Showing 60001 words to 63000 words out of 230725 words

Chapter 21 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1059

da hankalin Abbana ba. Zan dawo wataran."

Daga haka ta yi gaba, ba ta kara waiwayowa ba. Kallon gidan ma karyar da zuciyarta zai yi. Tana tafe tana ɗingishi ga hawaye. Duk wanda ya ganta sai ya kalleta, hakan ya sa ta rufe fuskar kasan da hijabi. Haka ta ƙarasa ta wuce gidan Umman Amrah.
  
***
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Oh ni jikar Mamman, yanzu shi Aliyun ne ya miki wannan dukan kamar an aikoshi?"

Fadin hakan da Umma ta yi sai ya kara karyar da zuciyar Ramlat. Ba ta ce komai ba banda kuka. Jiki na rawa Umma ta ɗauki waya ta dannawa Dr Abdullahi kira. Nan ta sanar da shi komai, ya bada umarnin ta taho da ita asibitinsa. Ba shiri Umman ta taimakawa Ramlat suka wuce asibiti. Har sannan Amrah ba ta dawo ba, a bakin Umman ta ke jin, za ta biya gidan kakanninta.

Dr Abdullahi bayan ya sanya an wankewa Ramlat ciwukan da ta ji, ya kirasu ciki ofishinsa.

"Me ya yi zafin da zai miki wannan dukan? Ba shi da hankali ne?! Da wani asibitin ne ba za'a karɓeki ba sai da sa hannun ƴan sanda. Wane irin hauka ne wannan? Ko yana shaye-shaye ne?"

Dr Abdullahi ke fadi cikin tsananin ɓacin rai kai ka ce Amrah aka taɓa. Koda dai dama ba ya bambantasu.

"Dama..dama..ya kwashemin gwala-gwalai ya tafi siyarwa. Shi ne na yi kokarin hanawa, ya hau dukana."

Salati Umma da Dakta suka sanya. Miƙewa tsaye Dakta ya yi yana huci.

"Wannan dole a dauki mataki don ba jaka aka auramishi ba. Jahili ke dukan matarsa, don an auramaki zaɓinki ba yana nufin za'a kyaleki muna ji muna gani a zalunceki ba. Kin fadawa shi Khalid din?"

Ta girgiza kai a tsorace.

"A'a don Allah kar ka fadamishi Baba Dakta saboda hawan jininsa."

Ta basu tausayi, ya ce Umma ta maidata gida sai ya nemi Aliyun sun yi magana. Hakan ya yiwa Ramlat dadi, Baba Dakta ya karɓi lambar Aliyu. Daga nan suka wuce gidan suka bar shi a ofis.

***
Amrah ta sha mamakin ganinta a gidansu, sai dai ta tsorata da yanayinta. Ba ta son yin kuka a gabanta don haka sai ta shige banɗaki da zummar yin wanka ta ɓige da kuka. Kukan tausayin aminiyarta.

Ta fito ta sameta kwance tana kallon wayarta kamar mai jiran wani abu.

"Allah Yasa ba kiran Aliyu kike jira ba."

Ta ajiye wayar ta dubeta gami da gyara kwanciyarta. Murmushi kawai ta yi ba tare da ta tanka ba.

"Dakta ya ce ya kira Aliyun ya ce ya zo yana son ganinsa ya kuma fadamasa kina gidanshi, ya ce toh amma kinga har tara bai zo ba. Ina da tabbacin ba zai zo ba yaron nan."

Umma ke maganar cikin takaici tana duban Ramlatun. Ta kasa cewa uffan banda taunar abinci da take yi kamar mai cin magani.

Amrah ce ta taya Umma takaicin har ta bata labarin abinda ya yi musu a gidan, ita dai ba ta sa baki ba. Karshe Umma ta musu sai da safe ta fita. Ramlat ta ɓallo magani ta kora da ruwa.
Cikin son daukemata hankali daga tunani, Amrah ta yi ta jan ta da hirar abinda aka yi a makaranta yau, har ta fiddo handouts tana yi mata bayanin da za ta gamsu.

***
"Ranka ya dade." Cewar Malam Musa bayan ya rufe ƙyauren gidan. Abba wanda shigowarsa kenan daga masallaci ya dakata gami da dubansa fuska a sake.

"Ya aka yi Malam Musa."

Malam Musa ya ƙaraso ya ɗan russuna kadan.

"A gafarceni Alhaji, farko na so na yi shiru saboda yanayin jikinka, toh kuma kaga bansan halin da shirun nawa zai jawo ba."

Abba ya gyara tsayuwarsa.

"Faɗi kawai Malam Musa. Meyafaru?"

Malam Musa ya sauke ajiyar zuciya.

"Ɗazun da rana ne Ramlatu ta zo fuskarta duk a kumbure, bakinta da goshi na fitar da jini. Yanayin dai babu kyau don naga har ɗingisawa take yi kuma..."

"Ramlatu? Ta zo gidannan? Hatsari ta yi ko me? Meyasa ba ta shigo ba?"

Yanda Abban ya rude sai da ya tsorata Malam Musa, ya yi danasanin furtawa. Wannan yasa cikin rawar murya ya karasa.

"Ta tambayeni kana gida na ce eh sai dai ba ka jin dadi. Hakan yasa ta fasa shiga ciki."

Abba ya dage goshi yana salati.

"Haba Malam Musa, meyasa tun ɗazun ba ka sanar da ni ba?"

Bai saurari kalamansa ba ya koma cikin gidan da sauri.

Ganinsa a hargitse yana kwalawa Hajiya kira, ya kaɗa hanjin cikinta, miƙewa tsaye ta yi ta tarbe shi.

"Abban yara lafiya?"

"Mukullin mota za ki ban, dauko da sauri. Ramlatu ba lafiya. Ta zo gidannan dazu."

Yanda ya rikice itama sai ya ruɗa ta. Ta kama shi ta zaunar

"Don Allah ka samu nutsuwa Abban Yara, In Sha Allah ba abinda zai samu Ramlatu, ka nutsu bari na kawomaka mukullin."

Ya zauna yana ajiyar zuciya akai-akai kamar wanda ya yi gudu.

"Daukomin, yi sauri. Yaron nan kashemin ita zai yi."

Cikin sauri ta shiga ciki bayan ta ba A'isha umarnin kawomishi ruwa. Maimakon ta dauki mukullin, sai ta dau wayarsa ta shiga kokarin kiran Munir. Sai dai kiran Dakta da ya shigo ya katse mata yunkuri. Gani ta yi hakan ma faduwa ce ta zo daidai da zama, ta daga gami da sallama. Bayan sun gaisa ya ce ta ba shi Abba.

"Don Allah Dakta ka lallaɓashi, ya rikice an ce mishi Ramlatu ta zo dazu, so yake ya yi tuƙi..."

"A'a ki ce mishi tana gidana. Bani shi mu yi magana."

Jin haka sai ta mutu da mamaki.

"Kina ina ne Rabi? Ba ki gani bane wai?"

Ganin Abban ya shigo har sannan a rikice, ta sanyamishi wayar a kunne hadi da fadin.

"Dakta ne, ku yi magana."

Nan Dakta ka sanarmishi Ramlat na gidansa, ya fadamishi ya kwantar da hankalinsa ba wani abun tashin hankali bane.


"Dare ya yi, ka zauna don Allah. Gobe da kaina zan kawomaka ita a yi magana."

Abba ya shiga jinjina kai kamar yana ganinsa.

"Shikenan Dakta. Amma fadamin, sakinta ya yi?"

Abban ya ƙarashe zuciyarsa a karye, koda ace bai son Aliyu, a rayuwa ba ya fatan ɗiyarsa ta yi aure ta fito har a dinga ƙirgamata aure. Tausayinsa ya ratsa Dakta.

"Bai saketa ba Alhaji, kar ka damu don Allah, in Sha Allah gobe da safe zamu shigo."

Abba ya yi ta godiya har sai da Dakta ya katse wayar don bai ga bambanci tsakanin Amrah da Ramlat ba.

Ya ɗago ya dubi Hajiya sannan ya zauna saman kujera.

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!Nasan dukanta ya yi, nasan za'a rina. Ramlatu kaddararki kenan, Allah Ya shiryeshi. Ya kawomaki lamarin da sauki."

Hajiya ta amsa da Amin.

***I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/SsZqCOwIcab


🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

19)

Dakin ya yi shiru, ba ka jin komai sai sheshshekar kukan Ramlat. Abba jikinsa ya yi sanyi jin abinda Aliyun ya aikata ga ɗiyarsa. Ga duka ga kuma kwatar dukiyar da ta ke mallakinta a yanzu.

  "Wannan yaron anya zai zo?"

Fadin Dakta wanda ransa ya soma ɓaci da shirgasu da Aliyu ya yi. Abba shima nashi ran a ɓace yake.

"Ka rabu da shi Dakta, idan ma bai zo ba, za ta koma. Kawai dama so nake ya zo din don na gargadeshi akan duka, ba jaka ba ce."

Hajiya dai banda uhm ba abinda ta ce. Ita kuwa uwar gayyar yanzun ma kukan ya kasa fita, ta yi shiru kawai tana kallon kafet da kumburarrun idanunta.

Har aka kwashe awa daya, Dakta ya mike ya yi musu sallama zuwa wurin aikinsa. Shima Abba ya mike ya shirya ya fita.

"Duk abinda ke faruwa ke kika jazawa kanki Ramlatu! Gashinan tun ba'a je ko'ina ba kin fara girbar abinda kika shuka. Kin bude baki kin nunawa namiji ƴan uwanki ba sa sonsa, kin jawowa kanki da kuma iyayenki raini. Kin kafe akan ke lallai sai yaronnan, yanzu ai gashinan auren da ba'a shekara ba an soma jibgar Amarya. Ban kuma san me zan ce ba."

Hajiya ke maganar a zafafe, sai kuma ta miƙa ta bar falon ranta na ƙuna. Ramlat ta yi shiru tana tauna maganar Hajiyar. Tabbas ko me ya faru ita ce silarsa. Wani duka, zagi, cin mutunci da akai mata kafin aure, ba wanda ba ta faɗa wa Aliyu ba. Asalima shawararsa ta ke bi ta aikata duk abinda ta aikata.

'Shi yana zagin nasa ƴan uwan a gabanki banda iyayen Muhibbat da suka ɓata ransa?'

Faɗin wani bangare na zuciyarta, tabbas ta sani, ko batun ƴan uwansa za ta yi, zai ce ba ya so. Ta sharesu tunda shi za ta aura. Ba su damu da shi ba, amman shi kam bai yarda an wulakantasu ba. Sai ita ce wawuya ta saki baki har ya rainamata ƴan uwa?

Sai a sannan ta ji hawayenta sun zubo.

"Na yiwa kaina illa da kaina."

Ta furta a fili, dakyar ta mike ta shige tsohon dakinsu wanda yake mallakin A'isha a yanzu. Kwanciya ta yi tana tunane-tunanenta kafin wahalallen baccin ya kwasheta.

***
  "Tana gidansu!" Ya fadi cike da tsawa ganin Abulle na neman takura mishi da tambaya. Ita kuwa gani ta yi daren jiya da kuma safiyar ranar duk a gurinta ya ci abinci.

"Idan ma abincin naki ne ba kya son na dinga zuwa ina ci ai shikenan, sai na zauna na mutu kowa ma ya huta. Komai Aliyu! Komai Aliyu! Ƴan uwannawa ma ba sona suke ba, da Ni mai arziki ne bibiyar da za'a dinga yimin ba kaɗan ba."

Abulle dai ta kama bakinta ta yi shiru jiki a sanyaye. Ta gane yau ran Zakinnata a ɓace yake. Sai da don kansa ya ci gaba da shan shayin da biredi da kwai sannan ta soma magana a nutse cike da rarrashi.

"Allah Ya huci zuciyar Gadanga ƙusar yaƙi. Haba Zakina, mene abin fushi don nayi tambaya? Abin bai kai nan ba ka ji, ba wanda ba ya sonka, halinka suke cewa sun tsana wannan ma nasan don ba su baka damar kun zauna tare ba ne. Ita kuwa Ramlatu me ya yi mata zafin da har ta tafi gidansu?"

Ransa ya ɗan sosu, idan yace bai yi kewar matarsa ba toh wannan karya ne. Yana son Ramlat, irin son da bai yiwa wata mace ba. Haushin da ta ba shi akan me ba za ta taimaka mishi lokacin babu ba. Yana sane ya ƙi zuwa gurin iyayenta, tsoro yake kar ace ya saketa, shi kuma ko sama da ƙasa za ta haɗe  bai ga wani dan adam din da zai sa ya saki matarsa ba.

"Hutu na ba ta, za ta dawo."

Abinda ya cewa Abulle kenan, ganin za ta matsa ya mike ya mata sallama ya wuce.

A kofar gidan suka yi kiciɓus da Malam mahaifinsa.

"Kai zo nan."

Ya karasa ya ɗan russuna yana cin magani.

"Meke faruwa ne kai da iyalinka? Mahaifinta ya kirani akan yana son ganinka."

Ya kara tamke fuska.

"Ba abinda ya faru, anjima zan je."

Malam ya yi shiru yana dubansa, yana son yaron, halinsa ya tsana. Girgiza kai ya yi. Da alama shima da nashi kuskuren, ko kusa ya watsar da lamarin Aliyun ba ya ta tashi sam. Ya fi bada kulawarsa ga ƙannensa.

"Aliyu ka ji tsoron Allah a lamuranka. Wannan yarinya amana ce ta Allah a hannunka. Duk abinda ka yi mata ka sani Allah sai Ya tambayeka. Har sai yaushe za ka gyara halayyarnan taka ka zamo abin so da kauna ga kowa a dangi? Aliyu ba fa kai muka tsana ba, halayyarka ce ba ma so."

"Toh Malam don ba kwa so ai hannunka dai ba zai ruɓe ka yar ba. Addu'a za ku ci gaba da yi mini."

Takaicinsa ya kama Malam, haka yake. Ba dai a yi magana bai maida martani ba.

"Shikenan addu'a ko? Za mu ci gaba da yi, za kuma mu ɗora akan wanda muke yi. Yanzu dai don Allah ina rokonka, don yanzu ka fi karfin na umarceka, ka je ka taho da matarka. Ka dawo da ita ɗakinta. Duka-duka yaushe aka yi auren? Shikenan za'a soma ƙirgamaka aure?"

Ya shafi ƙeya, ko ba komai yau Malam din ya fadi kalamai masu nuni da sassauci da kuma kwantar da hankali a gareshi. Ba kamar yanda ya saba haduwa da ƴan uwansa su yi mishi caa ba. Sai ya tsinci zuciyarsa da yin sanyi kadan.

"Zan je anjima idan na tashi daga kasuwa."

Murmushi Malam ya yi.

"Ko kaifa, Allah Ya shiryeka. Ya yi maka albarka."

Ya amsa da amin, ya mike ya tafi. Ya manta rabon da maganar arziki ya shiga tsakaninsa da Malam din.

***
Tana daki ta yi jugum tana tunanin yanda ta yi fashin makaranta. A gefe guda Aliyu ne a ran, tunaninsa da kuma so da kauna su ke addabar zuciyarta. Ta yi kewarsa ba kaɗan ba. Don Aliyu wata jarrabawa ce daga Allah wanda ba za ta iya tsallakewa ba. Mutan gidan ba laifi sun sakarmata musamman Abba.

A ranar misalin biyar na yamma ta ji Abba na fadin Aliyu ya zo. Gabanta ya fadi. Ta koma cikin daki ta zauna bakin gado, can kuma sai ga A'isha ta shigo tana kallonta a fisge.

"Ki zo inji Abba."

Ta mike ta zura hijabinta ta fita. A falon saukar baƙi suka ta iskesu. Kallon juna suka yi da Aliyu, kowannensu da abinda yake saƙawa a zuciya. Ta kauda idanunta ganin Abba na hankalce da su.

  Abba ya bata dama ta fadi duk abinda ya faru, Aliyu nan take ya amsa duka laifinsa. Ya kuma ba da hakuri da daukar alkawarin ba zai kara dukanta ba. Ya kuma ce muddin ya samu kasuwa ta koma daidai zai mayarmata da zinarenta. Abba ya tambayeta ko  ta yarda da hakan, nan take ga mamakinsa ta yi na'am. Ya jinjina lamarin, sai kuma ya yi dan murmushi.

"Ai shikenan, Allah Ya kara kauda fitina, Ya kiyaye gaba. Ki je ki shiryo ku wuce."

Ta mike ta koma ciki. Ba jimawa ta fito ta dubi Hajiya dake zaune a falo.

"Hajiya Abba ya ce na bi shi."

Murmushi Hajiya ta yi. A ranta dama tasan Ramlat fushinta na ƙalilan ne.

"Toh, Allah Ya kiyaye gaba."

Ta amsa. Har ta yi gaba Hajiya ta yi magana.

"Ko kina son jar miya sai na bayar a yi miki, gobe a kawo kinga zai taimaka maki saboda karatunki."

Ta rasa kalar farin cikin da za ta yi, ta hau washe hakora.

"Ina so Hajiya. Nagode sosai."

Hajiyar ta murmusa kawai. Ta bi ƴarta ta da kallo a raunane.

'Allah Ka zama gatanta. Ka shaida, na yafewa Ramlatu.' Ta furta a ƙasan ranta.

Falon Abba ta shiga yana zaune shima.

"Abba zan wuce."

Ɗago kai ya yi ya dubeta. Shiru na ƴan mintuna kafin ya nisa.

"Shikenan Ramlatu, Allah Ya tsare gaba. Don Allah ki dinga kiyaye harshenki, miji ya fi gaban wasa. Ya wuce dukkan wani matsayin da kika sani. Aljannarki na gareshi. Ki yi mishi biyayya, ki kuma kasance mai hakuri a rayuwarki. Ramlatu addu'a, karatun Alkur'ani, su ne babban makaman kowane bawa da kike gani. Ki rike su ba da wasa ba. Wannan rayuwar ta sauya, ku dinga nemawa kanku tsari daga sharrin masu sharri ta ko'ina. Musamman matan aure yanzu, wata Alkur'anin ma ba daukarsa take ba balle har ta karanta. Sai ki ga abin kunya mace na cewa ita rabonta da tilawa ma ta mance. Karatun sai na Sallah, wata ma sai a sallar ta kakare idan ta idar ta bude ta duba inda ya kufcemata shikenan ta mayar ta ajiye. Me ya yi zafi? Me muke nema a duniyar? Ramlatu kar ki wasa da Alkur'ani, kar kuma ki yi wasa da ibadarki. Idan na ce ibada har bin mijinki. Kinji?"

Ta gyada kai gami da furta Toh. Da gaskiyar Abba, ita kam tunda ya bata Alkur'ani sai dai ta dauka ta goge ƙurar ta mayar ta ajiye amma ba za ta ce ta bude ta karanta ba. Addu'a ma tana yi amma ba ta dagewa yanda ya kamata.

"Nagode Abba, zan kula In sha Allah. Abba ba zan gaji da neman gafararku ba..."

"Sau nawa zan ce na yafemaki Ramlatu? Toh idan ba ki gaskata ba yau ki gaskata. Wallahi ni Khalid na yafemaki duniya da lahira. Allah Ya miki albarka, Ya baki ikon cinye wannan jarrabawar. Sai hakuri Ramlatu, ko yaya bawa ya yi ba daidai ba, ko ya ya zai ga sakamakon hakan. Ki yi hakuri, ki ƙara hakuri a kowace tafiya. Maza idan suka shiga halin babu ba abinda ba zasu yi ba, zuciyarsu kan tunzura ne nan da nan. Komai mace ta yi sai zuciyar ta ayyanamusu cewa saboda yanzun basu da shi ne. Shima ki dinga tayashi da addu'a, addu'ar mace ga mijinta babu hijabi."

Kuka take, kukan da ta kasa riƙewa. Abba kuwa ban baki yake ba ta gami da nasiha har sai da ya sanyata dariya. A ranta kaunar Abbannasu na kara shiga zuciyarta. Abba mutum ne mai riko da fushi, sai dai tana mamakin sauyawarsa. Dama mutum kan sauya har haka?

Shi kuwa Abba ji yake kamar ya tambayeta Aliyun ya daina shaye-shaye amma sai ya bar wa cikinsa. Addu'ar da ya ce ta shafe komai.

***
  A hanya suna tafe cikin ɗan sahu, don Aliyu bai je da mashin ba. Kowannensu ya yi shiru babu mai kula dan uwansa, asalima kowanne wuri daban ya zauna. Shi yana karshen kofa, itama haka. Tsakiyar suka bari fili ba kowa. Har suka isa gidan ta shige shi kuma ya tsaya sallamar ɗan sahu.
Kallon ko'ina ta hau yi, ya yi kaca-kaca, dama tasan hakan ce za ta faru. Yana daga cikin mazan da basu iya koda tattara kaya ba, balle akai kan shara. Kai tsaye ɗakinta ta faɗa ta shiga banɗaki ta dauro alwalar Magriba jin an soma kiraye-kirayen.

Sai da ta idar kafin ta faɗa wanka, garin ba laifi sanyi ya soma shigowa kadan-kadan. Doguwar rigar bacci ta sanya ta ɗora zani a saman. Yanda ta bar dakin haka ta iskeshi, ta rufe kit ta mayar mazauninsa, ta tattara ko'ina.
Tana kokarin fita falon suka ci karo a bakin ƙofa. Dauke kai ta yi daga cikin nashi shanyayyun idanun masu kashe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login