Showing 42001 words to 45000 words out of 230725 words
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
14)
Kallo ɗaya za ka yi mishi ka hango annashuwa a zuciyarsa. A jikinsa yake ji komai ya zo karshe, a jikinsa yake jin ya samu soyayyar Ramlat da yardar Allah. Sai dai bai san meyasa kirjinsa ya hau bugu bayan daka motarsa da fitowarsa ba. Ya ɗan yi shiru yana kallon kofar gidan, bai jima da rabuwa da babban amininsa Ma'aruf ba. Sosai ya ba shi shawarwarin da suka dace game da zamansa da Ramlat. Ya dauka dari bisa dari.
Ya kalli sama, walkiya ake yi sosai ga hadari. A hankali ya sauke ajiyar zuciya sannan ya yi kari cikin gidan.
Ya rufe kofar falon sannan ya ƙaraso ciki da sallama, falon ya tsaya ƙarewa kallo. Ɗakin Amarya kam ya yi kyau iyakar kyau, abu daya idan ya tuno yakan dakushe farin cikinsa sai dai kuma karfin gwuiwar da ya samu daga Amininnasa shi ya rinjayi komai har ya sa shi nufar hanyar ɗakinta da sallama. Bai son gayyar abokai da sunan rakiyar Ango.
Ya cika da mamakin rashin ganinta zaune a saman gadon kamar yanda ya zama al'adar aure.
"Ramlat." Ya kira da tattausan murya yana karasa shigowa dakin.
"Tooh." Ya kara ambata ganin farin laffaya da ɗankwalinta yashe saman gadon, hanyar banɗaki ya kalla, kai tsaye ya shiga bayan ya ajiye babbar riga da hula saman gadon. Nan ma wayam, sai tashin kamshin turaren wutan da aka sanya da kyallin fararen tiles da ya kashemishi ido.
"Gani nan!"
Sautin muryarta a sama, wannan ne ya sa shi juyowa da sauri yana kallonta baki sake. Ya kai duba ga jarkar da ke hannunta na hagu da kuma ashanar da ta rike a dayan hannun. Tana tsaye a tsakiyar dakin, kallo ɗaya za ka yiwa idanun ka san ta ci kuka ba kaɗan ba. Tana tsayen amma jan majina take yi, ga wasu hawayen da ke ƙara sauka saman fuskarta.
"Ramlat? Me ya haka?"
Ya furta cikin nuna dakiya sai dai zuciyarsa tamkar ta fasa kirjin ta fito tsabar tashin hankali. Duban tsana take mishi.
"Ka fini sanin mene haka Hilal tunda ka nace akan lallai sai ka zauna da ni! Nace bana sonka! Na fasa aurenka! Amma ka tursasa lallai sai da aka auramaka ni! Dole ne? A farko wa ya yimin dole? Ba ni na kawoka gidanmu na nuna ina sonka ba? To na fasa! Na fasa! Bana sonka amma ka nunan kai maye ne! Kafin ka cinyeni ni zan soma kashe ka! Dama ni rayuwata ta kare tunda har aka daura aurena da mutumin da na fi tsana! Muddin ba ka sake ni ba wallahi ina maka rantsuwa da Maƙagin dare da rana, yanzu ba anjima ba, zan watsa fetur dinnan kuma na kyafta ashana mu mutu gaba daya! Kar ka yi tunanin guduwa domin na rufe ko'ina a gidannan! Na rufe ɗakunan!"
Tunda ta soma maganar ya ƙuramata ido, mamaki da baƙin ciki suka cika zuciyarsa. Bai taɓa kaiwa ƙoluluwa a ɓacin rai bisa yanda take mishi ba irin yau. Bai kuma taɓa zaton za ta aikata makamancin hakan ba.
"Ramlat? Yau soyayya ce ta koma ƙiyayya? Dama ƙiyayyar ta yi zafin haka? Kin manta Hilal? Kin man..."
Bai kai ga ƙarasawa ba ya ga ta ɓalle murfin jarkar ta hau watsa kalanzir a tsakar dakin har da bangwaye, ba ta ko damu da yanda ya ke jiƙa riga da hannunta ba. Cak ta ji ya riƙe hannuwan wanda ya yi sanadin faduwar jarkar a ƙasa. Idanunsa sun kaɗa saboda tsananin tashin hankali da ɓacin rai. Ganin yanda take kici-kicin kwatar kanta ya sanyashi watsi da hannun har hakan ya yi sanadin faɗuwarta a ƙasa, har lokacin ba ta bar kuka ba, ganin ta na kokarin kyafta ashanar ya sa ƙafa ya buge hannun, ashanar ta faɗi a ƙasa. Durkusawa ya yi saitinta.
"Ba sai kin kai ga kashemu ba! Ki je ki auri wanda kike so, ni Hilal na sake ki. Sai dai ki sani, idan har da hakkina, Allah zai min sakayya. Shakka babu kin yimin butulci, kin tarwatsa dukkan farin cikina. Kaicon wannan ranar." Daga haka ya mike yana kallon yanda take dariya tana share hawayen fuskarta. Ya juya saboda kallonta ma kuma ɓata ransa yake. Shakka babu mai hakuri bai iya fushi ba.
"Ina za ka? Ai da saura!"
Bai yi niyyar tsayuwa ba sai dai dole ya tsaya din jin ya murɗa kofar amman ko gezau. Jakar hannunta ta nufa ta fiddo karamin littafi (Memo) da aka raba na bikinsu, a take ta yage bangon ta yar a ƙasa, ya bi bangon da kallo, hotonsu ne, bai mance ko ranar da za'a yi hotunan sai da ta gasamishi maganganu masu zafi, sai dai hakanan ya danne ya shanye. Kallonta kawai yake yana ƙara mamakin yanda so ya koma ƙi. Ramlat da a baya zai iya bugun kirji ya ce ta fi sonsa kan yanda yake sonta. Yau ita ce ta juyamasa baya lokaci guda. Bai dauka abin zai biyo har cikin aurensu ba. Ba kyawunta ne ko diri ya ruɗeshi ba, kaunarta yake da zuciya ɗaya. Da ace ɗayan biyun da ya lissafa ne, ba zai rabu da ita ba tare da ya gogamata tabon da har ta mutu ba za ta mance ba. Bai kuma mance yanda Ummansa ta ɓatamasa rai ba duk akan ya nace sai ya aureta.
"Tunanin me kake? Karɓa ka rubutamin a rubuce."
Daddaɗar muryarta da a yanzun ta zama kamar ta zakanya a kunnensa ta katse shi. Ya karɓa yana kallon kwayar idanunta, ta yi amfani da wannan damar ta harareshi ta tsuke baki gami da kauda kai. Ya maida kai ga takardar yana kammalawa ta karɓa. Bakinsa na rawa ya ce.
"Ban mukullin."
Ba ta ko kalleshi ba ta ciro mukulli cikin riga ta miƙamasa. Ya karba da sauri ya bude kofar ya fice zuwa falo.
A gaggauce ta mike ta zura hijabinta dogo na sallah da aka daukomata. Ta dauki jakarta ta fito. Yana zaune a falo ya dafe da hannuwansa biyu yana fidda hawaye kirjinsa na suya. Ba ta ko kalleshi ba ta fita, burinta ya cika.
"Duk abinda ya faru, ka so faruwarsa!" Ta furta a fili kuma a hankali sa'ilin da take share hawayen fuskarta.
Tana tafe tana sharar hawaye, ga wata irin iska da ake yi da walkiya. Allah Ya taimaketa ta samu abin hawa kai tsaye gidansu ta nufa. Ta yarda idan ma kasheta za'a yi, su kashe. Ko mene su yi mata. Amman ita kam ba za ta iya zama gidan Hilal ba da sunan mijinta kuma a waje tana cin amanar mijin aurenta na sunnah ba. Ba za ta iya wannan munafuncin ba don ta san karshen abinda soyayyar Aliyu da auren Hilal zai jawomata kenan.
***
Abba ya dubi Hajiya da murmushi a saman fuskarsa.
"Yau ina cike da farin ciki. Na kashe matsalar Ramlatu, fatana yanzu Allah Yasa ta zauna lafiya da mijinta."
Hajiya dake kakkaɓe shimfiɗa ta yi murmushin yaƙe. Har lokacin hankalinta bai kwanta ba. Sam ba ta da wata nutsuwa.
"Amin."
Ba tare da ta kalli Abban ba, ta ci gaba da aikinta. Ya sa hannu ya riko hannunta, hakan ya dakatar da ita ta dubeshi. Tsoro, fargaba su ya hango cikin kwayar idanunta.
"Ya aka yi? Ashe ba za ki fawwalawa Allah komai ba? Ki bar tunanin wani abu akasin alheri."
Ta gyada kai kawai tana jin saukar ruwan hawaye. Hayaniyar da suka jiyo na mutanen gidan ya sanya su kallon juna cike da rashin fahimta.
"Meyafaru?" Fadin Abban hankali a dan tashe, Hajiya kuwa kirjinta ne ta shiga bugu fiye da baya. Da hanzari suka fito suka nufi babban falon gidan na Hajiya.
Tana tsaye jikinta sharkaf sakamakon ruwan da ya yi mata duka cikin adaidaita sahu, kuka take yi yayinda taron dangin uwa da uba suke neman ba'asi hankali tashe. Hajiya ji ta yi jiri na shirin kayar da ita hakan yasa ta samu ta zauna saman kujera tana salati.
"Ya isa haka!" Tsawar da Abba ya daka cike da karfin hali don jikinsa ma rawa yake yi, shi ya katse su duka.
Kai tsaye ya karasa ga Ramlat ya kama hannunta suka shiga bangarensa. Irin su Zulaihat da Amrah da suka san komai dangane da auren, kuka kawai suke yi sanin cewa koma mene Ramlat ta shuka wata tsiyar ne.
***
"Daina kuka Ramlatu, ya isa, ya isa. Ki fadamin meke faruwa?"
A hankali ta ciro takardar a jakarta, babu inda ba ya rawa a jikinta ta mikawa Abban.
"Don sonka da Annabin rahma s.a.w, Abba ka yafemin. Ba zan iya zama da Hilal ba."
Ta furta tana sheshsheka sosai. Abban ya fita shiga tashin hankali,ya fita shiga ruɗu. Hannunsa rawa yake, kirjinsa zafi yake. Yana ji inama mutuwa ta taddashi tun kafin ya haifi ɗiya kamar Ramlat?
Daidai lokacin da Hajiya ta turo kofar ta shigo.
"Wace irin ƴa na haifa? Rabi'atu wace irin ƴa kika haifamin?! Anya ba'a yimin musanye a asibiti ba?! Don ina mamakin kasancewar Ramlatu jinina!"
Ta riga ta gane, ba'a hayyacinsa yake ba, ta san ɓacin rai ne. Ta ƙaraso sosai gwuiwa a sanyaye ta kai karbi takardar da Hilal ya rubuta sakin.
Na saki Ramlatu saki daya bisa tursasawarta. Allah Ya zaɓamin wacce ta fiyemin ita alheri. Itama Ya bata abinda take so.
Abban ya mike zuwa dakinsa. Waya ya ɗauka ya kira Yaya Munir ya fadamishi dukkan abinda ya faru. Ya kara da fadin.
"Gobe da safe ka zo muje gidan su yaronnan. Ina rantsuwa da Allah, muddin ina numfashi Ramlatu sai ta auri zaɓinta. Sai ta auri wanda ta ke so."
Daga haka ya katse kiran, ya zauna ɗabas gefen gado. Bai san ya akai ya soma gani bibbiyu ba, sai ji ya yi ya kife zuwa ƙasa.
***
Hajiya tana kuka ta ke magana a falon.
"Kaicon mai taurin kai da bauɗaɗɗen hali irin naki. Kaicon ƴa da ba za ta yi biyayya da iyayenta ba. Ina jiyemaki makomar rayuwarki Ramlatu."
Kowannensu kuka yake, Hajiya ta mike har hakan ya zaburar da Ramlat don a zatonta duka za ta sha, sai dai ta ga ta shige daki ta bar ta nan zaune.
Ita kuwa Hajiya ba ta ga dalilin dukan ba, wanda ke jin magana kuma ya ke da gatan a fada ya ji ko a tursasa ya bi, shi ne suke da ikon idan bai ba su daga hannu su daka. Banda Ramlatu, ta nuna musu iyakarsu.
Mijinta ta hango kwance a ƙasa rub da ciki. Hannu ta sanya a kai cike da matukar gigicewa ta buga salati iyaka ƙarfinta. A zabure Ramlat ta shigo, Hajiya tana jijjiga Abban tana kiran sunansa.
"Kar ka mutu Khalid! Ba ita kadai ka haifa ba! Kar ta kashemana kai!"
A can falo kuwa jin salatin Hajiya ya shigo da mata da ƴan samari (baƙin Daura) ƴan biki cikin falon Alhajin. Sai dai ba wanda ke da ikon ƙarasawa dakin Abban sai Zulaihat da ta nufi ciki da sauri. Idanun Rafee'ah ya wacce ta zauna dalilin jin wani murɗi da cikinta ke yi ya kai saman takardar da ke kan kujera, ta dauka tana karantawa, sai ta ji kamar an karawa tsohon cikinnata ƙaimi wurin murɗawar. Ta matse takardar da karfi tana rike cikin da salati. Daidai sadda aka fito da Abba, samarin suka tari Hajiya da Zulaihat suka rikeshi aka fita.
"Ku dube ni!"
Cewar Rafee'ah da ke murkususu riƙe cikinta ɗan wata bakwai, ga hawaye caɓe-caɓe saman fuskarta. Ai tuni wasu cikin iyaye aka yi kanta aka taimaka ta mike, ga ciwo a jikinta, ga tunanin Abbansu da kuma wannan tashin hankali da bakin ciki da Ramlat ta jawomusu a wannan rana.
Motar Abba har ta yi gaba, har lokacin ruwa ake ba ƙaƙƙautawa. Itama Rafee'ah motar kai yara makaranta aka ciro, daya daga cikin baƙin Daura ne, Dauda, direban tasi. Shi ya tuƙasu cike a Bus zuwa asibitin.
Tana gefe tana kuka kamar ranta zai fita, ba wanda ya kara kallonta, duk wanda ma ya kalla ya tambayeta meke faruwa ba ta ko kallonsa balle ta amsa. Amrah ce ta nufi inda take ta ja hannunta suka shiga daki ta kulle kofar. Ta dubeta a gigice, idanun sun yi ja. Kasancewar Amrah farar fata ya sanya hatta da fuskar ta dauki ja na wacce ta ci kuka.
"Me kika aikata?"
Ramlat ga ɗago ta dubeta cikin sheshsheƙa.
"Me ake zaton zan aikata don Allah Amrah? Me ake zaton zai faru da aure irin nawa? Ya sakeni. Ya sakeni saki ..."
Bata kai ga ƙarasawa ba Amrah ta fidda hannu ta dauketa da lafiyayyan mari. Marin da ya hargitsata ya kuma sa ta cika da dumbin mamaki. Amrah ƙawa kuma Aminiya ita ta fidda hannu ta mareta? Abinda koda wasa ba ta zata ba, ya zo mata a hagunce. Kafin ta farfaɗo daga tunanin da ta faɗa na tuna ƙarfin alaƙarsu da Amrah din. Ta ji kaifafan kalamai na fitowa daga bakinta.
"Wallahi ba ki da hali! Ba ki da hali! Na tsaneki! Haka kika zaɓarwa kanki? Haka kike da son kanki? To ki sani, tun kafin wani ya wulakantaki! Ke kika soma wulakanta kanki! Tun kafin wani ya ci zarafinki! Ke kika soma nuna ke din ba kowa bace ba ki da daraja da mutunci ko ƙanƙani! Ki yi kuka da kanki Ramla! Ki kuka da kanki bisa duk abinda zai biyo baya! Sai dai ki saka a ranki! Allah Madaukakin Sarki Shi ne Ya ce mu bi iyayenmu! Sun mana komai, sun kyautata mana. Ke kuma kin zaɓi ki saɓamusu saboda wani banzan Aliyu! Saboda wani shashasha da bai san ciwonki ba! Wallahi Aliyu ba ya sonki! Kema kuma ba sonsa kike ba! Hauka kike! Ni Amrah Abdullahi ki sani, a yau a wannan rana kuma, babu ni babu ke! Ba zan iya ƙawance da mai hali irinnaki ba. Ban yi sa'ar ƙawa ta gari ba mai daukar shawara. Yau idan Abba ya mutu saboda banzan son rai irinnaki, ki sani kina cikin masifa. Bani babu ke! Na tsaneki."
Tana kaiwa nan ta bude kofar ta fice daga dakin a guje tana kuka. Ramlat ta zube a wurin tana kuka sosai har da sheshsheka. Sosai maganganun Amrah sun shigeta, kuka take kamar ranta zai fita. Mutuwar Abba da ta ambata shi ya fi komai tsayawa a ranta don haka ta mike a gigice ta fito. Matan da ke falo suna jimami suka dubeta.
"Ke Ramla ina za ki?! Ke!"
Fadin Yakumbo yar uwar Abba. Masu kwari suka bi bayanta dakyar ta yarda ta zauna ta jira su dawo gidan. Idan Abba ya mutu ba za ta yafewa kanta ba! Da gaskiyar Amrah, tana da son kanta da yawa.
***
Da gaggawa aka shigar da Abba ciki, itama Rafee'ah an miƙata Labour room don an tabbatar haihuwa ce ta tahomata kuma bakwaini.
Hajiya na zaune tana kuka har lokacin ba ta cewa kowa komai ba, Hajja ta zauna gefenta. Cikin fada take magana.
"Wai menene ke faruwa Rabi? Bamu kai mu ji bane? Haba! Tun a mota nake tambaya an min shiru!"
Baba Hajara diyar Hajja ta biyu ta caɓe.
"Nima dai Hajja abinda ban gane ba kenan. Sai kuka ta ƙi magana. Ga Rafee'ah ma na naƙuda. Ki fadi meke faruwa ko hankulanmu zai kwanta."
Zulaihat ta ƙaraso wurin rike da takardar sakin Ramlat da Rafee'ah ta damƙamata kafin a shige da ita daki. Ta dubesu tana kuka.
"Sakin Ramlat fa aka yi. Ita ta sanya Hilal ya saketa. Wannan ne dalilin faduwar Abba, da kuma naƙudar Rafee'ah."
"Wace Ramlatun aka saka?" Cewar Hajja, tambayar dake zuƙatan maza da matan gurin kenan saboda rudewa ma sun kasa gasƙata batun Zulaihat.
To mene abin ɓoyon? Abinda komai ya riga ya bayyana, zubewar girma da bada kunyar da ake tsoro ya afku. Irin ABINDA AKE GUDU (Batool Mamman) ya riga ya faru. Don haka sai ta musu filla-filla yanda zasu gane. Sai ga mata na kuka da salati.
"Ni dama na san ba inda dolen nan zai kaimu. Kamar na sani Rabi'atu na ce ki fadawa Khalid a fasa. Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Wannan wane irin zamani muke ciki? Lokacin da aka mana auren bamu san mazajen ba ma, mu ce me?"
Hajja ke wannan batun tana kuka.
"Amm, don Allah Mama ku yi hakuri. Kun yi yawa a asibitin nan, ga marar lafiyarmu ba ya son hayaniya. Don Allah ku ragu, ko kuma ku yi shiru. Kuna damun sauran marasa lafiya su ma."
Likita ke wannan jawabi a tausashe. Ya dubi Zulaihat don fuskarta kadaiya shaida sai ta Hajiyar.
"Kina iya biyoni ofis."
Ta amsa da toh tana share hawaye ta bishi a baya. Can kuwa Nos ta fito ta na fadan ba wanda ya tsaya wurin Rafee'ah gashinan ta haihu kuma ana bukatar kayan amfani.
"Me ta haifa?" Har suna hada baki wurin tambaya.
"An samu namiji. Itama kuma da sauki jikinnata."
Suka sauke ajiyar zuciya, nan aka yiwa mijin Rafee'ah waya akan ya zo kuma ya taho da kaya da gaggawa, ta haihu. Abinda ya jefashi cikin ruɗu da mamaki kenan, an haifar masa bakwaini.
***
Likita ya yi faɗa kwarai akan yanda aka bari jinin Abba ya hau sosai, ya kuma ce anan zai riƙe shi har sai ya warware. Zulaihat kuka kawai take. Ya kammala rubutun ya miƙa mata takarda.
Har ta mike ta dawo.
"Dr don Allah ko za ka kiramin Munir a waya."
Likitansu ne, hakan yasa suka saba sosai da mutan gidan. Ya fiddo wayarsa ya dannawa Munir kira.
Shi kuwa Munir dama tun sadda ya dinga kiran wayar Abban ya ji ba'a dauka, ya fito ya taho bai ko damu da ruwa ba. Kwanciyar hankalinsa daya, uayi tozali da Abban.
Ya na hanyar nufar gidan ne, kiran Dr Sunusi ya shigo. Da mamaki ya ɗaga, maimakon ya ji muryar Dr Sunusi sai ya ji ta Zulaihat. Ba shiri ya gangara gefen titi kirjinsa na bugu ya ɗaga.
"Hello Baban Yasmin, Zulaihat ce."
"Meke faruwa Zulaihat? Ina Abba? Ya kirani ya yimin wasu zantuka marasa dadin sauraro."
Cikin kuka ta soma zayyane mishi dukkan abinda ke faruwa bayan fitar Dr daga dakin. Salati kawai ya ke, jiki na rawa ya katseta.
"Ganinan zuwa Zulaihat, don Allah a ragu a asibitin. Ki ban Dr, kar ya bar kowa ya shiga wurin Abba yanzu."
Ta amsa da to ta leka ta mikawa Dr Sunusi sannan ta yi gaba. Shi kuwa Munir ya jaddada