Showing 228001 words to 230725 words out of 230725 words

Chapter 77 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1046

tarwatse yana daga waje, ga kukan jariri yana ji kuma ana fadin ai ba ta kammala ba. Ga murna ga kuma tashin hankali da tausayin matarsa. Kalmar mutuwar da ta ambata har yanzu ba ta sakeshi ba, fargaba sosai ya ke ciki duk kuwa da ya sani mutuwar ba a baki ta ke ba.
 
Kukan jaririn da ya kara ji, sai ya rude, ya rasa na farkon ne ko na biyun, kawai sai ya cusa kai ba tare da neman izni ba. Aikuwa wata jaririyar ce aka kara cirowa Ramlat. Ita kuwa ta lumshe ido sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke yi.

Dole ya fita yana murna, kafin a kammala gyarasu ya shiga laluben waya don ya sanarwa Dada da ɗan uwansa sai dai wayam. Hakanan ya hakura ya dinga murna da farin cikinsa shi ɗaya. Gaba daya jariran aka kawomasa, Metron na fadin sai fa ya ba ta goron albishir, dariya ya yi yana ɗaukarsu.

"Ki biyoni bashi."

Itama dariyar ta yi ta miƙa masa tana fatan Allah Ya rayamasa.

Kammanin Dada sak ko kuma yace kamanninsa yake hangowa a fuskar yaran wadanda suma ke cike a kansu a saman fuskarsu.

Sumbatar kowannensu ya yi yana mai jin taruwar kwalla a idanunsa, ashe dai wataran mafarkinsa zai tabbata, zai ga gudan jininsa? Ya soma yiwa namijin huɗuba a kunne kafin ya juya ga macen.

Daga nan kuma ya yi zamansa yana ƙaremusu kallo, haka har aka soma kiraye-kirayen Assalatu. Aka ba shi umarnin ganin Ramlat, ya shiga ciki. Ta zubamusu do tana kallonsu cike da kauna, yana karasowa ta yi murmushi.

"Alhamdulillah." Ta furta, ya ajiye yaran a gefe kusa da ita ya sumbaci goshinta shima ya na hamdalar. Dakyar ya samu ya wuce masallaci. Ana idar da sallah ba jimawa sai ga AlHassan tare da su Dada.

Kowa ya ga ƴan biyunnan sai ya hau murna. Dada har da hawayenta tunawa da ta yi da Yayanta kuma ɗan uwanta Aminu.

Ranar dai Ramlatu ta sha baƙi dakyar aka fice aka bar ta ita kadai ta samu bacci mai nauyi ya fisgeta. Jariran kuwa su na hannu, wannan ya dauka wannan ya dauka har sai da Hussein ya yi ta maza ya ce ya isa hakanan su ma a bar su su huta. Duk shaƙiyancin da ake mishi ko a jikinsa. Ya shimfidesu a kusa da uwar ya tsaya ya kuramusu idanu yana kallo. Ya kalli Ramlatun ya kallesu. Tausayinta ya kamashi, ba karamar wuya ta ci ba. A karshe dai ya fice ya bar su. Sai da Dada ta lallaɓashi kafin ya koma gida ya yi wanka ya sanya suturar arziki ya kuma biya shago ya siyo kayan jarirai na mace don kusan rabin siyayyar duk na namiji suka yi jin abinda scanning ya bayar.

Kwanan Ramlatu biyu aka sallameta, sashin Dada ta koma inda Baba Mariya ke wanketa tas ita kuwa Dada ke wanke jarirai.

Hussein ko yana ofis ba ya rabo da waya. Ranar suna aka sanyawa yara suna Amina da Aminu, farin cikin Dada ba ya misaltuwa. Daidai da iyalan Kawu sai da suka zo suna wannan karon har da Umma matar Baba Dakta, Hajiya ma ta so zuwa sai dai makarantar yara ta sanya dole ta hakura amma itama kam zuwa lokacin kewar diyarta take ji. Abinda ya yiwa Ramlatu dadi bai wuce na zuwan Muhibbat ba. Sosai ta yaba da wannan karar da ta yi mata, abin mamaki kuma har saƙo ta samu na kayan jarirai daga iyayen Hilal, matar Hilal ta kira ta mata barka ta kuma yi mata fatan alheri. Koda ta ke ba su Rafee'ah da suka zo suna labarin wayar, dariya suka yi.

"Ai ke yanzu wacce da kika sani a baya yanzu ba ita ba ce, ko ma dai mene ai yanzu dole ta sauko tunda aure zai ƙara kuma yanzu ko ba komai ta ga  kin auri wanda ya shanye mijinta a komai da komai na rayuwa.
Jinjina kai kawai ta yi tana murmushi a ƙasan ranta tana mai hamdala da Ubangiji.

***

Rayuwa sosai ta ke yiwa Ramlat da mijinta dadi, zuwa lokacin gininsa da yake ya kammala sai fenti da ake yi da kuma zuba furnitures da ya yi saura. A wannan lokacin ne kuma ba zato ya yi mata albishir da kai ziyara Kano. Dama tun sadda ta yi kwanaki arba'in ta ke saka rai da hakan, ya nuna ba yanzun ba. Har faɗa suka yi ta gama fushin ta haƙura ta sauko. Haka ta dinga shirya tsaraba, Dada ma ta haɗamata da nata.

Hajiya ba karamin farin ciki ta yi ba, abincin da Ramlatun ta fi kauna shi ta girka mata, hakanan Umma itama ta aikomata girki. Su Ummi kamar su haɗiye ƴan biyu wadanda suka dauko hasken mahaifinsu kamar ka latsa jini ya fito. Duk ganin da Ramlat ke yiwa Ummi tana da gashi sadda tana ƙarama ashe ba komai bane idan aka haɗa da na Meena. Kamar yanda suke kiran Amina don Dada sam ta hana a ɓoye suna.
Hisham kuwa koda ya ga amininsa sai ya hau dariya da zolayarsa ganin yanda ya ajiye naman wuya ya ƙara zama wani fresh. Har gidan su Hisham din ya je ya gaida mahaifiyarsa kafin ya koma masauki.
  Washegari ya juya Adamawa ya bar Ramlat, sati biyu kawai ya ba ta hakanan ta hakura don a son ranta ne ta yi wata guda cif. Ai kuwa a sati biyun ta zage yan uwa da abokan arziki, koda ta je gidan Yaya Munir ta kara shan mamakin zamantakewar matansa wadanda tuni ya haɗe su gida daya. Salma kanwar Bilkisu ita kanta ta sauya ta yi sanyi. Anan suka hadu ta dinga ba ta hakurin abinda ya faru a baya, banda murmushi ba ahinda Ramlatun ta yi don har ga Allah ita kam yanzu dukkan kunci ko bakin cikin da ta shaƙa a baya ta bar sanya damuwarsa a rai sai dai ta tuno ta auna da yanzu ta godewa Allah.
  Ana jibi zasu tafi ne ta fita tare da Amrah, daga gidan Muhibbat suke kafin su karasa wani katafaren shago don nemawa Kausar wani man jiki da ta addabeta a kansa. Dama daga Kano ake aikamata, wacce kuma ta ke siya wajenta, nata ya ƙare.
  Sai da suka fito Amrah na kara yi mata bayanin wani maganin mata da ta ba ta, ba zato ta ji an kirayi sunanta. Juyawa suka yi a tare ita da Amrah, mamaki ya kama su ganin Chairman da wasu ƴan matan yara da zasu kai shekaru goma sha biyu zuwa goma, bayan yaran sun gaishesu ya basu umarnin shiga shagon kafin ya zo. Ya juyo ga su Ramlat, suka gaidashi fuska ba walwala. Sai da ya soma da neman gafarar Ramlatun kafin ya dora.

"Kina da labarin rasuwar Hajiya  Zeenatu ko?"

Kusan a firgice ita da Amrah suka ce.

"Hajiya Zeenatu?!"

Ya jinjina kai da mamakin rashin saninsu.

"Ta rasu yau wata hudu kenan, tun dai iftila'in gobara da ya afkawa shagonta ta samu matsalar shanyewar  ɓarin jiki. Haka dai a sanadin jinya komai nata ya ƙare. Sau ɗaya naje duba ta na kuma bada tallafin kuɗi domin a yi mata abinda ya dace. Na isketa cikin mawuyacin halin da har babu wani ko wata da ke tsaye a kanta domin jinya. Nima saƙo ta bayar ta hanyar Ƙawarta Hajiya Batool akan a faɗamin. Ta bar min wasiyya akan duk sadda na haɗu da ke ko Hussein na nemamata gafararku. Ita kanta yanzu Hajiya Batool din kokawa take da tata lafiyar, ciwon Kansar Gaba take fama da shi. Abin dai babu dadi don yanzu haka ɗanta ma ba ya ƙasar, ya juya da iyalinsa ƙasar waje."

Chairman na kaiwa nan ya girgiza kai, kansa a ƙasa kafin ya ɗago ya dubi su Ramlat wadanda tsoron Allah ya kuma mamayesu. Wai Hajiya Zeenatu ta mutu. Lallai Allah abin tsoro.

"Ki yafemin nima Ramlatu, ko aurenki da na je nema banda soyayya har da sa hannun Hajiya Zeenatu."

Ya basu labarin komai, take Ramlat ta ce ta yafemishi, aka rabu suka wuce shi kuma ya shige ciki.

"Allah Kenan! Kin ji yanda jikina ya yi sani Ramlat?"

Amrah ke zancen tana matsar kwallar tunanin rayuwa, shakka babu DAN ADAM ba a bakin komai yake ba. Ramlat ta sa hannu ta share nata hawayen.

"Bari kawai Amrah, duniya abin tsoro. Allah Ya gafartamata. Ni dama ban riƙe ta ba, wadanda ta yiwa su ne abin ji."

Amrah ta gyada kai.

"Allah Ya basu ikon yafemata."

Ramlat ta amsa da amin. Haka suka dinga maganar su na kara roƙon Ubangiji akan cikawa da imani.

Washegari kuwa duk yanda ta so Hussein ya amincemata da ziyarta Halima a gidan yari kamar yanda ta ƙudurta, sai dai ina! Hussein ya ce bai lamunta ba. Dakyar da siɗin goshi ta shawo kansa ya amince akan ta nemi Yusufa ƙanin Halima ta isar da saƙo ta hannunsa. Hakan ba yanda ta iya kuwa, ta aikata. Yusufa ya zo har gidansu Ramlatun, bayan sun gaisa ta ke tambayarsa batun Halima.

"Yaya Halima tana nan, wallahi wacce kika sani a baya yanzu ba ita bace Anti. Ina nufin sauyi a ɓangaren ɗabi'u da halayya, ta samu sake litattafai da dama na addininta. Koyaushe idan na kai mata ziyara sai ta tambayeni ko ina da labarinki. Amma in sha Allahu yanzu kam ina da labarai kwando-kwando da zan kai mata har da na twins."

Ya fadi yana kara sumbayar goshin yaran, Ramlat ta yi dariya. Basu rabu ba sai da ta ba shi kudi da nashi, da kuma na siyayyar abin bukata da ta ce ya yiwa Halima. Ta kara da fadin.

"Ka isarmata da saƙon gaisuwata sosai."

Yusufa da farin ciki ya sa kwalla taramasa, ya yi ta yiwa Ramlat godiya, ita dai ta karbi yaranta ta yi cikin gida.

***

Koda suka koma Adamawa, ba ta ɓoyewa Hussein komai ba, har faɗa ya dinga yi akan don me ta tsaya kula wani ƙaton a waje. Dakyar ta lallaɓashi ta nemi gafara ya hakura ya sauko. A karshe kuma ya ce bai son batun Hajiya Zeenatu. Hakanan ta kyale zancen sai dai ta ci ɗamarar ƙara yinta ko nan gaba ne. Ɓangaren Dada kuwa koda ta ji murmushi ta yi.

"Babu sauran tabon matarnan a zuciyata, ni tuni na mance da ita. Na kuma yafemata, Allah Ya gafartamata."

Ramlat ta amsa da amin cike da jin dadi. Hakanan bangaren AlHassan shi dama mai sauki ne.

Satinsu biyu da dawowa Adamawa suka tattara suka tare a sabon ginin gidansu. Gida ƙerarre flathouse mai shegen kyau. Tsayawa fasaltawa ma ɓata lokaci ne. An ɗan yi liyafa ƙarami wanda yan uwa da abokan arziki suka zo, daman kafin nan sai da aka yi saukar Alkur'ani a gidan. Kowa ya yaba ya kuma sanya albarka. Daga bisani aka watse aka bar Hussein da iyalinsa.

***
BAYAN SHEKARA ƊAYA

Rayuwa mai tsari da kuma daɗi su ke gudanarwa, ƴan biyu sun yi wayo sun yi ɓulɓul abinsu. Duk inda ka gansu sau sun burgeka, Amina ta fi Aminunta ƙiba sosai, sai dai duk ƙibarta idan rikici ya haɗasu yanzun zai kirɓeta. Ita kuwa ta wangale baki da kuka, idan kuwa ka ce za ka ɗau mataki akan Aminun, yanzun za ta hau taremishi tana dukan wanda ke kokarin dukansa. Shiyasa iyayen basu shiga rikicinsu.

Yau ma Ramlatu na zaune jiki duk babu kuzari, gaba daya damuwa ta bayyana karara saman fuskarta, tun safe ta yi test na ciki da pt-strip sakamako ya bata positive, tana jin Aminu na kukan cizon da Amina ta narka mishi a gadon baya, ya kuwa bi ta a guje ya shiga bugu, aikuwa da Ramlat ta fusata ta yi kansu duka biyun ta zane tas. Suka haɗa kai su na kuka ita kuwa ta shige ɗaki don takaicinsu. A haka uban ya shigo ya iskesu. A rikice ya karasa su ma suka faɗa jikinsa, ya rungumesu sosai.

"Ya isa my twins, wa ta taɓa ku?"

Suka hau nuna ɗaki.

"Mamiiii" Amina ta faɗi tana kuka da taɓe pink lips dinta. Ya miƙe ransa a ɓace ya shiga ɗakin. Sai dai ganinta a kwance tana hawaye ya sanyaya jikinsa, duban yaransa ya yi ya kuma dubeta, bai ce komai ba kawai ya kama hannunsu suka bar ɗakin. Sai da ya rarrashe su ya basu kayan cakulet din da ya siyomusu ya ga sai washe baki suke da dariya kafin ya sumbaci kowannensu ya mike zuwa ɗakin.

Gadon ya hau ya shafi gefen fuskarta. Ta dubeshi don tuni ta bar hawayen.

"Sannu da zuwa."

Cike da kulawa ya ce.

"Meke damunki? Kukan me kike?"

Ta mike zaune ta fada kirjinsa.

"Ciki ne da ni."

Ya yi murmushi.

"Shi ne ki ke kuka saboda ba kya son haihuwa da ni ko me?"

Da sauri ta ɗago ta girgiza kai.

"Wallahi aa, kawai dai tausayin kaina naji, duka-duka twins ko shekara biyu ba su cika ba."

Ya ɗaga rigarta ya sumbaci cikin kafin ya ɗago ya sumbaci lips dinta yana murmushi.

"Shi ne me? Tun yaushe nake maki fatan samun cikin? Ina ce har zargin ko kima shan maganin hana ɗaukar ciki nayi maki? Ba halak za ki haifarmin ba? Ramlat ko yara goma za ki haifamin akai-akai, wallahi ina son abina. Ashe dalilin da yasa kika huce akam yarana kenan? To ki shirya dagaske sai na rama musu."

Ta harareshi da wasa, ya ɗan ba ta mintsili kuwa a kafaɗa. Ta rike tana kuka shagwaɓa gami da fadin wash.

Haka ya dinga lallaɓata kafin ya jawo ta jikinsa.

"Akwai goron albishir babba, yana nan tafe nan da wata uku."

Ta yi farr da idanunta.

"Watan Azumi fa kenan."

Ya jinjina kai yana murmushi.

***
BAYAN WATANNI UKU..

Kamar yanda ya yi mata alƙawari sai ga shi ta sha mamaki, ashe dama dalilin yi nata Passport kenan? Tafiya ce Umarah za su yi, don murna ranar haka ta rukunkumeshi tana kuka tana sumbatar duk inda bakinta ya kai. Tare da Dada da su AlHassan da matarsa duka za su wuce. A waya suka yi bankwana da mutan Kano da zummar sai sun dawo za ta kai ziyara.

Azumi nada kwanaki goma sha biyar suka tafi. Sosai sun yi ibada. Anan ne kuma Ramlat ta ƙara zuwar ma da Hussein roƙo akan ya yafewa Hajiya Zeenatu, da murmushi ya rungume matarsa ya sumbaci goshinta.

"Na yafemata, Allah Ya yafemata."

Ramlat ta rungumeshi itama da jin dadi.

Koda suka koma ɗaki, kasancewar ƴan biyu na tare da Dada, wata ibadar suka shiga yi. Bayan komai ya kammala ya zubamata idanu sadda ta fito wanka tana goge jiki, garin na Makkah ya karɓe ta sosai, ga cikinta ya fito. Ta kara mulmulewa ga kumatu da suka yi mata kyau. Ƙarasawa ta yi ta yi amfani da jelar gashinta ta watsamishi ruwa a fuska, ya kai hannu zai riƙota ta ja baya. Girgiza kai ya yi gami da sauke numfashi.

"Wallahi ina sonki."

Yanda ya fadi sai da ya ratsa dukkan sassan jikinta, tsikar jikinta ya mike. Ba ta san sadda ta taka zuwa gareshi ba ya kuwa rungumeta sosai suka lumshe idanu. Ji suke kamar su haɗiyi juna.

"Ina maka son a baki ba zai misalta ba My Hussein, Abban Twins. Na soma sonka daga sadda na soma ganinka."

Ya ɗago ya haɗa fuskokinsu wuri guda, maimakon amsa, sai ya haɗa bakunansu. Can kuma ya ɗago kai ya dubeta.

"Sai dai fa a sake sabon.."

Ba ta bari ya karasa ba ta rufemishi bakin da nata. Gaba daya ta ruɗa shi. Ta sakeshi tana murmushi da maida numfashi.

"Na shirya yin duk abinda zai farantamaka."

Daga haka ya sa hannu ya ƙara kashe fitilun ɗakin ta hanyar amfani da makunnin dake gefen gadon. Salo ya sauya.



ƘARSHE..

_*Alhamdulillah. Ina godiya ga Allah da Ya nunan kammala littafin Karfen Kafa lafiya. Ina kuma godiya gareku masoya masu karfafan gwuiwa da kuma hakuri da juriyar bibiyar labarina duk da irin tsaikon da akan samu. Ina kara ba ku hakuri bisa duk wani kuskure da ku ka ci karo da shi, dan adam ajizi ne. Ina maraba da kofofin gyara ko shawara amma don Allah ba ta hanyar cin fuska ba. Allah Ya kara haɗamu a wani littafin nawa. Na gode kwarai. Son so fisabilillah mutan Rof, Rof2, Karfen Kafa group, both whatsapp & Wattpad fans duka ina godiya. Allah Ya bar zumunci.*_

_*Godiya Ta Musamman gareki BARR FIRDAUSI KABIR, wallahi ina maki son so fisabilillah. Kaunar da kike yimin ba zan ce komai ba gareki tare da sister dinmu, FADILA KABIR. Allah Ya bar zumunci.*_

_*Ummu Abdoul my editer, chairlady of Fikra. Allah Ya saka da khairan, Sis Batool Mamman, Donutfairy da ma dukkan masu bibiyar Karfen Kafa marubuta. Ina maku son so. Allah Ya bar zumunci. Ameen.*_
  

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login