Showing 150001 words to 153000 words out of 230725 words
Taimakon gaggawa likitocin suka shiga ba Hussein har Allah Yasa ya dawo hayyacinsa. Hajiya Zeenatu ta rasa sukuni, banda safa da marwa babu abinda ta ke yi a harabar bakin kofar dakin da Hussein ke kwance. Can ɗaya daga cikin likitocin ya fito, da hanzari har mayafin na sulalewa ta ƙarasa.
"Dakta ya farfado?"
Daktan ya yi murmushi gami da gyara zaman gilashinsa.
"Alhamdulillah Hajiya, ɗanki ya farfaɗo, ki kwantar da hankalinki."
Ta tamke fuska.
"Mijina ne."
Mamaki karara a fuskar likitan kafin kuma ya haɗiye don ba abinda ya shafeshi ba ne.
"Ok, idan ba damuwa ki biyo ni zuwa ofis."
Daga haka ya yi gaba.
"Matsalar Hussein damuwa ce da ta haddasa masa ciwon kai mai tsanani. Sai jininsa da ya hau, sai kin kula sosai da cimarsa har ma da walwalarsa domin irin ciwonsa na bukatar kulawa kuma ba ya son yawan tunani."
Hajiya Zeenat ta yi shiru a ranta tana jin takaicin Hussein da zai sa damuwar wani abu bayan ita ce duniyarsa.
"Kin ji abinda na ce?"
Tambayar ta katse tunaninta. Ajiyar zuciya ta saki.
"Naji kuma zan kiyaye. Yanzu ina iya ganinsa?"
Likita na ƙaremata kallo ya gyada kai.
"Eh Hajjaju."
Ta mike tana watsa masa kallo mai kama da harara, ba shiri ya janye idanunsa tunda ya san shi ya jaza wa kansa da ya bita da kallon kurilla. Ba kuma don sha'awa ba, sai don ya ga abinda ya kwaɗaitar da mara lafiyarsu da ta kira da Hussein har ya ji ita ya ke da muradin zama abokiyar rayuwarsa.
"Su ta shafa." Ya ƙarƙare tunanin ta hanyar furta hakan a fili.
Hajiya Zeenatu ta shiga ɗakin da Hussein yake, wannan karon babu kowa sai shi ɗaya. Idanunsa a lumshe, a farko ta yi zaton bacci ya ke, sai dai rufe ƙofar da ta yi yasa shi kallonta. Ta sakarmasa murmushi tana mai ƙarasowa ta zauna gefen gadon ta kama hannunsa.
"Sannu Hussein, ya jikin?"
Gyadamata kai kawai ya yi ya kara kauda kansa.
"Ba zan kwana a nan ba, su sallame mu."
Yanda ya yi zancen ka san iyakar gaskiyar kenan ba wasa. Cikin rarrashi ta shigo kokarin fahimtar da shi kuskuren hakan, sai dai yanda ta kafe haka ya kafe har abin ya tsorata ta. Aikuwa dai karshe sai sallamar aka ba su da lodin mgunguna bayan an ƙara jaddada masa akan ya kula sosai da jikinsa.
Su na komawa gida ma'aikatan suka tarbeshi tare da yi mishi sannu.
"Dalla Malamai ku matsa! Ba kwa ganin yanayin jikinsa ne?"
Hussein ya dubi Hajiya Zeenat, a fuskarsa ta gane bai ji dadin abinda ta yi ba. Ya tsaya ya amsa gaisuwarsu ita kuwa ta yi gaba tana tsaki. Godiya ya yi musu san nan ya shige ya bar su da gulmarta.
Sallar Magriba ya soma yi san nan ya shiga wanka. Yana fitowa ya kimtsa, Hajiya Zeenatu kuwa tana ƙasa ta na bada umarnin abinda za'a girkawa mijinnata.
Ya dauki wayarsa, ya ga missedcalls din Hisham sai kuma na wani abokin aikinsa. Data ya kunna ya leƙa whatsapp. Shiru ya yi ya ƙurawa sunanta idanu yana kallon saƙon da ta aiko ba tare da ya buɗe ba, ya hangi dai sallama da gaisuwa, sauran ne bai da masaniya. A hankali aka zare wayar daga hannunsa. Hajiya Zeenatu ce, gabansa ya faɗi.
"Haba Yallaɓai, yaushe ma ka farfaɗo da za ka ɗauki waya? Ba dai ka manta sharuɗɗan Dakta ba?"
Ta ƙarashe tana duban wayar, tuni ta shiga key, shima yanda ta ke kallo haka ya ke kalla, ganin ta rufe ya sanya shi sauke ajiyar zuciya. Gaba daya ta kashe wayar tana mai duban soyayy duk a kokarinta na gudun kar ya sauya shawarar da ta kawomasa a ɗazun.
"Wayar a hakura a bar ta zuwa gobe. Yanzu mu je ƙasa ka jira abinci sai ka sha magani."
Ta faɗi gami da riƙe hannunsa. Ya ciji leɓɓansa, haka nan ya ji bai kyauta ba bisa rashin ba da amsa ga Ramlat sai dai maganganun Hisham na faɗomasa a rai sai ya yi gaggawar fidda tunanin.
***
Mintuna kusan goma sha biyar sai ga kiran Amarya a wayar Rasheedat.
"Muje na yi miki rakiya."
Haka kawai Ramlat ta ji faɗuwar gaba, ta amsa da toh tana mai haɗiyar yawu mai ɗaci.
Da sallamarta ta sa ƙafa a falon. Dattijo cikin shigar kamala, kana ganinsa ka ga cikakken bafulatani. Tundata shigo yake yiwa fuskarta kallon tsanaki don son tantance ko akwai inda ya santa ko kuwa yau ne farkon ganinsa da ita. Ta karasa ta gaishe shi, Amarya tuni ta mike zuwa ɗaki. Hakan kan faru, idan har Modibbo nada baƙo, sukan ba shi wuri ya gana da ita.
"Baiwar Allah daga ina?"
Ya tambaya cikin hausarsa da har sannan ba ta ginu kamar ta Bahaushe ba.
Ta hadiyi miyau gami da ambaton Allah. Ta gabatar da kanta sannan ta ɗora bayan ya shaidamata eh ya san Malam Abdullahi kakanta kuma ɗan unguwar da yake, Yakasai.
"Kawu dama magana ce da ta danganci Hussein, dan uwan AlHassan da ake nema."
Shiru-shiru, ba ta ji ya ce uffan ba don haka ta ɗago kai. Yanayin dake shimfiɗe a fuskarsa ya tsorata ta, ya kuma kaɗa hanjin cikinta.
"Kina da labarinsa? Ke wace ce?"
Wannan ne tambayoyin da ta samu da suka ƙara cilla ta a kogin tunani da mamaki.
I just published "BABI NA ARBA'IN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/gqyFr6qwCcb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
45)
ALLURA TA TONO GARMA...
"Kurma ki ka koma?"
Ta dawo hayyacinta ta kalle shi gami da girgiza kai. To me za ta ce bayan ta gabatarmasa da kanta?
"Ina gargaɗinki da ki cire kanki a abinda bai shafeki ba. Idan kina son tsira da lafiyar kwakwalwa da na gangar jikinki ki fita hanyar Hussein da Zeenatu."
Da wani irin razana ta dubeshi, wannan ƴar fara'ar dama tun soma labarin ya kauda ita a saman fuskarsa sai ya zama kamar wani Mugyambo a idanunta. Kwallar da ta cika kurmin idanun suka soma sharara.
"Ka...ka..san Hussein yana nan? Ban ambaci Zeenatu ba, ka san..."
"Ke Bingel! (Yarinya). Ke wacece da za ki tuhume ni? Ina gargadinki karo na biyu kuma na ƙarshe ki tashi ki binne maganarnan a nan wurin da kike zaune. Idan ba ki ƙi ji ba, ba kya ƙi gani ba. Duk abinda ya faru gareki sanadin fasa wannan zancen, ki yi kuka da kanki!"
Ramlat kirjinta na bugu, hawayenta na kwaranya, kwakwalwar ta tsaya cak ta bar aiki. Ta kasa haɗa kowane lissafi, jin ta take yi kamar ba'a duniyar mutane ba. Kamar wata duniyar ta daban ta ke ciki mai tsananin ruɗani da azaba. Kallonsa ta ƙara yi, girman tuni ya zube ƙasa warwas! Kallo ne kamar wacce ke zaune gaban sa'anta.
"Ka na da hannu a komai? Ka na a ɓatar da Hussein daga zuri'arku? Me ya yi maka haka da zafi?"
"Kina ƙara dulmiyar da kanki cikin tafkin nadama da da na sani, kalaman da kike yi za su rushe duk wani farin ciki na rayuwarki. Ki kama kanki! Ki tashi ki bar min gida tun kina da sauran lafiyar aikata hakan!"
Miƙewa ta yi a sanyaye, har za ta fice ta juyo ta dubeshi yana faman muzurai. Dattijon da bai kama daraja da girmansa ba, babu amfanin ganin ƙimarsa.
"Kawu ka sani, Allah na bayan masu gaskiya. Ƙarya fure ta ke ba ta ƴaƴa."
Daga nan ta bankaɗa labule ta fice, ba ta jin za ta iya jiran yin sallama da Amarya. Babu inda ta ƙara shiga a gidan haka ta fice tana hawaye.
Tafiya ta ke ƙafafun na harharɗewa, kalaman Kawu daki-daki ta ke tunawa tana ƙarin fahimtar dagaske dai akwai hannunsa a cikin ɓatan Hussein.
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!"
Ta ambata a fili, tausayi sosai da wata irin ƙauna ta Hussein ya ƙara mamaye zuciyarta. Ji ta ke komai za ta iya aikatawa muddin hakan zai dawo da Hussein cikin ƴan uwansa. Wayarta ta yi ƙara, Hajiya ce. Yanda ta ke kuka ba ta jin za ta iya amsawa, don haka ta mayar da wayar jaka. Kafin ta bar lungun sai da ta tsaya ta saita kanta ta share fuska. Abin hawa ta tsayar ta faɗa.
"Malama ba ki faɗi inda zan kai ki ba."
Ta haɗiyi miyau. Dakyar ta faɗi sunan unguwar ta yi shiru, kanta ke sarawa ga wani zazzaɓi-zazzaɓi.
***
Tsam! Modibbo ya miƙe ya shiga ɗaki, Amarya na zaune na kallon wani ƙaramin bidiyo na Ibro tana dariya, ganin mutum ya faɗo ba sallama ya sa ta ɗan razana kafin ta sauke ajiyar zuciya. Tun kafin ta nemi ba'asi ya katsemata hanzari.
"Fita zan yi, ki je kawai idan na dawo zan kiraki. Akwai uzurin da zan gabatar."
Ya faɗi a kausashe, ta miƙe jikinta a sanyaye ta fita fuskar cike taf da tarin tambayoyin da babu mai amsa mata sai Ramlatu. Sai dai sama ko ƙasa babu ita, hatta su Rasheeda sun yi mamakin da ba ta biyo ta musu sallama ba.
Fitar Amarya ya ba Kawu Modibbo damar buɗe sif ɗinsa ta kaya, can ƙasan ya zura hannu ya ɗauko wani ɗan akwati mai girma da duk faɗin gidan babu wanda ya isa ya taɓa. Hankalin ma bai kai gareshi ba. Cikin rigarsa ya zaro mukullin da ba ya rabo da shi a jikinsa, ya buɗe, kwakwalwa ce! Kwakwalwa ta ƊAN ADAM! Ta yi baƙiƙirin a madadin jan da ta ke da shi har da jini-jini a shekaru masu yawa. Idanun Kawu Modibbo suka kaɗa.
"Ita ce! Ita ce yarinyar!"
Abinda ya faɗi kenan a fili kafin hannu na rawa ya maida ya rufe. Gumi ya shiga tsastsafowa daga fatar jikinsa. Ya sa hannu ya share. Tun komai bai ƙarasa lalacewa ba zai yiwa abin tufka. Ya ayyana hakan a ransa yana jin tsanar Hussein tsagwaronsa a fili da ɓoye. Miƙewa ya yi ya dauki waya ya danna kira direbansa.
"Kana ina?"
Daga can aka ba shi amsa kafin ya dora.
"Ka fiddo mota, fita zamu yi."
Daga nan a gaggauce ya dauki hula ya rufe kansa ya fita yana zuba sauri.
***
Ramlat bakinta ya yi mata nauyi, ta kasa ba Hajiya labarin abinda ya faru. Damuwar da ke kwance samam fuskarta yasa Hajiya ta fahimci ba lafiya. Ganin ta shige daki sai ta mara mata baya.
"Ke mene ne wai? Shi Kawun ne ba ki samu gani ba ko wani abin ne ya faru da Husseinin?"
Girgiza kai ta yi. Tunanin ta faɗa ɗin ya rinjayi komai, ko ba komai Hussein na bukatar addu'a, don haka ta karya bille ta labartamata duk yanda suka yi da Kawun. Hajiya ta saki salati.
"Ni Rabi wannan rayuwa da ban mamaki. Ban taɓa jin labari makamancin haka ba tunda uwata ta haifeni. Kai.."
Hajiya sai ta soma hawaye, ita kanta tausayin Hussein ke ɗawainiya da ita. Hatta da abokin haihuwartasa ma tausayinsa take ji. Miƙewa ta yi tana jan hanci.
"Addu'a zamu dage da yi, ke kanki yanzu ki dage da addu'a don mutum idan aka ce mugu ne komai ma zai aikata. Bari na kira Malam na faɗamasa, shima ya tayamu da addu'a."
Daga nan Hajiya ta fita ta bar Ramlat da tarin damuwa. Dakyar ta iya mikewa ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar isha'i, zaman dirshan ta yi saman dardumar jefi-jefi tana sharar hawaye.
Addu'a sosai ta yi kafin ta miƙe ta nufi gefen gado ta zauna. Hayaniyar su Affan ta ishe ta don haka ta kora su waje. Waya ta ɗauka ta hau kan whatsapp, babu alamar Hussein ya hau. Yau ɗaya ta ɗaura ɗamarar kiransa. Don haka ta sauka ta danna masa kira. Wayar a kashe. Damuwarta madadin ta ragu sai ta ƙaru, ganin dukan na nema ya yi mata yawa, sai ta miƙe ta koma falo ta yi jugum. Ba jimawa Hisham ya kirata. Ta ɗaga.
"Antinmu shiru, ina jira na ji yanda ku ka yi."
Ta haɗiye hawayenta da ɓacin rai. Komai ba ta ɓoyewa Hisham ba, ya dinga salati da salallami karshe dai ya kwantar mata da hankali.
"Kar ki sanya damuwa a ranki Ramlat, in sha Allah kamar yanda kika ce toh hakan ne, Allah Ya fi su. Mu dage da addu'a."
Ta amsa da toh. Kamar ta tambayeshi ko sun yi waya da Hussein sai ta share.
***
Washegari haka ta shirya ta fita wurin aiki ranta a jagule. Ga wayar Hussein da ke a kashe. Ta gwada kira har cikin dare don tsautsayi amma ba ta shiga. Tuƙi ta ke kusan ba za ta ce a cikin hayyaci ba. Don haka ba ta kawo da cewar an basu hannu ba sai da ta ji wani ruɗaɗɗen Hon daga bayanta. Hakan ya fusata ta, ta madubi ta ke duban mai shi. Ido da ido suka kalli juna, yana cin magani. Wannan karon ba Tinted glass din a motar da yake. Yanda ya ɗaure fuska ba alamun fara'a ya fi komai ruguza lissafinta. Asalima ba wani wawan overtaking da ya yi ya kaɗa hancin motarsa sai da ya daskarar da ita ya jazamata ɗaukewar numfashi na ƴan dakiku.
"Me nayi masa?" Ta ambata a fili, da rawar jiki ta ja motar bayan ta gaji da tsinuwa da zagin mutanen da hankalinta ba'a kansu yake ba. Koda ta gangara sai ta nemi wuri ta tsayar da motar. Hankalinta ya gushe na ɗan lokaci. Tunaninta abinda ta yiwa Hussein, shi dai ta gani kamar yanda ya gan ta amma ya kauda kai. Wannan abu ne da bai taɓa afkuwa ba tsakaninsu. Ta ɗauki wayarta da karar shigowar saƙo ya katsemata tunani, kuɗi ne har dubu ɗari aka aikomata. Ta kai duba ga lambar mai account din. Aliyu Dikkl. Hakan ta gani a rubuce. Ranta ya ƙara ɓaci, ga babu lambar acc balle ta mayarmasa. Ta ja tsaki. Kai tsaye ta ƙara kiran wayar Hussein, wannan karon ringing ta ke yi sai dai har ta katse bai ɗaga ba. Ta kuma kira nan ma shiru, a karo na uku ma babu alamar za'a ɗaga. A na huɗu sai ji ta yi an kashe wayar gaba ɗaya.
"Meke faruwa?" Ta ambata a fili. Kawai sai ta ji zuwa wurin aikin ma ya fita a ranta, don haka ta ba kanta mintuna kusan biyar a tsaye tana jin karatun Alkur'ani tana hawaye kafin daga bisani ta samu ƙwarin gwuiwar da za ta tashi motar. Gidan Amrah ta nufa, a hanya ta kira ɗaya cikin abokan aikinta, Hindu. Uzurin rashin lafiya ta bayar domin dagasken ba ta jin dadin zuciya da gangar jikin.
***
Amrah ta yi mata duban tsanaki bayan gama sauraron dukkan bayanin Ramlat. Ita kanta kwallar ce ta cicciko mata.
"Yanzu AlHassan ɗin bai shigo ba?"
Ramlat da kanta ke jikin kujera sakamakon zazzaɓi-zazzaɓin da ta ke ji. Ta girgiza kai murya a dusashe.
"Mun yi waya da shi yanzu da zan fito, abin hawa ne ba'a kammala gyara mishi ba, yana tunanin ma bar musu zai yi ya biyo motar kasuwa."
"Kai! Wannan lamari akwai wata sarƙaƙiya a cikinsa Ramlat. Sai dai kuma ki zauna don Allah ki yi tunani ko dai akwai abinda ki ka aikata ga Hussein har ya ɗauke maki wuta haka? Ni fa gani nake da walakin goro a miya."
Cike da damuwa ta ɗago ta zauna sosai tana duban Amrah da ciki ke ƙara girma.
"Da ace akwai abinda nake jin zan ba dukkam girma da kulawa bayan iyaye, ƴaƴa da ƴan uwa, wallahi ya biyo bayan Hussein. Kin san ni, kin kuma san halina Amrah. Ina son Hussein, son shi nake yi da ban san iyakarsa ba. Akan me zan ƙuntata masa? Ni duka-duka ma yaushe rabon da ko chatting nayi da shi balle haɗuwa face to face? Ban sani ba, ban san me na yi ba. Ni dai babban burina koda zai zama abu na ƙarshe da zan mishi, shi ne na sada shi da ƴan uwansa da taimakon Allah."
Amrah ta jinjina kai, shakka babu Ramlatu na son Hussein, so mai yawa. Tana tsoron tarihi ya maimaita kansa idan har dangin uwa da uba suka dage mata akan auren Chairman. Sauƙinta ma wannan karon su Hajiya na goyon bayanta.
"Ko Hisham zan tambaya?"
Maganar Ramlat din ta maido ta hayyacinta. Gyada kai ta yi.
"Ki tambayeshi tunda amininsa ne. Ba zai rasa abinda ya sani ba."
Da haka ta danna wa Hisham kira. Yana ɗagawa suka gaisa.
"AlHassan din ya iso kenan?"
Ya nemi sani.
"Aa, wannan tsakanina da Hussein ne."
"Ina jinki Ramlat."
Ta ba shi labarin irin sauyin da ya ke mata.
"Ko akwai wani abu da ya ce maka na yi mishi don Allah?"
Shiru ya biyo baya kafin Hisham ya ce.
"Ya Salam!"
Jin haka ta gyara zama tana kallon Amrah don dama a speaker ta sanya. Suka nutsu.
"Meyafaru?" Ta tambaya kirjinta na dukan uku-uku.
"Ki yi hakuri, ina ga wannan laifina ne, yanda na ɓata kuma ni zan gyara. Kar ki damu don Allah. Zan kira ki anjima ko kuma ince zai yi kiranki da kansa. In sha Allahu."
Daga haka ya katse kiran. Suka dinga mamaki. Tunanin Ramlat me Hisham ya faɗawa Hussein?
"Hisham ya san batun aurenki da Chairman?"
Amrah ta nemi sani. Maganar Ramlat ji ta yi kamar an sokamata mashi a ƙahon zuci don haka maimakon amsa sai ta harareta ta ja guntun tsakin da ya ba Amrah dariya.
"Allah Ya ba ki hakuri. Mancewa nayi fa."
Ta cije lebɓa gami da girgiza kai ba ta ce komai ba.
***
MISALIN ƘARFE SHA ƊAYA..
Rubutu yake kamar wani Mango Park ba ya ko kallonsa, Hisham ya ƙuramasa idanu da mamaki. Ya sauya kamar ba Hussein din da ya sani ba.
"Malam ya ina magana ka kyale ni? Ba ka ji me nace ba?"
Ya ɗago ya dubeshi, ya ji, dukkan wani labari da ya ba shi, ya ji ba wai bai ji ba. Sai dai duk da hakan shi bai ga ta inda zai fara rage KISHIN Ramlat da ya ke ji ba. Ya soma yarda da abinda ya ƙaryata da gangan, ba kuma ya son sanya ta a matsala. Wannan ne dalili sauyawar sai dai ya ji wani sanyi kaɗan a maimakon tsananin zafin da ya ɗauka a farko duk