Showing 219001 words to 222000 words out of 230725 words

Chapter 74 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1086

ƙafa ba.

Aikuwa hukuncin da ya dauka a kanta mai tsauri ne don har makaranta ya ce ta zauna sai ya yi magana sannan ta ci gaba da zuwa, amma fita dai ko nan zuwa farfajiyar gidan ce ya hanata. Ya kuma rantse muddin ta kara gangancin yin waya da Taheer sai ya saɓa kamanninta. Da wannan bakin cikin ya bar Hafsat ya fice abinsa.

***
NIJAR-KANO

Sun ɗau hanya miƙaƙƙa daga Maradi don dawowa Nijeriya, garin Kano. Zuƙatan kowannensu farin ciki ne marar misaltuwa, duk da irin wata azaba da su ke ji a tsakanin mazaunansu, hakan bai sa sun kasa yin murnar samun nasara ba. Kowaccensu ta matse kwalin aikin da ta karɓo a ƙasan ƙafafu, idan kuwa wuri ne mai gargada, sai su yi maza su riƙe dakyau a hannunsu. Har suka isa Kano tulun nan yana matse da su.

  Gidan Hajiya Zeenatu aka soma zuwa, suka rabu da Hajiya Batool direba ya yi gaba da ita. Ma'aikatan na ta kallon Madam din tasu riƙe da kwali, abinda suke ta tunani bai wuce ko meye a cikinsa ba. Ita kuwa tana shiga ɗakin ta samu wuri mai kyau ta killaceshi. Yanzu gaba daya tunaninta shi ne na tafiya Adamawa a gobe-gobennan, don ta fi son komai ta yi shi da gaggawa sai dai kuma yanda ta ke jin bayanta naaa azabar da radadi da ciwo, dole sai ta ji sauƙinsa. Don haka ba ta zauna ba, bandaki ta shiga ta haɗa ruwan ɗumi. Sai dai koda zamanta wani uban ƙara ta saki na azaba. Ranar dai wuni ta yi jiki ba dadi don har da su zazzaɓi. Haka ta samu labari daga Hajiya Batool, ita kam har wani ruwa ta ke fitarwa.

Wasa-wasa zazzaɓi ya tsananta ga Hajiya Zeenatu, har washegari da ta ke fatan tafiya Adamawa, abin ya gagara. Dakyar ta iya daukar waya ta kira likitanta. Har gidan ya zo ta kira Emma a waya ta ba shi iznin a shigo da shi. Ya karasa har dakinta,  ya yi mata allura. Koda wasa ba ta bari ya san ɗaya ɓangaren na ciwonta ba, yana kammalawa ya fice abinsa. Aikuwa wani wahalallen bacci ya yi awon gaba da ita.

Ta fi awa hudu tana bacci, kafin ta farka, ba laifi ba kamar sadda ta kwanta ba, kusan ma babu zazzabin sai uban gumi da ta ke yi. Wayarta ta jawo, ta bude rututun missedcalls da ta gani na Manajanta mai kula da shagon gwal-gwalanta. Kafin ta gama shanye mamakin, wani kiran ya ƙara shigowa. Ta ɗaga da saurinta.

"Hello! Hajiya, gobara! gobara ta cinye shaguna har da namu! Ga wuta har yanzu an kasa tsayar da ita!"

Daga jin yanda ya ke zancen a matukar rikice ya ke don ba laifi shima yakan haɗa da nasa jarin ya juya. Wani irin miƙewa tsaye da Hajiya Zeenatu ta yi, sai ga ta a kan ƙafafunta, jikinta ko'ina ya ɗauki rawa, shi kenan dukiyar da ta ke taƙama da shi yanzun kaɗai a duniya.

"Me ka ke cewa Bala? Me kake nufi wai?!"

Inaa! babu kwakkwarar amsa, tana ta hello amma kamar babu service ga kuma hayaniyar jama'a ta cika wurin. Ai ko mayafi ba ta tsaya ɗauka ba, mukullin motarta kawai ta ɗauka ta fito hankali tashe. Ma'aikatan na ganinta suka nufota.

"Hajiya lafiya?"

"Ba za ku gane ba! Yi sauri budemin gate! Gobara a sabon gari!"

Hakan da ta fada duk sai suka fahimci inda zancen ya dosa tunda duk sun sani tana da shago a sabon gari, wato dai an samu matsala, da sauri Emma ya karbi mukullin ya ce ta bari ya kai ta ba ta da nutsuwar yin tuƙi. Ba musu ta miƙa masa jiki na rawa ta koma mazaunin kusa da direba. A hanya kamar za ta yi tsuntsuwa, duk irin gudun da Emma ke shararawa ba ta gani. Tuni ta nemi ciwo ta rasa.

Cunkoson ababen hawa da na yan sanda har ma da motocin kashe gobara, ya sa dole Emma sai wuri ya samu ya ajiye motar suka karasa da kafa. Hajiya Zeenatu na ganin yanda shagon ya ƙone ƙurmus babu abinda ya bari kawai sai ta faɗi yanke jiki ta faɗi. Nan fa mata da maza aka yi kanta, bakinta tuni ya karkace tana fidda yawu, idanunta kuwa kamar mai harara garke. Emma da ma wasu aka taimaka wurin daukarta zuwa asibiti, Manaja ya yi danasanin kiranta a waya sai dai hakkinta ne ta sani. Kusan ma akwai wadanda sai da suka sume, wasu kuwa banda kuka ba abinda suke yi kama su yi hauka.

Asibiti kai tsaye Emma ya wuce da Hajiya Zeenatu cike da tashin hankali, Likitan dai da ya zo mata dazun, Dakta Salisu, wurinsa suka je. Ya yi matukar mamakin ganinta a cikin wannan yanayin, anan Emma ya labartamasa komai. Nan da nan likitoci suka rufu a kanta sai dai kuma  sun makaro, Hajiya Zeenatu an samu ta ɗan dawo daidai amma fa ta hadu da shanyewar ɓarin jiki hakanan tana magana a jagwalgwale miyau na kwaranya ta gefen bakin. Banda hawaye ba abinda ta ke yi, ba abinda ke yawo a ranta sai kudirinta na zuwa Adamawa. A yanda ta ke jinta, ko a wane hali ta ke sai ta je. Sai ta samu Hussein ko ta halin ƙaƙa.

Nan kuma Dakta Salisu ya ba Emma umarnin sanarwa mijinta da yan uwanta, Emma nan take ya sanarmasa cewa Ogansu ya rabu da ita. Dama kaf dinsu sai da ya bisu da alheri kuma ya yi musu sallama da zummar ya tafi kenan. Ba su ji dadin hakan ba amma sun mishi murnar rabuwa da muguwar mata irin Hajiya Zeenatu, ko ba komai sun jima da sanin munanan ɗabi'unta da yanda Ogansu ke shakkarta.

Ba wacce ta fado a ran Emma sai Hajiya Batool, ya san matar aminiyar Madam ce, don haka ya fice daga asibitin ya nufi gidanta.

   Hajiya Batool na zaune tana jin wani mugun farin ciki yanda ɗanta ya kira waya yana sanarmata da cewa a gobe-gobennan zai taso saboda kewarta da ta cikashi, kuma a shirye yake da bin umarninta, dama ita kiranye aka bata, kuma har gshinan kwalliya ta biya kudin sabulu, ta kuma ci burin dole ta sanya ya saki Fa'iza ya auri wacce take so.  Ta kira wayar Hajiya Zeenatu ya fi a ƙirga don ta ba ta labari amma ba ta samunta, karshe ma ta ji wayara kashe.

Tana shirin sake gwada kiran, sai ga Mai aikinta ta shigo tana sanarmata da batun zuwan Emma daga gidan Hajiya Zeenatu. Nan ta bada umarnin ya karaso, Emma bayan sun gaisa ya fadamata halin da Hajiya Zeenatu ke ciki. Hankalinta ya tashi ba kadan ba, ta kaɗu sosai. Ba shiri ta ce ya je za ta leka asibitin. A yammacin ta je, ta yi mamakin yanayin da ta riski aminiyarta a ciki.

"Zeenatu! Ke ce haka?"

Hajiya Zeenatu sai ido da kuma hawaye. Da harshenta wanda maganar ba ta fita sosai ta ce.

"Ni..ce. Batool ki kai ni wurin Hussein."

Hajiya Batool ta girgiza kai ta riko hannunta.

"Ki bari ki warke, ki nutsu kiyi zamanki a asibiti a dinga yi maki magani tukunna. Zan turo Dije ta dinga tayaki zama, za ki warke. Da kafarki za ki je wurin Hussein."

Hajiya Zeenatu dai sai hawaye, a ranta kawai bakin cikin abinda  ya faru ta ke ji, da ace ta san hakan za ta faru da tun farko ba ta amsa wayar Manaja ba balle ta je kasuwar. Ji take inama ta kama hanyar Adamawa. Ta kara kallon Hajiya Batool dake ba ta labarin dawowar da ɗanta zai yi, haka kawai maimakon ta tayata farin ciki sai ta ji hassada da kishi sun kama ta, wato aikin Hajiya Batool har ya yiwu ita kuwa babu ɗaya da ta aikata, don aikin tulun ba zai yi tasiri ba sai ta je ta barbaɗawa Hussein hodar da Buzu ya ba ta. Haka tana ji tana gani Hajiya Batool ta fice daga asibitin gami da jadddamata za ta turomata Dije. Ita dai Hajiya Zeenatu gyada kai kawai ta yi, a yau ta ji takaicin rashin ajiye ƴar aiki mace da ta yi.

***
  ADAMAWA

Baƙin Kano sun sauka lafiya a family house, suka yada zango a ɓangarensu, wannan karon ma an musu tarba sai dai ba kamar yanda aka saba ba. Kawu dai jikinsa duk ya yi sanyi, a ranar da yammaci ya tara manyan dattawan gidan maza da mata yana kuka yana roƙar gafararsu.

"Sharrin shaiɗan ne, ku yafemin domin Allah. Itama Aminar da yaran yanzu zan je na nemi afuwarsu."

Kowa kam ya yi farin ciki da jin hakan,  ko ba komai har da rashin nadamarsa ne ya ba mutane haushi. Nan dai bisa jagorancin wani ɗan uwan Babansu, Surajo, tsoho mai ran ƙarfe, suka ɗunguma har iyalin Kawun, a yammacin zuwa gidan Dada.

***
Kwance yake saman doguwar kujera, yayinda ta ke kwance saman kirjinsa. Sai cuku-cukun miƙewa ta ke yi sakamakon raɗan da ya ke mata a kunne amma hakan ya gagara. Ta ko'ina ya matse ta gam! Ai kuwa bai yi aune ba, yana kai bakinsa saitin nata, ta yi azamar kama leɓensa na ƙasa ta ciza. Bai san sadda ya sake ta ba gami da kama baki.

"Aush!"

Ramlat na dariya ta mike, daga ita sai riga sky-blue marar nauyi, da kaɗan ta wuce gwuiwarta. Gashinta wanda tuni ta warware kitson yana tufke a baya.

"Sorry." Ta fadi tana ɗaga yatsunta bayan ta ja baya sosai tana dariyar mugunta. Hussein ya lashi leɓensa ya manna mata harara.

"Zan kama ki, yau ba mai kwatar ki."

Ta narkar da fuska.

"Haba don Allah Haskena, kai ɗin ne ka ƙi hakuri ka bari na kammala girki. Nikam kana sane ka ce sai wani satin za ka fara zuwa aiki. Don.."

Ganin ya yi wani irin miƙewa ya na kokarin cafkota ya sa da wani irin gudu ta shige kicin ta rufe tana dariya. Ya jingina jikin kofar.

"Za ki fito ki same ni, na san maganinki."

Murmushi kawai Ramlat ta yi mai bayyana haƙora ta ƙarasa wurin tukunyar miyarta, ba don na wutar kaɗan-kaɗan ta ke ci ba, ta tabbatar sai ya ƙone.

Shi kuwa gogan yana shirin komawa ya zauna, aka kwankwasa ƙofar falon da sallama. Ya amsa da ba da umarnin shigowa.

Hafsat ce, gaba daya jikinta a sanyaye. Ya dube ta fuska a tamke don har lokacin bai gama saukowa daga fushinta ba. Ta gaida shi ya amsa ciki-ciki.

"Dada ce ke kira."

Ya gyaɗa kai kawai ita kuwa ta miƙe ta fice kirjinta na dukan tara-tara. Tana tsoron abinda zai biyo baya idan ya ga waɗanda suka zo gidan. Sanin halin zuciya irin nasa ne yasa Dada kiran AlHassan a waya akan ya zo gidan bayan ta mishi bayanin komai. Wannan yasa ba ɓata lokaci, AlHassan ya kamo hanya don ba tazara sosai tsakaninsu.

"Heart, bari na je Dada na kirana. Kinji ko?"

"Toh."

Ta amsa ba tare da ta buɗe ƙofar ba. Ya gyara zaman brown tshirt dinsa ya zura silifas dinsa baƙaƙe na maza na yawo a gida ya fice. Tun a farfajiyar gidan ya ci karo da motoci, wannan ya ba shi mamaki ya tabbatarwa kansa baƙi suka yi, amma daga ina? Shi ne tambayar da babu amsarta a yanzun. A ƙofar falon ya ci karo da takalman maza da mata. Haka kawai ya ji gabansa ya fadi da sauri kuwa ya karasa ciki da sallama. Idanunsa bai sauka kan kowa ba sai a kan mutumin da ya fi tsana nan duniya zaune kusa da Dadarsa su na kuka. Ya fahimci komai, ya gane kuma Dada ta sauko ta yarda da dukkan ƙarairayin da ya shiryamata don haka shi ba shi da bukata. Tsigar jikinsa gaba daya ta tashi tsabar ɓacin rai, yayinda idanunsa suka kaɗa, ya ƙaraso ciki da zummar ƙarasawa kai tsaye ga Kawun ya shaƙe wuyansa babu ko tunanin yaransa da ke zaune a falon. Da sauri Baffa Surajo ya mike ya shiga tsakani. Ganin girma da cikar haibar dattijon mai tsananin kwarjini ya sa shi kasa ƙarasawa sai hawaye da suka shiga zubowa kawai daga kwarmin idanunsa.

"Me ya kawo shi nan?"

Baffa Surajo ya dafa kafaɗar Hussein kafin ya ja hannunsa ya bishi suka zauna saman kujera dakyar. Hussein banda girgiza ƙafa ba abinda ya ke yi yana hararar inda Kawun ya ke, ganin haka Baffa ya riƙe ƙafar.

"Ya isa ɗana. Ya isa."

Kawu ya taso zai ƙaraso inda Hussein ya ke, da wata irin tsawa ya dakatar da shi.

"Kar ka sake ka ƙaraso nan! Kar ka yi wannan gangancin!"

Daidai da shigowar AlHassan da sallama, ya kalli mutanen falon ya kuma dubi Hussein mai magana ya sauke ajiyar zuciya. Ya san dama hakan za ta iya faruwa, bai ma yi tsammanin zuwan wannan ranar nan kusa ba, sai dai Allah ne Mai shiryarwa.

Ya karasa ya gaisa da Baffa Surajo da matan Kawu har ma Kawun. Ya koma gefe ya zauna gefen Hussein.

"Ka yi hakuri mu ji ta bakinsa, ya riga ya zo kuma da iyalinsa baki daya, ka tuna, idan shi ne ya yi mana laifi, iyalinsa ba su da laifi tunda shi ne shugabansu."

Da kalamai irin haka Baffa da AlHassan suka taushi zuciyar Hussein. Ya yi shiru bai kara magana ba, wannan ya ba Kawu damar soma magana cike da jin wani tsananin kunya, wato wannan a duniya kenan ma, ina ga na lahira? Allah Ya tsaremu.

"Ku yi hakuri, ku yafemin. A ƙiyayyar da na nunamaku har da sharrin zuciya da shaidan. Na sani, Innarmu a baya ita ce kan gaba wurin ƙara rura wutar ƙiyayyarku a zuƙatanmu,  sai ya kasance ni abin ya zame min ciwo domin kuwa ya juye zuwa hassada da tsana. Ban ƙara jin tsanar Amina da Aminu ba, sai bayan auren Amina da mutumin da nake ganin ban kama ƙafar arzikinsa ba. Wato dai Marigayi Naziru, ban kuma gama farfadowa daga wannan bakin cikin na ci gaban da Amina ta samu ba a rayuwa, sai ga Aminun da muke tunanin ma ya mutu, ya dawo. Tun kan ya zo Kano wurina, labari ya riskeni, na yi bakin ciki sosai, Karime kanwarmu ta fadamin da murnarta ni kuwa ban ga abin murna ba a dawowarsa musamman da naji labarin ai rayuwa ta mishi kyau ya dawo har da matarsa da kuma yaransa ƴan biyu. A wannan halin sai ya kawomin ziyara duk kuwa da tarin kiyayyar da nake mishi, sai dai na gasamishi baƙaƙen maganganu wanda har ya mutu a lokacin ban yi dana saninsu ba sai ma dadi da naji a lokacin ganin ya bar min filin duniyar na ci karena babu babbaka."

Kawu ya numfasa saboda kukan da ya shaƙe shi, iyalinsa da su Dada kuka suke yi cike da mamakin irin wannan salon ƙiyayyar da bawan Allahn ke yiwa ɗan uwansa na jini. Shi kuwa Hussein ba zai ce ga yanayin da yake ciki ba, sai dai ko kallon Kawun ba ya son yi.

Kawu ya ci gaba da magana bayan ya sharce majina.

"Bayan shekaru da dama, a wani ziyara da Amina kika sa Husseini ya kawomin, lokacin ya samu hutun karatun da yake yi a Dubai. A wannan zuwan ne yaron ya ban tsoro har nake ganin nan gaba zai iya cin mutuncina a gaban ko su waye. Saboda tunda nake da ke da Aminu, babu wanda wuyansa ya taɓa yin tsaikon da zan faɗa ya faɗa, sai Husseini, ko Hassan bai taɓa yimin cin fuskar da nake ganin  Husseini ya yimin a lokacin ba. Wannan ne dalilina na farko da na ci alwashin sai na tarwatsa rayuwar Husseini. Sai ya rasa dukkan farin cikinsa. Sai dai me? Kafin na kai ga aikata duk wani abu da na yi niyya, na samu labarin ɓacewar Husseini, ya gudu ya bar gida ba'a san inda ya shiga ba. A lokacin idan ka tona zuciyata banda tsananin farin ciki babu abinda na ke ji, har addu'a nayi Allah Ya dauki ransa ma. Bayan watanni uku da ɓacewar Husseini, wataranar lahadi ba ni mancewa, ni da kaina ke tuƙi a mota daga kasuwa zan koma gida, a hanya na hangi wata tsohuwar kwastama ɗita, a baya takan zo ta sararwa Hajiyarta atamfofi a shagona ko kuma yadika na maza ta tafi, a sannan tana budurwa ko kuma nace mace mai zaman kanta amma a karkashin ikon wata Hajiya mai safarar yara zuwa Makkah da sauran ƙasashen waje don aikatau ko akasin haka. Zeenatu kenan, tun a baya Hajiyar ta sha  aiko ta shagona tun ban kai ma ga auren ita Maimuna ba, (Anti Amarya), tun a wancan lokacin muka saba, nakan ba ta shawara akan ta yi aure gudun kar ta ɓata rayuwarta don ni nasan wace ce Hajiya Balki uwar ɗakinta, saboda na sha zuwa gidan muyi cinikin kaya ta siyawa ƴan matan yaran da ke gabanta ko kuma ta siyar, na kuma san irin kalar sana'arta. Daga baya kuma sai na bar ganin Zeenatu, sai wata Raliya ake turowa. Koda na tambayi Raliya, ta bani tabbacin ai Zeenatu ta tafi Makkah, a sannan na ji ba dadi kwarai don ban so ta cuci kanta ba sai dai dama daga yanayin Zeenatu na fahimci maganata ba wani shigarta ya ke ba."

Kawu ya numfasa, nan kuma dai dakin tsit ya yi babu mai kuka sai jin wannan labarin mai ban mamaki daga bakin Kawu. Ya ɗora zancensa.

"Ganin da na yiwa Zeenatu a haɗaɗɗiyar mota, bai sa na kasa ganeta ba, asalima fuskarta ko kaɗan ba ta sauya ba duk kuwa da ɗumbin shekarun da aka ɗiba. Parking ta yi a gaban wani katafaren shagon siye da siyarwa na maƙulashe, na juya kan mota da sauri na faka a gefenta. Sai dai ban kai ga fitowa ba, idanuna su ka sauka akan Husseini, ba karamin razana nayi ba, sai nake ganin abin kamar a mafarki, fuskokinsu kadai ya nuna suna cikin tsantsar farin ciki. Ban karasa ba, har suka shiga suka fito, mantuwa suka yi ko mene? Ban sani ba, na ga Husseini ya fita ya koma ciki, har zan je wurinta sai naji tsoron kada ya fito ya gan ni, sai kawai na koma cikin mota na jira har ta tashi motarta ta kama hanya ta bar wurin, na bi su a baya har suka isa gidansu. Koda na ga gidan kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login