Showing 9001 words to 12000 words out of 230725 words

Chapter 4 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1041

yi mata wawan karta. Matsakaicin bakinsa yake motsawa yana magana, ba alamun wasa a fuskarsa. Kunnuwanta suna iya tsinkayar kaɗan daga abinda wani ke fadi cikin mutanen gurin don kuwa shi ba ta samu damar jin nashi sautin ba.

"Tunda har ya ba ka hakuri don Allah ka yi hakuri Yallaɓai, nayi amannar ba shi da abin biyanka wannan ta'asa. Don Allah ka yi hakuri."

Buga bayan motarta da wani ɗan Karota ya yi gami da fadin.

"Hajiya muje mana!" Ya yi sanadin da mutumin kallo inda take, ko da ace akwai gilashi a idanunsa, tabbas ita din ta ga alama yake kallo, da azama ta dauke kai ta ja motarta tana mai jin faɗuwar gaba.

***
Jin sallamar Maminsu ya sa duk suka rugo a guje suka rungumeta har twins din Anti Zulaihat. Tana dariya ta turesu ta zauna a kujera mafi kusa da kofar falon.

"To nikam a kyaleni kar a faɗar da ni don Allah."

"Kuma fa tsaf zasu iya faɗar da ke din, don yanzu ba wani nauyi za kiyi ba."

Cewar Anti Zulaihat, Ramlat na dariya ta dubeta.

"Kai Anti. Happy Birthday my twins." Ta fadi tana ture Affan wanda ke kokarin hawa cinyarta ta kamo hannun Hassana da Hussaina.

"Kai Sis kamar ba za ki zo ba? Kada dai a gidan Hilal kika wuni."

A'isha ta ƙarashe cike da zolaya don ta ji ƙishin-ƙishin an gumamata a gidan daga bakin Hajiya. Harararta ta yi ta kauda kai.

"Kema kinsan za'a rina ai wai an saci zanin mahaukaciya. Gobe ma kya kara."

Itama Anti Zulaihat ta ƙara iza wutar ɓacin ran a zuciyarta.

"Allah Shaida na je domin Hilal, kuma duk abinda mutum ya yi don kansa. Can ta matse musu."

Taɓe baki Anti Zulaihat tayi tana murmushi sai dai ba ta ƙara magana ba ganin mijinta ya shigo. Ramla ta gaidashi. Dr Shareef ya amsa yana kokarin zama.

"Ramlatu manyan ƙasa masu kuɗin gwamnati, ke dai ganinki wuya yake. Yanzun ma nasan yaranki kika biyo."

Ta yi dariya kafin ta amsa Zulaihat ta cafe.

"Aa toh, ashe Abban Khalifa ka gane. Ai karfi da yaji ta maida kanta wata kifin rijiya, yanzu daga Ofis sai gida. Allah dai Ya kyauta."

Murmushi ya yi.

"Aure zamu yi mata mu huta ai. Allah Yasa ma wanda za ta aurar ya hana aikin gaba daya mu ga yanda za ta yi."

Ya ƙarashe cike da barkwanci. An zo gaɓar da ba ta so, wannan ya tilasta mata miƙewa tana duba agogon dake manne a bangon falon.

"Nidai bari mu wuce, Hajiya ba ta kaunar tuƙin dare."

"Ahaf, ai daga an dauko batun aure sai ta sauya akalar, toh ma ga iya gudun ruwanki. Ba inda za ki je."

Fadin Zulaihat. Ita dai ba ta tanka ba sai kallon da ta watsawa A'isha dake dariya sannan ta yi gaba tana yi musu sai da safe.

Har bakin motar Zulaihat da yaranta biyar suka musu rakiya. Ta rankwafo saitin Ramlat.

"Malama akwai muhimmiyar maganar da zamu yi. Idan ma ba ki samu shigowa ba Ni zan shigo gidan."

Ta dan dubeta fuska a yamutse.

"Allah Yasa zancen gizo wannan karon ta bambanta da ta ƙoƙi."

Harararta ta yi.

"Idan ma ta zama daya ya zama dole ki bi, ba ki da zaɓi. Ko ma mene idan muka tashi yinta za ki ji. Sai da safe ku gaidamin tsohuwata."

Daga haka ta kama hannun yaranta suka koma ciki, twins na kuka akan a bar musu su yaran su kwana. Su kansu ba da son ransu ba sai dai makaranta ta share dukkan son ransu.https://my.w.tt/ub8deMQ0g9


🕯️ *ƘARFEN ƘAFA* 🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

04)

***
*ADAMAWA*

_*ALHASSAN AMINU*_

Ya kai tsawon mintuna uku tsaye a falon sai dai nisan da ta yi a tunani bai sa ta hankalta ba. Dattijuwa ce da za ta yi kimanin shekaru sittin a duniya. Ya daure ya kara maimaita sallamar, sai a sannan ta ɗan yi firgigit ta dubeshi da amsa tana kokari kauda kai da share fuska.

"A'a, Biyu? Yaushe ka shigo? Sannu."

Ta furta duk a lokaci guda, ya karasa bayan ya cire bakaken silifas din ƙafarsa ya durkusa gabanta gami da riko hannunta.

"Ya isa, ya isa haka don Allah Dada. Har yaushe za ki ci gaba da damuwa akan abinda ba'a hannunnu yake ba? Addu'armu ita ya fi buƙata. Kiyi hakuri, akwai ciwo, sai dai mun yi imanin komai yana da lokaci."

Ta dubeshi, ta girgiza kwarai ganin yanda ruwan hawaye suka ɓata ɗan farin gilashinsa har suka biyo saman fuskarsa. Hannunta ta zare ta cire mishi gilashin gami da dauke hawayen da tafin hannunta.

"Sau da yawa wasu abubuwan fin ƙarfin zuciyoyinmu suke. Rauninmu ya sa bamu da karfin aiwatar da abubuwa da dama. Nauyinmu yakan rataya a wuyanku. Na daina, na daina Biyu, kar ka kara. Ganin kukanka damuwa zai ƙaramin. Allah Ya magance mana, Ya karkato da hankalin ɗan uwanka gida a duk inda yake rayuwa."

Da murmushi ya amsa da Amin a hankali. Shi yana ji a jikinsa kamar da wuya ace dan uwannasa na raye duk tsawon wannan lokacin. Idan ma yana raye to ya manta da wanzuwarsu a doron ƙasa.

"Ya su Fatima?"
Ta tambaya cikin harshen fulatanci, ya maida mata amsa fuska sake, cikin son kawar da duk wannan damuwar.

"Tana nan, gobe zan kawomaki ita ta yi miki sati ma."

Nan da nan kuwa ta washe haƙora.

"Allah Ya kaimu."

Ya amsa da Amin sadda yake kokarin maida gilashinsa.

"Ina waccan ƴar ƙauyen?"

Murmushi Dada ta yi.

"Ba ta jima da ficewa ba, ta raka Addarku gidan ƙunshi."

Gyada kai ya yi, ya kawar da zancen da batun tafiyar da ta zo mishi zuwa Kano, ya kara da fadin.

"Darakta ya ce na wakilceshi a wani meeting da za'a gudanar."

Ta fadada fara'arta.

"Sai ka karasa ka gaisarmin da Modibbo."

Jin ta ambaci Modibbo ya sanya annurin fuskarsa raguwa.

"Me hakan ke nufi?"

Ya dubeta, shi take duba da son jin abinda zai fito daga bakinsa. Gane hakan ya sanyashi murmushin yaƙe.

"Zan je in Sha Allah Dada."

Ta yi murmushin itama

"Allah Ya yi maku albarka. Ya yayemana damuwarmu."

Ya amsa da Amin cike da tausayinta. Ta sanya rai a abinda har abada ba ya zaton za su ƙara ji ko gani daga gareshi. Fatansa Allah Ya ƙarawa Dadarsu hakuri da dangana.

Washegari kuwa sai da ya biyo ya saukemata Fatima sannan suka kara sallama ta kara jaddada mishi ziyartar Modibbo ya amsa da toh kawai sannan ya kama hanyar Kano.

***
*KANO*
 
  _*Lamiɗo Crescent*_

  Wata hamshaƙiyar mace ce mai kimanin shekaru arba'in da ɗoriya zaune saman ɗaya daga cikin kujerar dinning, an jera kayan maƙulashe kala-kala a gabanta. Waya take tana zabga murmushi ga dukkan alamu tana jin dadin tattaunawar. Hajiya Zeenatu kenan.

  Hankalinta ya kai ga mijinnata wanda ke saukowa daga matattakala sannu-sannu kamar mai ciwo a tafin ƙafa. Kallo ɗaya ya yi mata ya kauda kai. Daidai sadda ya ƙaraso ta cire wayar a kunne bayan sun yi sallama da abokiyar wayarta ta.

  Ta dubeshi kamar ta haɗiye sa'ilin da yake zama saman kujerar dake fuskantarta. Kallo take ƙarewa matashin mijinnata wanda da ace ta yi aure da wuri da kuma ƙuruciya, da ta haifi sa'ansa ko wanda da kaɗan ya rage ya kai shi a girma. Hannunta ta ɗora saman haɓa ta zubamishi idanu shi kuwa banda danna waya ba abinda yake. Yana sanye da wata shadda da aka fi kira da Commisioner fara ƙal, an mishi dinki ba mai hayaniya ba kuma na zamani irin na matasan da ke ji da gayu da kuma kudi. Baƙin agogon fatar da ya ɗora a tsintsiyar hannunsa na hagu shi ya ƙara taimakawa wurin haskaka fatarsa mai cike da gargasa a idanunta. Ta kara kallon halittar ƙira da kuma fuskarsa wanda ke ƙara sanyawa ta ji shi ɗin nata ne ita kaɗai a duniya, don ita aka halittoshi. Har abada babu wata da za ta raɓarmata wannan inuwa da ta ke ganin don ita kaɗai aka ƙagi ni'imarsa. A yanzun da ya zauna nesa da ita, gani take kamar an jonamata mayen ƙarfen da ba zai rayu ba tare da ya kusanci ƙarfen da ke hakilonsa ba. Wannan ya sa ta miƙewa gami da nufar kujerar dake gefensa ta zauna bayan ta ja shi sosai zuwa jikinsa. Wayar hannunsa ta karɓa, wannan yasa shi ɗago kai gami da dubanta, duk da irin saƙon da ta karɓa bai sa ta girgiza ba. A ganinta wannan ba komai bane idan har ita din mace ce mai jarin juyawa, to ko birnin Sin ne za ta iya takawa ta je don cimma kowace manufa.

  "Lafiya?" Ya furta yana ɗan lumshe idanu wanda hakan halittarsa ce, halittar da ta bambanta shi da halittu irinsa. Wanda da kallo ɗaya za ka bambancesu.
Hajiya Zeenatu ta sauke wani ajiyar zuciya don jin so da kaunar matashin mijinnata na ƙara yin amai a cikin zuciyarta.

  "Komai ma anyi Ranka Ya Daɗe, ni wannan fushin ba zai wuce bane? Daga radda aka yi ai ya ci a ce ya wuce kuma an rufe babinsa. Na ba ka hakuri tun a ranar, me zan maka bayan wannan don Allah, uhum?"

Ta ƙarashe cikin sigar jan hankali irin na gogaggun matan boko kuma ƴan shagwaɓa. Nan da nan ya ji tsikar jikinsa ta tashi, kwanakin nan kawai dannewa yake sai dai zuciyarsa na tsananin kaunar su shirya, yanda yake kwana da wuni da tunaninta haka ita kuma ta ɗaure fuska ta sauya mishi akan laifin da ba shi ya gayyato ba.

  "Ya wuce."

Ya furta dakyar bayan ya tattaro nutsuwarsa. Ta ɗago hannunta wanda ya sha adon awarwaro da zobuna na gwal ta ɗora gefen fuskarsa da saje ya zagaye.

  "Ka tabbata?"

Murmushi ya yi ya kalleta gami da dauke kai, bai c komai ba. Dama ta san ba lallai ya ce din ba, mafi yawan lokuta shirun ne amsarsa. Da rawar jiki ta shiga serving dinsa tana jan sa da hira, nan da nan ya sake suka ci abincin suka haura sama sai turaka.

Tana gefen gado zaune tana waya ya fito daga wanka. Ganin yanda take tsuma ya sanyashi maida hankali gareta.
   "Su a banza a wofi!! Ko sun manta mu ne gwamnatin?! Bar ni da su!"
Kiit! Ta kashe wayar.

  "Ofishin haraji zamu je." Abinda kawai ta iya ce mishi kenan itama ta faɗa banɗaki.

*🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem

05)


Safiyar talata da misalin karfe tara da mintuna, ta shiga ma'aikatar Revenue wurin aikinsu. Kai tsaye ofis dinsu ta  wuce bayan ta gaisa da idon sani. Nan da nan ta haɗe fuska ganin wanda ke zaune tare da abokan aikinta suna hira. Mutumin nema yake ya takuramata, sallamarta ya sa duk aka amsa, ya kuwa zubamata ido kamar ya haɗiyeta.

"Kai kam Oga Ahmad ka taki sa'a ga dukkan alamu. Ga wata ga zara."

Ba ta san sadda ta watsawa Halima mai wannan furucin kallo ba, itama Halimar ta yi don zolaya, hakan yasa ta basar da hararar gami da dariya ciki-ciki.
 
"Ai kuwa dai Halima. Gwara da Allah Yasa na yi sammako. Ganin na Ramla wuya yake."

  Ba ta tankawa kowa ba ta zauna saman kujerarta ta maida hankali ga Rabi suna gaisawa. Jin maganar mutum ta yi a gefenta yana fadin.

"Haba Gimbiya Ramla, wannan ɗaurewar fa? Ina fatan dai ba daga ni bane?"

Ko kallo bai isheta ba, to girman ne ya zube warwas!  Ya riga ya tureshi tun radda ya bayyana fitsararsa ƙarara. Ya gama bambamin surutunsa ya fice.

"Ba ki da wayo Ramla, da ni ce da damarki, za ki yi mamaki."

Ta maida duba sosai ga Halima,

"Idan wannan shi ake kira da rashin wayo Halima, to ki jera Ramla a sahun farko. Kema ina roƙamaki shiriya."

Daga haka ta maida kai ga aikinta ba ta saka baki cikin caa da abokan aikin maza da mata suka yi ga Halima ba wacce ranta ke susa da maganganun Ramla. Ta kuma ci alwashin sai ta rama ko ba jima ko ba daɗe.

    ***
Suka yi parking ɓangaren da aka ware don ajiye ababen hawa. Kusan a tare suka fito. Kai tsaye  Hajiya Zeenatu ta fiddo waya ta dannawa Chairman kira. Suka ɗan yi magana sannan suka kashe. Da kwatancensa suka nufi ofishin, ba tare da wani jinkiri ba aka yi musu iso zuwa ciki.
 
  Aliyu Dikko matashin da zai shekara arba'in da ɗoriya ya dubeta fuska a washe.

"Manya gatan wasa, ganinki sai da dalili."

Ta yi dariya tana mai zama sa'ilin da suka zauna.

"Ai ku ne gwamnati, shiyasa dole ku za'a bi ko an ƙi. Ba don wankin hula na neman kai ni dare ba ai ba ka ganni ba."

Ya ƙyaƙyace da dariya gami da maida hankali da matashin da tun gaisuwar da suka yi bai ɗago ba balle ya shiga maganarsu, asalima waya yake sarrafawa.

  "Ah lallai kam. Wannan ƙaninmu ne?"

Tambayar ta sa ya ɗago kai ya watsamasa wani irin kallo kafin ya dubeta fuska a murtuƙe.

"Please mu yi abinda ya kawomu."

Ganin haka ta shiga nutsuwarta ba shiri.
 
"Chairman jama'arka sun min laifi duk da dai da nawa laifin. An ƙullemin shago saboda kuɗin haraji. Wannan abu ba ƙaramin tozarci ne a gareni ba don haka na zo nayi clearing komai."

Ya jinjina kai, zai so ya san wane saurayin da har ya iya jan Hajiya Zeenatu kamar raƙumi da akala sai dai kuma ba fuska. Waya ya ɗauka ya danna kira kai tsaye ga department ɗin da ke kula da wannan ɓangare. Mintuna kaɗan shugaban department din ya hallara. Cike da girmamawa ya gaida Chairman. Ya saurari dukkan jawabinsu kafin su mike su bi bayansa don aiwatar da abinda ya dace.

  "Bismillah ku zauna."

Oga Ɗalhatu ya umarcesu bayan sun isa ofishinsa. Ya kira abokiyar aikinsa da ya ke da tabbacin takardun Hajiya Zeenatu a hannunta suke.

  Ramla na zaune ta dukufa shigar da wasu bayanai kwamfuta, tana yi tana hamma da duban lokaci. Sa'arta ɗaya ba ita ke da alhakin ɗauko yara ba a'a ranakun Litinin zuwa Alhamis bisa yanayin aikinta wanda sau da dama sai huɗu suke tashi. Sai dai a yau ɗin gani take ta gaji ba kaɗan ba, kamar ba za ta iya kai wannan lokacin ba, haka kawai ba ta jin dadin jikinta. Kiran da Oga Ɗalhatu ya yi mata ne ya katse komai da take yunƙurin yi, ta miƙe ɗauke da file din Hajiya Zeenatu har wani abokin aikinta Salihu na faɗin Hajiya ta ji wuta ta kawo kanta suna dariya.

Da sallama ta shiga ciki bayan an amsa mata. Gaba ɗaya sun bata baya, sai Oga Ɗalhatu dake fuskantar ta.

"Yauwa ƙaraso Ramlatu."

Ta shigo sosai, ido hudu ta yi da Hajiya Zeenatu, hakan yasa ta gaisheta da ɗan murmushi. Ita kuwa ta amsa ciki-ciki tana kauda kai. Ba ta ga dalilin da za ta sakarwa kowace ɗiya mace fuska ba muddin tana tare da Mijinnata. Tana kishinsa, kishi mai tsanani. Ramla ta kauda kai da mamakin hali irin nata, sam ba ta ko kalli mutumin da suke tare ba balle ta maida hankali gurin gaidashi.

  Bayanin Oganta take sauraro kafin ta karkata ga Hajiya Zeenatu ta fara yi mata bayanin duk abinda ya dace ta yi kuma ta biya cikin kwarewa da sanin makamar aiki.

  Ya ɗago kadan ya kalleta, aka ci sa'a itama idonta ya sauka a kansa sadda ta ɗan rausaya ido duk cikin bayani. Kirjinta ya harba, ina za ta mance fuskar da tun kallon farko ya kasa ɓacemata? Shi ne, shi dai da ta yiwa ɓarnar dubunnai ya yi mata afuwa. Ya haɗe cikin maroon voyel sai hula da ta hau da kayan. Ɓata lokaci ne ka tsaya siffanta tsatsar kyan da Allah Ya mishi. Gareshi kuwa, kallo ɗaya kwaƙƙwara ya mata sai ya ɗauke kai.

"Aikinki za ki yi ko kuwa kallon mazan wasu?!"

Ta ji kalaman Hajiya Zeenatu tsakar kanta, sai sannan ta ankara da tafiyar tsutsar da kalamanta suka soma yayin furtawa sakamakon kallon sanin da ƙurillar da take yiwa abinda bai shafeta ba. Sai dai zafin kalaman Hajiyar ya sa ta ɗaure fuska. Har aka kammala komai suka tafi ba ta ko ƙara kallonsa ba, balle shi kuma da ba ta gabansa.

"Kinsan Allah mijinta ne, makwaftan wata ƴar uwata ce. Wallahi a ranar farko da na gansu tare sun fito daga gidansu ban yarda ba don har ina cewa ta samarmin lambarsa, ƙarshe na yarda don akan na gaidashi a bakin ƙofa, matarnan har ɗaga hannu ta yi da zummar marina ya riƙe hannun sannan ya ja hannunta suka koma ciki. Tun daga ranar ban ƙara wannan gangancin ba."

Hirar Najaatu da Halima ta tsinkayo daga nasu mazaunin, tsalam ta ji Salihu ya sa baki.

"Ke Hali dubu! Yanzu wannan mijinta ne?"

Tana ji Halima ta hau rantsuwa da fadin kwarai kuwa.

Nan da nan aka hau yin caftarsu, daga mai cewa kuɗi ya gani ya yi wuf da ita sai mai fadin bai yarda ba saboda sam saurayin bai yi kalar babu ba.

Uffan ba ta ce musu ba har lokacin tashi ya yi, ta haɗa tarkacenta ta yiwa kowa sallama ta fice.

Tuƙi take sai dai hirar da akai akan matashin da Hajiyar da aka kira da matarsa ya tsayamata a ƙahon zuciya.

'Me ya kai shi? Da ƙuruciyarsa da komai? Kyakkyawa kuma ɗan gayu irin wanda babu macen da za ta ganshi ba ta ji sonsa ba? Me ya kai shi auren wacce ko ba ta yi sa'ar mahaifiyarsa ba, za ta zo a babbar yayarsa?'

Nan da nan zuciyar ta warwaremata zaren da ta ƙulla ba tare da shan wahala ba.

'So! So ne! Ba abinda ba ya sa wa, kamar yanda ya sa na aikata abinda bansan zan iya ba.'

Ta haɗiyi miyau tunanowa da ranar da ko daga bacci ta farka za ta bada labarinsa.

***
  _*SANADI*_

Bini-bini sai ta kalleta ta ci gaba da tafiya tana murmushi. Ƙarshe Ramla ta gaji ta kai mata duka a baya tana dariya.

"Wai ko ke aka sanyawa ranarnan sai haka!"

Dariyar suka yi gaba ɗaya.

"Wallahi ba ki ji yanda nake murna ba. Ba don na gama tsallena cikin gida ba da yanzun ƙarawa zan yi."

Tsaki da dariya ta yi kawai ba ta ce uffan ba. Sai da suka ƙarasa har titi Ramla ta samu ɗan sahu kafin su yi sallama ta soma ƙoƙarin tsallakawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login