Showing 36001 words to 39000 words out of 230725 words
suna tattaunawa game da biki tare da ƴan uwansa kafin ya fice.
***
Washegari da karfe hudu na yamma aka sallami Abba ya dawo gida, hakan bai hana wasu cikin abokan kasuwancinsa zuwa dubiya ba. Hajja ma ba'a bar ta a baya ba, ta dinga fadan meyasa ba'a sanarmata da wuri ba. Dakyar aka lallaɓata.
"Jiya fa aka kai shi Hajja. Kiyi hakuri don Allah." Cewar Yaya Munir da ya gaji da mitarta.
Ya mike tsaye, ya dubi Bilkisu da ta zo dubiya, sai raba ido take cike da burin sanin meke faruwa har haka, sai dai babu wanda ta ga alamar zai fadamata.
"Mu wuce."
Maganar Yaya Munir ya katse mata tunani, ta mike ta kara yiwa su Hajiya sallama sannan ta bi bayansa suka tafi. Ta saka a ranta sai ta san meke faruwa a gidan.
Bayan da kowa ya watse ne Hajiya ke labartawa Hajja halin da ake ciki, Hajja ta hau salati ta sa aka kira mata Ramlat.
"Yanzu ke Ramlatu wa zai ɓata ran iyayensa saboda son zuciya? Anya kina da hankali? Yaron da koyaushe yabonsa muke, yana zuwa har gida ya gaishemu? Inace kwanaki har Daura kika cemin ya je an gaisa?"
Ta maida akalar zancen ga Hajiya dake ji kamar ta murɗe wuyan Ramlat din kowa ya huta.
"Hakane ya je."
"Ahaf, irin wannan yaron kike so mu watsawa ƙasa a ido? To ba ki isa ba! Don ƙaniyarki a farko wani ya ce ki kawomana shi ki ce kina so?"
Maimakon ta samu goyon baya irin wadanda kakanni ke yiwa jikokinsu, sai ta ga saɓanin hakan. A barta ma ta ji da abinda ke damunta, a barta ta ji da rashin ji da ganin Aliyu. Gobe ne take da jarrabawa wanda daga shi takarda biyu ta yi musu saura su kammala duka, ko ta halin ƙaƙa a goben sai ta yi yanda za ta yi ta haɗu da shi.
Rankwashin da ta ji a ka yasa ta farfadowar ba shiri.
"Don ƙaniyarki shine ina magana kika yimin shiru?"
Ta ɗago rinannun idanunta da suka faɗa ta dubeta hakan ya yi daidai da zubar ruwan hawayenta, to me za ta ce? A yanzun wa ya ke ta ita a gidan? Wa ke damuwa da ci ko shanta? Hakanan Indo za ta kawo abinci ta maida ba ta ko kalla ba, da ta gaji da horar yunwar don kanta ta yiwa kanta fada take ci duk kuwa da cewa ba wani dandanonsa a bakinta.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Ke Ramlatu, ashe zan ga rana irin haka? Wane zamani muke ciki ne da yara kana musu magana amma hankalinsu na can wani wuri? Ina rabaki, ina rabaki da namiji! Matukar kika bari ki ka shiga hannunsa sai kin manta hanyar garinku."
Hajja dai har ta yi ta ƙare ba abinda Ramlat ta ce sai kuka, Hajiya don takaici ma tashi ta yi ta koma wurin mijinta wanda ya samu bacci. Sai a sannan Ramlat ta mike tana share hawaye rai a ɓace.
"Ni dai don Allah ki kyaleni Hajja, wannan fa rayuwar aurena ce, idan kuwa kun matsa na auri Hilal, za ku tarar da gawata a gidansa."
Daga haka ta sa kai ta bar falon inda Hajja ta yi sokoko tana bin ta da ido don ita lamarin ma tsoro ya ba ta. A haka Hajiya ta risketa, ganin ba Ramlat a wurin yasa ta sanin inda zancen ya dosa, ba ta kai ga zama ba Hajja ta dubeta.
"Wai ni Rabi'atu, kina yiwa yarannan addu'ar neman tsari kuwa?"
Wani murmushi Hajiyar ta yi.
"Hajja kenan, idan dai lamarin wannan yarinyar ne toh ki kwantar da hankalinki. Ta yi nisan da ba ta jin kira, ba kuma ta jin maganar kowannenmu. Don haka mun zubamata ido, idan an yi auren ma je mu yi mata sutura a miƙata gidanta na gaskiya. Kinga ai sai ta girbi abinda ta shuka sannan."
Hajja ta san halin diyarta idan ranta ya ɓaci don haka sai ita ba ta ja zancen ba, banda Allah Ya kyauta ba abinda ta ce.
***
Cikin sauri-sauri ta shirya cikin uniform ta fito, Hajiya na falon ta gaidata. Ko kallo ba ta samu ba balle kuma ta amsa.
"Na tafi."
Nan ma ba amsa, idanun Ramlat suka cicciko da kwalla, ta mike ta kama hanyar fita.
"Idan bamu isa da ke ba, idan ciwon da kika jazawa mahaifinki bai isheki darasi ba. Ki je ki hadu da Aliyu a yau, sai dai ki sani idan magana ta shiga tsakaninku ban yafemaki ba."
Ji ta yi kamar an zaremata dukkan lakar dake jikinta, an kashe duk wata gaɓa na jikinta. A hankali ta juyo ta dubi Hajiyar. Itama Hajiyar kallonta ta yi.
"Kin raina karfin alaƙar da ke tsakanin uwa da abinda ta haifa ko? Ko kina dauka shekarun da muka yi a duniya mun yi su ne a wofi? Ki gyara lamuran rayuwarki, lokaci bai ƙuremaki ba Ramlat, kar duniya da abinda ke cikinta su ruɗeki, kar ki wannan kuskuren."
Ta tsinci kanta da furta toh kafin ta juya ta soma tafiya tana bitar maganganun Hajiyar, masu sauki a baka sai dai kuma nauyinsu wane dutsen dala. Hawaye take har dakyar take ganin gabanta, a karshe ta share, ta kuma daukarwa rai da gangar jikinta alƙawarin za ta kiyaye haduwarta da shi, za ta daure.
Amrah ta tareta sadda suka fito daga jarrabawa. Ɗago kai ta yi tana kallonta. Tausayin Ramlat ya sanya hawayen da take riƙewa tun ganinta da ita a safiyar ranar, ya soma tsiyaya.
"Haba Ramsy, ki tausayawa kanki ki tausayawa rayuwarki da tamu don Allah. Kin sauya kin koma wata daban da bamu sani ba. Kin illata walwala da farin cikinmu da kuma naki, akan me? Allah da Ya halicci soyayya bai halicci hakuri da dangana ba? Ko kuwa kin fi karfin ki rungumi ƙaddara kamar kowane bawa? Ballantana ina da tabbacin muddin kika zauna da mutum irin Hilal ba za ki taɓa dana sani ba."
Wani murmushi mai ciwo Ramlat ta yi gami da ɗan kauda kai kafin ta kara dubanta.
"Ita soyayyar ba ƙaddara ba ce? Ko kin manta cewa bawa bai isa ya ɗorawa kansa abinda Allah bai ɗora mishi ba? Hakuri ana yinsa idan bakin alƙalami ya riga ya bushe, sai dai nawa alkalamin har yanzu a jiƙe yake. Na dauka idan duk duniya za'a haɗa kai a ƙi goyon bayana, banda ke Amrah. Sai ki ka shayar da ni mamaki, ki ka kara fahimtar da ni nisan alaƙarmu, kin bada tazara ba kaɗan ba. To ki sani, yanzu na soma son Aliyu, kuma in sha Allah zan zama mallakinsa ko ba jima ko ba daɗe."
Daga haka ta gifta ta wuce itama tana nata sharar hawayen. Amrah ta bi ta da kallo cike da kara jin tsanar Aliyu har cikin ranta, babu irin haka da ta taɓa faruwa garesu sai a kansa.
"Da yardar Allah ba za ki taɓa auran Aliyu ba Ramlat, wannan Aliyun ba alheri ne ga rayuwarki ba."
Ta furta a fili.
***
Ga Ramlar kuwa, tana fita ta yi turus, ta kasa koda motsi don gani take kamar mafarki, Aliyu a makarantarsu?
'Kema kinsan zai iya faruwa, mutumin da ba ya ji kuma ba ya ganinki?'
Fadin wani sashi na zuciyarta tana mai ci gaba da kallon Aliyun dake tsaye ƙasan wata itaciya a kofar makarantarsu. Shima ita ya zubawa idanun, kamar yanda ta rame shima haka ya rame. Ta shiga kalle-kalle, sai da tabbatar babu alamar an taho daukarta kafin ta soma yunkurin tsallakawa. A gaggauce ta isa wurinsa ta tsaya suna kallon juna, abubuwa biyu suka faɗomata a rai lokaci guda. Na farko dokar makarantar da ta hana tsayuwar taɗi, muddin aka lura da hakan to fa za'a ɗau mataki. Na biyu zantukan Hajiyarta da suka fi komai tsayawa a ranta. Sai ta soma ja baya, ga samu ga rashi. Ya yi nasarar riko gefen hijabinta, a dole ta tsaya ta kuma juyo sadda ya saki.
"Ba zan iya hakura da ke ba, ke din nake so Baby. Zan iya jure komai saboda na aureki. Rashinki kwanakinnan yana wahalar da zuciya da gangar jikina. Me zan yiwa Abba ya so ni? Kamar yanzu ba kya tausayina kema, kar ki manta na sadaukar da komai saboda ke. A dalilinki na rabu da Muhibbat, bana kula kowace mace. Kar ki sakamin da auren wani ba ni ba, ba zan jure ba."
Duk zantukan tana jinsu har ƙwaƙwalwa, ji take inama za ta iya cewa wani abu, sai dai ba za ta saɓawa Hajiya ba. Dabara ta faɗomata, a gaggauce hannu na rawa ta sauko da jakarta a baya sannan ta durkusa ta ciro takarda da biro. Shima bai yi ƙasa a gwuiwa ba wurin durkuson, maimakon abinda ta maida hankali wurin yi (wato rubutu), sai ya maida hankali wurin kallo da karantar yanda ta rame idanunta suka zurmuƙa ciki. Siririn karan hancinta ya ƙara fitowa, ji ya yi inama yana da damar da zai iya daukemata hawayen da suke bin karan hancin zuwa baka. Ta kammala rubutun ta miƙa mishi takardar, ya karba yana dubanta har suka mike a tare. Dakyar ta iya juyawa da sauri yana kiranta ba ta ko waigo ba. Tasan a hakan ma ta saɓa umarnin Hajiyarta, dole kuma ta nemi gafara. Ta taki sa'a har za ta koma cikin makaranta wata ta kirata wai an zo daukarta. Ta juyo da azama za ta nufi mota, Amrah ta hango tsaye a wurin Aliyu tana mishi magana shi kuwa yanzu ya bada baya maimakon a farko da yake kallon gaba. Hankalinta ya tashi, sai sannan ta kula da wanda ma ya zo daukarnata, Abbanta ne. Ba damar ta je garesu, ganin kaifafan idanun Abban a kanta ya sa dole ta bude motar ta shiga.
Ita kuwa Amrah sosai ta ja wa Aliyu kunne akan ya rabu da kawarta.
"Ka raba ta da iyayenta, ka raba ta da mutumin da zuciyarta ta soma so a duniya. Me kake nema haka? Ance ba za'a ba ka ita ba, meyasa ba za ka hakura ba? Ka daina bibiyarta, ba don na zo na zama katanga tsakanin fuskarka da na mahaifinta ba, da yau ban san halin da ganinka zai jefashi ba."
Sai a sannan ya fahimci dalilin zuwan yarinyar da kuma dawowarta ɓarin da dole zai juyo. Manufarta ta burgeshi sai dai kalamanta sun ba shi dariya hakan yasa shi murmusawa.
"Ban taɓa ganin Amrah ba sai yau, duk kuwa da cewa kafata ta taka kofar gidansu ya fi a kirga a dalilin Baby. To ba zan yi mamakin kalamanki ba, amma ina so ki sani. Daga ni har Ramlat, Allah ne Ya haɗa soyayyarmu. Ina mai ba ki hakuri sai dai ki yiwa yar uwarki uzuri, shi so ba ruwansa da komai, ki mata uzurin halin da take ciki yanzu. Ba yin kanmu bane. Addu'arki ita ce abin bukatarta da ni dinma a yanzu, abu daya kawai nake so ki rike a ranki. Wannan dai banzan Aliyun, idan Allah Ya ƙaddara shi ne mijin Ramlat, babu mahalukin da ya isa ya tsayar. Na bar ki lafiya."
Ya wuce ta bishi da kallo, takaici biyu. Wato dai ba zai saduda ba, a gefe kuma ta tuna sadda ta ambaceshi da banza. Amman ai ba ta furta a gabansa ba, hakan na nufin Ramlat na ba shi labarin duk wani abu da aka ce game da shi. Wani wawan tsaki ta ja tana mai jin kamar ta samu Ramlat din ta yi mata dukan kawo wuƙa.
***
_*Ba zan iya ce maka uffan ba bisa alkawarin da na dauka sanadin Hajiya ta, ina kaunarka Sweet Aliy, har gobe kai ne zaɓina. Ka sa a ranka babu mai yimin dole, babu shi. Ko an yi ba zan zauna ba. Zan fito kawai domin na aureka. Na maka wannan alƙawarin. Abba bai da lafiya, an kai shi asibiti yana da hawan jini, a yanzu dole za mu ɗan yi hakuri mu rage haɗuwa. Don Allah ka dinga cin abinci. I love You._*
Ya ninke takardar ya zura a aljihu, son wannan yarinya ba zai kashe shi ba. Kai tsaye gida ya nufa wurin Abulle.
"Kai Zakina, kana kuwa cin abinci? Wannan uban ƙashin wuya? Kodai so kake a maido maka da matarka yanzun nan na kira Babanta na tursasashi?"
Ya ja guntun tsaki gami da shafar suma. Kwantar da kai ya yi jikin kujera ya lumshe ido. Nan da nan Abulle ta sa aka kawo mishi abinci.
"Maza ci wannan daga gidan Babanka Alƙali ne, irin wanda kake so."
Abincin gidan Justice kusan ya fi kowanne dadi wannan ta sanha jikokin ke rububi idan an aikowa Abulle. Ita kuwa ɗan gaban goshinnata take ajiyewa.
A dole ta sanyashi a gaba ya dinga ci kamar mai tauna magani. Karshe ma ya ture kwanon.
"Ni fa aure zan yi."
Nan da nan Abulle ta washe haƙora.
"Kai Alhamdulillah, ko kai fa. Wa ka samu?"
Ya runtse ido.
"Wacce nake so iyayenta ba sa sona. Sun mata miji, kuma itama nan duniya ni take so."
Nan da nan ta daure fuska.
"Kar dai wacce Babanka Abdussalam ya ce iyayenta sun aiko nemanka akan ka fita hanyarta?"
Ya dubeta sosai, sai kuma ya daure fuska.
"Na meye za'a dinga yawo da zancen kuma? Wannan kuma ya zama terere. "
Abulle ta yi mishi daƙuwa.
"Nace karbi nan, don an fadamin shi ne terere? Kai yanzu ba abin kunya bane ma a ji wai kana son yarinya an turo a yi maka kashedi don ka rabu da ita? To ahir dinka! Ka rabu da ita tun wuri kafin ka jawomin ƙananun magana cikin gidannan."
Ya taɓe baki, shi kam ba wanda zai iya rabashi da Ramlat, ba zai yi dakon so a banza ba. Duk ma macen da ya hango sai ya ga ba ta kaita ba, idan kuwa ya rasata ya yiwa kansa.
***
*A KWANA A TI think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/Dbu9FChHQ9
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
13)
*A KWANA A TASHI..*
Su Ramlat sun kammala karatunsu sun yi bankwana da makarantar Sakandire.
Ranar da za'a yayesu kuwa, duk wani farin ciki da ƴan ajinsu ke yi, banda ita a ciki don a ganinta babu wani abin ƙayatarwa musamman ganin yanda gadan-gadan mutan gida ke shirin biki. Bikin da aka matso da shi aka rage lokacinsa, duk sanadin kar ta ƙara tadamusu batun Aliyu. Yanzu da kowa ke murna ana hotunan bankwana, ita din tana zaune a gefe saman kujeru sanye da gown ja wanda wuyar rigar da kuma hannun aka mishi kwalliya da yellow. Gashinta a tufke babu kitso, ta ɗora hular gown din a kanta ya zauna ɗas. Duk irin kyan da ta yi, ganin muninta take, ace rana irin ta yau babu wani nata da ya zo tayata murna, sai iyayen Amrah da yayyunta da suke kokarin jawota jiki duk domin kar ta ƙuntata. Ramar da ta yi ba karamin tada hankalin Umman Amrah ya yi ba har ta ja ta gefe ta yi mata fada sosai akan ɗorawa rai abinda ba shi ba.
Yanzun da ta ja gefe ta zauna, suna daukar hotuna ne, a ganinta hakan zai fiyemata don ba wani kyau za ta yi ba, a ganinta ramar kadai ma ta dusasar da ita. To ma idan ba ta rame ba me ake so ta yi? Ba ta iya bacci balle cin abincin kirki, Hajiya ba ta yaɓamata magana sai dai magana ta kwakkwaran mintuna biyar ta bar haɗasu. Abba kuwa jan ta ya shiga yi a jiki ganin yanda uwar ke mata duk don ta sake, ta hakura kuma ta fawwalawa Allah lamuranta. Shi kam ta tabbatar banda yau zai je Daura tare da Yaya Munir, to zai zo mata a wannan rana. Su Zulaihat dama ba ta sanya rai ba.
"Ramsy!"
Ta daga kai ta ga mai kiran, JJ ce. Itama dai ajinsu take. Inda ta mata nuni da yatsa ta bi da kallo kafin ta ce
"Ki zo!"
Daga nan ta juya ta tafi, ita kuwa Ramlat tunda ta ɗora idanu ga wanda aka nunamata, ta ji kamar kwai ya fashemata a ciki. Sanye cikin shadda sky blue, ya kafa hula zanna bukar. Sajensa a kwance luf-luf. Yanda take karantar ramar da ya yi a satittikan da suka yi basu ga juna ba, don kuwa batun waya takan ari wayar Indo a ɓoye ta kira ba tare da ko Hajiya ta sani ba. Rokon Allah da Annabi s.a.w take yi mata akan ta ɓoye sirrinta.
Ta yi zurfi cikin tunani da kuma kallonsa babu ko kyaftawa, ya gaji ya biyo sahunta ya ja kujera ya zauna kusa da ita a cikin hall din mai jama'a maƙil.
"Kin wahalar da ni fa, dakyar aka ganomin inda kike. Baby kin yi kyau. Bari na miki hoto."
Ya fiddo wayarsa Blackberry wacce ake kan yaayi a lokacin, ya shiga daukarta bai ko damu da murmushin yaƙen dake a fuskarta ba. Jiki a sanyaye kuma ya maida kai ga kallonta.
"Baby ki yi magana ko na samu nutsuwa, gaba daya kin yi wani sanyi kamar ba Babyna ba wacce daga ta yi tozali da ni take manta komai da kowa."
Ji ta yi ya kara karyar da zuciyarta, sai ta soma kuka bayan ta saka tafukan hannunta ta rufe fuskar. Duk yawan danginsu a rasa mai zuwa tayata murna ranar da ta fi buƙatar hakan?
Kukan ya tashi hankalin Aliyu. Bai san ma sadda ya kama hannuwan ba ya saukesu daga saman fuskar.
Ya yi daidai da shigowar Abba da Yaya Munir cikin hall din. Har zasu kama hanya Abban ya ga rashin kyautuwar a rana irin ta yau bai je wa diyartasa ba hakan yasa shi umartar Yaya Munir akan su soma biyawa kafin su wuce. Ba don Yaya Munir na so ba ya bi umarnin. Tun shigowarsu suke rarraba idanun inda zasu hangota. Amrah ce ta soma hango Abban, da sauri ta taho ta gaidashi. Mahaifinta ma ya ƙaraso suka yi musabaha cike da fara'a.
"Ai da ace ba ka zo ba, har gida zamu je mu sameka mu ji dalili."
Fadin Dr Abdullahi mahaifin Amrah cike da zolaya.
"Ban isa ba, sai dai kuma da nasan za ka zo din da ban zo ba, zuwanka ma ai ya wadatar. Yaranmu ne."
Suka yi dariya sannan Yaya Munir dake ta kalle-kallen ko zai hangota ya gaisheshi. Abba cikin murmushi ya dubi Amrah.
"Na tayaki