Showing 105001 words to 108000 words out of 230725 words

Chapter 36 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1080

har ta ƙaraso inda take a matuƙar fusace.

"Ke! Wai ke wace irin mayya ce?! Duk yanda na kai ga nesantaki da mijina hakan bai isheki ba? Wannan wane irin bibiya kike mishi?!"

Ba Ramlat ba, gaba daya mutanen wurin suka maida hankali ga Hajiya Zeenat dake tsaye tana cika da batsewa. Ramlat ta kai maƙura da irin wannan cin mutuncin da Hajiya ke mata. A yau ta ji shirun ya gagareta don haka ta watsamata banzan kallo sama da ƙasa.

"Daga ke har mijinnaki ba ku isheni kallo ba. Kuma ma banda abinki Mama, ai matar da ta yarda da kanta a zuciyar mijinta, ta kuma yarda da mijinnata, babu wata ɗiya mace da za ta razanata balle har ta damu kanta. Sa'arki ɗaya, ba zan iya haɗa miji da sa'ar uwata ba, da babu abinda zai hana ni auren mijinki ko don na nunamaki bambancin aya da tsakuwa!"

Hannu Hajiya ta ɗaga da zummar marinta, caraf ta riƙe hannun tana murmushi kafin ta yarfar.

"Kin yi kaɗan Mama. Mari wata dai ba Ramlat ba."

Tana kaiwa nan ta juya a fusace ta kama hanyar barin wurin, tana jin Hajiya na kwalawa Maigadin wurin kira, har suka kusan cin karo da Ramlat, tana sauka yana hawa, ta kuma ji sadda ta ke bada umarnin koda wasa ya ƙara bari ta shigo wurin ya tabbata ranar barin aikinsa kenan.

Ranta a tsananin ɓace  ba ta ko kallon gabanta sosai, ba ta yi aune ba ta yi karo da mutum, tsantsin tiles da ya kusan kifar da ita yasa ta saurin riƙe kafaɗarsa da dukkan hannuwanta. Ƙamshin tsadadden turarensa ne ya kashe dukkan wata lakar da ke jikinsa. Ko sakan ba ta yi ba ta saita kanta gami da kauda hannunta a jikinsa, kallon kallo suka yi. So yake ya tambayeta dalilin ɓacin ranta, amma ganin wacce ke saukowa tana haɗa matattakala bibbiyu zuwa uku yasa shi yin shiru.

"Dama na faɗa! Yarinyarnan karuwa ce! Karuwa ce! Kun gani ko? Kun ga kalar iskancin da ta ke yi a jikin mijina ko?!"

Samari da ƴanmatan da aka bari a sama tuni suka garzayo ta jikin gilasai suna kallon ƙasan. Wadanda basu taɓa ganin mijin Hajiyar ba sai a sannan suka ganshi, ƴanmata ido ya soma wani kakkarwa, basu taɓa zaton haka mijin Hajiyar yake ba. Wasu kuwa suna ganinsa a wurin don mafi akasari don shi suke takowa su zo, amma basu taɓa kawowa a ransu mijin wannan uwar matar ba ce.

Ramlat ta dubeshi da idanunta wadanda ɓacin rai ya sauya, gani take ya kamata ta rama abinda Hajiya ke mata. Babu ruwanta da abinda zai biyo baya, idan har hakan zai baƙantawa Hajiyar to a wurinta daidai kenan.

Murmushinta da ba kowa ke ganin irinsa ba ta jefamasa gami da yi mishi kallon da sai ka rantse wani masoyinta ne take tare da shi. Shi kuma har sannan ɓacin ran abinda Hajiya Zeenatu ta yi bai sakeshi ba, fuskarsa a ɗaure. Sai dai ganin irin murmushin da Ramlat ke mishi, bai san ya akai ba sai ya tsinci kansa da maidawa kura aniyarta.

"Ka yi hakuri Heart, ko ma mene zan jure a kanka. Kar fa ka yi tunanin zan bar ka a kowane yanayi, wallahi ta yi kaɗan ta firgitani. Soyayya kuma yanzu muka fara. Ina jiran kiranka."

Tana kaiwa nan ta ɗaga yatsunta biyu tana murmushi ta bar wurin, Hajiya Zeenatu ta kunduma ashar gami da ɗaga ƙafa da zummar bin bayanta, caraf ya riƙe damtsen hannunta.

"Ba girmanki bane!"

Abinda ya fadi kenan cikin sanyin muryarsa kuma ƙasa-ƙasa yanda ita ɗaya ce za ta ji, samari da ƴanmata  wurin da abinda Ramlat ta yi ya burgesu suka hau tafi da ihu har da masu fiito. Baƙin ciki da takaici ya sa Hajiya watsawa mijinta kallon banza da jajayen idanunta, ta yi rantsuwa akan sai ta kashe Ramlat da hannunta. Hussein sai ya raina kansa a hannunta. Ga mamakinta kamar karamar yarinya ya shiga jan hannunta suka fita daga wurin ya cusata a motarsa, fitowa ta yi ya dubeta.

"Ina za ki?"

Wani banzan harara ta watsamasa da ya sanya shi rudewa. Ya kasa magana sai faduwar gaba.

"Ki yi hakuri."

Bakin ciki bai bar ta ta yi magana ba, ta rasa wannan wane irin aiki ne, wani sa'in ya yi tasiri a kansa, ya dinga shakkarta, wani sa'in kuwa sai ka rantse babu ko ɗigon asiri a kansa.

"Ai ba kai ka kawoni ba! Ka motarka ka bar wurinnan tun kan na yi maka abinda za ka yi nadamarsa!"

Kamar wanda mahaifiyarsa ke ba shi umarni, ya bude gidan gaba ya shiga. Gilasan duk a sauke.

Kallonsa Hajiya Zeenatu ke yi har ya tashi motar, fuskarnan ba'a sake ba kuma ba'a ɗaure ba, duk iyakar nacinta ta kasa gano kalar rikiɗewar da maganganun Ramlat ya jefashi ciki. Idan ta tuna ranta baƙi yake, komai dangane da Ramlat take da buƙatar sani. Wannan kuma ba zai mata wuya ba, ta ci alwashin rusa dukkan farin cikinta koda za ta rasa dukkan abinda ta mallaka. Jikinta ke ƙara ba ta ita ce yarinyar da Isuhu da Gora suka yi mata gargaɗi a kai.

Har ya bar wurin ba ta fasa kallonsa ba kafin a rikice ta shige nata motar ta bar wurin. Kai tsaye gidan Hajiya Batool ta nufa.

***
"Me na faɗamaki?! Ke kin tsaya kan lallai ba za ki bar garinnan ba da hannunki za ki ɗauki mataki a kan yarinyar! Ai wallahi Zeenatu ji nake kamar na ɗaukeki na jefa a wuta tsabar haushin da kika bani!" Hajiya Batool ke zuba wannan ruwan masifar kamar ta ari baki. Dama cike take da ɓacin ran yanda tana wankan magani a tsakar gida Maigadinta ya ganta, takaicin ya ɓatamata aiki ne yasa ta sallameshi ta kuma yi mishi gargadi mai girma akan yunƙurin tona asirinta.

Hajiya Zeenatu ta share hawaye.

"Wannan bala'i da me ya yi kama, yarinya ta zamemin ƘARFEN ƘAFA? Yarinyar da a haife a haifi wanda ma ya girmeta balle ita? Wallahi ina kara fadamaki kowane gari zan je tunda har aka tabbatarmana sai ya aureta toh za ta biyoshi tunda mayya ce. Abu ɗayan dai shi ne mafita, na kasheta da hannuna ko kuma na gallabi rayuwarta ta yanda na lahira ma sai ya fi ta jin dadi. Batool ina son Hussein fiye da yanda nake son rayuwata, ba irin mazan da ake dandanawa bane a kyale, kuma wallahi wallahi ko zan yi yawo tsirara sai na ga bayan Ramlatu."

"Au kin ma san sunanta ashe?"

Ta gyada kai.

"Har inda take aiki na sani, zan kuma ci ubanta."

Hajiya Batool ta jinjina kai cike goyon  bayan aminiyarta.

"Duk abinda ya dace ki aikata ki yi idan har zai nesanta ta daga Hussein. Amma kafin komai, ki soma yi mata kyakkyawan gargadi, idan ta ji shikenan, idan kuwa bai samu shiga ba sai ki aikata yanda kika so."

Da haka suka ci gaba da saƙe-saƙensu akan Ramlat.

***
  Ramlat kuwa, wani wurin ta nufa ta yi musu siyayya, ko kusa ba ta ji ko ɗarr da abinda ta aikata ba asalima wani irin murmushi da dariya take ita kadai a mota cike da nishadi. Ko ba komai yau ta rama abinda Hajiya Zeenat ke mata akan zargi da baƙin kishi irinnata. Da wannan nishaɗin ta isa gida, Hajiya sai da ta kasa hakuri ta tambayeta. Ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta sanarmata duk yanda lamuran suka faru. Baki sake Hajiya ke dubanta.

"A'a Ramlatu, kar fa ki jajiɓomana abinda ya fi ƙarfinmu. Ke ko tsoro ba kya ji."

Taɓe baki ta yi haɗe da murmushi tana kokarin kai tsokar nama bakinta.

"Hajiya kar wannan ya dameki, daidai nake da ita tunda ita ba ta da hankali. Ni wallahi ban yarda da ita  ba ma."

Jinjina kai Hajiya ta yi.

"Ba dai ruwanki da ita, idan ta yi miki sanadin aiki ai ta gama da ke tunda ta san  inda kike aiki."

"Da yardar Allah ba ta isa ba."

"Ai shikenan."

Faɗin Hajiya ta ƙara da addu'ar neman tsari, Ramlat ta amsa da amin gami da lumshe ido kadan tana tuno da irin kallon da Hussein ya ke jifanta da shi, kallon da ya nemi rikitata ta kasa abinda ta ci burin aikatawa, taimakon Allah ne kaɗai yasa ta ƙarasa jawabinta ta bar wurin. A gefe guda tausayinsa ne ya mamaye zuciyarta, ta kuma ƙudurta taimaka mishi da addu'a don hankalinta bai kwanta da Hajiyarsa ba.

Misalin karfe sha daya na dare, tana kwance Affan a gefenta ya yi bacci, ita kuwa tana kan whatsapp suna hira da Amrah tana bata labarin abinda ya faru yau suna dariya har Amrah ke gargaɗinta akan irin wannan gangancin acewarta irin su Hajiya ba haka suka tsaya ba. Dawowar mijin Amrah ne yasa suka yi sallama ta ɓige da kallon status. Da sauri ta mike zaune tana ƙara kallon sunan Mutumin Mall kamar yanda ta yi saving lambarsa. Status ya dora na wata yarinya kyakkyawa da ba ranar ta soma ganinta ba.

"Dama yana whatsapp ban taɓa lura ba?"

Ta fadi a fili kamar mai jiran amsa daga wani ko wata. Kallon hoton yarinyar ta shiga yi tana murmushi.

"Fatima." Ta furta a fili sannan  ta yi screenshot. Hoto na gaba ne ya kusan zautar da tunaninta, ji ta yi cikinta ya murɗa, ta ajiye wayar ta faɗa banɗaki sannan ta fito. Gumi na tsastsafomata ta ƙara ɗaukar wayar tana dawo da hoton baya ta kalla.

Su biyu ne cikin shigar ƙananun kaya iri ɗaya sai bambancin kala. Ɗaya yana sanye da farin t-shirt, ɗayan kuwa sky blue ce. Banda hakan da kuma farin gilas din da ya ɗaya ya sanya a idanunsa, za ta iya rantsewa ta ƙara duk na hoton mutum ɗaya ne. Kuma nan take za ta ce HUSSEIN ne. Rubutun da ya yi a ƙasan hoton ne yasa ta yin salatin da ba ta shirya ba.

"Idan kana raye Hussein, ina riƙon Allah Ya bayyana mana kai. Ƙwaƙwalwa da zuciya ba zasu taɓa yarda cewar ba ka tare da mu ba."

Cikin sauri ta yi screenshot na hoton sannan ta yi cropping ta yanke wurin rubutun mai kama da cigiya kafin ta yi saving, hannunta har rawa yake yi. Tana so ta ce mishi ta san inda dan uwansa yake amma ta fi son ta tabbatar da zarginta. Tana son Hussein ya yi ido hudu da hoton ta ga yanayin da zai faɗa. Anan ne za ta san yanda za ta ɓullo ta faɗawa mutumin mall inda ɗan uwansa yake. Dama ita sam ba ta yarda da Hajiya Zeenatu ba, yanzun kuma ta ƙara tabbatar da zarginta. Ta kara komawa kan Status din, ga mamakinta ya cireshi. Sauke ajiyar zuciya ta yi, tunda dai ta yi screenshot ai shikenan.

A daren dai baccinta ragagge ne, ita kanta ba ta san inda za ta ƙara haɗuwa da Hussein ba balle har magana ta haɗasu na dogon lokaci sai dai hakan bai karyamata gwuiwa ba. Ba za ta fasa abinda ta yi niyya ba.

***
Tuƙi yake amma murmushi yake yi akai-akai, daki-daki yake tuna kalamanta da irin kallon da ta jefeshi da shi, koda ace bai kai zuciyarta ba, ba ta da masaniya akan tasirin da ya yi mishi.

Ya ɗan kalli garin yanda ya yi luf luf, yammaci ne kuma babu rana dalilin damina da ke kokarin shigowa, wurare da dama a garin Kano ya samu labarin an yi ruwa. Bai tsaya ko'ina ba sai a wurin  Gym dinsu. Ya fito sanye da wandonsa three quarter sai rigarta marar hannu sai baƙar jaka da ya rataya a kafaɗarsa. Da wannan ya nufi ciki inda nan ya tarar da Hisham ya dage sai ɗaga ƙarfe ya ke. Suka yiwa juna dariya gami da cafkewa.

"Shegen sama! Ban tsammaci ganinka nan kusa ba ai. Ka biyewa aure ka soma ajiye tumbin."

Dariya Hisham ya yi yana tsane gumi da ɗan ƙaramin towel.

"Ba'a magana kai kam, aure ƙarshe ne. Wallahi ba don kai ba bazan fito ba don bani da niyya, sai gashinan ka shanyani sai yanzu."

Zama Hussein ya yi yana gyara ɗaurin igiyar fararen canvas ɗinsa.

"Yi hakuri. Ban kyauta ba kam."

"Ina jinka, ya akai?"

Hussein ya ɗan yi shiru don bai san ta inda zai fara ba, can dai ya numfasa.

"Za ka tuna yayar Madam dinka da na kai gida?"

'Anzo wajen.' Hisham ya ayyana aransa, murmushi ya yi.

"Yes, Antinmu Ramlat."

Ya gyada kai yana shafa suma,

"Ita, sun samu matsala da Madam ɗita. Ina kuma tsoron kar ta yi mata sanadin aiki da ma abubuwa da dama. Nasan halinta da baƙin kishi."

Cikin rashin fahimta Hisham ya ce.

"Yimin dalla-dalla."

Tun farkon ganinsu da Ramlat har zuwa abinda ya faru a A&Z bai ɓoyemishi ba. Hisham dai ya cika da mamaki, diramar ƙarshe ta ba shi dariya sosai ya kuma yi mamaki don bai zaci Ramlat din za ta aikata ba. Ɗaukar ta ya ke matsoraciya kuma shiru-shiru marar son hayaniya.

"Mamaki nake."

Hisham ya fadi yana ci gaba da dariya gami da riko hannun Hussein da ke binsa da kallo kamar ranar ya soma ganinsa.

  "Wai meye hakan?"

"Um um, amma fa duk da bansan wannan Madam din taka ba, gaskiyar magana ta ɗauki hanyar da ba zai ɓullar da ita ba. Kishi ko hauka? Ba ta san yanzu kai ya waye ba? Nikam Ramlat ta burgeni wallahi, wannan ma.."

"Nima ban ce ba ta kyauta ba, amma na fi ta sanin matata. Idan a kan kishi ne komai ma za ta aikata. So nake ka ja mata kunne don Allah, ta nesanta kanta daga inda zasu haɗu balle har wani saɓanin ya ƙara shiga tsakaninsu."

"Abinda ban gane ba, tausayinta kake har kake son ba ta kariya ko kuwa tsoron Madam dinka kake?"

Hussein ya yi shiru bai amsa ba can kuma ya dubeshi.

"Alaƙar da ke tsakaninta da  matarka na duba, amma fa zahirin gaskiya ba ta kyauta ba. Ko ba komai dakyar na shawo kan Madam ta fahimci dagasken ba komai tsakanina da ita. Kar ka ƙara cewa ina tsoron matata." Ya ƙarashe cike da rashin gaskiya, shi kansa ya sani yana shakkar Hajiya Zeenatu.

"Kuma dagasken ba komai tsakaninka da Ramlat?"

Gabansa ya fadi, ya kauda kai daga duban Hisham gami da ɗan murmusawa.

"Yarinyar kallonta nake kamar irin Boss ɗin nan, komai ta yi dariya yake ban, tana burgeni. Amma ban taɓa son wata irin son da na yiwa Hajiya ba,har gobe bana jin akwai wacce za ta kai Hajiya a zuciyata."

Ya ƙarashe da wani irin rauni na zuciya da gangar jiki, a karon kansa yake ji kamar ba hakan bane, amma a wani ɓangaren na zuciyarsa ji yake kamar ana ƙara tabbatar mishi da cewa eh! Ba shi da kamar Hajiya Zeenatu.

"Owk!" Abinda Hisham ya ce kenan, ya ji kuma ba don ya yarda ba. Ya hango abubuwa da dama a saman fuskar abokinnasa. Can ya ƙara karambanin watsamasa tambayar da ya taɓa kwatanta yinsa bai ji da dadi ba.

"Kai wai yaushe za ka kaini na gaida Mummynmu ne?"

Kamar walkiya, ya nemi annurin fuskar Hussein ya rasa, kamar wanda ya haɗiyi garwashin wuta, haka fuskarsa ta soma wani ja-ja ga gumi da ya soma tsirfowa saman goshinsa. Miƙewa ya yi kamar wanda aka mintsila ya dauki jakarsa. A ruɗe Hisham ya miƙe tsaye ya riƙe mishi kafaɗa ya fisge har hannunsa na bugun wani ƙarfen motsa jiki, koda da zafi, bai ji ba. Yatsa ya shiga nunawa Hisham. Ya soma magana da muryar da ta ɗauki hankulan jama'ar wurin.

"Kar ka ƙara! Wannan ne gargaɗi na ƙarshe da zan maka! Bana so! Har abada banda kowa a duniyata sai Hajiya Zeenatu! She meant everything to me! Ita kadai ce dangina. Ka rike wannan ka ji?"

Ya ƙarashe a sanyaye, abin mamaki hawaye ya shiga fitarwa, a hankali ya juya ya soma taku ya bar Hisham tsaye a wurin baki a bude. Ga mamakin Hisham da mutanen wurin, faduwa ya yi. A guje suka yi kansa, Hisham ya tallafoshi, idanunsa a rufe sai numfashi yake fitarwa sama-sama

"Hussein, me ya yi zafi haka? Ka yi hakuri don Allah."

"Maida ni gida." Abinda ya iya fada kenan cike da wata iriyar kasala. Jama'ar na ta yi mishi sannu, wani ya riƙe jakar yayinda Hisham ya saƙalo hannun Hussein a wuyansa suka nufi motar Hussein din. Sai da ya zaunar da shi kafin ya koma da sauri shima ya dauko tarkacensa ya zuwa a aljihu suka bar wurin. Yau ne zuwansa gidan Hussein karo na farko, dakyar yake mishi kwatance wannan karon muryarsa ta bude ba kamar ɗazun ba kamar yanda idanunsa suka bude sosai. A gaggauce Maigadin ya bude ƙyaure ganin motar maigidan, Hisham ya tura hancin motar ya faka.

Hajiya Zeenatu na zaune a falo tana amsa waya ta ji sallamar da ba muryar mijinta ba. Turus ya yi kamar yanda itama ta yi tsaye tana dubansu.

Ganin yanayin Hussein ya sa ta ƙarasawa da sauri.

"Habeebee meke samunka? Kai kuma waye?"

Hussein ya zauna ya amsa.

"Hisham ne."

Ta dubi yanayin Hussein din sannan ta dubi Hisham wanda ke gaidata. Ta amsa fuska na yabo ba fallasa ganin irin duban mamakin da ke saman fuskarsa. Ya riga ya gane matsayinta wurin Amininsa don tun shigowarsu idonsa ya kai ga makekan enlargement din da ke dauke da fuskokinsu. Daga irin rikon da ta yiwa Hussein kadai ya ci ace duk mai hankali ya gane alaƙarsu.

'Taɓ!'  Abinda ya ce kenan a ƙasan ransa. A ƙarshe ya daure ya ɓoye mamakinsa ya saki fuska. Zai ba ta bayanin abinda ya faru ne ya ji Hussein ya tareshi cikin rawar murya.

"Amm..dama kaina ne ke ciwo da jiri, ganin ba zan iya tuƙi ba yasa nace ya kawoni. Kiyi hakuri idan ganinsa ya ɓatamaki rai."

Sai lokacin ta wayance gami da sakin fuska

"Haba kai kuwa, mene abin ɓacin rai don abokinka ya kawoka? Wani zubin kamar yaron goye idan ka fadi wani zancen. Sannu, zauna mana bari na kawomaka ruwa."

Hisham ya girgiza kai yana dariyar yaƙe.

"A'a ba komai tafiya zan yi, nima yawa Amaryar na jirana."

Suka yi dariya, ya yi mata sallama sannan ya fice cike da tsantsar mamakin wacce ya gani matsayin matar abokinsa.

"Akwai wata a ƙasa." Abinda ya ce kenan bayan fitarsa daga gidan. Jikinsa ya ba shi akwai wata a ƙasa.

Har ya koma wurin Gym ya dauki motarsa ya yi gida, bai bar tunanin lamarin Hussein da matarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login