Showing 201001 words to 204000 words out of 230725 words

Chapter 68 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1095

sanyaye.

"Dama kun san juna?"

Dada ta jefo tambayar ga Hajiya Zeenatu.

"Eh, Ƙawata ce."

Ta amsa a dake, saura kaɗan dariya ta suɓucewa Kausar, AlHassan ya sa ƙafa ya ɗan taka ta don ta gimtse.

"Bayan an zauna sai Hussein ya fidda waya. Hafsat ya kira ya ce ta taho sashin Dada tare da Amal. Hakan da ya fadi yasa ta fahimtar komai, don haka da toh kawai ta amsa.

***
Ramlat da tun soma wayar Hafsat ta kafeta da ido.

"Hamma Hussein ya ce mu je."

Ta gyada kai, ta yi wankanta ta ci ado da wata shadda da aka yi mata dinkin doguwar riga ya sha aiki. Ta cakare ɗaurin ɗankwali don Ramlat ba baya ba. Ta ɗora mayafi a saman kayan ta zura takalmi suka fita tare. Hakanan ta ji gabanta na bugu da sauri-sauri, ta kara kallon Hafsat wacce ke wani zumudin suna tafiya sai janta da hira take amma ba ta fadi dalilin wannan rawar ƙafar ba.

A ƙofar falon farko suka yi sallama, kunya sosai ya kama Ramlat don ba ta zaci ganin sauran jama'a ba. Ta durkusa a kunyace ta gaishesu. Cike da fara'a aka amsa, nan kuma wata tsohuwa ta ɗauki guɗa da biyu. Jin haka daga cikin dakin, sai ga Kausar ta leƙo, Hafsat na ganinta ta tsallaka.

"Adda, dagaske ta zo?"

Hafsat ta tambaya da raɗa-raɗa, Kausar ta yi dariya ta nuna ƙofar falon.

"Tana ciki."

Hafsat ta harari ƙofar.

"Makira, yau ƙarshenta ai ya zo."

Suka yu dariya sabida duk da harshen fillanci suke maganar, Ramlat ta karaso.

"Muje ko?"

Sai kuma ganin Kausar suka shiga gaisawa, wasu mutan falon duk sun mike sun biyo baya don ba su kaunar abinda za'a yi ya kasance babu su.

Gaba ɗaya ana zazzaune har Hajiya Zeenatu da ta soma sakewa ganin Hajiya Binta har su na hira. Tana so ta tambayeta yanda su Dada suka ɗauketa amma babu dama tunda ba su keɓe ba. Ba su kadai ne a falon ba. Sallamar da aka yi duk ta dawo da hankulansu bakin ƙofar musamman ganin yanda wuri ya ɗauki guɗa.

Hafsat ce ta soma shigowa sai Kausar, bayansu kuwa Ramlatu.

Wani irin miƙewa tsaye Hajiya Zeenatu ta yi a matukar gigice. Babu chanjawar da za ta yi ta kasa ganeta tsabar tsantsar tsanar da ta yi mata. Ido waje ta ke duban Ramlatu, daga kan kafafunta har zuwa dukkan gaɓoɓinta babu inda ba ya rawa. Ba ta ƙara razana ba sai da ta ji muryar wata na fadin.

"Ƙaraso ciki ki zauna, Amaryar Husseini. Lale lale da kyakkyawar halittarnan."

Wani ihu Hajiya Zeenatu ta kurma kafin ta yi tsalle da nufin isa ga Ramlatu.




I just published "BABI NA SITTIN" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1021339453?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=4X2TU9EgqK9sZlhD1RiJLYSmRa3JHzKonALRYeMQgs42rcaB4hSZEFfZEuyDyjNLmgxQTxRGGIYovRiJIB7fWJjhHoMqPgV6u1FPxMnKYkUE%2FDXuKH3NHflk4iDkMg3R



🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

60)


Caraf aka damƙe hannunta, ta dubeshi tsakar ido ya yi mata wani kallon banza, kallo na tsana da ya jima yana dannewa. Idanun Hajiya Zeenatu ya yi wani mugun kaɗawa. Ganin komai ta ke kamar a mafarki. Wani irin uban zufa ya haɗemata duk da iskar da fankokin ke bayarwa. Yarfar da hannunta ya yi. Bai kuma yi wata-wata ba ya dauketa da mari hagu da dama. Kallo daya idan ka yiwa fuskar Hussein za ka fahimci tsantsar ɓacin ransa. Abu ne da ya jima yana dannewa. Hannunsa har rawa yake sadda ya ke nunata da yatsa yana magana.

"Ko a mafarki! Kar ki ƙara tunanin cutar da matata!"

"Hussssseiin.." Ta furta da rawar murya ga hanjin cikinta da ta ke jin sun dunkule wuri guda. Idan ba ta yi ƙarya ba ma, ta ji fitar tagwayen tusa daga jikinta.

"Yes, Hussein ne. Wanda kika kashewa rayuwar shekaru biyar! Kika raba shi da asalinsa! Ki ka tauye kuruciyarsa don kafirin zuciya da zalunci irin naki! Idan ke mahaukaciya ce da ba ki gano kuskurenki ba, kika daukemu shashashai ki ka ci gaba da yin yanda ki ka so da tunanin kin ci galaba ko kuma tunanin ni Hussein ina sonki, kin yi ƙarya. Kin manta yanda muka hadu kuma muka rabu a farkon haɗuwarmu? Har tunaninki ya ba ki damar hango ni matsayin masoyinki? A'a, kin yi kuskure! Dama wannan ranar nake jira. Na auri mafi soyuwa a wurina da iyayena, mafi ƙi a wurinki sannan na yar da ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda! Ko ba komai yanda kika tako garinmu kika daukeni cikin dangina, hakanan na dawo."

"Hussein! Karya ka ke! Karya ka ke wallahi! Ni za ka ci wa mutunci?! Ka san irin son da nake maka?! Ka rasa wa za ka auro sai wannan baƙar ashanar?"

Nan fa ta tubure ta dinga maka ashariya, wani marin ta ji, wannan karon ba Hussein ba ne. Dada ce da fuskarta ta gama jiƙewa da ruwan hawaye.

"Rufemana baki! Makira azzaluma kawai! Kina zaton wawaye ne mu! Allah Ya isa tsakaninmu da ke! Alhakinmu da kika ɗauka na tsawon wannan lokacin sai Allah Ya sakamana walla.."

Kuka ya ci karfin Dada har muryarta na shaƙewa, kusan ma da yawa hawayen suke yi musamman don tausayin Dadar wacce ta yi uban jinya da Hussein ya ɓace kafin ta samu waraka amma fa koyaushe cikin kuka ta ke da addu'a. Ramlat ita kanta kukan ta ke yi sosai, daidai sadda Hussein ya zura hannu a aljihu ya fiddo takarda ya kama hannun Zeenatu ya damƙamata.

"Meye wannan?! Me kake nufi? Dama ka kawo ni cikin danginka don ka ci mutuncina? Me ka ke son ka cemin?"

Tana maganar tana jijjiga takardar yayinda take kuka har da majina.  Ɗigon tausayinta ba wanda ya ji don dama kowa da tabon shekarun da ya yi cikin zulumi da kewar Hussein a zuciya.

Wani irin tsalle ta daka da zummar shaƙo wuyan Ramlat sai dai tuni matan suka damƙe ta, Hussein shi kallon mamaki ma ya tsaya yi mata na irin wannan ƙarfin halin wai ɓarawo da sallama. Zagi take ƙudundumawa tana kiran sai ta hallaka duk wanda ke shirin rabata da farin cikinta.

"Modibbo ya yi gaskiya! Dama ya ce kar na zo! Kar na zo! Ba sona ku ke yi ba! Ashe da gaskiyarsa! Wallahi Hussein ka yi kaɗan! Zamanmu har abada ba na ƙare ba ne! Yanzu aka fara!"

Gaba daya Hajiya Zeenatu ta birkice, fuskarta kace-kace da hawaye ga majina tana aikin jansa. Idanunta yanda ya rufe har ba ta san me ke fita daga bakinta ba.

Kowa a dakin ya shiga salati jin sunan da ta ambata.

Hussein ya ma kasa magana sai murmushi, ga duk wanda ya gani kuma zai fahimci na zallar takaici ne kawai. Dama shi kadai ya zarga, duk kuwa da bai gama tabbatar da hakikanin lambar wayar da ya ɗauka a wayarta ba tunda ba shi da lambarsa, amma daga kiran da ya yi sau daya da kuma muryar da ya ji, jikinsa ya ba shi tare suke komai. Hannu kawai ya harɗe a kirji bayan ya ja baya ya ci gaba da kallon diramar da kowa ya ke jin  sunan wanda ta ambata, babu wanda ya zata. Dada kuka sosai ta ke yi don har numfashinta na sama, wannan ne yasa AlHassan janyeta zuwa ɗaki don kwantarmata da hankali. A hankali Hussein ya juya zai fice, wannan yasa Hajiya Zeenatu bin bayansa fuuu bayan ta ture duk wanda ke gabanta. Koda ta kalli Ramlatu, wani banzan kallo kawai ta watsamata na za mu haɗu sannan ta yi gaba don tasan ba damar taɓa ta yanzun. Hafsat ta yi caraf ta dauki jakar Hajiya Zeenatun ta buɗe ta cusamata takardar da Hussein ya bata wanda ta yi wurgi da shi a tsakar ɗakin sannan ta bi bayanta da sauri.

AlHassan dake ɗakin tare da Dada  jin ƙugin tashin mota ya mike da sauri ya fito. Ganin babu Hussein a falon yasa da sauri ya fita.

"Kar ka sake ka budemishi gate!"

Ya fadi da ɗan ƙarfi yanda Maigadin zai ji kuma da harshen fulatanci. Nan da nan Maigadin ya fasa. Hussein ya ci burki, ita kuwa Hajiya Zeenatu dake bubbuga gilashin mota tana bin motar don ya saurareta, itama ta tsaya cak. Hafsat wacce tuni ta jefamata jakarta tana tsaye kallon dirama da ƙarfin hali irin na Zeenatu. Daidai sadda Hussein din ya fito daga motar. Hajiya Zeenatu ta cakumi wuyan rigarsa bai yi wata-wata ba ya hankaɗata. Sai yanzun ya tuna da akwatin kayanta da ke boot din motar, tun a can gidan ya nunamata za su kwana biyu gidan Dada, don haka ta haɗo komai na kayanta. Ya buɗe ya fiddo akwatin kafin ya ja hannunta tana binsa ta na magana kamar zautacciya.

"Hussein ina sonka! Ban taɓa son wani namiji dagaske ba sai kai! Ka yimin rai kar ka rabu da ni! Kar ka manta da dukiyarmu, na tuba ka yafemin don Allah."

Wannan karon da alamun karaya sosai a muryarta, shi kuwa shareta ya yi bai ce uffan ba har sai da ya fidda ita daga ƙofar gidan gaba ɗaya. Daidai sadda Rasheed ya dawo gidan don ya ɗan fita. Ganinta ya gane abinda ke faruwa don yana sane da shirin Amininnasa. Akwatin ya diremata ya dubeta a wulaƙance.

"Sai ki kama hanya ki bar garinnan idan kinga dama, idan ba ki gani ba ki zauna ki ƙara gwada kashe Ramlat ki gani ko zan bar ki da rai."

Daga haka ya juya ya dubi Buzun maigadinsu mai jin fulatanci, cikin fulatancinsa wanda ya ɗan farfaɗo ya ba shi umarnin koda wasa kar ya bari ta shigo gidan. Daga nan ya komai ciki tare da Rasheed.

"Na dauka wurin Kawu za ka je. Shiyasa na fito don tsayar da kai."

Alhassan ya furta yana dubansa. Ya shafi suma gami da runtse idanu, radadi  ya ke ji idan an ambaci sunan Kawunnasu azzalumi kuma maƙiyinsu da har yau sun rasa gane kan ƙiyayyarsa.

"Nan na so zuwa amma na fasa. Zan jira hukuncin Dada."

Daga nan ya shiga motar,  AlHassan ya yiwa Rasheed ido alamar ya bi bayansa. Ba musu ya zagaya gefensa ya bude ya shiga. Kallonsa kawai ya yi bai ce uffan ba, bisa umarnin AlHassan din ya bude masa ƙyauren ya fice. A hanya suka ga Hajiya Zeenatu jaye da akwati tana tafe tana waige. Ganin motarsa har hannu ta sanya da nufin tsayar da shi, ya ƙarawa motar wuta gami da jan tsaki.

***
Tun faruwar wannan lamari, tsoron Allah ya ƙara shiga zuciyar Ramlatu. Ta ƙara tsoron ƊAN ADAM tunda har nasa bai kyale ba. Wane irin zamani ne wannan? Haka ta yi ta tunani bayan ta koma sashinta. Waya suka yi da Hajiya ta labartamata dukkan abinda ya faru. Salati Hajiya ta sanya gami da ƙarawa, ba abinda ya girgizata sai na jin sunan Kawun Hussein din da ya fito a maganar. Addu'a ta yi gami da ƙara jan kunnen Ramlat akan addu'a da kuma kiyaye Azkar safe da yamma. Daga bisani ta kira wayar Amrah wadanda basu jima sosai da isa Kano ba. Nan ma dai duk hirar suka yi.

"Wannan kaɗai zai nunamaki ba karamin matsayi kike da shi a wurin Mijinki ba. Sai ki zage damtse ki kwantar da hankalinsa a wannan gaɓa, kinsan ba karamin damuwa zai shiga a kwanakinnan ba."

Wannan shi ne zancen Amrah, nan fa daga Rafee'ah ta kirata, sai Maman twins can kuma A'isha. Kowa mamakin jin abinda Hussein ya yiwa Hajiya Zeenatu ya ke yi, a gefe guda kuma ana tayata farin ciki don zama da Hajiya Zeenatu masifa ne.

Don kanta ta gaji da wayar ta ce musu chajinta ya ƙare ta kashe. Miƙewa ta yi ta shiga daki, wanka ta ƙara yi, ta fito ta zauna gaban madubi ta na kallon fuskarta da ta mulmule ta kara kyau adalilin gyaran da ta sha.

_*Ki shiryawa haɗuwarki da Uwargidana. Anan za ki gane so da kuma ƙiyayya.*_

Ta tuna kalaman Hussein, a hankali ta ci gaba da murza man a wuri guda na fatar hannunta. Kenan yana nufin ita ɗin ya ke so? Ita ce abar sonsa? A abinda ya faru, zallar ƙiyayya ta gani ya nunawa Zeenatu yayinda ita duk wani a wurin zai shaidi yana sonta. Wannan tunanin ya janyo ta sunne kai tana murmushi, murmushin da ya fito tun daga ƙasan ranta. A hankali ta ɗago kai ta dubi madubi, ba zato ta hangeshi tsaye jikin ƙofar ɗakin. Ta yi sauri ta kauda kai. Kasa motsi ta yi gaba ɗaya don ba halin ta miƙe sakamakon guntun tawul dake jikinta.   Tunaninta ma tun yaushe ya ke tsaye a kanta. A hankali kuma ta ga ya juya ya fita bai ce uffan ba. Ta dafe kirji gami da sauke ajiyar zuciya sannan a gaggauce ta mike bayan ta fesa abinda za ta fesa. Ko ba'a faɗa ba, mijinnata yana tattare da damuwar da ya ke buƙatar kulawarta. Ta gama gane irin ɗaukar da Hussein ya yi mata kamar yanda ta soma amanna da zancen soyayyar da ya ke magana bayan aure.  Riga da siket ta sanya na atamfa, ta yi ɗaurinta tsaf sannan ta fesa turare ta fita gabanta na faɗuwa. Fatanta Allah Yasa ya huce. Koda ta fito ana kiraye-kirayen sallah, har a sannan ba ta samu tsarki ba. Ba ya falon amma ya ajiye wayoyinsa da agogo, wannan ya sa ta fahimci alwala ya shiga don haka itama sai ta koma ɗaki don kunya ta ke ji ya fahimci halin da ta ke ciki. Tana ji sadda ya fice daga falon sannan ta fito. Mintuna kaɗan bayan idar da sallah sai ga Hafsat tare da Kausar. Fatima ta ruga a guje ta rungumeta yayinda Hafsat ta karasa ta ajiye kwandon abincin hannunta saman tebur. Zama suka yi aka gaisa. Nan kuma aka shiga maida zance.

"Nifa Adda Amal ba wanda ya bani mamaki sama da Kawu. Wallahi ban san rashin kaunar da yake yiwa iyayenmu da mu ya kai girman hakan ba. Ai shiyasa yau nima na rama a kan ɗansa, ya kirani har ya gaji ban ɗaga ba, karshe ma na aikamasa da zazzafan saƙo. Rasheeda fa ki ga ta kasa zama ma a gidannan ta tafi gida Adda Fati saboda kunya da kuma bakin cikin abinda Babansu ya aikata. Anti Amarya ma wai mijin ya kira ta je can yana nemanta."

"Toh ke Hafsat ai dole, amma bana goyon bayan ki wulakanta Tahir tunda ba shi ya yi maki ba. Asalima ke da bakinki kin faɗi irin zafin da ya ke ji na yanda Uban yake hana su zumunci da mu."

Kausar ke maganar kafin ta maida hankali ga Ramlat.

"Kinga shawarar da zan ba ki,wallahi ki tashi sosai ki riƙe mijinki hannu bibbiyu. Kar ki ga kin rabu da Hajiya Zeenatu ki ɗauka shikenan, ba ita kaɗai ce mayya me kwacen miji ba musamman ma a garinnan. Mijina gashinan har yau ban gama fidda ran watarana ba zai ƙaromin abokiyar zama ba don yanda ƴanmata da zaurawa ke farautarsa tamkar nama."

Suka yi dariya. Kausar ta girgiza kai ta nuna Hafsat da yatsa.

"Ba abin dariya ba ne, ke ai kin san komai. Ke za ki ba da labari, ko ƙawayenki na makaranta ba sai da na takamusu burki da zuwa gidana ba?"

Dariyar dai Hafsat ta ƙara, ita kuwa Ramlat sai ta ɗan tsunduma tunani, wato dai bayan wani yaƙin akwai wani, amma bai kai wancan ba. Motsin bude kofarsa ce ta sanya su jan baki su yi shiru don ɗazun dama sun baro shi ya shiga bangaren Dada, tare  yake da AlHassan. Zama suka yi Hussein na mai kama hannun Fatima da ta yi tsalle ta faɗa jikinsa. Da wani murmushin samun nutsuwar zuci da gangar jiki adalilin nasiha da ban bakin da Gwaggonninsa suka yi mishi. Ramlat ta gaida AlHassan ya amsa fuska a sake.

"Lafiya lau Amarsu, ya kwanan baƙunci?"

Ta yi murmushi ba ta ce komai ba. Bai wani jima ba AlHassan din, bayan fitar su Kausar don ta je ta harhada kaya su tafi gida, ya ɗan yiwa Ramlat har ma da Gogan yar nasiha akan zamantakewa sannan ya yi musu sallama ya miƙe ya yi gaba.  Shima Hussein ya miƙe ya dubeta, duban shauki da kauna.

"Ban mintuna kaɗan, zan je na dawo."

Ta gyaɗa kai.

"Allah Ya dawomin da kai lafiya."

Ya ɗan tsaya ya dubeta na sakanni, kamar ya yi tsokana kawai kuma ya murmusa cike da jin dadin addu'ar ya fice.

***
Kawu Modibbo gumi kawai ya ke sharcewa, labarin komai ya riskeshi daga bakin jama'a, hakan yasa don ya tabbatar ya umarci Anti Amarya da dawowa. A bakinta tana kuka cike da takaicinsa ta sanarmasa duk yanda aka yi ta kara da fadin.

"Mece ce ribarka idan ka cutar da ɗan  ɗan uwanka? Abu ɗaya da wannan zuri'a ta yi maka da sunan laifi, ba za ka iya tunawa ba saboda babu shi. Babu dalilinsa. Ka ji tsoron Allah tun lokaci bai ƙuremaka ba, ka tuba ka je ka nemi gafararsu."

Tana kaiwa nan ta bar shi da shi da Uwargidansa Hajiya Fatuma wacce ita kanta jikinta ya yi mugun sanyi. Ta san ba su kaunarsu saboda bakin cikin daukakar da suka samu, amma ba ta taɓa tsammanin mijinnata zai aikata wani abu makamancin wannan ba. Tambayoyi ne birjik a kwakwalwata na yanda akai ma ya san matar Hussein, har ta soma tunanin ko shi ne ya haɗa auren amma babu mai ba ta amsa, mai amsawar ba ya a hayyacinsa. Ta kara dubansa yanda ya ke faman sharce gumi sai ta kula har wani hawaye ya ke fitarwa, na nadama ne ko akasinsa, ba ta da masaniya.
   "Ku harhaɗa kayanku, gobe za mu koma Kano."

Ta bishi da kallo har ya shige ɗaki, ranta ya ɓaci, wato dai ba shi da niyyar aikata abinda Anti Amarya ta ce? Ta girgiza kai don ba ta jin zata ɗara ko nan da can ba tare da ta nemi gafarar Dada da yaranta ba na irin kiyayyar da ta musu kuma ta tara yaranta su nema su ma.

***
  Misalin karfe goma na dare ya shigo gidan, a lokacin Ramlat har ta gaji da zaman jiransa ga yunwa. Ƴan Maiduguri sun shigo sun mata sallama kasancewar da Asuba za su tafi. Ta sha nasiha sosai sannan suka bar sashinta.

Ta ƙarasa ta nufeshi da zummar karɓar ledojin hannunsa, hannunsu ya haɗu wuri guda, ta ji wani yarr, da sauri ta janye ta yi gaba zuwa cikin falon ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login