Showing 171001 words to 174000 words out of 230725 words

Chapter 58 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1068

tsaye gami da juyowa ya kalli tsaka idanunta. Duk sai ta ji ta rikice, hanjin cikinta sun kaɗa. Ta haɗiyi miyau, Hussein zai je Adamawa?

Hannunta ya ɗan riƙe ba don ya so ba.

"Ya naga duk kin sauya? Ba kya son na je na ga ƴan uwana?"

Ta yi murmushin yaƙe.

"Ko kusa aa, amma na ji haushi da ba ka shirya tafiya da ni ba, da ace ka yi niyyar muje tare za ka sanar da ni akan lokaci."

Ya yi ɗan murmushi.

'Makira.' Ya furta can ƙasan ransa. A fili kuwa ya shafi gefen fuskarta.

"Ki yi hakuri, bansan yanda za su kalli lamarin aurenmu ba. Gwara naje na yi musu bayanin komai a tsanake cewa auren soyayya muka yi. Kinga hakan zai fi armashi."

Ta ji wani sanyi kamar kankara, tana so ta yi shakku akan zancensa sai dai kuma ta kasa. Ta shiga gasƙata dukkan kalamansa. Hussein ya ci gaba da yi mata daɗin baki har sai da ta gasƙata da kanta cewar dagasken Hussein sonta ya ke yi ba wasa a ciki. Da wannan ta ji salama amma duk da haka tana tsoron a hana shi dawowa.

"Za ka dawo garinnan kuwa?"

Ya yi murmushi ya lumshe idanu.

"Wa zan bar wa ke?"

Ya fadi ba da manufa biyu, ta ji wani sanyi har sai da ta dara cike da shauƙi. Da wannan suka kwanta bacci.

***
ƘARSHEN ALEWA..!

A ranar Talata sha biyu ga watan Maris, kotu ta yankewa Halima da Gwaska hukuncin shekaru goma zuwa sha biyar a gidan yari a dalilin yunkurin kisan kai.

Halima ta yi kukan nadama sosai, karshe ta nemi alfarma wurin ƙaninta akan ya je ya nemar mata gafarar Ramlatu. Yusufa na hawaye haka suka rabu da Yayarsa aka tsitsa ƙeyarta suka bar kotun.

A can gida, Ramlat ta ji labarin komai a waya daga Hisham, kuka sosai ta yi na tausayin Halima. Haka ta dinga samun kira daga tsofaffin abokan aikinta na ma'aikatar Revenue, da yawansu sai yanzu suka san dalilin kamen da aka yiwa Halima. Sun jajantawa Ramlat gami da yin Allah wadai da son abin duniya irin na Halima wanda ya kai ta ya baro.

"Ai godiya za ki yiwa Allah don yau kam duka ranarki ce. Ga shi dai an yankewa wadanda suka zalunceki hukunci, ga Kawunki Jamuli ya karɓi kuɗi, ya kuma tabbatarmin da kansa yau ba gobe ba, zai damƙawa Chairman kayansa. A yi ta ta ƙare. Ke kuma ya ce idan kima kara warwarewa ki je yana son ganinki.

Maimakon farin ciki sai ya ci gaba da hawaye jin kalaman Hajiya, dama tun safe ta karbi Atm card din kuma ta fice tare da Munir. Uwa daban ta ke, ita ta tsaya tsayin daka tare da Hajja wurin karɓar mata ƴanci.

Sallamarsu ce ta katse dukkan tunaninta. Suka dube su. Shaddar ba iri guda ba ce, sai dai kowannensu fari ƙal ya sanya. AlHassan da hula a kansa, yayinda gogan ya fidda nashi a mota, sai sumarsa kwance. Hajiya tun shigowarsu take murmushi da yi musu adduar neman tsari da kariya a ƙasan ranta.

Ita kuwa tun da ta kalle su ta sunkuyar da kai cikin sanyin jiki. Suka karaso suka durkusa suka gaida Hajiya ta amsa fuska a sake. Suka yi mata murnar shari'ar da ta gudana, ta ta yi ta musu addu'a sosai. Ana haka sai ga Zulaihat da Rafee'ah  suma, sun ji labarin sallama.

Suka karaso daidai sadda AlHassan ya dubi Ramlat.
"Kanwata ya jiki?"

Ta yi murmushi. Ta gaishesu. Ya amsa shi kuwa Hussein ya yi kamar bai ji ba yana kallon twins din Zulaihat.

Bayan zamansu aka kara gaisawa su na muu godiya.

"Zamu wuce Adamawa Hajiyarmu."

"To ƴaƴana, sai kuma yaushe?"

Hussein ya amsa wannan karon.

"Nan ba da jimawa ba za mu dawo in sha Allah."

Ta jinjina kai ta yi musu fatan isa lafiya. Hakanan suka kama hanya. Rafee'ah ta yiwa Ramlat ido, ba musu ta mike ta takamusu, ba laifi yanzu hannun da sauki sosai. A daidai barandar shiga dakin ta ci burki.

"Allah Ya tsare, Ya kaiku lafiya. Na gode sosai."

"Ke za mu yiwa godiya sosai. Allah Ya bar zumunci."

Ta yi murmushi.

"A gaidamin Fatina."

Ya yi murmushi.

"Za ta ji in sha Allahu."

Daga haka ya yi gaba, Hussein ya dube ta.

"Yarinyar da kika aikomin hotonta?"

Ta gyada kai tana murmushi. Sai a sannan ta ga ya yi mata murmushin shima.

"Ina kara godiya gareki. Allah Ya ba ki miji nagari. Oh, ashe kin samu. Allah Ya nunamana aurenku."

Ya karashe yana taɓe baki. Ta rasa ma me za ta ce, ya bita da wani irin kallon da ta kasa fassarawa.

"Ki kula da shan magungunanki, kada ki tsorata, likita da kansa ya rubuta da kaina na karɓomaki. Ba za ki mutu ba."

Ta dan yi murmushin yaƙe, ya juya ya  tafi. Jiki a saluɓe itama ta koma ciki.

***
HUSSEIN AMINU MAMMAN MODIBBO...


Alhaji Aminu Mamman Gidado, haifaffan garin Adamawa ne gaba da baya. Su goma sha biyar cif mahaifinsu ya haifa. Mamman Gidado yana da mata uku, uwargidansa wacce suke kira da Inna, ta haifamasa yara tara cif a duniya, sai mai bi mata Yakumbo wacce ta haifi yara biyu. Hassan da Hussaina wanda a karshe suka koma hannun Inna da zama. Hajara (Hajjo) kuwa tana da yaranta  huɗu cif a duniya.

  Wani irin rayuwa ake gudanarwa a gidan Mamman Gidado, rayuwar da hatta da maigidan shakkar Inna yake yi balle a kai ga mata da yara. Inna wata irin mace ce murɗaɗɗa mai baƙar zuciya, a duniya ba ta kaunar ace wani ne sama da ita koda a matsayi ko wani abin. Auren gida na zumunci aka yi musu da Mamman Gidado.
Sai kuma cikin ikon Allah ya zamana Yakumbo ta fito daga gida na sarauta a garin Mubi. Mahaifinta shi ne wazirin Sarki. Wannan girma da nasaba ta Yakumbo sai ya jazamata baƙin jini fiye da na kowa a wurin Inna.

Ita ta soma yiwa Yakumbo gorin zama bare a gidan don Hajjo ma ƴar aminin kakansa ce aka aura. Yakumbo tana shakkar Inna sosai, tana kuma bin ta sau da ƙafa.

Mijinsu ba karamin so yake yiwa Yakumbo ba, tana matsayi babba a zuciyarsa da bai jin ko Inna ta samu. Wannan ta sanya mutuwarta ba jimawa  shima ya soma jinyar ajali. A gaban idanunsa Inna ta sha hana Amina da Aminu abinci, wataran Hajjo a sace take basu. Dangi kuwa ba'a taɓa ganin laifin Inna don a waje nunawa take nan duniya tana sonsu kuma tana riƙe da su da amana. Wannan tasa hatta ga yaranta maza da mata sun tsani su buɗe idanu su ga Amina da Aminu musamman ganin irin kyauta da gatan da ake nunamusu duk sadda suka kai ziyara Mubi suka dawo. Kayan da Inna ba ta sanyamusu kenan, duk zuwansu dama gargadi ne sosai da jan kunne ta ke musu akan kar su sake su yi yunkurin tonamata asiri.

Modibbo wanda ya kasance ɗa na bakwai a wurin Inna, kusan shi ne babban mugun da ya fi kowa tsanar yaran Yakumbo. Ya sha kama su a makaranta ya jibga ya kuma kwace abincin da Hajjo ta girkamusu. Gori na uwa da uba bai fasa yi musu ba.

"Wai meye amfanin riƙon da ake musu anan? Tunda suna tutiyar dangin uwarsu masu arziki ne, ki tattara ki maida su mana!"

Modibbo ya fadi a zafafe. Yar uwarsa kuma Yayarsa Adda Salma ta karɓe.

"Ashe ka gane, ni wallahi haushinsu nake ji,wannan Aminar ma kyanta ya yi yawa, ko makaranta muka je sai a yi ta wani zuwa ana daukarta. Ji nake kamar na shaƙeta na huta. Da zan samu reza na tsaga fuskar ma zai fi."

Sauran suka yi dariya har Inna Idan ka cire Karime da Adamu wadanda su kadai suka fita zarra akan sauran, basu taɓa nuna kiyayya ga Amina da Aminu ba. 

"Allah ne Ya ba ta kyan, kuma ai..."

Buge bakinta Modibbo ya yi da ƙarfi.

"Dama ke da Adamu ina kula da yanda ku ke shishshigewa yarannan! Marasa zuciya da kishin uwa!"

***
Da wannan irin kiyayyar Amina da Aminu suka taso, boko dai basu isa su je ba sai yaran Inna, islamiyya kadai suke zuwa. A wannan rayuwar, Waziri ya fadi ya mutu, kasancewar mahaifiyar Yakumbo ta jima da rasuwa ne yasa babu wanda ya kara waiwayarsu balle ya maida hankali wurin kula da su daga Mubi. Yar uwar Yakumbo tilo, Zahida, ita kuwa tana aure a Saudiyya. Kafin ta shigo gari akan jima sosai.

Shekaru suka ja a wannan halin, Aminu ya yi saukar littatafai da dama na addini. Mutum ne mai matukar kokari da saurin daukar karatu. Lokaci ɗaya kuma ya bazama neman ilimi a garuruwa daban-daban. Inna ko a jikinta, don a ganinta ba wani ci gaba da zai samu face ya ƙare a almajiranci. A sannan babbar ɗiyarta Hansatu, ta kammala karatunta a fannin shari'a a jami'ar Adamawa. Yayinda Salma ta karancifannin Kasuwanci. Duk an musu aure a sannan.
   Modibbo yana ajin karshe inda shima dai yake karantar fannin Kasuwanci. Adamu da Karime su ne a babbar Sakandire sai Hadiza, Safiya, Tahir a karamar Sakandire,  Maimuna Autar Inna a firamare.

A islamiyya ba su taɓuka abin a zo a gani, gwara ma Karime, tana da kokari sosai don ta yi sauka.

  Yaran Amarya Hajjo hudu, suma duka suna karatu.

Bayan tafiyar Aminu almajiranci da watanni biyar sai ga Hajiya Zahida da yaranta daga Saudiyya. Sun dawo kenan sakamakon sauyin wurin  aiki da mijinta ya samu zuwa Adamawa. An saukeshi daga Ambasada. Kai tsaye wurin ƴaƴan yar uwata ta soma zuwa. Ranar da ta je ta tarar da Inna na jibgar Amina da sunan wai ta tsaya sauraron bare wanda kwata kwata ma ba jinin Fulani ba ne. Da biyu Innar ta yi hakan ganin yaron mahaifinsa mai kudi ne, sunan zuri'arsu ba ɓoyayye ba nema ƙasar. Ya ganta ne a hanyar dawowarta daga islamiyya.

Wannan tashin hankalin da Hajiya Zahida ta tarar yasa ta rantse ko sama da ƙasa za ta haɗe sai ta tafi da Amina. Kaca-kaca suka rabu da Inna, a karshe ta ci nasarar dauke Amina tana kukan rashin sanin inda Aminu ya tafi.

Da wannan suka wuce Mubi, sosai ta nunamusu ɓacin ranta akan yanda suka yi halin ko in kula da yaran Yakumbo, hatta aiken da takan yo a kai musu ba ya riskarsu.

Da wannan bakin cikin ta zauna, sati na cika ta tattara yaranta har Amina suka wuce sabon gidansu a cikin Yola.

Wannan ne dalilin ingantuwar rayuwar Amina wacce gaba daya yaran ke kiranta Dada. Babban ɗan mijin Hajiya Zahida  (ɗan Uwargidansa da ta rasu, riƙonsa ya koma hannun Zahida) Naziru, tunda ya dora ido a kan Amina ya ji nan duniya ita yake so da aure.

  Sosai abin ya yiwa Hajiya Zahida dadi, hakanan shima mijinta bai ƙi ba. A yan uwan mahaifiyarsa ba wanda ya nuna kiyayyar abin ko don irin rikon da Hajiya Zahida ta mishi, ba jimawa kuwa aka sha bikinsu. Amina ta yi kukan rashin dan uwanta a kusa, haka ta hakura ta fawwalawa Allah suka tare a gidan Naziru wanda babu nisa sosai da gidan Hajiya Zahida.

***
  Bayan shekaru masu dama, Dada ta haifi yaranta uku duk mata, tana da cikin na hudu ne ba zato ba tsammani Naziru mijinta ya ɗaukesu sai gidan Hajiya Zahida. Wanda ta gani ne ya sanya ta zuwa a guje ta rungumeshi sai kuka, tana yi shima yi yake. Ta ɗago ta dubi wata mace fara ƙal da ita kyakkyawa, a gefenta wasu kyawawan yara ne su biyu da zasu girmi yaranta, komai nasu iri daya. Haka kawai jikinta ya bata wannan iyalin Aminu ne. Ta rungume matar kafin ta rungumi yaran tana cike da farin ciki.

Sai bayan an zauna an nutsu ne ya ke basu labarin inda ya je.

Ashe bayan tafiyarsa da tawagar almajirai ba inda suka yada zango sai Maiduguri, ya fada hannun wani Malami kuma barebari cikakke, Malam Banakura. Mutum mai sanin daraja da ƙimar almajiransa. Aminu bai ɓoyemishi komai dangane da Asalinsa ba. Tausayi da kaunar Aminu suka shiga Malam. Ya rikeshi tamkar ɗan cikinsa, duk da tarin Almajiran Malam, Allah bai ba shi haihuwa ba. Kuma matsalar daga gareshi ne. Uwargidansa Yakura, mace ce mai halin Dattako, ta rike yaran yan uwa da dama ta kuma aurar da su. Yara biyu kadai suka rage a hannunta sannan, Zahra da Yusha'u.

  Zuwan Aminu sai ta haɗa da shi ta rikesu duk kuwa da cewar ya girmi Zahra nesa ba kusa ba. Sai dai zai iya sa'an Yusha'u.

Haka suka rayu har suka kara girma, noma da kiwo shi ne sana'ar Malam bayan koyarwa, Aminu ya tsunduma wurin taimakawa Malam.  A hankali kuma Allah Ya sanyawa abin albarka. Koda shekarun aure suka kai, Malam ya fahimci irin soyayyar dake tsakanin Zahra da Aminu, bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya auramasa ita da iznin iyayenta. Mahaifinta buzu ne kuma Maigadi, mahaifiyarta ce ƙanwa ga Yakura matar Malam. Kyakkyawar mace mai gashi har ƙugu, yarinya mai yawan ibada da kunya.

  Zamansu ya yi albarka sosai, sai da suka shekara kafin ta samu cikin ƴan biyu. Ta sha wuya sosai kafin ta haifesu. Sai da ƴan biyu suka shekara goma cif a duniya, Malam ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Sosai ya gargadi Aminu kamar koyaushe akan ya je ya nuna iyalinsa a gida. Wanna tasa ana yin arba'in na Malam, shima hankalinsa ya yi gidan.

Shi ne zuwan da ya yi a yanzun, Dada ta ci kuka ta kuma yi korafin nisanta kansa da ya yi da ita har ba ya tunanin halin da ta shiga. Hakuri sosai ya ba ta, ɗan uwa rabin jiki, nan da nan kuma ta mance da komai. Ya nemi labarin abubuwan da suka faru bayansa, anan yake jin labarin mutuwar Inna bayan ta yi fama da jinya. Addu'a kawai ya yi mata tsoron Allah na ƙara shigarsa. Nan yake jin auren da Modibbo ya yi da kuma zaman da ya koma yi a Kano inda yake kasuwanci, sai Adda Salma da mijinta ya koma Gombe. Sauran yan uwa kuwa suna nan a Yola, Karime ma ta yi aure hakanan Adamu.  A yaran Amarya Hajjo ma, autanta ne kaɗai bai kai ga yin aure ba sannan. 

Washegari suka dunguma zuwa dangin mahaifinsu.

Sun samu tarba ta ban mamaki a wurin yan uwan mahaifinsu wannan ya kara tabbatar musu cewa dama can shakkar Inna ce ta sanya ake baya-baya da su, ko dai kuma don yanzun Dada na auren mai kudi ne shima kuma Aminu ya samu rufin asiri daidai gwargwado ne don har gidajen gona da dabbobi yana da su? Oho, ba su da masaniya.

Aminu bai yi ƙasa a gwuiwa ba sai da ya je gida yayyunsa mata duka idan ka cire Adda Salma da ke Gombe. Ya yi mamakin ganin yanda har sannan babu ɗigon kaunarsu a cikin idanuwansu, asalima sai da suka goranta masa na auren Bare a cikinsu don dukkansu auren gida akai musu.

"Kai da Amina kun fita zakkah! Gwara ita, ta auri Fulani kai kuwa bayinmu ka je ka kwaso mana. Har abada ba zamu taɓa daukarki daya a cikinmu ba. Tsana yanzu aka fara."

Wannan shi ne munanan kalaman da Gwaggo Hansatu ta watsawa Zahra da har ya sanyata hawaye.
Karime ce dai ta rasa inda za ta sanyasu don farin ciki. Ta rungume HASSAN DA HUSSEIN cike da murna da jin dadi har da kukanta.

Haka aka rabu cikin aminci, suka dunguma zuwa Mubi. Nana ba laifi an musu tarba.

Aminu bai ƙasa a gwuiwa ba sai da ya shirya zuwa Kano sada zumunci da Modibbo. Ya tarar da matansa biyu, Hajja Fatuma da Amarya. Tun shigowarsu ya dinga watsamusu banzan kallo yana gyara zaman malun-malun. Ba haka ya so ganin Aminu ba, so ya yi rayuwarsa ta lalace yanda rigar jikinsa ma zai gagareshi. Ya mishi tsanar da ko a inuwa ba ya son ganinsa sai rana. Da harshen fulatanci Aminu ya gaida shi.

"Gaisuwar ta mece ce? Ni waye a wurinka? Shekaru nawa ka tafi yawan maula, sai yanzun ne za ka je ka dawomana da SADAKAR YALLAH?"

Cikin dakiya Aminu ya amsa.

"Ba sadakar Yalla ba ce, sunanta Zahra. Matata ce."

Harara Aminu ya watsamata, ƴan biyu suka ƙara nanewa a jikinta suna bin wanda aka kira Yayan Babansu da kallon tsoro da tsana.
  "Bare ce! Yanda uwarka ta shigo gidanmu tana matsayin bare, kaima haka ka je ka kwasomana abin fadi da gori! Har abada wannan matar ba za ta zauna cikin zuri'armu ba. Sai yanzun ka tuna da mu ka kwaso jiki ka taho zumunci ko? Toh ni Muhammadu, ban sanka ba! Bani da wata alaƙa da kai, ƙafarka na ƙara gani a gidana Allah Ya isa. Duk abinda na yi maka kuma kai ka ja wa kanka. Ku kuma kuma kallona kamar Mayu!"

Ya maida akalar zancen kan Hassan da Hussein da suke kallonsa, duk da karancin shekarunsu, haka bai sa sun gaza fahimtar wasu abubuwan da yake faɗi ba don Hausa sak ya yi ko don ya baƙantawa Zahra.

Da wannan cin kashin da rashin mutuncin na Modibbo, Aminu ya tattara iyalinsa suka juya ko kwana ba su yi ba. A mota ya yi ta rarrashin Zahra da ban hakuri. Ita kuwa murmushin yaƙe ta yi kawai ta nuna ba komai tunda dai bai ɓoyemata alaƙarsu da su ba tun farko. Labarin komai na irin riƙon da ya samu a hannun uwarsu ta sani.

  Watansu daya suka yi shirin komawa, nan fa Dada ta rikice da kuka da rantsuwar ba ta yarda ba, a karshe ta dage ma sai dai a bar mata ƴan biyu ta riƙe, dabararta na yin hakan, don kawai su dawo da wuri a dinga ganinsu. Aminu ya rasa ya zai yi da yar uwarsa, ga mamakinsa Zahra da kanta ta riƙe hannun Hassan da Hussein ta damƙawa Dada tana murmushi.

"Yarana mallakinki ne Dada. Gasunan na bar miki su duniya da lahira."

Wannan abu har gobe Dada ba za ta mance shi ba, kuka sai ya koma dariya. Har tasha suka yi musu rakiya suka dawo. Abin mamaki Hassan da Hussein ko a jikinsu don sosai sun saba da Dada da iyalinta a ɗan zaman da suka yi tare.

***
Mummunan labarin hatsarin mota da rasuwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login