Showing 84001 words to 87000 words out of 230725 words

Chapter 29 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1082

kan ta isa take kiran sunan Aliyu.

  Yana naɗe saman gado, shi kadai yasan kwanakinnan da bai sha abin maye ba ya yake ji. Ga damuwar abinda abokansa suka yi mishi na cinsa, ya kasa samun nutsuwa, zuciyarsa na tursasashi akan ya je ya sha ko zai ji sanyi amma yana yiwa kansa faɗa da tunasarwa kansa har abada ya daina.  Jin yanda Ramlat ke kiransa ne yasa shi miƙewa a razane ya tarbeta har tana kokarin faduwa. Hanya kawai take nunawa tana kuka.

"Baby nutsu please, fadamin meke faruwa?"

"Abba, Abba ba lafiya Aliyu. Ya ce na je, don Allah ka kaini Aliyu."

"Kiyi shiru, yanzu zamu je ki ganshi. Kiyi hakuri."

Daga haka ya fito rike da hannunta, hijabinta da ta cire ya dauka ya mayarmata. Bai yi karambanin daukarta a mashin ba gudun kar ta kifemasa a hanya. Titi suka nufa suka sami abin hawa.

***
  Kusan a guje ta shiga dakin da Abba yake kwance a asibitin. Gaba daya iyalin Abban ne a dakin sai Baba Dakta wanda bai jima da shigowa asibitin ba.

  Kai tsaye ta yi kan Abban.

"Abba! Abba!!"

A hankali ya bude ido lokacin da Zulaihat ta janyeta. Munir na gefe yana ji kamar ya je ya shaƙe Ramlatun. Ko ma mene ai ita ce ta ja.

Hannu Abba ya mika, ba musu Ramlatun ta saka hannunta cikin nashi tana wani irin kuka.

"Ya cuceni, ya cutar min da ke Ramlatu."

Aliyu wanda har ya murɗa kofar dakin zai shigo ya tsaya cak ya fasa. Ya juya ya koma da baya ya zauna saman kujera cike da jin kunyar kansa da kansa.

Abba ya ci gaba da magana dakyar.

"Meyasa tun farko kika dage akan sai shi? Ba ki hango abinda na hangomaki ba ko? Ba ki hango aibunsa ba Ramlatu. Yanzu shikenan ya cutar min da ke ya sanyamaki ciwon da ba'a warkewa."

Ji ta yi numfashinta ya tsaya cak, ta shiga jawoshi da ƙarfinta.

"Abb..Abba...me..kake nufi?"

Abba ya runtse idanu yana jin saukar hawaye. Ba shi kadai ba, hatta da mutanen dakin abinda suka kawo shi ne, Ramlatu ba ta san komai game da ciwon mijinnata ba.

"Abar zancen haka Alhaji Khalid, ba'a son yawan maganarnan naka. Don Allah ku ragu a dakin."

Abba ya girgiza kai.

"A'a Dakta, bana jin ciwonnan nawa na tashi ne. Ka bar ni na yi sallama da iyalina. Ni kadai nasan me nake ji."

Ya fadi gami da runtse ido sai hawaye. Hakan ya kara ruɗa mutanen dakin. A'isha kuka har da sheshsheka hakanan su Rafee'ah. Shi kuwa Munir idanunsa ne suka kaɗa sai sauke ajiyar zuciya yake.

"Abba an ce maka Aliyu nada ƙanjamau ko? Abba wallahi karya ne, ko wa ya fadamaka karya yake!"

Abinda Ramlat ta fadi kenan sakamakon tunanin da ya zo mata. Yan uwan da ma iyayen kallonta suke cike da takaici, wannan wane irin so ne da har ciwon Aliyun ma ɓoyonsa take?

"Ramlatu kinsan Aliyu na dauke da ciwo kika yi shiru? Tun yaushe?"

Hajiya da ta kasa hakuri ke wannan tambayar tana duban diyarta a kidime.







 
I just published "BABI NA ASHIRIN DA SHIDA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/f5qPHpmrzab




🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

26)

Cikin kuka ta dubi Hajiyar.

"Wallahi Hajiya ba ƙanjamau ce da shi ba. Jita-jita ce kawai. Ciwon zuciya ce ke barazanar kama shi sakamakon shaye-shaye, sai Infection da ya jawomasa gudawa shine har ya kwanta asibiti na kwana ɗaya. Abba ka tashi don Allah, Abbana kar ka mutu saboda damuwata. Abba ka yafemin. Kaicona "

Kukanta ya ƙi tsayawa, Abba ya kara damƙe hannunta.

"Rabi ki yi shiru. Ki yi shiru. Haka Allah Ya tsara wa Ramlatu. Dakta."

Ya maida dubansa ga Baba Dakta.

"Ka taimakamin a yiwa Ramlatu gwajin jini, idan har tana dauke da cutarnan don Allah a gaggauta dora ta kan magani."

"Abba, wallahi lafiya kalau. Abba dagaske nake maka, ina rantsuwa da ..."

"Kina da tabbas? Mene hujjarki?!"

Munir ya katse a zafafe. Ta dubeshi sai kuma ta kasa magana. Baba Dakta ya bada umarnin duk a fita a bar Abban. Suka fita dukkansu, likitan Abban ya shigo ya kara dubashi sannan ya fito.

"Muje Ramlatu." Fadin Baba Dakta. Ramlat ta dubeshi kamar wata wawiya, yau ita za'a yiwa test akan cutar da ko a mafarki ba ta taɓa ganinta da shi ba? Me ya jawomata wannan tozarci da wulakancin?

'Auren Aliyu.' Cewar wani ɓangare na zuciyarta. Sai a sannan kuma ta tuno tare ta zo da Aliyu, ta waiga baya wurin hakan yasa ta maida dubanta ga Baba Dakta.

"Baba Dakta wallahi wallahi..."

"Yi hakuri, yi hakuri Ramlatu. Kwantar da hankalinki, ki bari ayi din ko don samun nutsuwa da kwanciyar hankalin Abbanki. Kina so ya samu lafiya ko?"

Ta gyada kai gami da jan majina.

"Yauwa ko kefa, muje."

Ta bi bayansa bayan ta bi yan uwanta da kallo. Munir harara ya watsamata, ta kauda kai tana kuka.

Test aka yi mata na jini sannan ta dawo wurinsu ta zauna.

"Ya ake ciki? Me sakamakon ya bayar?" Fadin Hajiya tana dubanta.

Ta bude baki za ta amsa sai ta kasa, kuka ya ci ƙarfinta ga wani bakin ciki da ya tsayamata a ƙahon zuci. Auren Aliyu ya jawomata wulaƙanci, yau ita ake yiwa kallon mai cutar ƙanjamau?

'Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!'

Ta fadi a karo na barkatai.

"Hajiya nifa banda komai, bana dauke da kowace cuta. Hajiya don Allah ki yarda da ni. Wallahi ba ƙanjamau ne da Baban Ummi ba."

"Allah Ya tsinewa kalar so irin naki Ramlatu! Son da har za ki ɓoye cutar mijinki ki rufamasa asiri ki cuci kanki! Wallahi Hajiya ya ci ace kun fidda hannunku a lamarin yarinyarnan, wanda fa ya yi nisa ba ya jin kira! Sanadinta Abba ya fada cikin wannan halin, ai ba ita kadai ku k haifa ba! Tunda ita ba ta bi ku ba, kuma bai kamata ku damu da lamuranta ba. Ta je idan ma mutuwa za ta yi ta mutun mana idan har Abba zai rayu! Mtsww!"

"Kai kuma mene sunanka?! Me za mu kiraka da shi? Ka tsaya kana fada alhalin Abba ba lafiya? Wannan shi ne girman?!"

Zulaihat ke maganar a fusace, tun ɗazun ya kai ta wuya dannewa kawai ta yi.

"Ke! Ni kike faɗawa magana?"

"An fadamaka din! Don kawai kana babba..."

"Ya isa! Haba mana!"

Hajiya ta katsesu a tsawance, faɗan Muniru da Zulaihat sakamakonsa bai fiye kyau ba.

Muniru ya juya a zuciye ya bar wurin, Hajiya ta dubi Zulaihat.

"So ku ke ku nunan halinnaku a asibiti? Shikenan ai."

Ta ƙarashe a fusace. Rafee'ah dai banda hawaye ba abinda take yi, magana ma ta kasa saboda tunanin Abban yayinda A'isha ta kwantar da kai a cinyar Rafee'ah ta yi shiru tana kallon kowa. Ramlatu kuwa kukanta ma har ya yi yawa.

Suna nan zaune Baba Dakta ya nufosu fuskarsa dauke da murmushi. Suka zubamishi idanu.

"Alhamdulillah, koda Aliyu na dauke da wannan kwayar cutar, bai kai ga shafamaki ba Ramlatu. Komai naki lafiya kalau yake. Ki kwantar da hankalinki."

Gaba daya suka sauke ajiyar zuciya. Murnar da suke bai wuce yanzun Abban zai farfaɗo ba idan ya ji sakamakon gwajin da aka yiwa Ramlatun.

Baba Dakta ya shiga dakin ya karasa har gadon Abban yana murmushi, sai dai me? Cak murmushin ya dauke da sauri cikin rawar jiki kuma ya kai hannu bisa tsintsiyar hannun Abban. Ya kara kaiwa saman kirjinsa don bai gasƙata abinda ke faruwa ba.

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!"

Baba Dakta ya furta kafin ya dubi fuskar Abban, kamar za ka kira sunansa ya amsa ga wani dan murmushi. Hannu ya sa ya ja zanin rumfar ya rufemishi fuska.

Ya jima a tsaye yana tunanin t hanyar da zai sanarwa iyalin rasuwar Abban. A karshe dai ya daure ya fita ya fadamusu. Kowannensu ya saka salati.

Dif! Kukanta ya dauke sai kallo. Ta kalli wannan ta kalli wancan.

"Kuka ku ke yi? Abba ai bai mutu ba. Ku daina kuka."

Abinda ta fadi ne ya tabbatarwa Baba Dakta ba'a hayyacinta ta ke ba, ya karasa ya riko hannunta. Ta dubeshi tana murmushi har dimples dinta na lotsawa.

"Abbana bai mutu ba, bai mutu ba fa Baba Dakta. Muje na ganshi, zan fadamasa lafiyata kalau. Zan fadamasa bana dauke da ƙanjamau. Yanzu za ka ga ya tashi, baccin wasa yake."

Ta ja hannun Baba Dakta zuwa dakin Abban. Gaba daya suma suka shiga ciki banda Muniru da har lokacin bai dawo ba.

Mayafin ta yaye ta riko hannun Abba.

"Abba bacci ko? Ka tashi don Allah. Na warke, Baba Dakta ina result din?"

Ta juya a firgice ga Baba Dakta, sai kuma hankalinta ya kai saman tebur ta hango takardar maganin Abba wanda a zatonta shi ne na test din. Ta ɗago ta na nunawa Abban kamar mahaukaciya.

"Abb..Abba, ka ga, negative. Banda komai wallahi. Aliyu ma na fadamaka lafiyarsa kalau. Abba ka yi magana."

Hajiya ta ja hannunta suka fita bisa umarnin Baba Dakta, ya maida marufin ya rufewa Abban fuska.

***

Suna tafe zuwa mota tana sambatu, Hajiya na damƙe da hannunta.

"Hajiya bai mutu ba, wallahi Abbana bai mutu ba. Haba! Haka ake mutuwar?! Ai ba haka bane! Mutuwa ba haka take ba! Abba bai mana sallama ba! Um um Hajiya, Abba fa bai mutu ba. Wayyo Allahna!"

Hak rike kai da karfi kafin ta yi baya, Allah Ya taimaka Zulaihat na bayansu, ta riketa da karfi. Tuni ta suma. Ba shiri da taimakon wasu mata a wurin aka rirriƙeta zuwa ciki.

Dawowarsa kenan daga masallaci ya hango taron mata, har ya kauda idanunsa, hankalinsa ya kai ga Rafee'ah da ke kuka. Cikin sauri har yana tuntuɓe ya karasa.

"Ke lafiya?"

Ta dubi Muniru kafin ta faɗa jikinsa tana kuka. Ya ɗan tureta.

"Abba?" Abinda ya fadi kenan ya yi saurin nufar cikin asibitin. Hawaye kawai ya shiga fitarwa sadda ya ci karo da gawar Abban.

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Ya fadi a fili.


***
Kafin ka ce me, mutuwar shahararren dan kasuwan Alhaji Khalid ya karade garin Kano. Mutum ne mai jama'a kuma mai girmama mutane. Yana da saukin kai da tausayi ga gaskiya da amana.

Mutum ne mai son zumunci kwarai. Shakka babu an ji mutuwarsa ba kadan ba.

Jama'a da dama sun halacci jana'izarsa, mutanen Daura an zo sosai.

Aliyu ya girgiza matuƙa da mutuwar surukinnasa. Abban da ya ke yiwa kallon maƙiyinsa a baya kafin ya fahimceshi da kuma irin kaunar da ya ke yiwa Ramlatu. Bai mance nasihar da ya sha yi mishi ba a duk sadda zasu hadu ko kuma ya je gida. Adalilin faɗa da Ramlatu. Shakka babu ya tausayawa iyalinsa musamman Ramlatu dake kwance gadon asibiti har aka yi jana'izarsa ba ta san ina kanta yake ba.

***
Hasken rana ne ya tasheta daga nannauyan suman da ta yi, ta yi cak tana nazarin dakin da take. Tabbas gadon asibiti ne, ta dubi hannunta, ruwa ne ake ƙaramata. A hankali ta motsa.

"Sannu kin tashi?" Ta tsinci muryar Indo a gefenta. A hankali kuma ta gyada kai. Indo ta fita da zummar kiran likita kamar yanda ya ba da umarni. Firgigit ta mike.

'Abba! Ina Abba?' Ta yi tambayar da babu mai amsamata, ta fisge ruwan da ake ƙaramata ba tare da jin nauyin cikinta ba ta nemi hanyar fita.

Karo suka ci da likita, duk yanda Dr Sunusi ya so ta tsaya hakan ya faskara, a dole ya kyaleta suka wuce gida da Indo. Kuka take yi sosai don tuni ta gano abinda ke faruwa, ta yarda kuma yanzun cewa Abban ba ya duniyar nan da take ciki.

"Ya bar min duniyar, ya tafi ya bar ni da abinda na zaɓa sama da su. Ya bar ni nayi yanda na so. Shikenan babu sauran mai sona..."

"Haba Ramlatu, ki yi hakuri, ki dauki dangana. Kar ki manta kina da Allah, don ya karɓi abinda ya ba ki aro sai ki ce don me?"

Ta girgiza kai kawai. Indo ta ci gaba da ba ta baki. A nan take fadamata anan Aliyu ya kwana, ya je don kawo abin kari ne daga gida. Ba ta ce komai ba har Indon ta kira lambar da Aliyu ya sanyamata ta fadamishi sun wuce gidan.

A falon ta iske mata maƙil, ta karasa ciki har wurin Hajiyarta ta zauna. Nan kuma aka shiga yi mata sannu da gaisuwa, kawai ta rungume Hajiyar ta shiga kuka mai tsuma zuciya. Wannan ya kara yiwa Hajiya fami, ta shiga sharar hawaye. Su Zulaihat kam ba'a magana dama, idanun sun yi ja.

"Ba'a bar ni na ga Abba ba."

Ta fadi cikin sheshsheka.

"Sai hakuri Ramlatu, haka Allah Ya tsara. Allah Ya ba ki lafiya."

Ta kasa amsawa Hajja, dakyar aka lallaba ta yi wanka ta sha ruwan shayi.

***
BAYAN KWANA ARBA'IN

Har sannan Ramlatu na gidansu, su Zulaihat ma dakyar suka koma nasu gidajen sai da Yayan Hajiya, Kawu Dauda ya yi musu fada ba shiri suka tattara a kwana ashirin suka tafi. Ita kuwa Ramlatu ta kasa lekawa ko waje ballantana ta fita.

Aliyu kusan kullum sai ya zo, har abin ya soma isar Hajiya. Ta kira Bana Dakta ta mishi maganar. Da kansa ya nemi Aliyu suka je yin gwaji bayan ya ba shi hakuri ya fadamasa dalili.

Koda sakamako ya fito ya yi mamaki ganin Aliyun shima lafiya kalau yake, ya kara jinjina lamarin Allah. Ya tabbatar ajali ne kawai ya riski Abban ta wannan hanyar.

Washegari Baba Dakta da kansa ya zo ya tisa Ramlatu a gaba suka wuce ya kai ta gidanta. Ranar ta yi kuka kamar ranta zai fita sakamakon famin da hakan ya yi mata game da mutuwar Abbanta. Murmushi da dariyar Abban sun kasa gushewa a zuciyarta. Kalamansa na nasiha gareta daki-daki su ke faɗomata a rai, wannan kadai ma yana kara sanyata zubda hawaye. Komai na duniyar ya fice a ranta.

***
Zamansu da Aliyu ya sauya, ta koma wata shiru-shiru. Aliyu na shaye-shaye ko ba ya yi, ya zama ba damuwarta ba. Ta daina shiga hayaniya, ta daina shiga lamarin kowa da komai. Ummi har sannan ba ta dawo ba, tana wurin Hajiya.

Tana lura da yanda Aliyun ya chanja, yakan wuni a gida idan ya so, wataran kuma ya fita kasuwa. Duk yanda ya so ta saki jiki ya kasa. Koyaushe cikin kuka.

"Dana sani ban aureka ba, da na sani na bi zaɓin Abbana."

Abinda takan yawaita fada kenan wanda take sosa zuciyar Aliyun da shi. Shi kansa yasan ya mata rashin kyautatawar da ya ci ace ta yi nadamar aurensa, sai dai ko mene ne ai shima ya zalunci wata a dalilinta.

***
BAYAN WATANNI BIYAR

Cikin Ramlatu ya cika watanni tara. Abin da ya bata mamaki tun a wata na takwas Aliyu ya haɗomata komai da ta bukata na haihuwa, abu ne da ba ta zata ba. Zuwa sannan ta ɗan saki zuciyarta, addu'a babu ranar da ba ta saka Abbanta ciki duk sallah. Kulawa sosai suke ba wa Hajiya daga ita har ƴan uwanta. Kowannensu gudun ɓacin ran Hajiyar yake yi. Ɓangaren Aliyu kuwa, ta ga sauyi sosai don ga dukkan alamu ya bar shaye-shaye. Koda ya na yi ba ta taɓa kamashi a gidanta ba. Ba ta dai gajiyawa da yi mishi nasiha da tsoratar da shi game da rayuwa da mutuwa. Tana dai godiya ga Allah yanda ya soma chanjamata shi, ya soma shiga cikin ƴan uwansa, har Alkur'ani yakan dauka ya yi tilawar inda ya iya. Har a sannan ba su koma makaranta ba.

Ranar wata juma'a da rana Allah Ya taimaka Aliyu na gida, naƙuda ya kama ta. Suna zuwa asibiti ba tare da daukar tsawon lokaci ba ta haifo ɗanta namiji.

Sai da aka gyarasu ita da jaririn sannan Aliyu ya sanarwa jama'a. Hatta su Zulaihat sai da suka zo ganin jariri banda Hajiya.

"Wannan dai kamanninki ya dauka Ramlat." Cewar Rafee'ah tana dan murmushi, dukkansu har sannan ba su gama maido kumarinsu ba. Abba ne ya faɗomata a rai sadda aka haifi Ummi. Wani irin kuka ya kwacemata, tun suna cewa mene hakan? Har su ɗin ma suka shiga sharar hawaye. Kowannensu ya fahimci tunanin dan uwansa. Ganin yan uwan Aliyu sun soma zuwa ya sanya suka danne abinda ke zuƙatansu cike da jimami. A ranar aka sallameta ta koma gidanta. Abulle ce ta turomata wata dattijuwa da za ta taimaka mata da wanka na sati biyu.

***
"Mu sanya masa sunan Abba?" Ya fadi yana dubanta, ta kurawa yaron idanu kafin ta girgiza kai.

"Meyasa?" Ya fadi cike da mamaki.

"Saboda abubuwa da dama, ka yi hakuri ka yi mishi huduba da duk sunan da ya dace. Amma banda sunan Abba."

Ya ƙuramata idanu kafin ya jinjina kai kawai. Bayan ya kammala ya dubeta.

"Sunansa Ansar. Allah Ya rayamana."

Murmushi ta yi ta dauke kwallar idanunta na tunawa da Abban.

Haka suka ci gaba da rainon Ansar, ba'a yi taron suna ba. Suna cika sati biyu, dattijuwa Yaha ta tattara da goma ta arziki da Ramlatu da Aliyu suka hadamata ta bar gidan tana ta godiya.

Sai da suka yi wata goma cif suna yajin aikin makaranta tukunna aka koma.

***
BAYAN SHEKARA DAYA..

*Allah Mai iko akan kowane bawa, Shi kadai buwayi gagari misali. Mai shiryawa kuma Mai Rahma.*

"Zan bi ka Abba."

Ummi ke fadi har da kukanta, Ramlat dake zaune tana shayar da Ansar ta dubeshi.

"Don Allah Baban Ummi ka taimaka ka tafi da ita. Ba sai ka sauketa wurin Hajiyar ba? Magiyar ta isa."

Aliyu na gyara zaman hular kansa ya harari Ramlat kadan.

"Kin ji? Yarinyarnan dai nema take ta koma gidan Hajiya din din din, wato shikenan mu sai dai ta kawo mana ziyara ko? To na ƙi wayon, nima ina sonta kusa da ni."

"Anya ba ka fi son Ansar ba?" Ta fadi tana mai kanne mishi idonta guda. Ya ɗan daure fuska.

"Na hanaki tada abinda ya wuce ba kya ji Baby."

Ta yi dariya.

"Afuwan." Abinda ta ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login