Showing 57001 words to 60000 words out of 230725 words

Chapter 20 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1393

ba halinta ba ne!'

Faɗin wani sashi na zuciyarsa.

***
Awanni kaɗan bayan farfaɗowarta ya shiga. Ta ɗago idanu ta dubeshi sai ta soma hawaye.
  "Kaga abinda halinka ya jazamana ko?"
Ya zaune gami da riko hannunta.

"Laifinki ne, meyasa ba ki ɗaga wayata ba ina ta kira? Tunawa nayi na ajiye a fridge shiyasa na so na gargaɗeki."

Ta kauda kanta kawai, cike da bakin ciki. Abin kunya sanadin shaye-shayen mijinta, cikinta ya zube.
 
  "Kaicona." Ta furta a fili, sai kuka. Kewa, kewar iyayenta take. Don haka ta juyo ya dubeshi.

"Bani wayarka."

"Ki yi me?"

"Abbana zan kira."

Ya daure fuska.

"Ki ce mishi kin sha abin maye cikinki ya zube? Asirinmu za ki tona? Dama ya lafiyar giwa ballantana an jefeshi da kashi? Toh ki je ki gwada tona asirin namu. Naki ne zai fi wari, ni dama ba ganina suke da gashi ba."

Daga haka ya mike ya sa kai ya fice a zuciye. Ta bishi da kallo, wani malolon abu ta ji ya tsayamata a maƙogwaro. Tana jin haushin irin kalaman da Aliyu ke yi akan iyayenta. Ko ba komai iyayenta kuma su suka haifeta. Dole ta takawa abin burki.

'Kin manta ke kika bada ƙofa.' Cewar wani bangare na zuciyarta, hakan sai ya karyarmata da gwuiwa. Ta yi shiru ta soma hawaye. Tana jin haushi da tsanar kanta akan duk abinda ya faru tsakaninta da yan uwanta, a gefe guda kuma don Aliyu ya zama kamar bugun numfashinta wanda ba ta jin za ta iya rayuwa babu shi. Sai dai kuma hakan ba zai hana ta janyo ƴan uwanta jiki ba, ta dinga ziyartarsu koda ba su zo mata ba. Ta kudurta sauya takunta tun kan abu ya yi nisa.

***
  Sai da ta yi kwanaki uku aka sallameta daga asibiti. Shi ne lokaci na farko da ta ga matan mahaifin Aliyu a gidanta da sunan dubiya. Ba su kadai ba, har su Abulle da Mamar Muhibbat sun zo. Kana ganin fuskokin za ka san dole akai musu.

"Ikon Allah, kema dai ina ce ba shi ya jawomaki ɓarewar cikin ba?"

Cewar matar Malam (mahaifin Aliyu) ta farko, Atine.

"Wane zancen banza ne haka ke Atine? Wa kike nufi da ɓarar da ciki? Au dama sharrin da za ku yiwa Zakina kenan?"

Fadin Abulle cikin masifa. Wannan yasa Atine fadin

"Allah Ya ba ki hakuri Baba."

Abulle ta yi kwafa. Ramlat dai tana zaune ta dukar da kai a saman kujera don Abulle ta hanata zama ƙasa.

   Sun jima a gidan don har sai da Abulle ta saka yanmatan jikokinta su yiwa Ramlat girki a risho. Haka suka shiga suna kunkuni. Har gobe ba sa kallonta da gashi, Muhibbat ce tasu. A karshe kowa ya watse aka bar ta ita daya ta yi ta godiya kuwa.

Komawa ciki ta yi ta ga yanda suka yi kaca-kaca da kicin din, ta kuma sani da biyu suka yi hakan. Haka ta daure ta kimtsa ko'ina. Tana jin sadda Abulle ke cewa Zalihat diyar Atine ta zauna ta kwana biyu yarinyar ta yi kememe uwarta na turata ta fice ta shige mota. Murmushi ta yi mai ciwo. Ta dauki waya cike da so da kewar iyayenta ta dannawa Hajiya kira. Ringing uku ta ɗaga da sallama.

"Hajiya." Ta fadi a raunane zuciyarta a karye.

Daga dayan bangaren Hajiya ta ji gabanta ya fadi, ta daure. Kwanakinnan da tunanin Ramlat take kwana da tashi. Tun sadda aka ce ta yi ɓari ta kira Zulaihat da Rafee'ah akan su shirya su je. Yanzu kam sun amince zasu je bisa umarninta.

"Ramlatu, ya gida? Ya jikinnaki?"

Wani sanyin dadi ya saukarmata a zuciya. Yau ne karon farko da Hajiyar ta kira sunanta ta kuma bata kulawar da ta dace.

"Jikina da sauki Hajiya. Hajiya yaushe za ki zo? Ki yafemin don Allah Hajiyata."

Kukan da take riƙewa ta shiga yi.

"Hajiya kin yi shiru. Hajiya ki yafemin."

"Na yafemaki Ramlatu, na yafemaki duniya da lahira. Ki kwantar da hankalinki. Ki bi mijinki, Allah Ya yi maki albarka. Gobe yayyanki zasu zo."

Rasa kalar farin cikin da za ta yi ma ta yi. Sai ga ta nan tana dariya. Suka yi sallama da Hajiyar ranta fari sol. Ta ɗago kai kenan ta hada ido da Aliyu. Yana jingina kansa cikin bangon falon yana zuƙar taba da fesarwa. Ganin ta kammala wayar ya tako ya zauna gefenta.

"Su waye zasu zo?"

Ta mance da batun wani sigari ko warinsa, rungumeshi ta yi sosai cike da farin ciki ta amsa.

"Tayani murna, Hajiya ta yafemin, ga Anti Zulaihat da Anti Rafee'ah zasu kawomin ziyara gobe."

Ga mamakinta sai ta ji ya ja tsaki. Ta ɗago tana kallonsa.

"Da yake ba ki da zuciya ko? Duk irin rashin kaunar da suka nunamana akan wani banzan Hilal bai ishemu ba? Wane irin kalamai ne ita Zulai din ba ta ce a kaina ba? Ita kuwa Rafee'ah wato tsabar tsana har.."

"Ya isheka! Ya isheka!!" Ta tsinci muryarta da fada, bakinta da kakkarwa, jikinta da rawa. Ta miƙe tsaye kyam da ƙafafunta. Idanunta a rufe cike da masifa! 

Kallonta kawai yake yana zuƙa da fesarwa, maimakon ɓacin rai, murmushi yake, murmushi sosai har da dora ƙafa daga saman Centre Table.

"Ƙarya nayi?"

Shi ne abinda ya furta.




 I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/xcmnTANK99


🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

18)

"Nace ƙarya na yi?"

Ya kara maimaita tambayarsa ganin ga tsaya cak tana kallonsa. Sai sannan ta kauda idanunta daga kansa.

"Ya isheka! Aliyu ya isheka! Ban raina iyayenka ba, ban taɓa faɗar kalma marar dadi a kansu ba, kar ka fara da nawa. Kar ka koyamin. Ba zan dauka ba. Ko ba komai sun haifamaka ni."

Wata dariya ya yi kafin ya kashe sigarin a karamin farantin tasar Ramlat din da ya mayar na kashe taba.

Miƙewa ya rungumeta tana kaucewa.

"Sorry Baby, Allah Ya ba ki hakuri. Ba zan ƙara ba."

Ta zame jikinta kawai ta nufi daki. Dakyar ta sauko ta bar fushin ganin yanda ya ke lallaɓata kuma ta san kwanan zancen sai dai dole ya hakura don ba dama.

***
WASHEGARI

Tun zamansu a falon suke kallon ko'ina gami da taɓe baki.  Can kuma Zulaihat ta dubeta.

"Matar Aliyu, ya jikin?"

Ba ta son suna kiranta da wannan sunan, ta fi kaunar Ramlat din da aka yankamata rago da shi, sai dai furta hakan tasan wata baƙar maganar za ta ƙara tofamata, don haka ta haɗiye ɓacin ran ta yi yaƙe tana ɓarewa Khalifa ledar alewa.

"Jiki da sauki. Na warware. Yau dai Allah Ya yi kun zo min."

"Yanzun ma don kin haɗamu da uwarmu ne, gudun ɓacin ranta ne ya kawomu gidanki. Kinsan ba duka aka taru aka zama ɗaya ba."

Fadin Rafee'ah kenan wacce dama tun ɗazun take ba Daddy nono tana wani jijjiga ƙafa. Murmushi Ramlat ta yi.

"Kowa dai da irin kaddararsa."

Tsaki Rafee'ah ta ja, ita kuwa Zulaihat ta yi dariyar rainin wayon Ramlat.

"Allah Ya kyauta, Ramlat baki abin magana."

Ta yi murmushin da bai kai ko'ina ba.

Duk a zatonta zuwan yini suka yi mata, ashe ba haka ba. Duka-duka basu fi mintuna talatin ba suka miƙe. Baki sake ta ke dubansu.

"Wai ba dai tafiya ba?"

"Ah, me zamu zauna mu yi? Ko an fadamaki namu mazan ba sa sonmu suka bari muka zo?"

Zulaihat ke fadi sa'ilin da take gyara zaman mayafinta.

Idanunta suka cicciko da kwalla.

"Don Allah ku tsaya ku ci abinci, wallahi na yi girki kuma idan ba ku ci ba zai iya lalacewa."

Tausayinta ya ɗan tsirga Zulaihat, ko ba komai kanwa ce garesu, ta lura babu wani ƙiba na amarci da Ramlat ta yi face rama. Hasken fatar ma ta tabbatar ma cuta ne.

"Ke kika san wannan, nikam muje Sis. Baban Khalid bai ce na jima ba, kuma kinsan zai dawo daga Gusau."

Zulaihat ta koma ta zauna.

"Mintinan kadan zamu ƙara Rafee'ah, yi hakuri mu ci abincin. Yunwa nake ji dama."

Ta fadi ne kawai don Ramlat din ta ɗan ji sanyi ganin har ta soma hawaye. Guntun tsaki Rafee'ah ta ja don ita ba ta son ma tuna cewar a gidan Aliyu da Ramlat take.

Ganin haka da sauri Ramlat ta faɗa kicin ta shiryo musu lafiyayyan jellof din shinkafa da taliya da ta girka musamman domin su, ya ji alayyahu da kifi. Cima ce da ta san suna masifar so musamman idan Hajiyarsu ce ta girka da busasshen kifi. Tun kafin ta ƙaraso ƙamshin ya bugesu. Rafee'ah na zaune tana buga game  wayarta, Zulaihat kuwa ta kwashi gara suna hira. Ana cikin haka, sai ga Amrah ta kira. Daga makaranta takanas ta taho dubiya. Cike da farin ciki ta yi kwatance, ta leka ta tarbota a gate. Ita kanta ta yi mamakin ganin su Rafee'ah a gidan.

Wannan shine taimakon da Ramlat ta samu, abincin ya ƙare tas sai wanda zasu ci ita da Aliyunta. Zuwan Amrah ya daukemusu hankali aka shiga hira sosai, sai dai Rafee'ah na kaucewa hirar da za ta haɗata da Ramlat din.

***
Shaf ya mance da batun wasu baƙi, abu ne da ba'a saba ba. Ya saba ya wuni kasuwa ya dawo ya riski matarsa ita daya. Kusan ma a fusace yake, mashin dinsa a waje ya bar shi, wayar da abokin kasuwancinsa Nabil ya mishi ita ta ƙara fusatashi. Shikenan ba dama ka ranci kuɗaɗen mutane sai su takura maka a waya. Ya ci alwashin cika abinda ya yi niyya yau, ya tabbatar hakan zai ba shi ribar da zai maida bashin ya kuma kashe wata matsalar.

"Dalla malam nace maka gobe zan ba ka kudinka! Dan ....uwarka ka rabu da ni!"

Jin abinda ya ce, Nabil ya fusata shima ya shiga surfa mishi ashar. Shima bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya hau ramuwa har ga shigo cikin falon. Idanunsa sun rufe bai ko lura da mutanen da ke zaune ba.

Gaba daya idanunsu yana kansa, Ramlat kirjinta ne ya shiga bugu da sauri.  Wani irin ashar yake ƙundumawa kamar tsohon ɗan tasha. Zulaihat ta dubi Rafee'ah kafin ta maida dubanta ga Ramlat wacce ke jin kamar ƙasa ta buɗe ta nutse a wurin. Ta saci kallonsa, ya gama wayar ya zaro lighter daga aljihunsa, sanin me hakan ke nufi ya sa Ramlat saurin miƙewa gami da ƙarasawa inda yake.

"Sannu da zuwa. Muna da baƙi fa."

Ta furta murya na ƴar rawa. Sai a lokacin ya san da ita a falon, ba ma ita din ba, ya ankara da mutanen da ke zaune. Mutanen da ya kira da maƙiyansa. Kallon da ya watsamusu kallo ne na raini, kafin ya maida duba ga Ramlat cikin halin ko'in kula.

"Sai me? Inace ke suka zo dubawa? Me zan musu? Ai wanda ke yi da ni, da shi nake yi. Mtsw."

Ya ƙarashe da tsaki ya yi ciki, ta daskare a tsaye, ta kasa koda juyowa ta dubesu.

Rafee'ah a fusace ta mike tsaye ta ja zanin goyon Daddy ta saɓeshi.

"Sai ku tashi mu bar gidan. Gobe idan an ƙara ganin ƙafarmu a yi mana fin haka. Dama wane mutunci ko karramawa za'a samu wurin wannan mutumin?"

Rafee'ah ke maganar a fusace, ba ta jira komai ba ta fisgi gyalenta daga saman kujera ta ɗauki jakarta ta yi gaba.

Ita kuwa Zulaihat jiki a sanyaye ta mike tana ƙara maimaita Allah Ya kyauta kamar wani karatu. Ita abin dauremata kai ya yi da kuma mamaki. Bangaren Amrah kuwa, itama miƙewa ta yi ta hau gyara zaman ɗankwalinta da ya sunce. Sannan suka kama hanya.

Ramlat ta juyo tana dubansu, sai a sannan ta yi yunkurin magana ta karasa da sauri ta tsayar da su.

"Don Allah ku yi hakuri. Wallahi ransa ne a ɓace. Ba haka yake ba, ku yi hakuri don Allah."

Wani murmushi Zulaihat ta yi.

"Ai ba ke kika yi mana ba, mijinki ne. Kuma ko ba komai gidansa muka zo, kinga ko shari'a ta kayar da mu. Koma ciki kawai, ma yi waya."

Tana kuka kuma tana ji tana gani suka kama hanya. Ta riko hannun Amrah.

"Sakarni don Allah Ramlat, ma haɗu a makaranta. Ko me ya faru ke kika ja. Ke ce silar komai. Ke kika bada ƙofa aka daina ganin naki da mutunci."

"Abu ba zai wuce ba Amrah?"

Maimakon ta samu amsarta, sai Amrah ta kwace mayafinta ta ja hannun Khalifa suka bi bayan su.

Rafee'ah tuni ta yi waje, tana tsaye tana jijjiga Daddy dake kuka, ita kanta hawayen take fitarwa, hawayen takaicin Ramlat. Tana ganin Zulaihat ta dubeta.

"Me aka gujemata tun farko? Dama ai wanda bai ji bari ba zai ji hoho. Me dama za ta samu a wurin mashayi idan ba irin hakan ba?"

Zulaihat ta mata ido ganin Amrah ta taho, sun dauki sirrin shan sigai da kayan mayen Aliyu matsayin sirri da ba kowa ne ya sani ba. Suna jin kunyar Amrah ta ji sai dai kuma basu da masaniya itama tana da labarin waye shi. Haka suka dunguma gwuiwa a sake su ka bar unguwar Rafee'ah ma faman mita. Zulaihat itama tana kiran sai ta faɗa wa Hajiya.

"A'a Anti don Allah kar ku yi haka. Ko don Abba, kar fa ku manta har yau Abba na kan shan maganin hawan jini. Don Allah kar ku jefasu cikin damuwa. Ramlat ai ba ta je ta faɗa ba, kuma da alama mu din ne bai son gani a gidansa saboda ta riga ta nunamasa bama ganinsa da ƙima da mutunci. Shirun zai fi zama alheri ga su Hajiya."

Amrah ke maganar a tausashe. Sun fahimci manufarta, don haka suka yi na'am da hakan. Sai dai kowa zuciyarsa ba dadi.

***
  Kai tsaye ɗakin ta shiga da hawaye caɓe-caɓe saman fuskarta. Abinda idanunta ya gane mata ne ya sanya ta sakin baki ta haɗiye kalamanta. Sif din kayanta ya bude ya fiddo karamin akwatin sarƙoƙinta yana bincikawa. Wani dan gida wanda ta sanya auduga ta saka gwal dinta na wurin Abba a ciki shi ya fiddo. Sai wani set na gwal din da ya siyamata. Da sauri ta karasa ta fisgesu.

"Mene haka? Me kake nufi?"

Kallonta ya yi  fusace.

"Me nake nufi kike tambaya? Siyarwa zan yi! Kudi nake so! Bashi ya min yawa, shagona kaya sun tasar ma ƙarewa, ko so kike ku rasa komai ne?"

Zuciyarta na wani irin tuƙuƙi ta shiga girgiza kai.

"Wallahi ba za ka siyarmin da zinaren da Abbana ya siyamin ba. Ko wanda ka siya  ai ya tashi daga naka, nawa ne. Don haka ba ka isa na ba ka ka siyar ba. Anya Aliyu kana cikin hayyacinka kuwa?"

Hannu ya fidda ya ɗauke ta da mari Wanda ya yi sanadin zubewar gidan sarƙar, suka tarwatse a ƙasa.

"Bayan laifin da kika yimin na kawomin tumakai cikin gida, hakan bai isheki ba sai kin kirani da mahaukaci?! Sarƙa kuma naga shegen da zai hana na siyar, idan kuma ubanki ne ya bani kudin na siyamaki sai ki faɗa!"

Tana kuka ta shiga tattarawa ta dunkule a hannunta, ya shiga kokarin kwacewa.

"Ba za ki saki ba? Wallahi zan miki dukan kawo wuƙa yanzu!"

Ya ƙarashe gami da kai mata naushi a ciki. Ƙara ta saki, kafin ta ce.

"Shikenan! Zan ba ka naka ka siyar amma wallahi banda na wajen Abba."

Bai ko saurareta ba sai da ya kwace duka, zai fita ta rike ƙafarsa, wani harbin ya kai mata da ya samu bakinta, nan da nan ya kumbura ya soma fitar da jini.

"Kar ka yimin haka! Ai Abbana ya siyamin shima! Ka bani na wajen Abba!"

Ta miƙe a guje ta bi bayansa har harabar gidan, zai fice ta rike rigar gam tana kuka. Ya tureta, ganin ta ƙi sakinsa ya sanya a aljihun gaban rigarsa ya hau kai mata duka yana ashariya. Kira yake ita ce silar karyewar arziƙinsa.

"Banza mai farar ƙafa! Ba abinda ubanki ya ban da na aureki ai. Shi waye da ba za'a ci arziƙinsa ba!"

Wani karfi ne ya zo mata, ta kama hannunsa ta ciza iyakar ƙarfinta. Jin zafin ya ratsashi ya finciketa ya kai mata mari ga ci gaba da narka tana ihu. Yana ji ana kwankwasa gidan ya ƙi budewa. Sai da ya mata lis sannan ya bude ya dubi makwafcinsa dake tsaye.

"Aliyu lafiya? Hayaniyar me nake ji?"

Wani banzan kallo ya watsamishi kafin ya fito gaba daya ya rufe kofar gam!

"Malam ba matsalarka ba ce, wannan hurumina ne da iyalina."

Daga haka ya hau mashin ya tayar ya fice. Ramlat jikinta ya yi mugun tsami, ta kudurta a yau ba za ta kwana gidan Aliyu ba. Haka ta daure ta mike tana ɗingishi ga fuska a kumbure ta nufi ciki. Dogon hijabinta ta zura sannan ta dauki wayarta da purse dinta wanda ta tabbatar akwai kudi a ciki ta fita.

Sa mukullinta ta yi amfani ta bude gidan, kai tsaye gidansu ta nufa. Ɗan sahu na kallonta ta madubi tana kuka, ya tausayamata don daga gani an san duka ta ci.

Har kofar gidan ya sauketa. Ta fito ta karasa, cak kuma ta tsaya tana kallon kofar gidan. Tunani take ta shiga ko kar ta shiga, yanzun ne ta tuna da komai, yanzun ta tuna da irin rabuwar da aka yi. To amma ya za ta yi? Su kadai ne tilas dinta, don haka ta shiga kwankwasawa. Malam Musa ya leƙo, ganinta sai ya hau mamaki. Ga fuska duk a kumbure.

"Hajiya Ramlatu, kece a tafe? To .."

Ya bata hanya da sauri, ba ta tsaya ko gaidashi ba ta tambaya ko Abba na gida. Ya tabbatarmata yana ciki.

"Kwana biyun nan bai fiye fita ba saboda yanayin jikinsa da ya motsa."

Ta dubi Malam Musa da hawaye saman fuskarta.

"Meke samunsa?"

Cike da tausayi ya amsa.

"Kamar dai naji Babban Yaya na cewa hawan jininsa ne ya motsa. Amma da sauki ai."

Ta yi shiru, ba za ta iya tunkarar Abbanta da abinda zai kara dagula lissafinsa ba, ta dubi gidan nasu. Wasu hawaye masu ɗumi suka zubomata. Shikenan ba ta da cikakken ƴancin zuwa gidansu kamar sauran ƴan uwanta? Ba za ta zo ana murna da ɗokin ganinta ba?

A hankali ta sauke ajiyar zuciya, ta juya ta fita.

"Ya za ki tafi? Ya kamata ki shiga ciki Ramlatu, dubi yanayin da kike."

Tasan yanayin bai wuce na dukan da ta ci ba, har wani dan jiri take ji. Ko a islamiyya ba'a taɓa yi mata irinsa ba. Ta yi murmushin yaƙe ta girgiza kai. Dakyar ma take iya ganin fuskar Malam Musa saboda ruwan hawayen da suka taru a kwarmin idanunta, jan majina ta yi.

"A'a ba zan iya shiga na tayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login