Showing 27001 words to 30000 words out of 230725 words
bugawa ya sa Amrah ƙara gasƙata zurfin soyayyarta ga wannan mutumin.
"Allah Ya kyauta, Ya hanemu mugun ji da gani." Abinda ta iya furtawa kenan kuma magana ta karshe tsakaninsu kafin su mike su shiga aji karfe uku don gabatar da lesson duk a cikin shirin zaman jarrabawa.
***
Juyi yake yana kara tunanin zantukan da ya yi da Ramlat game da shirin aurenta da aka fara, gaba daya kansa ya kulle don ji yake muddin ya rasata ba shi da sauran nutsuwa balle kwanciyar hankali, ya kai duba ga inda Muhibbat ke kwance tana bacci sannan ya mike ya dauki wayarsa ya fice daga dakin. https://my.w.tt/At99ZcOeF9
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
10)
Tarr ta bude idanunta jin motsin bude kofar. A hankali ta kai hannu saman dirowa ta dauko wayarta gami da duba lokaci, karfe uku saura mintuna, mayarwa ta yi ta ajiye kirjinta na wani irin zugi tana cin ɗaci a maƙogwaro. Miƙewa ta yi ta nufi hanyar falon, kunnuwanta ba zasu iya juriyar sauraron hirarsu ba don haka ta dawo dakin. Banɗaki ta shiga ta kama ruwa gami da ɗauro alwala, nafila ta yi raka'a biyu, ta jima cikin sujjada tana zubar hawaye gami da kai wa Allah kukanta kafin ta ɗago ta sallame. Nan ma Alkur'ani ta jawo ta karanta a karshe ta yi addu'a ta shafa.
Shi kuwa Aliyu tun da ya kira ya soma zazzaga ruwan kalamai ga Ramlat mai nuni da kewa da kuma damuwar halin da za su shiga idan wani abin ya afku.
"Na kasa bacci, na kasa samun nutsuwar yi, kin kuma san ke ce. Ina tsoron na rasaki Baby."
Ya ji motsin rufe kofa, ya waiwaya sannan ya kara kishingida ya ci gaba da wayarsa hankali kwance.
Daga ɓangaren Ramlat ta kara cusa kai cikin bargo yanda A'isha ba za ta motsa ba.
"Na fi ka shiga wannan zulumin, Sweet Aliy babu ta yanda zan rasaka in sha Allahu. Ka kwantar da hankalinka."
Murmushi ya yi mai sauti. Nan kuma suka shantake suka shiga hira har da kyakyacewa.
Muhibbat zaune saman darduma ta zurfafa cikin tunani, ta ji labarin kaddarorin aure da dama, sai dai irin nata ya bambanta da kowanne. Ta yi sanadin sauyawar lamura da dama. Ta rugurguza farin ciki da dukkan tanadin da ta yi a zamantakewar aurenta.
Shigowarsa dakin ya katse tunaninta, ya kai duba ga inda take, sai kuma ya dauke kai ya koma saman gadon ya kwanta gami da juyamata baya. Ta tsayar da idanunta ga kallon bayannasa, a duniya ba namijin da take so irin mijinnata, dama so na rikiɗewa har haka? Da me wannan baiwar Allahn ta fi ta? Meyasa yake ƙuntatamata saboda ita? Meyasa ta kasa samun zaman lafiya a rayuwar aurenta duk a dalilinta? Ta dauka duk mace mace ce!
Wasu hawaye masu ɗumi suka zubomata ganin halin ko in kular da yake nunamata aduk sadda irin hakan ta faru. Bacci har da sakin munshari ta tsinceshi yana yi. Ta kai hannu ta shafi cikinta ɗan watanni biyu kacal, a hankali ta lumshe ido tana addu'ar neman sassauci da kalar rayuwar mijinta.
***
Hajiya ta yi mata ƙuri da ido.
"Kwanakin nan kin fiye yawo, kin je gidan Amrah ya fi a kirga, yau kuma Muniru ki ka tuna? Yaushe sabo mai karfi ya shigeku har haka?"
Ta turo baki kadan.
"Dan uwana ne fa Hajiya."
Abba dake karanta jarida ya ɗago kai yana dariya.
"To kinji amsarki ai. Kwana nawa ne za ta tattara ta bar miki gidan ke da autarki? Ki bar ta ta sada zumunci, ta samu lada biyu. Na juma'a da kuma zumuncin."
Ramlat ta sauke ajiyar zuciya, dama tana sane ta tambaya a gaban Abban don tasan zai goyi bayanta. Tun safe Hajiyar ke cin magani tana mitar wai ta sauya daga Ramlatun da ta sani akan ta shigo tana waya ta yi shiru har ta fita daga dakin. Wannan ne kuma ya tabbatar da zargin Hajiyar cewa akwai saurayin da ke huremata kunne a yanzu. Koda Hilal bai ce komai ba, ita ta lura ɗiyar ta bar rawar kafa a kansa da komai ma.
"Ban wayarki. Idan kin dawo kya karɓa."
Maganar Hajiyar ya daskarar da ruwan jikinta, ta bude baki za ta yi magana sai dai tuni miyan bakinta ya daskare jin muryar Abba na magana cikin nuni da goyon baya.
"Ba ta idan har za ki tafin. Tunda gidan Yayanki ne ai ba damuwa. Zuwan dai ake kokarin hanaki."
Ba haka ta so ba don dama da biyu take son fitar, Aliyu na son ganinta ko ta wane hali don su tattauna su samarwa kansu mafita sai dai kuma da alama karyarsu ta kare muddin wayarta ta shiga hannun Hajiya. Ba ta da zaɓin da ya wuce ta fiddo wayar daga jaka ta miƙa wa Hajiyar.
_Idan lokacin bayyana soyayyarmu bai yi ba har yanzu, sai yaushe? Sai yaushe ne za'a san abinda muke ta ɓoyansa? A soyayya ba'a shakka balle tsoro. Idan aka yi hakan ba'a yi mata adalci ba, ba'a fitar da hakkinta ba._
Wadannan kalaman Aliyu ne, nan take ta ji wani kwarin gwuiwa. Ƙarƙari Hajiya ta bincika wayarta ta kuma bibiya shiga da ficen kiranta. To me ta aikata? Ai ba haramtacciyar soyayya ba ce.
'Nema cikin nema?'
Ta ture tunanin ta hanyar yi musu sallama ta fita, Abba ya bita da kyakkyawar addu'a yayinda hankalin Hajiya ya koma ga wayar ta yi mishi ƙuri kamar mai jiran amsa daga cikinta.
"Menene wai Rabi'atul Adawiyya? Meke damarmin ke da zuciyarki? Kwanakin nan ina lura da tsaurin da kike ƙara yi game da yarinyar nan. Ta yi wani abu ne?"
Hajiya ta yi shiru tana dan kallonsa, ta fi kowa sanin halin mijinta, yana da sauki amma idan ranshi ya ɓaci babu kyau. Bai fiye zargi ba kamar yanda bai fiye daukar magana ba idan har ba shi ya ganewa idanunsa ba ko kuma yana da hujja. Tasan idan ta furta wani abin bisa zargin zai iya yiwuwa nata ne zai yi wari don haka ta ɗan murmusa.
"Ba komai Abban yara, tunaninka ne kawai ya ba ka hakan. Ramar da take yi ne kawai bana so, a kanta aka fara aure?"
Ya riko hannun Hajiya yana murmushi.
"Kar ki damu, ko kin manta ban da auren shirin zana jarrabawa ta ke? Na dan lokaci ne In Sha Allah. Ko kin manta kalar naki zullumin dab da aurenmu?"
Da sigar wasa ta harareshi suka yi dariya gami da yiwa Ramlat din kyakkyawar addu'a.
***
Cike da fara'a Anti Bilkisu ta tarbeta.
"Lale marhabin da Amaryarmu. Yau an tuna da ni?"
Ramlat ta kama hannun Maama babbar ƴar Yaya Munir suka zauna saman kujera. Tana dariya
"Kai Anti, ko wata fa ban yi ba rabona da gidannan."
Taɓe baki Anti Bilkisu ta yi tana dan murmushi.
"Ai shikenan, nasan da mutuniyata ce har da kayan kwananta zan ganta. Kin dai wanke kanki tunda kin zo. Yau na huta da shiga kicin."
Dariya ta yi kawai sanin halinta, wato dai tana nufin A'isha don sun fi ɗasawa, dama murnar da take na zuwannata kusan da biyu ne. Wata irin mace ce mai son jiki da ba ta son aiki, burinta kawai a yi mata, wasu lokutan akwai ta da shan ƙamshi da kuma sakarwa mutum hidima duk sadda ya kai mata ziyara, wannan ta sa ba ta fiye zuwan ba. Da ace ta san ma dalilin zuwannata da sai ta ji kamar ta shaƙeta.
"Mutuminki kuwa jiya kusan wuni ya yi a gidannan, kinsan fa ni ya damƙawa haɗa lefe don haka ki min biyayya idan kina son ganin tsala-tsalan kaya."
Tsaki ta yi wanda ba ta san ma ya fito fili ba, da mamaki Bilkisu ta dubeta.
"Tsaki ki ka yi?"
Sai ta ɗan basar.
"Wayata na tuna na bari a gida, kuma ina son yin waya. Don Allah ban aron ta ki."
"Au, toh ki gama wayar a karshe ki ce ya turon kati don nasan ƙararwa za ku yi."
Ta ƙarashe tana mai sanya kai ta fice daga falon zuwa ɗaki. Da sauri Ramlat ta mike ta nufi kicin, lambobin da suka riga suka zama tamkar lazimi a wurinta shi ta shiga rubutawa kafin ta danna kira. Sai safa da marwa take yi a kicin din har kiran ya shiga.
"Assalamu alaikum."
Ta tsinci muryar mace, muryar da ba ta yi kama da ta Muhibbat ba don akwai sadda ta taɓa kiran Aliyun, ta daga ta ce ba ya kusa. Ranar ta tabbatar sun kusa yin kaca-kaca da Aliyu don har rantsuwa ya yi mata a kan idan tana so ma zai sauwakewa Muhibbat duk a dalilin kishin da ta motsamata.
"Hello."
Aka kara fada daga can bangaren sai dai ta kasa magana. Tana shirin katse kiran cike da faduwar gaba ta tsinci muryar macen.
"Kanwarsa ce Habiba, Yaya Aliyun yana ciki wurin likita su na magana."
Da wani irin matsanancin tsoro ta watsamata tambaya kamar a tsawance.
"Meya sameshi?! Wane asibitin ne?"
Habiba sai da ta ɗan yi shiru kafin ta yi magana cikin rashin wayo.
"Anti Muhibbat ce ta yi ɓari, ya bar wayar a dakin ne, idan ya dawo zan fadamasa kin kira."
Da sauri ta katse kiran ta kuma goge lambar daga wayar. Tasan ba ta son Muhibbat, ba kuma tsana ba, a'a, kishinta take. Sai dai fitar cikin ya zo mata a bazata, ba ta san sadda ta shiga fitar da hawaye ba, ta ajiye wayar a gefe ta hau fiddo kayan girki jikinta a sanyaye. Ba ta taɓa jin tausayin Muhibbat din ba sai a wannan rana.
Tana cikin gyara kayan miya ta tuna ba ta ma tambayi Antin abinda za'a dora ba, tana niyyar fita ne kuma ta ji wayar ta dauki ƙara, jiki a sanyaye ta karasa ta daga, lambar Aliyun ne.
"Ki yi hakuri, waccan ƴar rawar kan ce ta ɗaga. Ta fadamaki muna asibiti ko? Kar ki damu fa zan zo din. A ina za mu hadu?"
Ita kuwa wane irin rashin adalci ne wannan da zai sa ta nemi ganinsa a yau duk da tashin hankalin da matarsa ke ciki yanzu? Ko ba komai a yau Muhibbat ta cancanci duk wata alfarma. Don haka ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta shiga girgiza kai kamar yana gabanta.
"Ka yi hakuri, nima ce maka zan yi Hajiya ta karɓi wayata har sai na koma gida sannan za ta maidomin. Yanzu haka ina gidan Yaya Munir, wannan wayar Anti Bilkisu ce."
"Kenan ba zamu hadu ba?"
"Ka yi hakuri don Allah Sweet Aliy, a yau Muhibbat na bukatar kulawarka. Ka ce ina mata sannu. Zuwa gobe zan san yanda za'a yi mu hadu ko bayan tashi daga makaranta ne."
"Yau ita ta samu wannan alfarmar a wurin sarauniyar masu kishi?"
Ya fadi cike da zolaya yana ƴar dariya. Murmushi kawai ta yi mai sauti.
"Ai ina tunanin gida zasu wuce da ita har sai ta samu lafiya. Naga yayyunnata sai wani kallo suke watsamin kamar ni na janyo zubewar cikin. Mtsw, ita kanta In-law ba don darajar Granny ba sai na fadamata maganar da za ta hanata bacci."
Ta gane In Law din da yake nufi, wato Mama mahaifiyar Muhibbat, a duniya ya sha fadamata ya tsani matar saboda ko kallo bai isheta ba har gobe. Idan ma ya gaidata amsawar kamar mai taunar maɗaci haka ake yinta.
"Allah Ya bata lafiya."
Ta furta cike da tausayi.
"Ke na yi wani karambanin. Wayarki na soma kira kafin wannan. Har kuma saƙo na aika da ban ji kin ɗauka ba."
Ta fiddo ido waje game da riƙe kirji.
"Dagaske?"
"Yes, amma ya naji kamar kin razana? Mene a ciki? Mene don Hajiya ta san da zamana? Ko kina tunanin lokaci bai ba da zamu bayyana abinda ke zukatanmu? Saboda Allah na gaji da wannan ɓoyon!"
Ta ɗan sauke ajiyar zuciya.
"Me ka rubuta a sauƙon toh?"
"Idan kin koma gidan kya gani. Sai anjima."
Ya katse kiran, nan da nan hankalinta ya tashi har garin saurin ta kirashi, kiran Yaya Munir ya shigo ta katse. Sai da ya kusan katsewa sannan ya daga.
"Me za ki cemin kuma?"
Ta marairaice.
"Ka yi hakuri. Wallahi nima yanzu bana tsoron kwan ya fashe kowa ya ji. Kawai dai na tambaya don na sani, amma ka yi hakuri."
Sai da ta kwashi mintuna uku tana bada hakuri, karshe ya hakura ya shiga karfafamata gwuiwa akan kar ta kusa ta ji shakkar komai akan abinda yake ƴancinta. Ya na kara nunamata muddin ta bari ta auri mijin da ba ta so za ta tafka kuskure. Ita kuwa ƙara hawa take gami da hango gaskiyar hakan. Tana ji kira na faman shigowa ta ƙi maida hankali a kai, sai da aka soma warning na karewar kati sannan ta tuna ita ta kira suka yi sallama bayan ya dorata kan hanyar da za ta bi ta fidda abinda ke ranta idan Hajiya ta mata zancensa. Ba tare da ɓata lokaci ba ta goge dukkan shiga da fitar da lambarsa ta yi a wayar. Hamdala ta yi kafin ta fita ta kaiwa Antin wayar.
"Me zan dafa?" Ta katse Anti Bilkisun dake kokarin daga wayar mijinta, cikin maida hankali ga wayar a gaggauce ta amsamata.
"Duk abinda kike so ki dafa kawai. Hello."
Ta ƙarashe da daga wayar Munir. Cikin sauri Ramlat ta yi gaba tana ji Anti Bilkin na ba shi hakuri da cewa ba ita ke amfani da wayar ba, can kuma ta ji tsakinta da masifa. Taɓe baki Ramlat ta yi don ta san kaɗan daga aikinta kenan. Ko a jikinta don tana da tabbacin zai wahala Yaya Munir ya isketa cikin gidan.
Ai kuwa ta ci sa'a don tana kammala girka shinkafa da miya, suka ci. Ba ta ko biyewa mitar Anti Bilkin ba na ta karar mata da kudin kira kuma ta hadata faɗa da miji, ta tattara ana la'asar ta yi gaggawar barin gidan cike da kwarin gwuiwa ta doshi gidansu don kuwa tana ji daga zuciya da gangar jikinta, yanzun tana da abin faɗa, tana kuma da abin kare kanta. Ta gaji da ɓuyar.
***
"Gida zan tafi da ita, ba zan bari ta koma gidansa a wannan halin ba. Ba kuma zan bari kakarku ta ci gaba da juyamin yarana ba son ranta. Dole wannan karon a yiwa abin tufka."
Fadin Mama tana huci cike da takaicin halin da Muhibbat ke ciki. Duk wannan karfin ikon tana yi ne bayan tafiyar Abule gida don a farko Abule ta kasa ta tsare cewa kafarta kafar Muhibbat din, ita za ta kula da ita, acewarta ta ga jiya kuma ta ga yau, don haka sai dai ta koyar da wankan jego. Dakyar su Justice suka lallaɓata ta bar asibitin.
Ta zubawa mahaifiyarta idanu tana mai jin hawaye na sauka bisa kuncinta. Sosai ta goyi bayan hakan, ta ji ta kuma gani za ta koma gidan iyayenta. Komawar da za ta zama na har abada. Wannan na nufin alaƙarta da Aliyu ta ƙare. Lumshe ido ta yi bayan ta share hawaye ta yi shiru kamar mai bacci tana ci gaba da sauraron yanda yayyunta maza da kuma Mamar suke fadin albarkacin bakinsu. Don babu wanda bai taɓa ganin cin kashin da Aliyu ke mata ba, musamman mazan da suka fi kowa sanin har gobe bai bar shaye-shaye ba.
Ta tuno yanda komai ya faru har ya yi sanadin faduwarta da kuma suma.
_Tana zaune a falo ta zubawa talabijin ido sai dai rabin hankalin ya tafi ga tunani, cikin wannan halin ta ji bugun ƙofa kamar za'a ɓalla. Da hanzari ta mike ta fito tsakar gidan, shakka babu bugun ne. Wannan yasa ta tuna bai fita da mashin dinsa ba, asalima mashin din kwana biyu ta bar ganinsa, ta kuma ji yana waya yana kiran siyarwa zai yi ya siya wani._
_Hijab ta zura gami da daukar mukullin gidan jiki na rawa ta nufi kofar a ranta tana mamakin abinda ya hanashi daukar nasa mukullan. Kai tsaye ta bude gami da kaucewa ganin mutum ya shigo a hargitse kuma yana tangaɗi. Ji ta yi cikinta ya yi wani irin juyawa, tabbas yana sha, amman duk ranar da ya yi niyyar sha zai umarceta da fita daga dakinsa ya kulle, takan sa kunne ta ji yana tamɓelansa har bacci ya kwashe shi. Kusan rabin mayen a kiran sunan Ramlat ko kuma Baby zai ƙare sai kuwa zage-zage._
_"Ki rufe ƙofar kin tsaya kina kallona kamar farin wata."_
_Ya yi furucin da muryar ƴan maye. Jiki na rawa ta rufe suka koma ciki tana ambaton Allah a'a zuciya. Abinda kawai take tunani bai wuce na kasancewar mashayi uban ɗan cikinta ba, ta shafi cikin da tun da ya murda bai saki ba tana kuka sosai. A haka ta iskeshi ta zube a saman dinning table yana bude kulolin abinci gami da watsar da murafan a tsakar falon. Ba don plastic bane da ya fasamata._
_"Ke, ban hanaki yimin tuwo a gidannan ba?"_
_Ta share hawaye, ya za ta yi? Abinda ke cikinta shi yake da muradi, ta kasa cin komai tun safe. Ganin kuma sun jima ba su ci bane ya sanya ta girkawa._
_"Ka yi hakuri."_
_Miƙewa ya yi ya ƙaraso inda ta ke, ba zato ta ji ya ɗauketa da mari, abinda tun da take za ta iya cewa ba'a taɓa marinta ba da girmanta. Wannan ta sanya ta yin baya a gigice, ba kuma zato ta bugu da bangon dake gefen 3 steps na hawa dinning din wanda ya yi sanadin gocewarta ta fadi akan cikin da ko fitowa bai yi ba. Ba shiri ta saki wani mugun ƙara gami da ambaton Allah, a hankali ta daina motsi. Shi kuwa ya nuna ta da yatsa._
_Tsabar raini ya shiga tsakaninmu shi ne za ki kwanta bacci ina magana? To don uwar ubanki ki yi ta baccin mana! Aikin banza!"_
***
Ta ƙara runtse ido, tabbas ta ji wannan kalamin can tsakar kanta kuma kamar a mafarki, koda ta farka a gadon asibiti ta ganta Abulle a gefanta tana sharar hawaye da surutan kada Allah Ya sa ta mutu ba ta ga yaran Aliyu da Muhibbat din ba. Ta kudurta wannan buri na Abulle ba zai samu ba da yardar Allah, ta hakura da Aliyu koda sonsa zai zama ajalinta. Ta ba shi damar auren wacce duk yake so. Ita kam karatunta da yace ba ya