Showing 180001 words to 183000 words out of 230725 words

Chapter 61 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1049

ba yana aikin karkaɗa mukullin hannunsa, ya dubi Hajiya.

"Ba ta yi mata rauni ba, ni ne dai na raunata Bilkisun, kuma na kora ta gidansu na sake ta."

"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Kana da hankali kuwa? Yanzu kai ba za ka iya hakurin zama da mace ba? Haba Muniru! Ai idan rai ya ɓaci, hankali ke dawo da shi."

Ya saki baki don mamaki, duk irin cin kashin da Bilkisu ke yi amma ana kiran meyasa ya sake ta? Hajiya sosai ta yi faɗa ta ce ta ba shi nan da gobe ya maida aurensa da Bilkisu kafin ransa ya ɓaci. Ganin bai samu goyon baya ba haka ya tattara ya fice sai gidan Baba Dakta. Nan ma dai duk kanwar ja ce, sai dai ɗan saukin da ya samu jin cewar Baba Daktan zai kira Kawu Jamilu su je gidan tare a washegari.

***
Kwanaki ukun da Baba Dakta ya ba Ramlat na cika, bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya ƙara kiranta don jin ta bakinta. Kai tsaye cikin fawwalawa Ubangiji lamarinta ta ba shi damar yi mata zaɓi a wannan karon.

"Idan har shi ka zaɓarmin Baba, na amince zan zauna da shi kuma ba zan ba ku kunya ba."

Baba Dakta sosai ya ji dadin batunta, ya sa mata albarka karshe ya ce duk abinda ya yanke daga baya za ta ji. Da wannan suka ajiye maganar.


"Kar ki yi gaggawar amincewa da Baban Hanif." Amrah ta furta bayan Ramlat fitar Umma daga dakin kasancewar ta dawo gida an sallame su. Ramlat da ta ƙurawa Zayyan idanu, yaron Amrah, ta yi murmushi.

"Ba zan yi ba in sha Allah. Watakila shi ne alherina, na dai bar wa Allah zaɓi, duk abinda Baba ya yanke kaina shi ne daidai. Idan ya amince da aurena da Baban Hanif shikenan."

"Ba ki tunanin Hussein kan iya dawowa watarana?"

Ta hadiyi miyau a kokarinta na danne damuwarta.

"Koda ya dawo mene ne haɗina da shi? An faɗamaki kalmar so ta taɓa shiga tsakaninmu?"

Amrah ta sauke ajiyar zuciya, ta sani da gaskiyar Ramlat. Hussein bai furta yana sonta ba, kuma ko a waya ba ya nemanta.

"Amma sai naga kamar yana sonki."

Ta girgiza kai.

"Tunaninki kenan, yanzu dai a bar zancen ba shi da wani amfani."

"Ai shikenan. Allah Ya yi maki zaɓi na alheri."

Daga haka Amrah ba ta kara tada zancen ba.

***
  BAYAN KWANAKI UKU...

BAZATA.....

Tana kwance a saman doguwar kujera tana karatun wani littafin hausa mai suna KE ALHERI CE a wattpad, dariyar Nene ta ke yi sosai har ɗankwalinta na zamewa. Tana sanye cikin riga da siket ƴan kanti da ya yi mata kyau. Ummi da su Ansar suna farfajiyar gidan su na wasa, sai ji ta yi su na ihun oyoyo Uncle. Ta yi ƙasaƙe tana sauraro can kuma ta yi murmushi don jikinta ya ba ta idam ba Hisham ba toh Hilal. Mikewa zaune ta yi ta gyara zaman ɗan kwalin kanta, ta mike gaba daya da zummar ɗauko mayafi, sai dai sallamar wanda ta ji ya katse dukkan yunƙurinta.

"Wane ne ya zo ne nake jin...Au, Husseini?"

Hajiya dake fitowa daga daki bayan idar da sallah ta ke tambayar, ganin wanda ke tsaye bakin ƙofar suna kallon kallo da Ramlat yasa ta katae tambayar. Ramlat da sauri ta fada daki don ɗauko hijabi, shi kuaa ajiyar zuciya ya sauke ya ƙaraso ya durkusa yana gaida Hajiya da bakinta ya ƙi rufuwa. Gaba daya ya sauya sai ka ce wanda ya fita ƙasar waje, ya ƙara kyau da ƙiba abinsa.

"Dama za ka dawo ɗannan? Ni na ɗauka kuma sai dai mu bi bayanka da kayanka. Nan abokinnaka shima ya zo ya gama jajensa."

Dariya ta ba shi.

"Ayi hakuri Hajiya, na yi laifi ko a waya  ban sanar maku batun zuwana ba."

"Ba komai ai."

Nan kuma aka shiga hirar yaushe gamo, Hajiya ta aiki Ummi kiran Maminta don kawo ruwa. Ta fito cikin dakin  ba ta ko kalli inda yake ba ta shige kicin. Hussein yana nazarinta a hankali. Har ta kawo ruwa ta ajiye da murya ƙasa-ƙasa ya ce.

"Kin fi koyaushe kyau."

Ta ɗan dubeshi, ya watsamata lumsassun idanunsa yana murmushi. Ta kauda kai kirjinta na bugu da sauri-sauri. Zubamishi ta shiga yi a kofi hannu na rawa. Koda ta miƙa maimakon ya karɓa sai ya ɓige da tambayar Hajiya.

"Na yi zaton zan tarar an yi bikin Ramlat."

Ta dube shi ranta na zafi, wato dai yana kara tabbatar mata babu ita a shafin rayuwarsa. Ta mike ta nufi daki sadda Hajiya ta soma ba shi labarin yanda ta kaya da Chairman.

Bai katse ta ba har ta kammala.

"Allah Ya kyauta." Shi ne kadai abinda ya furta. Daga bisani ya sanyo wata hirar daban inda a karshe ya kira Dada a waya video call ya haɗa su suka gaisa, Dada godiya ta shiga yi sosai da sanyawa Ramlat albarka. A karshe ta nemi gaisawa da Ramlatun, Ummi ta karɓi wayar ta shige dakin a guje ta kai wa Ramlat da ke kwance saman gado.

"Mami, ga Dada."

Tana shirin magana sai ganin fuskar Dada ta yi saurin mikewa zaune ta maudo fara'arta. Suka gaisa har ta ba Hafsat ma suka gaisa. Godiya kam ta sha shi, tuni Ummi ta fice daga dakin. Daga bisani suka yi sallama ta katse kiran, dama a wayar Hafsat ne. Hankalinta ya kai ga hotonsa dake saman screen din, ya rungume throw pillow guda a kirjinsa yana kwantar da kai yana murmushi. Sai take ganin kamar ita ya ke yiwa murmushin hakan yasa ta yi saurin jan guntun tsaki gami da hararar wayar kadan kafin ta cillar da zummar sai Ummi ta shigo ta maida mishi.

Kwanciya ta yi har sai da ta ji ƙarar shigowar saƙo a wayarta. Ta jawo ta duba, lambar da ba ta sani ba. Ta bude.

_*"Wayartawa itama raba ni da ita kike son yi yanda ki ka yimin iyaka da HEART?"*_





I just published "BABI NA HAMSIN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1013598891?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=1t7u8q%2B2i2CmVekKWI5wFx%2BLsRJJivM5TtUSxqfucEgX0H3IsSDvgfmbOaj%2FRM2R1oO3SAwAvV7%2FIJ95dbqOXcbxCoIbZ9MIciCSdP0fW4VijXfBR0gyHI42Cn5Za4Rc


🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

54)


Ranta idan ya yi dubu to ya ɓaci, takaici ya sa ta wurgi da wayar gami da hararar wayarsa da ke ajiye ta ja tsaki. Ta rasa gane me Hussein ya ke nufi da ita, ba ta san wane matsayi ya ajiye ta ba. Ta cije lebbanta tana karkaɗa ƙafa daidai sadda Ummi ta faɗo ɗakin a guje.

"Mami, wai inji Uncle.."

Ba ta bari ta ƙarasa ba ta yi saurin yi mata nuni da wayar.

"Maza dauka ga ta can ki miƙa masa."

Ummi wacce ba shi ya aiko ta ba, ta girgiza kai sai dai ba ta fasa ɗaukar wayar ba kazalika ta ci gaba da zancenta.

"Wai ki zo zai tafi."

Harara ta watsawa Ummin.

"Ki ce ba ki ganni ba."

Ummi ta bude baki.

"Mami kin fa hana mu.."

"Kika karasa sai na buge bakinki. Naji ba zan zo ba wuce ki ban wuri."

Rai ba dadi Ummin ta fice, Ramlat ta sauke ajiyar zuciya. Kwanciya ta yi sai dai karatun littafin da ta ke yi ma ya fice a ranta. Ba zato ta ji muryar Hajiya.

"Ramlatu yaushe ki ka sauya? Baƙo ya zo domin ya gaishemu shi ne za ki aikamasa mugun kalamai? Me kike nufi da ba za ki je ba? Wani abun ya haɗa ku ban sani ba?"

Jikinta sai ya yi sanyi, Hajiya ta ba ta umarmin fita, a dole ta mike tana ba ta hakuri sannan ta gyara zaman hijabin ta fice ranta na tururi.

Ba kowa falon sai wata ƙatywar leda a gefe, don haka ta tsaya gami da juyowa da zummar komawa ciki, suka yi kiciɓus da Hajiya. Harararta ta yi.

"Ki je yana waje tare da yara. Tsaraba ya kawomusu. Ki mishi godiya don Dadarsa ta aikomin fura da nono."

"Toh." Ta amsa a ciki-ciki tamkar ba ta so sannan ta fice, ita dai Hajiya bin bayanta da kallo ta yi da mamakin wannan sauyi a fuska da gangar jikinta.

***
Yana zaune a mazaunin direba ƙafarsa ɗaya a waje, alewa ce a hannunsa yana kokarin ɓarewa Affan.  Ta kauda kai daga kallonsa ganin ya ɗago nashi kan, kallonta yake da murmushi a saman fuskarsa. Sai kuma ya miƙawa Affan alawar ya dube su.

"Oya ku shiga ciki."

Dama haka suke jira musamman Ummi da ke rike da ƙatuwar ledar kayan kwalam da ya damƙa mata su je su sha. Ba ta son hararar da uwar ke watsomata wannan ta sa ita ce farkon sheƙawa a guje sauran ma suka mara mata baya.

Ta rasa dalilinsa na korar yaran don haka ta ja numfashi ta furzar. Cikin dakiya ta dubeshi kirjinta na bugu da sauri-sauri.

"Hajiya ta ce na kara miƙa mata godiya. Allah Ya saka da alheri. Mun gode sosai da ɗawainiya."

Ya murmusa yana shafa sumar kai. A hankali ya kai hannu ya bude dayan murfin na motarsa. Dubanta ya yi.

"Dan zagayo ki zauna ki ban aron koda mintuna biyar ne, magana zamu yi."

Ta yi shiru ba ta tanka ba, karshe ma ta daure fuska don ta san wani sabon rainin hankalin ne.

"Please." Ya furta a sanyaye, sai ta ji ba za ta iya jan musu ba don haka ta zagaya ya bita da kallo har ta shigo ta zauna. Shiru ya biyo baya har dai ta ƙosa amma ba ta ce komai ba, shi kuwa yanda ta ke hura hanci ke ba shi mamaki da dariya. Ya ɗan murza karan hancinsa kafin ya soma magana cikin nutsuwa.

"Satina sama da biyu a Adamawa, ba ki samu damar yimin ko gaisuwar juma'a ba, why?"

Ranta ya sosu ainun.

"Ina tunawa  da wadanda suka tuna da ni. Bana sanya ka layin wadanda suka zamemin wajibi na nema balle na gaida."

Ɗif ya yi kamar mutuwa ta ratsa, ta daurewa zuciyarta ba ta kalleshi ba sai dai ta ji wani irin sanyi a zuciyarta ko ba komai ta ɗan huce daga maganar da ya gasamata. Sai ta tsinci kanta da murmusawa. A hankali ta saci kallonsa don ganin yanayinsa, ga mamakinta murmushi sosai yake haƙoransa a waje, ya juyo rabin jikinsa ya tallafi haɓarsa da hannunsa ɗaya yana kallonta. Ta kauda kai.

"Hakan ma na gode sosai. Kin burgeni. Rashin wancan mutumin ne yasa ki ka sauya har ki ke gasan magana ko? Hum, za ki huce."

Ba ta ce uffan ba hakan yasa ya gama shan ƙamshinsa ya ɗora.

"Alhamdulillah, na sadu da iyaye da yan uwana lafiya. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin Talikai. Wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da har abada Hussein ba zai mance da Ramlat ba. Na je Mubi kuma na je Maiduguri. Ban taɓa zaton  zuwan rana makamancin hakan ba, komai ya faru bisa jajircewarki akan dukkan lamurana. Na gode. Ina kara godiya da fatan alheri gareki. Har abada ba zan mance da halaccin da ki ka yi gareni ba. Allah Ya ba ki abinda kike so kuma ya ke sonki."

Ta dubeshi, idanunsa a lumshe har lokacin murmushin ya ke, ganin zai bude yasa ta janye nata idanun kirjinta na bugu. Ta rasa wane irin so ne na Hussein a zuciyarta. Son da ba ta jin ya kai irin wanda ta yiwa ALIYUNTA. Idan Aliyu da dadin kalamai ya rinjayi zuciyarta, ta rasa da me Hussein ya rinjayi nata zuciyar.

"Zan tafi."

Abinda ya ce kenan.

Ta sa ƙafa kawai ta fice ta rufe mishi ƙofar ba ta ce uffan ba kamar yanda bai tanka mata ba har ta yi gaba abinta. Murmushin ya ƙara yi gami da lasar lebbansa. Allah kadai Yasan sirrin da ke cikin zuciyarsa. Ya sauke ajiyar zuciya ya tashi motar ya fice.

***
Hajiya Zeenatu ta rausayar da kai ta ƙara duban Hajiya Batool da ta saki baki tana kallonta,  murmushi ta saki ta ce.

"Kina mamaki ne?"

Hajiya Batool ta furzar.

"Kema ai kin san dole akwai mamaki Zeenatu, shi Hussein din ne ya sauyamaki mota? Har ya ke tambayarki abinda kike da buri a yanzu? Kuma ya amince da ku bar ƙasar babu wata gardama? Anya kuwa Zeenatu ba wani tarkon ya ke shiryamaki ba? Ƴan uwansa kuma sun yarda da zamanku tare? Anya babu lauje cikin naɗi?"

Ɗaure fuska kaɗan Hajiya Zeenatu ta yi.

"Me kike son ki ce? Na fiki sanin Hussein, bai iya yaudara ba. Ko a baya balle kuma a yanzu. Duk isar mutum bai isa ya kawo mishi wargi ba balle ya yi ƙarya dominsa."

Hajiya Batool ta tsaya kawai tana yi mata kallon sakarya.

"Ke ba wannan ne damuwata ba, wasu shegun ƙuraje ne suka fesomin a cinyoyina. Ba ƙaiƙayi balle zafi, su dai gasunan ne kuma suna ɗurar ruwa."

Hajiya Zeenatu ta katse tunanin Batool, kusan ma katse zancen ta yi don ba ta son ji.

"Ya kamata dai ki je asibiti. Tunda dai ko ba komai za ku ci duniyarku da tsinke yanzun."

Suka sa dariya gami da cafkewa duk kuwa da cewar jikin  Hajiya Batool bai gama gasƙata sauyawar Hussein ba.

***
Tsaye suke a farfajiyar katafaren shagon na A&Z, Hisham sai faman shan ice cream yake a roba yayinda Hussein ya maida hankali ga danna waya. Tattaunawa suke yi game da abinda ya ke son shiryawa akan Hajiya Zeenatu. Shi Hisham ma duk haushi ya ke ba shi don haka ya ja guntun tsaki.

"Kai nifa wallahi haushi ka ke ban idan kana zancen matarnan. Ban taɓa zaton ko second ɗaya za ka iya ƙarawa da ita a gida ɗaya ba. Ban zaci za ka ƙara wayar gari ka gan ta kuma ka bar ta a gidanka ba. Da kunnenka ka ji ita Halima na yimin rantsuwar cewa akwai sa hannun matarnan a abinda ta aikata. Na ji, babu kwakkwarar hujja mai ƙarfi da kotu za ta kama Hajiya Zeenatu da shi akan hakan, amma kai kana da hujjojin da za ka iya ɗaukar kowane mataki a kanta ba dole sai hukuma ba. Kafin na furtamaka cewa Zeenatu ce ta sa Nos Khadija aikata kisa, kai ka soma furtawa kuma ka sa na nemi gidan yarinyarnan da kaina na nunamata hoton Zeenatu ta tabbatarmin cewa ita ce. Me ya yi saura? Me kake jira bayan komai ya fito fili."

Hussein ya yi murmushi gami da zaro hankicif a aljihu ya miƙamasa.

"Goge bakinka, ya ɓaci."

Hisham ya harareshi kafin ya warce ya goge ice cream din da ya ɓatamasa gefen baki tsabar masifa.

"Ba na abu kai tsaye, na fi kaunar komai da cikakken hujja Hisham. Sannan ma tsaya, me kake nufi game da Matata? Ina sonta fiye da yanda ta ke sona. Har abada ba na jin akwai wani ko wata da ya isa ya raba ni da Zeenatu. Zan iya yin komai don ganin na sanya ta farin ciki. Kar ka damu da komai, komai da na fada ko kuma ya faru, ba komai bane. Abinda zai faru a gaba shi ne abin kallo. Shi ne abinda zai fi burgeka a lamarin soyayya."

Hisham ya bishi da kallon taɓaɓɓe, sai dai wacce ya gani tsaye bayansa ta jikin gilashin motar Hussein, yasa ya gano dalilin sauya maganar Hussein din. Shigowarta wurin kenan daga gidan Hajiya Batool, a waje ta yi parking ta ajiye motarta don ba jimawa za ta yi ba tana sauri ta koma gida ta girkawa mijinta abinci, wani abun ta mance a ɗazun dole ta dawo ɗauka.

Hussein wanda ya yi kamar bai ganta ba, ya ci gaba da magana.

"Kar ka yarda da maganar mutane, Zeenatu ba za ta taɓa kisa ba balle har ta sanya wani ko wata ya yi yunkurin yi. Na fika saninta. Don haka duk wanda ya faɗamaka Zeenatu ita ce silar shigar Ramlat wannan yanayi, karya ce."

Wani gumi ta ji ya yankomata, ta yi saurin juyamusu baya ta sharce. A hankali ta saita nutsuwarta kafin ta juyo ta tako inda suke tana murmushi.

"Ah, ku na nan?"

Sai a sannan suka yi kamar lokacin suka ganta.

"Sannunki, yaushe ki ka zo?"

Ta maida duba ga Hisham tana jifansa da wani irin kallo kafin ta maida ga Hussein.

"Yanzu na shigo, mantuwa nayi zan dauka. Sannu abokinmu, ya gida?"

Hisham ya sauke ajiyar zuciya, dakyar ya ƙaƙalo murmushi ya jefamata.

"Lafiya kalau Uwargidan Hussein."

Ta gyada kai.

"A gaida mutan gida."

"Za su ji."

Daga haka ta yi gaba, Hisham ya bi bayanta da harara. Murmushi Hussein ya yi.

"Hararar fa?"

Tsaki Hisham ya ja.

"Kai dai ban san sadda ka koyi makirci ba."

Dariya kawai Hussein ya yi, shi kadai ya bar wa cikinsa abinda ya ke shiryawa.

***
"Resigning?" Darakta ya maimaita da mamaki da kuma jin wani irin karyewar zuciya. Cike da ladabi Hussein ya jinjina kai.

"Yes Sir."

Kwata-kwata abin bai mishi dadi ba, samun mutum irin Hussein da ya iya gudanar da kasuwanci da amana da kuma ƙwarewa abu ne mai matuƙar wahala. Kwandala idan ba ta Hussein ba ce ba zai taɓa ci ba kamar yanda duk wani marar gaskiya da ha'inci, nan da nan ya ke ganoshi kuma a take ya yanke masa hukunci kafin ya sanarmasa.

Hussein bai katse tunanin Darakta ba don dama ya san za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya, Darakta Sa'ad mutum ne da ya ke kaunarsa kamar ɗan da ya haifa. Don ma Hussein din bai fiye son shigewa mutane ba, da ya tabbata zumuncinsa da Daraktansa sai ya fi haka.

"Meye uzurinka amma?"

Darakta ya tambaya ransa ba dadi. Murmushi sosai Hussein ya yi yana jinjina wannan kaunar.

"Adamawa zan koma da zama, cikin dangina."

Da mamaki ya ce.

"Dama kai din ɗan Adamawa ne?"

"Eh."

"Ikon Allah."

A karshe dai suka yi magana mai tsawo kafin Darakta ya dakatar da shi zuwa lokacin da zai samu wanda zai maye gurbinsa. Da wannan suka ajiye magana.

***
"Wai nikam Alhaji na rasa gane kanka. Ban san me zai sa zuciyarka ta sauka daga dokin fushin da ka hau ba."

Kawu Modibbo ya daure fuska sosai yana kallon Anti Amarya.

"Me kike son ki ce?"

Anti Amarya ta sauke ajiyar zuciya.

"Ya dace ace zuwa yanzu ka watsar da makaman yaƙinka kamar yanda ƴan uwanka suka watsar. Ya dace ace yanzu gabar da ke tsakaninka da su Dada ya wuce. Ko maƙiyin Dada ya kira ya tayata murnar ganin Hussein amma kai kam na..."

"Ni kike faɗawa maganar banza da wofi?! Ke kinsan waye ni kuwa? Idan har kina so ki tsira da mutuncinki da kuma aurenki, ki yi gaggawar fita a idona! Wannan ne gargadi na karshe da zan maki game da lamarin Amina da iyalinta. A wurinki ki ke ganin komai ya wuce, amma ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login