Showing 111001 words to 114000 words out of 230725 words

Chapter 38 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1071

burgeshi karshe. Tana jin fitarsa ta mike da azama ta hau sama tana nishi da gyara ɗaurin zaninta da ke neman faɗuwa. Sai da ta soma fiddo ruwan maganinnan ta faɗa banɗaki ta yi tsarki da shi tas ta maida cikin jarkar sannan ta maidashi maɓoyarsa. Daga nan ta sanya layar a jaka ta dauki mukullin motarta ta fita.

  Maigadin dai ba abinda ya shallesa, tashi ya yi ya bude ta fice ya maida ƙyauren gida.

Tuƙinta take tana mai jin wani ƙarfin gwuiwa na zuwarmata wanda ke ƙara sanyata jin ba za ta fasa abinda ta yi niyya ba. A farko ta dauka lamarin Ramlat mai sauƙi ne da za ta iya maganceshi da hannunta, gari ne ba za ta bari ba, asalima ba za ta taɓa aikata yin wanka a tsakar dare ba kuma ba don ba za ta iya bane, sai don a ganinta asarar lokaci ne don babu abinda zai sa ta bar garin saboda Ramlat. A cewar ta Ramlatu ta yi kaɗan, gwara dai ta yi wanda za ta mallake Hussein yanda fita ma sai da izninta zai yi. Kallon sararin samaniya ta yi yanda ake zuba walƙiya. Ta ƙara maida hankali ga tuƙinta tana sharara gudu kamar wata namiji.

Ba ta tsaya ko'ina ba sai a wani filin Allah da ba gida gaba babu a baya. Gari sai walƙiya ake yi da iska mai daɗi. Wani rami ne ƙato wanda a ƴan unguwar basu komai da shi sai aiken almajirai su zubarmusu da shara sai kuwa ƴan shaye-shaye da kan zo su maida wurin matattara. Babu tsoron jinnu balle shaiɗanu ta nufi bolar gadan-gadan.

Tsammaninta babu kowa a wurin saboda yanayin iskar da ake da kuma walkiya, a zatonta za ta yi aikinta ta kammala kamar yanda Isuhu ya ce kar wanda ya ganta, sai dai tana hawa saman bolar gami da kokarin zura layar, wata fitila ta hasketa ga kuma hasken walƙiya.

"Kaii...wa..ye anan?"

Daga yanayin maganar za ka san ɗan maye ne.

Cikin Hajiya ya ɗuri ruwa, ba ta yi aune ba wani ruwan hawaye ya tahomata, ba wai tsoron ɗan mayen ne ya shigeta ba illa ɓatamata aikin dubunnan da aka yi.

"Allah Ya isa Batool!"

Abinda ta ce kenan a fili don da shawararta ta zo wannan bolar, sam ba nan ta so zuwa ba.

Hankali a tashe ta sauko duk da hakan sai da ta soke layar. Daidai nan ɗan mayen hannunsa riƙe da wuƙa ya zagayo yana ƙara kallonta sosai. Zobunan gwal ne a hannunta duk da ta saka mayafi bai hana a gani ba. Da sauri ta ce.

"Kana so? Gwal ne?"

Wata dariya ya yi yana rangaji. Ta saba karawa da irinsu. Kafin ya kai ga magana ta ciro ta damƙa masa.

"Kai Hajjaju! Kin san homular! (Formular)"

Ita dai haushinsa take ji kamar ta shaƙeshi,  ta fice a wajen yana ta mata kirarin da ba ta ma fahimta don a hargitse ta ke.

***
Ga Ramlat kuwa, kasa sanarwa Hajiyarta ta yi akan abinda ya faru a wurin aikinsu ta yi, ta dai sanarmata dalilin kiran da Hisham ke mata.

"Toh kinga wannan ma kadai ya isa ki yiwa kanki faɗa ba ruwanki da shiga harkarta ballantana har ta kaiku da samun matsala. Àllah Ya rufa asiri dai."

Daga haka suka rufe zancen.

***
Hussein ya yi shiru ya kuma baza kunne yana sauraron Hisham har ya kai aya, fuskarsa kadai ka kalla za ka ga damuwa da ɓacin rai kwance.

"Kenan duk abinda nace ba ta ji ba?" Fadin Hussein a kausashe.

"Ramlat ko wa?"

Hisham ya nemi sani. Girgiza kai kawai Hussein ya yi kafin yace.

"Ka bata hakuri, ka kuma..."

"A'a Malam, wallahi na gaji. Nima fa ina da aikina ba masinja ba ne. Haka kawai sai a takuran da kaiwa da kawowa wurin faɗar saƙo. Toh na gaji fa, ana cin lokacinmu nisa Princess. Haba, aure ko wata ba'a yi ba an ban sabon aiki?"

Harɗe hannu Hussein ya yi a kirji yana dubansa fuska dauke da murmushi, ya maida idanunsa sararin samaniya yana ganin yanda ake zuba walkiya da kuma iska. Ba ta

"Give me her digits."

Ba Hisham ba da mamaki ya kusan kaiwa ƙasan gwuiwa, hatta shi ɗin da ya nemi lambar sai da ya ji faɗuwar gaba, ya nemi tsoro da fargabar abinda hakan zai haifar ya rasa, ji yake kamar akwai abinda ke danneshi.

"What did you say?" Hisham ya faɗi kusan a birkice. Maimakon ya amsa sai ya fiddo wayar ya ajiye saman mota ya bude murfin zaman direba ya shiga ya soma kokarin tayarwa. Ganin haka Hisham ya dauki wayar bayan ya fiddo tasa wayar, hannunsa har rawa yake yana mai jin wani farin ciki, fatansa yake so ya tabbata. Lambar Ramlat na Mtn da Airtel duka sai da ya ɗuramasa, kowanne ya ɗan danna kira amma sai ya kashe bai bari ya shiga ba, so yake dai lambobin su fada cikin Log.

Ta cikin gilas ya miƙa masa wayar.

"Shegen sama, gashinan ba ruwana kuma idan Hajiya ta gani, wallahi kar ma ka ambaci sunana. Ban yi saving ba, idan ka ga dama ka sanya Rabe a kan sunan ko Talle Mai Wanki."

Dariya sosai Hisham ya ba shi, suka hau yi can kuma ya ɗan lumshe ido ya bude.

"Zan rama ɗaya bayan ɗaya wallahi, ka yimin duk abinda ka ga dama yanzu. Sannan ni ba da wata manufa ma nemi lambar ba kar ka yi zaton akwai wata bayan Zeenat, wai don na ragemaka zirga-zirgar ce. That's it."

Hisham dai dariya ya yi bai ce uffan ba. Suka yi sallama ya ja motar ya nufi Rijiyar Zaki.

***
Washegari direba ta sanya ya kai yara makaranta, ko bakomai tana son yin baccin safe kadan sannan ta yi shirin Ofis. Ga garin ya yi luf sakamakon ruwan da aka samu a daren jiya. Wannan ne ya bata damar komawa bacci mai dadi bayan tafiyarsu. Ba ita ta farka ba sai da wayarta ta Soma ringing.

Duk yanda ta kai ta share hakan ya gagara don mai kiran bai yi ɗaya ya haƙura ba. Da wani irin takaici ta mike ta ja tsaki kafin ta duba sunan dake yawo sama screen. Hilal. Ɗagawa ta yi da sallama.

"Ayya na tasheki a bacci kenan. Shikenan ma yi magana anjima. A yi bacci lafiya."

Bai jira cewarta ba ya katse kiran, murmushi ta ɗan yi ta kara maida kanta cike da kasala. Wayar dai ta ƙara ringing, a dolenta ta miƙe zaune. Lambar Salisu na ofishinsu ke yawo saman screen. Ta ɗaga da sauri.

"Ramlat, kina ina ne?"

"Haba Yallaɓai, ba sallama ba komai?"

Ƴar dariya ya yi sannan ya yi sallamar suka gaisa, ya ɗora.

"Kiyi hakuri, abin ne naga gwara na sanar da ke shiyasa shaf na mance da wannan batun."

Cikin rashin nutsuwa ta zuro kafafunta ƙasa.

"Lafiya Salisu?"

"Ji nayi Oga Ɗalhatu na maganar an miki sauyin wurin aiki, za ki koma ɓangaren Chairman, a matsayin secretary ɗinsa."

Kirjinta ya bada dam! Koda ace ranta a ɓace yake jiya, ba ta mance irin shu'umin kallon da Chairman Aliyu Dikko ke watsamata ba. Ba ta son ta munana zato game da abinda ba ta da tabbacinsa kamar yanda take ganin baƙin jama'ar ma'aikatar da ke gulmar Chairman din da cewa ɗan iska ne. Don haka sai ta kyautata zato.

"Ko kina da masaniya ne Ramlat? Naji ba ki ce komai ba?"

Dan murmushi mai sauti ta yi.

"Banda ka faɗi bani da labari Salisu. Yanzu ai zan shigo ofishin In sha Allah. Sai na ƙaraso."

Daga haka suka yi sallama, shiru ta yi na ɗan lokaci, so take ta gani ko za ta iya fahimtar manufar yin hakan, sai dai duk iyakar tunaninta ba ta gane komai ba. Tasan dai ko mene ba alheri ba ne tunda mutumin Hajiya ne.

Miƙewa ta yi ta shiga wanka, a gaggauce ta shirya cikin doguwar rigarta na Atamfa, mai kawai ta shafa kafin ta zura hijabinta dogo ta dauki duk abinda take ɓukata ta fito. Sai a sannan ta tarar da missedcalls har uku duk daga mutanen Department dinsu ne. Ba wanda ta bi, ta karasa ta gaida Hajiya dake zaune suna hira da Ladidi.

"Yau dai babu niyya. Daga jin sanyin gari kin shantake."

Dariya ta ɗan yi.

"Wane sanyi? Ai da saura ruwan Hajiyarmu. Bai kankama ba tukunna!"

"Allah Ya bamu damina mai albarka dai." Fadin Hajiya, suka amsa. Ta gaidata karo na biyu kafin ta dubi Ladidi su gaisa sannan ta karya a gaggauce ta fita. Ba ta iya ta sanarwa Hajiya sauyin da aka yi mata ba, bar wa cikinta ta yi har sai ta je ta ji asalin abinda ke wakana.

***
AKWAI WATA AI just published "BABI NA TALATIN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/WcD6L9EP0ab



🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

34)

   AKWAI WATA A ƘASA...

Gaban Notice Board ta soma tsayawa, shakka babu dagaske Salisu yake, ajiyar zuciya ta sauke bayan kammala karanta bayanin sauyin da ta samu.  Sati mai zuwa za ta fara sabon duty dinta.

  "Allah Yasa hakan ya fi alheri." Ta fadi a fili sannan ta karasa cikin ofis dinsu wanda kiris ya rage ta bar shi. Bayan sun gaisa ta zauna.

"Za dai mu yi kewarki anan Ramlat, ko ba komai kin fi wasu a nan."

Fadin Oga Ɗalhatu, aka ɗan dara idan ka cire Halima da hassada da bakin ciki ya cikamata zuciya, yanda ta ke jin tsanar Ramlat a yanzun har ya fi na baya. Ta jima tana burin kasancewar mai aiki a ƙarƙashin Chairman duk kuwa da cewa hakan bai rage ko ƙara albashinta ba, amma dai tasan alhairan da ita za ta kwantar da kai ta samu wurin Chairman, ba lallai ne ita Ramlat ta yi ba.

"Ki dai bi sannu don kinsan ko waye shi."

Cewar Halima tana yamutse fuska.

"Kedai ba ruwanki, zato zunubi. Kuma kin fi kowa sanin Ramlat da halayyarta." Fadin Zuhra kenan.

Ramlat kallonta kawai ta yi ba tare da ta tanka ba, tsaf ta gama gane wacece Halima da kuma irin takun saƙar da take yi da ita wanda ita kam ba ta ga dalilinsa ba.

Da wannan damuwar ta dawo gida ta sanar da Hajiya halin da ake ciki.

"Toh ke meye naki na damuwa? Sauyi ne fa kawai, idan batun kamun kai ne ai na yarda da ke bana jinki a wannan ɓangaren. Allah Yasa hakan ya zamemaki alheri."

Ta amsa da amin.

  Bayan Magriba suna zaune tana koyawa yaranta Homework, Maigadi ya yi sallama a bakin ƙofar suka amsa. Jin saƙon wai ana sallama da Ramlat ya ba ta mamaki, ta dubi Hajiya, itama kallonta take tana murmushi.

"Ka ce tana zuwa."

Bayan tafiyarsa ta dubi Hajiya.

"Haba Hajiya, mutum da bansan ko waye ba, yanzun ai ba'a irin haka, da ace ya san ni toh ba zai rasa lambar wayata ba. Ta nan zai neme ni."

Harararta Hajiya ta yi.

"Kuma ya zama dole ki fita ba, naga alamar kin fi kaunar zama a haka babu aure, toh ya isa. Nima kamar Babanki Dakta, ba zan ƙara biyemaki ki kori masu zuwa wajenki ba. Idan ma a baya an yi bai wuce na tausayawa marayunnan ba. Tashi maza ki je."

Kamar ta yi kuka ta ce.

"To wa zai ƙarasa koyamusu?"

"Jeki, nasan duk daɗewa ba za ki wuce awa ɗaya ba. In Sha Allahu ma ba su kai ga yin bacci ba. Tunda kin sallami Affan ai da sauƙi."

Miƙewa ta yi ranta duk ba dadi, hijabi kawai ta zura ta kama hanya su Ummi na kiran a dawo lafiya, a tahomusu da alawa. Harara kawai ta watsamusu ta yi gaba ta bar Hajiya da dariya.

Sai dai me? Wanda ta gani ya matuƙar shayar da ita mamaki, sakin baki ta yi kafin kuma su yi dariya a tare. 

"Kai Yaya Hilal, yaushe ka zama baƙo a gidannan? Kuma fa ko Malam Bala bai fadamana wanda ke sallamar ba."

Dariya ya yi. Sanye yake cikin shaddarsa ruwan toka, ya karya hularnan ta zannah Bukar ta zauna caras a kansa. Yana daga cikin mota zaune a inda ya fiddo ƙafarsa ɗaya waje.

"Ke din ce sai da hakan, farko na so kiran wayarki sai kuma na fasa tunda nasan dai zai wahala ace a wannan lokacin ba kya gida. Malam Bala kuma ni na roƙeshi akan kar ya ce ni ne saboda yau zuwan naki ne ke ɗaya."

Ta ɗan sadda kai ta yi shiru, ta san tatsuniyar gizo ba ta wuce na ƙoƙi. Abu ne da ba ta jin har abada za ta iya aminta da shi.

"Ɗan zagayo mana ki zauna."

Ba tare da musu ba ta zagaya ta bude motar ta shiga, kamar yanda ya bar ƙofa a buɗe, itama hakan ta yi. Gaidashi ta soma tare da tambayar iyali da wajen iyayensa. Ya amsa mata cike da annashuwa.

"Kin ɓuya da yawa, ta ko'ina gujemin kike kamar rai da ajali. Na rasa hanyar ɓullomaki. Sai na kiraki ki share ki ƙi ɗauka, daga baya na samu text dinki wai ba kya kusa ne nayi hakuri. Anya kuwa?"

Kunya ta kamata, ashe dai ya gane. Ita kuwa dalilinta na yin hakan a ganinta mai ƙarfi ne. Kokarin nesanta kanta da shi ta ke yi ta kowace hanya don ba ta son jawowa kanta magana.

"Ka yi hakuri."

"Na yi, amma ba duka ba. Ramlat, Maman Ummi, Ansar da Affan. A karo na biyu ga Hilal nan, bai kuma zo da niyyar yaudara ba. Aure ne ya kawoshi idan har kin amince."

Ajiyar zuciya ta saki don dama ta san maganar kenan, jikinta ya yi sanyi da irin wannan soyayyar ta Hilal gareta. Ta dubeshi, shi dinma ita yake kallo babu ƙaƙƙautawa. Ɗan kauda idanunta ta yi.

"Ko da can ma ba ka zo min da niyyar yaudara ba balle kuma yanzu. Asalima ni ce na yaudareka. Ka yi hakuri Yaya Hilal. Don Allah ka yi hakuri."

Ta ƙarashe a raunane, ita sam ba ta san ta

"Ka yi hakuri."

"Ba hakuri za ki bani ba, dalilinki na guduna za ki faɗamin. Idan da wajen da na kuskuro na gyara."

Girgiza kai ta shiga yi, kwalla ta soma ciccikomata idanu. Hilal wane irin mutum ne mai matukar sanyi da hakuri? Wace irin soyayya yake mata da ya kasa ganin laifinta?

"Akwai abubuwa da dama da ya kyautu na gujeka dominsu. Ba ka taɓa yimin laifi ba, ba zan iya kallon danginka a karo na biyu ba a matsayin matarka. Bayan abinda ya faru wa kake tunanin zai ƙara kallon Ramlat matsayin matar kirki? Wallahi da kaina na faɗa, bani da kirki, ban yi halin hakuri da dattako na iyayenmu ba. Ka yi hakuri Hilal, mu ƙaddara ba'a rubuto aure tsaka.."

Ta kasa ƙarasawa saboda kunya da kuma irin hararar da ya watsamata. Can kuma ya numfasa ya runtse ido. Da ace ta san yanda yake jinta a rai da ba ta ce haka ba, a gefe guda kuma bai mance irin kalaman da iyayensa suka yi gareshi ba muddin ya ce zai aureta ko bayan ransu ne. Kansa ya yi zafi da yawa.

"Ka yi hakuri."

Ta kara nanatawa, a wannan lokacin tuni hawayen sun zubo. Ya bude idanunsa da suka kaɗa ya dubeta.

"Bana jin har abada zan manta da ke Ramlat, you are my first love. Ki daina bani hakuri, da ace zan iya da tuni na rarrashi zuciyata. Aurenki da Aliyu na dauki hakan matsayin rubutaccen al'amari wanda ba makawa sai ya faru. Albarkar auren gashinan mun gani (yana nufin yaranta), don haka ni wallahi tuni na yafe abinda kika yi gareni. Idan da naki a sannan, nima ai akwai nawa tunda ni na naace akan sai na aurekin ko ba so. Kar ki saurin yanke hukunci a kanmu, na baki nan zuwa sati kiyi tunani mai kyau, koda ba ki kirani ba, da zarar lokaci ya cika zan kawo kaina."

'Allah Sarki.' Ta furta a ƙasan ranta. Da wannan suka rabu ya bata kayan maƙulashe na alawa da biskit da ya siyowa yara. Ta karɓa gami da godiya suka yi sallama ta shige ciki.

  Hajiya zaune a falo ta a gyangyaɗi kaɗan-kaɗan, yaran sun ƙurawa talabijin idanu su na kallon Angrybird.

"Waye ne ya zo?"

"Yaya Hilal ne."

Hajiya ta mike zaune.

"Yaronnan dai dagaske ya ke yi."

Ramlat ta zauna jikinta a sanyaye.

"Na rasa ya zan yi Hajiya, ya dage aurena ya ke son yi. Na rasa hanyar ɓullomasa ya fahimci illolin da hakan zasu haifarmin a danginsa da wurin matarsa."

"Nima bana goyon bayan aurenki da shi, sai dai bamu san abinda Allah Ya ɓoye ba tunda har ya kasa hakuri ya dawo karo na biyu. Shawara ki dage da addu'ar neman zaɓin Allah, duk abinda Ya yi mai kyau ne."

Jinjina kai ta yi cike da gamsuwa.

***
A kwana a tashi ba wuya a wurin Mai Rahma, bikin Munir ya taho. Ana gobe za'a yi ɗaurin aure ƙalilan daga mutanen Daura suka iso don Hajiya ba ta yi gayyata ba duba da cewar ba'a jima da bikin A'isha ba.

  An daura aure lafiya, a daren aka yi shirin tafiya dinnerparty. Ramlat da yayyunta mata har A'isha da Amrah wacce basu daukarta bare cikinsu,  ankonsu iri daya na wani leshi peach colour. Kowannensu riga da skirt ya zauna ɗas a jikinsa.

Motarta daga ita sai Amrah don Yaya Munir ya ce babu yara. Suna tafe suna hira, anan take ba ta labarin sauyin da aka yi mata wurin aiki, ta kara da fadin.

"Tsorona daya, rashin sanin taƙamaiman manufar wannan Chairman ɗin. Ina tsoron ya kasance wani mugun abin ne."

Amrah tana taunar cingam din da ya zamemata ciki tun tana laulayi har a yanzun da cikinta ya shiga watansa uku.

"Kar wannan ya dameki, ai kinsan kanki. Daidai gwargwado kin san mutuncin kanki kina kuma karewa. Addu'a za ki yi ta yi akan Allah Ya kareki daga sharrinsa. Ba abinda zai faru amma shakka babu dai akwai wata a ƙasa!"

Jinjina kai Ramlat ta yi.

"Wallahi ko ba ki faɗa ba Amrah, ni ban taɓa ganin mace mai irin kishin na wannan matar ba."

Amrah ta ɗan muskuta.

"Af, kin ce za ki nunamin hotonsa."

Ta yi murmushi.

"Mu ƙarasa tukunna."

Daga nan suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login