Showing 168001 words to 171000 words out of 230725 words

Chapter 57 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1097

da rike baki da hannu ɗaya yana wani murmushi, AlHassan shi kansa abin nata dariya ya ba shi. Ido Hussein din ya mishi don haka ya shiga acting.

"Haba Hajjaju, ki kwantar da hankalinki. Komai ai na Allah ne. Ai ko shekaru miliyan za'a yi ana shuka rashin alkhairi, akwai ranar ƙin dillacin. Kinsan hausawa sun ce ramin ƙarya ƙurarre ne. Ina nufin da sannu kema Allah zai sada ki da naki ƴan uwan. Mun jima muna nemansa, a zatonmu ma ya mutu, sai dai kwatsam labari ya iso mana can Adamawa cewa an ga mai kama da ni a Kano, kamar da wasa ina zuwa na haɗu da shi. Ai ba abinda za mu ce ga Ubangiji sai godiya. Ya ban labarin irin kulawa da soyayyar da ki ke nuna mishi, muna godiya sosai sosai fa."

Mamaki, tsoro ko farin ciki? Oho, Hajiya Zeenatu ba ta san wanne ta ke ji ba. Dagaske ne Hussein bai zarginta da komai haka ma dan uwansa ko kuwa dai su na mata shigo-shigo ba zurfi ne?

_*"Kin manta waye Hussein? Mutumin da bai iya ɓoye ɓacin rai ba? Ga dukkan alamu son da ya ke yi miki ya hana ya zarge ki. Wannan ne zai sa ɗan uwansa ma ba zai zargeki ba. Ko ba komai daular kadai da suka tarar da dan uwansu a ciki, zai hana su zargi komai a kanki."*_

Wani sashi na zuciyar Hajiya Zeenatu ke mata wannan tunin, nan da nan ta gaskata hakan, wani farin ciki ya dabaibaye ta. Ta shiga rawar ƙafa gami da yin nan nan da AlHassan.

"Me ka fi so dan uwanmu, me za a girka maka?"

Ya yi murmushin da bai kai zuci ba.

"Ko me kika sa aka girka zan ci Hajjaju."

Ta yi dariya tana duban Hussein wanda ya dauke kai ya maida hankali ga wayarsa.

"Shikenan an gama! Kai fa Mijin? Me ka ke da muradin ci?"

Ba tare da ya dube ta ba ya amsa.

"Duk abinda ki ka sanya a girka."

"Shikenan. Ai yau da kaina zan shiga kicin, da hannuna zan muku girki don yau ranar farin ciki ce gare mu. Rana ce da ba za mu mance ba."

Anan ne Hussein ya ɗan kalleta ya yamutsa fuska. Ta wuce sama da sauri da niyyar sauya kaya. Bayan tafiyarta ya yi jifa da wayar ya riƙe kai zuciyarsa na zafi. Dakyar ya iya kai zuciya nesa bai shaƙe wuyanta ba.

"Akwai wuya fa, dakyar na iya jure kallon fuskar matarnan taka."

AlHassan ke maganar yana dubansa, ya dago ya ja guntun tsaki.

"Ka daina haɗa ni da ita please."

Murmushi kawai AlHassan ya yi ya dubi agogo.

"Ya kamata mu yi haramar tafiya masallaci, daga nan ina son wucewa asibiti na ga jikin Ƙanwata."

Shiru ya samu maimakon amsa daga bakin Hussein kawai dai ya mike ya nufi bandakin dake falon, can ya fito. Ganin alwalar ya yi  shima ɗan uwan ya mike ya shiga toilet.

Daidai sadda Hajiya Zeenatu ta sauko cikin wata doguwar riga ƴar kanti da ta matse ta, albarkatun tumbinta duk sun fito sun yi layi-layi. Ya kauda kai yana ji kamar ya yi amai da ya tuna tsawon lokacin da ya ɗauka yana haɗa jiki da ita.

"A'a, ya na ga kun miƙe? Ina shi AlHassan din?"

Hussein ya ci gaba da ɗora agogonsa bai ce komai ba. Don kanta ta ba kanta amsa.

"Oh, yana toilet kenan. Lallai kam don Magriba ta kusa. Bari na leka kicin sai na koma na yi alwalar nima."

Murmushin gefen kumatu ya yi jin wani sabon salo, kiran sallah da wutsir. Hajiya Zeenatu da batun ɗora alwala? Jinjina kai kawai ya yi ta sauke ajiyar zuciya ta yi hanyar kicin tana kwala wa John kira.

AlHassan na fitowa suka kama hanya. Daga masallaci, suka dawo suka shiga motar Hussein din, a waya ya ke sanarwa Hajiya Zeenatu fitarsu.

"Haba haba don Allah, girki fa zan muku yanzu."

Sai da ya daki sitayari gami da jan tsaki don wani irin ɓacin rai da shagwaɓar Hajiya Zeenatu ta jawomasa. Yana gani AlHassan na mishi hannu alamar ya nutsu. Ya daure ya amsa.

"Kiyi hakuri Madam, yanzu za mu dawo, ba wani jimawa za mu yi ba. Kayansa zan kai shi ya kwaso daga Hotel."

Bai bari ta karashe amsawar ba ya kashe wayar.

***
Yusufa wanda a kan idonsa mota ta fice daga gidan da Halima ta mishi kwatance, ya bi motar da kallo, ganin ba'a ganin na ciki ne yasa shi maido hankali ga Maigadin. Da sauri ya karasa tun kafin ya karasa rufe ƙyauren.

"Sannu Baba."

Maigadin ya dube shi.

"Yauwa ɗan samari, lafiya dai?"

"Lafiya kalau. Don Allah nan ne gidan Hajiya Zeenatu?"

Gyada kai Baba Maigadin ya yi.

"Eh kwarai, nan ne."

Sauke ajiyar zuciya Yusufa ya yi.

"Alhamdulillah, don Allah wurinta na zo. Idan ba damuwa ka yimin iso Baba. Ka ce mata Halima ce ta turo ni.  Sunana Yusufa."

"Toh banda abinka ɗan samari, Halima kawai babu wata inkiya ko wani abun? Idan ta ce ba ta gane ba fa?"

Yusufa ya yi shiru, ya san ko sunan ubansu zai faɗa a banza don ba lallai Hajiyar ta san ta da wannan sunan ba. Don haka dabara ta faɗomasa.

"Yauwa, ka ce ƙanin Halima ne ma'aikaciyar Revenue. Aikoni ta yi."

Kasancewar Baba Maigadi ba baya ba, daidai gwargwado yana da ilimin boko yasa fadin sunan bai ba shi wuya ba. Ya ce ya shigo ya tsaya daga bakin ƙyauren, Yusufa ya yi godiya ya shigo. Ya dinga bin tamfatsetsan gidan da kallo cike da jinjina irin dukiyar da ala narkar. Sai ya gan shi wani ƙaramin alhaki kuma wani almajiri a gaban gidan.

Koda Baba Maigadi ya isar da saƙon ga Hajiya Zeenatu, nan da nan ta daure fuska.

"Na ba ka damar barin ko wane kare da biri  shigowa gidana?!"

Baba Maigadi ya dan russuna a ladabce.

"Ki yi hakuri ranki ya daɗe, na dauka kinsan Halimar ne. Amma.."

"Kai dalla yimim shiru hakanan! Ka koma ka ce mishi babu wata Halima da na sani don haka ya gaggauta bar min gida tun kafin ya yi maka sanadin aikinka."

Jin haka ai da sauri Baba Maigadi ya kara bada hakuri tukunna ya kama hanya da sauri-sauri. Idan aka yi mishi sanadin aiki kuma ina ya kama?

Yusufa na hango shi ya ƙuramishi idanu. Maimakon ya ji ta ba shi damar ganawa da ita, sai ya ji akasin hakan. A ƙarshe ma Baba Maigadi bude mishi kyaure ya yi yana mai ba shi hakuri da roƙon ya tafi tun bai jazamishi ba. Haka Yusufa ya fita jiki a matukar sanyaye. Ta tabbata dai karshen Halima ne ya zo. Komai yanzun zai iya faruwa gareta tunda har ta bari zuciyarta ta rinjaye ta wurin aikata abin dana sani da kuma nadama.

***
A farfajiyar asibitin ya faka motar.

"Muje ko?" Cewar AlHassan ganin Hussein din ba shi da niyyar fitowa.

"Ka fara shiga, ina nan zuwa. Akwai wayar da zan amsa ne."

Bai takura mishi ba ya yi gaba zuwa ciki, Hussein ya kwantar da kai saman kujera gami da lumshe idanu. Hoton fuskar Chairman Aliyu Dikko ya kasa fice mishi. Ya kasa mance ganin da ya yi mishi a wajen Ramlat.

Kwankwasa gilashin motar da aka yi ne ya maido shi hayyacinsa, ya ɗago kai ya sauke gilashin. Ganin Hisham ya ja guntun tsaki. Hisham ya dora hannu saman windon.

"Yanzu na ga Twin brother dinmu, ya cemin kana mota shi ne nace bari na zo na ji abinda ha dakatar da kai daga shiga."

Hussein bai ce uffan ba, hannu kawai ya sa ya ƙaro volume na waƙar da ya ke ji.

Hisham ya zagayo ya bude mazaunin gaba ya shiga gami da kashe waƙar gaba daya.

"Kana da tabbacin abinda ka ke yi zai haifarmaka da ɗa mai ido? Kana da tabbacin wacce ka ke so za ta so ka a wannan halin? Meyasa ka ke kokarin hana zuciyarka abincinta a koyaushe?   Meyasa ka ke hana idanuwanka ganin irin sadaukarwar da Ramlat ta yi maka da gangan?"

Hussein bai ce uffan ba, bai kuma katse shi ba don haka ya ci gaba.

"Anya Hussein ka san wace ce Ramlatu?"

"Mutum."

Ya amsa kai tsaye yana murmushi gami da kallonsa.  Hisham ya harareshi.

"Eh mutum ce, amma ta bambanta da irin mutanen da ka ke mu'amala da su."

"Rabinta aljana ce?"

Ya ƙara watsamasa tambayar da ta ƙara kai Hisham bango.

"Kana ƙin gaskiya da gangan, amma magana ta gaskiya, Ramlat ba irin macen da namiji zai kyale ba ce."

"Ya aka yi ta rabu da uban ƴaƴanta?"

"Wai ban taɓa faɗamaka baban yaranta rasuwa ya yi ba?"

Hisham ya tambaya da mamaki. Hussein ya girgiza kai.

"Bana jin mun taɓa hirar, idan ma mun taɓa to na manta kam. Allah Ya yi mishi rahma."

"Amin."Hisham sai ya karkace ya hau ba shi labarin rayuwar Ramlat tun daga farko har zuwa rasuwar mijinta a tsakiyar filin sallar juma'a kuma cikin watan azumi.

Hussein ya yi shiru bai katse shi ba har ya kammala.

"To meyasa yanzu ba za ta auri Yallaɓai ba? Ko ba komai zai jiyar da ita farin cikin da za ta mance dukkan ƙuncin rayuwa."

Hisham ya ji kamar ya shaƙe shi.

"Ba wannan nake nufi ba, kai nake so ka auri Ramlat ko don irin son da ka ke mata. Wallahi ba ta dace da kowane namiji ba sai kai."

"Na taɓa ce maka ina sonta?" Hussein ya fadi kansa tsaye yana murmushi, wani irin murmushi tun daga ƙasan zuciya. Hisham ya kara jin haushi da takaicinsa.

"Dan iska kawai, sai ka zauna kar ka aure ta din!"

Yana kai wa nan ya bude motar ya fice. Hussein ya tashi motarsa ya yi ribas har ya kusa yin sama-sama da Hisham banda Allah Ya sa ya matsa gefe. Murmushi ya ke yi ganin yanda Hisham din ya fusata ya na surfa bala'i. Ya juya kan motar ya fice daga asibiti zuciyarsa kamar an narkar da ƙanƙara.

Awanni biyu zuwa uku, sai ga shi nan ya dawo niƙi-niƙi da kayan dubiya ya bar su a cikin motar, sai da ya shiga masallaci ya gabatar da sallar isha'i sannan ya karasa ciki.
Aka yi sa'a masu gadin Ramlat sun yi gaba bisa umarnin da Chairman din ya bayar. Sai kuma goben za su ƙara dawowa.

Kwankwasawa ya yi ya shiga da sallama,  gaba daya mutanen da ke dakin suka amsa. Ya karasa shiga bai ko kalleta ba ya durkusa suka gaisa da Hajiya. Ta amsa da fara'arta tana kara taya shi murnar haduwa da ɗan uwansa. AlHassan na zaune yana cin abinci kai ka rantse dama can wani irin mugun sabo aka yi da juna. A'isha ce abokiyar hirar, ana ta dariya. Hisham wanda ya kauda fuska bai ko kalleshi ba. Hussein ya mike ya nufi gefen Ramlatu, tun shigowarsa kirjinta ke harbawa da sauri-sauri.

"Sannu, ya jikin?"

Ya fadi ƙasa-ƙasa, hirar da su AlHassan ke yi ya hana Hisham mai kasa kunne jin gulma.

A hankali ta dube shi., fuskarta ta yi fayau.

"Alhamdulillah da sauki."

"Allah Ya ƙara lafiya."

Ta amsa da amin ta kuma yi mishi godiya. Har zai juya ta yi magana.

"Na tayaka murna, Allah Ya kara kiyayewa."

Ya juyo kansa ya dube ta. Ta kasa gane ma'anar kallon don haka ta kauda kai.

"Na gode sosai."

Daga haka ya koma wurin su Hajiya. Nan Hajiya ta ba Aisha umarnin ga zuba  mishi abincin. Bai yi musu ba don dama yana jin yunwar kadan kuma ba ya son ko loma daya na abina Zeenatu ta girka ya shiga cikinsu shi da ɗan uwansa. Kusa da Hisham ya zauna saman kujera maimakon gefen AlHassan wanda ke zaune saman darduma.

"Ka gama fushin?"

Ya fadi daidai saitin kunnen Hisham yana murmushi.

Murmushin shima Hisham ya yi. Ko ba komai zuciyarsa ta yi tas ganin bai ba shi kunya ba ya shigo. Aka zuba mishi abinci ya soma ci.

Ramlat gaba daya fa an kasa sakewa, ita ce ta ja mayafi ta gyara sai kuma ta ja zani. Har dai garin juye-juyenta ta fama ciwon aikuwa ta saki ƙaramin salati.

Ya ɗago idanu ya dube ta, ita din ma shi ta kalla. Sai ta janye da sauri tana amsa tambayar Hajiya.

"Lafiya lau Hajiya, fami nayi kaɗan."

"Sannu, ki dinga bi a hankali."

Cewar AlHassan. Ita kuwa Aisha ta mike ta nufi wurinta tana gyaramata zaman mayafin da ta ke ta fama da shi.

"Sis, wannan irin rashin sukuni? Ko duk a dalilin Hussein ne?"

Ta fadi murya ƙasa-ƙasa yanda Aisha din ce kadai za ta ji. Harara ta bi ta da shi ita kuwa Aisha ta yi ƴar dariya.


 









  I just published "BABI NA HAMSIN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1009630651?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=ynI1KGJjd7sQQHwi7y8Hy%2FURSw8ZoDbiFN7aldIK5sou8xXacVQ1hbP5MNPCrtXe3NJxi6hvqSx39DOvHzE2aH8gSWFQR%2FiXs3hPnnEYhollJSFusGkC3Jmu6jUkimqk





🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

51)

Shi kuwa gogan abincinsa kawai yake ciki fuskarsa cike da wani irin nishaɗi. Ya kammala ya dire farantin.

"Hajiya muna godiya."

Murmushi Hajiya ta yi don tagwayen ba karamin burge ta suke ba.

"Yaushe ne tafiyar taku Adamawa?"

AlHassan ya amsamata.

"Gobe da zarar an shiga kotu an fito za mu wuce."

"Allah Sarki, toh Allah Ya nunamana. Sai dai zan so na ji taƙaimaiman tarihin abinda ya faru gareku a baya."

AlHassan ya murmusa.

"Kar ki samu damuwa Hajiyarmu, in sha Allah komai za ku ji gaba dayansa."

Ta jinjina kai.

"Allah Ya nunamana lokacin."

Aka amsa da amin. Ramlat ta yi shiru, itama abinda ta ke son ji kenan, tana son sanin yanda har Hajiya Zeenatu ta yi nasara akan su.

Kwankwasa kofar da aka yi gami da sallama yasa duk suka mayar da hankali. Nos Farida ce. Suka gaisa sannan ta miƙawa Ramlat takarda. Cikin raɗa-raɗa ta ce.

"Gashinan, Khadija ta nemi da na ba ki."

Ta karɓa da mamaki ta kuma yi godiya. Daga nan Farida ta juya ta fice. Ta ɗago ta dubi mutan dakin wadanda ita suke kallo. Ta maida hankali ga takardar ta warware ta shiga karantawa.

_*Assalamu alaikum,*_

_*Ramlat ina miki fatan alheri da kuma samun lafiya. Akwai wani lamari da nake son sanarmaki. Wata mata ta yi barazanar hallaka ni matukar ban aiwatar da aikin da ta sanya ni ba, wato na kashe ki. Laifi ne da har abada bana fatan na aikata koda a kan maƙiyina ne. Ina mai ba ki shawara akan ki nar asibitin nan da gaggawa domin idan ma ni na kasa aiwatarwa za ta iya siye wani da kudi ya cikamata burinta. Taku mai kaunarku, Khadija Ashir.*_

Bakin Ramlat ya shiga rawa yayinda idanunta suka cicciko da kwalla. Tsam! Ya miƙe ya ƙaraso wurinta ba zato ta ji an zare takardar daga hannunta. Ta dubeshi, shima ita ya ke kallo cike da zargi kafin ya maida hankali ga takardar.

"Meyafaru ne?"

Hajiya ta nemi sani. Ya miƙawa Hisham, Hisham ya karanta a fili. Hussein ya sa kai ya fice daga ɗakin.

Su Hajiya suka sanya salati.

"Wai wace ce wannan matar mai neman ganin bayan Ramlatu? Oh duniya ina za ki da mu? Nikam ko maganin asibitin nan ban yarda a ƙara kawowa ki sha ba Ramlatu."

Maganar karshe na Hajiyar sai ya ba AlHassan dariya.

"Kar ki damu Hajiyarmu, ba abinda zai sami Ramlatu da yardar Allah. Sai dai ya kamata a bi shawarar Khadija, a ɗauke ta daga asibitin."

"Dama ai Likitan ya fadi, yanda take samun sauki zai iya ba mu sallama gobe ko jibi. To ai kuwa gwara a yi komai."

Can wayar Hisham ta yi ringing, Hussein ne. Hisham ya saurari bayaninsa sai ya yi murmushi ya katse kiran.

"Ga wanda ya fi mu can ma ya tafi nema maku sallama a darennan."

Da mamaki Aisha da AlHassan har su na haɗa baki wurin tambayar waye?

"Hussein." Aisha ta saci kallon Ramlat tana murmushi, itama Hajiya murmushin ta yi kawai ba ta ce komai ba.

Kamar dai da wasa, haka Hussein a daren ya yiduk cuku-cukun da zai yi har aka ba su Ramlat sallama a daren.  Suka haɗa komatsansu, Hajiya da Ramlat a motar Hussein, shi kuwa Hisham da madam dinsa suna tare. Amrah wacce har ta kamo hanya, sai waya suka yi mata suka sanarmata da batun sallama. Ita kanta ta yi mamaki.

A hankali ta ɗago kai don tun shigar ta motar kan yana a ƙasa. Caraf suka haɗa idanu ta cikin gilashin kasancewar AlHassan ke tuƙin wannan karon. Ta sauke kanta, shi kuwa ya samu damar ƙarewa fuskar kallo yanda duk ta faɗa kamar wacce ta yi cutar wata guda.

A hankali ya kauda kai, suka yi ido hudu da AlHassan da ke satar kallonsa, murmushi AlHassan ya yi mishi shi kuwa ya gyara zama gami da ɗan ɗaure fuska kadan yana shan ƙamshi.

Har gida suka kai su, Ummi da su Ansar duk suka fito a guje suna mata oyoyo, za su fada jikinta Hussein ya yi saurin riƙo Affan wanda ya fi kowa kusantarta, ita kuwa ta dafe hannu tana kiran wash!

"Ba kwa ganin ciwonta?"

Ya faɗi a hankali, suka fasa rungumeta su na dariya. Ya kama hannunsu zuwa wurin mota.

"Ku zo muje"

Ramlat ta bisu da idanu kafin ta juya ta bi sahun su Hajiya zuwa ciki. Shi kuwa Hussein ledojin dubiyar da ya loda a boot, shi ya ciromusu ya damƙa musu.

"Oya, maza ku je a kaiwa Mami sai ta ba ku."

Affan ya hau washe baki ganin Hussein ya fiddo alewa daga aljihu ha bude ya sanya mishi a baki. Murmushi sosai shima ya yi mishi ya bishi da kallo har ya ɓacewa ganinsa.

Bayan Hussein sun koma gida, Hajiya Zeenat ta tarbe su da fara'a tana mai danne takaicin da suka ɗuramata. Hussein ya dan sakarmata.

"Ki yi hakuri, gidan Hisham muka ci abinci ba haka na so ba."

Ganin yanda ya fadi cike da kulawa yasa nan da nan ta ji zuciyarta ta sake. Ko ba komai hanyar lafiya a bita da shekara. Yanzun dai kaffa-kaffa ta ke yi kar kwaɓarta ta yi ruwa. Da haka ya nunawa AlHassan dakinsa kafin shima ya shige nashi dakin. Hajiya Zeenatu ta yi mamakin da ya bari ta kwana tare da shi duk da bai yi mata kama ko hannunta ba, asalima baya ya juya da nufin bacci yake ji.Ta so su yi batun tafiyarsu London ammata share, har lokacin jikinta a sanyaye yake, burinta yanzu gari ya waye ta shiga asibitin da Ramlatun take ta ga ko ta aiwatar da aikinta.

"Gobe in sha Allah zan yi ƴar tafiya."

Hajiya Zeenatu ta tsinci maganar Hussein wanda ta yi zaton bacci ya ke kamar daga sama, ta mike zaune gami da kunna fitila. Har sannan ya bata baya. Ya yi crossinh hannaye  a kirji.

"Ina za ka je kuma?"

"Adamawa." Ya furta kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login