Showing 159001 words to 162000 words out of 230725 words
Hisham ya dubi AlHassan.
"Dama nayi mamakin ta yanda za'a ce wani abin zai sami Hussein. Ba wai ba za ya taɓa faruwa ba ne, sam aa, sai dai idan har zargina ya tabbata da hannun Hajiya Zeenatu a abinda ya faru ga Ramlat to ba zai taɓa zamtowa an riski Hussein a wurin ba. A irin son da Zeenatu ke yiwa Hussein ba za ta bari a haɗa baki a cutar da shi ko ya ya ba."
"Kai ma kana da labarin Hussein kenan?"
AlHassan ya tambaye shi da gaggawa. Ya gyaɗa kai yana duban agogo.
"Ina da labarin komai, na taƙaice maka Hussein aminina ne, bani da aboki sama da shi a faɗin duniya. Sai dai kuma ya dace ko me zamu yi kada ya wuce gobe, idan ba haka ba za mu rasa damar mu."
"Me kake nufi?"
Tiryan-tiryan Hisham ya ba shi labarin duk abinda ya sani dangane da Hussein. Ya ɗora da faɗin.
"Babu damar a yiwa Hussein zancen ƴan uwansa, ba ya so. Da zarar ka tambaye shi game da asalinsa, kansa zai ɗau zafi ya sauya gaba ɗaya. Ransa kuma idan ya yi dubu toh zai ɓaci. A ranar idan mutum bai yi dagaske ba girmansa zai iya faɗuwa a idanun Hussein."
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Mace ce? Ita ta rabamu da Hussein? "
"Hum, sai addu'a." Hisham ya furta, a ƙasan ransa yana jimamin yanda AlHassan zai ji idan ya gane da sa hannun Kawunsa ciki. Hakan yasa bai faɗamasa ba har sai gaskiya ta yi halinta.
"Ya za'a yi na gan shi yanzu? Bana so su kai ga barin ƙasar."
"Kada ka damu, a gobe da safe in sha Allah zan haɗaka da ɗan uwanka. Za ku ga juna."
Murmushi AlHassan ya yi mai haɗe da dariyar farin ciki, kasa hakuri ya yi sai da ya rungume Hisham yana murna.
"Na gode, Na gode sosai. Allah Ya bar zumunci."
Hisham ya yi dariya gami da dukan kafaɗarsa.
"Ameen. Kar ka samu damuwa. Ka kara godewa Allah, sannan Ramlat. Ba karamin namijin ƙoƙari ta yi akan ɗan uwanka ba."
Murmushi sosai AlHassan ya yi tare da fatan Allah Ya ba ta lafiya.
Hisham ya amsa kafin su yi sallama, shi ya nufi gida, Hisham kuwa ya zarce Police Station don jin abinda ake ciki.
***
_*LAMIƊO CRESCENT*_
Safa da marwa ta ke faman yi a tsakar falon, ta ɗauki waya ya fi a ƙirga. Kiran Halima ta ke jira kamar yanda suka yi alƙawari.Ta kira Hajiya Batool ya fi sau goma don ta ji ko sun yi waya amma shiru ka ke ji, Malam ya ci shirwa. Ta kara kai idanunta kan wayoyin Hussein da ke ajiye saman kujera. Baƙin kishin Ramlat ya ƙara ƙarfi a zuciyarta. Ta gwada amfani da yatsarsa ta buɗe wayar, hakanan ta gwada shiga lambobin Ramlat, HEART da ta gani a rubuce ya sanha ta saki ƙarar da har sai da John suka fito daga kicin zuwa falo. Ta dakamusu tsawar da dole suka koma.
Hajiya Zeenatu ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani malolon abu ya tokaremata maƙoshi. Awanni biyu kenan da ta ba Hussein lemo ya sha wanda ya yi sanadiyyar baccinsa, a wannan lokacin ba abinda ta ke burin ji sai saƙon mutuwar Ramlat. Wayarta ta yi ƙara da wani irin zumuɗi ta duba. Tsaki ta ja ganin lambar Kawu Modibbo, sai da ta kalli ƙafar benen ta tabbatar babu mai saukowa sannan ta amsa a fusace.
"Ina jinka."
"Ya ake ciki?"
Ta safe goshi gami da runtse ido cikin soma gundira da tunani.
"Ni kaina na gaji da tambayar kaina. Abinda ya fi shi ne zan nemi Halima har gidansu na bincika."
"Ga dukkan alamu lamura sun ɓaci."
"Ina tsoron hakan ta kasance."
Ba ta jira cewar Kawu ba ta kashe kiran.
"Zeenat."
Da wani irin ruɗewa ta juyo tana dubansa, yana dafe da goshi a hankali kuma ya shiga saukowa daga matattakalar. Ta yi kokarin saita kanta ta karasa gareshi da murmushin yaƙe.
"Sannu, ka sha bacci."
Hussein ya gifta ya karasa ya zauna saman kujera kansa na ci gaba da sarawa.
"Me ki ka ban na sha?"
Ya tambaya ba tafe da ya kalleta ba. Ta zauna gefensa.
"Ba ka samun bacci yanda ya kamata, ga gargadin likita da ya ce ka dinga samun hutu, shiyasa na sanyamaka maganin bacci a lemu na kashe wayoyinka."
Ya dubeta da idanunsa da har sannan ba ya jin baccin ya sakeshi.
"Haba Zeenat, shi ne dalilin sanyamin maganin bacci? Meyasa haka? Wane irin hutu ne ba na samu? Cuta ba ta Allah ba ce?"
"Hakane, to ka yi hakuri." Ya mike rai a ɓace ya ɗauki wayoyinsa ya haye sama. Ta bishi da kallon munafuki karon farko a rayuwarta.
"Ka ci darajar son da nake maka Husseini, da yau sai ka gane shayi ruwa ne."
Ta furta a hankali yanda ta san ba zai ji ba. Har hango hotonsa da Ramlat ta ke yi a kwayar idanunta. Takaicinta, meyasa ba ta nemi kwararrun ƴan daba sun aiwatar mata da komai ba? Meyasa sai Halima?
Ta ja tsaki tana sharce gumin da fargabar ko Hussein ya ji wayar da ta yi ya haifarmata.
***
"Ita kuma wace ce wannan?" Hisham ya tambaya yana karewa Halima da ke faman sharɓar kuka a bayan cell kallo.
"Sharrin shaiɗan ne wallahi, don Allah don Annabi s.a.w ku yafemin wallahi nayi alƙawari ba zan ƙara ba. Nima san..."
_*"Halima, ki tabbata koda wasa aka samu matsala, kar bakinki ya yi kuskuren ambaton sunan ɗaya daga cikinmu. Ki ce kawai dai kina kishin Ramlatun za ta auri Chairman dinku ne. Ki ka kuskura ki ka yi gangancin tonamana asiri, ki sani rayuwarki ce za ta ƙare a doron ƙasa saboda za mu bar ki ki rayu kuma ki mutu a gidan yari ba tare da mun ɗauki matakin fiddoki ba. Idan kuwa ki ka bar komai a cikinki ki ka faɗi yanda na ce, toh shakka babu ina mai tabbatarmaki ko kwana uku ba za ki yi a hannun ƴan sanda ba za mu sanya a fiddo ki kuma ki bar garin. Idan kunne ya ji....jiki ya tsira."*_
"Kin yi shiru? Me ki ke son ki ce?!"
Tana kuka sosai ta dubi Sajan da ke mata tsawa, a gefensa Hisham ke tsaye yana jiran ji daga bakinta. Girgiza kai ta yi.
"Nima sharrin shaidan ne."
"Ƙarya ki ke! Ba haka ki ka so ki ce ba!Ki fito ki faɗi wanda ya sanya ki!"
Cewar Hisham a ruɗe. Ya ja, itama ta ja. Gwaska tuni an yi asibiti da shi.
Dole haka Hisham ya hakura ya bar case hannunsu sannan ya wuce gida, lokacin sha biyu ta wuce.
***
WASHEGARI...
Da sassafe Hajiya Zeenat ta shirya. Motsinta ne ya tashi Hussein dake bacci. Ya dube ta sadda ta ke kokarin ficewa daga ɗakin.
"Lafiya? Ina zuwa haka da sassafe?"
A firgice ta juyo tana dubansa,ta wayance da yaƙe.
"Am..am..dama Hajiya Batool ta kirani ba lafiya har an kai ta asibiti ma. Shi ne zan je dubiya." Ya gyada kai kawai ya juya ya kara jan bargo, ta sauke ajiyar zuciya ta fice. Ta bar Hussein da tunanin irin nasu auren, wannan wane irin aure ne da mace ke da ikon fita ba tare da iznin miji ba? Anya kuwa hakan zai haifarmusu da ɗa mai ido?
Ya sauke ajiyar zuciya gami da lumshe idanu cikin tunanin laifinsa ne tunda tun farko haka su ke yi. Bai kuma san ya hakan ta faru ba.
Wayarsa ce ta yi ƙara, sunan Hisham ya gani yana murmushi ya ɗaga.
"Kira da safiyar Allah, bashin me na ci?"
"Haba Malam, ina ka shiga ne wai? Jiya na kira duka wayoyinka amma a kashe, lafiya dai ko?"
Hussein ya lumshe ido ya ja guntun tsaki tuno da shirmen Zeenatu.
"Share kawai, lafiya lau ne. Ya aka yi?"
"Ba ka da labarin an kai wa Ramlatu hari?"
Wani irin miƙewa Hussein ya yi gaba ɗayansa har santsin bargon na ƙoƙarin kifar da shi ƙas.
"What?"
Labarin komai Hisham ya ba shi.
"Tana wane asibitin?"
Ya sanarmasa.
"Yanzu zan zo."
Daga nan ya katse kiran bai jira komai ba.
***
MISALIN ƘARFE TAKWAS NA SAFE...
Hawaye ta ke fitarwa yayinda ta ke tariyo komai a kwanyarta. A yanzun da Hajja ke salati da tambayar wa zai aikatamata hakan? Itama a sannan kwakwalwarta ta shiga aikin tunani. Kasancewar ta juyamusu baya ya sa ba wanda ya lura da tashinta. Cikin dare dai ta farka sannan ta ƙara komawa bacci.
"Abin dai da ɗaure kai." Hajiya ta furta tana ƙara riƙe carbin hannunta da ta ke ja.
"Nifa ina zargin matar Hussein wallahi. Tunda..."
"Yi shiru kawai Rafee'ah, zato dai zunubi. Irin haka ne sai ki ga ana zaton wuta a maƙera sai aka same ta a masaƙa."
Rafee'ah ta yi shiru amma dai kam zuciyarta cike take da zarginta. Kwankwasa ƙofar da aka yi ne suka bada iznin shigowa. Hisham ne da AlHassan, suka karasa aka gaisa.
"Kada dai ace har yanzu ba ta farfaɗo ba?" Cewar Hisham.
"Aa, ta farfaɗo cikin dare, har na taimaka ta ɗan zagaya. Sannan ta yi salla da Asuba ma. Baccin ne dai ya ƙara kwasarta."
Ramlat da ke jin bayanin Hajiya sai ta runtse idanu, wani radadi kafaɗarta ke mata, sai dai idan har za ta iya jure wannan adalilin Hussein, idan har zaa iya yaudararta a kafamata tarko a kansa, toh ba karamin so ta ke yi mishi ba. Ta ƙara aminta da hakan.
"Au dama idanunki biyu?" Cewar Rafee'ah wacce ta zagayo domin gyaramata ɗankwalin kanta da ya zame.
Ta dube ta, ganin tana hawaye ta sa hannu ta shiga sharemata.
"Haba Ramlat, meye kuma na kukan tunda Allah Ya riga da ya tsare? Yi shiru don Allah. Ko za ki tashi zaune?"
Ta gyada kai. Da taimakon Rafee'ah ta miƙe zaune ta jingina da filo. Ta gaida Hajja da su Alhassan.
Wayar Hisham ta yi ƙara ya duba, shi kansa AlHassan tunda ya ji batun zuwan ɗan uwansa ya rasa sukuni. Burinsa kawai ya gan shi don ya tabbatar da komai. Aikuwa shi ɗin ne.
"Kana waje? Ok gani nan zuwa."
Yanda Hisham ya miƙe hakanan shima AlHassan ya mara mishi baya. Rike hannunsa ya yi.
"Ka yi hakuri, nan zai shigo, ka jira ya karaso ciki ka ganshi."
Ramlat da kirjinta ya tsananta bugu ta dubi Hisham a hargitse. Nan da nan wasu hawayen suka kwaranyo. Baki na rawa ta ce.
"Hussein..Hussein ne?"
Hisham ya dubeta.
"Shi ne, ku kwantar da hankalinku yanzu zan kawo shi."
AlHassan a dole ya dakata sai dai ya kasa tsayuwa wuri guda, safa da marwa ya shiga yi yana kallon ƙofa. Koda aka tura ƙofar aka shigo. Hisham din ne a gaba, a bayansa kuma Hussein. Kamar wani gunki haka AlHassan ya ja burki yana kallonsa ƙurr.
"Hussein...?" Ya furta, furucin da ya ja hankalin Hussein dake sanye da Maroon shadda da hula, ya dubeshi.
I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/IRx4QB4kMcb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
48)
Kallonsa yake yi sosai kirjinsa na bugawa da sauri. Ramlat ta runtse idanu tana mai addu'ar komai ya tafi daidai.
Da wani irin sassarfa AlHassan ya tako ya rungume Hussein kawai sai ya soma kuka.
"Hussein." Ya ƙara kiran sunansa karo na biyu, Hussein ya yi ɗif sai hawaye da ke zuba saman fuskarsa. Ji ya yi kamar ana saramasa guduma a tsakiyar kansa, a hankali ya soma ganin dishi-dishi, lokaci guda idanunsa suka juye yayinda baƙin kwayar idanun ta ɓace ɓat. Hisham da ke tsaye a baya shi ya lura da sauri ya karasa ya rike Hussein. Jikinsa wani irin kakkarwa ya ke yi.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!"
Cewa Hisham yana rike hannun Hussein, jin haka AlHassan ya ɗago wanda saura kiris Hussein din ya zube don kuwa da jikinsa ya samu madafa.
"Riƙe shi sosai." Cewar Hisham, suka taimaka suka fitar da shi sai wurin likita. Ramlat tuni ta miƙe tsaye. Su kansu su Hajiya sun rude. Ganin tana kokarin ficewa yasa Rafee'ah riƙo ta.
"Ina za ki je? Ba ki ganin halin da ki ke ciki? Idan kin je lafiya za ki ba shi?"
Ta girgiza kai tana hawaye, ta bude baki sai dai ta rasa me za ta ce don haka ta koma ta zauna. Hajiya ce ya fidda waya don ta kira Malam ta sanarmasa halin da ake ciki. Nan take ya ce maza ta aiko a karɓi ruwan da ya haɗa da ganyen magarya ya yi addu'o'in karyewar sihiri. Ba shiri ta yiwa direbanta waya ta ce ya biya Yakasai ya karɓo mata saƙo.
***
Duk iyakar awon da likitocin su ka yi ba su gano komai game da ciwon Hussein ba. Don haka koda suka samu ya bar jijjigar, idanun suka dawo daidai sai Likitan da ya karɓi Hussein ya fito wurin su AlHassan. Suka tarbe shi da gaggawa.
"Ku yi hakuri.."
"Mutuwa ya yi?" Faɗin AlHassan a gigice, girgiza kai Likitan ya yi yana mai riƙe hannunsa.
"Ko kusa ba haka ba ne, asalima yanzu mun samu komai ya daidaita. Sai dai hakikanin gaskiya ba za mu ce ga abinda ya jawomasa hakan ba, yanzu dai halin da ake ciki, dole zamu yi mishi tests don mu gano ainahin inda matsalar take."
Suka jinjina kai.
"Ba damuwa Dakta. Allah Ya ba shi lafiya." Cewar Hisham da hankalinsa ya ɗan kwanta.
Bayan wucewar Dakta ya dafa kafaɗar AlHassan wanda ya cire hular kansa tsabar gumin da fargaba ta haifarmasa.
"Kada ka damu ɗan uwa, na fadamaka dama duk sadda maganar dangi ko ƴan uwa ta haɗa mu da Hussein ya kan shiga wani irin hali, ina kuma ga yau ya yi ido huɗu da ɗan uwansa?"
"Hakane, sai nake ganin kamar ba na asibiti ba ne."
AlHassan ya faɗi bayan kai karshen nazarinsa.
"Hisham, ya jikinnasa?"
Suka juya, Rafee'ah ce. Ta karaso suka yi mata bayani.
"Allah Ya ba shi lafiya. Kada ku damu, Hajiya ta aika a karɓo ruwan ganyen magarya mai addu'o'in karya sihiri, da yardar Allah komai zai daidaita."
AlHassan ya sauke ajiyar zuciya yana ɗan murmushin jin dadi da wani irin kaunar zuri'ar da ke kara mamaye zuciyarsa.
"Na gode kwarai, Allah Ya sakamaku da alheri. Allah Ya bar zumunci."
Ta yi dariya kadan.
"Ameen. Ai yiwa kai ne. Bari na koma, dama Hajiya ce ta ce na sanarmaku sannan na gano halin da yake ciki don marar lafiyarmu ta tashi hankalinta sai kuka ta ke yi."
Murmushi AlHassan ya yi yana mai hasashen wani abu da tun a jiya ya yi zaman dirshan a kwakwalwarsa.
***
TA FARU TA ƘARE...
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Halimar aka kama?!"
Hajiya Zeenatu ta faɗi tana tsaye a bakin ƙofar gidan Kakar Halima wacce ke rike da ita. Ƙanin Halima uwa daya uba ɗaya wanda daga ita sai shi, su uku iyayensu suka haifa kafin rasuwarsu, dayayar Halima, Halima sai Yusufa. Kakarsu ta karɓi riƙo. Yusufan ya share hawaye yana duban Hajiya Zeenatu.
"Wallahi ranki ya daɗe, ɗazu aka yi mana waya, naje har ofishin ƴan sandan na sami Aunty Halima, wai dumu-dumu aka kama ta da bindiga za ta yi kisa. Wannan abu ne da ko a mafarki ba mu zaci faruwarsa ba. Su biyu aka kama, shi ɗayan ko Gwaska ko wa? Yana asibiti. Yanzu Kaka na kwance ba lafiya tun da ta ji halin da ake ciki."
Hajiya Zeenatu wacce ta yi mutuwar tsaye, ta yi sauri ta dawo hayyacinta. Baki na rawa ta ce.
"Ta..ta..faɗi wadanda suka sanya ta?"
Kallon da Yusufa ya yi mata na nazari sai da ya sa ta sakin ƙaramar tusa mai haɗe da fitsari ba shiri. Ya girgiza kai.
"Abin kunya ne ace saboda ɗa namiji za ta aikata hakan. Kishi ne kawai don uban gidansu na aiki zai auri abokiyar aikinta Ramlat. Haka ta sanarmin."
Ya karashe da wani irin jin kunya. Ajiyar zuciya Hajiya Zeenatu ta sauke ta juya za ta shige mota.
"Amm..Hajiya, na ce sai dai ban sanki ba. Kema wurin aikinta ki ke ne?"
Ta juyo.
"Eh, tare muke aiki." Tana kaiwa nan ta juya da sauri ta faɗa mota, ta ja. Kiyayewar Ubangiji ce kawai ta isar da ita gidan Hajiya Batool. Itama nan ta iske ta su na dambe da surukarta. Dakyar ta raba su. Ɗan Hajiya Batool ba ya nan ya yi tafiya Dubai, shi ne surikar ta zo gidan kwana.
"Haba Hajiya, me ya yi maki zafi za ki tsaya dambe da suruka? Ke kuma don ba ki da kunya wannan ba uwar mijinki ba ce?"
Fareeda wacce ke tsaye tana huci ta narkawa Hajiya Zeenatu uwar harara kafin ta saki dariya gami da tafa hannu.
"Ahayye! Ai fa da yake daga ke har ita jirgi ɗaya ya kwaso ku dole ne ki ga laifina! Tsoffin banza da ba su riƙe girmansu ba ai ba zan ji kunyar taka su son rai ba. Kin tauye hakkin yaro kin danne kina zaune da shi! Ko an fadamaki bani da labarin mijinki? Kina kai min uwar miji yawon bin bokaye don mijina ya ƙara aure ko? To wallahi karyar ku domin tun kan a haifi uwar mai sabulu balbela ke da farin kai. Don haka idan ku na son na lulluɓe dukkan sirrikanku to ku tabbatar an fasa batun auren Mijina da kowace shegiyar kucaka. Idan kunne ya ji..." Ta ƙarashe da rike kunne kafin ta wuce tana dariya ta bar su baki galala. Bayan shigewarta ɗaki Batool ta yi gaba ta haye sama, Hajiya Zeenatu ta bi ta a baya. Su na shiga ɗaki suka sa mukulli.
"Batool akwai matsala!"
Hajiya Batool da ta zauna rike da ƙugu tana ambaton wash sakamakon cizon da ta sha a wurin Fareeda. Ta amsa wa Hajiya Zeenatu kamar za ta yi kuka.
"Matsala nima cikinsa kika tarar da ni Zeenatu. Kamar Gora yaudararmu ya ke yi yana cin dukiya a ɓagas. Ni na rasa kan wadannan lamuran."
Hajiya Zeenatu ta yarfar da jaka da mayafi, da sauri ta faɗa banɗaki. Can kuma ta fito ta zauna tana sharce gumi. Ta kora dukkan bayani ga Hajiya Batool gaba dayanta a rude.
"Ya zan yi ne Batool? Ga Visa ta yi wuya an ce mu kara hakuri zuwa sati na sama, ga wannan lamari na neman kwaɓemin? Ba mu ga ta zama ba Batool, ta inda aka hau dai ta nan ake sauka idan ba haka ba mai afkuwa za ta afku. Ba ni da tabbacin Halima ba za ta tonamana asiri ba. Ban san iyakar lokacin da za ta riƙe sirrinmu matsayin sirri ba. Wannan fa barazana ce garemu. Tashi za ki yi mu kama ƙafa