Showing 72001 words to 75000 words out of 230725 words
fadamaka tana asibiti ko?"
"Eh yanzu zan taho."
"Allah Ya taimaka."
Abinda ta ce kenan ta yi gaba. Ya bi bayanta da harara cike da ɓacin rai, wato Ramlat har ta san ta kira gida ta ce tana naƙuda amma ta ƙi sanarmishi? Don ba shi da kudi ya talauce shi ne za ta mishi tonon silili a duniya.
"Idan naje asibitin Allah Ya tsinen." Abinda ya furta kenan bayan ficewar Hajiyar gami da jan tsaki da nufar ciki. Wanka kawai ya yi ya sauya kaya gami da nufar club.
Hajiya ba ta nufi asibiti ba sai da ta soma biyawa wani Nassarawa ta yi amfani da kudin da Abba ya bata ta rike ko za'a buƙaci wani abu ta siya duk abinda ya kamata na jariri bisa umarnin Abban wanda daga baya ta ga dacewar ta fadamasa. Ya jinjina lamarin ba kaɗan ba.
***
"Alhamdulillah." Abinda Hajiya da Indo suke fadi kenan sadda suka tsinkayi muryar jariri na tsala kuka. Nurse ta fito da fara'arta kamar ɗazun ba ita ke yatsina ba.
"Hajjaju ga fa kishiyartaki ta fito duniya."
Murmushi Hajiya ta yi ba ta amsa ba sai Indo ce ta amsa da Barka Barka.
***
Abba ya yi farin ciki sosai da jin batun haihuwar Ramlat, idar da sallar nafilarsa kenan yana mai roƙamata sauƙi da rangwamen naƙuda a wurin Allah. Ya yiwa kaf yan uwanta har Munir text ya sanarmusu da haihuwarta. Babu wanda bai kira ya tayashi murna ba, Munir bar wa cikinsa komai ya yi ya kira Abban ga mishi murna da tayashi farin ciki.
Abba ji yake kamar ba'a taɓa haifamasa jika ba.
"Allah Ka shiga lamarin Ramlatu, Ka yafemata kura-kuranta. Allah Ka dubeta da dukkan rahmarKa. Ka rayamata abinda ta haifa."
Ya furta a fili yana kara jinjina lamarin Aliyu da aka ce bai taka ƙafa ya je asibitin ba.
***
Ta bude idanunta tar bayan ta fito daga wanka inda ta kimtsa jikinta da taimakon Indo. Dinki ciki da waje aka yi mata, azaba kam ta sha ta godewa Allah. Idanu ta ƙurawa jaririyar tana kallo, so da kaunarta na ratsa dukkan sassan jikinta. Ta kauda kai ganin Hajiya na kallonta, murmushi kawai Hajiya ta yi ta cigaba da murje dukkan dauɗar jikin yarinyar. Yanzun ne ta siyo bahon wanka har da gado mai net na jarirai.
Aliyu bai zo ba, kuma bai kira ba, wannan ya fi komai taɓa zuciyar Ramlat. Ta fakaici idanunsu ta zubda hawaye. Wuraren karfe biyu Hajiya ta yi niyyar tafiya gida, Abba ya ce ta zauna ta kwana babu damuwa. Idan ma wani abu ne ita Indo ta dawo gidan saboda A'isha. Ta yi zamanta tana jinjina irin kaunar da Abba ke yiwa Ramlatun, ko Uwani (Zulaihat) mai sunan Hajja uwar riƙonsa ba ya yi mata hakan.
***
"Wai ke mijinki ba zai zo ba? Ki kirashi ki ce an sallameki."
Hajiya ce ta gaji da jiran gafara Sa ba ta ga ƙaho ba ta karya bille ta yi magana. Ramlat abin ya jima yana ci mata tuwo a kwarya, daidai da Abulle da wasu a dangin Aliyun sun zo ganin jaririyarta amma banda uban gayyar. Idan ta kira har ta gama ringing ba zai ɗaga ba, a karshe ma saƙo ya turomata ta waya cewar wallahi ƙafarsa ba za ta taka asibiti ba tunda ba shi ya kai ta ba. Wadanda suka kai ta su zamemata gatan su biya duk abinda aka kashe. Idan ma ta ga dama daga asibitin ta wuce gidannasu ba shi da kudin ciyar da ita da abinda ta haifa. Talaka ne Aliyu. Wannan shi ne saƙonsa.
Ta ƙara kallon Hajiyarta, tasan abin ya yi mata ciwo ne kuma ta gaji ne ta yi magana. Zulaihat da Rafee'ah suna gefe suna cin abinci ba wanda ya ce uffan.
"Hajiya ya ce ba zai zo ba."
"Ba zai zo ba kamar ya? Me yake nufi da hakan?"
Ta sunkuyar da kai tana fidda hawaye don ita wulakancin Aliyu har mamaki yake bata, kamar wanda aka shiga tsakaninsu.
"Uhum, Allah Ya kyauta."
Fadin Zulaihat kenan, Rafee'ah ta amsa da amin. Yau ne zuwanta na farko asibitin ita kam, hakan ma don Hajiyar ta kira ta mata tas a waya ne.
"Kenan suna ma bai shirya ya yi maki komai ba?"
Ba ta ko iya amsawa Zulaihat tambayarta ba, bakin ciki da kunya sun rufeta.
"Wannan abun ya yi yawa, wannan wane irin jahilci ne ke dawainiya da shi?"
Hajiya ke wannan sababin, har ta yi ta gama ba wanda ya amsa a yarannata don su kam gani suke ai dama wanda bai ji bari ba zai ji hoho.
***
Da yammaci bayan an yi sallama, Ramlat ta yi mamakin yanda Hajiya ba ta kara ce mata uffan akan Aliyu ba. Ba ta kuma san yanda aka yi aka biya kudin asibitin ba, ta san dai ba Aliyun ba ne. Ta tattara suka wuce gidansu da ita. Hakan ya fi komai yi mata dadi, idan ta juya ta dubi jaririyarta a hannun Rafee'ah, sai ta ji wani sanyin dadi ya rufeta. Ta lura ko ba komai yan uwanta na son yaranta kawai ita din da Aliyun ne basa kauna. Duk kauce kaucen Rafee'ah ta yi ta kyale ta hakura ta karbi yarinyar.
Har suka je gida ba wanda ya tayar da zancen Aliyun.
Daki guda aka bata da ɗiyarta. Hajiya da kanta ta dauki jaririyar ta kai wa Abba.
"Masha Allah." Ya furta yana murmushi.
"Kamar Ramlatu tana karama." Ya fadi gami da duban Hajiya. Murmushi ta yi maganar Aliyu na cinta sai dai ta bar wa cikinta tunda Abban ya ce a rabu da shi a zubamasa na mujiya.
"Wane suna suka zaɓamata?" Fadin Abban yana kallon Hajiya ganin bai fi saura kwanaki biyu ya rage sunan ba.
"Ina ya ɗaga wayarta balle ya faɗa? Sai dai a tambayota."
Abba ya murmusa, Hajiya dai ko yaya abu ya ɓata ranta sai ta san yanda ta fitar ko yaya ne.
"Tambayota."
Ya fadi kai tsaye.
***
Ramlat ta dubi Hajiyarta. Ita kuwa wa take da shi sama da Hajiyar yanzu? Iyayenta sun mata komai duk da irin tokar da ta baɗamusu a idanu.
"Kin kuramin ido, ko shima sunan sai kin tambayeshi?"
Hajiya ta furta a zafafe.
"A sanyamata Rabi'atu."
Hajiya ta ɗan yi shiru sai kuma ta fita. Kamar ta ce ba ta son jinin Aliyu da sunanta sai kuma ta share.
Tana fadawa Abba ta yi daki ta kyaleshi yana dariya. Kai tsaye ya yiwa yarinyar huɗuba.
***
Ranar suna komai da aka yi Abban ne karfinsa. Daga gidan Aliyun an kawo kayan barka, kamar yanda Abban ya ce, ba su nuna komai ba suka karba duk kuwa ba kayan a zo a gani bane.
Yarinya ta ci sunan Hajiya su na kiranta da Ummi. Hajiya tun tana kawaicin har ta saki ranta dalilin kaunar yarinyar da Allah Ya doramata. Balle kuma Abba wanda koyaushe tana hannunsa idan yana gida.
Wannan gatan kadai ya ɗan rage damuwar Aliyu a ran Ramlat, ta dai yi rama ta kuma yi duhu. Amrah na zuwa lokaci zuwa lokaci musamman daga makaranta, tana koyawa Ramlat abinda aka yi a ajin. Yaya Munir bai leƙo gidan ba koda wasa sanin da ya yi Ramlat din tana nan. Bilkisu kam zuwanta biyu gulma na kawota, duk irin habaici da za ta yi ko bakar magana, Ramlat ba ta kallonta balle ta amsa. A nan ma ta ke jin batun auren da Hilal zai yi, kai tsaye ta ce Allah Ya sanya alheri ta share batun wanda ba haka Bilkisun ta so ba.
***
Aliyu ba waya kuma bai zo ba har suka cika kwanaki arba'in cif a duniya. Kamar daga sama kuma suna cikin kwanaki sittin a gidan Hajiya, sai ga Aliyun.
"A kyaleshi, ban yarda a nunamasa wani abin ba. Wanda ya yi nagari, kansa. Ba yanda kika iya ke kuma, sai hakuri."
Abban ya fadi bayan ya je ya yi magana da Aliyu, hakuri kamar koyaushe shi Aliyun ya bada ya kuma ce ba zai kara irin kuskuren ba kamar dai alkawarin da yake yi a baya idan magana ta zo kunnen magabata. Tuban muzuru kenan tunda ba ya fasawa.
"Toh Abba." Cewar Ramlatu idanunta cike taf da kwalla. Ta mike tana gyara zaman mayafinta, bisa umarnin Abban ta je su gaisa da Aliyun kafin a sanya ranar komawarta.
***
Yana falon saukar baƙi ya yiwa jaririyar ƙuri da idanu, sallamarta ya sa shi ɗagowa ya kalleta. Gaba dayansu sun yi kewar juna. Ta kauda idanunta tana jin tsanar kanta da irin son da take yiwa wannan halitta.
Bayan ta gaidashi ya matso jikinta sosai.
"Baby dubi yanda rashinki ya ramar da ni. Baby ina miki Laifuka, wallahi ki sani, bansan ya zan yi na yaƙi wannan fushi da zuciyartawa. Kin fi kowa sanin ina sonki, ina son abinda kika haifarmin. Takaici da bakin cikina, kiran da kika yi waya a gidanku a kaiki asibiti amma kika kasa kirana. Haba Baby, kinsan ba ki kyauta ba."
Ta kalleshi da niyyar gasamishi bakar magana, sai dai hawayen da ta gani a fuskarsa ya kashemata jiki. Ya kwantar da kansa a kafaɗarta. Ta runtse idanu, wutar so da kaunar Aliyu na kara dagula lissafinta, yana don cin galaba a kanta kamar koyaushe. Ta ɗan ja jiki za ta matsa, ganin haka ya ɗago yana kallonta.
"Baby, wayo kika yimin. Ummi kamar ki ta dauka sak. Amma ta fi ki dimple mai kyau."
Ya ƙarashe yana sanya yatsansa dai dai inda ke lotsawa a kumatunta. Itama ta kurawa yarinyar ido, kaunarta na ratsata. Suka kasa kauda idanu daga kan diyartasu har sai da aka ɗauki lokaci.
"Aliyu kana wahalar da ni, kana cutar da zuciyata. Aliyu don girman Allah ka sassautamin."
Ta fadi a raunane don ba ta ma san wane irin sassauci ba, ai ba shi ta sanya sonsa a kirjinta ba. Kuma bai da ikon cirewa, balle ya yaye din.
"Fadamin, me da me kike so na bari, zan daina har abada. A kanki yau Malam har kuka ya yimin ya kuma rantse idan ban je na nemi gafararki da ta iyayenki ba sai ya kwashemin albarka."
Murmushi mai ciwo ta yi. Tasan a zuciya da zafi irin na Aliyu ba dai ya tako kofar gidansu a karan kansa ba. Dama dai da walakin goro a miya don Malam din shima har rago ya kawo na suna, ya zamana raguna biyu aka yankawa Ummi da na Abban. Ta kuma fahimci Aliyun da Malam yanzu ba laifi sun sami jituwa.
Ban baki, rarrashi, alƙawari daban-daban, ba irin wanda bai daukarmata ba kafin ya yi mata sallama da zummar zai kira waya.
***
Hajiya ta yi mata ƙuri da idanu yanda take ta shirin komawarta gidan Aliyu. Magungunan duk da ta kawomata na gyaran jiki ta shanye tas. Ta sallama lamarin Aliyu da Ramlatun, ta san kuma muddin wani ya shiga tsakani shi zai sha kunya. Tana da tabbacin abinda Abba ya hango kenan shi ne dalilin kama bakinsa da kuma rashin saurin yankewa lamarin nasu hukunci.
"Hajiya na shirya."
Maganar Ramlat din ya katse mata tunani, ta kara dubanta. Ta sha daya daga cikin atamfarta Holland wanda Abba ya siyamata na fitar suna, ta yi kwalliya daidai gwargwado abinta. Ummi an mata kwalliya itama sai kamshi take abinta. Ta kauda kai ta share ƴar kwallar da ta cika idanunta.
"Shikenan Ramlatu, Allah Ya kiyaye hanya. A ci gaba da hakuri dai. Kowa da kaddarar rayuwarsa. Tashi ki je Abbanki na falo."
Ta amsa da toh gami da nufar ciki. Hajiya ta bita da ido, duka-duka yarinyar ko shekaru ashirin ba ta kai ba amma jarrabawar rayuwa sun mata dabaibayi.
"Allah Ya kawomaki sauki cikin lamuranki."
Ta furta a fili.
***
A can ma Abba nasiha ya yi mata sosai kafin ya ba ta kudi sosai ya kuma ce ta yi kokarin bude bank account ko don ma makaranta. Ta yi ta godiya har da hawayenta sannan ta mike ta tafi ya bi bayanta da ido. Ji yake da yana da halin sauyamata wannan kaddarar da tuni ya yi, sai dai komai na hannun Madaukakin Sarki wanda zaɓi da kuma ikonSa ya fi na kowa da komai.
***
IDAN KIƊA YA I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/5VwehILsqab
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
23)
IDAN KIƊA YA CHANJA...
Watanta biyu da dawowa gidan, komai ya sauya. Shaye-shayen Aliyu ya ta'azzara duk kuwa da yanda yake kara ramar da shi, yake kara motsewa. Akwai sadda ta bar Ummi a falo tana kicin, sai fitowa ta yi ta ga hayakin shisha na tashi a falon yarinya na jan numfashi dakyar. Ranar har dukanta ya yi saboda cecekucen da suka yi. Ta gaji iyakar gajiya, wannan ne yasa gaba daya rabin hankalinta kacokan ya koma ga kula da Ummi. Idan ka ga dariyar Ramlatu toh tana tare da ɗiyarta ne. Tana yawan shiga wurin Maman Anas duk kuwa da gargadin Aliyu, har ya yi ya bari. Maman Anas itama takan shigo su yi hira ta kara bata shawara da adduo'i. Don halin Aliyu ba ɓoyayye bane.
***
Wataranar Talata ta dawo daga makaranta a gigice, Ummi ke kuka ta rasa meke damunta. Ta yi rarrashin ta shayar da ita amma shiru, kuka ya ƙi ci ya ƙi ƙarewa. Waya ta dauka ta kira Aliyu bayan ta yiwa yarinyar wanka ta sauyamata sutura.
"Ki kai ta asibiti mana."
"Da ace da kudi a hannuna kaima kasan daga makarantar zan kiraka na wuce. Wallahi kudin mota kadai..."
"Naji kar ki isheni. Nima dai kinsan ba wani kudin a jikina. Kuma dama sai yau kika san amfanina har kika kirani, kwanakinnan ai na dauka kin koma ƴar kanki mai cikakken iko. Tunda ko ba komai na bar ki kin koma jami.."
Ta katse kiran, ba ta son hayaniya, kukan Ummi kadai ma ya isheta. Ta dauketa bayan ta zura hijabi ta fice gidan Maman Anas.
"Kukan me take haka?" Fadin Maman Anas sadda ta sa hannu tana karɓarta.
Itama Ramlat kamar ta yi kukan ta ce.
"Wallahi ban sani ba, tun a makaranta take kukannan kinga ba mu tashi ba ma na taho kawai."
Nan Maman Anas ta taɓa cikin ta bubbuga.
"Ga abinda ke damun yarinya, cikinta ne a kumbure."
Daga haka ta yi mata dabarar su ta manya, gishiri kaɗan ta sa a ruwan ɗumi ta ba ta, aka samu cikin ya lafa ta yi shiru. Ganin haka ta miƙamata ita.
"Sa mata nono a baki."
Ba musu Ramlat ta karɓe ta, sai lokacin hankalinta ya ɗan kwanta. Ta shiga ba yarinya, karshe ma yarinyar ta daina karɓa ta yi shiru, can ta soma nishin kashi. Ganin haka Ramlat ta yi dariya. Harara Maman Anas ta watsamata cike da wasa.
"Kinji ki, sai yanzu kika samu nutsuwa kenan? Ramlatu kenan."
Dariya ta kara yi. Nan kuma ta mike hadi da yi mata godiya ta bar gidan.
A bakin kofa ta tarar da mashin din Aliyun, wannan ya bata tabbacin ya dawo gidan.
Babu fargaba ko shakkar komai ta shiga ciki, a falon ta tarar da shi yana safa da marwa, tana shigowa ya yi kanta kamar zai kai mata duka, ba ta ko kalleshi ba ta gifta ta wuce. Ya bi bayanta zuwa dakin.
"Don tsabar iskanci ina magana kin katse waya kuma kika fita ba da iznina ba? Ita Maman Anas dinnan ko uwarki ba kya jin maganarta yanda kike jin nata a yanzu! Toh wallahi Ramlat kika kara shiga gidan matarnan ban yafemaki ba!"
Kamar da dutse ya ke magana, haka ta yi shiru ta cirewa Ummi wando ta dauketa zuwa banɗaki don yi mata tsarki.
"Kee! Ni kika maida ɗan iska ina magana kin kyaleni?"
Tana jinsa ta yi banza har sai da ta gama uzurinta ta fito ta sakawa yarinyar wando ta shimfiɗe. Tana jinsa ya yi ƙwafa ya fice daga dakin a fusace. Sai a sannan ta bi hanyar da ya bi da kallo, kwanakinnan iskancin ƙaruwa yake. Tunda ya soma wani sabon chatting a waya wai shi Whatsapp shikenan ya zama shagalalle. Sai ya kai biyun dare yana hira a waya, abin yana mata ciwo matuƙa. A gefe daya kuma babban tashin hankalinta na ganin tun dawowarta gidan ba ta ga al'adarta ba, ga yanayin sauyi da ta ke ji na tashin zuwa da yawan ciwon kai da kuma baya.
Faɗan da ta yiwa kanta, shi ne ɗaure ɗamarar zama da Aliyu a kowane hali na rayuwa. Barin sirrin zamanta da shi a cikinta, ta gaji da yin abin kunyar daka yaji kuma ta dawo. Ga Abba da kwana biyunnan bai jin dadin jikinsa. Wannan ma babban tashin hankalinta ne.
Ta sauke ajiyar zuciya sadda ta ga dagasken dai Ummi ta yi nisa a bacci sannan ta mike ta kimtsa jikinta da neman abinda za ta sawa bakinta na salati.
***
Maimakon karfe sha biyun da ya saba shigowa a ƴan kwanakinnan, karfe takwas da mintuna ne daren ba zato sai gashinan ya faɗo gidan. Tana falon tana duba takardun makaranta, Ummi na gefenta kwance idanunta biyu ta ƙura idanunta ga takardun da fitila ta haskesu. Jefi-jefi takan kalli yarinyar ta yi murmushi ko kuma ta yi mata wasa.
Ko kallonta bai yi ba kamar yanda itama ba ta kalleshi ba har ya shiga ɗakinsa ya fito. Ƙamshin turaren da ta ji ya sanya ta kallonsa, ya sauya ƙananun kayan dake jikinsa zuwa shadda ruwan madara har da hula abinsa. Sai ya koma mata Aliyunsa sak wanda ta sani tun farkon haduwarsu, bambancin, wannan Aliyun a rame yake ga leɓɓansa da suka ciza suka ƙara yin duhu fiye da baya. Ance ko yaya mijinka ya kai ga lalacewa, kana kishin abinka musamman ma auren da aka yi akan tafarkin so da kauna. Hakan ce ta faru ga Ramlat, ji ta yi gaba daya ta rasa nutsuwarta, shi kuwa yana tsaye da taimakon fitilar karamar wayarsa da ya sanya a baki yake haska hannunsa yana gyara zaman links. Miƙewa ta yi ta je har gabansa ta tsaya. Ya dubeta gami da haske