Showing 126001 words to 129000 words out of 230725 words
ƙarshe ma ta fita don tarbarsu.
Har suka ƙaraso idanunta na wani gefen, ya fito daga motar sanye da dark blue din shaddarsa sai gilashin da ke ƙaramasa kyau. Ya karya hula kamar Bakano.
Yarinya karama ta fito ta sha ƙananun kitso shuku a kanta, an sanyamata ribbons masu kyau da ya ƙaramata kyau. Ganin har da dattijuwar da nan take jikinta ya bata cewar ita ce Dada, yasa ta ƙarasawa tana ƙara yi musu barka da zuwa. Kausar da Hafsat sosai Ramlat ta burgesu, ta jagorancesu har cikin falon Hajiya wanda aka ƙara kimtsawa, Alhassan ne dai ya toge a farfajiyar gidan ya ƙi shiga. Bayan sun zauna aka gaggaisa, can kuma ta shiga daki ta kira Hajiya. Su Zulaihat ma suka biyo bayanta.
Dada ba ta jin hausa sosai, a haka dai aka gaggaisa, wani abin Hafsat ce ke cin gyaranta.
"Kinga abin Allah mai haɗa zumunta."
Fadin Hajiya tana murmushi ganin yanda Fatima ta maƙalewa Ramlat kamar dama can sun taɓa haɗuwa.
"A bar ki a nan za ki zauna?" Fadin Hafsat tana duban Fatima wacce ke ƙara shigewa jikin Ramlat. Da sauri ta wangale baki gami da gyaɗa kai, duk sai ta sanyasu dariya.
Anan ne Ramlat ke ji dagasken dai su na da ƴan uwa a garin, kwatancen da ta yi yasa nan take suka gane gidan musamman Hajiya da Yakasai ya zama unguwar da ta ci ƙuruciyarta a ciki. Sai dai basu taɓa shiga gidan ba don ba wani fita suke yi ba sosai a unguwa, hakanan su ma mutan gidan ba kowa suke shiga sabgarsa ba sai wanda ya isa.
***
Hisham gwanin cika alƙawari sai gashinan ya zo tun ma biyar saura. Babban abinda ya ƙara kwadaita masa zuwan bai wuce na cewa da ta yi lamarin ya shafi Hussein ba. Ya faka motarsa a waje, Maigadi na shirin bude gate ya dakatar da shi gami da nuna yanzun shima zai fito. Bayan sun kammala gaisuwar ya ƙaraso ciki, ji ya yi kansa ya sara yayinda kirjinsa ya shiga dukan tara-tara. Ba don a yau ɗin ya ziyarci Hussein a ofishinsa ba, ya kuma san kalar kayan da ya sanya da ma kalolin motocin gidan Hussein din, zai iya rantsewa ya ƙara wannan na tsayen Hussein ne.
'Kenan Hussein ƴan biyu ne?' Ya jefawa kansa tambayar da nan take ta amsamishi da eh. Tambayoyi kala-kala ke ɗawainiya da shi. Ya ƙaraso ganin da ya yi Alhassan ya zubamasa idanu fuska a sake, wayar da yake dannawa ya mayar cikin aljihu gami da miƙamishi hannu. Musabaha suka yi, hatta da muryarsu sai ya ji tana mishi kamanceceniya. Ja ya yi ya tsaya cikin danne mamakinsa, damuwa sosai ya mamayeshi. Ya tuna gargadin Ramlat akan kar ya yi wata katoɓarar don haka ya daure yana jan Alhassan da hira da zolaya kamar ya sanshi. Anan ya kara tabbatarwa ba Hussein bane, wannan wani ne daga Adamawa kuma sunansa Alhassan. Yana so ya tambaya ko yana da wani dan uwan haihuwar amma ya danne.
Kafin dai Ramlat ta fito ta yiwa Alhassan iso don ya shiga gidan, Hisham da AlHassan hira suke yi sosai, ya fahimci kusan halayyarsu ta daya don har Alhassan ma ya fi Hussein sakin fuska.
Ramlat na ganinsu tare ta karasa, suka hada ido da Hisham wanda ke kallonta bakinsa cike da tarin tambayoyi, ta gaidashi. Ta yi musu jagora zuwa falon Hajiya.
Nan aka ƙara gaggaisawa sannan AlHassan suka koma sitting room. Abinci da komai ta kai musu. Bayan kammala ci, suka yi shirin tafiya.
Ya yi daidai da dawowar su Ummi daga makaranta.
"Yaranki ne?" Dada ta fadi tana kallon Fatima, murmushi ta yi kawai ta sunkuyar da kai.
"Ai Dada daga gani ma ba tambaya, wannan yarinyar tana kama da ita sosai." Kausar ta fadi tana mai jawo hannun Ummi da nutsuwarta ya burgeta.
"A'a, wallahi ta fi ta kyau."
Fadin Hafsat, tana nufin Ummi ta fi Ramlatun kyau.
Nan Kausar da Hafsat aka shiga musu, su Zulaihat me zasu yi ba dariya ba. A karshe suka yi musu sallama suka kama hanyar tafiya zuciyoyin kowannensu cike da farin ciki. Babu ma kamar Hafsat wacce kafin fitowarsu daga gidan Modibbo ranta ya ɓaci da yanda Modibbo ya amsa gaisuwarsu a wulaƙance. A hanya har rantsuwa ta dinga yi ba za ta ƙara zuwa wata sabgarsu ba. Ba wanda ya kulata don kowa ransa ba dadi.
A yanzun tana jin za ta iya zuwa ta yi fiye da sati ma a Kano saboda karamci irin na Ramlat da ƴan gidansu. Ko ba komai ta samu wasu ƴan uwa a garin.
A ɓangaren Dada ji take inama haka Modibbo da sauran ƴan uwanta ke sonsu, da ta tabbatar ba ta da sauran damuwa.
***
Bayan tafiyarsu Ramlat ta takowa Hisham har wurin motarsa. Cike da damuwa ta tari numfashinsa, kaf yanda ta haɗu da AlHassan ba ta ɓoyemishi ba. Ya jinjina kai ya ƙara sakin ajiyar zuciya karo na ba adadi.
"Wallahi kaina ya ƙulle Ramlat, wannan lamari da ban mamaki yake. Zargina ya tabbata na cewa Hussein rabashi aka yi da ƴan uwansa. Koda ba rabasun aka yi ba, toh lallai akwai wani laifi da aka aikata gareshi har ya yi sanadin da ya fidda kowa a babin rayuwarsa. Mutane masu mutunci da kamala, sun bani tausayi sosai na rashin sanin inda yake."
Ranta ya sosu, sosai ta ji tausayin Hussein ya ƙara mamayeta. Ta karyar da wuya.
"Bari kawai, ni kaina abin yana dauremin kai. Amma fa bana son sanar da su komai, ba kuma na son su haɗu da juna har sai mun gano bakin zaren."
Jinjina kai Hisham ya yi.
"Gaskiya ne Ramlat, don Allah ki dage, ki ƙara shawo kan Hussein yanda za ku shaƙu. Watakila ta hanyarki mu samu wani information din tunda na lura wallahi ya soma damuwa da ke."
Gabanta ya fadi. Ta dubi Hisham sosai.
"Bangane ba."
Murmushi ya yi don ba ya jin dariyar dalilin damuwa da tausayin abokinsa da ya mishi ƙatutu. Tayar da motarsa ya yi.
"Ke dai ki yi aikinki. In Sha Allah nasarar ma da kike tunani zamu samu fiye da ita."
Ta amsa da toh kawai ba tare da ta tanka ba, dakyar ta iya ba shi sallahun gaida A'isha. Har ya ja motar tana juya maganarsa ta ƙarshe, to wace irin damuwa da ita kuma? Ta kasa fassara wannan kalamin.
***
'Addu'a, shi ne abinda ban fiye maida hankali wurin yi ba."
Ya furta a fili cikin ba kansa amsa, shi kadai ne a mota yana ja bayan dakyar ya samu fitowa daga takunkumin Hajiya Zeenatu na yi mishi rakiya duk inda zai je.
Ya yi wannan maganar a sanadin wa'azin Mufti Menk da ya gama saurara a motar, malamin na tunadar da Bawa akan ya dinga zama yana yiwa kansa hisabi, mene ne abinda ya san yana aikatawa kafin lokaci ya ƙuremasa.
Damuwa da ƙunci suka cika zuciyarsa, ko sallah ya yi a gaggauce yake yinta, bai damu da zuwa Masallaci ba ya bi jam'i ko lokutan azumi balle kuma sallar Asuba wacce wani zubin sai rana ta fito take gabatar da ita. Idanunsa suka kaɗa, shakka babu shi laifukansa nada yawa a wurin Allah.
Ruwa ake yi tamkar da bakin kwarya bai fasa tuƙi ba sai dai yana tafiyar ne kamar wanda kwai ya fashewa a ciki. Wannan ma kadai ya isa ya jawowa bawa munanan abubuwa, yana da matsala babba ta wannan fannin.
Da wannan tunanin ya isa gida cike da tsantsar damuwa. Hajiya Zeenat ba ta nan wannan yasa shi kai tsaye nufar ɗakinsa, sai da ya rage kaya ya yi wanka kafin ya sauko ƙasa. Nan ya iske John ya jera kwanukan abinci saman tebur. Budewa ya shiga yi kafin ya ja tsaki ya maida ya rufe, babu ɗaya da ya burgeshi balle ya ji zai iya ci. Wayarsa ya jawo ya shiga dannawa, kai tsaye whatsapp ya shiga.
Shi ɗin ba ma'abocin bude Status bane, sai dai yakan bude na mutane masu muhimmanci a wurinsa. Sunan HEART da ya hango a jerin wadanda suka dora Status ne yasa kansa tsaye ya bude.
Hotonta ne zaune saman kujera a falo, ta rungume wata kyakkyawar yarinya suna dariya. Kirjinsa ya bada dam! Ya kara zooming ya kurawa yarinyar idanu. Da ace ya taɓa haihuwa, ba abinda zai hana ya kira yarinyar da ɗiyarsa. Can kuma ya tuna kamanni ne kawai, murmushi sosai yake yana kallon yarinyar da ita kanta RAMLATUN. Sun burgeshi sosai, yarinyar ta shiga ransa ainun. Ya yi niyyar screenshot sai ya fasa, wannan ba halayyarsa ba ce don haka suka ya zaɓi turamata saƙo kamar haka.
"Mutane sama da dari biyu sun ga Status dinki. Hakan daidai ne?"
Yana aikawa ya saki murmushi gami da sauka daga whatsapp din. Wayar ya ajiye, hakanan sai ya ji wani kwarin gwuiwar ya ci abincin. Ya kuma rasa ta ina.
I just published "BABI NA TALATIN DA TAKWAS" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/IcdWtyGJpbb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
38)
Shigowarta dakin kenan bayan sun yi sallama da Hajiya. Wani hamma ta saki tana mai rufe baki, a gajiye liƙis take jin ta. Kakkaɓe gefen da za ta kwanta ta yi, hankalinta ya kai ga wayarta, shaf ta mance da ita a chaji, ta cika tun awanni biyu ma da suka wuce.
Zareta ta yi ta shiga cikin whatsapp ganin saƙonnin da suka faɗo daga kunna Data.
Saƙon Hussein ya sanyata dariya ba kaɗan ba, ta maidamishi amsa.
"Ba fa celebrity ba ce."
Daga haka ta yi zaman jiran amsa har gyangyaɗi ya soma fisgarta, can dai ta hakura ganin ba ya kusa ta kashe wayar ta yi addu'a ta kwanta.
***
Ruwan da ake kamar da bakin ƙwarya ya sa ta barin yara a gida don sun kammala jarrabawa kusan wasa kawai ake a makarantar yanzun, itama ba don fitar ta zama dole ba da babu inda za ta je. Amrah ce ba lafiya, abin tsoron kuma lokacin haihuwarta da saura don duka-duka cikin bai kai wata shida ba.
"Ki je zuwa anjima ma leƙa. Kar dai ki manta da kiran Kawunnaki. Ki karasa Yakasan idan ruwan ya tsagaita."
Wani ɗaci Ramlat ta ji da bayanin karshe na Hajiyarta, tasan kiran da Kawun ke mata bai wuce akan aure ba. Ita shikenan yanzu kowa idanunsa a kanta, an takura akan sai ta yi aure. Dama tun da Hajiyar ta soma batun kai yara dangin Babansu don su ci hutunsu a can, ta soma jin ba dadi. Babban takaicinta yanda tun rasuwar Abulle babu wanda ya kara nemansu banda Malam da ke kira lokaci zuwa lokaci su gaisa ko kuma ita ta kira. Hakanan Justice duk sadda zai yiwa yaran ƴan uwansa kayan sallah toh zai haɗa da su. Kannen Aliyu ta yi musu uzurin aure, amma a ganinta hakan bai kai dalilin da zasu dauke ƙafa da hankalinsu daga kan yaransa ba. Ko ƙafarsu ba ta tako ba ai akwai waya.
"Kin yimin shiru kina wani ƙunƙuni, idan ba za ki je ba sai ki kira ki faɗamasa."
Hajiya na kaiwa nan ta mike a fusace ta yi ɗakinta. Sauke ajiyar zuciya Ramlat ta yi, ranta har sannan babu dadi haka ta gyara zaman mayafin abayarta maroon ta fita rike da kwandon abinci. Idan ka ganta ba za ka ce ta haifi yara har uku ba, Allah Ya yi mata baiwar jiki mai kyau kuma wanda ya samu kulawar da ta dace.
Har ta iso asibitin da Amrah suke ba ta cikin walwalarta. Ɗahiru ta soma kiciɓus da shi a barandar emergency, suka gaisa ya fadamata lambar dakin sannan ya fita. Ta karasa, Amrah na kwance tana bacci sai Umma a gefe. Ta karasa suka gaisa da Umma.
"Wai, gaskiya kin yi kokari, ana wannan ruwan kika fito?"
Murmushi ta yi.
"Umma ai dole ne, ƴar uwata guda ba lafiya fa."
Ƴar dariya Umma ta yi.
"Kinga da sauki ma, likitan ya ce wai Malaria ce kuma kinsan ba'a son Mai ciki da ita, amma yanzu Alhamdulillah. Ba ta jima da samun baccin ba ma."
Jinjina kai Ramlat ta yi tana maida dubanta saman fuskar Amrah, duk ta ajiye wani kumatu.
"Allah Ya bata lafiya."
Daga nan ta ajiyewa Umma kwandon suka shiga hira kadan-kadan. Sun kai kusan mintuna sha biyar kafin Amrah ta farka.
"Ya jikin?"
Umma ta furta tana dubanta. Gyada kai ta yi tana kokarin miƙewa zaune.
"Alhamdulillah, kan ya sauka ma."
Yanda ta furta ma ka san ba lafiyar. Suka yi mata sannu. Da taimakon Ramlat, ta shiga banɗaki ta yi alwala ta wanko baki. Suka dawo ta zauna, Ramlat da kanta ta zubamata farfesun naman ragon da ta kawo wanda ya ji karas da ɗankali. Ta haɗamata shayi sannan ta haɗa na Umma, itama ta zubamata farfesun.
Suna ci su na taɓa hira. Ruwa na tsagaitawa Umma ta wuce gida da zummar za ta turo kanwarta (ita Ummar), Magajiya ta zo ta zauna da ita.
"Ya na ganki wani iri?"
Amrah ta watsowa Ramlat tambaya tana dubanta. Murmushin yaƙe ta yi.
"Ba komai."
Girgiza kai Amrah ta yi.
"Karya ne wallahi. Dama shiru nayi don Umma na wurin amma tun da na dora idanu a kanki na gane akwai matsala."
Shiru Ramlat ta yi kafin kuma ta soma fitar hawaye, a yau dai zuciyarta ta motsa da kewa mai yawa na Aliyunta. Da ace za ta rasa duk abinda ta mallaka don kawai Allah Ya ba ta damar ganinsa su yi magana ko sau daya ne, da tuni ta aikata hakan. Sai dai kuma ita mutuwar gaskiya ce, barin duniya ce ta har abada da babu dawowa sai dai ka je ka tarar.
"Lafiya kuwa?"
Cewar Amrah kusan hankali a tashe, ganin tana neman jefa mai juna biyu cikin matsala ta yi saurin dauke hawayenta ta hau murmushin yaƙe.
"Ke ba fa wani abun tada hankali bane."
Nan ta kromata dukkan abinda ke faruwa, murmushi Amrah ta yi. Ta lura ba maganar kai yaran gidan kakanninsu ne tashin hankalin ƙawarta ba sai maganar auren da ake budemata wuta a kai.
"Yanzu don Allah Ramlat kin fi kaunar ki yi ta zama haka ba aure? Kina zaton hatta Abba idan ace yau yana doron ƙasa zai yi murna da zamanki haka? Ko a tunaninki Aliyu zai yi farin ciki da zamanki haka babu aure? Wallahi kin ji na rantsemaki cikinsu babu wanda zai so ki ƙare rayuwarki a haka. Kema fa mace ce, a karon kanki sai dai ki ɓoye, kinsan cewa kina bukatar auren. Kina son wanda zai kula da ke da rayuwarki."
Amrah ta ci gaba da kwantarwa Ramlat hankali ta hanyar nasiha da rarrashi. Tun Ramlat na jin haushin maganganun har ta soma gane dagaske duk abinda ta fadi babu ƙarya ko sharri a ciki.
"Batun yara kuwa kema kinsan ba ki isa hanasu zumunci da dangin mahaifinsu ba koda su din ba sa ta su."
Murmushi kawai Ramlat ta yi a nan.
"Ke ni ina Muhibbat ne? Kwana biyu na ji ta shiru a WhatsApp."
"Tana nan, ko juma'ar da ta wuce mun gaisa. Ta yi rashin lafiya kwana biyunnan wai."
"Allah Ya bata lafiya." Cewar Amrah.
Zuwan Baba Magajiya kanwar Umma ne ya ba Ramlat damar yi musu sallama ta tafi. Yayyafi-yayyafi ake yi garin ya yi luf-luf da sanyi mai sanya nutsuwar zuci.
Tana tafe tana tauna zantukan Amrah har ta isa ga motarta.
***
YAKASAI..
Kanta kamar ya tsage biyu, bakinta ya yi mata nauyi yayinda ta ƙurawa Kawu Bello idanu don ji take kamar babu sauran laka a jikinta. Ta rasa ma me za ta ce, ta kasa fahimtar idan bayanan suka dosa. Batun dai zai bayar da ita ga CHAIRMAN ALIYU DIKKO ya fi komai ba ta mamaki da kuma dariya.
"Kin yi shiru kin tsuramin idanu kamar wani sa'anki?! Sarai kin ji ai abinda na ce! Mun gaji da zubamaki idanu, ke ba ki kawo wani kin ce kina sonsa ba, kuma ke ba ki ba masu sonki dama ba! Toh na bayar da ke ga Chairman, zai soma zuwa hira wurinki ku fahimci juna. Nan da sati uku ma zan dauramaku aure."
Ya ƙarashe yana fitar da wani huci har da muzurai, bakin ciki ya sa hawayen ma kasa zubowa. Wato Chairman shigo-shigo ba zurfi ya yi mata kenan? Ta ya akai ma ya san gidan kakanninta?
"Ki je ki saurari zuwansa cikin satinnan, saura kuma wannan karon kamar yanda kika nunamana a baya, yanzun ma ki nuna ba mu isa da ke ba. Dama ai mai hali ba ya fasa halinsa. To mu zuba da ke."
Wasu zafafan hawaye suka zubomata, ta kasa duban Kawun har ya mike ya bar mata dakin. Jiki a sanyaye ta share hawayenta, ta mike ta koma sashen Dada. Nan ne ta samu Dada ta shiga kwantar da hankalinta da hanyar nasiha da nunamata muhimmancin auren a gareta. Ita dai ji ta yi gidan duk ya isheta, sallar la'asar kawai ta gabatar kafin ta yiwa Dada sallama ta yi ficewarta.
A zauren suka yi kiciɓus da Kamal.
"Ashe Ramlat arzikina kika raina ban sani ba, kin nunamin ba za ki iya aurena ba saboda a gidanmu ba'a sonki, yanzu ai gashinan da wannan maigidannaki ya fito kin kawoshi har ya ga Kawu. Ki dai bi a hankali duniya ce, ta fi bagaruwa iya jima!"
Yana kaiwa nan ya gifta ta ya wuce, ta bishi da kallo sannan ta fice, a hanyar tana tafe tana hawaye sosai. Komai ba ya mata dadi, wannan ne yasa ta zaɓi kaɗaicewa ita ɗaya ba tare da kowa a kusa da ita ba. Wani Rainbow Park ta je, wuri ne mai karancin hayaniya, mutanen da ke a wurin tsilli-tsilli, ba ruwansu da harkar kowa. Wannan ne yasa ta zaɓi can wurin da za ta je ta samu nutsuwar zuciya.
Cikin wata rumfar kara ta nufa inda aka jera kujeru, iska mai dadi wurin ke bayarwa. Akwai ƙarancin jama'a a Park din adalilin ruwan da aka yi.
Tunani kawai take tana fitar da hawaye