Showing 87001 words to 90000 words out of 230725 words

Chapter 30 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1060

kenan sadda ta cire nonon a bakin Ansar da bacci ya yi awon gaba da shi. Kwantar da shi ta yi sannan ta mike ta karasa ga Aliyun ta taimaka mishi da sanya links na hannu. Kallon juna suke yi cike da so da kauna, abubuwa da dama suka shiga dawo musu a kai.

"Idan ban godewa Allah da Ya ban mace ta gari kamar ki ba Baby, me zan yi?"

Ta yi murmushi wanda ke karamata kyau.

"Allah Ya yi miki albarka. Wallahi idan har ni Aliyu, aljannarki a ƙarƙashina take, na ɗagamaki na ƙara ɗagawa ki shigeta."

Ta yi dariya.

"Dagaske nake."

"Toh na gode sosai."

Ya ja karan hancinta.

"Ni zan fadi haka Baby."
Murmushi ta yi shi kuma ya daga Ummi cak ya ba ta sumba a kumatu.

"Daukomata takalmi."

Jin haka Ummi ta kara wangale baki, Ramlat na dariya ta karasa ɗakin ta dauko. Yana rike da ita ta sanyamata, rakiya ta musu har bakin kofa sannan ta dawo.

Kwanciya ta yi tana tunanin abubuwa da dama. Sauyawar Aliyu ya fi komai yi mata dadi a zuciya.

Tun mutuwar Abba, sai kuma abin ya zama kamar yayewar matsalarta. Tun tana ganin Aliyu kamar karya yake bai bar shaye-shaye ba, tun tana ganin kamar komai yana yi ne don ganin idonta har ta zo ta fahimci dagasken ya bari. Maimakon shan sigari sai ya koma ma'abocin shan ruwan shayi mai citta da kanumfari wanda hakan ya kara taimakawa wurin danne mishi kwadayin sigari balle kwaya.

Duk abinda zai tunamishi da bariki ya yi watsi da shi, ya dinga cusa kansa wurin mutane nagari, y kasance maimakon idan ya dawo daga kasuwa ya je matattarar yan iska, sai ya sauya da zama a masallaci tsakanin Magriba da Isha'i yana jin tafsirin Malamai. Wasu lokutan Ramlat takan farka ta ganshi durkufe cikin Sujjada yana kuka da addu'a. Ita kanta takan ji hawayen ya cika idanunta ta kasa komawa ta mike ta yi alwala ta yi zaman tayashi.

Abu kamar wasa, lamarin ya ci gaba da tafiya a haka. Malam har hawaye ya yi don dadi ganin sauyawar dansa, ya kuma kara yarda cewa bawa bai isa ya shirya dan uwansa ba idan Allah bai shirya ba.
Anan ne Aliyu ya gane cewar ashe ba shi ne ba'a so ba, halinsa aka tsana. Abulle ma ta yi kuka don murna. Akwai da yawa da suka kasa gaskata Aliyun, har lokacin basu shiga harkarsa. Dama haka rayuwa take, ba lallai ne kowa ya so ka ba, hakanan ba ka isa ka ce ba ka da maƙiya ba.

A bangaren Aliyu da yan uwan Ramlat din ma sai godiyar Allah, ya zamana zai je har su ɗan yi hira da Baba Dakta. Hajiya ma sannan ta sakar mishi sai dai akwai ƴar kunya tsakaninsu. Tsakaninsa da Munir kuwa ko gaisuwa bai haɗasu. Koda ya gaidashi ba amsawa yake ba. Ƙarƙari idan ya yi sallama zai amsa yana cin magani. Wannan tasa shima ya watsar da lamarinsa.

Har Gombe ya kwashesu suka je ya sada zumunci da yan uwan Innarsa, sun yi mamaki sosai don ganin abin suka yi kamar mafarki. Kusan Aliyu tun Innarsa na raye rabonsa da su. Wannan ta sa sosai suka tarbesu suna tattalinsa da iyalinsa har suka dawo.

***
Ta shiga binsa daga daki zuwa falo, da ya gaji sai ya tsaya yana kallonta. Ta turo baki kadan.

"Baby, meye wai?"

Ramlat cike da shagwaɓa ta amsa.

"Muhibbat ce fa Baban Ummi. Ta tako gidannan ya fi a ƙirga. Har ta haihu a yi suna ban je ba? Gaskiya ban kyauta ba wallahi."

Ya taɓe baki, ta kuramishi idanu tana murmushi cike da so da kaunarsa da yanzun ta ke ji ba kaɗan ba. Ya ɗan murmure hakanan ya yi haske kadan ba kamar a baya ba. Kasuwa ta dan dawomishi daidai don yanzun yana maida hankali sosai.

"Nayi zaton ma asibiti za ki cemin za ki, ashe ba haka ba ke yawo kike son fita."

Ta daure fuska.

"Ni lafiyata kalau, na fadamaka ba ba ciki bane. Ko ka manta na yi planning?"

"Planning wane iri ne wannan da za ki dinga amai da kwadayi? Yaushe rabonki ma da al'ada?"

Ta numfasa ba don ta wani dauki abin da muhimmanci ba don dama idan ba ta mance ba Nos ta fadamata cikin side effect din maganin har alamomin masu ciki ko daukewar jini zai iya jazamata.

"Shikenan zan je, amma daga nan zan wuce gidan Muhibbat. Don Allah!"

Ta fadi da sauri ganin yana kokarin cewa a'a, ya yi dariya.

"Shikenan, a gaishesu. Ki dai tabbatar kin je asibitin."

Ta rungumeshi gami da yin godiya. Ya bata sumba a kunci gami da bata kudin mota da na ganin likita.

Yana fita itama ta shirya tsaf ta goya Ansar ta fice.

***
RUBUTACCEN I just published "BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/pcYjI4bZBab


🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.


27)


  "Ke kam sai ayi magana ki yi shiru."

Maganar Muhibbat ya katsemata tunani a karo na barkatai, ta kakalo murmushi ta dubeta.

"Kai ban ji ba."

"Cewa nayi ina Ummina?"

Cike da kaunar yanda Muhibbat ke sonta da abinda ta haifa ta amsa.

"Tana can gidan Hajiya."

"Kai jamaa, da alama dai Hajiya ta kwacemana Ummi."

Dariya suka yi lokaci guda. Hira dai ta yi hira har hakan ya mantar da Ramlat damuwarta na cikin da ke jikinta. Duk da amsar da Likita ya ba ta sadda ta mishi tambaya hakan bai gamsar da ita ba sai da ta ƙara tambayar Muhibbat.

"Wai nikam Sis, dama ana iya samun ciki ko anyi family planning?"

Muhibbat ta dubeta, me za ta yi ba dariya ba. Yi ta ke ba kakkautawa har sai da Ramlat itama ta dara.

"Mene wai na dariya toh?"

"Ah ba komai fa. Sai dai na harbo jirginnaki. Ai idan Allah Ya so ikonSa, ba planning ba, ko mahaifar aka juya sai ki ga an samu ciki. Meyafaru?"

Jiki a sanyaye ta ce.

"Implant na saka, abin mamaki wai ana yimin test aka ga ina da ciki. Wai gocewa ya yi."

Jinjina kai Muhibbat ta yi.

"Ana haka, na sha ji ana fadin haka. Wata har allura ta yi amma bai karɓeta ba sai ga ciki. To ke me zai dameki? Ai ko ba komai Ansar ya shekara."

Ajiyar zuciya ta saki, kuma fa hakane. Idan a baya munanan ɗabi'un mijinta ne ta ke gudu, yanzun komai ya kau, ya zama labari da yardar Allah.
Muhibbat ta ci gaba da ba ta shawara akan kar ta damu ba komai. A karshe ta ji zuciyarta ta yi sanyi.

Sai wuraren yamma ta yi mata sallama ta bar gidan bayan ta diremata turmin atamfa cikin wadanda ta samu na barkar Ansar. Godiya sosai Muhibbat ta yi kuma ko kadan ba ta raina ba duk kuwa da cewar ta fi karfinsa. Har kofar falon ta yi mata rakiya suka yi sallama.

***
  Juyi ya shiga yi da ita yana karawa, ita kuwa banda dariya ba abinda ta ke, hakan da ya yi ya zo mata a hagunce don ta yi mamaki. Ba ta zaci ganin irin wannan farin cikin a fuskarsa ba. Farin ciki ne da ya taho tun daga ƙahon zuciyarsa. Ya shiga sumbatar duk inda bakinsa ya kai a fuskarsa.  Ta kauce gami da faɗawa kan kujera tana dariya lokaci guda tana mai watsa mishi harara.

"Kai don Allah Abban Ummi. Duk rawar ƙafar don cikin ne? Ciki na uku?"

Zama ya yi a gefenta gami da riko hannunta.

"Bar ni na yi murna kinji ko? Kyaleni Baby. Allah Yasa ki haifarmin mace na sanyamata sunanki. Kin cancanci komai daga gareni."

Ita dai murmushi take tana kara godiya ga Allah da tarin ni'imominSa wanda ba ya yankewa. Yau Aliyu ke ɗoki da zumuɗi mai yawa haka saboda ance tana dauke da juna biyu?

Kumatunta ya ja wanda ya maidota hayyacinta. Suka yiwa juna murmushi kafin ya jawota jikinsa ya soma aika-aika😜. Kukan Ansar ne da ya fado daga saman kujera cikin bacci ya katsemusu komai, kusan a tare suka isa wurinsa ya rigata daukarsa. Safa da marwa ya shiga yi yana jijjiga yaron, hakan ya bata damar tsayawa ta kurawa Aliyun idanu cikin duniyar tunani. Kwallar farin ciki suka cikamata idanu ta sharesu. Abbanta ya faɗomata a rai, ta tabbatar da yana raye zai fi kowa farin cikin shiryuwar Aliyunta.

Ta so ace Abba da Aliyunta sun yi rayuwa kamar na ɗa da uba tun a baya, ta so ganinsu tare a zaune suna hira da dariya. Sai dai kuma Allah bai nufi hakan da faruwa ba.

***
  Labarin cikinta har gidansu, ta sha dariya wajen su Zulaihat da suka hadu a gida.

"Dama za ki ka da yin Ubangiji ne? Kallonku kawai nake."
Hajiya ke wannan zancen tana gutsirar goronta wanda ya zamemata jiki.

Ramlat ta yi dariya.

"Yanzu dole ki yaye Ansar fa ko?"

Rafee'ah ke zancen tana dubanta.

"Anya kuwa? Ni gani nake kamar ba matsala tunda ta ce likita bai hana ba."

Fadin Zulaihat.

"A'a ba zai yiwu ba, dole ma a yayeshi. Idan ya rame itama ta rame fa? Ai dukkansu abin ba zai zo musu dakyau ba." Hajiya ta furta cike da kulawa. Kulawar da idan Ramlat ta dubi ƴan uwannata ta ga dukkansu a cikin lamuranta suka tsoma baki sai ta ji dadi da farin ciki sun lulluɓeta.

A ranar dai haka ta koma gida ba Ansar don Hajiya ta ce ba zai yiwu ya ci gaba da shan mama ba. Har da ƴar kwallarta na tausayin yaron, don ma dai yana da kumarinsa.

Ganinta ita daya Aliyu ya ci dariyar da ta ishe shi.

"Ai koda ba ki yayeshi ba, da hannuna zan daukeshi na miƙa wa Hajiya ko na kaiwa Amarya shi. Ta ya za ki zauna kina ci gaba da shayarwa ga ciki? Ba zan yarda ba."

Ta turo baki ta shige wanka ta kyaleshi zaune gefen katifa.

Allah Ya taimaketa ba ta yi ciwon yaye ba sai dai sun kara ciccikowa.

Hankalinta ya kwanta ta koma rainon cikinta da zuwa makaranta abinta.

***
  BAYAN WATANNI TAKWAS..

Binsa kawai take da kwando yayinda yake aikin lodar kayan jarirai kala-kala unisex.

"Don Allah ya isa haka Sweet Aliy."

Bai ko kalleta ba balle ya saurareta.

"A ina ka samu kudi haka?" Ta ƙara jefamasa tambaya don ita kam abin ma tsoro ya shiga bata duk kuwa da ta san yanzun Aliyun na samu fiye da baya. Ganin ta ƙi ɗaga ƙafa ta bi bayansa, ya janye kwandon ya yi gaba ya kyaleta yana duba wasu turaruka na jarirai. 

  "Wannan ba Ramlatu bace?" Jin an ambaci sunanta ne yasa ta juyawa bangaren da ta ji muryar. Kallon kallo suke da juna. Kamannin Hilal sak a fuskokinsu. Tuni ta gane su waye, Anti Fareeda da sai Murja da ƙaton ciki wanda haihuwa yau ko gobe.

Ta saki murmushi sadda suka ƙaraso gareta, Murja ko gaisuwarta ba ta amsa ba ta jefomata tambaya.

  "Kema wani cikin ne da ke? Bilki ta ce haihuwarki biyu yanzu ta uku. Kin ji labarin auren Hilal ko? Kinga Allah ba azzalumin bayinSa ba ne."

"Dadina da ke Murja wataran kamar yarinya kankanuwa, ke har sai an ce miki ciki gareta? Saukinta daya ma na sunnah ne. Uhum, gwara ma da aka yi yunwa halin kowa ya fito. Da yanzun da auren Hilal za ta haifi shegu."

Kallonsu take, kamar wacce aka ƙullewa baki ta kasa magana, kirjinta wani tafarfasa yake yi. Ta juya kawai ganin idanunta ya ciki da kwalla. Fareeda ta kara magana.

"Kinsan ma naji ance mijin ƙanjamau ne da shi. Ga duka na safe daban na rana daban."

Ta ƙara daga kafarta daidai sadda Murja ta kara magana.

"Ai dama Allah ba azzalumin bayinSa bane, tun ka aje ko'ina yarinya ta soma ganin sakayya. Ni dama kishiya ya ƙaromata muga ta karshen soyayya."

Tuni ta yi gaba ta bi bayan mijinta kamar ba ta ji ba. Karo suka kusan yi, da sauri ya riƙe kafarta. Kallon kallo suke da juna, ya sa hannu ya gogemata hawayen.

"Meyafaru? Keda wa? Ina can ina kokarin biyan kudi na waiga ban ganki ba. Lafiya?"

Ya ƙarashe yana daga wuya kamar zai hango abinda ya ɓata rannata, bai ga kowa ba sai wasu mata biyu dake kallonsu.

"Ba komai fa, abu ne ya shiga idona."

Ya daure fuska, zai kara magana ta yi saurin giftawa ta gefensa ta soma tafiya gami da fadin.

"Don Allah mu je."

Bai bi ta kanta ba ya wuce zuwa bangaren matan yana dan dube-dubensa, so yake ya ga ko zai ga fuskar da ya sani cikin ƴan uwansa ko na Ramlat din amma babu ɗaya. Zai wuce ne ya ji wata a gefensa kamar da rada tana fadin.

"Ko shi ne mijinnata?"

Ya waiga ya kara kallonsu, shi ɗin suke kallo dai, hakan ya ba shi tabbacin su ne silar hawayen Ramlatu. Ganin dai zargi ne ba shi da tabbas ya sanya shi watsamusu banzan kallo ya wuce, duk suka sha jinin jikinsu suka kauda kai.

  "Kinsan fa mashayi ne, kar ya kawomana duka." Fadin Murja a tsorace bayan tafiyarsa.

"Atoh, gwara ni banda komai, ke kam naƙudar dole zai sanyaki ko ya kaiki lahira."

Suka tuntsire da dariya sai dai fa ba haka suka so ganin Ramlat din ba. Alamun jin dadi sun bayyana a fatarta da kuma jikinta, sun so ganinta a yamushe yanda za su fi jin dadin kai labari, amma hakan ma da suka yi mata sun dandana mata wani bakin ciki. Wannan yasa hankali kwance suka ci gaba da siyayyar abinda ya rage ga Murja.

***
  Tun a hanya yake masifarsa jin diramar da ta yi a shagon da ya uwan Hilal,  har suka dawo gida, ita dai ba ta iya tankawa ba banda hakuri da take ba shi. Koda suka shiga  ita ya bari da baza kayan tana kallo, kallon take amma zafin kalaman su Murja ya tsayamata a ƙahon zuci.

"Mtsw. Sai ki zauna ki yi ta kuka akan abinda ba wanda ya isa ya sauyamaki. Ko mene ya riga da ya faru, akwai dan iskan da zai hana. Don ubansu me suka ce? Da shege za ki haifa a gidan Hilal din ko? Dama hakan ce ta faru naga uban da zai hanani dauko ƴaƴana!"

Ta dubeshi a razane, sai kuma ya shiga istigfari. Ransa sosai ya ɓaci don shi a duniya ya tsani a yi mishi abu bai rama ba. Ya so ace a gabansa suka yi yanda zai zazzagamusu bala'i ya nunamusu haukartasa.

A karshe kuma ya koma lallaɓata, ya shiga jan ta da hirar Baby gami da nunamata kayayyakin su ka shiga dariya zuciyarsu ta yi sak.

***
Rayuwarsu abin sha'awa, zama na so da kauna da aminci irin wanda Ramlat ta jima tana mafarki, Allah Ya tabbatarmata da shi. Tana zuwa makaranta abinta, Amrah na nan ta ƙi kula kowane saurayi don ta rantse sai ta kammala karatunta.

  Babu laifi suna zumunci da yan uwan Aliyu yanzun musamman wadanda suka hada uwa. Sukan zo itama ta jajjemusu tare da Aliyun.

A yanzun ba abinda ya fi burgeta sai zaman karatun da Aliyu ke dauka duk karshen sati wurin wani Limamin unguwarsu.

Haihuwar Ramlat ya kama a watan azumin Ramadana, alokacin bai fi sati uku ya yi saura a kama azumin ba.

A sannan karatu ya dau zafi don su na aji na biyu zango na farko sakamakon yajin aikin da aka dinga tafiya wanda hakan ya ɗan kawomusu cikas a karatun.

Wataranar Asabar tana zaune a tsakar gida ta dage tana research a Google na wani project da aka bata. Aliyu na daga gefenta ya kwanta saman filo ya zubawa sararin samaniya ido yana kallo. Shirunsa da ta ji ya yi yawa ne yasa ta dubansa. Ganin hankalinsa ma ba ya kanta ne ya sa ta mika hannu ta ɗan matsa yatsun ƙafarsa suka yi ƙara. Ya juyo ya dubeta gami da ɗan lumshe idanunsa ya bude.

"Lafiya? Me kake tunani?"

Murmushi ya ɗan yi.

"Rayuwa nake tunani Baby. Duniyar tsoronta nake kara ji, tuna watarana zan mutu fargaba hakan ke sanyani. Idan na zauna ina lissafi sai na ga kamar ban taɓa aikata abin kirki ba. Tun ina saurayi iyayena ke shaƙar bakin cikina, na tsoma kaina a harkar shaye-shaye. Na dauki rayuwar da ba tawa ba, yawo da ƴaƴan masu hannu da shuni, na ɗorawa kaina. Na baƙanta ran jama'a da dama, a karshe ko ban aikata zina ba, na shafa jikin matan da ba nawa ba. Idan na tuna akwai ranar da zan koma ga Allah, a binne ni cikin raminnan, a doramin itace a kara bina da kwali sannan a rufamin ƙasa a fuska, ina shiga matsanancin tashin hankali Baby.  Daidai da ɓangarenki na cutar da ke, na kasa daukar nauyinki, na kasa kula da lafiyarki, na kasa ciyar da ke a lokuta da dama kamar yanda sutura da shanki bai cikin damuwata a wasu lokutan. Ban tsaya anan ba na jawomaki abin gori, na kashe aurenki don na rayu da ke. A sanadina iyayenki sun zubar da hawaye a kanki, nayi amfani da karfin son da kike yimin na yaudareki. Anya duk wannan tarin saɓon da nayi, Allah zai dubeni Ya sanyani sahun muminan bayinSa?"

Kallonsa take tun soma maganarsa, kamar yanda take fitar da hawaye, haka shima yake fitarwa. Girgiza mishi kai ta shiga yi. Ta ture litattafan ta karasa gareshi gami da damƙe tafin hannunsa cikin nata.

   "Kar ka kara irin wannan kalaman, Ubangiji Mai Rahma ne. Wanda ma bai tuba ba, kira Ya ke yi akan ya zo ya nemi gafararSa zai yafemishi, ballantana wanda Ya kusantoShi da neman gafara ba? Ai shi At-Tawwabu ne Mai yawan karɓar tuban bayinSa. Koda wasa kar ka sake zuciyarka ta jefaka cikin kokwanto Allah Ba zai gafartamaka ba. Ka yi irin tuban da Ya ke so, ka kuma nemi gafarar wadanda  ka aikatawa ba daidai ba. Me ya fi wannan dadi? Abinda ya riga ya faru ba mu isa mu sauyashi ba."

Gyada kai Aliyu ya shiga yi sai kuma ya yi shiru, Hilal, shi ya faɗomasa a rai.

"Na nemi wata alfarma?" Ta tsinci muryarsa karo na biyu. Ta kara dubansa ta gyada kai.

"Hilal, ki nemar mini gafararsa, ki ce ya yafemin koda ace Allah bai ban ikon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login