Showing 30001 words to 33000 words out of 230725 words
so shi za ta koma yanzun. Bangaren iyaye sun dauka a karon kanta ta ce ba za ta koma makaranta ba, ita da Aliyun ne kaɗai suka san sirrin rashin komawarta. Duk don ya kuntata mata ya ce ba za ta koma ba.
Tana ji yayyunnata suka fita a dakin sakamakon sallamar su Amarya da sauran mutanen gidan.
***
Aliyu na tsaye a farfajiyar asibitin, shigowarsa kenan. Ko kallonsa ba su yi ba, shi kuwa ya bisu da banzan kallo da harara, yana tafe yana tunanin me ya yi mata? Daki-daki ya tuno dukkan yanda aka yi.
_Yana tangaɗi ya kife saman kujera bacci ya yi awon gaba da shi bayan ya yi magaginsa ya gama. Bai farka ba sai da sanyin asuba ya ratso falon. Cikin mamaki ya tashi gami da dafe kansa dake ɗan sarawa. A hankali ya shiga tariyo abinda ya faru daki-daki, shi dai ya san sun siya kayan maye da abokansa. Anan motar abokinnasa suka sha banda G Baba wanda ke tuƙi yana musu dariyar rashin hakurinsu na ƙarasawa gida. Duk cikinsu shi ɗaya ne ya yi aure banda su da ke kokarin hada takardun Degree. Bai manta sadda suka kawo shi gida ba suka yi gaba, bai kuma yi kasa a gwuiwa ba wajen budurin da suka yi da Muhibbat. Da hanzari ya mike ya nufi hanyar ɗakinta, ba ta nan, banɗaki ma haka. Ya fito da niyyar nufar nashi dakin ya hango mutum kwance a hanyar wurin dinning table. Jiki na rawa ya karasa, ba karamin kaduwa ya yi na ganin jini ba. Kai tsaye ya kira family doctor din su Muhibbat din da ma jama'ar gidan. Ba ɓata lokaci ya mishi bayanin halin da take ciki, sanin tana da ciki ya sanya shi bada umarnin kawo ta asibiti. A gigice ya fita da zummar kwankwasawa makwafcinsa, ya ci sa'a ya fito don zuwa Masallaci. Lurwan ya dubeshi._
_"Lafiya kuwa Aliyu? Meyafaru?"_
_"Muhibbat ba lafiya, taimaka ka kaimu asibiti nan kusa ne don Allah."_
_Ba tare da ɓata lokaci ba suka je asibitin aka karɓeta suka wuce masallacin asibitin suka yi sallah, likita ya tabbatar da fitar cikinta._
"Sai kuma shikenan a dinga yi min kallon mai laifi? Mtsw"
Ya ƙarashe da tsaki don shi dai yasan da ace a hayyacinsa ne ba zai yi wannan gangancin ba. To tunda ta faru ta ƙare kuma shikenan. A ranar aka sallameta bayan an tabbatar babu wata matsala, Mama ta tattara diyarta suka koma gida. Ita kanta ta ji dadi da ta ji Muhibbat na batun a raba aurensu da Aliyun. Ranar da take jira kenan.
***
Da sallama ta shiga gidan, ta yiwa Hajiya sannu da zuwa, ko arzikin kallo ba ta samu ba. Cikin sauri ta fice dakinsu, sai dai tana shiga ta ji an rufe kofar, da hanzari ta waiga. Hajiya ce tsaye da wayarta a hannu, ta ƙaraso tana dubanta.
"Zauna magana zamu yi." Ba musu ta zauna a ƙasa ta sadda kai.
"Banda Hilal, akwai wani da kike kulawa ne?"
Ta kalli uwar sai kuma ta sadda kai. Jin ba za ta yi magana ba yasa Hajiyar kara magana.
"Na tambayeki ba don ban riga da na sani ba, a'a, ina so ne da bakinki inji kin fada. Idan akwai ya sunansa? Kuma tun yaushe ku ke tare?"
Ta runtse ido tana mai jin ko'ina a jikinta na amsar kuwwar Aliyu, gwara kam a yi ta ta ƙare.
"Sunansa Aliyu."I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/RjJi0Rs2J9
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! A madadina da ƴan rof. Ina kara mika sakon gaisuwata ga Husna Yarbaiwa bisa rasuwar mijinta. Allah Ya mishi Rahma, Yasa aljanna makomarsa. Allah Ya raya yaransu.😭😭👏🏿
11)
Wani murmushi na bakin ciki da takaici Hajiya ta yi.
"Shi dai wanda ke karamaki ƙaimi wurin ganin kin bijiremana? Kin saɓa umarninmu? Kin ci amanar mutumin da ya yi dakon jiranki? Kina cikin hayyacinki kuwa?"
Daga kalaman Hajiya ta fahimci cewa r bincike ta mata a wayar. Ta ɗan turɓune fuska yayinda idanunta suka cicciko da kwalla.
"Wallahi Hajiya ina son shi. Kuma shi nake son au..."
Buge bakin da Hajiyar ta mata ne ya dakatar da ita lokaci guda hawaye suka shiga kwaranyomata.
"Kin isa?! Har kin isa kin kai ki bude baki a gabana ki ce wanin Hilal kike so?! Innalillahi wa inna ilaihir ra'ajiun! Na shiga uku ni Rabi'atu! Ashe zan ga wannan rana? Ke Ramlatu, ba ki isa ba! Nace ba ki isa ba don uwarki! Babu wanda zai hana aurennan! Wato kin raina mu? Kin raina mahaifinki! Uban wa ya ce ki ce kina son Hilal ki kuma amince da aurensa?!"
Hajiya ta ci gaba da fada, yi take tana ƙarawa ita kuwa Ramlat sai kuka, duk abinda Hajiyar ke fadi ji take ba abinda zai sa ta fasa son Aliyu. Tashin hankalinta kawai ɓacin ran Hajiyar, banda haka ba wani abu.
Hajiya ta gama faɗan sai kuma ta hau nasiha da nunamata kuskuren yin nema cikin nema da kuma hanyar da ta dauko wanda ba zai ɓille ba. Ita kam shiru kawai ta yi ba don tana aminta ba. Ba don kuma za ta sauya ra'ayi ba, asalima ji take kamar ana bude zuciyarta ana ƙaramata soyayyar Aliyunta.
"Kiyi hakuri Hajiya."
Ta fadi tana riko zaninta ganin ta mike a fusace za ta fice kuma babu niyyar za ta ba ta wayar. Kallonta Hajiyar ta yi, ita ta haifi Ramlat don haka ta san kafiya da taurin kai irinnata zai yi wuya lokaci daya ta saduda. Wannan kaɗai ya tashi hankalinta ganin cewa dagaske yanzun ba ta son Hilal, kuma dole ta aureshi.
"Hakuri daya ki cire yaron daga ranki. Don waya zan ba ki amman sai kin kammala jarrabawa. Ba abinda zai sa a fasa aurenki da Hilal, don haka ki bar ma mafarkin hakan."
Daga nan ta sanya kai ta fice. Kukan Ramlat abu biyu ne, kwace wayarta da kuma batun auren Hilal da Hajiyar ke jaddadamata duk kuwa da cewa ta san ba ta sonsa. Anan ta gane shirun ba zai mata amfani ba, kawaici da kauda kai ba zasu ƙareta da komai ba face tsananin bakin ciki da kuma nadama. Za ta cutar da kanta kamar yanda Aliyu ya faɗi muddin ba za ta fito fili ta nuna ta sauya ra'ayi ba.
Ranar baccinta ya kasance rabi da rabi, duk juyi Aliyu take tunani, sanin da ta yi baccinsa ragagge ne idan bai ji muryarta ba. Sai kusan Asuba sannan bacci ya yi awon gaba da ita.
***
Ranakun da suka biyo bayan su za ta ce ba mai dadi bane sam a wurinta don kuwa Hajiya ta sanyamata takunkumi akan waya. Ba tare da sanin cewa tun a satin da hakan ta faru ta hadu da Aliyu a gidan su Amrah ya kuma cika alƙawarin kawomata karamar waya yanda za su dinga magana a ɓoye ba tare da ta bari a gida an san tana da wayar ba. Nutsuwa da maida hankali ga jarrabawarsu ta Waec da ta yi har suka kammala ya sanya Hajiya ganin kamar ta fara mancewa da babin Aliyun.
Don ta Hilal suna hira a wayar Hajiyar bai kuma damu da jin cewa an kwace wayarta ba. Haka kawai hankalinsa ya kwanta da hakan. Ganin lokacin suna cikin shirin jarrabawar Neco ya sanyashi dauke kafa daga gidansu sai dai ta wayar, shi ɗin ma ba koyaushe ba dalilin yana dan jin nauyin Hajiyar.
***
A gefen Aliyu har sannan Muhibbat ba ta dawo ba don kuwa sosai ta tayar da bore akan ta gama zama da Aliyun. Iyayenta ba wanda bai ba ta goyon baya ba, Abulle ce ta yi tsalle ta dire akan babu mai raba auren. Sai da Muhibbat ta yi wata biyu cif a gida sannan Abulle ta taka har bangaren Justice da zummar maidata. Ta kuwa ce sai dai takardarta.
"Ke Hibbatu, kar fa kiga ina lallaɓaki don ina sonki, ba ki isa ki kashe sunnar ma'aiki ba. Aure abin wasa ne? Ko kin manta yanda kike kwana kina kuka akan son Zakina?"
Hawaye ta share tana kallon Abulle.
"Bana sonsa, yanzu bana kaunarsa, ba zan koma gidansa ba. Ki yi hakuri nidai kawai ya ban takardata."
Nan fa Abulle ta sanya kuka wai Maryama ta zuge ɗiyarta. A karshe ta tara meeting don ganawa da kowa. Anan ma Muhibbat ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta ce ita kam ba za ta koma ba. Da yake Allah bai ƙaddara nisan zama tsakani ba, duk son Abulle da auren hakanan ta hakura aka rabasu. Kowa ya budi baki shaidar Muhibbat yake da hakuri, kunya da kawaici. A ganin iyayen tunda har ta iya karya bille ta furta kalmar saki, akwai dalili babba wanda kuma aka bar shi a sirrinsu tunda ba ta ce uffan ba.
Sakin ya fiye mata duk da irin son da zuciyarta ke yiwa Aliyu, so wanda ta girma da shi kuma ta raineshi. Sai dai an zo gaɓar da ta hakura, ba kuma za ta iya ci gaba da tafiyar ba. A bangaren Aliyu sai da jikinsa ya yi sanyi amman kuma bai wani damu ba ko ba komai zai auri zaɓinsa kuma abar sonsa.
***
Jarrabawar NECO kadai ya ragewa su Ramlat wanda tuni aka soma. Ta rame koyaushe ba ta da aiki sai kuka da tunani. Hankalinta ya gaza kwanciya, matsowar auren da irin shirin da ake yi ya fi komai ɗagamata hankali. Zuwa lokacin Hajiya ta gama fahimtar har sannan ba son Hilal take ba, ba kuma ta ɓoyewa Anti Zulaihat da Rafee'ah ba. Aikuwa ranar da suka zo gidan suka tararmata.
"Kar ma ki fara wannan iskancin! Wallahi kika bari ya je kunnen Abba sai kin gane shayi ruwa ne. Ke ba abin kunya bane ba ma ace kin yaudari Hilal? Ya yi rayuwa a ƙasar waje, ya ga wacce ta fi ki komai da komai bai sa ya ji zai sauya sheƙa ba, sai ke da amana ta miki ƙaranci ko?"
Ta turo baki gami da tsuke gira, kalaman Rafee'ah ba karamin zafi da suka suke yiwa zuciyarta ba. Kai tsaye ta ba ta amsa babu shakkar komai.
"Ai ba ni na sanyawa zuciyata son Aliyu ba, Allah ne Ya haɗamu. Kuma da yardarSa, shi zan aura. Hilal ni na kawoshi na ce ina so yanzu kuma nace bana so bana ra'ayinsa, yanda ba'a yiwa wani cikinku dole ba nima..."
Marin da Anti Zulaihat ta watsamata ya sanya ta yin shiru da dafe kuncinta. Ta mance rabon da fuskarta ta ji mari, jin zafin zuciya da na marin na neman haɗemata ya sa a haukace tana kuka ta ci gaba da magana murya a sama.
"Eh! Eh! Ba zan daina son Aliyu ba! Zan iya kashe kaina muddin ku ka aurar da ni ga Hilal! Bana sonsa! Bana sonsa ko za'a yimin dole?"
Tana gama magana ta fice a guje daga dakin Hajiyar zuwa ɗakinta ta rufe kofar gami da sanya muƙulli ta zube kasa tana kuka. Sa'arta guda Hajiyar na sashin Abba.
Zulaihat da Rafee'ah suka shiga kallon kallo tsakaninsu da tsananin mamaki da kuma sanyin jiki.
"Cabɗi! Akwai aiki!" Fadin Rafee'ah bayan ta farfaɗo daga suman zaunen da ta yi. Ita kuwa Zulaihat salati ta yi ta shiga safa da marwa a tsakar ɗakin kafin ta tsaya ta dubi Rafee'ah mai fama da karamin ciki.
"Wallahi aikin asiri ne. Maza-maza Hajiya ta zo a san abin yi."
"Kamar kin shiga zuciyata wallahi. Ko waye shi kin san bai barta a banza. "
"Meke faruwa? Hayaniyar me ku ke yi?"
Kusan a razane suka juya, Abba ne a gaba sai Hajiya a gefensa. Shakka babu muryar Ramlat ce ta fiddosu.
"Bakomai Abba." Fadin Zulaihat cikin son kwantar da hankalin Uban nasu. Itama Hajiya shiru ta yi sanin abinda ke gudana, ranta na ɓaci don har wani huci take fitarwa, tuni ta gane hayaniyar Ramlat ce, kuma ba akan komai ba sai akan Aliyu. Tana jin Abba na fada akan kar su ƙara.
"Ku mata ne, bai dace a dinga jin muryarku a ɗage haka ba, bana so kar a kara."
Suka amsa da toh kafin ya fice Hajiya ta dubesu kamar ta yi magana sai ta fasa ta bi bayansa.
Ita kuwa Ramlat sai da ta ci kuka mai isarta kafin ta fito, kusan hakan ya zamemata jiki, duk sadda abu ya ɓata ranta, ta fi kaunar ta kulle ɗaki ta yi kuka har ta huce a karon kanta kafin ta fito. A falon ta iskesu gaba daya har Abba, a gefe ga Yaya Munir shima ya zo. Kusan ma a kanta suke tattaunawa, ta ɗan ja burki ganin ba su ganta ba ta dan koma baya. Batun furnitures ake yi sai kayan kicin da za'a damƙa ragamarsu a hannun Zulaihat.
"Komai na Ramlatu ina so ya zama na musamman, kamun kan yarinyar ya fi komai burgeni, ba ta biyewa samarin zamanin nan ba, ba kuma ta tarasu ba barkatai. Hakan ya fi komai kyau, kuma shi ya fi dacewa da dukkan wata ɗiya mace da ta san ciwon kanta. Allah Ya yi mata albarka da ku gaba daya."
Idan ka cire Yaya Munir da ya amsa fuska a sake, su Hajiya kam sun amsa cike da tausayin Abban wanda bai da masaniyar abinda ɗiyarsa ke shukawa.
"Ni kaina Ramlat ta burgeni ta kuma shayar da ni mamaki Abba. Allah Yasa ayi komai lafiya a gama. Ya basu zaman lafiya."
Aka amsa addu'ar Munir da Amin. Ta juya a hankali ta koma dakin, wani sabon kukan ta shiga yi. Ji take inama za ta iya ture dukkan komai ta mika zuciyarta ga Hilal, inama za ta iya wannan kawaicin ta auri Hilal ko don wannan kyakkyawar shaidar Abba da Munir gareta ya bibiyi rayuwarta. Sai dai kuma daga sadda dare ya raba, duniya ta dauki shiru sai kukan karnuka, kunnuwanta suka shiga sauraron kalaman Aliyu masu tsumata da ƙaramata dukkanin kwarin gwuiwa, daga sannan ta sanya ƙafa ta shure tunanin kalaman mahaifinnata da Yaya Munir. Ta ƙara rudewa susucewa akan Aliyu. Ta kuma kudurce da kara daukar mishi alkawarin yanda ya rabu da Muhibbat dominta, haka za ta rabu da Hilal ta aureshi.
Ta shagala iyakar shagala wurin fayyace mishi abinda ya wakana a yau da kuma irin tijarar da ta yi duk a kanss, ba zato ta ji an yaye bargon rufarta gaba daya. A gigice ta mike duk a zatonta A'isha ce, sai dai ganin Hajiya tsaye a kanta ya sanya cikinta ɗurar ruwa. Kafin Hajiya ta ce komai sai da ta ɗaga wayar ta haɗa da jikin bango ai kuwa ya fadi anan ya tarwatse,Ramlat jiki na rawa ta bude baki da zummar magana ta dauketa da mari hagu da dama.
"Waya?! Wayar dare?!! Har wuyanki ya kai wannan kaurin? Ramlatu wace irin jaraba ce wai! Wane irin jahilin so kike yiwa Aliyu? Anya ba asiri ya yi miki ba? Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!"
"Waye shi? Meke faruwa?"
Ba Ramlat ba, hatta da Hajiyar sai da ta ji hantar cikinta ta kaɗa. Abba ne ke tambayar tsaye bakin ƙofa sanye da doguwar jallabiya, basu san adadin lokacin da yake a tsayen ba, sai dai ya ji komai. Ba wani abu da bai shiga kunnensa ba. Jikinsa har rawa, kallo ɗaya za ka ga tsananin ɓacin rai da mamaki shimfiɗe saman fuskarsa, yake ya ƙaraso cikin dakin. Ya ji sunan Aliyu a bakin Hajiya sai dai ya fi kaunar ya gasƙata don tsoro yake ya zamana kunnuwansa ne suka sami matsala. Ya dubi Hajiya ya kuma kai duba ga Ramlat kafin ya dubi wayar dake a tarwatse a ƙasa.
"Dare ya yi, ko mene a bari zuwa safe." Abinda ya iya kokarin furtawa kenan kafin ya fice. Hajiya ta kwashi wayar da ta tarwatse ta dubi diyarta. Ramlat ta kaɗu da ganin hawaye a fuskar Mahaifiyarta, har ta fice ta ja kofar ba ta iya cewa uffan ba. Ta hada kai da gwuiwa ta shiga kuka, kuka iyakar ƙarfinta. Ba za su gane ba, ba kuma zasu fahimta ba, son Aliyu kawai take. So marar algus. Wannan daren ta rasa inda za ta sanya kanta, ta rasa kwanciyar hankali da nutsuwarta, a hankali wani bangare na zuciyar ya shiga yi mata tuni da addu'a ko ta samu mafita. Ko za ta samu Abba ya tausayamata ya bar ta da auren zaɓin ranta.
Shi kuwa Abba kasa bacci ya yi ya zauna gefen gado ya yi shiru. Koda Hajiya ta shigo, ya zaunar da ita a gefensa.
"Rabi'atu kar ki ɓoyen komai, fadamin dukkan halin da diyarki ke ciki."
Ta sunkuyar da kai cike da tsabar tausayinsa, duka-duka yaushe ne ya gama yabonta? Yau kunnuwansa zasu jiyemishi abinda ta san zai wahala idan bai yi mishi shamaki da bacci ba a wannan daren. Duk abinda ta sani game da Aliyu ba abinda ba ta sanarmishi ba.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Shi ne abinda Abban ya furta.
***
Ranar ta Asabar ce misalin ƙarfe tara da mintoci na safe, sai dai sakamakon hadarin da ya soma haduwa a sararin samaniya ya sanya garin yin luf-luf. Iska mai dadi na hurawa mai sanya annashuwa da walwala a zukatan bayin Allah idan ka cire zuƙatan iyalin Alhaji Khalid Mu'azzam da suke jin kamar sun yi rashin wani babban giɓi nasu. A haka Yaya Munir ya shigo gidan ya tarar da su, ya zo adalilin daurin auren da zasu je na ɗan abokin kasuwancin Abban. Ya yi mamakin ganin rayukan iyayen nasa a ɓace, ya kuma yi mamakin ganin taron nasu akan Ramlat ne wacce ta ƙunshe can gefe guda kanta a ƙasa tana kuka, wannan ta sa ya yi shiru yana son jin daga inda matsalar take.
"Ki fadamin waye Aliyu? Tun yaushe ku ka soma mu'amala? A ina kuma ku ke haduwa?"
Ta ɗago kai ta kalli Abban cike da firgici da kuma rashin abin fada don kwata kwata ba ta fahimci inda maganar ta dosa ba. Wace irin haduwa Abban ke nufi? Wace kuma irin mu'amala?
"Aliyu?" Fadin Yaya Munir da mamaki.
Abba ya ɗaga mishi hannu sannan ya dakamata tsawan da ya sa ta kara karfin kuka gami da soma magana.
"Ina rantsuwa da Ubangijin da