Showing 147001 words to 150000 words out of 230725 words
ya kai!" Cewar Sauda bayan sun gama sauraron labarin Chairman daga bakin Ramlat.
"Mtsw, iyayenmu ne abin duniya yanzu sai ya rufemusu ido wallahi, daga ƙin gaskiya sai ɓata fa. Yanzu idan aka bari kika aureshi mene makomarki? Nikam gaskiya ke na fi jin haushi ma wallahi Ramlat, kiyi hakuri kinsan ban iya ɓoye abinda ke raina ba. Amma kefa bazawara ce, ta ya ya kuma ta ina za ki zauna a tauye hakkinki? Kamar ba ke ce kika jajirce a baya har kika auri wanda ranki ke so ba?"
Naja ta fadi ranta na ƙuna, Ramlat dai dubansu take kowa da irin kalar ƙorafinsa. Zagi kam Chairman ya sha. Tsam! Ta miƙe ta fita dama hijab ne a jikinta, tana ji suna kiranta da tambayar ko haushinsu ta ji amma ba ta ko iya waigowa ba. Kai tsaye ɗakin Malam Yahaya tsoho mai ran ƙarfe, cikin maza shi ɗaya tilo ya yi saura a ɓangare iyayen su Abba, wato Malam Abdullahi, Mu'azzam da ma sauransu. da suka rasu.
Yana zaune yana shan fura ga rediyonsa a kusa, sallamarta ya dauki hankalinsa, ya amsa ta karasa ta zauna.
"Wace ce ne? Ko Uwani ce?"
Ya tambaya yana kakkanne idanu don ba kasafai ya ke gane mutane ba. Bakin har rawa yake ta amsa
"Malam ni ce, Ramlatu."
Ya yi ƴar dariya.
"Ki ce Amaryar Dikko ce. Ince dai lafiya?"
Kiranta Amaryar Dikko ya ɓata ranta ainun, ta haɗiyi miyau mai ɗaci. Idanunta sula cicciko da kwalla.
"Malam don Allah ka taimakamin, kai kadai za ka yiwa su Kawu Bello magana su ji. Wallahi bana son Dikko, don Allah ku ban lokaci na muku alƙawarin kawomaku wanda zan aura nan kusa da yardar Allah."
"Wane magana kike yi haka Ramlatu? Abinda ki ka aikata a baya ne kike kokarin maimaita shi a yanzun? Ki fita idona wallahi! Ni ba ubanki ba ne da kika raina."
Zuciyarta ta yi wani irin nauyi, ta kasa daurewa sai da hawayen suka zubo. Wannan baƙin fentin da ta gogawa kanta ba ta san sadda zai gogu har yan uwa su yi mata kallon mutum mai ƙima ba. Ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta zayyanemishi duk wasu munanan ɗabi'un Chairman da ta sani. Ya yi shiru yana saurare har ta kai aya. Shiru ya biyo baya kafin ya jinjina kai.
"Shikenan, zan wakilta Iro (babban ɗansa) ya bincikamin a can Kanon. Idan har babu ɓurɓushin gaskiya game da abinda kika faɗa lallai ki sani, ni da kaina zan ɗaura aurenki da mutuminnan."
Ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin dama-dama. Kusan tun zuwanta banda Gwaggo Hansai da ta fahimceta da ɗaiɗaiku cikin gwaggonnin nata, sai yanzu ta samu nutsuwar da ba ta ji ba. Ga zafin Hussein ba ta ƙara magana da Hussein ba yau kwana huɗu kenan da zuwanta garin.
A sanyaye ta mike ta fita, kiciɓus suka yi da Harira ɗiyar Amaryar Kawu Bello ta biyu, dagaske laɓe ta yi a zauren. Sai dai ta wayance.
"Af, ke ce a ciki? Dama abincin Malam ne Gwaggo ta ce na miƙa."
Ta gyadamata kai kawai ta yi gaba. Ta rantse dai ba ta auren Chairman. Don haka za ta bi ta salama ta san yanda akai ta rabu da shi. A baya ta yi tunanin za ta iya hakurin zama da shi ko ba so, sai dai yanzun da so da kaunar Hussein ke ƙara ruruwa a zuciyarta, ba ta jin ko kusa za ta iya. Allah-Allah ta ke yi su koma Kano don tuni ta samu cikakken sunan Kawun su Hussein dake Kano a wurin Hafsat. Dabara ta yi mata da cewar ta shiga Yakasan ta ga wata mai kama da ita. A haka har ta gangaro inda Hafsat ta yi mata bayanin cikakken sunan Kawunnasu. Babban burinta ta koma Kano ta je ta sameshi. Ta fi kaunar bin komai daki-daki.
Maimakon ta koma ɗakin, sai ta wuce sashin surukar Malam, matar Iro, Hajara, anan ta yi zamanta tana danna waya. Muhibbat ta kira suka gaisa sannan ta haɗata da su Ansar da Ummi aka gaisa. Ba karamin kewar yarannata ta yi ba, ta yi musu albishir na dawowarsu a gobe.
Saƙo ta ga ya shigo, saƙon daga AlHassan, ta mike zaune da azama ta shiga whatsapp.
*"Ƙanwata, kinsan wata Hajiya Zeenatu Bashir a Kano? Ta taɓa zaman Saudiyya, kuma tana taɓa siyasa a baya. Yanzu dai ban da masaniyar komai a kanta."*
Dafe kirji ta yi. Shikenan duk yanda aka yi NESA CE TA MATSO KUSA!
I just published "BABI NA ARBA'IN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/LUjPZHlQycb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
44)
_*"Eh na san ta."*_
Har ta rubuta hakan, sai ta goge da sauri. Toh idan ta ce ta san ta kai tsaye me ta yi kenan? Girgiza kai ta yi.
Shiru ta yi na ƴan sakanni ba zato wayarta ta shiga ringing. Ta duba, AlHassan ne. Ta danna gami da karawa a kunne. Dakyar ya samu nutsuwar amsa sallamarta.
"Kin buɗe saƙona ba ki ce komai ba. Kin san ta?"
Ramlat ta sauke numfashi.
"Ka yu hakuri sai dai magana ce mai tsawo da ba za ta yiwu ta waya ba, yaushe za ka samu shigowa Kano?"
"Ko gobe ne zan iya tahowa Ramlat. Ki amsamin da kin san ta ko aa."
Ganin irin ruɗanin da muryarsa ta nuna, yasa ta saurin amsa mishi.
"Na san ta. Har abinda ba ka zato duk na sani, idan da dama gobe.."
"Kar ki damu, gobe in sha Allah zan zo Kano."
Ya katse hanzarinta da gaggawa. Ta amsa da toh, godiya ya yi mata ya katse kiran.
Abu na farko da ya daurewa Ramlat kai, ta yaya Hussein ya gane zai iya samun wani bayani ta hanyarta? Sannan a ina ya san sunan Hajiya Zeenatu? Wannan tambayar babu mai amsamata sai shi da kansa don haka ya haɗiye abinta. Ta shiga zullumi ba kaɗan ba, ganin ta kasa danne abin, kawai sai ta kira Hisham.
"Ran Amarya ya daɗe."
Ta ja guntun tsaki, Hisham tun sadda ya ji labarin Chairman ya ke zolayarta.
"Ba wannan ba please, magana ce da ta shafi Hussein."
Jin haka sai ya maida hankali. Ta ba shi labarin yanda suka yi da AlHassan har da ƙudurinta na zuwa ganin Kawun Hussein dake zaune a Kano
"Da mamaki ace mutumin dake zaune cikin ƙwaryar Kano ya kasa sanin akwai wani jininsa a Kanon. Sai dai ban san irin raunin alaƙar dake tsakaninsu ba. Ina goyon bayan ki gwada zuwa ki sameshi. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ta ya ya Hussein zai soma fuskantar lamarin? Anya ba kuskure ba ne kai tsaye AlHassan ya tunkareshi ba?"
Ramlat ta jinjina kai.
"Shiyasa nake son zuwa na faɗawa Kawunnasu. Idan ma ya sani ka ga za mu sani, amma ba na jin zai sani. Haba, ɗan uwansu fa."
"Hum, shikenan Ramlat. Allah Ya maidoku lafiya. Ya ɗora mu a kansu."
Ta amsa da amin kafin ya ba Aisha wayar suka gaisa da taɓa hirar Daura daga bisani suka yi sallama.
***
WASHEGARI...
*LAMIƊO CRESCENT*
"Na yarda, wace ƙasar ki ka zaɓa mana?"
Mamakin amsar Hussein ya daskarar da Hajiya Zeenatu lokaci guda, ta ƙara matse layar hannunta domin ta yi imanin shi ne dalilin da yasa ya yi amanna da zancenta.
'Allah Ya yi maki albarka Hajiya Batool aminiyar kwarai.'
Ta fadi a ƙasan ranta bayan ta tuno shawararta ta bi ta je wurin Bokansu ta karɓo layar.
Farr ta yi da ido baki yaƙi rufuwa tana duban Hussein da rabin hankalinsa ke kan Laptop ɗinsa yana shigar da wasu takardu don son kauda damuwar da ke sukarsa a ƙirji.
"London nake son mu je, ka ga daga nan sai a binciki lafiyata sosai akan matsalar haihuwa. Kana iya ɗaukar annual leave."
Ta fadi cikin dabara tana mai kissimawa a ranta shikenan Hussein ya yi bankwana da Nijeriya har abada.
Ba tare da ya kalleta ba ya amsa a gaggauce.
"Ki yi duk yanda ki ka so."
Yana kaiwa nan ya miƙe ya nufi sama. Ba ta dakatar da shi ba don ita fa ya gama biyanta. Da wani irin farin ciki ta kira Hajiya Batool ta fesamata. Dariya suka yi lokaci guda.
"Habawa! Wa ya faɗamasa Borno gabas ta ke? Ai wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa."
Cikin nishaɗi Hajiya Zeenatu ta gyara zama.
"Allah Ya barmin aminiyar kwarai. Yanzu ki yiwa ɗanmu magana ina so ya yimin duk wani shiri na tafiya."
Suka yi dariya sannan suka ci gaba da ƙulla-ƙullarsu.
***
Kasa zama ya yi sai kwanciya, kwanciyar ma bai fi minti uku ba ya miƙe zaune gami da dafe kai. A hayyacinsa ya amincewa Hajiya Zeenatu, gani yake nisan da zai yi daga gareta shi zai sa ya mance da dukkan lamuranta. Hisham ba zai yi ƙarya ba don ya baƙanta ransa hakanan kawai, a farko yana mata kallon wata halitta ɗaya tallin tal da ta dakatar da shi daga biyewa Hajiya Zeenatu tun farko akan su bar garin, yau kam har Ƙasar ya amince su bari idan hakan zai ba shi farin ciki. Zai nisantashi da ita kuma ya yaye damuwarsa. To wa ya ke da shi da zai damu? Ba shi da uwa bare uba, ba danginsa babu na Hajiya Zeenatu. Wannan abu sau da dama kan ɗauremasa kai matuƙa kuma ya jefashi cikin tafkin tunani iri-iri. Nan da nan farar fuskarsa ta yi ja kamar yanda idanun suka kaɗa. Ya riƙe kansa da ke sarawa da ƙarfi yana salati. Tun yana gani daidai har ya dawo gani dishi-dishi. Ya yi kokarin mikewa tsaye sai ji kake tim! Ya fadi.
Ta turo ƙofar ta shigo ranta fari sol bayan kammala wayarta da Hajiya Batool. Turus ta yi ganin Hussein a ƙasa. Wani ƙara ta saki kafin da sauri ta nufeshi.
"Hussein! Hussein?!"
Babu alamar zai motsa, don haka ta dauko ruwa ta yayyafa, nan ma shiru. Ganin haka ta yi wurgi da robar ruwan ya malale a kafet ta fita daga dakin.
"John! John! Ola!"
Kusan lokaci guda ma'aikatan dake kicin har wajen su uku suka fito.
"Yes Ma!"
Umarni ta ba su akan su hayo su taimakamata. Da gudu suka nufi saman, suka cicciɓi Hussein. Mayafi kawai ta dauka sai mukullin mota da ta damkawa John ta bi bayansu tana kuka. Kai tsaye suka wuce asibiti.
***
Sun sauka lafiya a Kano. Bayan kimtsawa suka hadu suka ci abincin rana. Fuskar Ramlat cike da fara'a don tun safe bayan dawowarsu Muhibbat ta kawo su Ummi. Affan ya maƙale mata duk inda ta sa ƙafa yana biye. Labarin gidan su Aliyu da na Muhibbat kuwa ta sha har ta gode Allah. Ta lura dai ba su fuskanci kowace matsala daga dangin Aliyu ba don a yanda bakin Ummi ba ya shiru sai ta fesamata.
Da yammacin ranar gidan ya rage daga ita sai Hajiya da su Ansar don tuni masu auren duk sun tafi gidajensu. Ta shirya tsaf da niyyar zuwa ganin Kawu Modibbo kafin zuwan AlHassan wanda tun safe ya shaidamata cewar yana hanya. Ba ta ɓoyewa Hajiya komai ba na halin da ake ciki. Hajiya ta jinjina lamarin.
"Ramlatu Allah Yasa a dace. Allah Yasa karshen wahalar yaron nan ce ta zo."
Cike da tausayawa Ramlat ta amsa da amin. Suka yi sallama ta fita, ba ta ɗauki mota ba don haka kawai ta fice. Har za ta wuce ta ga kyautuwar leƙawa gidansu Amrah su gaisa da Baba Dakta. Wannan yasa ta karya kwana ta shiga gidan da sallama.
Umma ta amsa fuska a sake.
"Mutanen Daura, saukar yaushe?"
Dariya ta yi tana mai kama hannun Zaituna da ta maƙalƙaleta tana oyoyo.
"Tun safe muka iso, Hajiya ma ta kira ba kya kusa."
Umman Amrah ta bude baki.
"Af, an yi haka. Na ga kiranta toh da alama dai wannan ɗiyartaki ce garin son a kunna mata kallo ta kashemin ƙarar."
Murmushi sosai Ramlat ta yi gami da shafa kan Zaituna tana mitar yanda amosali ke cinyemata gashin. Can kuma ta ɗago.
"Baba Dakta ya na nan kuwa?"
"Ba ki taki sa'a ba Ramlatu, yana asibiti."
Ta mike tsaye.
"Toh Umma zan dawo anjima in sha Allah. Zan ɗan fita ne."
Umma ta amsa da toh, suka yi sallama ta fice.
***
Gidan ta tsaya tana ƙarewa kallo. Gida ne da ta sha zuwa ta wuceshi, ba ta mancewa akwai sadda suka taɓa shiga tun suna yara ita da su Amrah tsinko mangwaro aka koro su. Murmushi ta ɗan yi tunawa da cewar gidan ƴan uwan mutum mafi soyuwa a zuciyarta ne ashe. Ta ƙarasa ta yi sallama ga mazauna ƙofar gidan sannan ta sa kai ciki. Ɓangare biyu ta gani sai kawai ta faɗa na biyun. Wata baiwar Allah dattijuwa ta soma cin karo da ita zaune a tsakar gida, a gefenta wata budurwa tana gyaran alayyahu, wanda nan take ta gane fuskarta dalilin hotunanta da ta ke gani a status din Hafsat, sunan ne dai ba ta jin za ta iya tunawa.
Suka amsa sallamarta suna dubanta, duba na rashin sani.
"Sannu da zuwa, bismillah. Rasheeda kai ta falo ina zuwa. " Faɗin Amarya fuska a ɗan sake, sosai Ramlat ta ji dadin tarbar da ta samu. Ta bi bayan budurwar da aka kira Rasheeda zuwa falo. Falo ne mai girma ya sha ado. Ta zauna a saman ɗaya daga cikin hadaddun kujerun da aka zuba. Rasheeda ta gaidata ta amsa fuska a sake sannan ta je ta kawomata ruwa da lemun zoɓo.
"Na gode." Cewar Ramlat sadda ta dauki ledar ruwan ta sha kaɗan ta ajiye ragowa. Amarya ta shigo ta zauna. A ladabce Ramlat ta gaidata ta amsa fuska a sake.
"Sai dai kamar ban shaida fuskar ba."
Murmushi Ramlat ta yi.
"Eh gaskiya ba ki san ni ba Anti. Sunana Ramlat Khalid Mu'azzam. Kusan sanadin AlHassan Aminu Mamman dake Adamawa na san gidannan. Kwanakin baya ma sun zo biki nan suka biya ta gidanmu."
Kawai sai ta ga Rasheeda ta sa dariya haka Amarya.
"Ke ce Mamin Fatima ko? Mai zaɓamata takalmi? Ya bamu labari."
Da wani irin salama na jin dadin kalaman Rasheeda itama ta yi dariyar kadan.
"Ni ce, ai kema ina ganinki na shaidaki don ina yawan ganin hotonki a status din Hafsat."
Jin haka Amarya sai ta samu nutsuwa sosai da Ramlat, dama tun farko ba ta yi mata kalar mace marar kamun kai ba. Nan aka kara gaisawa da tambayar su Hajiya wanda ba karamin mamaki ya ba Ramlat ba. A karshe Ramlat ta gangaro kan abinda ya kawo ta.
"Ina neman izni ne, ina son ganin Kawu Modibbo."
Jin haka Anti Amarya ta amsa cikin kwarin gwuiwa.
"Wannan ba matsala ba ce Ramlat. Bari na yi miki iso, ina zuwa."
Hakan ya faranta ran Ramlat, ta dauka ganinnasa zai mata wuya ko kuma wani ko wata zai nemi sanin dalilinta na son ganinsa, sai dai akasin hakan ce ta faru. Ko ba komai ta gaskata kirki na Amarya, wanda ya sha bamban da na Hajja Fatuma kamar yanda ta ɗan ji kaɗan cikin labarin matannasa a bakin Hafsat. Yarinyar akwai hira idan ta so.
Jim kaɗan sai ga Amarya ta dawo, yanayin sanyin jikinta sai ya sa Ramlat shan jinin jikinta itama. Amarya ta daure tana murmushi mai kama da yaƙe.
"Za ki iya jira har bayan Magriba kuwa? Ina gudun kar ki dare."
Nan ta gano matsalar, don haka ta saki fuska.
"Lah ba komai Anti, Allah Ya kaimu."
Amarya ta yi murna da hakan, ta kunnamata kallo ta ba ta remote koda za ta sauya tasha daga nan ita kuma ta koma bakin aiki kasancewar girkinta ne. Ba jimawa da kunna kallon aka dauke wuta, nan take jin Amarya na ba Rasheeda labarin wai Hajja Fatuma ce ta ce tunda ba lokacinta ba ne sai ta yi hakuri da duk wani baƙonta da ke son ganin Modibbo, idan na ta lokacin ya shigo ta yi duk irin damun da ta so yiwa furarta.
Murmushi Ramlat ta yi na yaƙe, ta dai lura akwai takun saƙa tsakanin matan gida. Waya ta fiddo ta kira Hajiya ta fadamata.
"Anya kya zaunar musu har Magriba? Ba kya dawo ba ki hakura zuwa gobe?"
Girgiza kai Ramlat ta yi.
"Hajiya lokaci zai ƙuremin idan ya kai gobe, mu dai yi hakuri tunda kinga biyar da rabi ma ta wuce, kamar yanzu ne za'a kira sallar in sha Allah."
"Ai shikenan, Allah Ya kaimu anjima. Sai kin dawo."
Ta amsa da amin suka yi sallama. Ba ta kai ga ajiye wayar ba, kiran AlHassan ya shigo. Suka gaisa.
"Dole ta tsayar da ni a Gombe sakamakon lalacewar abin hawa. Na so kwarai na shigo yau, amma gobe da sassafe in sha Allahu zan taso."
Hakan ya dan yiwa Ramlat dadi, ko ba komai lamuran zasu tafi yanda ta so.
"Ayya ba komai, Allah Yasa hakan ya zama alheri."
"Amin, sai dai kin ƙi sanar da ni komai game da abinda na nema."
Sauke ajiyar zuciya ta yi.
"Ka yi hakuri, idan ka shigo har wanda zai ba ka mamaki duk zan faɗamaka kuma zan kaika ka ganewa idonka in sha Allahu."
Ya dan yi shiru, shirun da yasa Hussein faɗomata a rai, shi ya saba yi mata hakan. Kewar Hussein sosai ta ke ji ta kuma kudurce ko bai mata magana ba ita kam yau za ta taɓoshi ta whatsapp.
"Shikenan. Allah Ya jisshemu alheri."
Ta amsa da amin cike da tausayinsa. Dan uwan da Allah kadai yasan tun sadda ya ke bulayin neman ɗan uwansa. Ta ji idanunta sun cika da kwalla daidai sadda suka yi sallama. Ta shiga whatsapp ta aikawa Hussein saƙo, ta jima tana kallon profile dinsa wanda bai dora komai ba a idanunta tana wassafo hotonsa, karshe ta sauka.
Ba jimawa aka shiga kiraye-kirayen sallah, Rasheedat ta jagorance ta zuwa ɗakinta. Alwala ta ɗaura ta tayar da sallah saman dardumar da ta iske an shimfidamata.
Ta jima tana addu'ar nasara akan lamarin Hussein, shi kansa ta yi mishi addu'a kwarai kafin ta shafa ta miƙe.
Abinci aka zubomata, dolenta ta ci tana kallon tsarin yaran Amarya gwanin sha'awa. An idar da sallah ana kuma neman haddar karatun da aka biya na Islamiyya. Can kuma sai ga Amaryar ta fito sharr kamar sabuwa, ta shirya cikin riga da siket na leshi ta cakare abinta tsaf. Da fara'arta ta dubi Ramlat.
"Yi hakuri fa Ramlatu, bari idan na shiga zan miki magana sai ki zo."
"Toh Anti. Kin yi kyau tubarakAllah."
Hakan da ta fada ya ba su dariya har yaran. Amarya ta yi godiya ta wuce ɓangaren Mijinta. Sosai abin ya ƙayatar da Ramlat.
***