Showing 102001 words to 105000 words out of 230725 words
za ki kwantar da hankalinki yanda ya kamata."
Sai a sannan ta yi dariya sosai, ranta kuma ya koma ƙal kamar takarda.
"Na ci wuya kafin na cimma dukkan buri a kan Hussein, kema kin san da haka ai. Huum, sai yanzu rana tsaka bayan na gama sanin wa nake tare da shi, wata banza ta zo ta tadamin hankali. Anya kuwa ma dagaske Gora yake? Ni dama tun sadda naga ya hau canki-canka da matsalar da ta kawo wata budurwa, na shiga shakku a kansa."
"Toh ba na fadamaki ba, yanzu haka kawai kudinmu ya ci. Akwai irinsa da yawa ai, ba tsoron Allah su zalunci mutane su damfaresu." Fadin Hajiya Batool har da yamutse fuskarta mai kama da kashi. Ta mance su kansu ba tsoron Allahn suka sa gaba ba.
***
Washegari kuwa da sassafe sai ga wani tsamurmurin buzu mai jin Hausa raɗau ya zo Hotel din da suka sauka. Shi ya yi musu jagora har wurin Isuhu Bakka Tsoron Allah. Layi sosai suka tarar amma kasancewar ɗan rakiyar ba baƙonsa ne mutumin ba, yasa ya basu umarnin su jira sannan ya shiga ciki. Can ya fito ya musu umarnin su taso.
A bakin kofa suka tsaya suna ji mazauna wurin wadanda mafi yawansu mata me, su na zaginsu da yaren kala-kala, Hajiya Zeenatu da Hajiya Batool suka kalli juna don abin ma dariya ya basu.
"Wai fa harara a duhu." Fadin Hajiya Batool.
Wacce ke ciki na fitowa suka faɗa ɗakin bisa jagorancin ɗan rakiyarsu.
Wani ƙaton mutum ne fatarsa har wani ja ta ke yi, yana zaune saman wata ƙaton carpet gefensa kayan tsubbu ne kala-kala, ya naɗe fuskarsa da farin naɗi sai kayan jikinsa baƙaƙe. Kallo ɗaya za ka yi mishi ka san buzun ne na gasken gaske.
Suka gaidashi sai dai yarensu ma ba ji yake ba, ɗan rakiyar ya juya harshe ya shiga nanata abinda suke faɗa. Tun da ya soma bai katseshi ba kansa kawai yake gyaɗawa gami da yi musu kallon ƙurillah. Can ya watsa tambayar wacece a cikinsu. Saurayin ya nuna Hajiya Zeenatu ganin ita ke koro jawabin. Ya yi mata kallon tsaf sannan ya maida kai ga ƙasar dake shimfiɗe gabansa. Tambayar sunan mijinnata ya yi da kuma ita kanta.
Bayan an faɗamasa ya ci gaba da zanensa a kan ƙasa can ya ɗago ya dubi saurayin yana murmushi yana jawabi, sai da ya gama tsaf sannan saurayin ya dubesu, dama duk sun matsu su ji abinda ke faruwa.
"Cewa ya yi, ya ga ma mijinnaki saurayi ne, kuma ƴan biyu ne. Shi kansa ƴan uwansa basu zauna ba, suna ci gaba da nemansa sannan sun tashi tsaye da addu'a irin wanda sai an yi dagaske. Ya kuma ce akwai mace ɗaya da babu makawa sai ya aureta koda za'a shekara goma ne, rubutacce ne. Ita ce za ta rushe dukkan wani gini da kika yi. Ai ya ce ya gani, ba wurinsa kika soma zuwa ba, kafin zuwanki nan, akwai wanda ya yi maki aiki."
Hanjin cikin Hajiya Zeenatu suka ƙulle, iskar fankar dake kaɗawa bai hana gumi ya tsastsafomata daga goshinta ba. Ta haɗiyi miyau, ta dubi Isuhu don bilhakki fargaba da tsananin kishi ya mantar da ita ba ya jin yarensu.
"Ya kammanin yarinyar yake?"
Saurayin ya faɗamasa. Girgiza kai ya yi gami da yin yare. Duk suka zubawa saurayin idanu suna jiran jawabi.
"Ya ce ba zai ce ga kamannin ba, amma yanzun haka sun haɗu da juna."
Ta haɗiyi miyau hankalinta a matukar tashe, idanunta har hangomata Yarinyar kwance jikin Hussein yake. Dagaske dai Gora ba ƙarya ya faɗamusu ba. Nan da nan idanunta suka kaɗa har da ƴar kwallarta.
"Don Allah Malam ka taimakamin, wallahi ba zan iya haɗa Hussein da kowace ɗiya ba. Idan har Hussein ya rayu da wata mace koda ta hanyar fasiƙanci ne zan iya mutuwa wallahi. Nidai ko kasheta ne a yi kawai na huta. Idan har mutuwarta zai sauyamin kaddarata shikenan. Ko nawa ne zan biyaka wallahi."
Tana kaiwa nan, saurayin ya faɗamishi. Ya yi shiru yana ci gaba da bugun ƙasarsa kafin ya ɗago ya yi jawabi.
"Abu ɗaya ya ce za'a iya, shima yana da matuƙar wahala, bai kuma yi miki alƙawarin lallai ne ya yiwu ba. Idan har za ki iya ku bar garin da ku ke yanzu zuwa wani. Ya kasance komai naku ya sauya daga wannan garin don yana da tabbacin koma wace ce a garin ta ke. Amma kuma ya ce zai wahala shi mijinnaki ya amince da hakan. Sannan yana mai ba ki shawara da kar ki yi wasa da abinda zai ba ki na mallaka, muddin kika yi sake ƴan uwansa na dab da sanin inda yake. Bayyanuwarsa garesu kuwa daidai yake da rushewar duk wani tubalin da ki ka gina."
Hajiya Zeenatu ba baka sai kunni, gyada kai kawai ta ke. Ai ko bangon duniya ne za ta iya zuwa muddin mijinnata ba zai suɓucemata ba. Sai dai dagasken itama ta sani, abu mawuyaci ne ya amince da barin garin Kano.
"Naji, zan kiyaye ko menene. Zan bi dukkan tsarinsa."
Isuhu ya gyada kai cike da gamsuwa bayan ya ji bayanin daga bakin saurayin. Miƙewa ya yi ya shige ƙuryar ɗaki.
"Hajiya Zeenatu, ki ce gwara da muka zo?"
"Uhum, bari Hajiya Batool, gaba daya cikina ma ya kaɗa wallahi kamar na saki a wando. Jikina yana bani cewa wannan tsinanniyar yarinyar ce da ke bibiyarmu kamar mayya. Ai ko birnin Sin ya ce na koma zan koma balle kuma na bar garin. Naji na yarda zan damƙa amanar dukiyata ga Manaja, idan ya so ko mene ni din sai na dinga zuwa Kanon. Ba zan zauna a yimin sakiyar da ba ruwa ba. Shekara nawa ina yawon kashe kuɗi da fashi a maƙabartu akan Hussein? Ko wacece ta yi kaɗan."
Ta ƙarashe a kausashe. Hajiya Batool ta shiga jinjina kai.
"Nima ban yarda da ki zauna ki zuba ido komai ya lalace ba. Bari ya fito na shigar da nawa ƙoƙon barar akan wannan shegiyar surukartawa da ke neman mallakemin ɗa. Haba, komai yanzu nashi ƙarewa yake yi a wajenta?"
Hajiya Zeenatu dai ba amsa, kowa ya ji da nashi matsalar.
Ba jimawa ya dawo dauke da wasu jarkoki biyu na ruwan magani sai wata leda. Tiryan-tiryan ya yi bayani. Ɗan rakiyarsu ya kallesu.
"Wannan jarkar ya ce tsakar dare za ki tashi daidai sadda hasken farin wata ya fito, za ki fita tsakar gida tsirara ki yi wanka da shi har na kwana uku. Shi kuwa wannan ɗayan, tsarki za ki yi da shi ki yiwa Mijinki girki da shi har na tsawon sati daya ya ci. Sai wannan ƙullin maganin, ki tabbata kin sanya cikin turare irin mai maiƙonnan, ki dinga shafawa duk sadda mu'amala da ta haɗaki da shi. Shi kuwa wannan layar, a tsakiyar bola za ki binneta ba tare da kowa ya ganki ba, wannan layar shi zai sa ki mallaki mijinki yanda ko uwarsa ba ta isa ta ganshi ta ce ya biyota ya je ba. Shi kuwa abincin da za ki girka masa, shi zai mantar da shi yarinyar muddin ku ka bar garin, ba kuma zai ƙara tunawa da ita ba balle har ya ji yana son zuwa ya ganta. Kinga kenan babu damar da zai ƙara sanyata a ido, idan ya sanyata a ido toh komai zai rushe."
Tunda Hajiya Zeenatu ta ke, ba'a taɓa yi mata bayani kan aikinta ba ta ji ɗigon farin ciki ba sai a wannan karon. Gaba daya jinta take kamar wacce aka ɗaure da jijiyoyin jikinta, ta kasa kwakkwaran motsi banda kai da ta gyaɗa, shima sai da Hajiya Batool ta taɓota. Hawa saman bola ta binne ba matsalarta ba ce, ta shiga makabarta ma ta kwaƙule ido akan abin duniya wannan ba ta ɗaukeshi wani abu mai wuya ba. Tsakar dare ne ta tabbatar ba wanda zai iya ganinta kan bola, za ta iya wannan. Abu mafi ciwo mai sanyamata ta ji ta tsani kowace ɗiya mace, bai wuce na zuciyar Hussein da wata za ta mallaka ba. Wannan ya fi komai yi mata zafi. Gani take kamar ta hakura da sauya garin ta zauna ta bibiyeshi har ta yi tozali da yarinyar ta cakamata wuƙa a maƙoshi.
Murmushi ta yi, sai lokacin ta samu sukuni, sai a sannan ta samu mafitar da a ganinta ya fi na wannan Malamin. Koda ba ita ba, za ta sanya a kashemata ita yanda wata ma ba za ta ƙara sha'awar shiga rayuwar Hussein ba.
Har Hajiya Batool ta gama shigar da nata koken aka ba ta magunguna, Hajiya Zeenatu ba ta san anyi ba don ta tafi tunanin yanda za ta kashe baƙar dagar da ke shirin ruguza gininta.
Isuhu kallon Hajiya Zeenatu kawai yake yana nazari, a ido ma karantar mutum yake balle kuma ga ya buga ƙasa. A jikinsa yake jin ba za ta aikata yanda ya ce ba sai abinda zuciyarta ta saƙa mata. Murmushi kawai ya yi don ya ga irinsu da yawa. Ya kuma tabbatar za ta yi kukan nadama, da ƙafarta za ta dawo wajensa ta nemi wani taimakon, a lokacin ne zai nunamata iyakarta.
Suka kammala suka biya maƙudan kuɗi kafin su mike su fito, saurayin shi ya kai musu har mota sannan ya wuce da su gidan ƙawar Hajiya Batool, Hajja Mari (Maryam). Kasuwanci ne ya soma ƙulla ƙawancensu, saurayin yaronta ne yardajje mai mata ire-iren aikinnan. Ita ta haɗasu da shi don su je ayi musu komai.
Hajja Mari ta shiryamusu lafiyayyen abinci iri-iri, a karshe ta kara jaddadamusu kada su yi wasa da aikin Isuhu Bakka Tsoron Allah (Ba ka tsoron Allah) don shi ɗin aikinsa kamar yankan wuƙa ne. Duk wannan bai sa Hajiya Zeenatu ta sauya ƙudurinta ba.
Sun sha hira sosai a gidan Hajja Mari kafin su yi mata sallama saurayin ya maida su masaukinsu da zummar washegari zai zo ya kai su tasha su hau mota zuwa Maraɗi, anan ne kuma direban Hajiya Batool zai zo ya iskesu su wuce Kano.
***
ADAMAWA
Kusan a hargitse ya shigo gidan, Dada ya soma cin karo da ita zaune saman kujera tana faman haɗa zufa. Ya karasa da sauri ya zauna daga shi sai doguwar jallabiya.
"Dada lafiya? Meyafaru?" Ya yi tambayar yana dubanta da kulawa. Girgiza kai ta soma tana sharar hawaye.
"Mafarki nayi marar dadi akan ɗan uwanka. Jikin yana ƙara bani yana raye kuma a duk inda yake yana bukatar addu'armu."
Al-Hassan ya sauke ajiyar zuciya gami da ɗan runtse idanu ya bude cike da damuwa, ba ya son ya sanar da ita nashi kalar mafarkin kar hankalinta ya tashi, kusan shima kwanakinnan yana yawan mafarkinsa cikin wani irin yanayi.
"Kiyi hakuri Dada, addu'armu ya fi buƙata a duk inda yake. Idan ma yana rayen Allah zai amsamana roƙonmu, Zai sadamu da shi in sha Allah."
Dada ta share hawayenta ya fi a ƙirga amma kara tsiyaya suke.
"Kana ganin ina raye zan sake ganinsa?"
Da murmushi ya amsa.
"In Sha Allah Dada. Za ki ganshi."
Ta hau gyada kai. Can kuma ta ce.
"Kawunka Modibbo ya kira, ya gasamin maganganu masu zafi duk akan iyayenku, na dauka tunda basu duniyar komai ya wuce, ashe ba haka ba?"
Ya kara kallon Dada, twin sister din mahaifinsu, Aminu Gidado. Ubansu daya da Modibbo sai dai ba uwa daya ba. A dakinsu su biyu kacal uwarsu ta haifa kafin ta rasu.
A rashin Aminu da matarsa, ta riƙe Alhassan da Hussein tamkar yaranta na cikinta ko ma fiye da hakan. Don irin son da ta nunamusu ko iyayensu sai hakan. Yanda ta damu da rashin Hussein kai ka rantse ita ta durkusa ta haifeshi ba Aminu ba.
"Tunanin me ka ke yi?" Ta faɗi tana mai hankaltarsa. Ya yi murmushin yaƙe.
"Babu komai Dada."
Kafin Dada ta kara magana, wata kyakkyawar budurwa wacce kallo ɗaya za ka yi mata ka san bafulatanar ce ta gaske, siririya kuma fara tas. Hafsat kenan, Autar Dada. Hannunta dauke da Flask na ruwan zafi, ta saki baki tana kallon AlHassan, ya harareta, hararar da ta bata dariya.
"A'a me ya yi zafi? Ka zo ka rarrashi tsohuwar tamu ko? Yau tun safe ta rikicemin da koke-koke kamar wacce aka yiwa mutuwa. Ashe sai da ta kiraka ta samu sukuni." Fadin Hafsat sadda take shigowa falon sosai.
"Dada wataran sai na ɓalla ƙashin yarinyarnan kuma na dauketa na miƙa asibiti an gyara tas! Ta rainamin ke da yawa da sunan Auta, to kuwa maganinta zan yi, aure zamu yi mata."
Tuni Hafsat ta nemi dariyar da take ta rasa, nan da nan ta marairaice.
"Allah Ya huci zuciyarka Abu Fatima, don Allah ka yi hakuri."
Murmushi ya yi ganin ta yi mishi wayo, wato amfani da sunan da Kausar kadai ke kiransa da shi. Dada dai ba ta sanya baki ba sai murmushi. A karshe dakyar Hafsat ta shawo kansa ya janye ƙudurinsa. Ita a duniya ba ta da buri sai na zurfafa karatu. Wannan ne dalilin da yasa ba ta kula kowa, samarin zuri'arsu masu kawomata hari su ne suka tilastamata zaman gida ta daina shiga sabgar yan uwa gudun kar a ƙaƙabamata auren zumuncin da bai taɓa bata sha'awa ba.
Duk yanda Dada ta so AlHassan ya karya a gidan hakan ya faskara, ya lallaɓa bayan ya ga ta maido walwalarta ya yi gaba zuwa gidansa cike da damuwar rashin ɗan uwansa wanda a yanzu sosai yake ji a ransa cewa yana raye. Ba kamar a baya da yake tunanin ya mutu ba. Idan kuwa hakane, zai kara zage damtse wurin cigiyarsa.
***
KANO.
Ramlat da ƴan uwanta sun haɗu suna kallon lefen Hunainah Amaryar Muniru. Zulaihat tun soma kallo take murmushi can dai ta ɗago ta dubeshi.
"Wato dai wannan auren ko aurenka na fari ba ka saki bakin aljihu irinsa ba. Nidai ina ƙara faɗa, ka rabamusu gida wallahi don Bilkisu ba kanwar lasa ba ce."
Ya harareta.
"An fadamaki akwai macen da za ta firgitani har na kasa daukar mataki a kanta? Gida dole na haɗa su, ai idan ita Bilkisun ta ga kyautatawar da Hunainah za ta yimin shi ne da ta hankalta ta gyara."
Rafee'ah ta cafe zancen.
"Um um dai Yaya, wallahi naga irinku da yawa kuma daga karshe sai ku zo ku lashe aman da ku ka yi. Duk yanda kake tunanin mata ya wuce nan. Zama gida daya ba kwanciyar hankali."
Ya taɓe baki, ko ba komai yana cikin farin ciki ba ya neman rigima da kannennasa.
"Aikin banza kai, haka itama Hunainah ta dagemin akan lallai ba ta son zamanta da Bilkisu don kawai ta mata irin abinnan na mata, ta kirata a waya ta firgita ta da yi mata gargadin aurena. Ni kuwa a ranar hannu ne kaɗai ban ɗaga akan Bilki ba. Albarkacin su Yasmeen ta ke ci, ai na faɗamata. Ni akwai macen da za ta kawomin wargi ban yi kasa-ƙasa da ita ba?"
Ramlat ta ɗago kai ta dubeshi wani dan murmushi ya suɓucemata kafin ta maida kai ta ci gaba da jera kayan shafar da ta ciro. Yaya Munir kenan, ga dukkan alamu zai iya dukan mace idan ya so. Tana jiyemishi tsoron wani abu, sai dai ba ta furta ba don ba fata take mishi ba, ta bar wa cikinta. Amma kuma buɗar bakin Zulaihat ta ce.
"Af, wannan dai alamu sun nuna za ka iya dukan matarka. Kar dai ka zama Ali.."
Sai ta yi saurin yin shiru, har a ranta ba ta ji dadin sunan Aliyu da ya tahomata ba, ta dubi Ramlat da ko kallonta ba ta yi ba kanta a ƙasa. Rafee'ah ta yi mata ido akan ta yi shiru. Koda ma Rafee'ah ba ta fadi ba, ita mai kama bakinta ce, a kasan ranta ta roƙamasa gafarar UbangijinSa.
"Ki fita idona wallahi Zulaihat! Kar kiga kin haifi wadannan yaran masu kama da kulɓa har yanzu ba ki fi karfin na mareki ba."
Maganar Yaya Munir duk sai ya basu dariya har Ramlat din da ta haɗiye zancen Zulaihat, ko ba komai ta ga nadama a fuskar Yayarta. Zulaihat ba kanwar lasa ba, haka suka yi ta cacar baki da Munir a karshe dai fitowar Hajiya daga ɗaki suka yi shiru bayan ta tsawatar. Bai bar gidan ba sai da ya rantse Zulaihat ba za ta je kai lefe ba don cewa ya yi da ace banda Hajiyarsu, Abban yana da wata mata zai ce Zulaihat ba ɗiyar Hajiyarsu ba ce.
Haka ya gama bambamin faɗan ta rainashi ya zura takalmansa ya bar gidan.
***
Washegari aka kai lefen Hunainah, Umman Amrah ce ta jagoranci tafiyar, aka tsaida nan da sati biyu biki. Ramlat ba ta samu zuwa ba saboda aiki. Sai da ta taso kafin ta tsaya a wani katafaren wurin siyar da kayan maƙulashe na A&Z. Ba ta taɓa zuwa ba sai dai talalr wurin har a gidajen rediyo tana ji.
A duniya tana son ta ga ta faranta ran Hajiyarta da yaranta idan har tana da kuɗi a jikinta. Albarka sosai Hajiya ke sanyamata duk radda ta samu kuɗin da ta yo musu siyayyar kayan dadi suka ci. Kamar yanda ta saba, waya ta yi ta ce kar su ɗora tukunya, wannan abu ya fi komai yiwa mutan gidan daɗi. Ranta fari sol ta rufe motarta ta nufi ciki.
Da ace Ramlat na da masaniyar wurin ko mallakin wanene ko wacece, har abada ba za ta tako ƙafarta ciki ba.
Ko sakanni uku ba ta yi da shiga ba, wani al'amarin da ya kusan tarwatsamata kwanya ya afku.
I just published "BABI NA TALATIN DA BIYU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/gSzBjkXxTab
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
32)
Katafaren wurin hawa biyu ne, na farkon kayan snacks ne kala-kala, saman kuwa wurin siyar da ice-cream ne kowane irin ɗanɗano. A farfajiyar wurin kuwa kaji ne manya gashin inji ake siyarwa. Kai tsaye saman ta haye ta nufi wurin masu kula da wurin, ƴanmata da samari ne ƴan ƙarya a wajen, basu ko tsonemata ido ba, burinta ta yi abinda ya kawo ta ta bar wurin, sai dai tsayuwarta ba jimawa kamar ance ta waiga, ido huɗu suka yi da juna, daidai sadda ta fito daga wata ƙofa. Kallon mamaki da tsana ta ke yiwa Ramlat