Showing 90001 words to 93000 words out of 230725 words

Chapter 31 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1368

saduwa da shi ba a rayuwa."

Ji ta yi gabanta ya fadi, ta daure fuska gami da harararsa.

"Bana son irin wadannan kalaman naka. Kana magana kamar wanda ya ga mutuwa."

Ta ba shi dariya sai ya murmusa gami da shafa fuskarta ya sumbaci hannunta dake sarƙe da nashi.

"Ke kuma ba kya so ko me? Malam ya cemin hakan na karawa Bawa imani. Kinga yanzu ko ba komai mun samu lada. Ke tsaya ma, sai fa ki ce za ki yi aure idan na mutu ko? Duk wannan tarairayar wani za ki yiwa? Caɓ!"

Maganar ta ba ta haushi, fisge hannunta ta yi ta dauki littafi ta dauka ta shiga  makamishi a kirji.

"Bana so! Bana so! Ka daina yimin wannan zancen."

Ya riƙe hannuwanta gami da jawota jikinsa yana dariya.

  "Allah Ya huci zuciyarki toh. Na tuba, ai mutuwar ma sai dai ta daukemu tare In sha Allah. Sha kuruminki."

Sati uku da wannan maganar....

***
   DUK MAI RAI...

Ranar juma'a wanda ya kama acikin goman farko na azumin Ramadana, tun tashinsu take jin wani irin nauyin jiki, haka kawai ta ke jin babu dadi daga yanayin kallon da Aliyu ke bibiyarta da shi. Daɗin daɗawa, duk inda ta sanya ƙafa yana biye da ita, idan ta yi magana sai ya koma wurin yaransa wanda tuni ya cire kunya ya je gidan Hajiya ya kwaso su.

"Abban Ummi, lokacin sallah ya yi, ka tashi ka je tunda yau dai ka ƙi kasuwar."

Ya sauke Ansar daga saman cikinsa ya mike zaune. Daga shi sai jallabiya doguwa. Dan guntun tsaki ya ja yana murmushi.

"Yau din ne ganinan dai Baby. Jikin babu dadi kamar dai mai fama da zazzaɓi."

Ya ba ta tausayi.

"Toh ko za ka karya azumin ne?"

Girgiza kai ya yi lokacin da ya mike.

"Haba dai? A'a. Kedai ƙatuwar gandiya ki yi ta shan abinki, daga baya na sha dariyar ramuwar da za ki yi."
Ta ɗan harareshi kafin ta dubi su Ummi.

"Oya ku zauna nan ina zuwa."

Daga nan ta mara mishi baya zuwa dakin, wanka ya shiga don haka ta fiddo mishi farar shadda da hula. Yana fitowa ya shiga shiri.

"Ya kamata muje Daura idan kin haihu."

"Toh." Ta ba shi amsa gami da ƙarasawa ta shiga taimaka masa wurin shiri. Kallonta kawai yake bayan ya sanya kaya tana sharce mishi gashi da comb. Jikinta ya yi sanyi da kallon, ta hura mishi idanu.

"Wai lafiya Abban Ummi?"

Ya sauke ajiyar zuciya.

"Ba komai. Bari na gaggauta tafiya ko ya ya na samu huɗuba."

Ta amsa da toh, ta dauki darduma ta feshe da turare ta miƙa mishi, har kofar falon suka yi mishi rakiya. Ya dawo da baya ya dubeta.

"Kinsan me za ki dafamin yau?"

Kai ta girgiza.

"Ɗanwaken nan mai ɗan karan daɗi."

Ta yi dariya.

"Mutum ya yi azumi ya nemi ɗan wake? An shiga uku da wannan dan waken."

"Kema kinsan ina sonsa."

Ta gyada kai tana dariya, ita kuwa ta san yana son dan wake, har tayata sakin ɗanwaken yakan yi.

"Sai na dawo."

Ta amsa gami da yi mishi addu'a kafin ta koma ciki.

***
   Tun tana kallon ƙofa har karfe uku, kwakwalwarta ta bata ya biya wani wurin daga masallaci hakan ne yasa ta kwantar da hankalinta ta ci gaba da shirin kayan shan ruwa. Ba ta jin dadin jikinta dauriya kawai ta ke, da ace ta cika watanni tara cif, da sai ta ce naƙuda ne duk da cewar yanzun ma za ta iya haihuwa don sati kawai ya rage ta shiga watanni tara.

Kofar gidan da ake kwankwasa ne yasa ta saurin baro kicin din da murnarta ta fito, jikinta ke bata Aliyun ne sai dai ta yi mamakin dalilin da yasa bai tafi da nashi mukullin ba.

Maimakon Aliyun, sai ta ji muryar makwafcinsu Baban Maryam.

"Baban Maryam ina zuwa."

Ya amsa da toh, ta koma ciki ta dauko katon hijabi ta rufa, kirjinta na bugu, dakyar take jan ƙafa har ta karasa ta bude. 

"Amm, dama lambar wayar Malam nake so."

Ta gane Malam, mahaifin Aliyu. Ba ta yi mamaki don yasan waye Malam ba saboda kusancinsa da Aliyu a unguwar ya fi na sauran makwabtan. Dafe kirji ta yi.

"Lafiya?"

Murmushi ya kakalo.

"Lafiya kalau Alhamdulillah. Wata ƴar magana zamu yi."

Ta ɗan yi shiru, kamar ta tambayi mijinta sai ta ga rashin kyautuwar hakan. Komawa ciki ta yi ta dawo da wayarta ta bude lambar hannunta har rawa yake yi ta miƙa mishi ya kwafe. Godiya ya mata sannan ya wuce, dakyar ta iya rufe kofar.

Shi kuwa Baban Maryam gidan ya shiga a gaggauce ya nemi matarsa Hajara ta je ta zauna tare da Ramlat don Aliyu ya rasu a masallaci. Allah Ya taimaka tare suka tafi kuma sun samu zama cikin masallacin. Kuka Hajara ta sanya gami da salati. Ya yi saurin dakatar da ita.

"Ya isa don Allah kar ta ji ta razana, yanzu yana can mun kai shi asibiti don a tabbatar ko mutuwar ce. Ta gyada kai sannan ta rarumi Maryam ta goya a baya ta fice gidan Ramlat.

***
Ramlat na ganinta sai ta kara rudewa, dakyar Maman Maryam ta iya danne kuka da damuwarta ta shiga jan ta da hira da dariya kamar gaske. A karshe ta samu ta ɗan sake sai dai bini-bini za ta dubi wayarta, a karshe da ta gaji  ma duban Maman Maryam ta yi.

"Wai ke kam ba ki da aiki yau ne? An fa yi la'asar. Ki tashi."

Tausayinta ya kama Maman Maryam, tun zuwanta ta hangi damuwa tsantsa a saman fuskarta. Tasan ko ba komai jikinta ne ya bata. Maman Maryam ta daure ta harareta, za ta bada amsa kenan aka shiga kwankwasa kofar gidan. Kusan ma sakin ludayin miyar ta yi don yanzu a ɗan karamar cylinder na gas take girki, Maman Maryam ce ta karasa ta kwashe mata sauran ɗan waken ta kashe wutar. Ta bi bayanta tana salati don tasan yau kam mai faruwa ta afku, rabuwa ta har abada ce ta samu Ramlat da Aliyunta.

***
"Hajiya? "

Abinda ta ce kenan da mamaki ƙarara, idanunta suka cicciko da kwalla, ko'ina na jikinta ya fara rawa.

Hajiya ta shigo gidan sosai sai Umman Amrah. Ta ja hannunta suka shiga ciki ba ta ko tsaya amsa tambayoyin da Ramlat ke jifansu da shi ba.

"Meyafaru Hajiya? Kin yi shiru. Ki fadamin. Umma menene?"

Babu mai amsawa.

Sai da suka shiga ciki suka zaunar da ita suka yi mata doguwar nasiha da ya sanyata  kuka, Abba kawai ta shiga tunowa. A karshe suka sanarmata labarin mutuwar Aliyu. Abin mamaki sai kukan ya tafi, ta shiga murmushi, murmushi sosai.

  "Ramlatu, kinji abinda na ce?"

Hajiya ta fadi a ɗan tsorace don a zatonta ko taɓuwar hankali ce. Ramlat ta girgiza kai ta a murmushi gami da jan majina.

"Ya yi mutuwar da bai kyautu na zubar mishi da kwalla ba ai, ya yi irin mutuwar da kowane DAN ADAM zai so ya samu irinsa. Da azumin Ramadan a bakinsa, cikin dubban jama'a, a hanyar bautar UbangijinSa. Idan ba godewa Allah ba, na yiwa Aliyu addu'a, me ya kamata na yi?"

Wannan tawakkalin nata ya raunana zukatansu, ta kuma burgesu ainun.

Suka wuce da ita zuwa gidan iyayen Aliyu inda anan aka kai gawar Aliyun. Abulle tun da aka yi mutuwar tana kwance ba ta san inda kanta yake ba. Maza da mata kuka ake yi akan rashin Aliyu. Aliyun da dama a cikinsu suka tsana. 

  Tuni an mishi sutura, kowa kallonta yake da mamakin yanda ta daure. Da katon cikinta ta durkusa gaban gawar Aliyu ta yi mishi addu'a sannan aka ɗaukeshi a makara aka fita da shi. Wannan fitar ce ta daga hankalinta, ta sani idan aka tafi an tafi kenan. Ba za ta ƙara ganinsa ba, ya bar gidan kenan bari na har abada. Tun tana ganinsu daidai har ta soma ganin bibbiyu kafin ta zube a wurin.
   Koda ta farka bayan an yayyafamata ruwa, sai ta farka da wani irin azababben naƙuda. Tuni aka rarumeta zuwa asibiti.

  A wannan yanayin Ramlatu ta haifi ɗanta namiji.

***
  Rashin Aliyu babban rashi ne da ba za ta taɓa mancewa ba. Ta yi rashin Abba, ta zo ta rasa Aliyunta. Mutane biyu mafi girma da daraja a gareta. Cikinsu ba wanda bai taka rawa a rayuwarta ba. Sai a sannan ta yi kuka iyakar yinta, ta rungume jaririnta a jiki tana jin kamar ta hadiyeshi don so da kauna. Kamanninsa da Aliyu kamar an tsaga kara an karya, hatta da hasken fatar Aliyu ba abinda ya bari. Hirarrakin da ya dinga yi mata a kwanakin ne ya shiga dawomata, ta kuma fahimci ba na komai bane face bankwana. Irin ba kwanan da idan an tafi ba za'a ƙara waiwaye ba. Ba za'a kara dawowa ba sai dai a je a tarar.

"Sunansa Affan."

Abinda ta ce kenan tana duban Umman Amrah. Umman ta yi mamaki don ta dauka sunan mahaifinsa zai ci, sai dai ta gyada kai ta karɓi yaron ta kaiwa Malam don ayi mishi huduba. Ita kuwa sunan da Aliyun ya zaɓarwa ɗan kenan tun kafin ya zo duniya, ba ta ga dalilin da zai sa ta sauya ba.

  Tun daga lokacin rayuwarta ta dawo sabuwa, tun daga nan komai ya sauya. Ta koma mai yawan daure fuska a maimakon sakinsa, ta zama wata shiru-shiru irin shirun da sai ta so take sakin jikinta ta yi magana da dariya. Har ta kammala takaba ta koma makaranta ba ta sauya zani ba. Hajiya ta rungumi jikokinta kamar ita ta haifesu, nasiha da ban baki shi ne abinda take yiwa Ramlat koyaushe.

Dakyar ta soma sakin jiki har ta kammala karatunta ta hadu takardunta, a sannan ne kuma aka yi bikin Amrah suka bar ƙasar da mijinta. Baba Dakta da kansa ya yi cuku-cuku ya samarmata aiki a ma'aikatar kula da haraji ta ƙasa na branch dinsu dake Kano. (KIRS)

  A duniyar Ramlat, babu aure, babu kula kowane namiji da sunan soyayya. Ta hakura da kowane jin dadin rayuwa, ta gwammace ta kula da yaranta har su girma su zama wani abu a rayuwa. Wannan tasa ba ta taɓa bada fuska ga kowane namiji ba. Ta kame kanta, ta kuma rike mutuncinta. Duk nacin mai naci sai dai ya hakura.

Haduwarsu ta farko da Hilal bayan shekarun da suka biyo baya, abinda ta soma roƙonsa shi ne gafara. Ta nemi gafararsa akan laifinta kafin ta nemawa mijinta gafararsa. Ranta ya yi haske ta kuma yi godiya da jin cewar ya yafe tuntuni. Daga lokacin ne kuma ya dawo da zumunci a tsakaninsu. Tun tana kaucewa tana dauke kai, har dai ta hakura ta ɗaukeshi matsayin Yaya Munir a wurinta kamar yanda ta ke yiwa Muhibbat kallon yar uwa kuma ƙawa a wajenta.

***
   CI GABAN LABARI....
  


 

I just published "BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/z1qmOMpjFab



🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

28)

Ana saura kwanaki uku kacal bikin A'isha, Ramlat ta yi kitsonta yiri-yiri da ƙunshi. Da kanta ta ɗaurawa Ummi ƙunshi na gam bisa tilastawar Hajiya don ta rantse Ummi sai an mata ƙunshi.

"Kema dai Hajiya, wannan yarinyar za ki dinga biyewa. Ai gashinan ta ɓatan lokaci." Fadin Ramlat sadda ta ke goge ƙafar Ummi da ƙaramin tawul, lallen duk ya caɓa ya haura ba ta zauna ba.

"Ko ma mene dai ai ta yi din, ke wane irin caɓar da lalle ne ba ki yimin ba kina ƙarama?"

Dariya Ramlat ta yi ganin abin ya juyo kanta.

  Ana gobe za'a sanya A'isha a lalle suka shiga kasuwa tare da Rafee'ah, siyayya sosai suka yi na abinda ya rage na kayan daki, maimakon su yi gida, sai suka wuce kai tsaye gidan A'isha dake unguwar Badawa layout suka kai. Anan suka iske masu aikin wuta na ta fama. Sai da suka tabbatar komai sun saka yanda ya dace sannan suka baro gidan. A kan titin Rafee'ah ta saki baki ganin yanda Ramlat ke tuƙi kamar mace.

"Ke Ramlat, ki yi hankali da ni wallahi kar ki kashe Baban Daddy ni."

Dariya Ramlat ta yi sadda ta sha gaban wata Crv-Honda ta yi gaba.

"Kin cika tsoro wallahi, ina nake gudu?"

"Kinga ko? Kin gani ki daina wannan over-taking din, ki rufan asiri nidai. Shiyasa na tsani zama gaban mota ko a tafiya ne, haka kawai ki ƙashe ni lokacina bai yi ba."

Dariya sosai Ramlat ta yi daidai sadda mai Honda dinnan ya taho da mugun gudu ya sha gabansu.

"Wancan dai ya dauka tsere muke da alama, toh ba.."

Ai Rafee'ah ba ta iya ta ƙarasa ba ganin yanda itama Ramlat ta fisgi motarta ta kara shan gabansa tana mai duban motar ta gilashinta tana dariya. Ina wuta Rafee'ah ta jefata, nan ta shiga fada kamar ta ari baki. Wai tana mace tana wasa da rayuwarta.

"Shikenan naji na daina." Abinda ta ce kenan har sannan dariyar mugunta take. Junction din state road ne ya tsayar da su, anan ne suka tsaya dab da motar. Kamar ance su waiwaya, gaba daya suka dubeshi baki sake, an ci sa'a kuwa ya sauke gilashin.  Mamaki suke da murmushi gaba dayansu, shi kuwa dariya yake musu.

"Hilal?" Fadin Rafee'ah wanda ta fi kusa da inda yake. Suka yi dariya a tare. Ita kanta Ramlat ta sha mamakin ganin shi ne. Ba su san shi da wannan motar ba.

"Kai Maman Affan, wannan gudun naki gaskiya zai sa mu rabaki da motarnan." Ya fadi yana duban Ramlat bayan sun gaisa da Rafee'ah.

"Bar ta, ai ba ka ji yanda ƴan hanjina suka kaɗa ba wallahi. Sai da na gwammace bamu fita a motar ba, dama sai da ta ce mu hau ɗan sahu ni kuma na gwammace na zuba mai mu tafi a motarta."

Ita dai Ramlat kauda idanunta ta yi tana murmushi da kuma gujewa kallon da Hilal ke watsamata.

"Yanzu ina ku ka yi?"

Ya fadi sadda aka soma yi musu horn ta baya, shaidar an bada hannu. A gaggauce Rafee'ah ta ce.

"Gida muka nufa."

Kai kawai ya gyada ya fisgi motarsa, itama ganin haka ta ɗan bada wuta kadan.

"Allah Sarki, wannan bawan Allahn har yanzu fa sonki yake."

Ta yi kamar ba ta ji me Rafee'ah ke fadi ba, karshe ma ta ɓige da kunna muryar Umar M Shareef cikin waƙarsa na Zan rayu da ke.

Ji ta yi Rafee'ah ta kashe hakan yasa ta dubanta sannan ta kauda kai ta maida titi.

"Wato ba kya son maganar ko? Ke abu baya wucewa ne Ramlat? Idan shi ya manta abinda kika yi mishi ya dawo yana bibiyarki, ke kuma a wa da ba za ki mance Aliyu ba ki..."

"Don girman Allah mu bar maganar. Ina haɗaki da Allah ki yi shiru."

Ta yi ta roƙon Rafee'ah har abin ya dauremata kai, karshe Rafee'ah ta sauke ajiyar zuciya.

"Ai shikenan, rayuwarki ce."

Ba ta tanka ba illa dai har suka isa gidan ba wanda ya kara magana. Ta lura kowa ya tashi burinsa ta koma gidan Hilal alhalin ita tasan ba mai yiwuwa bane. Ba ma Hilal ba, auren gaba daya ta hakura da yinsa. Ai idan mace za ta iya rike kanta da mutuncinta shikenan. Wannan shi ne tunanin Ramlat.

***
Suna shiga kai tsaye wanka kawai ta yi ta sauya kaya sannan ta fita tsakar gidan inda mata ke aiki, wasu aikin sinasir wasu kuwa suna yayyanka albasa. Kowa dai da aikin da ya ke yi, ta wuce kai tsaye cikin sa'anninta su Naja'atu su Maryam. Ana yi ana hira da shewa. Wannan ya fi komai yi mata dadi, ta ji wata irin nutsuwa. Yaran duk suna falon Hajiya su na wasa. Hira suke na abinda ya danganci magungunan mata. Kowacce da kalar wanda take koɗawa a cewar ta ta ga aikinsa sosai.

"Ke Maryam, bari na fadamaki wani abu, wallahi kinji rantsuwa ta Allah, wanda na samu wajen Ƴar Maraɗi ba karuwai ba, daidai da masu kishiya, miji bai isa ya haɗa matsayinsu ba. Abin nufi komai naki zai zama daban, za ki bambanta da kowace mace a wurin miji."

"Kuma shiga hakki fa?"

Ramlat ta tsinci kanta da jefawa Sa'adah ƴar Daura wacce yanzun aure ya maido Kano, tambaya.

Sa'adah ta taɓe baki.

"Amma dai ai banda kishiya ko?"

"Ke Sa'adah, duk da haka fa ba daidai bane. Wasu magungunan ma duk haram ne amma mata son zuciya ya rufemana idanu."

Fadin Naja'atu kenan. Nan dai suka ci gaba da tattaunawa game da magungunan da mata ke amfani da shi duk don su samu gurbi a zuƙatan mazansu.

"Maman Affan, tun dazu wayarki ke ta ringing."

Ramlat dake hawaye saboda  albasan da ta ke yankawa, ta bude idanun dakyar tana kallon wata ƴar uwarsu Dije da ta damƙa amanar wayarta a hannunta. Karɓa ta yi tana sharce fuska gami da dubawa. Lambar baƙonta ne na Mall, ta yi mamakin dalilin kiran kuma a karo na biyu. Me kuma zai ce da ita? Take tambayar kanta, ta share kawai ta koma bakin aikinta, ba jimawa wayar ta ƙara daukar ƙara. Ganin shi ne dai yasa ta miƙewa ta bar wurin tana ji suna mata tsiyar wai ta gaji da nuƙu-nuƙun ta faɗa tarkon wani.

"Assalamu alaikum."

Shi ne abinda ta ce, maimakon ta ji muryarsa sai ta ji muryar yarinyar ya doki kunnuwanta.

"Waalaikumussalam wa rahmatullah wa barakatuhu. Mami."

Dan murmushi ta yi, madadin takaicin da ta ji a farko na shiga rayuwarta da mutumin zai soma, sai ta ji sanyi jin muryar yarinyar da ba ta wuce tsarar ɗanta ba.

  "Fatima, kina lafiya?"

"Lafiya kalau Mami. Ga Dada."

Kafin Ramlat ta ce wani abu, tuni ta damƙawa Dada wayar. Sai murya ta ji. A ladabce suka gaisa ta kara da fadin.

"Ki yi hakuri fa kin hadu da rigimar Fatima, tun dazu ta matsawa ubannata sai ya kiramata ke kun gaisa wai ita dai tana sonki wataran ya kaita ta ganki."

Dariya Ramlat ta yi.

"Ba komai Dada." Ta fadi kamar yanda ta ji suna kiranta. Suka ƙara gaisawa sannan suka yi sallama ta katse wayar.

Kallon screen din ta tsaya jiki a sanyaye. Tunaninta ya tafi ga mahaifin Fatima wanda kamanninsa tamkar an tsaga kara an karya da Mijin Hajiyar da suka zo ma'aikatarsu. Kodayake, ba nan ne haduwarsu ta farko ba sai dai ya tsayamata a rai. Tsayuwar da kawai so take ta san alaƙarsu da Baban Fatima. Ta kuma sani, ba ta da wani dalilin da za ta fake da shi ta yi tambayar.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login