Showing 12001 words to 15000 words out of 230725 words

Chapter 5 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1038

hannun da zai mayarta gida.

   "Ƴan mata bamu chanji mana."
Ta juya inda maganar ke fitowa, adaidaita ce ta yi parking a gabanta, sai da ta ji ba za ta iya yafewa kanta ba sa'ilin da idanunsu suka haɗu, da ba ta kalleshi ba, abubuwa da dama ba zasu chanja daga zuciya zuwa gangar jikinta ba. Sai dai kuma nan take ta ƙaryata. Shima da yake daga cikin ɗan sahun watsi ya yi da nashi a kwandon shara ya maida kai zuwa cikin abin hawar.

"Babu kenan." Ta ji muryar ɗan sahun sa'ilin da yake sauka yana nufar abokin aikinsa da zummar karɓar chanji. Bisa kuskure idanunsu ya ƙara sarƙewa, ta yi saurin janye kwayar idanunta shi kuwa an zo gaɓar da ya yi amannar hakurinsa ya ƙare.
  
Ta gifta napep din har ta  samu nasarar tsallakawa. Haka kawai take zuba sauri don ta isa gida, ba ta yi aune ba ta ji muryar mutum a bayanta.

"To ni kuma da ba ɗan unguwa ba kina wannan saurin idan na ɓata fa? Kar ki kaini gidan ƴan yankan kai."

Cak ta tsaya gami da juyowa, bata san sadda ta yi suɓutar baki ba.

"Biyoni ka yi?"

Duk yanda ta so kar ta ƙarasa faɗi bayan ta ankara da suɓutarsa hakan ya faskara. Murmushi ya yi ya ɗan tako kaɗan. Kusan a gigice take duban layin, fatanta kada koda wasa Yaya Munir ya ganta tsaye anan. Wannan yasa ta juyawa da zummar soma tafiya.

"Don Annabin Rahma ki tsaya."

"Sallallahu alaihi Wa sallam." Ta furta a hankali sannan ta dubeshi.

  "Malam wallahi an sakamin rana yau ɗin nan ma, don Allah ka yi hakuri ka daina bina. Matsala za ka jawomin a gida."

Ta furta rai a haɗe sannan ta soma tafiya kirjinta na harbawa. Fatanta Allah Yasa ya dakata.

"Ni duk ba wannan ba, nima inada matar aure. Kwatance za ki min."

Ba ta fasa tafiyar ba, bai fasa bibiyarta yana magana ba. Dole ta tsaya ganin an kusa shan kwanar layinsu. Ta dubeshi da idanunta masu firgita maza. Ya kuwa lumshe nashi ƙananan idanun masu kama da na mai jin bacci ya bude, shirunta na nufin tana jinsa kenan

"Wani gida nake nema, bansan kalarsa ba. Ba zan ce ga girmansa ba, kuma da ace ma da hali naga gidan ban ƙi ya zama mallakina ba na har abada. Amma kinsan me? Matar gidan ta nunan ba ni da wurin zama cikin gidanta. Ni ne da nacin tsiya na kasa haƙura. Idan na kasa mallakar gidannan, bana jin akwai gidan da zai ƙara burgeni koda kuwa ace wanda nake da shi yanzu ne! Ki tausayamin don Allah."

Ya ƙasashe cikin karaya, rabin hankalinta na ga kallon hanya rabin wajensa, ko kusa ba ta gane wannan tatsuniyar ba don haka kai tsaye ta ce.

"Wallahi ban gane komai ba Malam, ka rufamin asiri ka tambayi wani ko wata sai anjima."

"Saƙo na ƙarshe don Allah, nima daga nan zan juya na tafi kar na sha wahala."

Dole ta ja tunga ta juyo tana dubansa, shima ƙara narkar da idanunsa ya yi cikin nata gami da jingina kansa jikin bishiyar darbejiyar dake bayansa. Ta kauda kai tana ƙara yiwa kanta tunin wannan ba HILAL bane tsaye.

"Bana yiwa mace kallon da ya wuce biyu, amma kin janyomin sauka a unguwar da kusan bani da kowa, ban taɓa bin mace a baya ba, don wannan ba ya cikin sabgar ALIYU, kin sanya na biyoki. Bansan gaskiyar sanyamaki rana ba duk da cewa fuskarki ba ta maƙaryata bace, sai dai ki taya kaina da kuma ke addu'ar kada mu kasa cika alƙawarin waɗanda muka ɗauka matsayin abokan rayuwarmu. Fatan alheri MATAR GIDA."

Daga nan ya juya bai ƙara waiwaye ba, duk da dukan da kalaman suka yiwa zuciyarta, bai sa ta fasa ci gaba da tafiyar ba. Sai dai fa tana tafe tana yiwa kalaman filla-filla, sannu-sannu kuma take haddarsu. Ta kasa fahimtar manufar, ba kuma ta marmarin ta fahimta ɗin don a ganinta bai da amfanin komai, wannan ta sa ta yin watsi da shi. Sai dai daga lokacin Aliyu ya yiwa mafarkanta illar da har ta soma tunanin ba mutum bane!

Hilal ya zo suka yi sallama sadda zai wuce Malaysia, kowannensu wata irin kewa  yake ji, Ramla kuwa kasa jurewa tayi ta shiga hawaye.

"Aa please, za ki yimin illa babba fa. So kike ina tafe ina tuna kuka maimakon murmushinki? Kar muyi haka da ke. Kinji? Idan kin yi kuka ni kuma na yi me?"

Ganin duk yana neman hargitsewa sai ya ba ta tausayi. Ya shiga rarrashi.

"Ki kwantar da hankalinki kinji? Da kaina zan siyamaki waya na aikomaki don ba zan jure rashin jinki ba. Ramla ba don karatu dole ne ba kuma ina sonmu da shi wallahi Hilal zai iya ajiye karatun ya aureki daga baya ki ƙarasa naki a gidana. To ba zai yiwu ba, komai bisa tsari ya fi. Ki yi hakuri kin ji?"

Ta share fuskar tana murmushi. Kukanta biyu ya haɗarmata, kirjinta bugu yake bana wasa ba, tana ganin kamar akwai wani ɓoyayyen lamari da zai fi ƙarfinta, jikinta na bata akwai babbar matsala sai dai wani ɓangare na zuciyarta na ƙarfafarta akan kar ta ba shaiɗan damar wasa da hankalinta. Yanda Hilal ya dage rarrashi ma duk sai ya bata tausayi dole ta nuna mishi ta sauko, suka rabu kamar kar su rabun. Tuni ya yi sallama da su Hajiya da Abba, wannan tasa kawai wucewa ya yi. Hotunanta kala-kala na takarda ta ba shi har yana fadin zai sa a mishi enlargement dinsu ya kafa a ɗakin kwanansa na makaranta. Dariya kawai ta yi. Daf da zai bar gidan ya dakata gami da fiddo wani ɗan akwatin ƙarami na zobe, kai tsaye ya miƙamata yana murmushi.

"Karɓi mana."

Ta sa hannu ta karɓa tana kallo.

"Duk da ba zancen alƙawari yanzu, saboda inada yaƙinin irin kaunar da muke yiwa juna, ina da tabbas a kanki Ramlata. Ki sanya a hannunki, ya kasance har bayan dawowata shi zan tarar a hannunki. Wannan kaɗai zai sa ni farin ciki. Ina miki fatan alheri."

Daga nan ya fice a gaggauce don da alama ya soma karyamata zuciya.

"Azurfa mai kyau." Shi ne abinda Rafee'ah ke kira yayinda ita kuwa ta mike ta bar falon zuwa ɗaki. Kuka ta ci sosai na abu biyu da ta rasa da wanda za ta ji. Sai da ta yi mai isarta ta share fuska, ta ɗau alwashin rabuwa da tunaninsa balle ya kai ta da mafarki. Ta ƙara gaskata mafarkan  Aliyu duk kissimawar shaidan ce, shi ke mata yawo da hankali a mafarkanta.

"Daga rana irin ta yau babu ni ba tuna dukkan wani abu da ya shafeka Aliyu, har abada. Allah ina neman tsarinKa daga sharrin shaidan da kuma na zuciya da saƙe-saƙenta."

Sai dai kuma wasu lamuran sun fi gaban yanda dukkan bawa ke ɗaukarsu. Duk a rashin sanin cewar yanzu aka fara!

***
   Ƙarar ababen hawa ya cika kunnuwanta, dole ta saita kanta ga ci gaba da tuƙi cikin nutsuwa da kwarewa, a hankali ta sa bayan hannunta ta share fuska. Daidai wani boutique ta yi parking ta fito.  Kai tsaye ta shiga, tunda Ummi da Ansar suka ƙwallafa rai akan halartar Children's Day. Ta shiga ciki kai tsaye ta nufi ɓangaren kayan yara. Tun kan ta ƙarasa ta hango bayan mutumin riƙe da waya a hannunsa yana video call bai ko damu da tsilli-tsillin mutanen dake shagon ba wadanda wasu ke kallonsu suna dariya wasu kuwa su yi gaba.

"Wannan kina so?"

Ya ɗaga wani takalmin, yarinyar ta turo baki kamar mai shirin kuka ta girgiza kai da mirza idanu. Ya sauke ajiyar zuciya.

"Tee ya zan miki uhm? Duk wanda na ɗaga bai miki ba? So kike Mominki ta yi mana dariya ko?"

Matar shagon ta ƙara ɗauko mishi wasu tana dariya kaɗan-kaɗan. Ramla kallon yarinyar kawai take tana tasbihi ga Ubangijin da Ya ƙageta.

"Daddy ga wata Mami can a baya, ni ta zaɓamin. Dada ta cemin ba ka iya zaɓe ba."

Cewar yarinyar har tana riƙe haɓa da turo baki, jin abinda yarinyar ta faɗi yasa ta saurin juyawa ta ɗora hannu saman shelf din da ya fi kusa da ita kamar hankalinta bai kansu. Tana jin dariyar yarinyar, shi kuwa uban koda ya juyo sai ya ji kunya kaɗan cikin yaren fillanci ya yiwa yarinyar sallama ya katse kiran.
   "Ki ji fa, idan matar aure ce kuma fa?"

Ya yi maganar yana duban Matar dake aikin ciro mishi takalma, ta dubi Ramla da ke sauraron su kadan kadan. Ta yi dariya.

"Wannan Customer ɗinmu ce Oga,na san Madam ba ta da aure."

  Ya kara duban Ramla kafin ya mike da nufin aiwatar da abinda ɗiyar ta nema, a sannan ita kuwa Ramla har ta ɗauki wata doguwar riga mai hula wanda ta tabbatar zai yiwa ɗiyarta.

"Assalamu alaikum."

Ta dubeshi, zaro idanu waje ta yi. Ganinsa anan ya yi masifar ba ta mamaki da kuma tsoro. To ina Hajiyar? Yaushe ya sauya kaya daga voyel maroon zuwa shadda ruwan toka? Ta kasa magana, shi kuwa bai maida hankali wurin kula da hakan ba ya shiga neman alfarmar ta zaɓamasa takalmin da zai yiwa ɗiyarsa. Ta kasa magana don gaba daya ta tsorata.

"Hello."

Ya ƙara faɗi gami da ɗan rankwafar da kai. Ta ɗan yi firgigit sai ta basar cike da dakiya.

"Ba damuwa."

Suka ƙarasa wurin takalmin, ta shiga dubawa bayan ta tambayi size dinta. Jefi-jefi za ta kalleshi da tsantsar mamaki, sai dai duk abinta ba za ta taɓa yin shishshigin tambayar ko shi ƴan biyu bane. Wani takalmi ja ta ɗauki mai adon fulawa, tana murmushi ta miƙa masa.

"Wow, gaskiya Madam kin iya zaɓe." Fadin ma'aikaciyar wurin.

"Allah Yasa ya burgeta." Ramla ta fadi da murmushin da ya fi kama da yaƙe don har yanzu kirjinta bai bar bugu ba tsabar kamannin da ta gani ƙarara na wannan mutumin da mijin Hajiya.

Shi kuwa Alhassan banda murmushi ba abinda yake dokawa, iyakar burgewa takalmin ya mishi har cewa ya ke.

"Idan Tee ba ta so takalminnan ba to ba bulala za ta sha." Suka yi mishi dariya.

"In Sha Allah za ta so."

Daga fadin haka ta mike yana mata godiya, ta koma ga kayan maza hannunta rike da rigar da ta daukarwa Ummu. Sai da a kammala ta nufi wurin biya. Duk yanda ta nuna ba ta so hakan bai sa Alhassan fasa biyamata kuɗin kayayyakinta ba. A karshe godiya kawai ta yi, kusan tare suka fito kowa ya nufi motarsa suna kara yiwa juna godiya. Kallonsa take har ya bude mota zai shiga, hatta da tafiyarsu ɗaya ce, a yanzu ta yarda su ɗin ƴan biyu ne babu ko tantama. Har za ta tayar da mota ta ji maganarsa a gefenta.

"Mami, yi hakuri ki sanyamin number dinki, I promise you ina komawa garinmu zan kira na ba ki albishir takalmi ya burge ɗiyarki. Kuma itama ina son ta miki godiya ko?"

Ta yi jim kamar ta ce a'a, ya kuwa narkar da fuska. Sai ta yi murmushi ta karɓi wayar ta shigar da lambarta. Ya karɓa ya yi godiya suka yi sallama.

A hanya tunanin biyun masu kama kawai take yi wanda bambancin su fara'a da akasinsa. Banda wannan kamar ta yi yawa. Haka har ta isa gida  tana zancen zuci.

https://my.w.tt/ub8deMQ0g9


🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem


06)

***
Tun fakawarsa a gaban ƙaton ƙyauren na gidan Muhammad Modibbo ya ji ɓacin rai ya lullluɓe dukkan wata walwalarsa. Ya kalli gidan, abubuwa da dama suka shiga dawowa kwanyar Alhassan Aminu.

_"Tunda ubanku ya bijirewa umarninmu ya auri bare ai ko sata aka ce kun yi zan yarda. Har abada zuri'armu ba za ta karɓi Uwarku ba balle ku da ku ke yaranta."_

Ya runtse idanu tuna kalaman babban wan mahaifinnasu da ya yi. Ba don Dada ba ba zai taɓa shiga gidan ba. Sai dai matsayi da girmanta ya zarta hakan.

"Sai yau ku ka tuna da ni?" Dattijon mai shekaru sittin da ɗoriya ke wannan kalaman cikin harshen fulatanci sadda ya dubi Alhassan dake zaune a gabansa ya sunne kai. Murmushin yaƙe ya yi.

"Ba haka bane, ayyuka ne suka yi min yawa. Ayi hakuri."

Ya maida da harshen fillanci don Modibbo Hausar ba kasafai take fita ba.

"Ka koma, duk radda ka yi ritaya wurin aiki sai ka dawo a ci gaba da zumuntar." Daga haka Modibbo ya mike ya shiga ɗakinsa. Idanun Alhassan suka kaɗa, dama yasan a rina! Bai ma tsammaci zai yarda su gaisa ɗin ba. Ya mike gami da zaro hankicif a share goshinsa. Duba ya kai ga ƙaton enlargement din na yaran Mamman Gidado dake manne a falon, yaransa goma sha biyar cif har mahaifinsu wanda ke bi ma Modibbon. Ajiyar zuciya ya saki ya fice daga falon da sauri. Sashin matan gidan ya wuce, su biyu ne kuma duk daga zuri'a guda sai dai ɗaya ɗiyar wa, ɗaya kuma ɗiyar ƙani.
Ɗakin Uwargida Hajja Fatuma ya soma shiga. Kadahan-kadahan ta amsa mishi, wurin yaranta ne ya samu tarba sosai, bai yi mamaki ba don dama basu da matsala tsakaninsu su cousins.

A ɗakin Hajja Amarya kadai ya samu shimfidar fuska, dama can ita ke mutunta su da ɗan uwansa da mahaifiyarsu.
Anan ya shantake har girki ya kwasa suna dariya karshe ya mata sallama ta bada turarukan wuta a kaiwa Dada sai na matarsa.

Yara yasa suka shiga da kayan lemuka da ya yo tsaraba, bai ko kara shiga ba ya ja motarsa. Washegari kuwa sammako ya yi ya bar garin Kano.

***
  *ADAMAWA*

   Tana tsaye jikin madubin ɗakinta tana kokarin gyara zaman ɗaurin ɗankwalinta. Doguwar riga kalar ruwan madara ta sanya wanda aka yiwa aikin paint work.  Sauri-sauri take don tasan mijinnata na dab da shigowa gidan dalilin waya da suka yi ya sanarmata ya shigo gari. Sai dai saurinta ya kusan haifar da nawa sakamakon hon dinsa da ta ji a bakin gate. Ba ta san sadda ta turo baki ba don ita kam a duniya ba abu mai wuya wurinta irin ɗaura ƙaramin ɗankwali. Ta yi jifa da shi gefe ta koma wardrobe ta dauko karamin mayafin da ya dace da kayan ta fita. A falon suka ci karo, ya sakarmata murmushi gami da ajiye ledar saman kujera ya buɗemata dukkan hannuwansa, aikuwa da sassarfa ta ƙarasa ta shige, ya maida hannuwan ruf.

  "Sannu da zuwa Abu Fatima." Ta fadi tana mai ɗagowa daga jikinsa. Ya ja karan hancinta.

"Kema sannunki. Kin yi kyau sosai."

Ta yi godiya, daga nan suka faɗa ɗaki, ta taimaka ya yi wanka ya rama sallolinsa kafin su fito falon. Miƙar da ƙafafunsa ya yi saman kujera haɗi da kiran wash.

Ta ɗaga ƙafafuwan ta zauna sannan ta ɗora saman cinyarta. Cike da tausasawa ta dubeshi.

"Sannu Abu Fatima, ka kwaso gajiya."

Ya lumshe ido da murmushi.

"Bari kawai Ummina, na sha tafiya ba kaɗan ba amman Alhamdulillah tunda na cimma nasarar abinda ya kaini. Zuba abincin."

Ya fadi yana mai miƙewa zaune bayan ya sauke ƙafafunsa. Yana cin abinci yana mata hirar diramarsa da Fatima. Banda dariya ba abinda ta yi.

"Ci gaba da biyewa yarinyarnan dai, watarana sai ta ba ka kunya. Hum, naga kokarin ma Matar da ta biyewa shirmenku."

Harara ya watsamata.

"Shikenan, kin ja wa kanki na fasa ba ki taki tsarabar."

Ta kama kunne tana murmushi.

"Na tuba. A yimin afuwa."

Ya yi murmushi kawai. *Kausar* kenan, matarsa kuma ƴar uwarsa. Sun gina rayuwa ta fahimta, so da kuma kaunar juna. Ɗiyarsu guda a duniya Fatima, tun daga kanta Allah bai ƙara ba su haihuwa ba.

  Sai washegari ya je gidan Dada, bayan sun gaisa ya isar da sakon gaisuwar Modibbo da jama'ar gidansa  gareta, ta ji ba don ta yarda ba. Ya ba ta tsarabar da Hajja Amarya ta ba shi. Murmushi ta yi.

  "Wannan kam na yarda."  Shima murmushin ya yi bai ce uffan ba.

"Daddy takalmina." Fadin Fatima tana kara mannewa jikinsa gami da turo baki. Ya na dariya ya janyo leda, ya bude kwalin ya soma kokarin sanyamata a ƙafa.

"Wowww! Daddy ya yi kyau sosai."

Dariya ta basu shi da Dada.

"Sai ki zo ki yiwa Mamin Boutique godiya."

Ta mike tana tsalle ganin yanda takalmin ya yi kyau a kafarta kamar wata balarabiya.

Ƙarshe ta rungume wuyan Uban tana magiyar a kiramata Mamin Boutique. Ba musu ya fiddo waya ya danna kira.

  ***
KANO

Misalin ƙarfe biyar da mintuna ne na yammacin ranar, dawowarta kenan daga wurin aiki ta miƙe ƙafa a falon cikin yayyunnata mata wadanda a ƴan kwanakin suke shigowa dalilin bikin A'isha da ya taho gadan-gadan. Rafee'ah ke riƙe da takarda da biro tana lissafin kayayyakin da ya rage a siyo a kasuwa  yayinda Zulaihat ke nunamusu wasu hotunan sabbin warmers ƴan Dubai a waya.
 
  "Kai Maman twins, sun yi kyau sosai wallahi."

Fadin Ramla tana ƙara sanyo kai ta gefe ita da A'isha.

  "Kyau ai ba ɗaya ba Ramla. Nidai idan ma ba za'a siya wa Auta ba ina so zan siya."

  Fadin Rafee'ah tana ƙara kallon hotunan cikin santi.

"Kai Sis. Aa nidai ina so wallahi."
Fadin A'isha, ganin Hajiya ta kalleta sai ta ji kunya ta ruga ɗaki. Dariya suka yi gaba ɗayansu. Daidai sadda ta ji ƙarar wayarta, ta koma mazauninta ta ɗauka. Ganin baƙuwar lamba ne ya sanya ta yi mata ƙuri, sai dai tuna ko akan abinda ya shafi wurin aikinta ne ya sanya ta ɗagawa da sallama.

"Waalaikumussalam wa rahmatullah Mamin Boutique."

Ta ɗan yi shiru sanadin abu biyu, jin muryar namiji da kuma jin sunan da ya ambata.

"Sunana Alhassan Aminu, wanda ku ka hadu a Afrah Boutique dake kan..."

"Ayya sai yanzu na gane. Fatan kana lafiya?"

Ta katseshi da sauri ganin yanda ƴan uwan suka raba hankalinsu, wani a abinda suke wani kuwa a kallonta ana ƴar dariya ƙasa-ƙasa.

Suka ƙara gaisawa sannan ya miƙa wayar ga Fatima.

"Assalamu alaikum Mamin Boutique. Ina kwana."

  Yanda yarinyar ta yi sai da ta murmusa don kuwa ta burgeta. Ta amsa mata, nan yarinyar ta shiga zubamata hirar takalmi ya yi kyau Maminta ba za ta yi mata dariya ba. Ita dai Ramla ta biyemata, karshe Abbannata ya karɓi wayar.

"Idan kika biyemata sai ku cinyemin kuɗin wayar ai."

Suka yi dariya kusan a tare, ya ƙara yi mata godiya ta bada saƙon gaisuwa ga mutan gidan daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login