Showing 6001 words to 9000 words out of 230725 words
Bilkisu ne. Mahaifinsa Alhaji Aminu, yaya ne ga Alhaji Tijjani mahaifin Bilkisu. Su mazaunan unguwar Goron Dutse ne. Ya hada Degree dinsa a fannin Accounting, yanzu haka kuma yana shirin zuwa Malaysia haɗo Masters. Ta nutsu tana jin jawabinsa, a karshe ya dora da fadin.
"Tsakani da Allah nake sonki, kuma da aure. Ba don karatun ya zama dole ba, da sai ince a dauran auren kawai na wuce da ke Malaysia. Toh na tabbatar kema ɗalibar ce kamar ni, ko kuwa?"
Suka dan dara, har cikin ranta take jin ya kwanta mata dari bisa dari.
"Toh yanzu dai nima sai ki biyani bashin labari. Fadamin tarihinki."
Ya buƙata. Ta fayyace mishi asalinsu da kuma matakin karatunta a yanzu.
"Nayi murna da samunki My Future, kuma ina ji a jikina kece matata da yardar Allah. Muyi fatan Allah Ya cikamana burinmu. Kafin na tafi zan iya kawomaki ziyara?"
Ta kasa cewa komai din farin ciki, sai dai kuma tana shakkar Yaya Munir ya ji labarin ta soma tsayawa hira da wani namiji yanzun. Don haka ta girgiza kai.
"Ka bari da kaina zan gayyaceka gidanmu. Ka ji?"
Yanda ta ƙarashe zancen a shagwaɓe ya haddasar mishi da wani yanayi mai wuyar fassarawa. Ya yi gyaran murya kafin ya samu kwarin gwuiwar amsawa.
"Shikenan My Future, ni naki ne. A koyaushe kuma a kowane mataki na rayuwa da yardar Allah. Zan jiraki, ba kuma zan gaji da nayi ta jira har sadda Allah Ya so ba."
Murmushi take dagaske. Son Hilal na kara kewaya dukkan ilahirin jikinta. Sun shafe awanni suna hira sannan suka yi sallama. Ta kai duba ga masu yi mata ɗan baki, wasu sun yi bacci yayinda wasu ke waya. Miƙewa ta yi ta maida kan wayar ta ajiye sannan ta faɗa banɗaki don ci gaba da uzurinta.
***
Kamar da wasa, sabo mai tsanani ya shiga tsakaninta da Hilal, tun tana takatsantsan kada Hajiyarsu ta gane har dai wataran ta kama ta tana waya, Hilal ya kira lokacin Hajiya na kusa da wayar ta ɗaga. Kafin ta kai ga magana ta ji muryarta, ta yi mamakin jin kalaman soyayyar da ɗiyarta ke zabgawa. Karshe ta ajiye kan wayar ta leƙa ɗakin, tana tabbatar da ita ce din, kawai ta ja mata kofar. Idanun Ramla ya raina fata. Washegari da safe ta shiga kicin ta iske Rafee'ah na aiki. Tana ganinta ta yi kwafa gami da dariya.
"Kin ɓallowa kanki ruwa yarinya, Hajiya ta ji ki kina waya da Hilal. Za ki yi bayani dallah-dallah."
Ta ƙaraso gami da daga kafaɗarta idanu a waje. Rafee'ah ta ture hannun tana dariya.
"Wallahi kar ki cinyeni kina kallona da wannan manyan idanunnaki kamar mujiya."
Tsukke fuska Ramla ta yi, ba fada take nema ba, so take ta ji abinda Hajiya ta ce.
"Don Allah Sister ki bari, me Hajiya ta ce? Za ta fadawa Abba?"
Taɓe baki Rafee'ah ta yi tana tsamo dankali a cikin mai da cokalin girki.
"Oho, kya dai yi bayani, dama na lura ko karatun da kika saba duk karshen sati kin wani rage saboda soyayya, ke ga Laila ko? Toh ai idan ta fadawa Yaya Muniru ya lakaɗamaki duka kin huta."
Haushin Rafee'ah ne ya soma kamata, kawai ta juya bayan ta harareta ta fice daga kicin din. A falo suka yi kiciɓus da Hajiya tana taimakawa A'isha da tsifar kai tana mitar dama ita ba ta son kitso ya cika ƙanƙanta. Ganin Ramla sai ta daure fuska. Tun daga nan ta sha jinin jikinta. Ta karasa a sanyaye ta gaidata, maimakon ta amsa ta jefamata tambaya.
"Da wa kike waya haka karfe taran dare?"
Kirjinta na dukan tara-tara dakyar ta samu abin fada.
"Wani ne."
"Shi wanin bai da suna?"
Ta girgiza kai, kafin ta amsa mata, Abba ya yi sallama ya shigo, cikin Ramla ya bada wani sauti ƙululu. Ta san Hajiya ta fi Abba rashin fahimta sosai sai dai tana da saukin kai lokuta da dama, shi kuwa Abba akwai tsauri akan hukunci wasu lokutan. Idan ya ce a'a, zai yi wuya ya dawo ya ce eh. Wannan tasa ta tsoraci ya kwace wayarta ya kuma rabata da Hilal har abada.
Bayan an gaidashi, ya shiga yiwa Hajiya faɗan tsifa da safiyar Allah ko karyawa ba'ayi ba. Ta ba da hakuri sannan A'isha ta mike ta rufe kan ita kuwa ta fice wanko hannu.
"Zo nan Ramla, meke faruwa ne ke da Uwartaki?"
Ta mike ta ƙaraso ta zaune gefe sai dai ta kasa magana.
"Jiya ta sanarmin ta kama ki kina waya wuraren tara na dare. Fadamin, wanene shi? Kuma a ina yake?"
Da mamakin sauƙin kan da Abba ya nunamata ta sunkuyar da kai. Tiryan-tiryan ta shiga labartawa Abba wanene Hilal da kuma da niyyar da yake sonta.
Ɗan hade gira Abba ya yi.
"To shi haka ake neman aure? Meyasa ba zai soma yimin zancen ba? Sannan duka-duka a Ss1 kike yanzu Ramla. Kina zaton zan iya aurar dake yanzu? Ko kuwa kina ganin ya dace a cireki a makaranta ki yi aure yanzu ba tare da kin kammala ba? Inada burin naga kun yi karatu koda a gidajen mazajenku ne. Amma ban ce lallai ba, kuma a sanin da nayi maki kema kina da wannan ra'ayin. Me zai sa ki sauya?"
Ta ɗago kai sai a sannan ta kalli Abba idanunta rau rau kamar wacce aka ce kar ta ƙara shiga harkar Hilal.
"Abba dama ya ce yana son zuwa wajenka, ni ce ke tsoro. Kuma na fadamasa ni ba yanzu zan yi aure ba sai na kammala Sakandire."
Murmushin manya Abban ya yi, ya lura dai diyartasa da alama soyayya ta sauyata.
"Kin tabbata kina sonsa Ramlatu?"
Daga yanda ya kira sunan ta tabbatar ba wasa. Ta sunkuyar da kai tana murmushi. Ya kara maimaita wa, ta gyada kai. Ya kara maimaitawa a karo na uku, sai kuma ta tsinci kirjinta da bugu da sauri-sauri. Ta ji wani gumi da ba ta san dalilinsa ba ya ketomata a goshi. Wani yanayi na sanyin jiki ya mamayeta. Ta daure ta yakice nauyin da bakinta ya yi a lokacin ta amsa da "Eh Abba." Sai ta ga ya yi murmushi har haƙoransa suka bayyana.
"Shikenan, ki ce ina son ganinsa gobe."
Da toh ta amsa sannan ta mike ta yi daki tana jin muryar Rafee'ah dake jera kwanuka saman ledar cin abinci na mata dariya. Jikin kofar dakinnasu ta jingina, wasu hawaye ta shiga fitarwa da ba ta san asalinsu ba. Damuwa ce ko akasinsa? Murna ce ko bakin ciki? Babu daya da kwakwalwarta ta buɗamata. Wayar ta nufa ta kirashi, ya kuwa dauka ta sanar mishi abinda Abba ya ce sannan ta ajiye wayar ta koma falon. Ana cin abincin amma jikinta a sanyaye yake, abin mamaki sai sannan ta ga sakin fuskar Hajiyar, ba ta san dalilin fushinta a farko ba. Amma ta san dalilin sakin fuskar yanzu na murnar hukuncin Abban ne don har Rafee'ah na tsokanarta bayan fitar Abba akan za ta yi kewarmu. Tana fadin Autarhttps://my.w.tt/ub8deMQ0g9
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA* 🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
03)
"A farko nayi tsammanin irin samarin zamanin nan ne masu hurewa ƴanmata kunne da zantukan banza da dare. Sai kuma da naji ko waye, naga ashe na gida ne. Toh Allah Ya tabbatarmana da alheri."
Hajiya ke koro wannan bayanin sa'ilin da Ramla ke gyaramata gado ita kuwa tana gaban madubi tana goge jiki ta fito daga wanka. Murmushi Ramla ta yi ta kara maida kai ga aikinta.
"Allah kuwa Hajiya ba ruwansa. Kuma fa yace zan karasa karatuna."
Abin ya sanya Hajiya dariya.
"Ai shikenan ƴar nema, Allah Ya sanya alheri."
Ta amsa a zuci tana dariyar itama.
Hilal ya zo suka yi magana da Abba, sosai yaron ya shiga ransa. Karshe ya ba shi iznin zuwa hira sai dai ya ce ya kasance jifa-jifa saboda ɗaliba ce. Ya kara da mishi iznin turo magabata a tsaida ranar biki. Wannan magana ta fi kowacce yiwa Hilal dadi. Ya dinga godiya. Karshe suka dan taɓa hira da Abba cikin barkwanci, koda zai wuce Abba ya hanashi akan lallai ya tsaya ya ci abinci. A kunyace ya ƙaraso cikin falon.
Tana zaune tare da Rafee'ah a falo, sai ganinsa suka yi. A guje ta mike ta nufi daki don sanya hijabi, ita kuwa Rafee'ah me za ta yi banda dariya.
Ya zauna suka gaisa tana fadin.
"Masha Allah Angon ƙanwata. Allah Ya sanya alheri."
Cike da jin dadin wannan maganar ta Rafee'ah ya amsa yana shafa keyarsa. Abba ya shigo tare da Hajiya sanye da mayafi. Cikin girmamawa Hilal ya kwashi gaisuwa sannan suka dunguma saman ledar da tuni Rafee'ah ta haɗa komai na abincin dare. Abba ya shiga wulga idanu.
"Ina ita Ramlar? Auta kiramin ita maza."
A'isha ta mike da sauri ta nufi hanyar dakinsu. Daidai nan Yaya Munir ya yi sallama, a bayansa Amaryarsa Bilkisu. Hangame baki Yaya Munir ya yi ganin Hilal, shi kuwa sunkuyar da kai ya kara yana dariya ƙasa-ƙasa. Bai mancewa gidansa ya soma zuwa suna ƙusƙus da yar uwarsa Bilkisu game da zuwa ganin Abba. Koda ya tambayi wane Abban, sai ya bagarar yana fadin idan ta yi wari zai sanarmishi. Wannan ta sanya Munir kallon Bilkisu, ta yi mishi dariya cike da kunya ganin idon surukan a kansu. Ya dauke kai bai ce komai ba suka ƙarasa. A wurin cin abincin yake jin abinda ke wakana tsakanin kannennasa. Murmushi kawai ya yi gami da fatan alheri. Ajiyar zuciya Ramlat ta yi don ba haka ta zata ba.
"Kin ci sa'ar Yaya Munir, da alama dai giyar soyayya ke kwasarsa. Ba ki ga yanda yake nan nan da Anti Bilkin ba. Amarya ba ta laifi."
Zantukan Rafee'ah ya sanyata dariya. Hararar da Yaya Munir ya watsomusu tamkar ya ji abinda suke tattaunawa shi ya sanyasu nutsuwar dole. Bayan tashin iyayen, Yaya Munir ya dubi Hilal.
"Kai wato abin ƴar rufa-rufa ce ko? To gashinan ai ya fito fili. Allah Ya sanya alkhairi." Hilal ya murmusa yana satar kallon masoyiyartasa.
"Ameen Yayanmu."
Dariya Anti Bilkisu ta yi gami da riƙe haɓa.
"Oh ni, yau Mami ta zo ta ga autanta a gidan surukai."
Ya ɗan harareta don koda ta girmeshi da kaɗan, shi har yau bai ma yarda ta girmeshi din ba.
"Toh ke wa ya sanyamaki ido wai? Kuma ai ta san da zancen. Ni yanzu dai gaskiya a bani aron my wife to-be mu ɗan yi hira."
Ai Ramla ji ta yi kamar ta nutse. Ta kasa cewa komai, bayan sun keɓe da Hilal ya zubamata idanu kamar ya hadiyeta. Kunya ta kamata ta sanya tafukan hannunta ta rufe fuskar.
"Wai me? Kunya ko? Na ci alwashin kawar da shi wataran. Ko ince nan ba da jimawa ba da yardar Allah. Yau fa ina cikin farin ciki."
Ta sauke hannun tana murmushi. Ya nuna ta da yatsa.
"Ko ba ki faɗa ba nasan kema hakan ne."
"Yaushe ne tafiyarka?"
Ta sauya akalar zancen.
"Nan da sati biyu in Sha Allah. Zan fa yi kewa. Kinga da kin kammala zan iya tafiya da ke kawai."
"Gwara da ban kammala ba kenan."
Ya ɗan fiddo ido.
"Au bakya kaunar ki bi ni? Kin fi so muyi nesa da juna kenan."
Girgiza kai ta yi.
Sun ɗan jima suna hira sannan suka yi sallama ya wuce don dama ya yi sallama da mutan gidan.
***
"Kin tsaida Hilal matsayin mijin aurenki. Kar na ji ko kuma na ga kin tsaya da wani saurayin koda wasa. Duk wanda ya nuna yana sonki, ki ce an miki miji. Sannan banda yawan waya, muddin naga kin rage maida hankali a karatu da kaina ba saƙo ba zan amshe wayar har sai kin zana SSCE. Kin ji ko?"
Kirjinta ke wani irin bugu, ta ɗago ta dubi Yaya Munir, fuskarnan tamkar bai taɓa dariya ba. Daga ita sai shi a hanyar barandar fita daga cikin gidan, kiciɓus suka yi yayinda yake shirin fita. Ta gyaɗa kai.
"Magana za ki yi da bakinki."
"Naji Yaya, zan kiyaye in Sha Allah."
Sai sannan ta ga murmushinsa har abin ya bata mamaki.
"Shikenan." Abinda ya furta kenan ya yi gaba, ta bi bayansa da kallo kafin ta soma tafiya zuwa falon jikinta a sanyaye. Tana shiga nan ma Bilkisu da Rafee'ah suka yi mata ca da tsokana, nan take Rafee'ah ta kira Zulaihat ta fesa mata. Abin ya mata dadi itama sosai ta kuma yi musu fatan alheri.
***
Sati daya da wannan zancen, aka kawo kudin sa rana da karamin akwati daga gidan su Hilal. An sanya shekaru biyu da wata uku wanda ya yi daidai da sadda za ta kammala sakandire. Amrah a gidansu ta wuni ranar suna murna. Sai dai jikin wacce ake tayawar a sanyaye.
"Wai ke mene duk kin yi wani sanyi kamar ba ke ba?"
Fadin Amrah. Ta yi saurin riƙo hannun Amrah din ta ɗora saman kirjinta.
"Kin ji yanda yake bugu, bansan dalili ba. Tun soma maganar aurena da Hilal gabana ke faɗuwa, ki tayani addu'a Amrah."
Murmushi Amrah ta yi.
"Kar ki wani damu wallahi, kawai dai baƙon al'amari ne kike ji saboda zancen auren. Kinsan kowace mace dole ta ji sauyi idan aurenta ya taho, ko kin manta Anti Zulaihat da kika ce ita har kuka tayi ranar sanya ranarta?"
Ta gyaɗa kai tana jin wani sanyin dadi, hakane fa. Ta yi murmushin samun nutsuwa kaɗan.
Misalin hudu da mintuna na yamma ta sanya mayafin abayarta, fitowa ta yi da zummar takawa Amrah ta hau tasi. Ba tare da sanin kaddarar da ke bibiye da fitowar ta a daidai wannan lokacin ba.
Suka miƙa suka fito daga lungun gidan zuwa babban titi, hirarsu suke sha har da dariya.
Wannan fitar ita ce Mafarin komai. Ita ce silar soma shigarta cikin dukkan matsalolin da take fuskanta a yanzu.
***
Buga ƙofar ɗakin da ake yi ba kakkautawa ya katse dogon tunanin da ta faɗa.
Ta ajiye wayar hannunta wanda Hilal har ya gaji da kira ya hakura ya yi text, nan ma ba ta samu damar budewa ba.
"Wai Ramlatu bakya ji ne? Me kike yi haka?"
Jin muryar Hajiya ya sanya ta saurin miƙewa jiri na kwasarta. Murya a dusashe ta amsa.
"Ganinan Hajiya." Ta karasa ta budemata ƙofar. Hajiya ta yi mata ƙuri da ido tana kallonta. Kafin ta yi kwafa.
"Duk wanda bai ji bari ba, ai zai ji hoho. Haba Ramla, na ce miki karki je gidannan amman taurin kai irin naki da har yau kika kasa yaƙarsa ya sanya ki takawa gidan Hilal. Taurin kan da ya kamata a yanzu kin hankalta cewar halaka ce ga dukkan wani dan adam. Koda dai, ke za ki bada labari. Gashinan ai kin je kin jiyowa kunnuwanki. Ai tunda Muniru ya ce Balki ma za ta ni nasan ba za'a ƙi gasamaki mai zafi ba. To madallah, sai ki gama kukannaki ki fito ki damamin koko na sha magani. Ya yi kyau."
Da haka Hajiya ta fice ranta a ɓace. Ramla ta yi shiru, shakka babu kam ko me aka yi ita jazawa kanta. Sai dai kuma ya za ta yi ta watsawa mutumin da d Ta koma ciki ta faɗa banɗaki bayan ta rage kayan jikinta. Wanka ta yi sannan ta fito ta sanya kaya. Sai da ta kwashe mayafi da jakarta da ta cillar a tsakar ɗakin sannan ta ɓalli Paracetamol ta fito. Hajiya na zaune a falo tana kunce garin magani, tana ji tana yiwa Talatu bayanin maganin, wai na ciwon ƙafa ne ta samo wurin Hajja. Kicin ta shiga ta sha maganin kafin ta hau kiciniyar dama kokon. Sai da ta kammala ta fito ta ajiyewa Hajiya, itama ta ɗiba ta sanya sugar ta soma sha.
"Yarannan basu dawo ba." Harara ta samu daga uwartata, kafin ta amsa.
"Waye zai je daukosu?"
Sai sannan ta tuna cewar ashe ta ce za ta biya daga gidan Hilal su taho gida.
"Sai ki kokarin zuwa daukosu, na riga da na sallami Haladu sai gobe zai zo."
Ta amsa da to gami da duban agogon dake manne jikin bangon falon. Karfe shida da mintuna, magriba tana kan hanya. Tana jin Hajiya na yiwa A'isha waya akan kar su sake su taho a ɗan sahu, gatanan zuwa ɗaukarsu. Ba ta yi mamaki ba sanin da ta yi ko da can Hajiya ba ta fiye son shigarsu abin haya ba idan magriba ta wuce. A gaggauce ta shanye kokon ta nufi daki. After dress blue mai kauri ta dora saman doguwar rigarta ta dau wayoyi da mukullin mota ta fice. Hajiya ta bi bayanta da kallo, a kullu yaumin tana tausayawa rayuwar Ramla, matsalolinta sun girmewa shekarunta a nata tunanin. Sai dai kuma Allah Ya fi ta sonta.
Ta yi nisa don har ta hau titin unguwar Zulaihat, ƙarar wayarta ta dauki hankalinta. Ganin ta ƙi yankewa ne ya sanya ta dauka.
Murmushi wanda ya fi kuka ciwo ta yi. Shi wata irin halitta ne na daban mai halayyar ƴan aljannah. Da ace kirki na yawa, za ta iya auna irinnasa a wannan mizanin.
"Assalamu alaikum."
Ta furta a tausashe a lokaci guda tana hankalta da yanda take sarrafa sitiyari.
Ajiyar zuciya ya soma saki kafin ya amsa. Bai ko bari ta gaidashi ba ya dakatar da ita a ƙagauce.
"Shi kuma wannan aljanin ya sunansa ne Ramlat? Na fa gaji da yaƙarsu. Kimin rai ki daina zafafawa wurin yanke hukunci mana."
Ta yi murmushi mai sauti.
"Kar fa ka dauki hakkin bayin Allahn da basu da laifi. Ka yi hakuri na amsa laifina."
"Shikenan na hakura, kuma kema ina mai ba ki hakurin. Na ji hayaniyar ababen hawa, ko.."
"Ina hanyar gidan Anti Zulaihat, zan dauko yara."
Ta katseshi da hanzari kusan hankalinta ya tafi gurin cunkoson da ta hanga dab da ita. Ta ja burki ta tsaya sa'ilin da Hilal ke mata fatan sauka lafiya da kuma sallama.
"Nagode." Ta furta tana ajiye wayar gami da kara kallon mutumin da fitilun mota da mashin suka taimakamata da ganin fuskarsa. Dogo ne kuma mai madaidaicin jiki. Idanunsa rufe da bakin gilashi yayinda ya zuba hannuwa cikin aljihun cotton din wandonsa da aka rubuta Adidas a gefe. Rigarsa mai hula sai dai bai rufe sumar kansa da ita ba, fararen kafafun cikin bakin silifas, ya fita daban da ruwan tokar shigarsa. Ta kai duba ga inda hannunsa ya taɓa a jikin motar, ba kalar ta rannan ba ce, wannan wata ce maroon in colour, tana da tudu ba kamar waccan ba. Shakka babu an