Showing 216001 words to 219000 words out of 230725 words

Chapter 73 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1050

sha takwas kenan, wannan mutumin fa yana wankar mata, yanzu haka ma wani mugun aikin su ka zo ya musu."

Wani ya mike.

"Bari mu je mu ji, idan ma shi suka zo nema mu ba su labari ko Allah zai sa su tsorata da lamarin rayuwa su shiryu."

Ganin haka sauran ma suka mara mishi baya don ba za'a yi babu su ba.

"Hajiya wurin Gora ku ka zo?"

Hajiya Batool da Zeenatu wadanda sun rasa ta ina za su soma, su ka dubi saurayin kusa a tare suka amsa da eh.

"Ayya, ai a daren jiya gobara ta cinye gidansa tas babu abinda ya tsira. Shima ya mutu ɗazunnan aka dawo daga binne abinda aka tsinta na gangar jikinsa. Shima dai yaronsa Salmanu an tsinci gawarsa a filin makarantar Firamare  an kashe shi."

Hajiya Zeenatu sai da numfashinta ya bar motsi na wani lokaci kadan, ta kasa magana sai kawai ta ɗora hannu a kai ta fashe da kuka. Jiki na rawa Hajiya Batool ta ce.

"Shikenan Gora ya mutu dai ku ke nufi?"

Suka bisu da kallo kamar taɓaɓɓu, kusan ma duk kalar ruɗewar da sauran matan da suka zo suka yi, bai kai na wadannan Hajiyoyin ba. Mai magana ɗazu ya matso.

"Eh ya mutu. Duk wani mugun aiki da ya ke shukawa ya kare. Ya koma gidan gaskiya inda zai girbi abinda ya shuka din. Kuma ya kamata ku ji tsoron Allah ku tuba daga tafarkin shaidan tun kan lokacinku ya ƙure. Idan har ba so ku ke yi kuma ku zama tarihi ba, ku tafi a wofi."

Hajiya Batool ba ta ce uffan ba balle Hajiya Zeenatu da ke faman kuka, ashariya kawai ta ke narkawa Gora kamar ta mance da cewar ya mutu. Har dai dakyar Hajiya Batool ta maidata mazaunin kusa da direba ita kuma ta tuƙa motar suka bar layin, yara duk an cika ana binsu da kallo.

Haka suk isa gidan Hajiya Batool hankali a matukar tashe.  Ita kanta Batool din dakiya kawai ta fi Zeenatu, amma ba ta ga laifinta ba don kuwa ta fi ta zazzage bakin aljihu a wannan harkar. Nutsuwa ta gagaresu, Hajiya Zeenatu kawai zama ta yi kamar  kayan wanki a saman kujera tana ci gaba da surfa ruwan bala'i ga Gora da ya jima a gushewa.

"Yanzu shikenan Hussein da Ramlatu haka zan zuba ido ku cigaba da cin amanata?! Shikenan wai hakan na nufin sun yi nasara?! Wallahi ko zan yi yawo tsirara sai na ga bayan Ramlatu da Uwarsa! Sai Hussein ya dawo karkashin ikona. Ba zan dauki wannan dumbin asarar ba! Batool nemomana Maryama a waya! Zuwa Nijar ya kama mu, ya zama dole mu kara gwada aikin Bokansu. Buzaye ne!Za mu yi nasara, za mu yi nasara."

Ta na maganar kamar wacce ta samu taɓin kwakwalwa. Itama Batool ta gane zuwannasu Nijar din kawai shi zai zame musu mafita don haka ba musu ta zaro waya ta dannawa Maryama kira lokaci guda kuma tana sharce gumi. Magana sosai suka yi, ba ta ɓoyemata duka asarorin da ya hau kansu ba. Maryama ta jajanta musu sosai karshe ta ce musu za ta yi musu booking na layin ganin Boka Buzu, kawai dai da zarar sun saka ranar zuwa su fadamata.

"Gobe ma zamu taso jibi mu iso."

Hajiya Batool ta katse ta da gaggawa, ƴar dariya Maryama ta yi kafin ta amsa da toh hadi da musu fatan zuwa lafiya.

Washegari kuwa da sassafe suka kama hanyar Nijar, direba ne ya kaisu. Yardaddan direban Hajiya Batool, Audu. Wannan karon ma sun tattara maƙudan kudade don ita Hajiya Zeenatu ba ta bi ta kan Manajanta ba, ta nemi manyan gwala-gwalanta har biyar ta shiha kasuwa ta siyar. Itama dai Hajiya Batool sai da ta haɗa da siyar da kadara, kowaccensu ta taho cike da burin samun abinda aka je nema. Idanunsu ya rufe, gani suke yi tamkar ga su ga burinsu har ya cika tsabar imanin da suka yi da abinda zai kai su.

Wuraren karfe sha biyun rana da mintoci suka iso Damagaran, anan suka kwana washegari da sassafe suka kama hanyar Niamey.  Sun sha tafiya sosai kafin su isa Niamey, kai tsaye suka kira Maryama a waya. Da kwatance da tambaya suka iso katafaren gidanta wanda ya sha kayan alatu. Ta musu kyakkyawar tarba, ba kamar wancan lokacin ba, wannan karon gidanta ne na kanta ba na Maigidanta ba. Tun bayan rasuwar Mijinta ta siya gida inda ta ke harkar safarar yara zuwa Ƙasar faransa da ma wasu ƙasashen yawon bariki. A yanzun da su ke zaune a falon suna cin abinci bayan sun yi wanka, ba tare da kowaccensu ta damu da kallon gabas ba, ƴan mata ne ke safa da marwa cikin shiga mai ƙayatar da masu iri  halinsu na bin maza. Babu wacce ba ta fito ta gaida baƙin Madame dinsu ba, a karshe Hajiya Zeenatu ta kora ruwan sanyin da aka ajiyemusu ta dubi Maryama.

"Kin tabbatar dai goben babu fashi a zuwanmu wurinsa ko?"

Wani murmushi Maryama ta yi ta dauki tuffa ta gutsira.

"Haba Hajjaju, zan maki ƙarya ne?"

Ganin haka Hajiya Zeenatu ta saki fuska.

"Ba haka nake nufi ba, kin dai ji komai ai daga bakin Batool, banda haka nan da kike ganina duk sadda zan runtse idanu ba abinda nake haskowa sai Mijina tare da waccan karamar karuwar. Gani nake duk kwana daya tamkar shekara ce."

"Ki sa ranki a inuwa, za ki sha mamakin yanda komai zai lalace. Mijinki ya dawo kamar kwai a hannunki sai yanda ki ka yi da shi."

Dariya suka yi har da cafkewa, nan da nan zuciyoyinsu suka ɗan waske sai dai ko ya ya suka tuna asarar da ta hau kansu na miliyoyi sai sun tsinewa Gora. Basu ma batun nemar masa gafara.

Kamar yanda Hajja Maryama ta fadi, hakan ce ta kasance. Washegari bisa jagorancin yaronta sai dai ba wancan na farkon da ya taɓa yi musu rakiya ba, suka rankaya gidan Bokansu Buzu. Koda suka tsaya babu layi sosai, kamar wani layin asibiti haka aka basu kati karami mai dauke da numero (number). Wannan dai ba ɗayan bane, wani sabon Boka ne gagarumi da Maryama ta tabbatar musu cewa aikinsa wane wancan! Daga yanda ma ake yi a wurin ba ka ganin kalar talauci a wurin ka san harka ce ta manya don kowacce ta sha shadda mai dandasheshan kyau sai kuwa daidaiku masu leshi. Su da suka yi shigar atamfa ma sai suka raina tasu kwalliyar. Ba don komai ba sai don ba su zo da tsadaddun ba na gani a faɗa. Hankalinsu na kan aikinsu.

Sai da layi ya iso kansu suka yi zumbur suka miƙe, ganin su na kokarin shiga tare mai tsaron wurin ya dakatar da su. Cikin Hausarsa da ba ta fita sosai ya dakatar da su.

"Ba'a shiga mutum biyu komai kusanci."

Jin haka suka dubi juna jin abin banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Ba su taɓa zuwa an musu iyaka da shiga wurin Boka tare ba, karshe dai ganin mutumin na harararsu ya sa Hajiya Batool ta ja baya.

"Soma shiga bari na yi jira."

Hajiya Zeenatu ta shige ita kuma ta koma ta zauna.

Kwarjini iyakar kwarjini mai bada tsoro shi ta gani a fuskar wanda aka kira da Gamsheƙa, fuskarsa babu ɗigon walwalwa. Tana zama babu tambaya ya nemi sanin sunanta kawai kafin ya soma motsa wasu irin ƙaho da duwatsu da ke cikin wani ƙaton abu kamar tire kamar kuma ba shi ba. Sai da ya gama ya dubeta ya shiga kora jawabi.

"Mijinki da kika yiwa asiri mai suna Husseini, ya dawo hayyacinsa ya sake ki, ya kuma auri wacce a duniya kika tsana, kuma burinki bai wuce na ganin kin hallakata ba. Sai dai kuma ki sani, tuni kin makara don soyayyarsu babu karfin shaiɗancin da zai iya hallakata. Amma ina mai tabbatarmaki juya tunaninsa abu ne mai sauki idan kin aikata duk abinda za mu sanya ki babu musu."

Hajiya Zeenatu wacce idanunta ya rufe nan da nan ta hau gyada kai tamkar ƙadangaruwa.

"Wallahi a shirye nake, ko menene zan aikata idan har burina zai samu cika."

Ya jinjina kai da yin murmushi mai kama da na mai jin kashi.

"Shikenan, a yanzu za sadu da ke ta gaba da kuma baya, daga karshe zan ɗebi abinda ya fita daga jikinki na najasa na haɗamaki wani ƙullin magani wanda za ki tabbatar kin yi yanda ki ka yi, kin fesa a fuskarsa. Sai kuma wani tulu da zan ba ki wanda ke dauke da zucciyar mutum soke da allurai, shi ne mafi hatsari cikin ayyukan da zan maki. Kar ki kusa ki bari ya fashe, muddin ya fashe ki sani komai zai iya faruwa da ke, wannan hukuncin ya rage ga aljanun da suka satomin zucciyar. Don haka kin yarda kin amince za ki iya?"

Hajiya Zeenatu wacce tun sadda ya yi batun saduwa ta baya ta yi turus, kirjinta ya shiga dukan tara-tara, abu ne da ba ta taɓa aikatawa ba, bar ta dai da aikata zina shima a baya ne kafin shigowar jarumi kuma namijin duniya Hussein rayuwarta. Daga shi babu waki namiji da ta ƙara yiwa kallon abin marmari.

'Ki tuna fa, wannan namijin kike kwaɗayin maidoshi rayuwarki yanzu Zeenat, kada ki yi sake. Wannan ce kadai mafita.'

Wani ɓangare na zuciyarta ta mata tuni, nan da nan ta dubi Gamsheƙa da har ya soma gundira da shirunta.

"Na amince. Zan kiyaye dukkan sharuɗa."

Ya miƙe tsaye ya ba ta umarnin ta biyoshi. Daga haka ya nufi uwar ɗaga bayan sakin labulen window, hakan ya sa Maitsaron ya fahimci shugabannasa ya shiga aiki. Wannan yasa bai yi gigin lekawa ba.

Sun kwashe kusan fiye da awa ana abu ɗaya don Gamsheƙa dai ya samu ya da yake so, a karshe ya fito ya bar Hajiya Zeenatu da ɗibar abinda ya umarceta a kwalba sannan ta mike ta fada bandaki ta dauraye jiki ta fito. Koda ta dawo ta iskeshi har sannan ba walwala kamar ba shi ne ya gama kukan mage ba.

Gani ta yi ya haɗamata komai ya miƙamata sannan aka yi bayanin kudade ta biyashi da kudin Ƙasar don tun a Damagaran suka yi chanji.

Koda ta fito mai tsaron ya ba Hajiya Batool damar shiga, ita kuma ya ce ta fice don baa kara zama idan an fito, hakan laifi ne babba. A gaggauce ta fita, yaron Maryama zai karbi tulun hannunta dake cikin kwali ta yi saurin dakatar da shi ta ce ya bar shi. Don ji ta ke idan har ba ita ce ta riƙe ba to fa komai zai iya faruwa. Duk fargaba ta cika zuciyarta.

Tana nan zaune a motar har kusan shudewar awa guda kafin Hajiya Batool ta karaso, ita har da hawayenta ma don ita kadai ta san me ta ke ji a bayanta tun abinda ya gudana tsakaninta da Gamsheƙa. Hajiya Zeenatu ta kalleta kawai don ta san duk kanwar ja ce. Ita ba tulu sai wani kwalba a cikin kwali, ba su ba junansu labari ba sakamakon ba su daya ne a motar ba, haka suka kama hanyar gidan Maryama kowannensu da abinda ya ke saƙawa. Kamar yanda kowanne ke tunanin bala'in da zai sameshi idan har suka yi gangancin ɓata aikinsu.

***
  ADAMAWA

Kwanakin da suka biyo baya, banda soyayya ba abinda Hussein da Ramlat ke gurza, gaba dayansu sun sauya sun kara wani fresh da kyau. Hafsat ba ta bar aron wayar  Ramlat a faƙaice ba tana gaisawa da Tahir. Ita dai Ramlat a tsorace take da hakan sai dai ganin Hussein bai taɓa kamata da laifin ba yasa ta ɗan ji nutsuwa kaɗan.

Ranar da ta cika sati ɗaya cif a garin Adamawa, tana zaune a falonta, dawowarta kenan daga sashin Dada. Hussein ya shigo fuskarsa kaɗai ka kalla za ka san yana cike da tsantsar farin ciki. Hannu kawai ya waremata ba musu ta ƙarasa ta rungumeshi. Ya kuwa ɗagata cak yana juyi da ita, dariya ta yi bayan ya sauketa ƙasa yana nishi da riƙe ƙugu.

"Heart, kin fa ƙara nauyi."

Ta turo baki irin na shagwaɓaɓɓun yara, ya yi murmushi da jan karan hancinta kafin ya rungumota ta baya.

"Albishirinki."

"Goro."

"Alhamdulillah, bisa la'akari da workkng experience dina da kuma credentials, Yayanmu ya samarmin aiki a wani Kamfanin gine-gine. Sosai su ka yaba da komai nawa "

Ta juyo ta ba shi kyakkyawan sumba a kumatu. Ganin ya jefata da wani kallo ta kauda kai tana murmushi don har sannan wani lokacin Hussein dinta kwarjini ya ke mata.

"Congratulation, Allah Yasa a fara a sa'a. Ya kara daukaka."

"Ameen dearest one."

Daga haka ya jawota ya hau yi mata raɗa a kunne. Daidai sadda wayarta ta yi ringing, kasancewar shi ne a kusa, ya ɗauma, ganin baƙuwar lamba sai ya ɗaga kawai, bai kai da sallama ba muryar namiji ya ratsa dodon kunnuwansa.

"Assalamu Alaikum, Adda barka da rana. Taheer ne."

Wani irin kallo ya ke bin Ramlat da shi, Ramlat gabanta ya fadi, ta sani dai a dazun Taheer ya kira ya ce yana son magana da Hafsat zai mata wani albishir, ta ce ya bari idan ta shiga gidan sai ta kira. Shaf ta mance, kuma ba ta samu shiga ba sakamakon wankin undies dinta da ta tsaya yi. Jikinta ya bata akwai matsala. Ba ta gama tantancewa ba sai da ta ga Hussein ya miƙamata wayar ya kuma ƙuramata idanu. Ta karɓa da rawar hannu, gaba daya ta ruɗe, tunda suka yi aure ba ta taɓa ganinsa a wannan yanayin ba kuma ma adalilinta sai yau.




I just published "BABI NA SITTIN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1032619087?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=WqGcOpyrKLCeYJ2pB6S21O2rofM3hfkPhkl8xHn5YliOXRIEhSFgVvGwVllJASGRLQwGf8a%2FEFI9gUseG%2BLsfaQfid671L2Bpg0RFziPc0xIuxqo35SEHCqXV8izbKgB





🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

65)



_*Assalamu alaikum masoyan karfen kafa. Ina ba ku hakuri mai yawa. Na so kwarai na haɗa post din nan da na karshe na aiko gaba daya, sai dai na sani kun yi hakuri iyaka, makaranta da ma sauran abubuwa ke ɓoyeni da hana ni typing. Saboda damuwar da ku ka yi na hakura zan soma posting wannan, daga shi kuma sai BABIN KARSHE in sha Allah. Ku yi hakuri, na tabbata duk wanda aka ba hakuri baa aikatamasa daidai ba. Amma kuyi hakuri. Ina kaunarku fisabilillah.*_




"Hello. Taheer ba..ta..ba ta kusa."

Daga yanayin muryarta ya fahimci akwai matsala, bai kara magana ba ya katse wayar yana mai dana sanin kiranta duk da irin gargadin da ta yi mishi akan muddin ba ita ta nemeshi ba su yi magana da Hafsat, kar ya yi gangancin kiran wayarta.

Hussein juyawa kawai ya yi ya wuce ɗakinsa, ta dage goshi tana kiran sunan Allah, shakka babu laifinta ne ko me ya faru. Ta saɓa umarninsa na hana Hafsat waya, tunda yanzun ba amfani, abinda ya ke gudun, tana yi da wayarta.

Ramlat ta numfasa, tunani take ta bishi ko ta kyaleshi zuwa anjima kaɗan? Sai dai idan ta rabu da shi, tana tsoron kada ya ƙi cin abinci alhalin daga yanayinsa kadai ma ta fahimci ya kwaso yunwar.

Mikewa ta yi tsam ta nufi dakin. Ba ya nan, alamar an kunna ruwa yasa ta fahimci yana banɗakin. Ta nemi wuri gefe gadon ta zauna, ta ɗan jima zaune kafin ya fito ɗaure da tawul a ƙugunsa sai karami a hannun yana share ruwan gashinsa. Bai ko kalleta ba ya yi gaba zuwa gaban madubin, da saurinta ta karasa ta bayansa, ganin abinda ta ke shirin yi, wato rungumoshi, sai kawai ya juyo fuska ba walwala hakan ya dakatar da ita, ta sunkuyar da kai har idanun sun cicciko da kwalla.

"Don Allah ka yi hakuri, ba zan ƙara ba. In sha Allahu an yi na farko da karshe."

Bai ce mata komai ba ya juya ya bar gaban madubin bayan ya gama abinda ya kai shi. Ramlat jikinta duk ya yi sanyi, ta sa hannu ta dauke hawayen da ya gangaro. Shi kuwa gogan, yana kammala shirinsa cikin kananun kaya ya feshe jikinsa da turaruka masu kamshi, ya fice. Ta bi bayansa da sauri ganin ya dauki mukullin mota, da wani irin gudu da ba ta san ta iya ba ta rigashi isa da ƙofar ta tare. Duban tsakar ido suka yiwa juna, kowannensu sai da yanayinsa ya sauya. Ba tare da ta dauke idanunta ba ta ce.

"Don Allah ka saurareni, nayi maka laifi ka yi hakuri ka yafemin."

Kamar ba zai tanka ba sai kuma ya kare tamke fuska.

"Tun yanzu zan yi hukunci akan abu, ki nunan bai maki ba har ma ki goyawa wannan abun baya, wane irin kallo kike son na yi maki? Ke a yanzu sai dai ki ba wani labarin abinda ya gudana tsakaninmu da uban yaronnan, duk wannan ma bai min ciwo ba kamar yanda har kika iya take umarnina. Ko ban hanaki ba, tunda har kika ga na raba ta da wayarta kin san me nake nufi. Ban wuri na wuce."

Maimakon ta matsa sai kawai ta noƙe kafaɗa gami da marairaice fuska, kallonta kawai ya ke yi. Daga yanayinsa ta soma fahimtar ya soma saukowa don haka ta sanya dukkan hannuwanta ta rungumoshi ta kwantar da kai a saman kafaɗarsa.

"Ka yi hakuri, na tuba ba zan ƙara aikata laifi irin wannan ba. Please Haskena."

Shirun da ta ji har ta fidda ran zai sauko, ta soma kokarin janye jikinta ya riƙo ƙugunta dakyau, fuskarsu ya haɗe wuri guda yana bin karan hancinta da kallo kafin ya maido idanunsa cikinnata.

"Kinsan ba na iya fushi da ke ko?"

Ta yi murmushi ta lumshe ido gami da gyaɗa kai duk a lokaci guda, a hankali kuma ya shiga aikamata saƙo mai kashe jiki. Karshe dai Hussein fitar da bai yi ba kenan, dama sanadin bacin ran da yake ciki ne ya tilasta masa son fita. Can ta janye jikinta ganin yanda ta matsu da jikin ƙofa.

"What?" Ya fadi da dusasshiyar muryarsa. A shagwaɓe ta amsa.

"Yunwa."

Ya yi murmushi gami da ɗaga rigarta ya shafi cikin. Lumshe idanu ta yi.

"Allah Yasa mun samu ƙaruwa."

Ta harareshi da wasa kawai ta juya ta bude kofar, ya biyo bayanta don shi kansa yunwar ke cinsa. Sai da suka kammala ba cikinsu hakkinsa kafin kuma ya miƙe ya shiga ɓangaren Dada. Ramlat dai jikinta ya yi sanyi don har tausayin Hafsat ya kama ta, ta tabbatar yau kam Hussein ba zai ɗagamata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login