abin mamaki Hajiya ke roƙonsa ya bar kowace magana a gefe su wuce su koma gida. Ba ta da lafiya. Dole ya shiga motar bisa umarninta itama ta shige. Ba ta samu nutsuwa ba sai da ya doshi gate, sai dai kafin ya kai ga fita jikinsa kawai ya yi wani irin la'asar yayinda ya ji kirjinsa na dukan uku-uku, ya kalli bayansa ta mirror. Bai ga kowa ba face wani matashin da ba zai fi shi a shekaru ba, tsaye jikin mota ya juyamusu baya yana amsa waya.
"Ya kake tafiya kamar ba ka so? Ka yi sauri don Allah."
Maganar Hajiya ta dawo da shi nutsuwarsa, ya ɗan ƙara ƙarfin gudun.
"Wai meke faruwa? Naga lafiya muka shigo wajennan."
Girgiza kai ta yi tana share gumi.
"Nima dai ban sani ba. Watakila plantain da kwai da na ci ne ya ɗan juyamin ciki."
"Kuma kika ce jiri?"
Ta ja guntun tsaki ganin zai ƙureta, ita dai yanzu ta fi kaunar a kyaleta tayi tunani mai kyau. Wannan ya nuna twin brother din Hussein ya zo Kano kenan? Lallai dole ne ta hana Hussein zirga-zirga. A farin farko dai za ta bincika ta ji dalilin zuwansa, idan har zama ne na dindindin, barin Kano na har abada ya gansu ita da mijinta koda ba ya so. Haka ta yi ta tufka da warwara, Allah-Allah take su isa yanda za ta samu damar yin tunani mai kyau.
Shi kuwa AlHassan koda ya gaji da gaisuwar da wasu daidaikun ma'aikatan masu wucewa suke mishi sai kawai ya shige cikin motarsa ya zauna ya ci gaba da wayar. Har su Hafsat suka fito ɗauke da ledoji yana waya. Hayaniya kwakkwara hanasu ya yi, kusan har ya soma tuƙi suka yi tafiyar mintoci yana waya. Can dai ya katse ya ajiye, da murmushi ya dubesu.
"Sorry, ban kyauta muku ba ko?"
Fatima ta turo baki ta gyaɗa kai. Dariya ta basu.
***
"Hajiya Ramlatu, ina son ganinki."
Shi ne abinda ya ce kenan bayan ta saka wayar a kunne. Ramlat ta ajiye kan wayar ranta na zafi, tsabar raunin hankalin Chairman ya soma isarta, tana kallon abin kamar da biyu yake yi.
Ta mike ta gyara zaman naɗin laffayarta ta tabbatar ko'ina na jikinta ya ƙara rufuwa ruf sannan ta ƙarasa ciki.
Kallon haramun dai bai fasa ba don haka ta daure fuska.
"Gani Yallaɓai."
Ta faɗi a ladabce cikin basarwa don yanzu ta bar ganin ƙima da mutuncinsa.
"Amm..yanzu a kan aiki muke don haka ba zan ce komai ba. Sai dai idan ba damuwa ko za'a yimin iznin zuwa gida?"
'Anzo wurin.' Ta fadi a ƙasan ranta. Girgiza kai ta yi.
"Ka yi hakuri Yallaɓai..."
"A'a kinga Ramlat, ba batun nayi hakuri bane. Tsakani da Allah ba zan iya ba. Na fadamaki yanzun muna bakin aiki ne, magana ce kuma zan zo muyi ta fahimta."
Shiru kawai ta yi, ganin ta ƙi ce mishi uffan ne ya sa shi magana.
"Zan ba ki daga nan zuwa Monday, please ki yi tunani mai kyau. Ki sani, koda ace a baya sharri ne a zuciyata, yanzun babu ɗigon wannan Ramlatu. Wallahi babu."
Yanda yake magana kamar wani yaro sai ma ya so ba to dariya, ita dai ba ta ce komai ba.
"Shikenan kina iya tafiya."
Ta juya ta fice ba ta ce mishi uffan ba, Chairman ya bita da kallo kafin ya lumshe idanunsa ya sauke ajiyar zuciya. Sanin gidansu Ramlat abu ne mai sauƙi a wurinsa, sai dai ya fi kaunar bi ta hanyarta ko don ya goge wannan kallon girma ya faɗin da ta ke yawan jifansa da shi. Ko ba komai dai da gaskiyarta. Da niyyar cuta ya zo sai soyayyarta na gasken ya sauya komai.
***
I just published "BABI NA TALATIN DA BAKWAI" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/4aFXFyDdjbb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
37)
LAMIƊO CRESCENT
"Ki soma faɗamin wannan ƙullen da kike yimin na mene wai? Ina da aikin yi, kin hana ni fita."
Hussein ke maganar a tausashe da ɓacin rai saman fuskarsa. Zeenatu dubansa take yi don ta rasa ma hanyar ɓullo mishi. Ba ta son fitarsa, jinta take kamar wata zararriya, gaba daya babu aikinta ɗaya da ya tafi daidai. A baya ta rantse ba za ta bar garin Kano ba amma kam a yanzun a shirya ta ke da yin nesa da duk abinda zai sa Hussein ya suɓucemata.
"Tafiya zamu yi, Kano nake son mu bari."
Kallonta kawai yake yi cike da tunanin meke damunta har haka. Dariya ta so kwacemasa don shi kansa yana mamakin irin ƙwarin gwuiwar da ya ke samu na yi mata jayayya akan duk abinda ya zartar a yanzun.
"Kinsan me kika ce kuwa?" Ya fadi kansa tsaye yana kallonta har sai da ta ji ƙirjinta ya bada dam! Dakyar ta haɗiyi yawu.
"Me kake son ka ce? Jayayya za ka yi da ni? Ba za ki bi ra'ayina ba?"
Ya yi shiru kawai yana kallonta da wani mamaki, wani tsana yake ji kamar yana son tasomishi sai wata soyayya da bai san mafarinta ba ta zo ta danne wannan tsanar. Kauda kai ya yi gami da miƙewa daga saman gadon.
"Kiyi hakuri, abu ne da ba zan iyaba."
Daga haka ya faɗa banɗaki. A gigice Hajiya Zeenat ta miƙe ta fice zuwa ɗakinta. Wanka ta yi a gurguje ta shirya. Kamar yanda ta zata hakan ce, ya shirya da zummar zuwa ofis. Bai yi mamakin shirin da ta yi ba illa murmushi da ya yi, abin kam ya ba shi dariya. Wannan bibiyar bai san kuma ta mece ce ba duk da a bayan ma tana yi mishi don wani sa'in kamar daga sama haka yake ganinta a ma'aikatarsu.
Ya shirya suka fita tare, ita ke tuƙi don a cewarta za ta fita daga nan duba Hajiya Batool ba lafiya, bai damu da gasken take ko a'a ba. Ya dai amsa zuciyarsa a ɓace.
***
Tuƙinta cikin nutsuwa take yi, yau gaba daya ta makara a dalilin zazzaɓin da ya kama Ansar sai da ta kai shi asibiti tukunna ta maida shi gida. Ta so ta ƙi zuwa sai dai hakanan ta daure tunawa da aikin duba wasu files na Tax.
A harabar wurin parking ta ajiye motar ta ƙarasa ciki. Ko zama ba ta kai ga yi ba wayar dake saman tebur ta ɗau ƙara, tsuke fuska ta yi gami da jan tsaki ciki-ciki. Tun sadda suka yi haka da Chairman ta ƙi jinin abinda zai sa ta haɗu da shi sai dai ba yana ta iya. Wayar ta ɗaga da sallama, ya amsa gami da ba ta umarnin ta je. Dire wayar ta yi ta ajiye jakarta ta fita bayan ta gyara zaman hijabinta.
Yana zaune da manyan kaya har da babbar riga, idanunsa sanye da gilashi yana danna laptop. Shigowarta yasa shi kallonta.
'Ban yafe ba.' Ta furta a ƙasan ranta. A fili kuwa gaidashi ta yi a ladabce, ya amsa yana wani washe haƙora. Bayan gama jin dalilin da yasa ba ta shigo da wuri ba ya gangara kan abinda ke cin ransa. Chairman ke kiran yana sonta, dama tuni ta riga ta gane.
"Ke ba yarinya ce karama ba, nasan kinsan me nake nufi kike kaucemin. Wallahi na gaji, bani da burin da ya wuce na aurenki a yanzu Ramlat. Don Allah kar ki ce za ki ƙi. Na miki alƙawarin gidanki daban, ba zan haɗaki da matana ba."
Ya kammala surutansa tana sauraro, ƙarshe ta soma da ba shi hakuri.
"Inada wanda zan aura don har anyi magana."
Wata dariya ya kece da ita, hatta ita Ramlat sai ta ji maganar nata banbarakwai, ta kara hade fuska.
"Haba Hajiya Ramlatu, yanzu fa na gama fadamaki ke ba yarinya ba ce. Wane sokon ne zai yi gangancin tsallake sati biyu ba'a ɗauka muku aure ba? A'a ban yarda ba gaskiya. Nidai ki karɓi ƙoƙon barata ki ba address da kanki a ganina zai fi mana mutunci."
Ta yi shiru, ya ci gaba da magiya kamar ba Chairman mai cin magani a gaban staffs ba, haka ba don ranta ya so ba ta mishi kwatance. Ranar kowa ya kalleshi yasan yana cikin farin ciki marar misaltuwa.
Koda aka tashi, kai tsaye tsohon department din da take ta ziyarta. Ta kuwa ci sa'a duk suna ciki, aka gaisa ba ta ko bi ta kan Halima mai amsa gaisuwar ciki-ciki ba.
"Yanzun nake shirin shiga wurinki. Ƴar halak kin ƙi ambato."
Ta kai duba ga Naja'atu Azare mai wannan batu, suka yi dariya. Takardar gayyatar biki ta fiddo daga jakarta ta miƙa mata. Murmushi sosai Ramlat ke yi har fararen haƙoranta na bayyana.
"Kai na ji dadi sosai wallahi, ki ce abun ya zo. Allah Ya nunamana, Yasa muna raye." Aka amsa da Amin.
Hira ta tsaya yi a karshe suka dunguma gaba daya matan suka fita, Halima har lokacin fuskarnan ba fara'a.
"Wai ke me akai miki kike ta cin magani?"
Saudat ke tambayar tana dubanta.
"Ba komai, sai Allah Ya kaimu."
Daga nan ta yi gaba ta bar su.
"Wai nikam Ramlat kamar dai akwai wata a ƙasa tsakaninku da Halima, na lura duk sadda kike wuri ba ta fiye kaunar hakan ba." Samira ke wannan maganar tana duban Ramlat. Ita kam murmushi kawai ta yi, tana ji suna faɗin rashin kyautatawar Halima a lokuta da dama ita dai ta musu sallama ta nufi inda ta yi parking. Idan da sabo ya ci ace dama ta saba da halinta. Murmushi ta yi da wani bahagon tunanin da saƙe-saƙen zuciya ke jefawa ɗan adam ya ziyarceta, wato ace ta yarda da auren Chairman, Allah Kadai Yasan irin kiyayyar da za ta fuskanta daga Halima. Ba ma daga gareta kawai ba, har da yawa cikin matan wajen.
***
Zaune gaban Boka Gora, Hajiya Zeenatu ce da Hajiya Batool kowannensu rai a ɓace.
"Shekaru sama da goma muna tare da kai, kar ka yi mana haka. Ka taimakemu ka kula da damuwarmu. Bamu da wanda muke da shi da zai share hawayenmu face kai." (Wa'i'yazubillah)
Gora ya yi wata dariya ta shaiɗanun da suka riƙa kafin ya ɗaure fuska tamau. Ya kwalalo musu manyan idanuwansa da suka sha kwalli.
"Kar ku rainamin hankali! Wa ya fadamaku zan kasa sanin kun yi doguwar tafiya har wata ƙasa don a yi muku asiri? Cin amanar da zai biyo bayan dukkan taimakon da na yi muku a baya kenan! Yanzun da ku ka zo me kuke so nayi bayan komai ya warware! Komai ya lalace! Ke Zeenatu! Ki fara tattara kayanki ki bar ƙasarnan don asirinki ba zai je ko'ina ba sai tonu! Ita dai yarinyar da na gargaɗeki a kanta, ita ce silar rushewar dukkan ayyukanki! Ke kuma Batulu! Nan ba da jimawa ba, ɗanki zai zo da batun ƙarin aure! Auren da zai rushe duk wani asiri da kika yi tsakaninsa da matarsa! Anan ne duk abinda kika binne zai fito fili muraran!"
"Ƙarya kake! Wallahi ƙarya kake! Dama na faɗamaki kar mu zo wurinsa!"
Hajiya Batool ke maganar jikinta har yana ɓari, fuskarnan wacce man bleaching ya maida jawur, sai ƙara kyalli take. Ita kuwa Hajiya Zeenatu idanun kamar an watsa barkono. Ba ta san hawaye ke fita daga idanunta ba sai da ta ji suna kokarin shigewa bakinta. Shi kuwa Gora banda wata shegiyar dariya ba abinda yake yi don ko kaɗan kalaman bai ɓatamasa ba, ya saba ganin irin wannan hauka da jahilcin na mata.
Tsawa Hajiya Zeenatu ta dakawa aminiyarta ganin gaba ɗaya ma ta ƙi maida hankali ta nutsu su nemi mafita. Ita da take da tashin hankalin rasa miji irin Hussein ba ta yi gigitar da Hajiya Batool ta yi ba. Ta sa mayafi ta sharce gumi idanunta a kansa.
"Mun tuba, wallahi mun tuba ba zamu ƙara saɓawa umarninka ba. Ka taimakemu Gora, a wannan gaɓar idan ka ce za ka bar mu, ba wanda zai tsira."
Ya ci gaba da kallon ƙasar da ke shimfiɗe gabansa yana ƴar dariya gami da gyara hannun babbar rigarsa.
"Akwai tsada..."
Bai ma kai ga ƙarasawa ba duk suka tari numfashinsa.
"Zamu biya ko nawa ne, wallahi ko duka abinda muka mallaka ne."
Ya jinjina kai, kaf ba wacce bai san halinta ba a cikinsu. Yana da karatun kowaccensu don tun ana damawa da su a siyasa da bariki yake tare da su. Maida hankali kan ƙasa ya yi can kuma ya ɗago ya dubi Hajiya Zeenatu. Yanzu da ace zai faɗi ainahin abinda ya gani, toh ya tabbatar kuɗaɗen da suka Kaɗaita masa ba zai samu ba, gwara ma Hajiya Zeenatu akwai sakin hannu, anan ne suka sha bamban da aminiyarta da ta kasance marowaciya.
"Aikinku zai yiwu, sai dai dama ai na riga da na faɗamaku akwai kashe kuɗi. Batun kuma shi mijinnaki ina tabbatar maki ba zai haɗu da ɗaya cikin ƴan uwansa ba. Sai dai kuma ki kara kiyayewa ga barin kowace mace shiga rayuwarsa. Idan na ce kowacce, ina nufin hakan!"
Ya fadi kai tsaye, kusan bayanai biyun ƙarshe da ya yi sun kasance abinda ya hanga ɗin.
Jinjina kai Hajiya Zeenatu ta yi, nan kuma Gora ya shiga lissafomata abinda za'a siya. Da ta gaji ta bude jaka ta fiddo bandirin ɗari biyar sabbi har biyu ta ajiye a gaban buzunsa.
"Gashinan, na bar maka wuƙa da nama, duk abinda ya kamata nidai a yimin don Allah. Sannan idan da hali a yiwa ita yarinyar turen aljanu su zama silar ajalinta. Nidai ko haukatamin ita ne don Allah a yi Gora."
Wani murmushi Gora ya yi ya sa hannu ya dauki kudin gami da faɗin.
"An gama! Kedai kawai ki sha kuruminki."
Daga haka ya juya ga Hajiya Batool wacce ganin irin yanda ya kwantar da hankalin Hajiya Zeenatu da bayanan gamsuwa da kuma karfafa gwuiwa, itama sai ta ji nata ya kwanta. Nan ya shiga kora mata karya da gaskiya itama ta hau ta zauna ta cikashi da kudin. Kafin dai a bar gidan Gora an shirya, dariya ake yi har yana neman su ba shi haɗin kai yanda suka saba.
"Alƙawari ne mun yi maka, zamu cika mu ziyarceka da zarar aiki ya kammalu." Cewar Hajiya Zeenatu da take ji kamar an mata albishir da mutuwar ɗan uwan Hussein.
Wata dariya suka yi tare kafin su fice. Sai a sannan hankulansu ya kwanta.
***
BAYAN KWANA UKU.
Tun wuraren biyu na rana ta samu kira daga Alhassan (wanda tuni ta sauya mishi suna daga mutumin mall zuwa Alhassan kamar yanda ta ga username ɗinsa a WhatsApp). Sanarmata da batun zuwansu da iyalinsa ya yi, wannan tasa bata zauna ba, ita da Hajiya da Ladidi suka shiga kicin don yin kayan maƙulashen tarbar baƙi. Suna tsaka da aikin sai ga Zulaihat da Rafee'ah, mamakin irin wannan garar da ake shiryawa ta kamasu.
"Baƙi za ku yi ne Hajiya?" Cewar Zulaihat tana duban kajin da Ramlat ke soyawa.
"Au, ashe mu ba zamu ci daɗi ba kenan sai zamu yi baƙi?"
Dariya ta basu.
"A'a, amma dagaske naga kayan ne da yawa har da su zoɓo da ginger. Duk na waye?"
Murmushi Hajiya ta yi.
"Ku tambayi ƙanwarku."
Ramlat ta sanarmusu batun zuwan Alhassan wanda suka taɓa jin ta yi waya da su. Rafee'ah ta kama baki tana dariya.
"Ah lallai, ki ce surukinmu ne zai iso. Kai abu ya yi kyau."
Yamutse fuska kawai ta yi kafin ta murmusa, ita dariya ma suke ba ta idan suna haɗa ta da AlHassan. Ko za ta kwana ta na faɗamusu zumunci ne kawai tsakaninsu ba yarda zasu yi ba don haka ta ja bakinta kawai. Hajiya da su Zulaihat suka koma falo, itama tana kammala suyar ta haɗa chicken pepper dinta ta zuba yanda ya kamata, da taimakon Ladidi suka kwashi kayan zuwa saman tebur. Lemukan suka sanya a firij. Tana zama a falon ba jimawa, wani tunani ya faɗomata a rai, cikin sauri ta mike zuwa ɗaki. Wayarta dake hannun Ansar wanda ke kwance yana buga game ta karɓa haɗi da faɗin.
"Kaima Monday ta zo ba zama za ka yi ba sai ka je makaranta tunda ka warke."
Ya hau tura baki.
"Tashi ka je ga su Maman Twins da Anti Rafee.."
Ba ta kai aya ba, da murnarsa ya dira ƙasa ya fice. Murmushi ta yi kawai. Abinda ya shigo da ita ta tuna hakan yasa ta saurin kiran Hisham.
Bayan sun gaisa ya gama jan ta da tsokana yanda ya saba sannan ta samu damar magana.
"Idan ba damuwa don Allah ka shigo gidanmu kamar wuraren biyar haka."
"Toh Antinmu, ina fatan dai ba ƙarata Princess ta kawo ba? Dagaske sharri take min."
Murmushi Ramlat ta yi, Hisham ba ya rabo da zolaya.
"Ni ba haka nace ba, abu ne mai muhimmanci akan abokinka, sai dai duk abinda za ka gani kar ka yi magana. Please."
"Shikenan, kar ki damu, In sha Allah zan shigo."
Daga nan suka yi sallama ta faɗa wanka. Koda ta fito, ba kwalliya ta yi ba sai dai ta gyara fuskarta ta shafa hoda da man leɓe. Ko ba komai baƙinta ne. Ta shirya ta fito falon daidai sadda su Ummi suka dawo daga makaranta. Dakyar Ramlat ta korasu islamiyya har Ansar don a farko ganin iyayennasu sun so su ƙi zuwa.
Sai a sannan su Rafee'ah masu kwasar garar abinci suka yi wa Ramlat kallon tsaf ganin yanda ta sh sutura mai kyau. Ramlat ta yamutse fuska kadan.
"Ku faɗa kawai, abinda ku ke nufi ba shi bane."
Dariya suka yi.
"Kin ji yarinya da tsarguwa."
Fadin Zulaihat tana duban Rafee'ah. Taɓe baki Rafee'ah ta yi, ita me za ta ce? Ta dai lura Ramlat ba ta kaunar maganar aure don haka a yanzu nata mujiya. Aka bar zancen aka faɗa labarin gidan Yaya Munir wanda a yanzu don kansa ya zo ya samu Hajiya ya rantse rabawa matansa gida zai yi. Wannan kalami ya sa su dariya musamman Zulaihat abokiyar takun saƙarsa.
"Maganinsa! Tun farko nan ba na nunamasa hakan zai fiyemishi ba amma ya nunan shi din gwani ne. Kuma adali."
"Toh dai yanzu ko mene ai shikenan tunda ya riga da ya faru." Faɗin Hajiya kenan.
Haka suka yi ta hira kafin a kira la'asar duk su mike don ɗauro alwala. Wurare karfe hudu da rabi sai ga wayar Alhassan, nan ta ƙara yi mishi kwatance, a